ya ya dai Suhaila me ye ya faru na ga kamar kin yi kuka? Na
soma gaya mishi wasu hawayen suna zuba, cito wayarshi ya yi ya
danna lambobin Yaya Ashiru ya ya jikin Inna abinda ya fara tambaya kenan ya saurari bayanin da ake mishi na dan lokaci sai ya ce to
amma ko za a kawota nan National Hospital mu gani in ya so in bamu gano ainihin damuwar ba, in za a tafi da itaň sai a fita ya sake
sauraronshi sai n aji ya ce nan da awa daya dai za ku išo kenan? Tо sai kun zo, ya kalleni bari in taresu Suhaila sun kusa isowa, na ce to
cikin sauri ya juya ya, ya tafi muna gida muna suararon isowar su shiru, tun tara ya kamata su iso har sha biyu babu su babu dalilinsu n
ayi waya wajen sa'a ta ce mun tun asuba suka baro kuma itama ta
27
nemi Yaya Ashiru a waya ta ji layinshi a rufe nace wayyo Sa'a rmck
faruwa ne, kowa ya rufc la yi? Muna gida hankalinmu a tashe wajea karfe biyar na yamma sai ga Yaya Ahmad ina ganinshi
rungumeshi ina kuka tare da tambayar shi abinda ke faruwaya ce kwantar da hankalinki Suhaila tun taran safe muka iso National Hospital Dr Hakeem da wani likita jarfata sun yi wa Inna aiki kuma ALhamdulillahi ta farfado tana kuma cikin hankalinta yanzu k
shirya kawai mu je ku ganta muka dauko kulolin da zuba abinci dauki Suhaila anti Hama ta bar Ahmad wurin mai aikinta muka nuj
asibiti Yaya Bashir da Yaya Ashiru suna tsaye kan Inna yayin da
teacher yake ta faman gwaje-gwajen Inna tana kwance idonta biy
ina shiga Yaya Bashir ya ce mun kama bakinki ki yi shiru in kika yi
muna kuka yanzu zansa a koma dake gida likita ya gama ya yi rubuce
rubucenshi ya mayar da folder ya sagaleta ya cewa yaya Bashir zani gida yanzu zasu kawo magungunan da za a rinka bata mun gode Dr
abinda Yaya Bashir ya ce mishi kenan, yaya Ashiru ya bishi don yi
mishi rakiya, Anti Hama ta gaida Inna nima na matsa kusa da ita, ina
mata sannu tare da zare ido wai in ga inda aka yankata lokacin aikin
ban gani ba na tambayeta ina ak ayi aikin? Sai Yaya Ahmad ya cе
mun an yi amfani da na'ura mai kwakwalwane Suhaila aka cire mata
ciwon ba tare da an yanka jikinta ba ni kám duk bayanin da Yaya
Ahmad ya yi mun ban fahimci komai ba, illa iyaka dai na gode Allah
inna ta dawo cikin hayyacinta Yaya Ashiru ya dawo sai n aji wayar
dake cikinjakata tana kara na fiddota a hankali na ce hello teacher
Hakeem ya ce dadina dake ko kara baki daita wai ba zaki yi mun
rakiya ba sai na roka a gaban su Yaya Bashir to ban tafi ba ina jiran
ki kina fitowa ki yi kwana ta dama ina jiranki na ce, to a hankali na
fito ina zuwa inda ya gaya mun na ganshi a tsaye kayan llikita ya
kar6i teacher gashi komai ya saka sai ya kara mishi kwarjininshi
wani office ya bude muka shiga girman office din da kyan tsarinshi
ba kadan banc a nan ma ya rubuta kalmomin kamar haka, when
clambing the lada of succèss behind to those you met on your wey up
you may met tem again on your dawn' a kasa sai ya sanya sunanshi
cikin bracket, Hakeem Lamido. Ma'ana duk lokacin da kake taka
tsanin da ke kai ka sama ga cin nasara yi kokari ka aikata alheri ga
mutanen da kake wuccwa a hanya ta yiwu ka sake gamuwa dasu
28
yayin saukowarka kasa, na zauna muna fuskantar juna tarc da tunanin
hikima irin ta teacher a ko ina yake bai rabuwa da rubuta kalmomi na
yiwa kai nasiha,ya hada hannayenshi wuri daya ya dogaresu kan
tebur din dake gabanshi yana kallona cikin murmushi ya ce kiranki
na yi ki yi mun rakiya zuwa gida, na zaro ido ina kallonshi na ce haba
teacher me ye yasa kake mun irin wadannan maganganun ko kuwa
kana nufin, ya yi maza ya katseni yi hakuri Suhaila bana nufin komai
gani kawai na yi tunda zan je ne in dawo idan kin rakanin ba laifi bane, na ce to laifine ya ce na taba shi kenan ko? Na ce e, ya ce to
dazu muna magana da Ahmad sai ya ce wai daurin aurenshi saura bai
fi wata daya ba, na ce ko in turo iyayena ne Suhaila ko zai yarda a
hada da namu? Na ce kar ka wahalar da su ga nisa Yaya Bashir ba zai
yarda ba, ya ce ina mishi tsayuwar dare ban ni kawai in jarraba na ce
kama dai bar wannan maganar sai inna ta samu sauki ya ce to.
Kwana biyu kawai Inna ta yi a asibitin National Hospital cikin
matsananciyar kula daga wurin likitoci da nurse din saboda ganin
tsayuwar teacher akan ta ran da ta cika kwana biyun da yamma
teacher ya ce a maida ita gida, shi zai rinka zuwa yana dubata dakin
dake fakon kasa wanda dama Yaya Bashir ya shiryashi don saukarta
in tażo nan aka sanyata.
Kullum da safe teacher zai zo ya dubata inda sabbin magungunan
da zata sha ya zo mata dasu in an yi sallar isha'i ma zai dawo ya
dubata daga nan mu dan yi hira kafin ya tafi cikin kwanaki kadan shi
dai Hama suka zama abokan juna kullum teacher cikin aike yake ina
jin Yaya Bashir yana mita da Anti Hama ta gama mishi bayanin aiken
teacher ya ce ni-fa hidimar Hakeem din nan ta isheni ga dawainiyarasibiti da magungunan Inna ya ki cewa komai na sa Ashiru ya kai
mishi cek ya yi kememe ya ki karba gashi kuma agida ma bai huta ba
Hama ta ce to ka taimaka ka bashi wacce yake hidima saboda ita
mana kaga ai sai ya huta Yaya Bashir ya daure fuska ya ce a'a Hama
ni ba zan yarda a tilasta ni auren Suhaila yanzu ba yarinyar ta riga ta
wahala ba zan fauketa in baiwa wani ita yanzu ba, sai na tabbalar ta
murmure sosaio ta maida kyan jikinta kamar da, Hama ta kyalkyale
da dariya ta ce in dai ba jaririya kake so Suhaila ta zama ba ai iyakar
kyan da zata yi kenan suna ta maganarsu ni kam ina kusa da Inna ina
bata magani ba mu ce musu komai ba iyayen Hakeem maza da mata
29
sun zo duba Inna
mahaiſiyarshi
daga garinsu Gire an cc mun wai har da
suka zo din,
sai dai ni kam ban gansu ba, don ina da lacc a ranar da
arzikin ya
aiken teacher biyu wurin Yaya Bashir yana rokon daura mana aure a lokacin bakin Yaya Ahmad ga su Hama
saſc
a gida
misalin
suma sun matsawa Yaya Bashir ran nan ran wata Lahadi da
Yaya karfe goma wasu tsofaffi su hudu ne suka yi sallama da Bashir dukansu babu wanda bai haura shekaru tamanin ba hannu biyu ya karbcsu ya sa aka yi ta shiga musu da nau'o'in abinci iri-iri suka gaisa ya fito ya basu wuri don su gama ya shigo dakinda Inna take ya zauna à kasa cikin sanyin jiki yana cewa Hama. Hama kin ga dattawan da Hakeem ya turo mun yau saboda da Allah Yaya
zan yi dasu yanzu? Hama ta yi jugum tana tayashi jimami ya cc zan gaya musu kawai, ya turo ranar Juma'a a daura musu aure washegar asabar shi ne daurin auren Ahmad za a yi biki ayi komai amma
tarewar Suhaila gidanshi sai na shirya tukuna kar kuma ya dameni,
Hama ta ce e, to in ka yi hakan ai ka mutunta dattijan daya turo din
ya tashi ya koma wurinsu Hama tana murna tana cewa ai gara da ya yi mishi haka din Inna kam murmushi kawai ta yi suka shiga lissafin kwana kin da suka saura.
Hakeem ya turo jama'a don yuwa Yaya Bashir godiya nan da nan
kuma ya shiga aiwater da shirye-shiryen aurenshi cikin sati guda sai
gashi bayan gaisuwa, kayan na gani ina so kayansa lalle, kayan aure,
duk sun kawo Hama ta ce ni in ce ko ba a gaya musu Suhaila ba
budurwa bacc na yi dariya na ce to ai ko ke kin isa ki fallasani Ilama
tunda kin gayawa tcacher na haihu an kuma biya Sharif rakuma ta cсе
au hakanc amma duk da haka Hama bata ja bakinta ba sai da ta sake
yiwa iyaycn Hakecm maganar wai Suhaila fa ba budurwa bacc suka
ce e, sun sani amma su dansu saurayi ne don haka bikin saurayi da
budurwa za su yi ranar Juma'a aka daura aurena da Hakeem Lamido
washegari Yaya Bashir ya nufi Katsina karbar wa Yaya Ahmad nashi
auren hidimar biki an sha ta babu abindą za a cc sai Allah ya bayar da
zama lafiya, an yi biki an kammala ni kam ina žuane a gidanmu inna
gamu da teacher a jami'a 'ya yi mun tayin zuwa gidanshi in ki office
dinshi ma na daina zuwa tun daga ranar da ya ritsani a office din
bayan ya kulle ya yi ta yamutsa ni sai da ya gaji ya budeni na fila ban
sake yarda na shiga ba, shima bai cika zuwa gidanmu ba, mafi
30
yawanci ya kan zo ya gaida Yaya bashir nc idan har yana nan agari,
ran nan mun samu hutun jami'a da kwana uku bayan mun kammala jarrabawa hutun kuwa mai tsawo ne don na karshen semester ne mun
kammala karatun matakin farko wato 100 level, zamu shiga 200 ranar
da safc Hakeem ya żo gidanmu wajen Yaya Bashir ya zo, ya zo ne
peman arzikin wai in yiwa kakarshi sumaye da ta zo National
Hospital aka duba lafiyarta rakiya zuwa gida Gire don shi ba zai samu
tafiya lare da ita ba, Yaya Bashir bai yi musu ba don dama ya riga ya
ga tsohuwar tunda har ya kawota wurina ta kwana sai ma yayi mun
shirin tsaraba sosai, wai in kaiwa mahaifiyar Hakeem da 'yan
uwanshi, ni da Suhaila ne zamu yi rakiyar tun darc muka kammala
shirin kayanmu, itama sumayen ta zo gidanmu ranar anan zata kwana,
ni da mutanen gidan muka yi ta ina muka saka da ita, Washegari
wajen karfe tara direban Yaya Bashir ya kaimu airport muka hau jirgi
zuwa Yola, tunkafin Azahar muka isa Gire, gidansu Hakecm Lamido gidansu Lamido wani irn makadeden gidane kana shiga cikinshi zaka
gane gidan sarautane sassa-sassa ne gidan sashin mahaifiyarshi wacee
suke kira inna Abu daban babbane kwarai ko da mijinta ya dade da
rasuwa gidan a cike yake da jama'a yanayinta kawai in ka duba zaka
gane 'yar gata ce ba kadan ba masu aikine kewaye da ita bata cas bata
as duk gidan füllaci suke yi babba da yaro tun zuwanmu lasa aka
bude kofar wata katanga dake rufe aka shiga ana ta gyara, ni kam ina
kwance a dakinta tana ji dani kamar zata lasheni wajen biyar na
yamma Sumaye ta leko, war Suhaila, na ji ta fadi na dago ido na
kalleta ba tare da na san abinda ta fada ba, ta yi mun Hausar su ta
fulani wai tsami tsami na biyota muka shiga wannan katangar tana
mun bayanin ga sashin mijinki zo ki gani kafin ya iso, ban gane kafin
ya ison ba, amma kyan wurin ya dauke hankalina fadin tsakar wurin
ya yi kafa dari biyu har da hamsin, manyan gini ne guda biyu flat lat
daya a bayan dayan sune kawai ata gaban suaran filin kuwa katange
yake cikin waya an kana zuba su jimina, talo-talo agwagin ruwa farare sol sol, ana kiwonsu can tsakiyar wurin nasu an yi musu dan
madaidaicin tafki da aka zuba kifayc a ciki ga dogayen bishiyoyi da kannan nasu mangoro, gwaiba da lemo ga koriyar ciyawa an daidaita
tsayinta gwanin sha'awa can gefen flat din anan wata rumfacc cikinta
an zuba kujerun roba, wurin ya ban sha'awa lat din farko shi ne na
31
Hakeem komai na cikin shir irin na gidanshi na Abuja ne daya lat
din kuwa babu komai cikinshi in ji Sumayc shi ne nawa, na yaba
kwarai cikin zuciyata da tsarin gidan Hakeem min dawo wurin mahaifiyarshi muna zaune har lokacin jama'a basu daina zuwa
gaisheni ba, kowa dai ya zo ina kiyaye kalmomin farko da yake fadi
cikin fullancinsu wai "Debbo Lamido Jokkike" sai in ji an ce e, sai
kuma a zauna a gaisheni da wacce na iya 'yan mata biyune na fi lura
da su a masu zirga-zirgar gidan Mariya da Sadiya kyawawa ne gasu
da nutsuwa Şumaye ta kalleni, ta ce 'ya'yanki ne, babbar 'yar Hakeem
ita ta haifi Mariya mai binta kuma ta haifi Sadiya amma dukansu
anan gidan suka girma, misalin takwas na dare sai kawai na ji an ce
wai Hakeem ya iso, abin ya bani mamaki na cewa zuciyata amma bai
gaya mana zai zo ba.
Dakin mahaifiyarshi ya fara shigowa suka gama maganganunsu
cikin fullanci ban jin abinda suke fadi, ya kama hannun Suhaila ya
fita da ita, wajen tara da rabi Sadiya ta shigo ta ce mun dada wai in ji
kawu in zaku kwanta a kaiku can wurinshi, shi ya shiga gari, ban yi
magana ba, Sumaye ta ce to ni kam cikin zuciyata na kasa fahimtar
dama teacher ya san zai zo ko kuwa tafiyarshi ce ta sameshi babu
shiri? Mahaifiyar Hakeem ce ta bani umarnin tafiya can wurin in
kwanta, ra rasa yanda zan yi in yi musu da ita na ce zan jira Suhaila
ta yi murmushi ta ce kar ki damu nan gidan yara ne in ma ta dawo
bata yarda dasu ba zan sa a kawo miki ita, na ce to Mariya ta rakani
zuwa wurin Hakeem na gama komai na shirin kwanciya na kwanta
har n ayi barci sosai lokacin da hakeem ya dawo ya zo ya kwanta
kusa dashi shima barcin ya shiga yi da asuba muka tashi muka yi
sallah, teacher ya kalleni yana murmushi ni kuwa na sha mur sai nace
ina Suhaila? ya ce na sayar da ita, na ce kana sayar da mutane ne? Ya
ce ato shi ne na gani baki tambaycni komai ba sai inda na bar miki
Suhaila, na ce to yi hakuri ya yi murmushi ya ce tana wurin Inna, don
Allah Suhaila ki yi hakuri kin san an ce Allah daya gari ban ban mu a
al'adarmu amarya idan ta kwana a gida tana yin abinci ta ciyar da
mutanen gidan har da makwabta na sani ko baki yi ba, inna zata sa а
yi amma zan fi farin ciki in ga an yi dake in san abincinki aka ciyar
da mutane ba wasu ne suka yi ba, na ce to ai teacher ni bana zo zama
banc na yiwo rakiyanc kuma gobe zan koma, ya ce e, na sani amma
32
dai taimakeni ki yi mun na cc to.
Na shirya na fito na gayar da iyayen Hakcem na nuſi inda aka soma aikin na gane aikin gagarumi nc don ganin irin abubuwan dake zube shiga kicin din na yi na duba komai na karbi aikina na tsaya kan girkin don ganin komai ya yi kyau an fita kunyar mutane, ban da
naman saniya, raguna har hudu Hakcem yasa aka yanka ga kaji, na sa aka gasa ragunan ba tarc da an yanyankasu ba, ta hanyar sagalcwa, ayi ta juyasu akan wuta a hankali a hankali, naman slaniya aka yi danbun nama, kajin aka soycsu, kayan ciki kuwa na juyeshi cikin miya, shinkafa aka yi ta dafata tukunya tukunya, sai wajen azahar muka kammala na je na gayawa Sumaye na gama ta yi ta sa mun albarka, dama abinda tcacher ya ce mun in yi kenan in na gama in
gaya usu kawai su sun san yadda za su yi, na shiga wanka n ayi sallah
na shafa mai na fito cikin kwalliya ta burgewa sai daukar ido nake yi,
na yi nufin komawa sashin mahaifiyar teacher cikin wurin ya yi
yawa, ba zan iya kutsawa wurinsu ba, na hakuri na dawo wurina na
zauna, Hakeem ya shigo tare da wasu abokanshi su biyu ya sha
kwalliyar manyan kaya farare sol, ya yi kyau ba kadan ba, sai fara'a
yake yi ina ganinsu na jawo dan shaтa-sharan gyalena na rufe ido
suka zauna suna dariya, a'a amaryar kunyarmu take ji? Dadi ya kama
teacher ya ce ato gata nan sun dan yi fullancinsu wanda ban taba
sanin teacher yana ji ba sai ko yau sai ya ce mun Suhaila wannan abokina ne Ibrahim tun munaa yara tarc muka taso tare kuma muka yi
kakin yaya Bashir ma ya sanshi wannan kuma tare muka taho jiya abokina ne na wurin aiki Tijjani ban amsa ba, ina dai ganinshi ta cikin gyalena, da zasu tafi kudi masu yawa suka ajiye mun wai sun sayi bakin amarya, sai wajen magariba, ran nan na ga Suhaila hidimarta take yi gashi IHakeem ya maimaycta da kayan wasa kuma
su Sadiya sai ji da ita suke yi wajen sha daya ran nan Hakeem ya shigo ya kammala sallolinshi da addu'o'inshi ya zo ya kwanta naga kwanciyar tashi ba irin ta jiya bace rikici ya tashia tsakanimu na ce gaskiya ni ba tarewa na yi ba rakiya na yi, Hakceem ya ce shi bai san tarewa ba, daurin aure ya sani, kuma an yi don haka shi dauko matarshi ya yi ba zan sake komawa gidan ba, sai dai in je gaishesu,
na soma yi mishi kuka, dana ji ya ſadi haka ya ce kukanki ba zai
hanani neman hakkina ba, don na saba ganinki kina yi sai kuma ya
33
shiga rarrashina haba Suhailata ke kin ga ya yi daidai a daura mun
aure acc in jira wasu shekaru biyu nan gaba? Kafin a kawo mun ke?
A farko na dauka za ki bani hadin kai in ya so idan Yaya Bashir ya ga
za a haihu mishia gida ya tattara ki ya kawo mun ke to na ga alamar
ke ma ba hadin kan zaki bayar ba, don haka na dauko matata in an
kwana biyu sai in je in bashi hakuri shi kenan zance ya kare nana yafe
kar a miki komai in shi ne shirin, ni zan yi ba shi kenan ba? Har cikin
dare ina kuka da kyar teacher ya iya shawo kaina na yi shiru da asuba
mun idar da sallah Hakeem ya fita gayar da iyayenshi na jira ya dawo
nima in je in gaishesu yana shigowa sai kawai na ga ya shiga kulle
kofa, ya shigo dakin yana tube kayan jikinshi a kidime na tambaycshi
teacher me zaka yi? Ya kalleni kawai ya ce koma me zan yi in kika yi
hakuri ai zaki gani, ya iso inda nake hannu biyu ya saka ya sureni
zuwa wani daki da ban san da shi ba, ke matata ce Suhaila abinda ya
fara gaya mun kenan, kafin in ce komai ya shiga sumbatata ya hanani
sakat na kasa aiwatar da komai, Hakeem ya mallake komai nawa,
kusan awa guda da wasu minto6i Hakeem ne kawai yanda ya ga
dama haka yake sarrafani ni kam kasa hakuri na yi kuka nake mishi
saboda ji nake tamkar yau ne zan fara Hakeem yana kwance a can
gefe magana yake mun a hankali, Haba Suhaila menene na yin kuka
haka? Iye yi hakuri don Allah zo kiji ya kara jawoni a jikinshi haba
Suhaila ke ma kin san ina sonki bana daukoki don raina Yaya Bashir
bane amma na gaji da jiranki Suhaila na gaji taimakeni don Allah ki
bani hadin kan da nake bukata a wurinki tsawon lokaci yana
rarrashina har barci ya daukeni ji na yi ana mun tausa a hankali a
hankali shi ne abinda ya tasheni na bude ido na ga Hakeem tausa
yake mun yana ganin na bude ido ya saki murmushi lokacin sallah ya
yi Suhaila Azahar ta yi na dafe kirjina cikin kaduewa Azahar
Hakeem, ban fa gaida su Inna ba, yau yanzu in na fita me zan ce
musu? Ya ce haba Suhaila gidan mijinki ne fa, kowa ya san ke matata
ce meye abin jin kunya, a ciki? Na ce ni kam ka mayar dani gida yau
ne kuka yi da Yaya Bashir zan koma gashi har azahar ta yi babu
alamar tafiya, to ki yi wanka ki yi sallah lokaci ya yi ya fita na idar da
sallah kenan Mariya ta shigo Dada wai ki zo in ji Inna Abu na ce to
na fito ina tunanin da wane ido zan kalli mutanen nan kila dukansu su
ganc mun yi wani abu da teacher shi ne ya sanyani irin wannan dogon
34
barcin daurcwa na yi na shiga ſalon bayan ta amsa sallamar da na yi
na shiga falon bayan ta amsa sallamar da na yi Suhaila kin tashi?
Barcin gajiya ko? Na kalli tambayar tamkar da biyu na dai daure na
dan yi murmushi, Lamido ya zo ya cc wai kuka kike yi kina so a
kaiki gida shi ne na ce a kira mun ke mana in rokeki haba Suhaila nan
ai gidan mijinki ne kin ga maganar tarewar nan ba fa dole bane a
shari'a daurin aure shi ne muhimmi amma tunda kin ce cewa ya yi ki
yiwa Inna rakiya na yarda kina da gaskiya ya maida ke ya tsaya
kawai tunda an daura aure abashi matarshi amma ina so in rokeki kin
ga tun zuwanki abokanshi da 'yan uwanshi suna ta zuwa ganinki to
bari ya yi ko sati biyu a gida kin ga hutu ya dauko sai ku tafi ko?
Nauyinta kawai na ji na ce to Suhaila na hango cikin motar yara tana
tuka abinta na bita da kallo Inna ta ce ina Sadiya ku kawowa matar
kawunku abinci ku hado mata da madara ta sake kallona tuntuni na so
a tasheki ki ci wani abu kafin ki kwanta Lamido ya ce a barki barcin
gajiya kike yi ina cikin cin salad mai wadataccen kwai 'cgg salad'
Hakeem ya shigo ta hakurine Inna? Inna Abu ta ce a'a zan roketa ne
ta ki amma ai ba ka kyauta ba ya ya zaka ce ta yiwa Inna rakiya
sannan ta zo ka nemi hanata, komawa? Ta dai yi mishi fada ta ce to
sati biyu ka mayar da ita gidansu, ya ce to Allah ya kaimu.
Na dai shawa teacher mur na kwana biyu kafin daga baya nà
hakura na watsar saboda ba zan iya ganinshi cikin 6acin rai ba, muka
koma zamanmu na cin amarci ina dai tunanin in naje gida kome zan
ce wa Yaya Bashir oho, kwanana hudu a Gire ran nan ina sallar
La'asar teacher ya shigo ya ce idan na idar ina shirya in rakashi asibiti
zaije duba marasa lafiya naidar na shirya na fito ba tare da na san a
ina asibitin yake ba, hudu da rabi daidai muka isa asibitin wani
makadeden asibiti ne a jikin Saint Pot dinshi an rubuta Lamido
Memorial Hospital mun shiga ofice din Hakeem yana mun bayanin
asibitin sai ga wani likita ya shigo da folders na marasa lafiyar da Dr.
Ilakeem zai duba ya gaishemuya yi mishi bayani teacher ya ce a fara shigo da mutanen daya bayan daya suka yi ta shigowa yana dubasu
wasu ya rubuta musu magani wasu yace su sameshi a garki rana kaza
sai da ya gama ya kuma zaga dani naga wurin yana mun bayani ya gina asibitin ne don tunawa da babanshi komai da ake yiwa marasa
lafiya kuwa kyauta ne in dai ba basu da maganin abin anan ba, sai su
35
H
n
C
Π
a
S
n
g
rubuta ajc a saya yana wannan aikin ne da ſatan Allah ya kaiwa
babanshi ladan cikin Kabarinshi na kalleshi a hankali na cc amin,
tcacher kwanan mu bakwai a Girc ran nan da yamma mun hadu a
falon mahaifiyar tcacher muna zaunc hirarsu suke yi da fullanci
Sumaye ta ce kai kuwa lamido matarka tana zaune sai ka rinka
fullanci ba zaka yi Hausa don ta ji ba, ya kalleni da gefen ido ya ce in
tana jin haushi sai ki ga ta koya nan da nan amma in ina yin Hausa
tana jin dadi ai ba zata koya ba, kin san na san halinta ta yi dariya, ta
ce zaka sani dai tukuna yashcnc aka yi auren naku da har ka wani san
halinta? Cikin sauri ya ce lah Sumayc ai na dade da sanin Suhaila kin
mance yarinyar da na rinka baki labarinta sanda nake koyarwa a Jos
me cinyc mun gyada mai gishiri? Tana murmushi ta ce ban mance
labarin ba, ya ce to ita ce wannan yana nunani da dan yatsa gaba daya
suka yi dariya ni kam murmushi kawai na yi wayar Hakeem ta yi
motsi kadan don "No care" ce bata kara sosai ya dauka ya kai
kunnenshi kamar zai amsa wayar anan sai kuma muka ga ya yi maza
ya tashi ya yi waje sai can an jima ya dawo yana murmushi ya се
Inna Yayan Suhaila ya ce a gaisheku Inna ta rike baki ta ce muna
amsawa ni 'yasu ya ganku shiru ko? Teacher ya sake wani murmushin
ya cc ya ce ne a gaya muku gobe in Allah ya kaimu iyayen Suhaila za
su zo ta ce kai madallah nan da nanta shiga àike gidan yayun
Hakeem mata da kannc wadanda suke gidan miji a gaya musu gobe iyaycna za su zo makwabta da abokan arziki duk aka bisu teacher ma
ya shiga kaiwa da kawowa ni kam bar na yi barci ban san shigowarshi ba.
Washegari tun kafin azahar sai ga su Anti hama sun zo da yawa fiyc da