Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
adon nace, uh ta gyada kai tace to Allah ya bada sa'a nace amin Suhaila tana falone don kar taga fitana tayi kuka, tace tana wurin yayanki nace to na fito ba tare dana bari ta ganni ba motar Anti Hama na hau Honda Prelude ash colour na iso jama'a kafin lokacin paper ta har na dan kara yin nazari tare da kawaye na mun fara paper wajen karfe goma ne da minti biyar zamu yi awa daya da rabi karfe sha daya daidai naga tsayuwar wata mota Honda Accord 98 Model mai farin fenti a gindin bishiyar darbejiya dake kusa da ajinmu teacher ne ya fito daga cikinta yana sanye da farin takalmi Italian shoe a kafarshi farin wandon chinose product din D.K.N.Y sai brown T. Shirt ita kuma product din D.K.N.Y ya yi matukar yin kyau yana fitowa naga-wasu mutane su biyu sunje wajenshi ni kam na yi kokari na maida hankalina kan aikina karfe sha daya da kwata na mika paper tan a dauki jakata na fita, waje. Teacher yana ganina ya salami mutanen ya kalleni cikin wani lallausan murmushi, kallo na sama da kasa ya yin a nuna yabawa da kwalliyar tawa ina zamu mujc office dina ko ina? Nace office dinka a ina? Yace a dan nan bayanku wani lokaci ina daukan medical student lectures, nace uyu to muje mana muka jera muna tafiya ya dan kalleni kai nima dai da karfin hali nake yadda kike da kyan nan Suhaila in mijinki ya ganni ina jerawa dake ai ban san irin hukuncin da zai mun ba, naki amsawa muna shiga medical department dalibai suka yi ta tasowa suna isar da gaisuwarsu 18 Dr. barka da zuwa wani ma ya zaburo Dr kana da darasi damu ne yau? Yace a'a nazo ziyara ne har muka isa office din yasa aka bude muka shiga ya nuna mun kujera office din babbane kuma ya yi matukar tsaruwa hoton wato dattijuwa ne kawai a ajiyc a kusurwar table din dake gaban kujerarshi wanda na tabbatar mahaifiyarshi ce don yaso ya yi kama da ita a wata kusurwa kuma ga abinda ya rubuta. Ma'ana nasarar dan adam a rayuwa ba ana aunashi da matsayin da mutum ya kai bane, a'a ana gane nasarar net a gwagwarmayar mutum kafin ya cimma nasarar tashi can gefe daya kuma ya rubuta sunanshi Lamido. Na gama kale-kallena na dawo da nutsuwata ga teacher wanda ya kafa mun ido yana kallona tare da wata 'yan yatsunshi yana ganin na dawo gareshi ya yi murmushi, yaushe rabon ki da Eze? Ya yi tambayar cikin zolaya ko shima kin mance shi? Na yi murmushi nace tun ranar parting mun agama primary school Eze bai biya kudin party ba yazo aka hanashi shiga wurin sai ya zagayo ta window din da nake zaune na kama hannunshi ina so in taimakeshi ya shigo ta window yaran class suka ganni suka sa ihu suna cewa teacher wai ga Suhaila zata shigo da mijintata window tun da na ski hannurshi ya koma har yau ban sake ganinshi ba, teacher, ya yi dariya yace Allah sarki Eze yana cikin yaran dà nake tunawa, "Bery funny" dashi nace uh yaci gaba da yi mun tambayoyi ina bashi amsa Yaya ka yi kika yi lattin zuwa jami'a? nace haka kawai. Ya harareni yace kila dai da bai yarda bane? Nace uh, yaranki nawa? Nace biyu, saboda Allah dai nake so ki gaya mun nace to daya ya kalleni me yasa ba kya son gaya mun gaskiya? Nace Allah kuwa dayane-yace, to na yarda shi fa maigidan wa sunanshi nace to ai kasan sunan mijin farine bana fada, yace uyu ya danyi shiru jumawa kuma sai yace to yaya Baba? Na danyijim na wani lokaci don in har akwai abinda na kasa sabawa da fadinshi ta mutuwar babana, ya zaro ido yana kallona ya sake cewa Suhaila nace ina baba? A hankali nace mishi ya rasu, hannu biyu ya saka ya dafe kanshi tare da yin kabbara. Allahu Akbar yaushe? Hawaye suka soma zuba a dona shar shar shar, teacher ya kidime ki yi hakuri Suhaila, Bery painful, amma ya ya zamu yi? Ya shiga yi mun nasiha ban sani ba Suhaila da ban tambayeshi shi ba da inna kawai na tambayeki inda take don inje in yi mata ta'aziya na kasa tsayar da hawayen dake zuba 19 mun, "Oh my God" abinda yake ſadi kenan ya taso daga kujcrarshi ya dawo inda nake zaune ya yi nufin tallabo kaſadata yaga kuskuren yin haka din ya miko mun handkerchief, dinshi share hawayenshi ki yi bakuri muje in kaiki gida ko kina ganin ranshi zai baci in ya ganni? Nace nazo a mota, cikin sauri yace okey muje in rakaki sai da teacher ya bude mun kofa na shiga na zauna ya rufe sai yace mun sai yaushe Suhaila? Sai yaushe zan sake ganinki? Zan iya zuwa nan ajinku in ganki? Nace kar abin ya yi yawa teacher cikin mijina ya ya katseni stop it Suhaila, stop it, na dai gane kawai, Thank you bery much, ki gayar mun da bebinki ya juya ya koma cikin jami'a ni kuwa na dauki motala na tafi har muka gama jarrabawarmu ban sake ganin teacher ba har muka samu hutu na kasa kwanciyar hankali sai ganin laifın kaina nake yi me yasa? Me yasa nace mishi ina da aure? Ina son ganin teacher akai akai ko meye dalili? Oho mun koma jami'a ina sa ran ganin ya kawo mun ziyara shiru sannan na gaji na kasa daurewa ina son ganin teacher ko da yake dai da kunya ni in nemeshi to amma kuma ai zan iya sakewa da girmamawar dake tsakanin malami da dalibi in ziyarceshi da wanann tunanin na nufi sashinsu wato department of Medical Studies, ina shiga yaron da yazo ya tambayeshi labarin ko suna da darasi na fara gani yana ganina ya tareni muka gaisa sai yace mun yaya jikin Dr Lamido? Na kalleshi a kidime nace basher da lafiyane? Yace ai ya kwana biyu ni na dauka ma kina da labarinshi ne yasa na tambayeki, nace uh uh bani da labari yana ina ne yanzu? Yace baki san gidanshi ba? Nace a'a yace ai kin san shi ne likitan zuciya na National Hospital gidanshi yana nan a inda gidajensu yake shi ne No 72A in kin je nace mishi na gode na koma aji na koma aji na dibi littattafaina cikin hanzari na koma gida ban 6oyewa Anti Hama inda zani ba shiri sosai nayi nayi kwalliya ta kayatarwa na shirya Suhaila na sanyata a bayan mota, motar Yaya Ahmad na hau don yazo yana gari, na biya Super Markct, na yi mishi sayaiyar kayayyakin da akc yiwa mara lafiya tsaraba dasu sai da na isa gidan mai lamba 72A a jikinshi nayi parkin gabana sai faduwa yak yi gashi nayi wauta ban dauko katon gyale ba balle in na tarar matarshi tana nan in gamsar da ita cewar nima matar aure ce, tunda na manta ban mace a gidan tambayi yaron da a mun kwatance gidanshi ko yana da ba, karfin hali nayi na kwankwasa kofar dake rufen a hankali sai dana 20 sake kwankwasawa naji muryar shi daga ciki yana ccwa, 'Just comc in the door is open'na bude kofar ina rungume da tsarabar da nayi mishi da hannu daya daya hannun kuwa ina rike da hannun Suhaila a haka muka shiga yana kwance kan darduma mai laushi a kasa karatun jarida yake yi, yana ganina ya mike cikin mamaki da bude idanuwa Suhaila a gidana? Abinda ya fara fadi kenan, ya dauki Suhaila ya runguncta, Bery beautiful girl as mother as daughter, na wucesu na shiga kicin don in ajiye kayan dana ke rungume dasu ya biyoni kicin din dame zan yi miki sannu da zuwa Suhaila, ya kafa mun ido cikin murmushi, with a kiss or with a smile naja da baya nace da mijin nawa teacher kayi mun kiss? Ya danyi jim yacc mijin nakine yana sakaci da yawa. Nace uhun day a barni inzo in duba lafiyarka amatsayinka na tsohon malami na shine sakacin nashi ko? Yayi dariya yace daina kirana tsohon malaminki ni har yanzu malaminki ne, a shekarun baya kina yarinya na karantar dake darussan turanci da lissafi a yanzu kuma kin girma zan karantar dake darussan sumba da runguma na tsuke fuska nace to kar dai ka manta ga yarinya nan kusa da kai tana jin abinda kake fadi, ya juya ya kara kallonta yace wannan bata san komai ba, ya sake surarta ya rungume ya zuba mata ido, mutumin nan ya cuceni Suhaila wannan yarinyar ai dani take kama, na yi dariya nace sannu karfin hali mun koma falonshi mun zauna wanda ya yi matukar tsaruwa ko a Turai falon teacher ya isa a kirashi falo, komai a falon a cikin tsari yake an ajiyeshi a yanda zai bayar da sha'awa babu wani abinda tsayinshi ya zarce wani hatta bishiyoyi da furanni da ake iya hange daga falon tsawonsu bai zarce na kayan dake cikin falon ba, hoto daya ne a falon na wani kyakkyawan dattijo cikin nadi wanda ke nuna mun yaa da wata sarauta ta gargajiya a jikin hoton an rubuta 'Mai martaba hakimin Gire Alhaji Lamido Gire, abinda ya fahimtar dani shine mahaifin teacher me za akawo muku Tambayar data dawo dani daga kallon hoton kenan na kalleshi nace ba zamu ci-komai ba, ya harareni yace bazaki ci ba dai ke baby wa sunanki? Tace Suhaila, ya zaro ido ya kalleni ke kice mutmin nan ba karamin so yake miki ba, matarshi Suhaila 'yarshi Šuhaila, nace c, soyayya ya gyada kai yace me kike so Suhaila, tace mishi ice cream da cokolet, cikin hanzari ya mike ya fita ya kira wani mutum ya bashi sautu a sayo mishi ice cream da cokolet tare da wasu kayayyakin ciye-ciye da yara ke sha'awa ya 21 dawo ya zauna ya jawota jikinshi ya kalleni yace tunda ke ba zaki ci komai ba, to ni yi mun girki, na kalleshi nace in maka girki fa kace? Yace e, haka nace, to ina matar taka? Ya tabe baki yace bani da ita ban taba yin karyar ina da mace ba kowa ya tambayeni cewa nake yi ni saurayine ban taba aure ba, na yi murmushi nacc kai tuzuru dai teacher, yace e, to ni tuzuru sai me? Nace to yaya jikin ance baka da lafiya yace na fara jin sauki yanzu yunwace tali damuna taimakeni ki yi mun girki ko zan dan ji dadin jikina na shiga kicin din teacher abincin mai sauri na shirya mishi dafa dukan taliya supergetti nayi mata hade-haden kayan lambu gami da wadatacciyar hanta sai kuma na shirya mishi, "African Beef Stew" sai na hado mishi da ruwan lemo mai sanyi, ina shirya mishi abincin kan dardumar da yake zaune shi kuwa yana gefe daya ya bude kafafunshi a mike ya dora Suhaila kan cinyarshi guda daya ya tasa mata kayayyakin ciye-ciyen da yasa aka sayo mata sai dana sharta take'yi suna hira sai ya kalleni cikin fara'ar da ban san abinda ya yi mishi dadi haka ba, yace saurayi maganar yarinyar na Suhaila nace menene? Sai naga ya kalleta yace Suhaila tuna mun na manta dazu me ma kika ce mun sunan babanki? Ta yi shiru taki kulashi ni kuwa na kafa mata ido, sai yace au na ma tuna ashe cewa kika yi sunan babanki guda biyune, Hakecm da Lamido ya tunzurota da sauri tace mishi ba haka bane, yace to tuna mun Suhaila daga yanzu bazan sake mancewa ba, amma in zaki tuna mun ki fadi sunan da karfi don ya shiga kunnena sosai, da karfi ta bude baki tace nace maka sunan babana biyu da baba Bashir da Yaya Suhaila, ya dago ido ya kallen yana murmushin gamsuwa ya sake juyawa gareta yace "What is your name" Taee my name is Suhaila Bashir Imam yayi dariya ya sake kallona yace yarinyar tana da wayo zata iya fallasa karyarki wannan 'yar yaya Bashir ce, naga kamanninta dake ne don ta yi kama da babanta. Ya kalleta yacc zaki ci abinci? Ta gyada kai nuna ta koshi yace 22 dauki 'yar bebinki da aka sayo miki je ki daita wajen tsuntsayen dana nuna miki itama ta gansu, ta suri katuwar 'yar bebin da gudu, na ga ta nufi wata kota ta turata sai kuwa na ji kukan tsuntsaye daga ciki tana shiga ta turo kofar teacher ya mike yaje ya kulle kofar falonshi da dan makulli sai binshi da kallo na ke yi yana dawowa yazo inda nake zaune ya kamani yana kokarin cusa hannuwanshi cikin rigata da karfi kokawa sosai muke yid a dai na ga ba zan iya hana shi ba sai nace "Subhanallahi" yana jin haka ya yi maza ya sakeni ya zuba min ido yana kallona tare wani irin murmushin da ban san abinda yake nufi ba, nace me ye haka? Yace zan yi cajinki ne, ina so in sani kin haihu ko baki haihu ba? Zan taba cikinki da nononki ne in ji don na gaji da karyarki na daure fuska naçe to ko na haihu ko ban haihu ba tunda ina da miji ina ce shi kenan? Ya ce, to hell with your husband Suhaila, ba zai iya hanani komai ba, nace to kana sake tabani ihu zan yi maka, yace sai me? Illa iyaka makwabta su shigo, ko akanki suka sameni ba zai ban kunya ba, baza su ga sakarcina ba don kuwa kina da kyau kina da abubuwan da zasu nuna musu sune suka tilastani yin hakan mijinki imma kina dashi cutata yake yi ba kuma zan barshi ya ci gaba da cutar da yake yi mun ba, a shirye nake zan karbeki daga hannunshi nace in ina sonka ko? Yace uhun wannan ya rage naki "I don't care ko a yanzu ki ce kiana sona ko kar kice kima sona, oho ni dai na san ina sonki ban taba burin auren wata mace ba, in ba ke ba kece kika takura rayuwata kika hanani sakat in banda haka da tuni ina da aure, lokacin dana ji labarin kin yi aure na yi bakin ciki Suhaila kishi ya kusa ya haukatani amma duk da haka na kasa fitar da sonki cikin zuciyata na shiga fatan kawai ko da mijin naki ina so in sak ganinki don in kwace ki daga gareshi, na kalleshi a hankali nace a in= kaji labarin na yi aure? Yace ai kina nufin dawowa na daga turai ba nemeki ba? Na je har gidanku na yi sallama wata tsohuwa ta fito, y kwatanta min ita ta tabbatar Hama ce, ita ce ta gaya mun cew Suhaila an dade da yi mata aure tana Bengazi bans ake tambay kowa bane na juya na tafí shi yasa bata bani labarin rasuwar baba nace to yanzu na gaisheka zan tafi, yace bari in gama cinyc abinci sai ki saukeni a inda zani, nace gaskiya ba zai yiwu ba, sai ku aganni da katon namiji a motata? Ya yi murmushi yace ai ma b san katancina ba sai nan gaba kadan, na mike na shiga wurin Suh 23 tana zuane sai kallon tsuntsaye take yi wurin ya yi matukar kayatuwa, wurin hutuawa ne, dangogin tsuntsaye kala-kala masu kuka iri daban daban ga shimfidaddiyar koriyar ciyawa ko grass capet a malale, 'yan bishiyoyi da furannni masu kyan launi tabbas Hakeem mai son hun ne teacher ya shigo cikin shirin fita shigar kananan kaya ya yi "Coporet wears" kayan sun karbeshi ya ce baby zo mu tafi ta kalleshi ta ce ina son tsuntsu daya ya tsuguna kusa da ita nuna mun wanda kike so in kamo miki sai ki tafi dashi na yi maza na ce yi hakuri teacher ka barta kawai zan rinka kawota tana ganinsu, yanzu in muka je gida da tsuntsu kasan sai mun yi bayanin inda muka samoshi ya yi dariya yace to kin ji Suhaila sai ki yi hakuri zan zo har gida in kawo miki tsuntsu ta ce mishi to. Mun ci gaba da haduwa da teahcer a cikin jami'a muna hirarmu sai dai na ki yarda da amsar gayyatarshi da ya yi mun zuwa gidanshi har sau biyu wai in je in yi mishi girki nace lalle wai ni me ka dauki aurena ne? Yace yanda mai shi ya daukeshi mana Suhaila na ce to babu inda zani, yace to babu laifi, ran nan ranar Lahadine ina kwance a gida ban je ko ina ba ni da Suhaila ne a dakinmu lokacin da wayata ta yi kara nasa hannu na dauka na kai kunnena cikin sauraro in ji muryar Engineer Mahammad Yakub sai na ji muryar teacher yace na bugo ne in tambayeki ko ya ya bashir yana nan? Har zan gaya mishi sai na tuna nace yaya zaka tambaye ni Yaya Bashir gidanmu daya ne kuma ma waya baka lambar wayata? Ya kyalkyale da dariya mai karfi na ji ta har cikin kunnena ya cc asirinki ya tonu Suhaila jiya naje na yiwa Inna ta'aziyya a gidan Yaya Ashiru na ci abincin rana na ci na-dare a gidan Hama na ketarki tana da yawa miskilaneinki zai sa ki yi kisan kai Hama ta ban labarin komai yanzu zan zo ne in kawo kararki wajen Yaya Bashir don kin zalunceni shekaru goma da n ayi ina wahalarki ba su isheki ba, yau wata tara da gamuwarmu kin ki ki gaya mun gaskiya sai kwana kwana kikc yi mun nace kar ka zo wurin Yaya Bashir da maganata ba zai karbeka ba ya riga ya ce ba yanzu zai yi mun aure ba, ya sake kyalkyalewa da dariyar ya ce sai yaushe? Ko yana so sai ya ga an yi mishi tabargaza tukuna? duk yanda ya kai da sonki tilas ya bayar da aurenki Suhaila don akwai ki da bukata wacce shi ba zai iya yi miki ba, na ce a'a ni bukatuna duka yana biya mun su, ya ce to babu laifi gani nan zuwa ya ajiya wayar, misalin 24 karfc biyar da rabi na yamma na fito yiwa Engincer Muhammad rakiya ni da Suhaila don tun Ia'asaryake gidanmu kwalliyar jan leshi na yi riga da buba da zani da dan kwali na yi amſani da dankwalin na rufe kaina ba tare da na daura shi ba na yi kyau sosai, ina shirin budewa Engineer Muhammad kofar motarshi ya shiga inrufe kafin in yi mishi godiyar alhcrin daya yi mun dashi sai ga wata mota lexus jeep baka tana shigowa harabar gidan taje ta yi parking wurin ajiye moloci Hakeem Lamido ne,ya fito daga cikinta,yana sanye da suit dark brown a jikishi wando iri daya da suit din shima dark brown sai shirt din cikin long sleeve light hrown da nect-tie shima dark brown dukansu product din calvin klin, sai takalminshi shi kuma brown lopes ya yi matukaryin kyau daga inda muke muna shakar kamshin turarenshi, Suhaila tana ganinshi ta saki hannuna ta nufi wurinshi da gudu tana cewa kawu teacher oyoyo Engineer ya dan kalleshi ya kawar da kai wannan fa wurinki ya zo? Na ce kai an ya uh uh, teacher ya wuce yana rike da Suhaila ya nufi falon Yaya Bashir ni da Engineer muka yi sallama ya tafi na yi dab dab dab na haura sama dakina na hau gadona na yi kwanciyata kusan awa daya da wasu mintoci kafin ya ya Bashir ya riko a kirani na samesu a falonshi shi da teacher su biyu na tsuguna na ce mishi gani ya kalleni a hankali ya ce ba ki ga zuwan Hakeem gidan nan bane? Kamar in ce ban ganshi ba sai na fasa na ce na ganshi ya ce to ba ku da komai ne a gidan ba akawo mishi ba? Na ce akwai ya ce aka wo cikin girmamawa teacher ya ce mishi ai ma yanzu za a yi sallar magariba ina ganin zan tafi gida, Yaya Bashir ya ce don me? Ka yi sallah anan mana, ya kalleni Suhaila bude mishi wancan falon sai ki shirya mishi abinda za ki kawo mishi acan na ce to na tashi na fita ina tunanin lalle Yaya Bashir yana jid a teacher tunda har ya bada umarnin in bude mishi wannan falon, sai bayan da tcacher ya gama cin abinci sannan na jе falon na sameshi tuni har Suhaila ta yi barci a wuirinshi na zaune gefe daya muka dan gaisa hirar da muka yi ba mai yawa bace ya fara lambayata wayc na gani kina yiwa rakiya? Na ce abokin Yaya Bashir ne, bai sake daga zancen ba sai ya soma yi mun bayanin abubuwan da suka tattauna da Yaya Bashir a kaina ya nuna mun jin dadınshi yanda Yaya ya karfeshi wai batare da ya yi mishi wani bayani ba ya gane shi ne Lamido gire ya harareni ya ce amma ke wai baki ganeni ba, ko 25 dayake ya gaya mun kina da problem na ido, a raina na ce oh Yaya Bashir yau yau zai fara mun fallasa, muna cikin hira sai n aji ya yi ajiyar zuciya ya ce mu fuskanci gaskiya Suhaila zamana haka ya isheni ina bukatar mace a gidana ta aure na ſuskanci Yaya Bashir da gaske bashi da shirin aurenki yanzu amma kika ban hadin kai al'amarin zai zo mun da sauki ke kanki kina bukatar miji Suhaila Hama ta gaya mun haihuwar da kika yi rabone kawai don ba wani hadin kai kika bayar ba saboda ba kya sonshi ya kallcni yana wani irin murmushin dana san bakinshi yana shirin yin wata tabargazar da gaskene yanda mutumin ya gayawa Hama ko kuwa ya ambaci biyun ne don a biyashi rakuman nashi? Na mike tsam da nufin tafiya in barshi nace sai da safe, da sauri ya kamo hannuna ya jawoni na fada jikinshi tallabeni ya yi sosai ya makaleni da kyau ya şumbaceni son ranshi sai da ya ga Suhaila ta yi juyi kamar zata tashi sannan ya sakeni yana mai da numfashi ni kam tsugunawa na yi na hada kaina da gwiwa cikin jin kunyar abinda teacher ya yi mun, ina jin shi ya mike y ace sai da safe, ya tafi ni kam na jima a nan wurin ina tunanin ashe haka sumba take? Ban ta6a sanin yanda ake ji in an yi ta ba, na ce haba gaskiya mana wani lokaci nake kuskuren ganin Yaya Bashir da Anti Hama suna sumbatar juna, na tuna Sharif da aurenshi na tambayi kaina anya shi ya ma san wani abu wai sumba kuwa? Da kyar na iya tashi na dauki Suhaila muka tafi dakinmu. Cikin dare misalin karfe daya Hakeem ya yi mun waya me kike yi yanzu Suhaila? Nace barci nake yi kai ka tasheni ya ce kin ji dadi Suhaila kina iya yin barci ni na dade ban yi barcin dare ba, kullum cikin tunaninki nake babu abinda nake so irin in ganki a gefena muna kwance tare kina matsayin matata, ba zan iya jiran lokacin da Yaya Bashir ya ambata ba, na cewar sai kin kammala karatunki, zan je Gire in turo iyaycna su zo su yi magana dashi, nace kai teacher da sauri haka? Ya ce ni a wurina ban yi sauri ba gobe da safe zan zo mu kara tattaunawa na ce e, to amma bisa sharadi guda daya, ya tambayeni shi ne me? Na ce ba zaka sake yi mun irin abinda ka yi munin dazu ba, ya kyalkyalc da dariya ya ce sai na zo zamu yi wnanan maganar, zan fi jin ta da kyau, ya ajiye wayar, washegar ma wayarshi ce ta tasheni mc kike yi yanzu Suhaila? Na ce a kwance nake teacher ko kai ba ka jin sanyin nan da ake yi ne? Cikin suari ya ce ina ji mana ai dole ne mu ji 26 sanyi Suhaila mu kadai bamu da abokin taya hira ni na san inda muna kusa da juna sanyin ba zai rinka shiga mana jiki haka ba, ko ba haka ba? Na gaji da yiwa teacher musu nace haka ne cikin sauri da jin dadi ya ce to ki yi wani abu mana Suhaila Yaya Bashir yana sonki in kika nuna mishi kina da bukatar aure zai sashi ya dan sassauto daga cewar sai kin gama karatun tunda dai maganar da yake yi din bai wuce tausayin wahalar da kika sha a baya ba, na ce gaskiya ba zan iya ba teacher ka yi hakuri kawai Allah ya nuna mana lokacin, ya kife wayar ba tare da ya ce wani abu ba, na gaji da kwanciya muka tashi muka yi wanka ni da Suhaila muka fito falon kasa Anti Hama ita kadai sai Ahmad yana ta wasa sai da na gama baiwa Suhaila abin karyawarta na zo na ce mata Anti Yaya Bashir yana barci ne? Ta dago kai a hankali ta ce tun ukun dare ya tafi Jos da sauri na ce lafiya Anti? Ta ce Ashiru ne ya yi waya ya shaida mishi cewar jikin Inna ya tashi, sulalewa na yi a kasa na soma kuka ina salati ina cewa wayyo inna wayyo Allah na, ke me za mu rasa ki kamar yadda muka rasa baban mu tasowa anti Hama ta yi ta rungumeni tana cewa haba Suhaila ki yi hakuri mana, inna ta yi rashin lafiya iri iri ba kyanan ta ji sauki wannan nan ma in sha Allahu zata samu lafiya, Suhaila ta kankameni tana tayani kukan da nake yi muna cikin haka mai aikin Hamamata ta soma shigowa da wasu manyan kwalaye tana shiga kicin tana ajiyewa ta koma ta dauko sai da taa gama ta zo ta tsuguna ta ce mata mutumin da ya zo ne jiya ya zo, ya ce in yimishi sallama da Anti Suhaila, ta ce to a shigo dashi na ce a'a Anti bari kawai in sameshi a waje mu gaisa ya tafi na tafirni da Suhaila, yana ganina ya zuba mun ido

Chapter 3 of 7