ya ce ni ce na zubar mishi, haba Suhaila ai ba
zai yi haka ba ai gara a gaya mishi don ya san abinda kike ciki na
soma yi mata kuka ta shiga rarrashina to yi hakuri Suhaila shi kenan a
barshi kawai ai shima da laiſinshi na yi zamana anan inna kuwa ta
shiga hidimata tana ina taka saka dani komai yi mun take yi ina jin
inda da hali ma da ta karbeni numfashin da nake yi, Hakcem yana
Abuja sai dai waya yake yiwowa yana tambayar yaushe zan dawo,
ina ce mishi kwanan nan ina lura mishi da asibitine ina tayasu aikin
jama'a ya bani Suhaila mu yi magana ta gaya mun yau baba teacher
ko baba Lamido ya kaita wuri kaza da kaza ya saya mata kaza da
45
Ashiru ta Kara haihuwa Lamido da kanshi ya kaini sunan muka yi
da
an
na
ga
na
ai
la
kwana daya muka wuce Abuja muna dawowa na fara zuwa asibitin
Garki awon ciki shi kanshi likitan mata na asibitin da ya ganni da ciki
Karamin murna yayi ba don kuwa dama kusan kullum sai mun zo
gabanshi ni da teacher kan matsalar rashin ciki kulawa ta musamman
samu a asibitin, kan harkar karatun kuwa na ci gaba da zuwa
jami'a karbar lacca, teacher kam hankalinshi da matsuwarshi suna kan
cikin danake dashi shima Yaya Bashir kusan hakane kowane lokaci
ai turo Anti Hama wai ta zo ta dubani, itama Hama zirga-zirga ya
semeta ta kai ta kawo, gashi dama teacher ya ki yarda da yawan ufiyc-taliya ko Jos zashi zuwa duba lafiyar Inna kamar yanda yake yi
aduk karshen wata tun daga lokacin da ya yi mata aiki baya yarda ya
je dani wai shi jami'ar da nake zuwa ma a dolene, kuma wai da yake
ya san yana da kyau in dan rinka motsa jiki amma ba mai tsanani ba,
tun cikin yana da wata shida Hakeem ya gama shirye-shiryenshi na
haihuwa a Gire da Abuja ya kammala shirya dakin jaririn kullum
yana baiwa Suhbaila labarin nan bada dadewa ba zata samu dan uwa
ita kuwa ta yi ta tambaya ta Antina zaki kawo mana sabon baby nc?
In ce in sha Allahu Suhaila, ko ciwon kaina ce ina yi zai kaim asibiti
cikina ya kai wata bakwai, ya yi girma sosai tamkar ba cikin kuruciya
ba, sati biyu na kara kan wàta bakwai din hakeem ya yi tafiya zuwa
Legos kwana uku kawai zai yi tafiyarshi dakwana daya na wayi gari
ina matukar jin nauyin jikina, fuskata, idanuwana da kafafuwana
gaba daya suka tattashi ban dai damu dahakan sosai ba saboda na
saba ganin mata masu ciki da makamancin wannan kumburin a ranar
da Hakcem zai dawo ne na wayi gari ina fan ganin alamar jiri-jiri
waya na yi Garki na shaidawa likitan da nake gani Dr Tijjani na gaya
mishi abinda yake faruwa cewa ya yi in zauna cikin shiri yanzu zai
turo a daukeni muna gama magana dashi na bugawa Anti Hama cikin
sauri ta iso, tarc muka tafi asibitin Dr Tijjani ya gama gwajin da zai yi
ya labbatar mana da ccwar dan dake ciki yana gicciyene bayan haka
kuma yana cikin matsala Yaya Bashir ya iso don jin abinda ake ciki
likita ya yi mishi bayani ina ganin yana da kyau a sanar da Hakeem
ko da dai yau zai dawo ina cikin fama da wahalar kokarin da ake yi
na gyara kwanciyar yaro sai kuma na samu da ciwon nakuda, haka
e
r
a
aka hakura aka zubawa sarautar Allah ido Hakeem ya iso asibitin
47
kusan sallar Azahar ne hankalinshi ya yi matukar tasbi ga balin da
nake cikı ga zullumin dan da za a haifar mishi wajen hudu da rabi na
yamma Hakeem yana cikin likitocin dake tsaye & kaina na haifi
sambalelen yaro namiji wanda girmanshi ya kai masu wata tara gashi
jazur sambalele gwanin sha'awa sai dai numfashi ya gagara babu
juyin da ba ayi da yaron ba ya yi kuka abin bai yiwu ba cikin banzari
Dr Tijjani ya fita dda yaron zuwa wani daki wai za su sanya mishi
abin taimakon numfashi Hakeem yana tsaye jikin gadon da nake
kwance yana rike da hannuna cikin wani irin yanayin da ba zan iya
bayyanawa ba ta ko ina gumi sai keto mishi yake yi har aka fito dani
daga dakin haihuwa aka kawoni inda zan kwanta, in huta Dr Tijjani
ba su fito daga dakin da suka shiga da yaron ba Yaya Bashir ma yana
wurinsu ni kaina a kidime nake ina son sanin halin da ake ciki na
kalli Hakeem a hankali na ce Lamido duba mana su mana ya yi
murmushin karfin hali ya ce babu amfanin zuwana Suhaila bar ni in
zauna kusa dake ganinki yana sanyaya min zuciya bana zaton yaron
zai rayu sai dai Alhamdulillahi tunda kina da lafiya, hawaye suka
gangaro mun a ido yayi maza ya sharesu ki yi hakuri Suhaila kar ki yi
kuka zaki sani cikin matsananciyar damuwa yaya Bashir ne ya fara
shigowa Dr Tijjani yana biye dashi ya iso inda muke a hankali ya cc
Hakeem sai mu yi hakuri Allah ya sa yaron ba wanda za a ci
amfaninshi anan bane sai mun je can tukuna sun yi iya kokarinsu har
ya dan fara numfashi yayi kamar sau biyar sai kuma ya tsaya, ka sani
kokari kawai ake yi amma rayuwa ta Allah ce, Hakeem ya ce haka
ne, ni kam kasa hakuri n ayi kuka sosai nake yi Dr. Tijjani ya kama
hannun teacher suka fita, Yaya Bashir ya matse kus adani yana mun
nasiha, har dai na hakura na yi shiru, an sallamomu mun dawo gida,
jama'a suka yi ta zuwa gaishemu ni kam kunci ya dameni cikin raina
tausayin wahalar tcacher na yi ta yi da irin yanda ya matsu ya samu
da gashi an samu namijin da yake nema, gashi bai rayu ba na tuna
haihuwar da na yi a gidan Shariftunda na yi cikin har na haihu Sharif
bai taba bata lokacinshi wajen sanin abinda cikin ke ciki ba, amma na
haifar mishi 'yar shi a raye, satina biyu dahaihuwa na nemi teacher ya
kaini wurin mahaifiyata bai yi musu ba, ina shiga falon Inna
kwanciya na yi a jikinta kukan da kullum nake daurewa bana yi agaban teacher don ganin da nake yi tamkar ya fini dmauwa kar in
48
mishi da yawan kuka ran nan kasa daurowa na yinaco wayyo
Inna ni karn ya ya zan yi? Duk wani abinda nako so mutuwa yake yi
nabarina, na shiga kuka sosai, yi bakuri Suhaila, hakuri ake yi,
huwar da ya mutu akwai ciwo to amma kuma akwai sakamako
i yawa ga iyaye masu hakuri da tawakkali, tsawon lokaci tana
wazikafin su teacher da yaya Ashiru suka shigo tare don dama
danya fara shiga, bayan tafiyar Yaya Ashiru Inna ta sake yi mana
asiha ni da teacher kan mu mayar da dukkan al'amuranmu ga Allah,
arokeshi alheri mu yarda kuma da duk abinda ya yi mana koda Lbanin abinda muka sone shi ne mafi alherin a garemu, kwana dayan
muka yi a wurin Inna mn samu cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar
ankali da karfin jiki muka dawo Abuja ni kam na koma zuwa jami'a
sukar karatuna teacher kuwa ya ci gaba da ayyukanshi shi dama ba
azauni bane, yawan aikine dashi ga duba marasa lafiya, masu ciwon
uciya a Garki gashi yana daukar dalibai masu karatun likita a jami'a
asibitinshi na Gire wanda duk karshen wata sai ya je ya duba
arasa lafiya da ciwonsu ya yi tsanani ga tafiye-tafiyenshi kan
kinshi ran nan teacher ya dawo daga London sati uku ya yi a can,
na kwance kan doguwar kujera wai barci yake so ya dan yi anan
ma ba mai yawa ba don yana son zuwa duba wani mara lafiya da
ke shirye-shiryen yi mishi tiyata a wannan satin.
Ina zaune ta wurin kafafunshi ina matsa mishi su kafin barcin ya
ukeshi sai na ce mishi ni kuwa teacher ina damuwa fa ban dai gaya
aka bane amma kuma abin yana kara damuna ya bude ido yana
llona tare da tambayar me ya faru? Na ce to ni tunda na haihu ban
al'ada ba balle in sa ran sake samun wani cikin amma kuma tun
ekaranjiyar can sai in ajin kamar wani abu yana mun motsi a ciki
kara zuba mun ido ya ce musu ne dake Suhaila tun kwanaki nake
miki ina ganin kamar kina da ciki kika ki yarda wai ke baki ma yi
ada ba tunda kika haihu sai ki shirya mu je Tijjani ya dubaki in na
ma da wannan mutumin sai in zo in sameki in ji abinda kuka yi, n
to ina kwance kan gadon fikita Dr Tijjani yana tsayc a kaina
van ya gama gwaje-gwaje da aune-aunenshi Yaya aka yi haka ciki
girma a jikinki amma baki sani ba? Na ce to ni bana jin komai
a kawai nake yi amma bani da wata lalura, ya ce to kiki wata hudu
ma 'ya'ya biyune na rike baki cikin mamaki n ace don Allah Tijjani
49
kar ka gayawa llakeem a barshikawaı ya san ina da ciki bana son ya
sake kwallafa ranshiakan cikin da yawa Dr Tijjani ya yi murmushi
ba tare da ya ce mun komai ba, Hakeem ya gama zaga marasa lafiyar
da yake dubawa a asibitin ya dawo ya sameni yaya dai Tijjani?
Abinda ya fara fadi kenan yana kallona yana 'yar fara'a Tijjani ya
tayashi murmushi ya ce to ai kaima dama ka san dashi Dr. Hakeem ya
cc a'a to ai ni an yi mun musu, Tijjani ya ce to akwai har ma ya yi
kwari don wajen wata hudu ne har da kwanaki, muna dawowa a
hanya tcacher yana zolayata har yau din nan fa ba ki cika wata shida
da wancan haihuwar ba, wannan karon dai ina jin gami da kasawa
kawai aka yi na ki kulashi, to ga Mr Biggs a gabanmu zaki shiga ko
kuwa mu wuce? Na ce a shiga zan shi shawarma, ya ce uhum ai kuwa
in banda nima da tun lokacin da na ga an tsananta mun aiken
shawarma har in na mance ayi mun fushi sai na sake fita na kawo da
tunlokacin kawai na soma lissafi, wannan cikin ya bambanta kwarai
da wancan gashi dai an gaya mun 'ya'yan biyune a cikin nawa amma
kuma garau nake ji na bana jin wani kasala ko tashin zuciya kuma a
yanzu ne na yarda da zancen teacher cewar mace mai ciki kafin ya
girma sosai tana da yawan bukata, kullum cikin tsala kwalliya nake
don in kara jan hankalinshi gareni, kowane lokaci cikin soyayyarmu
muke sai ko yawan barci mai dadi yawancin aikace-aikacen da da
nakc yi a yanzu Hakeem ya karbeni su Suhaila dai mai renonta ke
kulawa da komai nata, ni kuwa ran da na samu dama in yi mana girki
ni da mijina in ban samu ba in yi kwanciyata in ya dawo y ayi mana
in kuwa naga zai yi magana in langwabe in ce mishi ga wani abinda
na ji bai mun ba a jikina sai kuma ya shiga tambayar ko ya akaini
asibiti in ce a'a zan ma ji sauki nan da an jima, cikina yanagirma a
hankali a hankali, yana tafiya tare da watanninshi saßanin wancan da
ya yi girma na farat daya ya bayyana kowa ya ganshi cikin kankanin
lokaci wannan bin jikina ya yi sai dai ni da nake dauke dashi nina san
nauyinshi a wannan lokacin na shiga zana jarrabawata ta karshe ta
kammmala karatuna na digirin farko kan ilimin harhada magunguna
wato Pharmacy teacher ya yi iyakar yin shi wajen ganin ya taimaka
muna gidane ko a makaranta, kulawar da teacher ya nuna kan
jarrabawata mai yawa ce dake mun komai yayi ko wani dan aiki ya
zo ya samu in ayi karbewa yake yi ya ce je ki ki zauna Suhaila ko ki
50
C
E
Eha
ka
ha
tar
ka
da
kol
mu
shi
hat
ek
kav
mo
na
ma
an
un
kwanta ki huta an jima zan tasheki ki yikaratu ko kin manta gobe ko
jıbi za ki zana paper kaza da kaza, in ce to Hakeem ai wannan din ne
ya ce kawo kawo ki gani nima na iya zan yi miki ya karba yayi in
kuwa karatu nake yi to komai darc ba zai kwanta ba sai in nace mishi
na gaji zan kwanta in na bukaci wani bayani kan karatuna daga
wurinshi ya rinka yi kenan da baki da biro har sai na ce mishi na
gane, ya ce mun to fadi abinda kika ganen in ji, in gaya mishi уa сe с,
to na yarda kin gane saboda haka jarrabawa mai dadı na yi nayishi na
gama cikin kwanciyar hankali ba tarc dana gamu da wata matsala
data tayar mun da hankali ba, muna kammala jarrabawa teacher ya
shirya mun liyafa kasaitacciya don tayani murnar kammala karatuna,
'yan uwan, abokan arziki har daga Gire mutane sun zo da yawa,
cikina ya shiga wata shida da sati biyu ina kwance kan gadona shan
iska nake yi na bude windon nan dakin gaba daya iska sai kadawa
take yi, Hakeem ya fito daga toilet din dake cikin dakin nawa wanka
ya yi ya zo ya tsaya a kaina, Suhaila bude mun cikin nan in gani na
harareshi na ce tafdijan haka kawai kuma sai in bude maka ciki a
waje kayi ta Kallonshi shi ba kyau ba ba komai ba, ya ce bude mun
kawai kece baya miki kyau akwai abinda nake so in gani, na ce
menene ya ce to bude mun mana ni fa ban yarda da awon da ake miki
ba a ganina yara biyu ne a cikin amma kallum kika dawo na
tambayeki sai kice wai basu ce miki komai ba mu gani zan dubaki da
kaina na ce a'a teacher abinda na saba jin kana yi shi ne duba zuciya
da abubuwan da suka shafcta, amma ba da a ciki ba barni kawai in na
koma asibiti zan gayawa Tijjani ka ce baka gamsu da awon da ake yi
mun ba sai ya dubamaka ni ko ba haka ba? Na gama abinda zan yi na
shigo wajen tsuntsayen Hakeem ina watsa musu abinci sna ci wasu
har sauka a jikina suke yi don mun riga mun saba da juna, teacher ya
leko zo ki rakani nan Suhaila na ce to na yi maza na fito,jallabiya cc
kawai a jikinshi sai silifas din wanka na biyoshi na ga ya shiga
motarshi Honda 98 model, nima na shiga na zauna ina tambayarshi
ina zamu, bai cc komai ba, ya fara tuki sai gamu a gidan Tijjani
matarshi bata nan don haka a falonshi muka zauna, lafiya na ganka
yanzu? Hakeem ya ce lafiya Garki na yi nufin zuwa in sameka sai na
tuna kana gida so nake yi abinda ke tafiya game da cikin Suhaila, Tljjani wake lura da awon nata ne ni fa ban gane ba, Tijjani ya сc
51
kamar ya ya Hakeem ya yi mishi bayani Tijjani ya dan yi murmushi
sai ya ce ita ta hanani gaya maka biyune, Hakecm ya kalleni ranshi a
bace sai Tijjani ya ce amma fa ta yi haka ne don a baka mamaki
kuma wai ta rage maka yawan zumudin abin ina ganin taimakonka ai
ta yi ko kuwa? Ya ce to ni ba a burgeni ba, kuma har dakai dukanku
masu laifine, ya ce to na ari bakinta na nemar mana gafara ya ce to an
gafarta muku.
Duk da sanin da Hakcemya yi 'yan biyune a cikina komai a cikin
nutsuwarshi yake yi sabanin wancan karon da komai yake yin shi
cikin zumudi a yanzu ya fi maida hankalinshi wajen yin addu'o'i
rokon Allah ya in haihu lafiya yaran ma lafiya a wannan karon
Hakcem bai taba ambata abinda ya fi so ba ko ni ce na zolaycshı na
ce ace dai in haifi 'yan mata biyu masu kama daya da sai in yi ta yi
musu kwalliya iri daya su yi gwanin sha'awa, dariya yake yi ya cc
duk abinda Allah ya bamu muna so Suhaila, Allah dai ya bamu masu
albarka, in ce mishi amin, wannan lokacin Hakeem ya samu shiga
cikin kungiyar lafiya ta duniya "WHO" wato "WORLD HEALTH
ORGANIZATION" har ma sun nadashi wakilinsu mai kula da
jihohin arewa masu gabas guda shida Baushi, Borno, Yobe,
Adamawa, Taraba da Jigawa a wannan lokacin ayyuka sun iwa
Hakeen yawa ga tafiyc-tafiyc inna ta aiko mishi cewar ya malar dani
Gire in haihu a can kusa da ita ya ce a bata hakuri ta barni in haihu a
Abuja a babban asibiti inda zan samu cikakkiyar kulawa dani da
yaran duka don haka sai ta turo Sumaye wai ta zo ta tayani zaman
gidan, Sumaye jarumar tsohuwace wacce ko kadan baya son ganin
kazanta ksua da ita don haka na ji dadin zama da ita ba kadan ba,
cikina ya shiga wata na tara lokacin da takardun tafiya hidimar kasata
suka fito zan kuma yi ne anan Abuja dama abinda teacher ya nema
kenan, tare da teacher muka je hedkwatar 'yan bautawa kasar na yi
komai da zan yi a matsayina na sabuwar zuwa da muka gama sai
kuma muka mika takarda mai d'auke da sa hannun likita na umarnin
in huta a gado wato bed rest har sai na haihu suka amince.
Hakeem yana wurin taron kungiyar lafiya ta duniya wanda a
wannan lokacin ake yi a babban birnin kasar [Holland, taken laron a
wannan lokacin kuwa shi ne "Illar kanjamau ga tattalin arzikin
duniya.' Na wayi gari da safe ranar litinin ina ciwon mara da baya ni
52
kam na san nakuda tunda ba baihuwar farko zan yi ba ta uku ce don
baka kai tsayc na shaidawa Sumaye cewar nakuda nake yi Sumaye ta
so wai in daurc in haihu a gida amma ban yarda ba bawai don ba zan
iya dauriyar bane, a'a sai don sanin da nayi cewar matukar na zauna
na haihu a gida to ko jariran da zan haifarwa Lamido sune za su fi
kowadannen jarirai lafiya sai ya nuna mun bacin ranshi don kuwa
kullum a cikin gargadi yake ko juyi kika yi irin wanda baki saba
dashi ba ki yi waya a zo a duba ki ran nan wai ni zan zolayeshi na ce
haba Hakcem a gidan Sharif fa ni kadai na haihu a dakina kawai na
ga fuskarshi ta canza ranshi ya baci ya zuba mun ido kamar zai yi
mun magana ya kuma fasa ya juya zai tafi da sauri na bishi
durkusawa na yi na kama kafarshi taba nakc Lamido Allah ya huci
zuciyarka ban taba zaton ambaton sunan mutumin nan a kusa da kai
zai iya bata mka rai ba gani nake kasan komai ka san yanda aka yi na
shiga hannunshi kasan zaman da na yi a gidanshi ka san shi ne
mutum na karshe da zan zabarwa kaina to meye abin jin zafinshi?
Hannu biyu ya saka ya kama kafadura ya dagoni na tsaya ya ce duk
dahaka wani lokaci ya kan mintsini zuciyata Suhaila yawan sonki kan tilasta mun kishin mutumin duk da na san bai taba samun matsuguni
a zuciyarki ba, duk da haka gani nake tamkar ya zalunceni tunda ya
karbe mun budurcinki wanda ya kamata ace nawa ne na yi narai-narai
da idanu tamkar hawayc zasu zubo na ce amma ba haka muka yi da
kai ba Lamido na yi maka korafi tun farko cewar kana bukatar
budurcina ne wanda babu ya tafi ka ce mun ba budurcina ne
muhimmin abinda kakc son mallaka a jikina ba zuciyata kake son
mallaka muhimmin al'amari a wurinka shi ne kana sona ka kuma
sameni don haka ba zaka waiwaya baya ka kalli komai ba don ba zai
yiwu ka tuhumi kaddara dalilin da ya sa ta yi aikinta ba amma kuma a
yau kana gaya mun wai kana jin za fin budurcina da ka rasa alhalin ni
na sani budurcina a haka kawai ya tafi don shima bai mori komai akai
illa wahala da matsananciyar azaba, yi hakuri Suhaila na tuba Suhaila
ba zan sakc miki maganar komai na baya ba, Suhaila gaba kawai zan rinka kallo in har zan yi waiwayc tunda an ce shi ne adon tafiya to
zan waiwayoki ne a aji in tuna shiriritarki ke dasu Eze in tunaki lokacin da kullum sai na kawo mun sunanki cikin masu surutu,
murmushi na yi na kwanta a kirjin tcacher shi kuwa ya sa hannu biyu
53
ya kankamenıi, don haka na baiwa Sumaye hakuri na ce mu je asibiti
kawai awa uku bayan isarmu asibiti ina kwancene tare da jariraina
guda biyu na ce da namiji macen kamarta daya da Lamido ya dauko
tamkar kakinshi ta yi Anti Hama ta tasasu agaba sai kallonsu take yi,
Sumayc kuwa sai tasbihi takc yiwa Ubangiji tana cewa godiya ta
tabbata gareka ya Allah da ka azurta zuciyarmu da wadannan
lafiyayyun yara, a ranar kawai aka sallamoni muka dawo gida yaya
Ashiru da matarshi Sa'a har da yaran su gaba daya suka iso gidana
ganin yara muka sha hira sai yamma ya tafi gidan Yaya Bashir ya bar
Sa'a da yara muka kwana sai washegari ya zo ya daukesu akan sai
kuma suna shima Yaya Ahmad tare matarshi da 'yarsu Aisha suka zo
suka wuni suka tafi, Haka bata zo ba saboda mijinta bashi dalafiya,
Yaya Bashir kuwa da matarshi babu abinda zance musu sai dai Allah
ya saka da alheri hakika Yaya Bashir wa ne na kwarai dake rikidewar
ya zamewa kannenshi Uba tsayayyc mai tsarewa 'ya'ya dukkán
hakkuwansu, in kaga yanda 'yan uwan Lamido da iyayenshi kai in ce
ma danginshi gaba daya da mutanen garinsu ke ta zarya tsakanin Gire
da Abuja kai kace tafiya ce da fa bata fi 'yan kilomita kadan ba sai in
an ce maka nisan wurin ya kusa kilomita dubu ka rike baki don
mamaki abokan Hakcem suma ba a barsu a baya ba, sun nuna halarci
yara sna da kwana uku a duniya Yaya Bashir ya zo ya sameni kan
maganar yiwa yara huduba na gaya mishi bayanin da mahaifiyar
Lamido ta yi ya yi murmushi ya ce anya ayi haka Suhaila wannan ai
shi ne wani da tusa wani da karbe riga, na yi murmushi kawai ban ce
mishi komai ba, komai na shirye-shiryen suna ya kammala tamkar
Hakeem yana gida aka yi haihuwar gashi Yaya Bashir ya ki yarda a
aike mishi da labarin haihuwar wai abarshi kawai in ya dawo ya
gansu, su Tijjani tare da su Yaya Bashir suka isa Gire gidan kanin
mahaifin Hakeem sunayen da Yaya Bashir ya yi musu huduba dasu
su din aka sanya musu wato Ahmad mahaifin Hakeem da kuma
Zainabu Abu mahaifiyarshi, sa6anin yadda da Innarshi ta yi kara ta се
asa sunan Yaya Bashir dana Innārmu hidimar suna kam babu abinda
zan ce sai Alhamdulillahi, satinmu biyu innarmu tare da Hama suka
zo dubani zuwan Inna na farko dakina tunda nake aure na yi ta ina
naka saka dasu sumam suka yi ta yi da 'ya'yana har na rokesu sun
yarda za su kwana a wurina kawai misalin karfe takwas na dare sai ga
54
mota daga gidan Yaya Bashir an dawo mun da Suhaila da taje wuni
gidan kuma wai a tali mishi dasu Inna haka dole na hakura sai dai
kam gaskiya na zobara baki na yi ta korafi kan Yaya Bashir baya so
ya ji wani ya kwana a gidana, satinmu biyu da kwana uku Dr.
Hakeem Lamido ya dawo gida da asuba misalin karfe hudu da kwata
sun yi isowar darene, oyoyon da na yi mishi ya yi matukar girgizashi
daga baya kuma ya bashi sha'awa ya faranta mishi rai bai lura dani
sosai ba don aki sanya fitila mai haske sai da ya rungumeni a jikinshi
ya ji fayau nan da nan ya bar rungumar ya kai hannunshi cikin ya
shafa, Suhaila ina cikinmu? Na yi murmushi na ce ciki ya fiddo yaran
dake cikinshi tcacher mai jegoce nan a tsaye a gabnka ya sureni da
gudu ya nufi dakin da dama ya shirya don yaran "Alhamdulillahillazi
lamyahid ya lam ya lad wa alm ya kun lahu kufuwan ahad" Ma'ana
godiya ta tabbata ga sarkin da bai haihu ba ba a haifeshi ba, kuma
agareshi kadai ne bashi da abokin tarayya, irin godiyar data fito daga
bakin Hakeem kenan sanda ya ga 'ya'yanshi ya fara daukar macen ya
sumbaceta ya yi mata addu'a, ya tofa mata ko ina har a gabanta ya
tubeta gaba daya ya kare mata kallo yana fara'a tare da murmushi ya
ce wannan dai ni ne Suhaila bari kuma in ga malamin shima ya yi mishi yadda ya yiwa 'yar uwarshi ya tubeshi yana kallonshi dariya ta subuce mishi saboda ya kasa daurewwa ya ce Suhaila wannan ai Inna
ce ya ya aka yi haka? Ya juyo yana kallona ya sake cewa "Hamdan kasiran daiyiban mubakarakan fihi" Sannan ya mayar dashi ya kwantar ya zuba musu ido yana kallonsu ya ce to gaya mun sunayen da kika zabar musu da dalilin da ya sa kika yi hakan na ce wannan dai Hakeem ne wannan macen kuwa Suhaila ya-kyalkyale da dariya ya ce ban yarda ba ai sai ace mun yi rashin kunya za mu yi Hakeem da Suhaila amma sai a can gaba ba yanzu da sauri haka ba na ce to kai ka cika ya ce uhh ina jin dai wannan babana ne Ahmad mace kuwa sunnan Innar Jos Aisha in dai da nine na zabi sunayen abidna
Inna
zan sanya musu kenan na yi murmushi na gaya mishi sunayen da
sanya
ta
Ahmad
ce asa da yanda nima na baiwa Yaya Bashair shawarar ya
sunan iyayenka da Aisha shi kuma ya ki yarda ya ce a sanya maka
murmushin jin dadin
duka, ya cc wato Zainab cc anan a kwance na yi
ce to ALlah ya yi musu
karin farin cikin dana gani a fuskar teacher ya albarka Suhaila n ace amin, muna barin wurin
55
ga 'ya'yanshi da a yanzu haka su biyar ne banda Suhaila don baya ma
sata a lissafin