ki ji ta tashi ba tsufan da nayi
kinga kaina babu furfura ko daya, ya cire hularshi yana nuna mun kan
nashi nikam murmushi kawai nayi suka fita tare nacewa direba ina
kwana da sauri cikin girmamawa ya amsa yana kokarin yi mun
magana sai ga Yaya Ahmad ya shigo rungume da kaya bandir din
shadda mai yadi goma goma masu asalin kyau kala uku da atamfofin
mata kala shida da kudi naira dubu ashirin ya mikawa mai tasi yace
gashi in ji Yayanmu yace ayi maka godiya bisa taimakon da kayi
mana ko? Ya karba yana murna Yaya Bashir ya shigo ya mika mishi
hannu suka Kara sallama zai fita Yaya Bashir yace rakashi mana
Suhaila na bishi na yi mishi rakiya har wajen motarshi wai zai mun
wani bayani na yi murmushi nace ka gaida matarka na gode na juya
cikin gida, da yamma ran nan ni da Yaya Bashair da Hamamata da
Yaya Ahmad muka fita a mota daya sayayya yaya Bashir ya yi mun
har ban iya fadin irin kayayyakin da ya saya mun da muka gama da
kasuwa sai yacewa Yaya Ahmad wanda shike tukin motar ya wuce
damu wani asibitin ido nan ma idona aka duba aka bani magunguna
akace sati guda zan dawo.
Sati biyu Yaya Bashir ya diba yace su zan yi kafin inje Jos ganin
Inna. Cikin sati biyun nan kuwa sai gani na mayar da wara-waran Inna
a hannuna sun zauna cikin sati biyun nan ba karamin canzawa nayi ba,
zan ma iya cewa na dawo kamar asalin yanda nake kafin rasuwar
babana, ran nan kwalliyar da na yi zan iya cewa ban taba yin kyau
haka ba wara warai da zobunan zinari, sun kama hannayena ga 'yan
kunnc da sarka sun kama jikina sai walkiya nake yi atamfar Holland
mai ruwan bounbita na faura takalmina da jaka tare da gyalenta irinsu
daya gashi sai kamshi nake yi a ſalon kasa na samu Yaya Bashir a
tsaye cikin shirin tafiya Ilamamata tana sanya mishi link din rigarshi
yaya Ahmad kuwa tuni yana waje shi da dircban Yaya Bashir
Hamamata tana magana cikin yanayin shagwaba tunda yayanki yace
ba zai je dani ba Suhaila bari in aike ki wurin Inna na yi murmushi
nace to Anti llama da sauri ta haura sama sai gata da leda a nade ta
miko mun gashi kar ki bude abatashi a haka a kuma ce ina gaisheta
Ilama kuwa ki gata mata uwargidancin dana bata fani kafin in gama
9
cin amarcina zan karbe tunda sau biyu ina aike mata bani dalafiya har
yanzu bata zo ta dubani ba, na yi murmushi nace to sai mun dawo.
A unguwarmu naga abin mamaki yanda unguwar ta canza a
shekarun da na yi ban zo cikinta ko gidan da Yaya Ashiru ya dandasa
ya isa abin kallo a kofar gidanmu dircban ya tsaya gidan yana nan
kamar yadda na sanshi Yaya Ahmad ya nufi gidan Yaya Ashiru don
ganin mutane a kofar gidan yasa suka ce yana ciki ni kuwa nabi bayan
yaya Bashir zuwa cikin gidanmu Hamace a tsakar gdia ina jin Yaya
Bashir yana ce mata yau dai Allah ya taimaki Alhaji Ali na kawo
mishi amaryar da zata rinka zama mishi a gida ba kamar ke ba Hama
kullum sai kin fito kin zo gidan nan in anyi magana kice 'yarki kika zo
dubawa kafin ta mayar mishi da martini sai kawai ta gani wacece
wannan kamar Suhaila nayi murmushi nace Suhailace Hama ni da
Hama muka rungume juna Hama kam kuka take yi tana cewa Allah
sarki Suhaila ashe da rabon zan Kara ganinki a rayuwata a dakin Inna
kuwa na sameta zaune kan kujera suna gaisawa da Yaya Bashir yana
gaya mata labarin zuwa na ina shiga na durkusa gaban Inna na
kwanatr da kaina a cinyarta Inna ta dora hannu a jikina cikin farin ciki
tsawon lokaci suna magana da Yaya Bashir yana yi mata bayanin
komai da ya sani a kaina wanda da can bai gaya mata ba ya bata
labarin rasuwar Malam Ahmad abinda ya yi matukar baiwa Inna
tausayi har tazubar da hawaye suna hirarsu ni kama ina shakar
kamshin Innata ina tunawa da al'amura iri-iri an dan jima kadan nace
bari in je in ga Yaya Ashiru suka ce to.
Ina shiga cikin falon gidan Yaya Ashiru da Yaya Ahmad suna
tsayc cikin shirin fita Yaya Ashiru yana ganina ya bude baki cikin
mamaki rungumeni ya yi cewa Alhamdulillahi yau ga Suhaila ta dawo
gidansu kai Ahmad Yaya baka gaya mun tare kuka zo ba? Ina gaisawa
da Yaya Ashiruu yana tambayata yaushe nazo ina gaya mishi ina bashi
labarin yadda aka yi na dawo sai ga Sa'a tana shigowa rike da tire a
bannunta alamar wani abut a shiryo musu tana ganina ta kwallara ihu
tare da yin jifa da tiren dake hannunta, Suhaila da karfi ta sake kiran
sunanan muka rungume juna cikin farin ciki, kama hannuna ta yi ta
jani zuwa wurinta ta wuce falo muka shige can cikin dakinta muka
fadi kan gadinta Suhaila ta sake fadi Allah sarki ai yau din nan zan
vıwa Yaya Ibrahim waya in gaya mishi kin dawo ai bayan taliyarkı
10
kamar zai yi hauka, ta shiga bani labari iri-iri har labarin aurenta da Yaya Ashiru har tana mun albishir wai cikine da ita wata biyu, hira
sosai muka tsunduma kafin waya ta katsemu yaya Ashiru ne ban san
me yace mata ba na dai ji tana magana cikin hira da jan hankali tana
cewa na sani Yaya ban mance ba sai dai ina yi laifi sai ayi hakuri don
Suhaila ce ta sani ban san abinda yace mata na daiga ta yi murmushi ta ajiye wayar ta kama hannuna zo mu shiga kicin din sa'a ta hadu
hakanan itama ta iya girki. Kamar in kwantanta girkin nata da na
Hama sai kuma naga hakan ba zai yiwu ba don kuwa ita Hamamata
girkin mijina kawai take yi sauran mutanen gidan mai girki ke yi
musu, yayin da Sa'a take girkin mutane da yawa, na taimaki Sa'a ta
kammala nau'o'in abincin da ta shirya inda ta yi abinci hark ala hudu
dafa dukan shinkafa mai hade-haden kayaiyakin lambu, sai kuma
potato cheese pie, wanda ta yi amfani da dankalin turawa butter, kwai
sai fulawa 'yar kadan, datagama wannan sai ta hada 'curried rice, salad
inda ta yi amfani da shinkafar kwali madaidaiciyar kaza, jajayen
tumatur koren tattasai da jan tatasai albasa, kwai gishiri da curry dan
kadan daga karshe sai ta shirya 'fish noodle dish' wanda ta yi da danyen kifi manyan kwanuka ta samu ta zuba abincin a ciki ta
shiryasu kan firo tire yaya Ashiru ya turo aka diba daga gidan Inna har bayan La'asar ina wajen Sa'a muna ta hidimarmu Yaya Bashir ya aiko
maza inzo mu tafi da gudu na shuri takalmana na koma wajen Inna na
samu Hama tan ace mishi anya maigidan bazaka bar mana Suhaila,
kwana biyu bay ace a'a zamu tafi ina so in gama mata shiryeshirye ta
koma makaranta taci gaba da karatunta, sai ga Sa'a da lullubinta nace lah ban baki izni ba kika fito? Ta harareshi a kofar falon ta-tsuguna ta
gayar da Inna ta gayar da Yaya Bashir cikin girmamawa sai tace Yaya da nace ko zaka yi hakuri ka bar mana Suhaila sati daya sai in rakota
ta dawo, bai yi musu ba yace to Sa'a ta dan sunkuyar da kanta tace na gode ta tashi ta fita Hama tace uyu wannan da yake surukarka ce ai ka bar mata ita wajen biyar da rabi da shi da Yaya Ahmad suka tafi
rannan a gidanmu na kwana a dakin mahaifiyata akan gadonta ina kwance a bayanta muna hira muna baiwa juna labarin al'amuran
rayuwa iri-iri da muka gani washegari da safe nima na shiga gidan baban Sa'a na gaishesu na yi musu hira kamar yadda jiya suka zo mun da Azahar naje gidan Alhaji Ali sai dare yaya Ashiru ya zowa IHama
11
bira ya lasoni agaba muka dawo gdia tare rannan a gidanshi na kwana
tare da Abba don shima biyoni ya yi wai zai kwana tare dani ziyara,
sosai na yi tun daga 'yan uwa abokan arziki, kawaye har
makarantarmu naje mafi yawancin malaman dana sani suna nan sunyi
murna kwarai da ganina, ganin da na yi Sa'a da iyakacin gaskiyar ta
take yi zata mikewa Ibrahim da labarin dawowana yasa na lalla6ata
nace ke Sa'a kyale Ibrahim ya yi abinda ya kaishi kin dai san America
ban an kusa bane bashi da amfani ki gaya mishi gani bayan yana can
wata duniya kuma nib a aure zan yi yanzu ba, ina ganin ki bar shi
kawai ai zai dawo ya sameni, tace to shikenan a hirarmu da Hama ne
na ji labarin Hamamata cikine da ita har wajen wata biyu amma babu
lamar hakan a tattare da ita na kara yarda da kyan halittar Hama na
kuma yarda macece mai kamun kai da ņutsuwa sati daya na yi Yaya
Ashiru da Sa'a suka maidani Abuja gidan Yaya Bashir shima Yaya Ashirs ba karamar sayayya yayi mun ba har da wayar GSM ya hada
mun.
Na dawo na samu Yaya Ahmad ya gama mun shirye-shirye shiga Edtra Moral Classes don in yin karatun shirin zana jarrabawar gama
karatun sakandire wacce makrantarmu ta amince in je in zana a can, na
fara zuwa babu dadewa Yaya Bashir ya yi mun kyautar ban mamaki.
inda ya saya mun mota Honda Cibic sabuwa dal mai jan ruwa ya
kuma umarci Yaya Ahmad da ya koya mun tuki, zamana gidan Yaya
Bashir babu abinda zance mishi shi da matarshi sai shukura kullum a
tayashi tattalina take macece da iya zama da mijinta tasan abinda zata
yi ta kara karfin soyayyarta wurin mijinta tun zuwana gidan ban taba
ganin wani abu da tayi wanda ya sosa mun rai ba, Yaya Bashir ba
mutum bane, mai yawan dariya ba sai dai fara'a kawai amma in har
Hamamata tana kusa dashi to zaka jishi yana yawan kyakyatar dariya
ko me take gaya mishi oho? A wurin Yaya Ahmad ne kawai na ji
labarin wai a farkon zuwania ba wani kirkine da ita ba ta fara fito da
halaye iri-iri na rashin kirki sa'ar da muka yi kawai shi ne shi Yaya
Bashir da wai ba wni sonta yake yi ba, itace ta yi ta zaman jiranshi wai
har akwai wani lokaci da aka taba yin waya aka ce mata Inna bata da
lafiya amma bata gaya mishi ba, har aka wuni aka kwana, sai da aka
sake yi mishi waya yace ba a gaya mishi ba, day a kirata ya tambayeta
sai tace mishi wai mancewa ta yi shine yace aka gaya miki uwata bata
12
da lafiya kika mance? To jeki gidanku Inna dawo zan zo, bai je ba har
sati biyu suna ta aike da kyar Alhaji Ali yaje ya dawo da ita shine kika
ga yanzu komai take yi lafiya, lafiya na yi dariya nace lalle baka gane
tsakanin Yaya Bashir da matarshiba, daga yau kar ka sake tunanin ba
wani sonta ke yi ba in ka lura da kyau duk lokacin da zai ambaci jiran
da Hamamata tayi mishi yana matukar girmama lamarin banda
wannan in har tana kusa dashi bai iya rufe bakinshi shi dai irin
mutanen nan ne da bai yarda mace duk yanda suka kai da sonta ta
wulakana mishi iyaye ko 'yar uwa matukar su din basu ne suka zubar
da girmansu a wurinta ba, sannan a ganina Hamamata ko an aureta
akan ba a sonta tana da halaye da dabi'u da zasu sa mijinta ya sota ko
ba komai yanzun nan ka gama gaya mun tunda ta gane mijinta ba zai
lamunci a raina iyayenshi ba tasa hannu biyu ta rungumesu ka gani ta
nuna maka ita macece ta kwarai mai biyayya, uhun ke dai kina sonta
kawai in ji Yaya Ahmad na yi dariya muka shiga wata hirar.
Karatu sosai na shiga yi na addini dana bokon cikin watanni
bakwai na zamana gidan Yaya Bashir na zama tamkar ba bakar fata
bace ni saboda kyau ga ado da nake zubawa ga motocin da nake hawa
bayan Honda cibic din day a saya mun wacce zamana take yi gaa daya
motocin gidan babu wacce bana hawa inna yi ra'ayi abokin yaya kuwa
tunda a lissafinshi ya gane wai n agama idda kusan kullum sai yazo
gidanmu hira hidima kuwa da sayayya iri-iri, rannan ina shirya mishi
abinci don ya shaidawa Yaya Bashir cewa daga office yake bai koma
gida ba don haka yana bukatar abinci ina aikin ina jin yaya Bashir
yana ce mishi gaskiya Engineer ba wai bana son baka Suhaila bane ai
kai aminina ne na kuma sanka da kyau to amma abin shi ne tausayin
Suhaila nake ji tafi kowa maraicin ubanmu auren nan da suka yi mata
yawan rainc kawai ya fiddota a yanzu na fi son ta huta kafin ta sake
wani auren na gama shirya abincin na kawo mishi Yaya Bashir ya
tashi ya haura sama wurin matarshi wacce bamu dade da dawo daga asibiti ba saboda lalura irin ta maj tsohon ciki muna bira tare da Engineer Muhammad Yakub yana cin abincinshi yace ashe matar
Ashiru ta haihu har annyi suna amma da zaki baki gaya mun ba, na yi murmushi nace gani nayi kamar harkar suna ta matane, ya harareni
yace e da yake kina son yi mun wayo ba? To me muka samu? Nac
sunan babanmu aka sanay mishi, yace a'a to ai sai musa rana ki rakan
13
in gano shi nace ni ko wane lokaci a shirye nake in ka shirya kawai
kazo mu tafi yace to shakenan ran nan da asuba muka kai Anti Hama
asibiti tana cikin dakin haihuwa ni da Yaya Bashir ne a waje ina
kallon kaiwa da kawowar Yaya Bashir ina kallon yadda hankalinshin
yake a tashe ya kasa zama sai kallon agogon hannunshi yake yi yana
ganin lokaci na tausaya mishi na tuna rayuwar Sharif da matanshi
mutumin da don ance mish matarshi ta kwana tana nakuda a daren jiya
bai hanashi bin rakumanshi kiwo in ya tali kuwa ba zai juyo don yaga
abinda baya ta haifar ba sai lokacin dawowarshi na kullum ya yi gab
da za a yi salar walaha wajen karfe tara na safe aka shaida mana cewar
Hamamata ta haifi diya mace ni da Yaya Bashir muka shiga Yaya
Ahmad kuwa yana yin waya zuwa gida yana fadin haihuwar ban iya
fadin kyan yarinyar nan da murna Yaya Bashir, muma dukanmu
murna muke yi ban taba ganin yarinyar da nake so irinta ba, 'yan uwa
suka yi ta zuwa taya mu murna Inna ma ta zo ganin yarinya rana suna
Yaya Bashir ya rada mata suna Suhaila ni kam kidimewa na yi saboda
urna na kara sonta bani da aiki in ina gida sai na tattalinta ita kam
Hamamata tana wurin mijinta duk da yarta bata fi sati shida ba
wurinshi take kwana na tuna Sharif da aurenshi wai in cikin mace
yakai wata shida shi kenan bashi ba ita sia ta haihu ta yaye tukuna.
• Na rubuta jarrabawata 'sai dai sakamakon bai yi kyau sošai ba
credit uku na samu lissafi, physics da Islamic studies abinda na iya
samu kenan sauran darussan kuwa duka D1 ne da P Yaya Bashir kam
ya gamsu da abinda na samu a cewarshi wai ba karamin kokari na yi
ba in aka yi la'akari da dadewar da na yi ban yi karatun ba, gashi kuma
dama ba kammalawa na yiba don haka Remedial na Science na smau a
jami'ar Abuja nan danan n agama shiri na tsunduma na fara karatu a
jami'a. Rayuwata ta zamo wata sabuwa fil, samari ta ko ina bullowa
suke yi sai dai ban basu hadin kai saboda kullum Yaya Bashir a cikin
yi mun fada yake in har ya ga wani sabon saurayiu ya zo ba fa zan yi
miki aure yanzu ba Suhaila bana son ganin mutune suna zuwa wurinki
ko shima Engineer da kike gani yana zuwa dòn shi abokinane in yi
murmushi in ce mishi to.
Ran nan na dawo daga shan ice cream ni da Suhaila a cikin
motata Honda cibic da fita kuwa ba karmain kwalliya na yi ban a
kuma toshe idona da bakin madubi ina dosowa get din gidan mu na
14
hango Sharif da baba Ilamza suna farwa da maigadi ya barsu su shiga cikin gidan ya hanasu ina isowa maigadi ya bude mun get din nazo daidai wurinsu na zuge glass din motar na kalli Sharifnacc Mallam daga ina? Nan da nan ya zube a kasa yana cewa ranki ya dade taimakeni na biyo sawun matatane wacce ta gudo daga Bengazi na dai
gane Sharif bai ganeni ba shima kenan mijina balle kuma baba Hamza
dadi ya kamani na kalleshi nace kai kar ka kawo mana halinku na
buzaye matarka kake neman anan gidan? Maigadi kira mun 'yan sanda
su kamashi Sharif yana jin haka ya zube a kasa yana tuba wai inyi
hakuri shi kuwa baba Hamza da bai riga ya karaso ba yana jin an
ambaci sunan 'yan sanda ya karta da gudu, ganin zan yi dariya yasa
naja motata na shie gida bayan na baiwa maigadi umarnin ya shigo
dasu na dauki Suhaila na rungumeta a kirjina da sauri nah aura sama
na leka dakin Anti Hama wacce ke fama da laulayin wani cikin na
gayamata labarin zuwan su Sharif da abinda na yi musu tana dariya ta
tashi ta fita na ske saukowa na smau mai aikin gidan ta kawo musu
abinci suna ci na gaishesu na tashi na tafi, sai bayan dawowar Yaya
Bashir ya aiko a kirani muu gaisa da su Baba Hamza nace to na sauko,
na tarar Baba Hamza yana ce mishi ai tun zuwan mu Suhaila bata leko
mu ba ina zama Yaya Bashir ya soma yi mun fada nace mishi ai nazo
na gaishesu nice ma naje nacewa Anti Hama'sun zo Baba Hamza ya
zuba mun ido ai kece Suhaila kece kika bani tsoro da 'yan sanda kika
sani garin gudu har na buge gwiwa? Ya shiga nuna mun gwiwar yana kuka Yaya Bashir kuwa ya tunzura ya yi ta yi mun fada har ya koreni daga falon na yi tafiyata dama na fi son haka. Kwanansu bakwai a
gidan kullum nayiwa Sharif hira in muna zaune babu abinda yake yi sai kallona wani lokaci kaga har kamar yawu yana zuba a bakinshi sai in ya daurc ya yi karfin hali sai yace yanzu shikenan ni dake Suhaila? In cc ai watarana zanzo Bengazi, Sharif ko don in ga 'ya'yanka sai kuwa ya yi murna, ya ji dadi, Baba Hamza ya gayawa Yaya Bashir rakuman Sharif da yaci sune suak fi damunshi, yaya Bashir ya biya
alkairi
Sharif kudin rakumanshi yace ya sayi wadansu, ya kuma yi musu mai yawa.
aka nuna
Yaya Ashiru da inna ma haka ita kam IHama kuka ta yi ta yi da mata Sharif akace shi ne mijina na da, shi kam Yaya Ahmad yana Kaduna wurin da yake aiki tunda ya zo ya gansu suka gaisa ya
15
tafi bai dawo ba, na samu kanımala karatuna na Remedial da
gagarumar nasara na samu wucewa zuwa karatun digiri, inda zan
karanta Pharmacy, Anti Hama ta sake haihuwa mun samu da namiji
sannan Malam Ahmad ya ci nice kuwa na zabi sunan. Karatunmu na
zangon farko ya zo karshe har ma mun fara jarrabawa na fito daga aji
ran nan bayan na kammala paper ta cikin sauri na nufi inda na yi
parking din motata tarc da tunanin wayar da Engincer Muhammad
Yakub ya yi mun cewar a gidanmu zai ci abincin dare ina tunanin
abincin da zan shirya mishi sai naji daga baya na an kwala mun kira,
Suhaila Imam, na ja na tsaya a raina ina tambayar waye mai yi mun
irin wannan kiran? Na juya na hangoshi yana zuwa wani doon mutum
sosai yana da maidaicin jiki daya bashi damar zama ingarma fari ne
sol gashi da kwarjini, tafiya yake cikin kasaita, bangane shi ba,
Kasaitarshi kuma ta bani haushi na juya na ci gaba da tafiyata a
zuciyata ina cewa kaji mu mutum don Allah ya tsayar dani kuma zai
mun kasaita ko ina ruwana dashi oho. Na ji ya sake kirana Suhaila
tsaya mana, nace ai sai ka yi naja tsaki daidai lokacin dana dora
hannuna kan murfin motata zan bude in shiga sai kawai naji ya cire
hannun nawa a jikin kofar ya mayar da ita ya rufe jarumtakarshi ta ban
mamaki da haushi na dago kai cikin tsiwa muka haďa ido gabana ya
fadi kwarjininshi ya dan firgitani sai dai ban bari ya gane ba, ban
kuma fasa tsiwar da na yi nufin yi mishi ba, nace "Look who are you?"
Ya yi wani lallausan murmushi yace "I am no body." Ya sake
fadin Suhaila cikin wata irin murya data kadani, na yi karfin hali nacе
ba fa sunana kenan ba kuma da ka bani wuri don kar mijina yaga shiru
ya biyo bayana ya ganka ya dan motsa kafadarshi cikin gwanintar
nuna ko in kula sai yace bana tsoron mijinki zan kuma ci gaba da
tsareki anan matukar baki amsa kece Suhaila Imam ba kan iya kaiwa
gobe da safe muna tsayc anan ba dai zai zo ya ganmu anan yace
nayiwa matarshi fyade ba ko? Wane irin nacaccen mutum ne wannan?
Na tambayi kaina a ina ya taba ganina, a ina ya sanni? Tambayoyin da
suke zuwa mun zuciyata kenan, na sake dago ído da nufin in kara
kallonshi ko zan yi sa'a in tuna inda muka taba gamuwa, idanuwanmu
suka sake haduwa gabana ya sake faduwa, na ji ba zan iya ba, ba zan
juri kallon da yake mun ba na mayar da bakin madubina dake rike a
hannuna na toshe idona dashi don in rage karfin kallon nashi, ya yi
16
murmushi yace gara ki rufe idonki, Suhaila don ki jid adin bijirewa
gaskiya, ban taba zaton zaki iya bijircwa sanina ba, ya soma magana
cikin sanyin jiki da nadama na dauka saduwata dakc zata zamo abin
farin ciki da tuna al'amura da yawa, nayi ta fata tare da addu'ar komai
tsufa Allah ya bani ikon sake ganinki, jikina ya yi sanyi jin
maganganunshi na rasa me zan yi? Na kasa fahimtar wannan mutum,
Suhaila ya sake kiran sunan a hankali naga bani da bain yi illa in sauke
jin wani abu in tambayeshi kawai ya tuna mun inda ya sanni, nace ban
fa ganeka ba, yace ai ba zaki ganeni ba, saboda kin dade da mancewa
dani, kin dade da maye gurbina a zuciyarki, kin dade da mancewa da
cewar wata rana zamu sake saduwa, amma ni ban mance dake ba, ban
daina fatan sake ganinki ba, ganin dana yi miki jiya shine ya dawo
dani yau, ga zatona karshen bakin cikina ne ya zo, ban sani baa she
wani sabon babin ne zan sake budewa cikin rawar murya nace wallahi
ban ganeka ba, yace rantsuwar kice kawai zata sani in gaya miki ko ni
waye? Ya kalleni yana murmushi yace na yi amaki kuma raina ya baасі
da har kika iya mancewa da Teachern kin a primary four Hakeem
Lamido, habawa tsugunawa na yi a kasa na 6oye fuskata cikin tafin
hannuna cikin jin kunya mutumin da kullum nake fatan sake ganinshi
in gaya mishi nima na yi maraici naji yanda yaji naga fiyc da abinda
ya gani na rasa me zance mishi sai nayi karfin håli nace to ai kaine
Teacħer ka canza da yawa, ya yi murmushi yace abin kunya dai kin yi
shi ai canzawata bata kai taki ba, kefa tafiya nayi na barki ko kirgen
dangi baki gama ba, na sake jin kunyar maganar teacher, tsawon minti biyu babu wanda yace wani abu, sai yace tashi mana Suhaila tashi kar
ki yi dalilin da zan tabaki, inna zo dagaki tunda kince kina da aure ko? Nayi kokari na mike tsaye sai dai har lokacin bana iya hada ido dashi
saboda jin kunyar tsiwar da na yi mishi, na dan kawar da fuskata nace
ka yi hakuri teacher, yace haba Suhaila kar ki samu damuwa yanzu dai
tunda magariba ta kusa maigida kuma yana jiranki sai kije gida kar inyi ta tsayar mishi dake ai gobe ma kuan da jarrabawa ko? Na yi hanzarin cewa e, yace to gobe zan dawo da wuri don mu dan gaisa ko? Nace to yaushe kike da paper na gaya mishi da rana, yace to inzo kafin ku fara ko sai bayan kun gama? Nace ka bari sai mun gama, to na gode, sai da safe nace nima na gode kayi hakuri na shiga mota na tafi
na barshi anan yana tsayc ran nan gaba dayan daren kasa barci na yi
17
ga karatun jarrabawana na gobe ga tunanin teacher Hakeem a zuciyata canwarshi ta yi matukar ban mamaki komai nashi ya canza kwarmin idonshi ya ciko fatarshi ta zama fara sol maimakon wankan tarwada tsayinsi yayi matukar karuwagashi ya yikiba a haka na kwana gari ya
waye, wajen karfe tara na safe na kammala shirina kwalliya sosai nayi
ban san dalili ba ina son burge teacher wani yadi material mai ruwan
malmo na saka dinki buba, riga da zani da dankwali ya zauna dab a
jikina gashiu sai rawa yake yi, yana daukar ido na sanya takalmiuai
tsinin diddige tare da jakarshi da gyale iri daya hadin daya dace da
kayan 'yan kunne abin wuya wara warai da zobunan hannuna duka na
zinarene na fito dakina ina rike da jakata tare da littattafaina a hannu
Anti Hama ta fito daga dakinta zata shiga kicin ta kalleni tace kai
Suhaila wannan kwalliyar duka ina zuwa? Na yi murmushi nace Anti
kin manta ina da paper karfe goma, ta sake kallon tace kina nufin
jarrabawa kika yiwa wannan