An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MATTO DUNITA2Hoj. Halsat C. Sodangi
(Mrs Abdullahi Dabai)
WAYYO DUNIYA
2
Na
HAJIYA HAFSAT C. SODANGI
GODIYA
Har kullum godiyata ga Allah takc daya bani lafiya da
basira na rubuta wannan littafi, tsira da aminci su tabbata ga
shugaban manzanni Annabin Rahama SAW
TUKWICI
Wannan littafin tukwici ne ga masu karanta littattafai da
masu zuwa don mu gaisa, nag ode Allah ya bar zumunci, amin..
SADAUKARWА
Ga 'yan uwan masu zumunci da hakuri da junansu Allah ya
kara dankon zumunci da hakuri baki daya, amin.
Nuni hankalin mutanen dake cikin jirgin ya dawo kan Sharif T
wanda yake gab da yin kisan kai tarragon da suke ciki ya
cika makil da jama'a wani gabjejen katonc yake kokarin
banbare hannun Sharif daga wuyan matar nan yana yin nasarar hakan
kuwa ta zube a kasa sharaf alamar ya jikkata, shima Sharif din haki
yake yi yana numfarfashi na rantse in baki nuna mun inda matat take
ba yanzun nan zan karasa ki abinda yake fadi kenan cikin karfın hali
da jarumtaka don shima a gajiye yake. Ana cikin hakan ne na ji an
bude larragon da nake ciki ta baya na ji an kamo kafafuwana ana jana
cikina ya sake bada wani sauyin na kulululu saboda tsoro yana
fincikoni daga cikin buhunnan nan ya kama hannuna biyoni kawai
abin da ya ce dani kenan ban yi mishi musu ba, ya rinka ketawa da
gudu dani da cikin dajin dake bayan tashar jirgin nan kusan minti
goma sha biyar muna gudu bamu tsaya ba gab naked a sarewa in fadi
kasa saboda gajiya, ban sani ba ko ya gane hakan ne sai na ji y ace ki
kara hakuri ki kara dauriya wancan kauyen da kika fara hangowa nake
so in kaiki in suka kamamu bamu riga min kai ba to kashinmu ya zai
bushe wani sabon karfin ya sake zuwa mun gudu sosai muka yi har
muka iso kauyen nan bamu tsaya ba kai tsaye ya shiga dani wani dan
gida dake zagaye da kara da su aka yiwa gidan Katanga a jikin
katangar kuma bishiyoyin zogala ne gidan a share yak etas rabon da in
ga tsabta irin wannan har na manta ga wani shimfideden dutse mai
fadi can nesa an yi rumfa a inda yake da alama hutawa suke yi a wurin
muna shiga na ji ya soma kwala kira ina Ramatu take? Daga cikin
dakinta na ji t ace gani yau lafiya malam ya dawo gida yanzu? Y ace
to ki fito mana kya zauna a daki kina tambaya? Ta fito tana gyara
daurin zani sannu da zuwa malam tana ganina ta saki murmushi
bakuwa muka yin e y acc e, kawo mata ruwa ta shat a je ta dibo min
ruwa a randarta mai sanyi ta kasa ta kawo mun ta nemi wuri ta zauna
tana sauraron bayanin da mijinta ke mata, ya soma yi mata bayani tun
daga lokacin da naje wurinsu neman jirgi mai tafiya sadan, wandani in
banda na ji yace sun a tambaya ban san na taba ganinshi ba, da ganina
da ya yi lokacin da Hajiya takc sawa ana sanyani cikin tarragon kaya
da hirar Sharif da baba Hamza da yaji inda baba Hamza yake cewa ko
shakka babu in har suka ganni to suna komawa gida shi zai karya mun
kafa daya don kuwa na wahalar dasu, Sharif ya ce a'a dai yi mun
1
dukan tsiya amma kar a karyani shi za a bari da daiwaniya baba
Hamza yace sam duka wane iri ne ba a yi mun ba tunda bai san a
daina kokarin komawa gida ba to yanzu karyawanc ya kamace don
haka day a ga irin kamun kazar kukun da Sharif ya yiwa Hajiya ya
kuma tabbatar ko bata kaunar uwarta dolene ta nuna musu inda nake
shi yasa taga bai kamata ya bari in sake shiga hannunsu ba don haka in
gaya mishi gaskiya meke tsakanina dasu?
Na yi mishi bayanin komai tun rasuwar mahaifina zuwana
Bengazi da yanda Baba Hamza ya aurar dani ga Sharif mutuwar
Malam Ahmad da yanda Sharif ya dauko takardar sakin aurena ya
bani babu abinda ban gaya mishi ban a kuma nuna mishi takardar
sakin da Sharif ya bani ya karba ya gani ya bani na mayar cikin bujen
siket dina. Ramatu ta tashi ta kawo mun kunun tsamiya na karba na
kwankwada ya mike tsaye bari in koma Ramatu kar su gane bana
wurin su yi zaton ko ni na tafi da ita da ikon Allahzan samar miki
mota mai tafıya Sudan yau komai dare dare in Allah ya yarda za ki
koma cikin 'yan uwanki nace nag ode Allah ya saka da alheri yace ba
komai yarinya ai da na kowa ne ya fita ya barni da matarshi wacce
take ji dani ta tausaya mun kwarai nan da nan ta juye mun ruwan zafi
naje na yi wanka naji dadin jikina ta turara mana gurasa muka ci muka
sha ruwa bayan sallar La'asar sai ga maigidan ya dawo da saurinshi ina
yarinyar nan? Ramatu tace gata nan yace to maza fito zo mu tafi ga
motar katako na saman miki sai ki shiga ki tafi, nace to muka yi
sallama da Ramatu har tana kwalla muka kamo hanya ni da mutumin
nan yana gaya mun wai komawarshi ya tarar an sauke duk wani kaya
dake cikin jirgin nan wai ana nemana saboda Hajiya tace a cikin
buhuna tasa aka 6oycni da basu ganni ba kuma suka ce sam basu
yarda ba suka tasata a gaba wai zasu kaita gaban hukuma tashar mota
mutumin nan ya wuce dani daidai an gama lodin motar da yake shirin
sanyani a ciki ya kira direban wanda yarone matashi yace mishi ga
yarinyar nan dana gaya maka don Allah in kunje Sudan ka sanya mu
ita a mota mai tafiya Nigeria. Direba yace to ai babu damuwa ya
taimakeni nah au gaban motar na zauna muka yi sallama da mutumin
nan dircba ya hau mota ya tayar zamu fara tafiya na ciro kullin kudina
na kasar Libiya duka na mika mishi ya yi ta murna yana sanya mun
albarka mun iso Sudan kusan asuba tashar da nuka tsaya mahadacc
2
sosai ta garuruwan Alirka, muna shiga muka ji &na ccwa in amai tafiya
Kano Nigeria, direban motar dana zo wanda ya dan fita zageye ya
dawo yana rike da lcda baka da kaza gasasshiya a ciki mai dumi ya
miko min yana tambayata karamar mota zaki shiga ko babba? Nace ko
wace aka samu. Yace to in kina da isasshen kudin mota zo muje ki
shiga wancan Karamar tafiyar zata fi miki dadi, nace mishi to yazo ya
sanyani cikin Peugcout station wagen na zauna a ciki bayan na biya
kudin motar na kalli direban mai dimbin kirki nayi mishi godiya aka
samu ciko muka kamo hanya, gamu nan gamu nan har muka iso
Tashar Kuka a Kano anan cikin tashar na dauki shatar tasi, nace mishi
Abuja ya gaya mun abinda zan biya ban nemi ragi ba nace muje tare
da mika mishi katin yaya Bashir ya kalleni ya kara kallona yace to
kudi na fa ko sai munje can maigidan zai biyani nace c, yace to shiga
Asokoro ai ba karamin wuri bane ko baki da ko kwabo zan kaiki don
nasan ba zamu ace an rasa kudin da za a bani ba muka fara tafiya
direban mai dan Karen surutu sabanin wanda ya kawoni Sudan wanda
shi aikinshi kawai ya sanya a gaba, wannan son hira ne dashi sai
lambayoyi yake yi mun ya yi aka yi kika samu wannan katin? Nayi
shiru, waye kika sani a gidan Engineer Bashir Imam? Na sake yin
shiru ko kuwa babankine yake aikin gadi a gidanshi? Nace e, ya gyada
kai yace na yi muku murna don yazo Nigeria a sa'a tunda har ya samu
aiki a wannan unguwar, ya shiga bani labarin Asokoro da irin mutanen
dake zaune a cikinta. Ni kam shiru na yi ba uh babu uh uh, amma bai
hanashi yin magana ba cikin zuciyata nikam tunani nake yin a kubuta
kenan daga hannun baba Hamza da Sharif nan da dan lokaci kankani
zan sake saduwa da mahaifiyata da 'yan uwana da abokaina da Adah
na saba dasu, na matsu kwarai in sake ganin Innata bayan rabuwarmu
ta kusan shekaru uku da rabi bamu sa juna a ido ba to amma na sani gidan yaya Bashir ya kamata in sauka a yanzu shine madadin babanmu shi ya kamata in fara zuwa wurinshi shi ya kamata ya riga kowa sanin Allah ya kubutar dani daga wahalar da ya sameni cikinta shi ya kamata in dankawa takarda sakin aurena da Sharif.
Mun iso Asokoro bari in rinka bin gidajen a hankali ina kallon lambar dake rubuce a jkin katangar ba zance ki tayani dubawa ba tunda ke kam nasan baki san komai ba ko yaya kika ce 'yanmata,
wannan duka bayanin direban tasin da nake cikine bance mishi komai
3
ba muna cikin haka muka iso jikin wata Katuwar Katanga mai farin
fenti bisanta ya kai kafa goma sha uku can saman kuwa an zagayeshi
da sikiriti waya tsawonta a mike zata kai kafa dari biyu daga inda
muke bana iya hangen cikin gidan ya miko mun katin dana bashi ba
tare da ya juyo ya kalleni ba dubi lambobin dake jikin katin nan irin na
jikin katangar nan ne, ina ganin naci kudina na kawoki gidan da kike
nema sai ki fita ki kwankwasa kofar get din kinsan dai ba zaki turani
in kwankwasa get din gidan nan ba don ban iya tsokalar sama da
tsinke ban a tsaya na kalli get din gidan cikin zuciyata nace anya nan
ne gdian Yaya Bashir din kuwa? Ko kuwa an yi bata kaine aka baiwa
gidaje biyu lamba guda daya? Surutun mai tasi ya kutsc mun tunani ya
sani fita babu shiri na doshi katangar gidan inda naga get na dan
kwankwasa babu bata lokaci naga anzo an bude kofar maigadine wani
matashi majiyin karfi yana kallona sama da kasa na yi karfin hali na
tambayeshi gidan Engineer Bashir Imam nake nema ya sake yi min
wani kallon a lalace kafin yace nan ne lafiya? Wa kike nema? Na
hadiye yawun bakina kafin nace mishi matar gidan nake son gani, ya
sake kallona bana zaton zata ganki yanzu in dai ba itace tace miki yau
kizo ba don jiya ta dawo daga Canada ita da mijinta tun safe kuma
bata ga kowa ba, nace gaya mata bakuwace daga Bengazi ya juya ya
shiga gidan yana fadin zan dai jene kawai don naji ance maigidan
yana zuwa Bengazi amma ku sadakar yalla ai kun riga kunci ganye
kuma hikimomine daku iri-iri na rokon jama'a, daga bayana kuma
direban tasi ne yake kwala mun kina kina fa 6ata mun lokaci in sun
salami baban naki ne ki tambayesu in sun san inda ya koma sai kizo in
kaiki ina cikin sauraron maganar mai tasi na hangeta tana tahowa a
bayan mai gadin doguwar mace sanbaleliya wankar tarwada mai
asalin kyau kana ganinta zaka san lalle Yaya Bashir ya iya zaben mace
mai kyau tana isowa ta kalleni sama da kasa tun kafin ince mata komai
sai naji tace anya ba Suhaila bace a tsaye a gabana nace nice rike baki
tayi cikin mamaki kafin tace komai sai muka hango Yaya Ahmad ya
bullo ia daya kusurwar gidan da karfi ta kirashi Ahmad ga Suhaila da
gudu ya taho yana isowa ya sureni ya sabani a kafada ya juya da gudu
ya nufi cikin gdian Suhaila oyoyo Suhailar inna oyoyo Suhailar Yaya
Bashir oyoyo abinda yake ta fadi kenan tamkar wani dan yaro bai
ajiyeni a ko'ina ba sai da ya wuce dani ya kaini falon saman gidan
4
tukuna ya ajiyc Suhaila ya sake fadi daidai ya zauna a kasa a gabana,
Hamamata ta hauro tana dariya hala baka san ta gaji da gudun mota ba
kake wani gudun da ita? Suhaila ta ambaci sunana cikin fara'a walwala
da farin ciki lalle yau zan karbi goron albishir wurin yayanki don ni na
fara ganan mishi ke nayi murmushi ta sake cewa kai kinsha hanya
barka da dawowa gida na dai san kin dawo kenan, nace bakunta ta na
zo, tayi dariya tace ina ai yayanki yayi alkawarin koda Sharif kika zo
kasar nan ba zaki sake komawa ba nayi murmushi kawai ta juya cikin
sauri ta ſita shikam Yaya Ahmad kallona kawai yake yi mutumin da
yake na kara figewa a dalilin wahalar dana gamu da ita da kuma
faduwar gaba da nasha Hamamata ta dawo dauke da katon faranti cikc
da kayan ciye-ciye, iri-iri ta ajiye Ahmad hala baka san Suhaila tana
jin yunwa ba, dan bata wuri ta ci abinci mana nace zamu ci tare fara'ar
Hamamata da yanda farat daya ta nuna mun kauna tamkar ta dade da
sanina nace wai ni yaya aka yi kika ganeni daga ganina? Tayi dariya
tace lalle baki san yadda kike ba wurin yayanki ko ina a gidan nan
kina nan a samane ko a kasa, ko bayanki can kika duba kece a wurin
na juya na kalli inda take muna mun din hotona ne ni kadai ina tsaye,
na tuna lokacín dana dauki hoton a wurin liyafar da Ibrahim ya shirya
mun ne.
Mai gadin gidan ne yake ta sallama yaya Ahmad ya leka falon
kasa daga benen Yaya dai Malam iro? Ya tambayeshi bana jin abinda
yake fadi sai Yaya Ahmad kaga rashin kara ko? Mun shigo mun bar
mai taso din da ya kawo Suhaila a waje ka shigo dashi falon kasa yaci
abinci. Yaya Ahmad ya dawo yana yiwa Hamamata magana nikam ina
ta cin abubuwan data tara mun wadanda don dadinsu nake jin tamkar
bazan taba koshi dasu ba. Yaya Ahmad ya sauka kasa wurin mai tasi
Hamamata ta kama hannuna tace zo mujc ki shiga daki, dakin dala
kaini ya tsaru muka shiga ciki tace ina ganin wannan ne ya kamata ya
zama dakinki, ta wuce ta zuba mun ruwan wanka tare da turaren
wanka cikin ruwan daga nan inda nake nikam kamshin nake ta ji ta
ſito zata fita tace mun shiga kiyi wankan nace to ina shiga bandakin na
ganni cikin mudubiu na matsa kusa dashi ina kara kallon fuskata
wacce ta yamutse tamkar ta tsohuwa saboda wahalar duniya na
tambayi kaina ko yaushe rabona da kallon mudubi oho? Na kalli
tsunmokaran dake jikina na ciro kullun zinarina da kudina da wara5
waran Innata da takardar sakin aurena na hadasu wuri daya kayan ma
na saka su wuri daya, na shiga cikin ruwan nan na kwanta tun kain in
cuda jikina datti ya mamaye saman ruwan don an zute maganin fidda
datti a ciki na fito na zubar da wannan na sake zuba wani ruwan nayi
wanka na sake na kara har said a naji fatata tana santsi tukunna nan
take najini sakayau don rabon da in yi wanka irin wannan har na
manta ita fito na daura tawul din dake ajiye a toilet din na shigo dakin
tuni har Hamamata ta ajiye mun dogayen riguna cikin ledojinsu
alamar ba a taba sakawa ba har kala shida ga underwears a zube na
tsaya gaban mudubi da kyar na iya taje gashina saboda shi kanshi ya
manta rabon da yaji kum ya tabashi na zauna nayi shafa na gyara
jikina sai kamshi nake yin a zabi wata doguwar riga mai ruwan
madara tasha adon duwatsu a gabanta na rufe kaina da gyalenta nzyi
matukar yin kyau har na tuna da rayuwata a da kafin in rasa babana,
Ha mamata ta sake shigowa rike da kofin madara ta miko mun tana
murmushi ai mantawa nayi da na daukeki a hoto yayanki ya ganki
kafin kiyi waka nayi murmushi nace yaya Bashir ai ya ganni agidan
Sharif kin kuwa san Karewa kenan. Ta zauna ina shan madara muna
kara gaisawa ni kuwa bini-bini sai sunsuna jikina nake yi saboda
kamshin dake fita daga gareshi ice Suhaila nace kara jaddadawa
zuciyata don kar layi tantamar haka din babu ni babu Sharif abinda
nake ta gayawa kaina kenan, Baba Hamza kuwa ba zan taba gayawa
kowa abubuwan da yayi mun ba yayiwa kanshi da zumunci da ya
tozarta, a kofar dakina naji muryar Yaya Ahmad Suhaila ba zaki fito
bane ku, dan yi kira da wannan mutumin da ya kawoki? Nace kai rabu
dashi na riga na gaji da hirar tashi ba a sallameshi bane? Yaya Almad
yace a'a ai gara su gaisa da Yaya Bashir tukuna kafin ya tafi na dai
bashi kudin da yace kun yi tsada sai nayi mishi layin ko zai jira
maigidan ya dawo su gaisa tukuna? Yace to ni ka ina idar da sallar
isha'l na dare makadeden gadon nan na kwanta Ilamamata tana zaune
a gefe wai muna hira ai ban san lokacin da barci ya daukeni ba
mafarki irin wanda rinkayi ran nan suna da yawa har ban iya bada
labarin guda daya kwakkwara, Na farka cikin dare na jini daban
gabana ya fadi ina ganin ko dai a cikin barci nake mafarki sai dana
tuna ai na dawo gida na shafa filona na jike da yawun barci rabon da
a yi barci mai dadin wannan har na manta na kalli agogon dake sagale
6
1
a dakin karfe hudune na dare na daure na tashi na yi alwala nayi sallah
raka'a biyu na yiwa Ubangiji godiya da ya dawo dani cikin dangina
lafiya. Said a na idar da sallar asuba na sake hawa gadona zan kara
danashi sai ga Yaya Bashir shi da Hamamata dukansu sanye da kayan
barci sun shigo Hamamata sai lankwasa take mishi tamkar ta marce
ina wurin shima hankalinshi yana gareta, na tabbatar sudin suna
matukar sonjunansu yana fara'a tare da murmushi na dawo cikin dare
Suhaila Hama take ce mun kin dawo gida kuma ita ta riga kowa
ganinki hakane? Na yi murmushi nace hakane yaya. Tayi mishi wani
irin farin da tasa kunya ta kamani tare da cewa ato ai na gaya maka ta
fita, sai gata da kofin madara mai dumi ta miko mun na karba ina sha
muna gaisawa da Yaya Bashir yana tambayata yanda aka yi na dawo
gida, na bashi labari na ciro takardar sakin auren Sharif na mika mishi
na mika mishi zinarina da kudin dana iso dasu na kuma bashi labarin
rasuwar Malam Ahmad kusan awa biyu ni da Yaya Bashir ne kawai a
dakin muna hira yana tambayata abubuwa ina gaya mishi na dai yi
kokari na 6oye mugun halin Baba Hamza don kar in kara bata shi a
wurinshi ya bani labarin an yi auren Yaya Ashhiru da Sa'adatu na rike
baki cikin mamaki nace yaya aka yi? Yace to babansu Sa'a ne kin sani
mutumin nan babu abinda zamu ce mishi ya rike amanar dake
tsakaninshi da baba kusan ma dai ince miki shine mutumin da bai
juyawa gidanmu baya ba, na dawo kasar nan na samu Inna da Ahmad
cikin matsanancin hali Inna da Hama sun zama yau fari gobe tsumma,
na dai dawone ma na samu Inna cikin matsanancin rashin lafiya ga
Ahmad shi ne ya zama jagora a gida da kasuwa kuma ga karatunshi,
sai babansu Sa'a shi ne mai tallafawa zuwana ne al'amuaa suka soma
tafiya itama Inna ta dan ji dadi al'amura suka soma gyaruwa sai kuma
da aka ganni Suhaila wai lokacin ne tsofaffin abokai suka rinka zuwa
dubata to tun zuwana babansu Sa'a ya tuntubeni kan aurenta, naga ba
zan iya ba, ba don komai ba sai don zaman jiran da Hama tayi-tayi a
kaina wanda ina sane da irin kuncin data shiga a kaina, ana ganin taki
sauraron masu zuwa nemanta tana jiran wanda baya nan na kuma taба
yin waya da Ashiru muka yiwa juna ta'aziya bayan na samu labarin
baba ya rasu da yanda na ji labarin al'amura sai Ashiru yace mun yana
da kyau cikinmu wani ya auri Sa'a tunda an yi nufin hadaki da Ibrahim gashi hakan bai yiwu ba don mu kara karfafa zumuncin mu nace mishi
7
e, to sai dai ko shi don nikau ina da Hama, to dawowar Ashiru da na
yi mishi tuni kan hakan sai ya yiwa Alhaji Ali magana yaje ya tuntubi
babansu Sa'a babu wani bata lokaci aka sanya biki an yi namu babu
dadewa suma aka yi nasu nace to Allah ya sanya alheri nima na yi
murna da Yaya Ashiru ya auri Sa'a to yanzu yaushe zan je gida kenan?
Yace ai nan ne gidanki Suhaila nine ya kamata in zame miki uba sai
kin danyi kyan gani zan kaiwa Inna ke ta ganki bana son ta ganki a
haka, nama cewa Ahmad kar a gayawa kowa kinanan a bari a ganki
kawai yanzu dai an jima zamu fita zuwa zaga gari ko kin gaji? Nace
a'a ya tashi ya fita, tashi nayi na shiga wanka na sake bata loaci ina
goge jikina na fito ina shafa, na kalli mudubi ina gyara fuskata naga
kamar tadan ciko mamaki ya kamani yanda waji daga zuwana gida jiya
kawai har na dan canza na tuna tafiyata Bengazi haka na rinka
yamutsewa kullum na kalli mudubi sai na gane daga jiya zuwa yau na
kara ramewa wanda hakan ya tilasta mun daina kallon mudubi kwatakwata ban kuma sake ba sai jiya, wata doguwar rigar na sake sanyawa
mai ruwan malmo na gyara gashina na rufeshi da gyalen nan da nan
sai gashi wai har na fara yin kyau na feshe jikina da turare Hamamata
ta leko sai sheki take yi ta sha ado. Suhaila yayanki yana son ganinki a
falon kasa nace to cikin sauri na sauka falin Kasan dashi da na saman
komai nasu iri dayane su Yaya Bashir ne da Yaya Ahmad sai direban
tasi tare da wani abokin Yaya guda daya suna karyawa ina shiga falon
Yaya Bashir ya miko mun hannu zo nan Suhaila zo kusa dani ki
zauna, naje kujerar dake kusa da tashi na zauna abokin nashi ya
dakatar da shan tea din da yake yi ya rike kofin a hannu kar dai
kanwarka ta Bengazi da kake yawan magana a kanta ne tazo? Cikin
sauri yace itace Muhammad ni da nake ta fatan ko da bakunta tazo sai
gashi jiya tazo wai har da takardar sakin aurenta a hannu abokin Yaya
yace addu'a Bashir ai addu'a in dai kana yenta to Bi izinillahi Allah zai
kawo maka saukin al'amari hakane in ji Yaya Bashir ga bawan Allahn
da ya taimakeni ya kawo mun ita gidan nan tun daga Kano yaya
Bashir yana nuna direba shi kuma yana murmushi jin dadin an yabeshi
tamkar kyauta ya kawoni, mun gode kaji in ji Muhammad ya mike zai
tafi yacewa Yaya Bashir ni zan koma sai mun hadu in bakuwar ta hut
azan dawo mu gaisa sosai don tun wuri zan gaya maka ina ciki kar in
zo in yi magana kace na yi sakaci an rigani Yaya Bashir ya dan sha
8
mur yace a'a kar ma ka fara bazan baka ita ba don kuwa ka yi mata
tsufa, yayi murmushi yace ai rashin mutuncinka haka zaka hakura dole
ka mayar dani surukinka ke Suhaila kar