bad a ta ked a tarin ilmi kamar na tsohuwa
Hanifa.
Tsohuwa Hanifa ta kasance abin kwantace a
tsakanin al'uma tsohuwa me tsoron Allah gami da tarin
ilmi da kuma kokarin aiki da shi matar da ta maid a duniya
ba komai ba, ta kaskantar da kanta ta shagala wajen
bautar ubangiji mace me alkharii da kokarin kyautatawa
miskinai a ko da yaushe yabo ne a tsakanin ta da al'umma.
Zumuncinsu da hajiya Aysa da zuri'ar Alhaji Sa'ad
da zur'arsa danginta kai dama dangin mijinta sai kara karfi
yake dukkansu sun rikide sun zama dangi daya babu wani
banbanci ko sabani face kyautatawa da mutunta juna da ke
tsakanin su haka nan tsohon mijinta addu'a ce kadai a
89
tsakaninsu sakamakon kyautatawa gami da mutuntawar da
ya ke mata.
***** ***** *****
CIKA MAKIN LABARI
Har kullum addu'a ta fatan ubangiji ya jikan
mahaifana ya shayar da su ruwan alkausara a bisa ruwan
madacin da na shayar da rayuwar su. Tabbas jikina na bani
mahaifiyata ba ta a duniya Ina! Kwanaki sun hadu sun taru
sun haifar da tarin shekaru.'Yan uwana kuwa ni da su sai
dai a darus salam, in ina da rabon sake ganinsu kenan ni
Hanifa na yi kuskure na yi ksukure a rayuwa ta to Allah
gafurur rahim ne me yawan gafara da karbar tuba ina fatan
ubangiji jalla wa'azza ya yafe min kura kuraina.
Yan uwana dalibai wannan shi ne karshen labarina
kun ji irin gwagwarımayar da na sha duk a dalilin
SHARRIN ZUCIYA tare da d abin zabinta ina fata za ku yi
amfani da darussan da suke ciki masu kyau ku kuma yi
kokarin kaucewa masu muni, daga ciki.
Kada ku ksukura ku zamto masu kin bin umarnin
Allah tare da bijircewa iyaye.
Ni Hanifa abadan abidina ba zan iya taba mancewa
da kuncin da na haifarwa mahaifina ba wanda ya yi silar
ajalisan har ya bar duniya yana me kunshe da bakin cikina,
Tsohuwa Iya ta karashe maganar tana mai share hawaye.
Daukacin daliban yara da manya daga me share
hawaye sa ko me yin kuka shabe-shabe, kowannen su yana
me bayyana tausayawarsa. Tsohuwa iya ta lura da halin da
85
dalibanta ke ciki ta fara jawabi kamar haka `yan uwana
musulmi a duk halin da bawa ya kasane ya kasance me
hakuri da dogaro da Allah, kowane mutum da kuke gani
akwai irin kaddarar da Allah ya dora masa ama in banda
haka yarinyar da ta tashi cikin ingantacciyar tarbiyya tin
tasowar ta har yaushe na ta 6a tinanin hakan za ta faru gare
ni, to amma baka tara sani ga Allah abin da Allah ya
Kaddara wa bawa be isa ya hana ba, to tin kafin zuwan
bawa duniya tin yana cikin mahaifiyarsa lokacin da aka
aiko mala`ika ya busa masa rai ya rubuuta arzikinsa da
ajalisan da aikinsa dan wutane ko fan aljanna
Abu mafi muhimmancı shi ne ku ka ci gaba da taya
ni da addua'r neman gafarar ubangijı abadan abidin wannan
kam ba zan fasa ba. Sai abu daya da nake so ku gane a
farkon rayuwa tan a tashi bisa turba me kyau ma'ana na
aikata me kyau tsakiya tan a yi kuskure na aika ta badai-dai
ban a aika ata barna me yawan gaske karsehena kuwa Allah
Ubanigji ya shiriyar da ni ya dawo da ni bisa hanyar da tin
farko nake a kai hanyar da take abi sa siradi mustakim
nake kuma fatana ni da ku baki daya mu mutu a kanta.
Godiya ga Allah (S.W.T) da ya tserar da ni daga
cikin mutanen nan da Hadisain nan ke tasiri a kan su
"Ankarbo daga ABdurrahaman Abdullahi dan Mas'udu
Allah ya Kra yadad a gare shi ay ce....., Na rantse da sarkin
da babu waninsa cewa dayanku sai yai aiki irin na `yan
aljanna har sai ya kasance tsakaninsa da zuri'ar sai dai
kamu daya sai littafi ay rigaya a gare shi sai yai aiki irin na
'yan wuta saii ya shige ta, cewa dayanku yana aiki irin na
'yan wuta, bar sai ya kasacne tsakanisa da zuri'a sai dai
kamu daya sai littafi ya rigaya a gare shi sai yai aiki irin na
86
'yan aljanna, sai ya shige ta Bukhari da muslum ne suka
rawato wannan hadisi (Hadisi na 4 cikin arba'una hadith).
To me zan ce da ubangiji in ba godiya ba da ya
tserar da ni daga cikin kaso na farko, na sani a farkon
rayuwata na aikata me kyau a tsakiya zuciya da sharrin
shaidan suka rinjaye ni ga arkata mummuna a karshen
kuma Allah ya shiriyar da ni ya mai da ni bisa hanya
madaidaiciya, har kullum ina me addua'r ubangiji ya karbi
ruhina ya tsaida diga-digania ya bisa turbar da nake kai are
da daukacin musulmi baki daya ta ci gaba da cewa.
Mu yi kokarin tsarkake zukatanmu mu rinjaye ta
kada mu bari ta rinjaye mu, mu ci gaa da kokarin fin karfin
ta tare da forata bisa hanya madaidaiciya.
Idan kuka lura da kyau darasin mu nay au an gina
shi ne a bisa illar da SON ZUCIYA ke haifarwa ZUCIYA
BA TA DA KASHI ako wane lokaci mu yi kokarin fin
karfin ta mutan kwara ta zuwa ga nanya managarciya ubangiji ka ba mu ikon fin karfin zukaianmu amin suınma
amin. Tsohuwa iya ta ci gaba da cewa sai kuma gobe idan
Allah (S.W.T) ya ara mana numfashi in da zanmu zo muku
da wani sabon darashin ta sigar labari me nuni da illolin
HASSADA e haifarwa a duniya da lahira labarin zai
warware muku zare da abawa dan gane da wannan ciwo da
yake damun zukatanmu a halin yanzu wato HASSADA
wanda yai katutu a zukatan al'umar mu na wannen zamani.
Na kintsa na shiriya wajen kokarin zakulo muku
dalilan da suke haifar da hassada a zukatan bıl'adaına da
kuma kadan daga cikin illolin da koma bayan da hassada
ke haifar wa a rayuwar dan adam kazálika da hanyoyin da
za a magance su (Hakika hassada ciwo ne babba) duk zai
87
zo muku ne ta cikin sigar labari da zai ilmantar da ku gami
da nishadantarwa ku biyo ni bashi zuwa goben idan me
duka ya ara mana numfashi domin jin labarin ko kuma na
ce darasin da nai masa lakabi da HASSADA GA MAI
RABO........, sai mun hadu a goben kenan ubangiji ka
yarje min ka ara min nunfashi domin sauke nauyin da na
Saukarwa Al’umına a daidai lokacin falibai, suka amsa da
Amin suma amin.
Alhamdulillah Masha'allah tabarakallah.
Wassalamu alaikum wa rahamatullah.
ZUCIYA BA TA DA KASHI
CIKAMAKIN LABARI
BARAKALLAHU FINA WAFIK
ZAINAB KABIR BIROMAN
ADDU'AR TSARKAKE ZUCIYA TARE
KYAUTATA AIKI
DA
Allahumma tahhir kalbi minan nifak wa amali
minar-riyai wa lisani minal kadhibi wa aini minal-khiyanati
fa'innaka ta'alamu khainatal-a'yuni wa matukli fis-sudur.
ADDU'AR NEMAN TSARIN ALLAH DAGA
SHARRIN SHEDAN
Bismillahil-ladhi la yadhurru ma'asmihi shai'un
fitardh wala fis-samai wa huwas-sami'ul alim audhu bi
kalimatullahit-tanat min sharri ma khalak.
88
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
LAMARIN SO.. 1, 2, 3 & 4
ILAR ZAMANI 1, 2 & 3
KANGIN RAYUWA 1 & 2
JIYA BA YAU BA 1, 2 & 3
AUREN SADAKA 1, 2 & 3
KARYA TA KARE 1& 2
SAKAYYAA 1 &
ZUCIYA BA TA DA KASHI 1 & 2
PRINTED BY: AL-AMIN B/PRINTING & PUBLISHING COMPANY No.: 156 S/TITIN MANDAWARI KANO CITY. 08028411703.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels