da yawan
more amarci da amare kan yi bayan auren su (Hony moon)
hutun mako biyu ya dauka duk dan jin dadin rayuwar su.
Tabbas ba zai taba jin dadi ba mutukar ta zartar da warman
hukunci a kan idon mahaifinta yana cikin sharafa ta sakai ta
fice hannunta rike da 'yar karamar jakar matafiya.
Hanifa da Mas'ud suna can birnin ALkahira ta kasar
Masar domin more rayuwarsu, to a daidai lokacin da suke
tseka da aiwatar da sharholiya a dai-dai lokacin ne rai ya yi
halinsa ma'ana malam Sa'ad ya amsa kiran da duk wani
mahaluki me nufamshi sai ya amsa.
42
A cikin kwana bakwai da rasuwar Malam Sa'ad a
kuma ranar ne ake da niyyar yi masa addu'ar sadakar bakwai
da asubayin ranar ne Hanifa da Mas'ud suka dira a kasara
nan, nan din ma basu waiwayi gida ba sai bayan da sukai
masauki a Guest house dinshi tamkar su dawwama ahaka ba
sa son rabuwa ko kadan.
Misalign karfe goma sha daya na rana tai wa gidansu
tsinkaye. Dandanzon jama'r da ta gani a kofar gidansu shi ya
haifar mata da faduwar gaba a kidime ta shiga gidansu a daidai lokacin da babban limamin unguwarsu ke jagorancin yiwa
Malam Sa'ad addu'ar neman rahamar ubangiji.
Take ta yanke jiki ta fadi tana ihu da kururuwa ba
wanda ya ce mata kanzil har aka gama aka shafa to a sannan
ne daya daga cikinmakusantan babanta ya tsawatar mata gami
da umartar ta da Addu'a za ta yi masa ba kuka ba, amma ba ta
fasa ba tana rera kuka me karya jiki sai dai ga dukkan alama
babu alamun tausayawa a gare ta a lattare da zuka tan galibin
al'ummar da ke wajen, umma kan tan a sunkuye sai faman
kuka take yi bayan ta gama shafa addua'r da akaiwa mamacin
tsam ta mike kamar me shirin barin wajen babu wanda ya zata
sai gani akai ta kawo wa 'yar ta makure ta hada ta da bango
ta shake shakar da ta toshe mata duk wata kafa ta
numfashinta take idonta ya kakkate ta shiga kakari tamakar
me shirin barin dniya.
Cikin hanzari al'umar da ke wajen suka kawo mata
dauki da kyar da sidin goshi suka yi nasarar bambare
hannunta daga shakar da tai mata tana kuka tan a fadin ku
kyale ni ku kyale ni jama'a baku yi min adalci ba in kuka
hana ni aiwata da abin danake shizin yi meyc amfanin
yarinyar nan meye ribar ta a duniya ku kyale ni nai silar
ajalinta kamar yanda tai silar ajalin mahaifinta me yakashe
43
mahafinta in ba bakin bakincik;inta ba, rayuwar ta bata da
wani sauran amfani ba ni ba ke Hannifa ayau ina me bakin
ciki da takaicin fitowarki daka tsatsona na tsane ki tsaneki
yarinyar nan hakika rayuwarki bat ta dauwama kenan cikin
kunci da bakin cikin rayuwar kamar yanda su kikai silar jefa
mu.
To da kyar dai aka shawo kan Umma daga bakin da
take shirin yi ma ta (To tin yaushe ma). Tsawon lokaci kafin
ta dawo hayyacinta to sai dai ta farka cikn mummunan yanayi
abbin daya gudana ya dinga dawo ma ta daya bayan daya
yanzu shi kenan ta rasa mahaifitana babu abin d ya fi tsaya
mata a raiirin kalaman mahaifanta a na karshe a gare ta ashe
bankwana ne ashe shi ne karshen rabuwar ta da mahaifinta to
sai dai tana me jin zafin Ummanta dan me yasa za ta dora
alhakin rasuwar mahaifinta a kanta bayan Allah shi ke rayawa
shi kuma ke kashewa.
Da a son ran Umma Hadiza ne da ta umarci 'yar ta da
ta fice ta bar mata gidan sakamakon abind a ganinta ke haifar
mata to amma ba ta so ta zama me tirjiya ko rashin biyayya ga
dangin mijinta tin marigayi na da rai aka kasha wannan wutar
yai hakuri yai biyayya ga na gaba da shi to me zai sa ba za t
ayi koyi da me gidanta ba? To said ai fa gaskiya ita da babu
duk daya ne a gidan babu me shiga wurinta kamar yanda bata
isa ta shiga na sub a to ina ma tag a fusakar hakan ilahirin
Kannenta basu taba fushi ko jin tsanar 'yar uwarsu ba irin a
wannan lokacin tin basu da wayon gano matsalar da ke
tsakanin mahaifansu da 'yar uwarsu har ta kai ga sun fahimci
makasudin sabanin yanzu kam sun tabbatar da bakin cikin
'yar uwar su ne yai sanadiyyar mahaifinsu sun yi tur da 'yar
uwarsu sun yi fushi da ita fushi me tsanani.
44
Yanayin gidan ya sauya babu kwarafniya bare
hargowa ko yaushe za ka ji shi tsit saboda babban rashin da
suka yi alamun maraici ya bayyana a gare su karara barin
Umma da ako yaushe cikin alhinin me gidanta take da uwa
uba marayun Allah da aka mutu aka barta da su duk da eewa
‘yan uwan me gidanta suna temaka musu bakin gwargwado
duk da kasancewar suma din ba masu wadata ban e, to said ai
duk da haka rayuwar ta canja musu.
To sai me Hanifa ta dawo ruwa tsundum abin na su
kam kullum sai burunkasa yake kullum jiya ta fi yau abin sai
gaba yake ta kai ga har makwanni sai ta yi ba tare da ta leko
kofar gidansu ba galibi sukan tafi jahohin kudancin kasar nan
kai wani sa'ar ma har kasashen ketare suke ketarewa abin
kam babu dadin ji lamarin duniya akwai ban tsoro domin ko
in har mutuwar mahaifinta be isa karya gwiwarta ba a she
kenan ba muga abin dazai sa ta saduda ba.
Daukacin al'umma sun gaji sun gajiya da kwaroroton
halin da take ciki 'yan bani na iya abin fada ya kare a gare su
saura dame sun bar baje idanuwa tare da jian makoma.
Haka nan dangin mahaifinta lamarin na neman fin
karfinsu sun kasa hango hanya mafi suki da za su raba
tsakaninsu ga Umma kuwa ciwon zuciya na neman sarke ta
ciwon nan dai da ya kasha me gidanta wanan karan ma shi ke
addabar ta sakamakon bacin rai da bakincikin da 'yar cikinta
ta jefa ta, to ya za ta yi haka Allah ya shirya mata tsakaninta
da ita sai ido.
'Yan uwan mahaifinta ba daya ba ba biyu ba sun
umarce ta da ta fitar da mijin aure kamar yanda musulunci ya
bata dama a matsayinta na wacce ta taba aure.
Amsar nan dai daya ce a duniya ba ta da mijin aure
face Mas'ud dinta yayin da su kuma suka kafe suka nace
45
muddin ransu ba za a taba yin wannan aure ba kamar yanda
mahaifinta ya basu wasicci.
Lamarin dai sai du'ai wanda yai nisa baya jin kira irin
abin dake gudana a tsakanin wadannan bayin Allah abin kam
ya kazanta.
Kanta na sunkuye yayin da take fitar da hawaye masu
zafi, yanzu sabida Allah abin da yaya Hanifa tai mana ta
kyautawa rayuwar mu kenan, a gaskiya Umma ba zan taba
yafewa 'yar uwata wannan mummunan bakin fenti d ta goga
mana ba haba Umma makwanni biyu ya rage a daura aure
amma komai ya wargaje wane irin rashin adalci ne al'umma
take mana saboda Allah da me za mu ji ne a dai-dai lokacin da
kuka ya kwace mata.
Hankalin Uma yai mummunan tashi wane irin
kalubale ne yake fuskantar rayuwar ta da ta iyalinta ta runtse
ido tana me tunano kalubalen da ke fuskantar zuri'arta tun
bayan shekara daya zuwa biyu kenan 'yarta ta biyu wato
Nasiba yarinyar da ke biyewa Hanifa ta kammala karatunta
namakarantar gaba d primary a dai-dai lokacin ne watan bikin
Aurenta ke gab da kamawa suna shirye-shiryen aure ya gama
kankama an yi tanadin komai gwargwadon iko lokaci kawai
ake jira amma me? Komai ya wargatse cikin dan kankanin
lokaci tin bayan janyewaar iyayen angon.
A dalilin bakin fentin da 'yar uwarsu ta goga musu
tabbas duk me fatan samin zuri'a t gari ya zma dole ya
nemawa dansa mata ta gari d ta fito daga tsaftatacciyar zuria
amma ina lamarin 'yaruwarsu ya fata komai kacokan suka
dora lefin kan iyayenta, masu sake da sakaci da tarbiyyar
'ya'yansu to wannan takau saboda sanin ba yanda za su yi sai
dai tin daga lokacin babu wani tartibin tsayayye sa abu ya
knkama sai al'uma ta soke saboda haka babu wani tartibin
4-6
tsayayye har zuwa wannan lokacin, a wannan lokaci maganar
auren Nusaiba ta kankama to sai dai farin cikin Umma na
shirin komawa ciki tin bayan janyewar ango da kanshi tare da
goyon bayan iyayenshi abin da guda daya ne matsalar Hanifa
ba! Mafi muni daka cikinabin daake sukar su da shi shi ne
bazuri'a ce da za ka hada iri da su ba domin da zarar ka aure
su za su munafunce ka su haince ka kamar da yanda ya
kasacne ga 'yar uwarsu galibi abin daal'umma ke dogaro da
shi ke nan, to sai dai ba wannan ce ta fi bata ran Umma ba irin
kaskancin da wulakancin da dangin angon suka musu wani
abin ma sharri ne da kazafi, cike da damuwa ta fara cewa
Yanzu idan wannan aure ya kuma lalacewa ya y azan yi
kenan? Ta sa habar zani ta goge kwallar da ke shirin zubo
mata ta lura da hawayen da ke zubowa mahaifiyarta ta kada
kai cike da jimami Umma ki yi hakuri ki dena kuka, yayin da
ta ce gaba da cewa hakuri za ki yi Umma dan Allah ki de na
damun kanki da yawa. Dole in damu 'ya'yan nan yarinyar nan
ta cuce mu ta jefa mu cikin musifa mai yawan gaske nasiba ce
ta katse ta da cewa ba za ki san haka ba ma umma sai kin ji
irin cin zarafin da tonon sililin da al-kasim yai min ban taba
zaton haka ba ban taßa zaton zai rufe ido ya ci zarafina haka
ba ko me yaya Hanifa ta yi in za ai mana adalci ai be shafe mu
ba domin ba mu muka aikata ba ace har al'uma ta kai ga goga
mana wannan mummun nan bakin fenti yaya, ta cuce mu
wallahi za ki yi Mamakin surutan da ake yi a gari Nasiba се
ta katse ta da cewa, ya isa me yasa kike kokarin tayar da
hankalin Uimma ki bar ta kadai ma da abin da ya dame ta,
kyale ta Nusaiba gaskiyə ta fada in ba ta fada min damuwar ta
ba wa za ta faďawa ko ko meye bakon abu da idona be gane
min ba yarinyar nan ta cuce mu sai dai mu ce Allah ya isar
mana zuria' kam ta gama gurbata mana ita.
47
Duk iya tsare kai da kamun kai na iyalan Umma
Hadiza be sa al'umma ta goge musu bakin fentin nan da ta
shafa musu ba lefin nan dai na ‘yar uwarsu yana nan manne a
jikinsu tin ana samun me dan tayawa har aka rasa a halin
yanzu tsawon shekaru hudu kenan da tarwatsewar maganar
aurensu mafi muni a wannan lokaci babu ko me tayawa
al'umma ta kasa yi musu adalci. Bayan lefin wani baya shafar
wani to (Wake daya shi ke bata gari) wace tai silar faruwar
hakan babu abin da ya shalle ta duniyar tana gara mata yanda
ta ke so lamarin su da Mas'ud ya dada kazanta sai dai gyaran
Allah Umma ta gama yanke kauna ga lamarin 'yar ta illa
addu'ar ce dai bata fasa ba, tsakaninta da 'yarta ta cikinta
data tsuguna ta haife ta sa dai ido, ta rika ta tsaya kyam ta
inda babu me iya lankwasa ta tun sun zamewa junansu tamkar
musiba a tsakaninta da Mas'ud.
Irin halin tasku da bakinciki da 'yan uwanta tare da
mahaifiyarta suke dandana daga hannun al'umma abin babu
dadin ji Umma tai kuka tai bakin cikin kasancewar yarinyar
da ta ke janyo mata abin fada ta fito daga tsatsonta ne,
al'umma ta tsangame su ta kyamace su duk a dalilinta sun
zama abin zunde da zagi daga bakunan al'umma tai kuka tai
kakaici hart a rasa nda za ta saka kanta ga lafiya da ta kasa
inganta sakamakon bakinciki da yai katutu a zuciyarta.
A dalilin diyar da ta tsuguna ta haifeta ta rene ta ta
kuma sha wahalhalu da ita amma a yau gashi ta jaza mata
ciwo me wuyar sha'ani wato CIWON ZUCIYA. baya ga
hawan jinin da ke addabarta haka nan ragowar 'ya'yanta
kowanne na cikinmatsanancyar damuwa alal hakiika basa
cikin hayyacinsu da ka gan su za kai amannar basa cikin
koshin lafiya duk da cewa ba ciwo ne da ke addabar gangar
4-8
jikinsu ba ciwon ya na nan a karkashin ZUCIYArsu
sanadiyyar bakin cikin da'yar uwarsu ta jefa su.
Umma ta hanga ta hangi idan har haka zasu ci gaba da
zma cikin wannan hali hakika ba karamin kalubale za su ci
gaba da fuskanta ba a rayuwa to mcye abin yi? Ko ko ina
mafita? Tai nazari ta hanga ta hango mafitar nan dai da ya се
saura dame? Shawarar ta rage tsakaninta da 'ya'yayenta.
Matsanancin tunani ya sarke umma Hadiza cikin
talatainin dare baccin take ji amma zuciyarta ba za ta bari ta
runtsa ba. Sakamakon nauyin da aka aza mata wanda ta kasa
daukewa a duniya akwai mutumin da ya fita shiga kuncin
rayuwa? Shin akwai mutumin da ya fita kunyata a iidanun
al'umma? Amsa ita ce babu a duk lokacin da tai tinanin
hakan.
Shekara da shekaru tana cikin kunci gami da takaici
da bakin ciki rabon ta da kasancewa cikin kwanciyar rai tin
kafin wannan abin kunyar ya bayyana
Lamarin da ya haifar da ajaliyyar me gidanta kazalika
yake shirin yin ajalinta ita kam bata ta kan ta tafi matsuwa da
halind a ragowar 'ya'yanta masu jin kai suke ciki hakika ta
gama sallamawa rayuwa, da alama haka za ta dawwama cikin
dawwamammen bakin cikin da 'yar cikinta ta sanya ta ciki.
Take kuma shirin dawwamar da 'yan uwanta cikin
wahala da kuncin rayuwa ya zama dole ta samo mafita ko don
ta temaki rayukan bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba
babban takaicinta yanda har kawo yanzu suka kasa auruwa
ba kuma wai don basu da maneman ba a'a illa dai dan kawai
lefin 'yar uwar su da ya shafe su ta kan yi kuka har ta gaji ya a
duk lokacin da ta tina da manyan 'yan matan da ke gabanta.
Tabbas mutukar suna a wannan matsayi sun
dauwwama kenan cikin bakinciki hawaye ya ci gaba da zubo
69
mata lokacin da ta tina hukuncin da ta zartar wanda take ganin
shi ne kadai mafita bawai dan jin dadin rayuwar ta ba wannan
kam tin yaushe illa dai ingantuwar rayuwar zuria'rta tai kuka
tai takaici saboda kudurtar aiwatar da abin daba ta taba zato
ba a rayuwar ta.
Misalin Karfe tara na dare Hanifa tai kwalliya ta fitar
hankali domin daren yau za su raya shi ne a Guest house din
Mas'ud ta zo ta gifta ta gefen mahaifiyarta.
Sannu Umma sai na dawo zan je gaishe da Inna lami
ne wato 'yar uwar babansu wanda a zahiri Innar ta san ba
haka ba ne za ta tafi yawon sharholiyar ta ne to da'yake ta
tsame hannunta da ka kanta ba ta ce mata kartzil ba illa wani
kallo da ta bi ta da shi me cike da ban tausayi ita kanta ta ji
wani irin abu yarır. A jikinta kallon da ba za ta iya
mancewa da shi ba muddin rayuwarta amma dai da yake ba ta
iya ketare lamarinta da Mas'ud sai kawai ta kada kai ta tafi
abin ta.
Ba ita ta dawo ba sai wayewar gari lokacin har rana ta
bullo kai tsaye ta shigo cikin gidan ga mamakinta sai ta ji ko
ina tsit kamar gidan makoki a zatonta ahalin gidan bacci suke
kai tsaye dakinta ta shige kaya kawai ta cire ta fada kangdo
saboda gajiya sai misalin karfe uku na yammaci ta tashi kai
tsaye toilet ta nufa bayan da ta gama gabatar da duk abin daza
ta yi to fa a nan tinanitana ya dawo wai shin ina Umma ne?
kai dama sauran al'umar gidan? Zuciyarta ta ba ta amsa sun je
wani biki ne ko wani sha'anin to amma yaushe rabo? Yaushe
rabon Unma kai ko 'yan uwanta da shiga wani taro?
Sakamakon abin fadin da ta ja za musu karan farko ta ji ba
dadi ta tuhumi kanta da rashin kyautawa hakika bata
kyautawa mahaifiyar ta dama 'yanuwanta ba.
50
Har bayan sallar isha'I babu su babu alamarsu to daga
nan ne ta soma shiga damuwa, dakin mahaifiyarta ta fara
dubawa ga mamakinta sai t ji kofa wayam ta bude da sauri ta
fada ciki gabanta ne ta ji yai mummunan faduwa zuciyarta ta
shiga bugawa cikin matsanancin tsoro da fargaba sakamakn
abin dindaunta ya gamne mata wato dakin wayam babu komai
sai tsofaffin furnitures da suka rage a dakin sai ko 'yan
tsurarin wasu abubuwan masu girma wadan da za su yi
wahalar daukuwa, amma duk wani nau in suttura da ke dakin
babu shi kabet din ma a bude take wayam a kidime t a nufi
dakiu kannenta, tsohon dakin mahaifinsu kai dama duk wani
sako da lungu na gidan abin dai da ta gani a dakin
mahaifiyarta shi ta ci gaba da gani.
Komai na gidan a tarwatse kai a yamutse ma babu
wasu sauran kaya masu amfani sai tarkace wai meke shirin
faruwa ne?
A dai-dai lokacin ne idanunta ya kai kan wata katuwar
ambulan (Envelope) a gefen windon dakinta cikin
matsanancin sauri ta bude zungureriyar takardar da ke ciki ta
fara karatun karm haka:
Zuwa ga 'yata wacce ta bijirce ta karkace daga
mikakkiyar hanyar da ke turbar gaskiya da muka sanya ta a
kai. da farko kafin na fara cewa komai ina so in sheda miki
tun da nake a rayuwa taban ta ba tinani ko zaton wani daп
adam ziia sanya ni cikin kuncin rayuwa ba irin haka sai dai
ashe ban sani ba 'yar ciki n ace za tai silar jefa ni cikin kangin
da ban taba zato ba, kyawawan akidun da muka dora ki a kai
duk sun tashi a banza har said a kika sanya kanki cikin halaka,
zina da aurcnki, kai tir da wannan halayya kin keta haddin
aure bakika Allah ya na me fushi da ke mutukar baki tuba
kin koma ga turbar gaskiya ba malaifinki ya mutu da bakin
52
cikinki m da 'yan uwanki kin jela mu cikn msuba me yawan
gaske ba sai na sha wahalar bayyana miki abin daya faru ga
"yan uwanki ba domin kin fi mu sani wanda duk ke ce sila.
Al'umma ta kyamace mu, ta tsanemu, ta kasa yi mana
adalci, dan haka nema na yanke shawarar barin Kasar nan baki
daya, ba wai dan na tsira daga abin kunyar da kika sanya mu
ciki ba illa dai kawai dan rayuwar 'yan uwanki ta inganta
kunya kam, Hanifa kin gama bamu ita babu abin kunyan da
va fice wannan aikata Zina ba ga macen da take da aure.
Wa'iyazubilah! Shin akwai abin kunayar da ya fice wannan?
Kar ki sake ki yi yunkurin neman inda muke ni da 'yan
nwanki har abada ba za ki taba gano inda muke ba kar ki yi
tinanin zan huce kasata ta haihuwa ne (CHADI) sam kar ki yi
zaton ahaka na rantse da wanda raina ke hannunsa ni da kaina
ban san inda muka nufa ba.
Muna dai addua'r ubangiji ya yi mana jagora a bisa
duk inda muke ya kuma zaba mana masaukin da ya fi alkhairi
a gare mи.
A Karshe Inai miki nasiha da ki ji tsoron Allah ki tuba
kii bar aikata sabo, domin samun tsira ran ogbe kiyama na
yafe miki indai nice na yafe miki
Sai dai kash! Kar ki mance kar ki taba mancewa
mahaifinki ya mutu da bakin cikinki har ya cika ya na me
bakin cikn balin da kike ciki tabbas maghaifinki yakunshi
kunshin bakin ciki a dalilinki shin ya za ki yi da wannan
hakkin bawan Allah?
Allah ya shariye ki ya shirivar dam u baki daya abi sa
hanya ma daidaiciya Allahumma amın
Daga Mabaifiyarki
Uinme Hediza
52
Cikin rudani da matsanancin firgici ta kwalla
matsananciyar kara gami da ihu da kururwa abin daya ja
hankalin makwaftan gidan juyin duniya ta ki fadin me ke
akwai sa ihu da kururwa abin daya dada jan hankalina
mutanen unguwar da kyar suka iya shawo kanta dan jin me ke
akwai. Malam Mudi makocinsu na kusa shi ne ya fara cewa,
baki da kaico yarinya, wallahi baki da kaico kin cuci kanki
kin 6ata rayuwarki kin saka mahaifanki da 'yan uwanki cikin
musifa mahaifinki ya mutu da bakin cikinki amma baki
saduda ba jibi masifar da kika jazawa 'yan uwanki ba dole su
yi kaura ba ko sa tsira daga masifar da kika sanya su a ciki
yarinya ba ki ji dadi ba kin cuci rayuwarki, to fa abin dake fita
daga bakunan al'umma kenan.tsawon kwana da kwanaki tana
cikin damuwa babu ko duriyar Mahaifiyarta bare 'yan
uwanta, ta shiga cikin damuwa ainun damuwarta ta saukakа
ne lokacin da ta hango mafita tabbas wanan ita kadaiçe mafita
a gare ta aurenta da Mas'ud ba. Sannu ahankula dai komai ya
warwarewa Alhaji Khalil Mahaifin Mas'du na daga halín da
dansa ke ciki yai bakin ciki gami da takaicin halin da dansa
ya tsundunma kansa ciki. Mas'ud ya fuskanci 6acin ran da be
aba zaton zai fuskanta daga wurin mahaifinshi ba hakika ya ji
ba dadi a karshe ya dauki tsattsauran mataki a kan dansa
wanda yake ganin shi ne kadai mafita.
Zabi na karshe da ya ba shi shi ne a cikin sati daya
kacal ya fitar da macen da zai aura ko kuma shi Alhajin ya
zabar masa duk wacce ya yi ra'ayi wannan shi ne dama ta
karshe a gare shi Mas'ud ya shiga matsananciyar damuwa
saboda rashin shiriya aure a dai wannan lokacin da yake kan
ganiyar sa to wace mace ya kamata ya zaba?
'Hanifa' ya tambayi kansa yayin da zuciyartsa ta bashi
amsa da cewa sam ba ta dace da macen da ya dace ya ajiye
53
matsayin matarsa uwar 'ya'yansa ba yana san ta yana fatana kasancewa tare da ita to amma sam ba zai iya auren ta ba kai
duk wani abin dayake bukata daga gare ta ya ruga ya samu anya ko dama ba sha'awarta ce ta rinjayi son da yake yi mata ba, ya tambayi kansa to wan aure ne kuma zai shiga tsakaninsu? Dukkanin su rayuwarsu za ta fi inganta a irin matsayin da suke kai a ta kaice dai ya mai da ita abar hutawarsa butulci ne ko cin amana?
To ko dai da gasken sha'awar ce ta rinjayi son da yake mata? Suhaila diyar wani kwara me tsatso daga kasar Labanon ita ce macen da ya fitar amatsayin matar da zai aura yarinyar da suka shafe tsawon lokaci suna aiwatar da soyayya
a munafunce to sai dai fa kar da kiyashi ce (Daukar mara sani) domin tan dauke da cutar nan ta alaka-kai {KANJAMAU} ko kuma (AIDS) cikin dan kankanin lokaci komai ya kankama duk wani shiri na Alhaji ya kammala saura da me wayewar gari aka daura auren Mas'ud da Suhaila Nabil a daren ango da Amarya suka dage zuwa kasar japan inda mahaifinshi yai mishi cuku-cukun sama mashi aiki a babban kamfanin kera motoci na Honda.
A yai ta tashi cikin matsanancin farin ciki sakamakon
hukuncin da ta gama zartarwa zuciyarta tabbas ba ta san irin matsanancin farincikin da za ta shiga ba a ranar da burinsu ya kammala, to fa shi kenan duk wani kunci da take ciki ya kau
to wane buri ta ked a shi da ya wuce na malalkar gwarzon zuciyarta saura da me? Nemo mahaifiyarta dama sauran 'yan
uwanta shi ne abu na farko da za ta fara aiwatarwa da zarar
auren ta ya tabbata da Masu'd.
Office, Guest house, kai da ma duk wata mahadar da
suke haduwa ta je ba ta gan shi ba bata ga ko me kama da shi
ba ta kira wayarshi sau ba adadi completely ta ki shiga
54
tabbatar layin baya kan wayar ta dawo gida a gajiye cike da
damuwa a dai-dai lokacin ne wani dan matashi ya shigo
dauke da sakon zungureriyar takarda.
Ta karbi takardar taname juya ta sai kuma a ka ce ni
Hanifan za ka bawa? Ya daga kai alamar gasgatawa Eto.
kusan hakan ne mutukar dai ke ce me dauke da wannan
sunan, to wai waye ya baka takardar?
Wani mutum ne fari dogo ya zo a cikin wata bakar
mota da safiyar yau lokacin ba kuma bude kofa ba shi ne ya
roki alfarmar na isar da sakon gareki da zarar kun bude kofa
har ma yai min alheri bayan na shiga gida bacci ya kwashe ni
kafin in fito har kin fita domin kofar da za ta isar da kai zuwa
cikin gidan na tarar a kulle wanda hakan ya tabatar min da kin
fice tin lokacin ina shawagin ganin isowarki.
Tun bayan da ta cilli da takardar saboda rashin sanin
mahimmancinta da kuma damuwar da take ciki bata kuma
komawa ta kanta ba sai gefin almuru, ta kasance cikin laluben
layukan wayoyinsa har zuwa wannan lokaci wayoyin na kulle
lokacin ne hankalinta ya kai kan zungureriyar takardar
kamar kar t a daka sa dai ta ji tana me ra'ayin dubawa wani
irin ni'imtaccen sanyi ta ji sa'r da tai tozali da kyakkyawan
hand writing din masoyi abin kaunarta ta lumshe ido gami da
ajiyar zuciya ta fara karatun kamar haka:
a
A duk inda nake ki yi amannar kina tare da zuciyatai,
malsayinki ba zai taba gushewa daga zuciya ta ba a kamar
yanda sonki ba zai taba kankaruwa ba to sai dai me? Hanifa
ba zan rufe ki ba lokai daya ZUCIYA ta ta ruski kanta da
bijircewa aure a tsakanin mu ma'ana har abada maganar aure
a tsakaninmu ta rushe zuciyata ba ta taba aminta da hakan ba
to sai dai hakan ba wai yana nufin so da kunarki baya tare da
zuciyata ba aʼa ko kadan ba haka ba ne.
55
Ke ce macen farko da bana iya hada osunta da kowace
mace fatanamu kasance a matsayin da muke kai muddin rai Hanifa, hakika rayuwar mu za ta fi inganta a haka. a karshe
ina me takaicin sheda miki Alhajina ya matsa, ya takuran da maganar aure har abada ba zan yi fatan Abbana ya