office din mu ce dole ki bi ta ba tare da kin taka
ba.
To bari ki ji da office din da me office din ba su wuce
in taka su ini kwana lafiya ba. Da fadin haka ta sa kai ciki
ainihin ofishin ba ta yi kokarin hana ta ba saboda sanin
matsayinta a gurin mamallakin office din.
Yana zaune a kan kujera ya daga kanshi zuwa sama
gami da runtse idanuwanshi a lokacin da yake karkada
kafafunshi da alamar ya yi zurfi cikin tunani. Ta kare mishi
kallo sama da kasa da alamunar ashin kwanciyar hankali a
tare da shi. cikin sanda ta sidada ta bayanshi hannu ta zira ta
bayanshi ta rungumo shi gami da dora kanta gefen kafadunsa
da sauri ya dawo daga duniyar tunanin da yake. Kamshi ya
doki hancinshi wanda hakan ya tabbatar mishi da Gimbiyarshi
ce,. Be yi kokarin juyawa ba sai kawai ya zira hannu ta baya
ya janyo ta jikinsa. Sun dade a haka har zuwa lokacin da ta yi
dabarar janye jikinta. Ya lumshe ido Hanifa kin kyauta ke
nan? Kin kyautawa rayuwata ke nan? Bayan kin san rashinki
zai iya haddasa mummunan sakamako a gare ni why Hanifa?
kar ka zarge ni Mas'ud, ko kadan kar ka tuhume ni, ni kaina
29
na shiga damuwa de rashinka to apma ya zan yi Abba ya
matsa ya takura za ka tausayawa halin da nake ciki yavin da
ka gan ni a gida, iyaycna sun tsangwame ni sun yanke duk
wata alaka a tsakaninmu a dalilin kaunarka Mas'ud.
Ya girgıza kai gami da cije lebe me ya sa Abba zai
haka? Mc ya sa Abba va kasa fahimtarmu? Shin ya mance da
matsananciyar kaunar da ke tsakaninmu Hanifa? ta girgiza kai
cike da damewa bar wannan batu, bar wannan batu Mas'ud
hankaliamu ya karkata wajen samun mafita, to sai dai sun
jima suna tatteunawa ba tare da samu mafitar ba.
A waui yammaci ma suna tare bayan sun kare aikata
wacce suke ganin za ta fisshe su Mas'ud din ne ya fara cewa
ni fa wannan zaman ya ishe ni ya kamata mu san abin yi a ko
da yaushe ba u da yan cin kasancewa tare da ke sai dai ua
wasu daidaikun lokuta, lokaci ya yi fa da ya kama tara
bayyanawa Abba niyyar aurena a gare ki. Abin nufi na turo
magabatana. Ta katse shi da cewa Uhm! Mas'ud mu dai kara
lokaci amma wallahi Abba kai da ma umma suna cikin dumi a
halin yanzu.
Ni ban san me ya sa ba sun yi fushi da ni da kai ba ki
daya. Za ka yi mamkai irin wahalar da na ke sha kafin na kai
ga isa wajenka. Kin dai nace ne amma ai da na gwada sa'ata,
kin mance Abban yana da masaniyar dumbin son da nake
miki? Mu dai kara lokacin kamar yadda na ce ni na fi ka
hangen abin dakai ba ka riga ka hango ba. sannu a hankal
kisan a ko da yaushe suna tare da juna domin aikata masha'a
kusan koda yaushe akwai dabarar da take yi domin isa ga
wajenshi to shi dai bai isa ya ko taka kofar gidansu ba.
Sannu a hankali tun Abba da Umma ba su fuskane!
halin da 'yarsu ke ciki ba har suka kai ga gano abin dake
akwai abin daya dada ta'azzara ciwon Malam Sa'ad yayin da
20
Umma ke cikin damuwa kashi-kashi ga Hanifa bo ta san ma
suna yi ba domin dai idauta tuni sun ruga sun ruf da bin
ZABIN ZUC)YARTA.
Tana kishingide a gefeushi yayin da ta yi pillow da
cinyarshi a lokaci guda kuma yana wasa da kanannuu kalabar
da take kanta, ina ga karshen wannan kumbiya-kumbiya ta zo karshe, domin na samo mana mafita, kin gane ko?" Ci gaba
da maganarka ta ce da shi saboda zumudi to wane abu take so
a dai waanan lokaci da ya wuce ta mallaki Mas'ud dinta. Ya
ci gaba la cewa, abin danake nufi me zai hana ki shiryawa
komawa karatunki ina ga wannan ita ce hanya daya tilo da za
mku fake mu ci gaba da gudanar da rayuwarmu yadda ya
kamata. Mutukar ba haka ba wallahi ganinki ma
dungurungum sai ya gagare ni. Duba ki gani yau kwana nawa
rabon da ke sakamakon takunkumin dakike ciki? Ta yi ajiyar
numfashi da jin wani sanyi a zuciyarta wai me ya sa ne tun
farko ta kasa wannan tunani ya aka yi basirarta ta toshe ne? to
sai dai kuma in da ba kasa a nan ake gardamar kokawa, ta ya
za a yi ta fuskanci iyayenta da wannan batu a yadda suke jin
zafinta tamkar su gangama wuta su jefa ta ciki, ai ko Abba be
mata adalci ba tun fil'azal ya san da irin matsanancin son da
take masa.
Tana tsugune a gaban mahaifinta kirjinta sai dukan uku-uku yake saboda tsoron abin datake shirin tunkara. Ta vi
karfin hali dai, muryarta a sanyaye, Ta ce Abba na zo neman
wata alfarma ne a gåre ka, da fatan za ka slaren ahwayena. Be
ce mata komai ba tsawon lokaci ya girgiz. kai sannan ya се
wace alfarma kike nema? Wace alfarma ce ban miki ba
Hanifa? Ta dan sunkuyar da kai, dan Allah Abba so nake na
ci gaba da karatuna. Me ya hana ki ci gaba? Me ya hana ki
karasawa a can baya? Shashanci ko? Saboda kin kekashe
30
zuciyarki kin yi watsi da ingantacciyar tarbiyyar da muka
fora ki kai, kika shiga aikata alfasha a doron kasa ko? Ki sanı
ko me kake yi kome ka aikata shi za ka je ka riska ranar gobe
kiyama (Ranar nan me ban tsoro). Ki yi duba cikin Alkuir'ani
mai girma aya ta 281 cikin Suratul Bakara inda Allah yake
cewa, "Kuma ku ji tsoron wani yini wanda ake mayar da ku a
cikinsa zuwa ga Allah sa'annan kuma a cikawa kowace rai da
abin daya sana'anta."
Ina me dada jan hankalinki ki tuba ki koma ga
Ulbangiji ki yi kokarin karkata zuciyarki zuwa ga aikata
alheri. An akarbo daga dan Abdullahi Nu'umanu dan Bashir
ya ce, na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cccewa, "Hakika a
jikin mutum akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya
gyaru idan ta baci dukkan jiki ya baci, na'am ita ce
ZUCIYA." Bulhari da Musulim ne suka rawaito wannan
badisi. Hadisi na 6 Arba'una Hadisi).
a
ZUCIYA BA TA DA KASHI ki yi kokarin tankwasa
tankwasata a duk lokacin da take kokarin kai ki ga halaka.
Shin ya 'yata ba kya tsoron ranar da Ubangiji yake fadi
cikin littafi me tsarki, "A ranar da harsunansu da hannayensu
da kafafunsu suke bayar da shaida a kansú game da abin
dasuka kasance suna aikatawa." (Suratul Nur: Aya ta 24).
Bayan Ubangiji ya hane mu ya kuma gargade mu da
aikata alfasha a wurare da dama cikin Alkur'ani me tsarki alal
misali cikin suratul Nur aya ta 2,21,30. ko ko kinfi so ki
kasance daga cikin wadanda Ubangiji madaukakin sarki ke
fadi a cikin suratul Furkan aya ta 68: "Kuma ba su yin zina,
kuma wanda ya aikata wancan zai gamu da laifuffuka
aribanya masa azaba a ranar kiyama kuma ya tabbata a
cikinta yana wulakantacce." Shind an Allah wace riba ce ke
tattare da wannan aiki? Zina babbar illa ce a rayuwar dan
32
adam mafi muni zina da aurenki, ki yi gaggawar tuba ki koma
ga Ubangiji irin tuban da Ubangiji ke fadi cikin littafi me
tsarki (TAUBATAN NASUHAN) domin shi ne Gafurur
Raheem me yawan afuwa ga bayinsa, amma ki sani ni ba zan
ba ki lasisin sabon mahalicci ba da yawuna ba wannan karatu
da kike son komawa, fakat tashi ki ba ni waje.
Jikinta ya yi sanyi da kalaman mahaifinta, anya ko
tana kyautawa rayuwarta? Me ya sa ba za ta yi hakuri da
Mas'ud ba? ZUCIYA BA TA DA KASHI, take zuciyarta ta
ba ta amsa da cewa har abada ba za ta taba daina son Mas'ud
ba yadda ba za ta iya taßa rayuwa ba tare da shi ba hanyar ke
nan dai ta yi kokarin lallaßa mahaifinta.
Tsawon lokaci tana aikin rokon mahaifinta a kan dai
bukatar da ta zo masa da ita, Hanifa ba tun yau ki ka fara
bujircewa bisa turbar da na saka ki ba karatu ga shi ga ki nan
ki yi duk abin dakika ga zai fisshe ki tunda ni ban isa na hana
ki ba, Allah ya sani kuma ke ma shaida ce na yi bakin
kokarina wajen sauke nauyin da ya dora min. kamar yadda
Malam Sa'ad ya zata karatun da take ikirarin yi shi ne dai
lasisin sheke ayarta da Mas'ud zahirin magana in banda 'yan
daidaikun lokutan da takan shiga makarantar da sai mu ce ba
ta ma san hanyar makarantar ba sai dai duk abin dadalibi yake
yi wala attendance, test, exam, tamkar da ita ake yi
sakamakon tsaya matan da Mas'ud ya yi zahirin magana in ka
ga daular da take ciki za ka yi mamaki ko dayake dama can
suna cikin rufin asiri to amma iirn yanda yake mata bari da
naira abin zai daure maka kai to sai dai kuma wala Abba ko
Umma da ma ma kannanta babu me ko saurarar abin datake
da shi kai duk wani abu da ke da alaka da ita sukan kyamace
shi sannu a hankali kusan ko yaushe suna tare da Mas'ud ta
zame masa tamkar matarshi babu kunya babu tsoron Allah a
33
halin yanzu dai idanewansu ya gama rufewa ba su shayin
kowa sai tir da Allah wadarai ke fita daga bakunan al'uroтa
tare da aza laiun a kan iyavansu.
Lamarin Mas'ud kam sai gaba yake yi al'amaru ana dada
sharnic.wa yayin da a ke samun mummunan gibi da2
ofishinsa ba sau daya ba, ba sau biyu ba Alhaji Khalii Ya sha
jau kunnanshi gami da yi mishi nasiha dangane da la'marin
rayuwa to amma me? Ta inda ya ji ta nan yake fita ma'ana ba
ya daukar ingantacciyar hanyar da mahaifinshi ke kokarin isar
da shí to sai dai me? Hanifanshi kadai yake so ita kadai ke
gabansa (Ubangiji ka raba mu da irin wannan son, son da zzi
kai ka ga halaka.
Yanzu saboda Allah Malam haka za mu zubawa
yarinyar nan idanu muna ganin abin datake yi? ni da kai muan
da masaniyar abin datake yi anya Malam? Ina jiye mana abin
kunya fa? Yau she kuma? Tun yaushe abin kunya ya riske
mu, abin kunyar da ya wuce wanda muke ciki yanzu? Sai
kuma ya sassauta murya sa'ilin da hawaye ke zubo mishi Na
rasa yadda zan yi da yarinyar pan, na rasa inda zan saka kaina,
na yi fadan na yi nasihar duk a banza, saboda Allah wace irin
tarbiyya ce ban dora yarinyar nan bisa turbar ta ba? to me kike
so na yi da ya wuce na zubawa sarautar Allah ido,? Ni kam
ban sen abin dana yi wa Ubangiji ba ya jarabce ni da wannan
musibar, bakin gwargwado na yi kokarin sauke nauyin da
Ubangiji ya dora min to me na yi wa Allah kuma? Da sauri ta
katte shi, haba Malam kamar ba masani ba, ka yi hakuri ka
dogara ga Allah ka kuma yibiyayya a gare shi a bisa dukkan
wani abu da ya same ka me kyau ko marar kyau wannan shi
ne cikar imani, addu'a kawai za mu bi ta da ita Allah ya
shıryar da ita. Yana kokarin magana tari ya ci karfinsa a
lokaci guda haki ya tasar masa ya dinga wani irin nishi gami
34
da dafe kirjinshi da Seur Ucoma ta yo kansa sannu Malam,
sanru Ubangıjı ya yye maka wannan larura. Cikin dan kankanin iokaci ya fita hayyacinshi a yayin da Um.nant ake
neman agaji. A kuma dai-dai lokacin ne Hanifa ta dawo а
kidime ta yı yo kan mahaifinta amma ko kafin ta isa gare shi
wata irin tsawa Umman ta daka mata ba shiri ta ja baya jiki na
tsuma.
A gaskiya baba mutukar ba za ka yi kokarin fitar da
damuwar da ke zuciyarka ba jiniuka na shirin kaiwa ga
matakina karshe, ya kamata ka yi kokarin fitar da duk wani
abu da ke addabar zuciyarka. Cewar likita Mannir ya koma
kallonshi ga Umma, ya kamata hajiya a dinga kokarin
kaucewa duk wani abu da zai kai ga tayar mishi da hankali
don ingantuwar lafiyarshi.
Jikinta ya yi sanyi saboda larurar babanta me ya janyo
masa haka? Amsa ita ce Gacin ranta to me zai hana ta
shawarci Mas'ud ya zo su yi aure kamar yadda ya nema tun a
baya, ko babanta ya samu nutsuwa har lafiyarsa ta inganta.
Suna tafe a mota kan hanyarsu ta zuwa Kaduna wajen
kasaitacciyar Dinner da suka shiryawa babban abokinshi
Ammar domin taya shi munar samun kairn girma daga
captain zuwa major. Mas'ud ta ce da shi. be jiyo ba saboda
hankalinsa da ya tattara bisa titi ya aka yi Princess? Ka gane
ko Mas'ud ya kamata ka yi waui abu fa. Kamar yaya fa Abin
nufi lokaci fa ya yi da ya dace ka yunkuro daga lamarin
aurenmu, Abba ya danu da halin da nake ciki yana cikin
matsananciyar damuwa duk a dalilina.
Ya yi shiru kamar wanda aka zarewa laka, tun bayan
daidaituwar lamuransu ya ji maganar aure a tsakaninsu babu
ita ma'ana abin dayake kwadayin samu ga shi nan available .
duk lokacin da yake bukatar kadaicewa yana da damar hak1,
35
to me kuma zai sa su damu kansu damaganar aure bayan sun
yi amannar shi da ita sun aminta da juna ma'ana sun zama
mkallakin junanshi? Shi dai kam a nashi ra'ayin kamar
zamansu haka ya fiye musu komai, to amma ya za a yi ta
fahıka hakan?
K gane ko Hanifa ko mun yi aure ko ba mu yi ba
mun zaallakin juna, to me zai sa ki bijiro mana da wani
batun kukаm Tа бata rai ban fahimce ka ba? kana nufin haka
za mu yi ta zama? Kin kasa fahimta ta ba hakan ne manufata
ba, amma dai ina ga kamar lokaci be yi ba ma'ana ba na so
mu takaita rayuwarmu, mu tauyewa junanmu 'yanci, komai
da kika gani lokaci ne.
Cikin kufula ta ce, to na fahimce ka na kuma fahimci
inda ka sa gaba, kara so ka tagayyara rayuwata ko Mas'ud?
Na gode tsaya sauke ni kawai kowa ya kama gabanasa a
lokacin da take kici-kicin bude motar da sauri ya rike
hannunta sorry Hanifa kin kasa fahimta ta ne, amma duk mu
bar wannan batu zabinki shi ne zabina ki ba ni lokaci zan
aiwatar da abin dakike so. Ka kyale ni Mas'ud na gane kai
mayaudari ne. No Hanifa har abada babu batun yaudara a
tsakaninmu. Be gushe ba yana lallashi har ya shawo kanta.
Da misalin karfe hudu suka isa garin Kaduna sai da
suka fara yada zango a Gamji Gate nan cikin Kabala Kostin
nan din ma dai aka kara aikata batacciyar sannan suka yi
wanka suka kimtsa da misalin karfe bakwai dai-dai suka yi wa
Halal Hotel tsinke dake Isa Kaita Road, inda za a gabatar da
gagarumin shagalin, galibi mazajen dake wajen tare suke da
iyalansu in ka dauke tsirari su din ma suka bi 6angaren da aka
tanada dan masu iyali sai dai fa zahirin gaskiya martaba da
kimar da musulunci ya tanadarwa ma'aurata ba su tare da ita.
36
Uban taro Ammar ya yi murna da isowar abokinshi,
be yi zaton zai zo ba, kai be ma son zai zo ba sakamakon
tabarbarewar lamura a tsakanninsu duk a dalilin fadin
gaskiya, to fa tun daga lokacin zumunci ya yi rauni a
tsakaninsu amma ko sa'ar da ya hada ido da Hanifa sai farin
cikinshi ya koma ciki annurin fuskarshi ya bace. A dakile ya
amsa gaisuwarta babu alamar sakin fuska a tare da shi, yana
takaici gami da bakin cikin halin da kamillaliyar yarinyar (А
baya ke nan) ta jefa kanta a ciki, shi shaida ne domin daga ita
har shi kansa Mas'ud din yana da tabbacin a baya mutanen
kwarai ne be taba tsammanin haka ba, kai yaushe ma ya taba
zaton haka za ta farui da abokinshi, mutumin da ya kasance
ma'abocin kyamar alfasha da sauran kaba'irai. Jikin Hanifa
ya yi sanyi ranta ya 6aci da wannan kaskanci da Ammar ya yi
mata, ba ta taba zato ba, ba ita ba hatta shi kansa Mas'ud din
bai ji dadin abin daya yi mata ba, kafin a kai ga kare taron
tuni sun fice abinsu. Suna tafe kan hanyarsu ta komawa Kano
a cikin daren tana ci gaba da yi mishi mita dangane da abin
daAmmar ya yi mata ta ci gaba da c ewa, Ka ga irin abinda
nake nuna maka ko a gabanka dai ga abin dindaunka ya gane
maka, yanzu in aurena kake fa wa ya isa ya yi min wannan
tozarcin? Tabbas haka ne ya kamata ya yi wani abu a kai, to
saidai gaskiya yana ganin kamar ba ta cancanci zama
matarsa, uwar 'ya'yansu ba, kai zamansu a haka ma ya fiye
musu komai, ba ya ra'ayina ure a daiwannan lokaci.
Duk irin Allah wadarai da tofin alatsinen da al'umma
ke musu ba su san ma suna yi ba, habaice-habaice da
gulmace-gulamace da al'ummar unguwarsu ke gudanarwa a
kansu duk dai be dame ta ba, masoyinta kadai ke gabanta.
Tana tsugune a gaban mahaifinta bayan da ta sunkwi
da kai cikin sanyin murya ta ce, Dan Allah Abba ka yi hakuri
37
ka amincewa bukatata, ba ni da burin da ya wuce wannan
Abba, ina me neman yardarka kt amince da maganar auren da
ke tsakaninmu da Mas'ud, tsoro da rasbin sanin natsayin da
ka dauke shi ya hana shi isowa gare ka.
A duk inda tunanin dan'adam yake dan gane da
tabarbarewar wannan zamani to ya wuce uan, ke da kanki
kika zo nemawa abokin fasikancinki aure ko?dukiya rashin
kunya da lalacewar abokin shashancinki wato ke kin wucе
nan ko? Abadan abidina ban amince ba, ban yarje aure a
tsakaniniku ba, ban amince ba ni Sa'adu ba ko zan tabа
amincewa ba, ina yi miki nasiha ki tuba ki ji tsoron Ubangiji
ki koma gare shi ki fita harkar yaron nan, abadan abidin na yi
muku katangar karfe a tsakaninku aure kam babu shi muddin
rai. Muryarshi ta sauyą, cikin yanayin damuwa ya ci gaba da
cewa, "Yaron nan ya cuce ni, ya cuce ni, sakayyar Ubangiji ce
a tsakaniomu."
Saboda Allah me ya sa mahaifinta ke mata haka? Me
ya sa yake son yi mata karan tsayc a rayuwa? Hakika Abba
yana shirin aiwatar da íummunan gibi a rayuwarta mutukar
zai katange tsakaninta da cikamakin rayuwarta, dan dai ita
yarinya ce me biyayya sai a nemi tauye rayuwarta saboda
Allah? A ko da yaushe fadan Abbanta shi nc ta bar abin
datake yi to me ya sa Ahba yake kokarin mai da hannun
agogo baya?
Kullum jiya i yau, lafiya ta kasa ingantuwa a gurin
Malam Sa'ad ko don kasancewar mutum ne me mutukar saka
abu a zuciyarshi?
Shin ina zan sa kaina ni Malam Sa'adu kullum
lamarin yarinyar nana sai gaba yake? Da wane ido al'umma
za ta dube ni? Ubangiji ina ma ba ka kadarto yarinyar na.
fitowa daga tsatsona ba ko na huta daga musibar da ta jefa
38
ui.... Da sauri Umma ta katse shi, Umn. Malam kada ka
yi butulci ga Ubangiji a bisa ni'imar da ya yi maka, 'ya'ya
nawa Ubangiji ya azurta ka da su? Nawa ne daga ciki suka
kasance lalatattu? Hakika ka fi ni sanin amsar hakan. Ka yi
hakuri ka godewa Ubangiji da ya shiryar maka da ragowar,
mutane nawa ne za su hayayyafa amma babu na zabe a ciki?
Saboda Allah in dai ba butulcewa Ubangiji za mu yi ba ya
zama dole mu gode masa
Ba zana so ka kasance daga cikin mutanen nan da
ubangiji ke fadinsu cikin Jittafi me tsarki a kan rashin yarda
da kaddara, "Idan sha shfe shi ya kasa hakuri" (Suratul
Ma'arij aya ta 20) mu yi h akuri mu dogara ga Allah domin
ita din ma bamu fitar da raid a shiryiwartaba mu dai ci gaba
da yi mata addu'a. cikin karaya ya ce, Kayya, kayya na tsinke
da lamarin yaarinyar nan kullum abu ba sauki sai gaba ni fa
na san irin zantuttukan da suke zuwa kunnuwana jama'a ba su
yi mana adalci ba sun dora lefin kacokan a kanmu.sabi da
Allah da me zan ji wallahi ubangiji ya karbi ruhina ya fiye
min daga wanan rayuwar da nake ciki shiga jama'a ya yi min
wuya saboda ina jin kunyar abin dajinni na ke aikatawa
al'uma kuma ta kasa yi min adalci, zantuttuka na 6atanci duka
kai na da zuri'ata.
Sai kuma ya shiga shsssheka kamar zai kuka yarinyar
nan kin cuceni kin mana babbar illa a rayuwa ta da sauran
'yan uwanki dama zuria'rmu baki daya.... Sai kuka ya kwace
masa yayin da umman ta shiga lallashi hakuri za kai malam
hakuri za ka yikomai yai zafi maganinsa Allah, mu ci gaba da
yi mata addu'ar neman shirya da sannu Allah zai dubc mu.
A dai-dai lokacin misalign karfe goma ne na dare hard
a 'yan mintuna Hanifa tai sallama ta shigo tin bayan fitar ta da
39
safe kenan in ban da rashin maid a sallama a addinan ce babu
kyau da ba za a amsa mata ba cikin sanyin murya Malam
sa'ad ya amsa yayin da Umma ta amsa a ciki.
Jikinta a sanyaye ta ce Sannu Baba in ce ko ba jikin ba
ne? gangar jikina da zuciya baki daya ba za su taba gushewa
daga wannan larura da ki kai silar jefa ta ba mutukar ba
tsamme kanki ki kai daga wannan mummunar dabi'a da kika
saka kan ki a ciki ba, wannan ita ce rana ta karshe da zan ja
hankalinki ki ji tsoron ubangiji ki janye kanki, ki tsarkake
kanki daga musifar da kika jefa kanki a ciki ki je ki duba ki
hanga daga basirar da ubangiji yai miki shin abin dakike yi
dai dai ne? duk abin dakika ganin shi ne dai-dai ki dauka ki yi
amfani da shi.
Tofa Abba ya bata babban Assignment kanta ya dau
caji ta hada ta tara daga maganganun, mahaifinta daga bisani
ta rabe karya da gaskiya shin wane za ta dauka kenan?
Maganar mahaifinta na bisa turba ma'ana yana a ma'aunin
gaskiya, a hannu daya kuına lamarinta da Mas'ud ne a
ma'aunin karya to me ye abin yi take zuciyarta ta shiga zaba
mata abin datake ganin shi ne dai-dai, ta dau kashi na biyu
ne? Wato lamarin ta da Mas'ud ko ko ta bi zabii na daya
ma'ana batun mahaifinta wanda hakan ke nufin tai bankwana
damasoyinta abin kaunarta kenan a lokaci guda zuciyarta ta
karyata hakan.
Kai ina hakan ba zai yiwu ba har abada ba za ta tab a
rabuwa da Ma'ud ba ba za ta taba yin saken da zai subuce
mata ba tana sonsa, tana sonsa so mara iyaka. Uhm! ZUCIYA
KENAN ZUCIYA ВА ТА DA KASHI. Take'ta bi zabin
zuciyarta ma'ana tai ruko da karya tai shika da gaskiya,
malam Sa'ad ya fuskanci babu alamun sauyi ko sassauci daga
lamarin yarsa kullum abu sai gaba yake abin daya dada
40
ta`azzara larurar shi ako da yaushe jinin sa sai hawa yake
babu alamun yin kasa hart a kai ga jininshi ya kai ga mataki
na karshe malam Sa'ad kam na jin jiki.
Ako da yaushe Hanifa na kokarin tunasar da Mas'ud
lamarin aurensu bad an komai ba said an damuwar Mahaifinta
to amma a duk lokacin da tai masa maganar hakan sai yai
dabarar sha shanar da zancen..
Yau da gobe be gushe ba sai da ya shashantar da ita ta
ma dena yi amsa maganar baki daya.
A 'yan kwanakin nan ciwo ya matsawa malam Sa'ad
Kwarai da gaske a duk lokacin da ya tasar masa sai ya yi
kamar ba za kai ba ‘yan uwa da abokan arziki duk sun karaya
da wannan larurar tashi amma a hakan take sa kafa ta fice
domin gudanar da abin datake ganin sh ne daidai a rayuwar ta,
saboda rashin jin kai a wannan lokaci dai kwanan gidansu ma
be dame ta ba idan ma harta kwanan to be wuce kwanciyar
bacci ce ta kawo ta ba.
A wannand aren ma a kan idon Malam Sa'a d ta dawo
ttin bayan da ta fita d safiyar jiya ba iya ce mata komai ba illa
ido daya saka mata malam Sa'ad yai kuka yai kuka har ya
gode Allah, wayewar gari da sanyin safiya jikin nashi ba dadi
ciwo ya fina da hailala da salati kadai kai ke fita daga
bakinsa.
Ta kintsa ta hade cikin yadin tissue da akai amsa
dinkin 'yan birni me mutukr bayyana surar jikin bil'adama
dinkin ya dame ta tsam yayin da kan ta ke dauke da kananun
kalba da aka jona su da izgar doki kunbunangta an fente su da
fentin bature, tana gab da fita tai arba da mahaifitana yayin da
umma ke kansa tana mishi fifita gami da yi masa sannu
fuskarta knshe da matsananciyar damuwa da alama ciwon ya
fin a ko yaushe. 무
Sannu Abba ta fada cikin tausayawa a lokacin da ta
rusuna a gabansa ba zai iya tashi ba saboda halin da jikins ke
ciki a hakan ya kokarta ya tattara dan raagowar numfashinsa
sai dai duk da haka hakin be rabu da shi ba ban da ina tsoron
ubaagiji d hиmа Кокаrin sauke nauyin da ya dora min da ra
dai-daita kin a yi miki mugun baki kin bi duniya ko na huti
daga wannan kunci da kika sanya mu to na riga na san b
wani alfanu a tattare da hakan abu daya zan ce miki shi ne
duk abin dabawa ya yi me kyau ko a kasin haka shi zai girba
tin daga nan duniya har zuwa ranar gobe kiyama.
Don Allah Abba.... Ya katse ta ya isa bana son duk
wani furucinki na gode Hanifa. Da fadin haka ya mai da kai
ya kwanta ko ki tashi ki ba ni waje ko kuma ina iwa
tar miki da duk abin da zucivata ta rayan, ba shiri ta mike tana
shawara da zuciyarta ta koma ta zauna saboda larurar
mahaifitana Abin nufi ta hakura da muhimmin abin dake
gabanta kenan. Amma kuma in tai haka ba ta kyauta wa
masoyina ba.
Bayan ta san tsawon watani suna shirye-shariyen
wannan tafiya wato yawon bude ido ko kuma mu ce yawon
shan iska domin more rayuwarsu, me kama dai