tamakar me shirin barin doron Kasa, hankali da
nutsuwa ba ya tare da shi tun bayan sautin maganar da ya
tsinkayo ta layin wayarsa maganar da take barazanar
tarwatsa kwanyar kansa ba zai iya tantance muryar
mutumin ba da yake umartarsa da ya yi sauri ya isa Prince
Hotel a hawa na biyu daki me lamba hamsin da biyu domin
ganin abin mamaki a tattare da matarsa, ko ma dai waye me
wayar ya hakikance da muryar mace се.
Cikin sauri-sauri, gudu-gudu ya isa ga daki me
lamba hamsin da biyu a hawa na biyu cikin hanzari ya ja ya
tsaya sa'ilin da ya hakikance dakin da yake nema ne. har
ya kai hannu zai kwankwasa sai kuma ya tsaya to shin ma
me zai gani ne? zuciyarshi ta ba shi amsa da abin dakake
zargi kake kuma kokwanto shi Ubangiji zai nuna maka
ra'ayul ainun. Ya ciza lebe har abada ba ya fatan haka
domin ya fi so ya karkata zuciyarshi da cewa zargin ne dai
har abada fatan alheri ne a tsakaninshi da matarsa ba ya fata
ko nufin ta da sh arri. A lokaci guda yayi knociking kofar
ga mamaki sai ya ga ta bude be yi wata wata ba ya sa kai
ya shige, babu kowa akayataccen falon sai dai akwai
alamar akwai mutum a ciki ta la akari da yadda kaya suke a
barbaje ya dinga bin kayan da kallo daya bayan daya kama
daga wando jeans ash colour zuwa-farar shirt ta maza.
socks, belt sai dai kuma a dai-dai lokacin ne idanunshi ya
fara yi mishi nuni da kayan mace. Kama daga mayafi, riga
da zani na leshi, numfashinsa ne ya tsaya cak sa'ar da ya yi
arba da kyakkyawan leshi me ruwan omo-omo wato (cyan
16
colour) tabbas leshin ba zai taбa Бace masa ba saboda
mayatar sonsa da yake ya sawo mata shi takanas ta Kano
tundaga kasar China in bai mance ba duk dai shi ne ya kai
mata dinkin a nan titin gidan Zoo, kazalıka wannan ita ce
kyauta ta karshe a tsakaninsu a takaice ta tabbata matarsa
ce ke ciki tare da wani, kato, "Wa'iyazu bıllah." Take
hankalinsa ya gushe tunaninsa ya bace kamannınsa suka
sauya har ta kai da gashin jikinsa ya mimmike saboda
bacin rai hafurinsa ya kare sannú a hankali ya dinga bin
sako da lungu na dakin ya karya corner ya shige corridor
ya kara karya wata corner lokacin ya yi arba da kofar daki
a rufe, cikin matsanancin zafin nama ya kai mata wani
wawan duka take ta bude, to ko dai ba a rufe ba ne ko ko a
buden take Allah ne masani.
"Ubangiji ka kange idanuwanmu daga mugun ji da
mugun gani." Abin dayake fada ke nan a zuci lokacin da
idanunshi ya gane mishi abui mafi muni a kundun tarihin
rayuwarsa, matarsa halaliyarsa wacce ya danka ragamar
rauwarsa, mutuncinsa, gangar jikinsa, kai da komai ma
nasa yau ita ce ya kama dumu-dumu da wani kato da ba
kowa ne a wajenta ba face yau dai kam Allah ya nuna mishi
abin dayake zargi, ra'ayıl ainun KWARTO, wayyo duniyar
ta yi mishi ba dadi ya yi da ka ce ma Ubangiji be taбa
kadarta haduwarsu ba ko da na da kika daya ne, tunaninsa
basirarsa, hankalinsa kai da komai ma a dai wannan lokaci
ba ya tare da shi.
Ba Hanifa ba hatta shi kansa Mas'ud din ya gama
tsorata da yanayin shi suka shiga kokarin tserar da
rayukansu kafin su yi wani katabus ya riga ya cimmasu
idanunshi ya rufe zuciyarshi a makance, be saurari
17
kwarton ba ma ci amanar ya duaka ya shake makoshinta ya
hada ta da garu yayin da yake lurucin sai ya ga bayanta. la
tsorata ta kadu tun tana Kokarin kare kanta har ta kai
Karfinta ya Kare jikanta ya gaza, Mas'ud dake a gefe ya yi
yunkorin kawo mata dauki be iya katabus ba ya kai shi
Kasa warwas sai dai kafin ya kai shi Kasan sai da ya yi
nasarar danna yar na'urar dake ankarar da jani'an Hotel
din neman agaji. Ban da Allah ya taKaita jami an dake kula
da Hotel din sun kawo dauki cikin gagawa da sai an yi
batacciya, to ko yanzu din ma an yi sai dai abin ya takaita.
Yana kuka yana fadin, "Hanifa kin cuce ni kin cuci
rayuwata kin haifar da wawakeken gibi a rayuwata kin
haifar min da mikin da har abada ba zai taba gushewa ba.
na sake ki! Na sake ki!! Na sake ki sau ba adadi. Allah shi
kadai zai mana shiabi a tsąkaninmu.
Kabilar Hausa Fulani Kabila me kishin al'ummarta da
son junansu gami da kyautatawa junansu amma wannan
zamani, hassada, Kyashi da bakin ciki shi ya kankane
zukatansu daga kyawawan dabi'un da aka san su da su a baya,
a lokaci guda za ka aikata kyakykawa ko kuma wani abu na
alhen idan ya same ka za ka iske wani makocin ka ma be sani
be, znkatanmu sun gurbace ba su cika son wani abu na alheri
Da yayin da ka kuskure ka aikata ba dai-dai ba al'uınar
nguwarku ba duniya ma sai ta ji ka inda ba ka zato ba ka
isarnani sai ka riski lamarin a can, saboda hakan ne ake soca
1:.ukatanmu sun riga sun gurbace Kyashi da hassada ya y
katutu a ukatan al'ummar hausa Fulani. Na wannan zamani
to hakan ce ta kasance ga Hanifa nan danar zance ya
warwatsu a gari kai dama duk inda ba ka zato. Dangın mijinta
18
ga ko kadan ba ta karbu a gurinsu ba suka shuga Yamudrdi da
zancen to dama ya latiyar giwa.
Kai tsaye asıbitu aka tafi da ita don Kokarin nemo
rayıwarta gaba daya ba ta san inda kanta yake ba kwana da
kwanaki ana Kokariu nemo rayuwarta bar Allah ya sa ta
larfado ta dawo hayyacinta yayin da Kwakwaławrta ta shiga
tariyo mata abın daya gudara. Sai take jin abin tamkar a
makukr Wane irin tsautsayi ne ya atka musu ne haka har
sukanyr saken da asirinsu ya tona? Tambayar da take wa kanta
ke nan
Kwana hudu da faruwar wannan abu Uma da
Malam Sa'ad ba su da masaniyar abin daya faru sakamakon
rufa-rutat da ake musu da vake suna cikin tashin haukah ne na
rashin katiyar yarsa hankalmsu be kai ga gano makasudim
rashin zuwan megidan ba da ma danginsa. Komai ya kwance
mustu ne sa'ilin da suka isa gida. Innalillahi wa inna ilaihır
rajrtn. abın daya fito daga bakin Malam Sa'ad ke nan lokacm
da kunuwanshi ya jiye mishi zance mafi muni a rayuwarsa, sall
kawat gani aka yi ya yanke jiki va fadi yayin da Umma ke
fadin, "Na shiga uku yau na banu na lalace, yau wane irin abu
kunnuwana ke jiye mia? Wacce irin masifa ce ta atka n' Kaicona ni Hadıza hakiya
yau ita ce rana mafi man a kuedın tarihin rayuwała, yat nan
kin cuce ni kin euer zurilarnu, fasiKanci da aurenki? Wane
abin kunya ya fice wanman? Kat tir da haihuwarki." A lokacın
da ta kawo mata raruma idanunta va rute duka take da duk
abin daya zo hannumta.
Kwanakin Malam Sa`ad biyuu a assbiti samnan ya dawo
hayyacinsa, binciken da likitocr suka yt sur tabbatar da crwon
hawan pini ne ya kama shi malana jiinshi ya hau kwaraa da
gaske. Suna gaban fikita va ci gaba da cewa, taimakon farko
19
daya kamata a bawa me wannan cuta shi ne. Na farko a auna
junsa don gano matsalar da take damunsa, domin sai an auan
jininsa ne za a san a wane matakı jininsa yake, a ba shi
mágani dai-dai da awon jininsa, zuwa asibıti akai--akai.
kiyaye abincin 'da zan er mara gishiri da farin magi (kafi
Zabo).
A ba shi shawara, yana bukatar hutu. Hanyoyın da ake
bi dan gano mutum ya kamu da wannan cutar su ne. rashin
bacci, tunani. buguwar zuerya, yawan crwon kat a ko da
yaushe. kumburin Kafatu da fuska, jiri
Magungunan da ya kamata me wannan cutar ya sha su
ne: maganin da zai saukar da hawan jinı, magamn ciwon kat.
maganin hana tunani mai yawa. shawara a kan abincin da ya
kamata ya ci.
Nau'in abin daya kamata ya dinga ci su ne Abincin
da ba gishiri ko magi mai yawa, abinci mai gina piki, sař kuma
kayan itatuwa.
Likita ya Kare bayanin nasa da cewa mutnkar ana se
lafiyarsa ta inganta sai an bi wadannan matakan da suka
gabata.
Ga Malam Sa'ad mutuwarshi ta fiye mishi da dai irm
wannan abin kunyar da 'yar cikinsa ta jaza mishi
Isarsa gida ke da wnya ya yi tozali da ita ta hada kt
da gwiwa, ya ja ya tsaya a kanta duk da cewa jikinshi babu
Kwari magana ba son yin ta yake ba, tashi. tashi ki bar min
gida na tsana ki, na tsane ki Hanifa, ina me bakin ciki gami da
nadamar kasancewarki tsatsona, na tsani me hah irin nakı.
Bacen da gaı tun kan in kai ga yi miki baki Cikin kuka ta ce
Abba dan Allah ka yi hakuri kai min aikin gafara. Ya nuno ta
da yatsa fice, na ce fice ki ban waje. zama da fasiki Allah ya
tsareni. wallahi na yafę ki na yafe ki ga duiya ki je ki yi duk
20
abin dakike so Ubangiji ya yi min sakayya a bisa tozartar da
kika jaza min. ba ta da niyyar tashi ya fusata zuciya ta kawo
shi wuya wani abu ya tokare kahon zuciyarshi ya dafe
kirjinshi sa'ilin da yake kokarin faduwa.
A dai-dai lokacin ne Umma gami da 'yan uwan
Malam Sa'ad suka shigo bayan da suka gama debo 'yan
komatsansu daga motar da ta kawo su daga asibiti. Rafka
salati ta yi gami da hanzarin isowa gare shi, "Wayo Malam
me ya faru ne?" be iya cewa komai ba, hannunshi na dafe da
kirjinshi ya yi nuni da Hanifa to a nan fa ta ankara da ita ba ta
san sanda ta saki Malam din ba, Bacen da gani tun kafin na
Nai ga aikata miki 6atacciya, fice ki ba mu waje ki tafi duk
da ya yi miki, ki tafi duk inda kike so, duniya ce ga ta nan ta
ishe ki yadda kike so. Wallah ki 6acen da gani ko in sabauta
ki." Ta shiga fada ba ji ba gani, fuskantar tana neman yi mata
baki da sauri Malam iliya dan uwa ga Malam Sa'ad ya datse
ta gami da janye Hanifa.
Alal hakika Malam Sa'ad gami da Umma Hadiza ba
Karamar damuwa suka shiga ba, yau dai ga abind a 'yar
cikinsu ta jaza musu, 'yar da suka rene ta suka wahalta mata
ruwa da iska suka tarbiyyance ta bakin gwargwado
sakamakonda za ta yi musu ke nan a yau ta muzanta su sun
zama abin zunde da kwatance a tsakanin al'umma, shin wane
abun kun aya fice wannan ga rayuwar Malam bahaushe?
Ballantana ga cikakken Bafulatani da aka san shi da kunya da
kara Bafulatani kuma na hakika, masani ga addinin Islama,
me aiki da sunnar Ma'aiki Shugaba (S.A.W) mutum me
nutukar kima da daraja a tsakanin al'umma, abin kwatance da
kwaikwayo.
Allah me yadda ya so yau kuma shi ne haka ta faru ga
yar cikinsa, bakin gwargwado ya tarbiyyance ta bisa tsarin
21
iklama arima dk ta watsar da hakan a yau ga irin abin kunyar
da ta janyo musu, abin dazai vi mummunar illa ba ga ita
Kawal bad har ma da yar uwanta, danginta, kai da ma
zunaru baki daya.sMeyd amfanin haihuwa irin wannan?
Sakamakon da 'ya ya suke niayarwa da iyayensu ke nan?
пву ортип bayan faruwar wannan abu Hanifa ta kasance
eikin abtsananciyar damuwa musamman saboda halin da ta
jeta iyayanta Hahirha sangin mahaifinte sun zauna sun
Tattaond a tsakeninsu dangane da masifar da ta taso musu.
Nasiha da ban baki kaj da ma komai da ake lalalsar mutumin
da aka sabawn an yi amfani da shi a kan Malam Sa'ad da me
dakinsa akar dalsa bakura su amshi "yarsu tare da afuwanta
mata bisa kuskaren da ta yi to gaba da gabanta kuma bin na
gaba bin All dolsta sa Malam Sa'ad ya hakura ya yi
biyayya ga amrarniusu Maganar yafiya kuwa ba ta ma taso ba
har abade be jiu zai iya mancewa da wannan abin kunyar da
'yar cikinsa ta jaza masa, sun yi mata fada mara misaltuwa.
OasitusHakika sun gwada bakikanin Gacin ransu daga
Karshe suka yi mata nasiba me ratsa zukata, to amsar dai dake
ia dagalbakinta a ko da yaushe ke ran wato sharri akai mata.
2shirin gasklya har yanzu ba ta gane kurenta ba, ya ma za a yi
dir gehe bayan tuni ta doru a kan son duk abin dazuciyarta take
96yzu he ma take jin son Mas'ud so mara iyaka ruwa da
iska bloh me iyá raba su, amma da zarar komai ya lafa za ta
sabatur da shi ga iyayenta a matsayin mijin da take muradin
Waanan abu da ya faru ko a jikinta, sai take jin tamkar
ah firal da ita daga cikin wani dan akurki ne yanzu kam tana
Ca yancin da za ta wataya son ranta babu wani shamaki a
tsakaninta da masoyinta wanda take fatan aura da zarar komai
ya lafa, damuwarta daya shi ne damuwar da ta ga iyayenta na
Ciki, amena tsinke igiyoy in aurenta da tsohon mijinta ya yi be
22 10
dadata da Kasa ba shi ke nan ta huta da kwazzabar dangin
mijinta da suka kafa mata kabon zuka, 'Da' kuwa Allah ke
rayawa su je su rike abinsy ba ta wani damu ba da kwace shin
da suka yi damuwarta daya irin tozartar da tsohon mijinta ya
jaza mata. Ta kullace shi ta rike shi riko me tsanani kai ta ma
tsane shi baki daya tun da ya yi silar hada ta da iyayerta.
Zamanta a gidan mahaifinta zama ne dai ga shi nan
dai ba kyara bare tsangwama kai babu me ce mata ta tafas
hatta da kannenta mahaifinsu ya yi alkawarin duk wanda ya
shiga harkarta sai ya yi masa mumımunan sabawa, saboda
haka ma suke dari-darin kusantar inda ma take, dukd a ba su
da masaniyar menene mujazar haka, sai kallon kallo a
tsakaninta da mahaifanta domin babu komai amsa gaisuwarta.
A tun farkon faruwar lamarin Malam Sa'ad ya so ya je
ya ci zarafin Alhaji Khalil Mahaifin Mas'ud amma kuma sai
ya ga rashinf a'idar hakan lefin wani ba ya shafar wani haka
nan duk uba na kwarai ba zai taba son ya ji danshi cikin
mummunan hali ba to amma ſa yaron ay cuce shi Ubangiji
kadai ka iya yi musu shiabi ranar gobe Kiyama.
***** *** *****
Yana zaune kanshi a sunkuye a dakin mahafi arshi
yayin da take ei gaba da yi miski nasiha un farko Abdu ahir
na hane ka da wannan aure ka kafe ka nace ka jajirce to yau
ga baind a ka janyo wa kanka ka cuci kanka ka cuci zuri'arka.
ka bata kundin tarihin rayuwarka abadan abidin, sha`awa da
bin SON ZUCIYA ya haifar maka da haka. Eh! Mana dan me
ga 'yar uwarka da kuka yi shekara da shekaru kuna tare da
yarinyar nan rana daya ka watsar da ita ka ei amanarta ka bi
sonzciayarka, kyale-Kyalen banza ya debe ka shin kana jir.
23
hakkin yarinyar nan kadai be ishe ka ba? to wannan sai ya
zama darasi aa gare ka, hakika karkata ga bin son zuciyarka ya
haifar maka da mummunan gibi ba a gare ka kađai ba da ma
zuri'arka. Baki daya Yau meye sunan wannan yAro a gurin
danginka da ma sauran al'umma face DAN SHEGE. Da sauri
ya ce, "What? hajiya me kika ce?" me na ce ko ko me suka
ce? Abdulzahir ba Karamin kuskarue ka yi ba yau ga
mummunan kalmar da ake aibace zuri'ata da ita. Abu guda da
nake so shi ne ka je ka dau yaron nan a je wajen gawjin jini
dan a tabbatar da gaskiyar lamari. Cikin raunanniyar murya ya
ce, yanzu ke nan hajiya ke ma kin yarda da jikanki kuma
jinin jikina dan shege ne?
Ko kusa ko alama ban taba zargin haka ba dai-dai da
dakika daya wallahib sam ban taba tunanin haka ba, na yi
tunanin ayi hakan ne dan a fidda shakku a zukatan duk masu
zargin haka, ni na san irin abin dakunnena ke jiye min ko
makaho in ya shafa ai ya san Walid jininka ne dame ya
banbanta da kai, yaron da kuke kwabo da kwabo da shi halin
mutane ne dai ka sani ba a raba su da abin fadi. Allah daya ne
duk da cewa tun fil'azal ba son lamarin nan nake yi da
yarinyar nan ba to amma kuma hakan ba zai sa na nufe ta da
mummunan wani abu ba ballantana ga tsatsona, ka yi hakuri
ka je ka yi abinda na umarce ka.
Ya girgiza kai, hajiya ki yi hakuri ba wai na ki bin
umarninki ba ne, hakan sai na ga kamar wani tozarci ne a gare
mu, duk wanda yake ganin ya isa ya zo ya tare ni da wannan
iaganar mana. Ka dai yi hakuri ka bi umarni na gaba ake ji
ba baya ba, in mu ne yau ba mu ne gobe ba.
Yana jingine da 3 seater cikint alatainin dare ko kadan
ya kasa runtsawa kai tun da wannan abu ma ya faru yaushe ya
samu kwanciyar hankali da har zai bacci, to fa ga wata
24
sabuwa ta kunno kai, al'amarin ya kai ga shallake shi har ta
kai ga zuri'arsa, lallai ba karamar cuta Hanifa ta yi masa ba, a
yanzu ne ya dada gasgata haka, anya ko zai taba mancewa da
yankan kaunar da ta yi masa? hakika ba zai taba mancewa ba
ba kuma zai taßa yafe mata ba.
Ashe duk abin datake fada mishi karya ne yaudararsa
kawai take tana ha'intarsa, amma ba wai sonsa take ba kai
karya ne ma a ce ta ta6a Kaunatarsa in ko hakan ne da ba ta ci
amanarsa ba. sannu a hankali ya dinga tunano da farkon
haduwarsu a Sahad Store ya tuna da amsar da ta ba shi a
lokacin ashe da gasken akwai wanda take so, yana nan kuma a
zuciyarta me ya sa tun lokacin da ta gaya mishi gaskiya be
rabu da ita ba? Me yasa ya bi son zuciyarsa ya dinga tunano
da irin zaman da suka yi da irin sakaci da sako-sakonsa wanda
ya haifar masa da babbar illa a rayuwarsa, me ya sa be gano
hakan ba har sai da me afkuwa ta afku? In ba haka ina
tunaninsa, basirarsa yake lokacin da wasu abubuwa suka faru
da dama a gare ta har zuwa lokacin da ya fara samun sauyesauye a gare ta? Duk me ya sa ya kasa fahimtar wani abu a
lokacin?" amsa ita ce saboda sakaci da rashin kulawa irin
nasa. Ya tuna da kalaman megidanshi duk da tarin shekarunsa
da rashin nutsuwa saboda wahalhalun iyali amma har ya fi shi
tsinkaye da hangen nesa gami da kula da sa ido a kan iyalinsa
irin abin kam da ya ji daga bakin baba Megadi abun babun
dadin ji, KWARTO! Kwarto har cikin gidansa Allah ya yi
min sakayya a tsakanina da ke Hanifa. Abdulzahir ya tsinke
da lamarin mace ya tsorata ga lamarin mata maciya amana da
kokarin yi maka zagon kasa a duk inda suka samu dama, shi
da mace haihata-haihata.
Gaba daya zuri'ar gidansu kwansu da kwarkawta suna
zagaye da mahaifinsu don amsa kiran da ya yi musu. Bayan
25
dogon sharhi daga bakin Alhajin gami da nasiha ga zuri'asa
danganc da ce-ce-ku-cen da ake a bisa musibar da ta afkawa
San uwans. su hada kawunansu su rungumi kaddarar da ta
atka musu kada su bawa makiyi dama ya bukaci inda me
bukatar fadin wani abu ya yu to ba a samu me magana ba, sai
shi Abdulzahir din ne yake da ta cewa. domin dama shi ne
mutumin da ya assassa taron bayan da ya kai kukanshi ga
mahaifinsu a bisa kokarin bata masa zuri'a da 'yan uwanshi
suke shirin yi.
Bayan sallama ya fara da gabatar da Korafinsa tare da
shaida hujjojin da suke tabbatar da dansa ne halak malak. Ya
mika takardun gwajin jinin da aka yi mishi shi da yaron ga
'yan uwanshi wanda ke tabbatar da jinin jikinsa ne, inda me ja
ba musu ya dau Nesi zuwa dakin bincike na
kimiyya (laboratory) domin tabbatar da zahirin magana.
To dai galibin 'yan uwanshi maza ba su san da
wannan soki burutsun ba, tushen abin ya samo ne daga ‘yan
uwanshi mata. Kai karshen tika-tiki tik, daga Zakiyya
yarinyar da suke ciki daya da shi abin ya ba shi mamaki ya
bakanta ransa 'yar uwarshi ke mishi wannan mummunan illa
a rayuwa, saboda kiyayyar uwar yaron da ke zuciyarta, batun
yau ya lura da hakan ba, amma be taßa zaton kiyayyar zai
shati jininsa ba, ashe ita ba me iya suturta shi ba ce duk da
gatana da ya yi mata a baya. Ya gwada Gacin ransa ya
gaggaya mata magana duk da cewa ba tsarar yin sa ba ce, har
sai da mahaifinsu ya shiga tsakani. Ba ta gane kurenta ba ba ta
gano rashin kyautatawarta ba sai ma dauka da ta yi soyayyar
tsohuwar fasikar matarsa ce ta rufe masa ido ahar ya kasa
gano lefinta sai ita da ta fadi gaskiya zai dora mata karan
tsana. Ta ayyanawa ranta kila da ba dan idanunshi ne ya gane
mishi ba da ya ce sharri aka yi mata, a dai inda yake nuna
26
t
t
f
b
k
tiZ
ta
h
W
iyal
SU
ta
lam
in
ta
ra
an
Sa
kam
a
a
a
0
ai
e
Ba
da
a
a
ja
a
a
ח
a
a
a
n
ai
da
a
ar
a
ar
sa
ת
e
a
tsananin kaunarsa gae ta ba kuma ya kaunar genin lefinta. A
tunf arkon lamarin zakiyya ta yi murna ta yi farin ciki da
faruwar hakan ba ta 6oye abin a zuciyarta ba karara fita ta
bayyana har 'yar uwarta Najiba da suke uba daya tana
kwabarta ta cika da farin cikin yanda Allah ya kawo karsien
zaman Yayanta da gagarumar makiyyarta to sai dai in za ka
titsiye ta ba za ta iya bayyana maka makasudin kiyayyarta a
zuciyarta ba.
To dai Alhajin nasu ya kashe komai a karshe ya rufe
taro da addu'a, rikon yaron kuwa ya koma hannun kakarsa
hajiya Maryam har zuwa lokacin da zai aure to sai dai fa
wannan ba ta gabanshi.
Har kawo yanzu dai lamarin bai kai ga kunnuwan
iyayan Mas'ud ba illa iyaka sun dada kara kaimi wajen gano
abin daya yi silar haifar da damwua ga dansu da har ya
sukurkuce da shi haka. Yaron da suka san shi da nutsuwa tun
tasowarsa to sai dai fa gaskiya galibin danginsu sun san da
lamarin suna dai jin shakku da kunyar tarar Alh. Khalil Da
maganar ne, kamili kazalika mutumin kirki da kowa ke yabo.
Zaman gidan ya yi mata ba dadi sakamakon halin ko
in kula da iyayanta suke gwada mata, da uwa uba rashin ganin
tauraron zuciyara (Mas'ud) kimanin watanni uku ke nan
rabon ta da shi duk iya dabarar da zai yi donsu hadu ya yi
amma ba nasara, to da w.ne idon za ta kalli al'tma
sakamakon yamadidi da ke da ita a garin to sai dai wannan ta kau a yanzu ta mittsike idanunta ko me za a ce in dai akan Mas'ud ne sun yi a banza domin sai dai su yi su gama inda
matsalar take shi ne yadda za ta tunkari iyayenta da batun fita. To sai dai ta riga ta ggama kitsa wacce za ta fisshe ta. Tsugune take a gaban mahaifiyarta kanta na sunkuye
umma ina neman alfarmar yau zan je in gaida Gwaggo
27
Halima (wato 'yar uwar mahaifinta). Ba ta ce mta komai ba
sai ma dauke kai da ta yi ta kara lankwasa harshe gami da
neman alfarmar ta bar ta. Ta dade tana magana daga karshe ta
nuno ta da yatsa ke...., fita harkata kin ji ko, yi duk abin
dakika ga zai fisshe ki. Ta tashi ta bar ta tsugune a nan ya za
ta yi ta hakura da fita ke nan kai ina h aka ba zai yiwu ba. Ba
za ta juri rashin ganin masoyinta ba duk da cewa ba sa gganin
juna amma dai a koda yaushe yakan aiko da sakwanni ta
hanyar text message duk dai yana kara jaddada dumbin son da
yake mata da uwa uba halin da ya shiga a dalilin rashin ta
took wayar ma ba ta da 'yancin sakewar da za ta yi magana da
shi sai dai ko in ta fakaici numfashin iyayenta shi ma din dai
duk a gaggaucc.
Duk da rashin sanin abin daza ta tarar gurin
mahaifinta a dalilin ya yi fushi da ita fushi me tsanani sai ta
nufi can a yau kam ba za ta iya jure rashin ganin masoyinta
ba, babban abin daya fi damunta shi ne barazanar zuwa
gidansu da yake tun da ita ta ki yin dabarar da za ta zo gare
shi kamar yadda ya ce idan ko har ya zo din zai ji ba dadi
gurin mahaifinta tabbas zai kaskanta kaskantuwa mara iyaka.
izinin fita Tsugune take gaban mahaifinta tana neman
kamar yadda ta nema a gurin mahaifiyarta. Ko me kike so
kome kika zaba Hanifa ki yi mana na isa? Na isa na hana ki
yin duk abin dakike so ne? ina! Ni Malam Sa'adu ban isa ba,
ta dan dada russunawa dan Allah Baba ka yi hakuri ka
afuwanta....." ya katse ta da sauri kul daina ba ni hakuri babu
abin dakika yi min. ka amince Abba na tafi. Ya kada kai
Hanifa je ki duk inda kike so daga haka ya zari buta ya nufi
bayi.
Kai tsaye ma'aikatarsu ta nufa a nan ne kawai za ta
same shi a dai-dai wannan lokaci to sai dai sakatariyar
28
ofiushin ta yi mata 'yar fuska ta tarbe ta a wulakance saboda
kistinta da ke zuciyarta, ba tun yau ba take mutuwar son uban
gıdanta babu irin jan hankalin da ba ta yi masa ba duk dan su
inganta rayuwarsu amma ya yi mata fuska ya ma nuna be san
ma tana yi ba zuciyarshi Hanifansa kadai take so. Ta gane ita
ce matar da ubangidanta yake mayatar son a dalilin kyawawan
hotunanta da suka cika table din dake gabansa a cikin office
din. Hanifa ta dan jinjina maganar gami da lura da
wulakantaccen kallon da sakatariyar ke watso mata. Yanzu ke
nan ba zan samu damar ganinshi ba? ta tambaye ta. Cikin isa
ta ce, Kwarai kuwa tun da ba ku da appointment da shi
wannan dokar