shiga cikin damwua a dalilina balle har na bijirewa bukatarsa to a karshe dai na yi biyayya ga mahaifana na fitar da Suhaila diyar wani kwara da muka hadu da ita a can Kasar labanon (mahaifarta
kenan) shekarun baya.
Wayewar gari bayan an daura aurenmu kwatsam sai
wayar gari na yi Abbana ya na me dankamin takardun izanin
daukar ma'aikaci (Admission letter) a can kasar Japan tare da bisa da passport dina dana Amarya ta suhaila ban sani ba ban
kuma sani ba ba kuma shiri nab a ne.
Na tabbata lokacin da sakonnan ya isa gare ki tini
mun dage ko kuma ma mun isa kasar Japan.
Kar ki damu kar ki taba sa damuwa a zuciyarki a duk
ranar da Allah ya dawo da ni zamu ci gaba da kasancewa
kanmatsayin da muke kai a karshe ina me dada jaddada
kaunata a gare ki ki riken amanita kar ki ha'ince ni har zuwa
lokacin da zan dawo mu ci gaba da rayuwar mu yanda ya
kamata.
Naki har kullum.
Mas'ud Khalil.
La'ilaha illah anta subahanaka inni kuntu
minazzalimin: babu wanda ya cuce ni face ni kaina da na bi
son zuciyata ni Hanifa na shiga uku na banu na lalace na riga
nna gama daidaita kaina abin data fara tuhumar kanta da shi
kenan. Suma ta yi ko ko mutuwar tsaye ce ita dai ba ta sani ba
ta dai ji daukewar numfashinta ne na wucin gadi har dai daga
bisani numfshinta ya daidaita sai dai tai fa tan ta mike a haka
56
daga da irin wannan rayuwar a hannu daya kuma tana me
nazari tare da tuhumar tsohon masoyinta da lefin yaudara,
butulci, cin amana kai ba ta ma san da wane irin suna za ta
kira tsohon masoyinta Mas'ud ba! Ya cuce ta ya yau da
rayuwar ta ya riga ya gama nakasta mata rayuwa.
Ba ta dada shiga cikin tashin hankali baba ta kuma
dada fuskantar ba a cikin karamar masifar ya je fata ba, sai
lokacin da lafiyarta ta kasa inganta wasu irin kurarraji suka
feso mata a gabanta ga amsifar kaikayi da wai irin ruwa me
masifar wan da wajen ke fitarwa tin tana nuku-nuku har ya
zamanto ta fara zarya a asibiti ama babu wani sauki ciwo sai
gaba yake.
Ta dade akan layin har zuwa lokacin da layin ya zo
kanta mace ce doguwa me kyan diri tana sanye da farin
gilashi me kara karfin gani (Medical glass) a shekaru za su
kusan rubanya nata akwai wani dan karamin katako me
kunshe da cikakken sunanta wato Dr. Sa'adat Bello a gaban
teburin ta tarbe ta da fara'a 'yan mata meke tafe da ke ne? tai
hamdala gami da ajiyar zuciya domin a tsawon lokacin da tai
tana ziyartar asibitin bata taba dacen samun mace ba, ta yiwa
likitan gamsasshen tai shiru tana dogon nazari sa'ar da ta
gama jin abin dake akwai.
Ko za ki karamin haske na daga sauyin yanayin da
kika sami kankai ciki tin bayan fara wannan larurar, abin nufi
akwai was alamomi da kika lura da su a gareki.
Da sauri ta ce kwarai likita domin wanna abu kam na
damunta ta dai rasa me share mata hawaye ne ta ci gaba da
cewa Ina yawan yin fitsari akai-akaiwanilokacin ma me
zafingaske wajen fitar fitsarin sanan wani ruwa me kauri na
fitowa daga al'aurata ga yawan kai kaikayi da gabana ke min
ga yawan ciwonmara da baya.
57
Likita ta girgiza kai gami da'yan rubuce-rubuce daga
bi sani ta yi mata wasu gwaje-gwaje har zuwa lokacin da ta
tabbatar da abin datake zato 'yan mata kina ji ko? Hanifa ta
tattara hankalinta, kwarai ina ji likita, yauwa to kin gane ko a
dan binciken da nai miki da kuma amsoshin da na ji daga gare
kin a gano matsalar da ke addabar ki wanna matsalar ba wata
ba ce face ciwon SANYIkasancewar alamomin da ke nuni da
kamuwa da wannan cuta a kwai su a gae ki kamar yanda kika
she da min ta dafe kirji cikin saauri ciwon sanyi likita? Na
shiga uku ni Hanifa na banu na lalace. Relax 'yan mata kar ki
damu da yawa mutukar za ki bi sharudan d azan gindaya miki
cikin yardar ubangiji za kir abu da wannanlarura, ta ci gaba da
cewa da farko dai taimakon daya kamata a bawa me wannan
ciwo shi ne: na farko maganin yaki da kwayoyin cutar
maganin hana fitsari mai zafi, maganin hana ki kaikayi, yin
amfani da magungunan kashe kwayar cutar (Dettol).
To sai abu na gaba shi ne magungunan da mai cutar ya
kamata ya sha:, na farko maganinkashe kwayar cutar maganin
kare lafiya da kuzarin jiki, maganin kariya.
So duk na yi nazari na rurrubuta miki magunguna da
ya kamata ki yi amfani da su kusan duk baya sati biyu sai a je
ganin likita da alama magungunan basa karbarta dalilin kenan
da ya sa doctor saa'dat ke rubtua mata nau'oin wasu
magunguna masu kyau da dan karan tsada sai dai kuma
lafiyar nan dai dake nema taki samuwa a kullu yaumin jiya
tafi yau wannan abu kam na bawa Likita Sa'a mamaki duk
wasu ingantattun magunguna masu yaki da wannan cutar ta
bata amma ba nasara.
Lamarin ubangiji kena ya kan kyale ka ka yi abin
daka ga dama illa iyaka ka jirayı sakamako mutukar ba tuba
ka yi ba.
58
Dr. Sa'adat ta girgiza kanta gami da tuhumar patient
dinta anya ko Hanifa kina amfani da magungunan nan yanda
ya kamata ta girgiza kai gaskiya ban jin haka ykamata ki sani
ba karamar larura kike tare da ita ba ki tsaya ki nutsu ki mai
da hankali kar ki yiwa rayuwar ki ganganci domin akwai
illolin da ke tatare da wanna cuta a jikin dan adam ka dan
daga cikin sun e:-
Tana hana haihuwa (mata da maza), tana kashe
kwayoyin haihuwa ga mata, tana kasha manin da namıj, mafi
muni daga cikin illolinta shi ne tana iya zama HIV (Kwayar
cutar da take kawo kanjamau). Ina me baki shawara ki nutsu
ki mai da hankali wajen yaki da wannan cutar,
Duk da cewa ana daukan tsawon lokaci kafin a rabu
da ita amına idan aka maid a hankali ana amfani da
magunguna na kawar da kwayar cutar, cikin yardar ubangiji
za a rau da ita, to duk dai da cewa akwai hanyoyin da ake
kamuwa da wannan cutar alal misali:-
Yin amfani da makewayi mara tsafta barkatai, shaker
iskar numfashi, sai uwa uba ta hanyar jima'i ta dan girgiza kai
cike da alamun damuwa 'yanmata ki yi hakuri hakika kin
kamu dawannan cutar ne ta wannan hanya ta karshe wato ta
hanyar jima'l kuna a gaskiya cutar ta miki babban kamu
domin ta jima a jikinki ba tare da an dau kwakkwaran mataki
ba.
Hanifa tai shiru tai zugum lana tinani lallai hakika ba
karamar masifa Mas'ud ya jefa ta ba ya cuce ta va gama da
rayuwarta ya gudu ya bar ta da cuta me wuyar sha'ani kaicona
ni Hanifa ta fada gami da share hawaye.
Lamarin duniya akwai bantsoro duk inda dan adam ya
kai ga zatonsa be haka nantake ba a halin yanzu ko kudin da
za tai jinayar larurar da son zuciya ya haifar mata bata da shi
59
kai rayuwar ta mata kasance gwanin ban tausayi kusan komai
na ta ya kare ba da ta shi bata kuma da me ba ta duniya tia
mata ba dadi domin ta riga ta gama juya mata baya duniya me
juyi kenan kusan ba ta da kowa a halin yanzu, 'yan uwan
mahaifinta sun yi fushi da ita fushi me tsanani tin bayan
6acewar mahaifiyarta da 'yanuwanta wanda a fili take cewa
bakin cikinta ne ya bazama su shiga duniya bakin cikin ta ne
dai yai ajaliyar mahafinta kazalika dan uwansu wannan dalili
yasa suka kaurace mata suka yi fushi da ita babu me shiga
huruminta kai ita da mutumin da bashi da dangi duk daya
suke domin hatta da al'ummar unguwa sun kyamace ta sun
kaurace mata babu wata dangantaka a tsakaninsu.
Kimaniu shekara hudu kenan tana cikin wannan larura
ta rame ta kekashe ta fita hayyacinta, gaba daya ta fita
kamanninta saboda wahalar ciwo da zulumin rayuwa abin
dakan danganta ta da ciwon nan me karya garkuwar jikin danadam (Aids) tana ji tana gani akai mata kazafi aka lakana
nata wannan mummunar cuta to waye ba zai yarda ba ta
dauke da cutar? Bayan a baya tabi duk wata anyar da za a iya
kamuwa da cutar ba? Abin datake tuhumar kanta da shi kenan
kusan to dai komai da take da shi ya kare dangin mahaifinta
sun fita sabgar ta sun kasa tallafa mata babu ruwan su da
sha'aninta al'ummar unguwa sun yi shakulatin bangaro da
lamarinta babu me agaza mata babu me tallafa mata duk da
halin ha'ulain da take ciki.
Tai kuka taitakaici tai nadamar abubuwan da ta
shukawa rayuwarta ta dinga tinano da ingantcciyar kana
kyakkaywar rayuwar da mahaifanta suka dora ta akai amma
ina! ZUCIYA ta rinjayeta ta kasa aiki da abin dayake shi ne
daidai ta kasa tankwara ta ga zuwa mikakkiyar hanya to yau
dai ga dai zuciyarta ta raba ta da farin cikin ta muddin ranta
60
Eh, Mana mahaifin ta ya mutu da bakin cikinta duk da
kyautatawarsa gare ta mutum me mutukar kima da daraja a
zukatan al'umma amma sai da ta mayar da wannan alfarmar
da ke gare shi har al'umma na tuhumarsa da sakaci ga
iyalnshi bawan Allan da be ji ba be gani ba da ya yi bakin
kokarinsa wajen haka iyalinshi bisa hanya ingantacciya.
Mutum me hakuri kawaici da gudun zuciya amma
kuma sai da ta kure'shi yai fushi da ita fushi me tsanani da
har ya koma ga ubangijinsa yana me bakin cikin halin da take
cikı sanadiyyar bakin cikinta gami da abin abin kunyar da ta
jaza musu saboda Allah ina za ta kai hakkin wannan bawan
Allah, bawan Allan da ya kyautata mata ya inganta rayuwar ta
yake kokarin share mata hawayen duk abin dåta zo da shi
gwargwadon iko amma kuma shi tai wa wanan sakayya ina za
ta kai hakkinsa hakkinsa kadai ya isa ya dai-dai ta mata
rayuwa tabbas ba za ta taba ganinda kyau ba wayyo ina ma
bata bi SON ZUCIYARTA BA. to son zuciya daman 6acinta.
Mahaifiyarta ta yi kaura ta bazama duniya dama
sauran'yan wuyanta duk a dalilina shin ina zata ga da kyau a
rayuwarta? Ta tina da dinbin so da kaunar da ke tsakaninta da
'yan uwanta dama iyayenta amma duk a yau ya kau ni Hanifa
duk ni na tarwatsa hakan hakika ban ji dadi ba ban inganta
rayuwar iyayena ba kamar yanda su suka ingatan ni Hanifa na
yi asarar rayuwata.
Ta tina da kalaman mahaifiyarta a cikın wasikar
bankwana da tai mata sai ta sami kanta da rusa kuka marar
misaltuwa hakika ba karamar cuta Mas'ud yai mata ba a
baya ta yi zaton ba ta da masoyin da ya fishi a she ba haka
bane bayan shekaru, hankali da tsinkaye da hangen nesa duk
ya fita kasancewarsa namiji amma duk ya kasa nusar da ita
yana ji yana gani ta bijircewa iyayenta tai musu tawaye ta
61
saba musu ta musguna musu ta jefa su cikin abin kunya a
idanun al'umar da take mutukar ganin kimarsu har ga shi
karshe ta jefa su cikin uku ba me yawan gaske.
Duk adalilin son da take masa amma shi fa duk da son
da yai ikirarin ya nai mata idanunsa be rufe ba zuciyarsa bata
makance ba bare har ya kasa bin umarnin mahaifansa alhalin
yana ji yana gani ta bijirewa mahaifanta bata makance ba
bare har ya kasa bin umarnin mahaifansa alhalin yana ji yana
gani ta bijirewa mahaifanta duk a dalilinsa a karshe me ya
gwada mata? Ya fita hankali da nutsuwa gami da hangaen
nesa da uwa uba biyayya ga iyaye bayan cewa mace akafi sani
a wannan fagen.
Abu mafi muni daga cikin cutar da yai mata ya maishe
ta abar hutawarsa daga bisani ya yaudare ta ya ha'ince ta ya
butulce mata ya kuma ci amanar kaunar da ta gwada masa
bayan ya gama fata mata rayuwa ya riga ya gama 6ata record dinta.
Ya tsallake ya bar ta cikin kuncin rayuwa bayan day a
ci amanarta yai aure da wata macen da ba ita ba bayan ita a
dalilínsa na ta auren ya salwanta ta aikata unubı me girma
(ZINA) duk dai a dalilisan duk da kasancewar a baya ya sha
tabbatar mat a da zai aure ta da zarar ta kashe auren ta to
hakan ba ta yiwu ba har sai da me afkuwa ta afku Allah ya
bayyanar wa da tsohon mijinta ha'intar da take mata.ashe
batta sanı ba yaudararta yake yi ita ba komai b ace a gare shi
face abar hutawarsa, ta watsar da kima da darajar da ubangiji
ya danka mat a. ashe ba ta sani ba shirme take maganar aure a
tsakaninsu babu shi domin tini ya gushe daga zuciyar shi kai hakika ba karamar cuta yai mata ba da kuma ZUCIYARKІ
ba! Ta bawa kuma yau ta amsa saboda son zuciya idanunta ya rufe ta kasa hango tarin zunubin da take kwsarwa kanta duk
62
adalilin bin son zuciya, ZUCIYAR DA BA TA DA KASHІ.
Maimakon tayi kokarin lankwasa ta zuwa g aikin alkhairi
amma ina! Zuciya ta riga ta rinjaye ta ta makantar da
idanunta, kunnuwanta kai da makonai nata.
Sakayyar ubangiji a wannan lokaci sai ta riski kanta
da matsanancin so da kaunar tsohon mijinta soyayya ta
hakika burinta kenan be wuce ta malake shi ba amma ina! Yai
mata nisa aure ya riga ya harınata a tsakaninsu a badan abidin
zuciya ta riga ta kai ta ta baro.
To sai dai abin be tsaya a nan ba shin saboda Allah ina
za ta kai hakkin 'yan uwanta? Daga dai irin musifar data jaza
musu hakika wanda ta sabarwa suna da yawa ba ta kyautawa
rayuwar ta ba ina ma ba bi son zuciyar ta ba to ZUCIYA CE
BА ТА DA KASHI.
Ta kasance cikin matsaanciyar damuwa ga lafiyar ta
da ta kasa inganta ga uwa uba kazafin mummunar cutar nan
da aka yi mata wanda ya haifar da gagarumar tsana da
tsangwama daga hannun al'umma muiukar tana cikin wannan
gari cikin wannan hali tabbs za ta davvama ne cikin bakin
cikin rayuwa kwananta be kare ba wahalana shirin kashe ta
wayewar gari ta hada 'yan komatsanta ta tai banakwana da
garin ta na haihuwa tia da kanta ba ta saa inda ta dosa ba....
Allah sarki rayuwa kenan me juyi lamarinta akwai wuya ta
kan zo maka a duk idna ka dauke 14
留南沙我
Shekara Ishirin da daya cif kenan dabarun isohuwa
Hanifa gida ko kuma muce tsohuwa lya kamar yanda sunanta
ya koma a halin yanzu a tsawon wannan shekarun wahalar
rayuwa kam ta shhata har bata fatan dai-dai da dakika da daya
63
ta tina tin bayan barin ta gida ta zauna a garuruwa da dama na
Kaar nan Kaskanci da wulakanci kai dama duk wani abu d ke
tagayyara rayuwar bil adam tsohuwar iya ta fuskanta wahalar
duniya kam ta sha ta bayan tsawon shekarun da ta yi tana
fama da cutar nan da tai silar al'umma ta kyamaceta ta
tsangwame ta hart a ras ainda za ta sanya kanta a duniyar nan.
Tai aiki tai bauta ta yi duk wani abu da ke azabtar da
jikin bil'adama duk dan ta samu abin daza ta inganta lafiyarta
amma kullum jiya I yau duk abin da ta samu kan tafi wajen
neman magani irin aikace-aikacen da ta yi ba ita da kanta ba
za ta iya lissafa su ba. Rayuwar tai mata kunci duniayar tai
mata ba dadi zuciya ta kai ta ta baro ta gama kaskantar da
rayuwarta.
Al'umma na kyamatarta dalilin warin da take yi
rowan da ke fita daga jikinta ya haifar da hakan dalilin kenan
dab a ta jimawa a duk inda take aiki ko aiki kam na wahala
amma a karshe sai ai mata wulakanci a yi mata korar kare tai
kuka tai nadama gami da neman gafararubangiji a bisa
musibar da tsohon masoyointa ya jefa a she ba ta sanı ba ba
karamar cuta yai ma ta ba yau ita ce ta zama abin kyama ga
al'umma ta dinga tinano irin ni'imtacciyar rayuwar da ta tashi
a cikinta duk da cewa iyayenta ba mawadata ban e to amma
suna da rufin asirinsu dai-dai gwargwado.
Wane irin gata ne iyayenta basu nuna .mata ba har
abada ba za ta taba mancewa da wannan ba bata taba zuwa
neman wani abu gurin mahaifitana ko mahaiiyarta ba tare da
sun share mata hawaye ba mutukar suna da yadda za su yi
mahaifinta mutum me hakuri da sanin ya kamata me jumurin
neman na kansa da son kyautatawa iyalensa mutumin da ya
sadaukar da rayuwar shi dan rayuwar susta inganta haka abin
yake gurin mahaifiyarsu mace me kokarin share musu hawaye
64
a duk lokacin da bukatr hakan ta taso dukkan ilahirin abin
data samu ya kan kare ne a kanshi barin ita da tafi fifita ta
kasancewarta 'yar fari da ta gwada mata kauna fiy da sauran
'yan uwanta.
Amma a yau gad a abin d ta saka mata. Ta bazama ta
bar garin da tai shekara da shekaru a cikinsa duk a dalilin
bakin cikinta mafi munin abu da baza ta taba mancewa da shi
ba shi ne yanayin da suka rabu da mahaifinta yana me tir da
allah wadai da ita har ya bankwana da duniya wannan abu n
zuciyarsa saboda Allah ya ko zata ga da kyau?
Mas'ud ya gama da ita ya gama da rayuwarta ya kuma
kaita ya baro tsakanin da shi sai dai sakayyar ubangiji tabbas
ta san ta so shi a baya a halin yanzu ta gano cewa tin fil azal
so da sha'awa ta rinjayi komai amma babu batun kauna a
tsakaninsu idan harda kaunar ta fisabillillahi da basu kasance
a halin da suka jefa kansu ciki ba da kuma be yadda ya jefa
ta cikin musifa ba tabbas so da sha'awa ne a tsakaninsu babu
batun kauna tun shekarun da suka gabata ta gama gano
mutumin da take sonsa ta ke kuma kaunar sa. Kauna ta hakika
kauna ta dan Allah shi ne mutumi kaunace ta domin lillahi
wato tsohon mijinta Abdulzahir da ta ha'ince shi duk da
kyautatawarsa gare ta.
In banda ZUCIYA DA BA TA DA KASHI me kamar
Abdul zahir har me zai yi da wani da namiji to amma ina!
Kaddara ta riga fata ZUCIYA BA TA DA KASHI, ta riga ta
rinjaye ta (Har kululm bawa ya kasance me neman tsari da
zuciyarsa).
Hajiya Sauudat ita ce macen da ta dade tana aiki tare
da ita ita ce kuma matar da tai silar fitar da ita cikin larurar da
take ciki tsahon shekaru duk da cewa ba karamin kudi ta
kashe ba saboda ciwon ya ci karfinta tsohuwa iya ba za ta
65
taba mancewa da wannan 'yar tahalika ba mace me kyautayi
da sanin darajar bil'adama idan muka kawar da wannan halin
nata za mu ga cewa farat daya Allah ya hada jinsu da wannan
baiwar Allah ta riski kanta da kaunarta gani da tausaya mata.
To fa tin daga lokacin suke tare duk da cewa ba wani dadewa
tayi a gidan ba domin duka duka ba ta zarce shekara shida a
gidan ba.
Aikinta a gidan be wuce kula da yara ta shaku da
yaran fiye da zaton mutum wannan dalili ya dada kara dankon
kauna a tsakaninta da uwar dakinta sun zauna a garuruwa
kamar biyu har zuwa yanzu da suke zaune agarin Oshogbo
babban birnin Jahar Osun. Sai dai kuma me gidan be cika
zama a gidan ba saboda yawan aiyuka yau ka ji sh awanan
gari gobe ka ji shi a wancan kai wani lokacin kasar
dungurungum yake bari dalilin kenan da sai tsohuwa iya
tadau tsawon lokaci ba ta sanya me gidan a idonta ba
musamman da yake a duk lokacin daya sami damar yin hakan
ya kan tattara su lokacin shi ne ga iyalinshi mace daya tilo
kenan taıkar da dubu domin duk da kasancewar sun
manyanta girma cimma su hakan be hana su aiwatar da
dandasheshiyar soyayya ba.
Yanda take ji da shi take kuma kyautata masa haka
shi ma yake sonta ya ke kuma kyautata mata mutum ne me
Kokarin kyautatawa iyalinshi da ma duk wanda yake
Karkashinsa halayyarsa dabi'unsa ya kan mata kama da
matsawon mijinta mutumin da ba za ta taba dena kaunar sa ba
a badan abidina a wasu lokutan ma takan ga kamar ta san shi
wasu shekaru can da suka gabata to amma kamar ce domin ta
kasa tinano inda ta san shi rikicin tsufa ne kawai abin datake
ayyana a ranta kenan aduk lokacin da tinanin hakan ya zo
mata. 66
A halin yanzu shekarunta hamsin da bakwai zahirin
gaskiya za kai tsammanin ta fi haka nesa ba kusa ba alamun
tsufa sun bayyana a gare ta Karara to yanzu ne ma tad an yi
kyan gani dalilin zamanta gidan Hajiya Saudat. Abu uku ke
zuciyarta abu ukun nan ne dai muddin rai ba zai taba gushe
ma ta ba burinta tunaninta kai dama komai ya ta'allaka ne a
kan abu ukun nan wato mahaifanta da yan uwanta, mijinta sai
daya tilo da Allah ya huwace musu a mace yake a raye yake
ba ta sani ba tin bayan barinta gidan mahaifisan ba ta kuma
sanya shi a ido ba, so da kaunar gudun jininta ako da yaushe
shi ke zuciyarta.
Sai abu mafi mahimmanci a rayuwar ta shi nebatun
mahaifanta 'yan uwanta da kuma me gidanta burinta kenan ta
gansu ta nemi afuwarsu amma ina! Ba za ta ce ga a duniyar da
mahaifiyar ta da Rannenta suke ba amace suke a raye suke
Allah ne masani duk da cewa ta san inda tsohon mijinta yake
wato Ainihin garin ta na haihuwa to amma ina abadan abidin
ba za ta iya kusantar inda yake ba shin da wane ido za ta kalle
shi to sai dai babban abin day a fi tsaya mata shi ne batun
mabaifinta, Gwanda ragowar zata iya neman gafararsu idan da
rabon ganawarsu to shi fa? Bayan tini ya riga yai bankwana
da duniya ya tafi yana me dauke da bakincikinta ba tare da ya
afuwanta mataba mun sani cewa ranar gobe kiyama nafsinafsi ne ma'ana kowa ta kansa yake yi, ita ce ranar nan da
Allaly (S.W.T) yake fadi cikin al'kur'ani a gurare da darna
misali cikin suratu Abasa inda ya ke cewa: "Ranar da m tum
yake gudu daga dan uwansa, da matarsa dal ubansa, da
matarsa da diiyarsa, ga kowane mutum a ranar nan akwai
wani sha ani da ya ishe shi. Aya ta 34 zuwata 37.A
To shin ita da ba ta wanye da mahaifanta iafiya baya
za ta yi kenan a badan abin ba za ta taba samun nutsuwar
67
zuciyarta ba tai kuka tai takaicin halin da ta bari zuciyaarta ta
sanya ta a ciki a duk lokacin da ta tina haka ta kan yi kuka na
fitar hankali to a duk lokacin da irin hakan ta faru hajiya
Saudat ta kan matsa mata da tambaya amsar da ta kan bata dai
daya ce wato mahaifanta ta tuna da suka riga mu gidan gasiya
a duk lokacin a ta ji haka ta kan amsa mata ne amma a can
kasan zuciyarta tai amannar akwai abin dake damun wannan
baiwar Allah.
Ta lura da kyau gaba daya rayuwarta ta taa'allaka ne
wajen bautawa Ubangiji da neman gafarar ubangiji yawanacin
lokuta bakin ta ya kan kasance ne cikin azumi nafilfilun cikin
dare kuwa babu ranar fashi kai a kusan ko da yaushe ba
samun yin bacci saboda tahajjidi haka nan ida da rana ne har
zuwa yamımaci mutukar ba wani aikin take ba za ka iske
cikin ibada ne kai ko aikin take yi zaka iske ta rike da carbi a
hannunta to zancen ta kalamanta halavar ta duk abin koyì ne
ga me neman tsira ranar gobe kiyama. Hajiya Saudat ta kan ji
dama ita ce a matsayi irin aa tsohuwa iya tabbas ta ci ribar
rayuwa to sai dai duk das haka takan yi kokarin koyi da
kyawwan dabi'unta.
Tsohuwa iya kenan ma'abociyar iba da matar da ta
sadaukar da rayuwarta wajen bautar ubangiji tare da neman
gafarar sa mace me tarin sanin ilmin addini da kokarin aiki da
shi macen da tsufa dawahalar rayuwa be sa ta gaza daga
bautar ubangii ba tare da neman gafarar sa mahaifanta, 'yan
uwanta tsohon me gidanta dama dan da Allah ya huwace
imusu kan kasance sawun gaba wajen nema musu rahamar
ubangiji.
A ya suma shirye-shiryen taifya babban birnin tarayya
Abuja domn taya babban AMinin me gidan murnar bude
katafaren karnfenin sarrafa kayan cid a sha na gwangwani.
68
Tare da taya shu murnar samun shugabaneım yan kasuwa na
Kasa bakı faya.
Gia yanda tsohuwa iya Jag a iyayen gipata na y in
gagarumın shum domin ta ya abokin me gidan murnat
farincıkin abin Alkhairin da ya same sbi ta san ba karamn
matsayi mutumin yake da shi ba. a kashe garin ranar da za ya
ga yi gagarumin shi ne tare suka dira Abuía suka yi masauki a
katafaren gidan da ya zama mallakınsa ya tanade shi domin
saukar iyalınshi asokoro.
Wayewar gari sun yi ta ne cikin ruguntsimun shagalin
taya abokinsu murnar gagarımim ci gaban abokin mai gidanta
ya samu.
Da misalin Karfe hudu na yanmaci yalın Alhaji
Abdul, suke gabatar da nasu gagarumin shagahnea harabar
katafaren gidanshı, cikin wadan da suka halarei taron. hat da
tsohuwa iya dame dakinta da madaukacın yalınta. Kusan duk
wani abu su Hajiya Saudat ke gabatar da shi wanda hakan ke
nuni da matsayın da take da shi a iya gane-ganen tsohuwa iva
da kuma irin gawurtattun atta zirai da tat aikra Katkashms
zahirin gaskiya ba ta taba ganin gida me kyau haka ba kan ba
tama taba ganin ko me kamar sa ba ta saki bakı tana kallon
ikon Allah tamkar bakauyen da ya fara shiga birni.A duniyar
nan kuwa akwar wata matsala ko damuwa a tattare ga ahalm
gidan nan? Tabbas babu mutumin da Allah yaiwa ni ima irin
wannan me kuma ya rage masa da ya wuce kyátitata tsakanin
sa da mahaliccinsa abin da take rauwa zucryarta keu an
Wata yar kakkaywar yarinya yar kimanin shekara
bivar ta tawo da gudu yayın da 'yar uwarta ke bive mata da
alamun dai tsokana tar vo a dai-dai lokacin ta dire kan
tsohuwa tya