An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ZUCINA BА
TA DA KASHI
NA
ZAINASIKASR BIRONA
Mrs. Sunus Sanl Biscpe
ZUCIYA BA TA DA
KASHI
9
ZAINAB KABIR BIROMAN
(MRS. SUNUSI SANI BRISCOE)
e-mail Address:- zainabkabir2007@yahoo.com
Copyright 7ainab Kal
Hakkin Mallaka (N) Za
AN PARA BUGAWA
2007
Printed By Al amin Bookshop Pnauag& Pubhshing Company
156 S/T tun Mandawari
Kano Stale
GS.M 08044114269
2
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) tsira da aminci su
tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Mohd (S.A.W) har
kullum dai ina me dafa godewa iyayena tare da yan uwana ubangiji ka sakanta musu da gidan Aljanna da daukacin
musulmi baki daya.
TUKWICI
A gare ki Jummai Yunusa FGagge ma'aikaciya a Fagge
Clinic godiya mara iyaka gare ki.
GAISUWA DA FATAN ALHERI A GARE KU:-
Halima Isa Gambo Gumel
Aisha Ringim
Binta Madakı Bauchi
FatimaYan kaba
Fatina U/Uku
Halima Kaduna
Murjanat Kilishi Bauchi
Sharifa Gumel
KARIN HASKE
Ginshikin da aka gina labarin yai la'akari ne a kan ZUCIYA manzo (S.A.W) ya fada mana ceewa: Akwai
wata tsoka a jikin dan adam idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru idan ta bacii dukkan jiki ya bac. Na'am it ace zuciya.
Wannan ya nuan mana tasirin da zuciya ke da shi a
rayuwar Dan adam.
3
Hakika Ita zuciya me umarta ce da mummunan abu,
in ka ga me kyau to daga ubangiji ne. Abokin tafiyar
zuciya shi ne shaiddan domin shi ke dada ingiza ta. Ya
kama taď an adam y adage wajen karya akalar zuciayrshi
zuwa ga aiki me kyau.
A hannu daya kuma labarin yanai mana nuni a
bias halin da dan adam ya tsinci kansa a icki hairan ko
sharran shi ya jawowa kansa da wani laifi na sabawa
Umarnin Alah saboda faddin Ubangiji mađaukakin sarki:-
Shin kuma a lokaicn da wata musiba hakika tan ta same ku
alhalin kuwa kun sami biyunta, ka ce daga ina wannan
yake? Ka ce daga wurin rayukanku ya ke.., (Suratul
Ali'imrana aya ta 165).
Ubangiji ka bamu ikon karkata zukatanımu a bsia
turbar gaskiya ka kuma tsaida dugaduganmu a kan hakan.
'Yar uwarku A musulunci
Zainab Kabir Biroman.
GARGADI
Ban yi wannan littafi domin wani ko wa tab a, ban
kuam yadda a yi amfani da shi ta kowace siga ba ba tare da
izinin marubuciayr ba.
BUGAWA A NAʼURA
Mubarak Ahmad Kurawa
Yolawa Computers& Communications
Email: almubrak@yahoo.com
G.S.M: 08025475907, 064334983
4
1
nnalillahi wa inna ilaihir raji'un, wala haula wala
Kuwaa a babul aitht azin" Abin dake fie
daga bakin Abdulzahir ke nan sa'ar da idanunshi ya
gane mishi abu mafi muni a tarihin rayuwarshi, jikinshi ya
shiga wani irin 6ari da tsuma tamkar wanda aka sawa
shociking, idanunshi ya kada ya yi jajir. Ita ma din ta kadп
ta dimauce to sai dai fargaba da tsoro ya shafe duk wani
damuwa da takaici. Dakika biyar ke nan da mikewarta
wanda hakan ya yi dai-dai da sa'a biyar a gurin Mas'ud
saboda zakwadi da zumudin kasancewar da za su yi tare na
tsayin wannan dare, dan haka yake ganin dakika daya daidai take da sa'a daya, to dan me ya sa za ta nemi takaita
musu lokutan da suke da shi. Baya kaunar ko da kika daya
ta subuce Mus'ud aga dai wannan ni'imtaccen daren. Abu
mafi a'ala ya je ya sunkuto abarshi a sa'ilin da ya mike cike
da doki da nishadi, ya shiga fadin, "Darling ina kika labe
ne? kin san babu abin danake muradi a wannan dare face
kudindina da lallausar fatar jikinki." A dai-dai lokacin ne
idanunsa ya yi arba da mutumin da ba su taba mafarkin
ganinshi ba a dai wannan lokaci. Take hantar cikinsa ta
kada tsoro da firgici ya bayyana karara a tare da shi, ba
Mas'ud din ba hatta ita kanta Hanifa ta tsorata da irin
kallon da maigidanta yake masa kai ka ceba shi ne
Abdulzahir din nan me sanyi da saukin kai ba.
Shakeshi zai yi? duka zai sa masa ko kuma
makami zai samu ya soka a kawon zuciyarsa kamar yanda
shi ma ya huda tasa? Kai duk wani abu da ya aiwatar masa
ba zai taba kanakare mikin da ya dasa masa a zuciya ba.
"Ubangiji ka kawo wani sauki daga gare ni a bisa wannar
5
musiba da ta same ni, ka kuma tsa-ake zuciyata daga
rudin Shaidan."
Take ya ji zuciyarshi ta i ta sauke duk wani
kudiri da ta yi. Ya runtse idonsa ganı da nuni da hanya
ma'ana ya fice mishi daga gida. Ga Mas'ud ta fi nonofari
abin dakawai yake so a rayuwarsa ke nan a dai wannan
lokacı be ko tsaya ta kan princess din tasa ba bare kayansa
da ya bar su a falon ma'ana daga dai shi sai singlet da
gajeren wando ya fita. Take ya fadi ya zube a nan cikin
wani irin yanayi tamkar wanda numfashi be tare da shi. Та
kaďu ta tsorata sai kuma ta ji yana fadin, "Hanifa kin cuce
ni, kin cuci rayuwata, ba zan taba yafe wannan yankan
Kaunar da kika vi min ba." A zatonta a tunaninta zai sahale
mata ne amma sai ta ji shiru be ce komaı ba.
Tun bayan da wannan abu ya faru ne a ka shiga
zaman bebaye a gidan, ba ya tanka mata baya shiga
harkarta kamar yadda ita ma take kunya da tsoron kusanlar
inda yake. Ba ya cin abincinta ba ya sauraronta kai kusan a
komai ma ya yanke alakarsa da ita ila dai duk wani abu da
take bukata be yanke ba alaka ce dai a tsakaninsu ta ky au.
Ta damu ainun da wannan mataki da ya duaka haushi da
tsenar Mas'ud ya dirar mata domin duk shi ya haifar mata
da wannan matsala, ta san tana son Mas'ud kuma ba ta iya
hada sonsa da kowa ba, to amma fa tana mutukar gar in
Kima da mutuncin Abdulzahir shi ma din ba za ta ce ba ta
son sa ba illa dai soyayyar Mas'ud da ya rinjayi zuciyarta
(da kuma son zuciya ba!) har ta fara nadamar abin data
aikata abu mafi sauki ta yanke duk wata alaka da ke а
tsakaninta da Mas'ud duk da ta san abu ne me wuya amma
2a ta yi bakin kokarinta. 6
Ta shiga daniuwa kwarai da gaske a zatonta Abdul
Zai tozarta ta ya tona mata asiri, anma sai ta ga akasin haka
saboda Allab in ba me kaunarka ba wa zai maka haka?
Tambayar da take yi wa kanta ke nan. Yau da a ce ya kai ga
tona mata asiri ya zı ta yi ke nan? Dangin mijinta da sun
samu abin yi ke nan a dai inda suke gwada mata wannan
kiyayayar to ma duk ba wannan ba, shin da wane ido za ta
kalli iyayenta? Wane irin abin kunya za ta ja za musu ke
nan hakika da ta yi silar saka su cikin nummunan bakin
ciki marar iyaka, kai kila ma su tsine mata. Dole ta ga
girmansa kamar yadda ya zaına dole ta yanke duk wata
alaka da ke tsakaninta da Mas'ud duk da son da suke wa
junansu, matakin da ta fara dauka shi ne kashe ilahirin
wayoyinta ta gida da ta hannu, fita kam daman tun lokacin
da wannan abu ya faru ko kofar gida ba ta taka ba to da
wane idon za ta dube shi har ta nemi izanin fita? Ko da
yake wannan ba wani abu ba ne a gurinta satar fita ba, in
dai a kan mas'du ne ba sau daya ba sau biyu ba sai dai kar
a kara.
Kwanaki ishirin da uku ke nan da faruwar wannan
lamari har yanzu dai babu abin daya sauya daga irin zaman
kuramen da suke. Abdul ya yi fushi da ita mara iyaka har
yanzu zuciyarshi ta kasa dai-daituwa guri guda. Be taba
zato ba, be taba tsammanin Hanifan da yake ganinta
kamila, me tsoron Allah gami da rikon addini za ta aikata
haka ba. ya yi takaici ya yi bakin cikin abin dindaunshi ya
gane mishi, matarshi da wani ba! kai wannan abu ba zai
taba mancewa da shi ba, ashe kaunar da take gwada mishi
duk karya ne, soyayyarshi a gare ta ashe duk zance ne,
yaudara ce kawai, tana nan tana ha'intarsni duk be sani ba,
7
Karshen wulakanci ke nan, Karshen cin zarafi ke nan kawo
mishi kwarto gida ba. akwai abin daya fi wannan? Akwai
mutumin da ya taba yi mishi yankan kauna irin wannan?
Babu shi, to shin ma waye wannan mutumin da ta kawo shi
har cikin gidanshi? Amsa ita ce be sani ba, sai dai ya yi
alkawarin binciko ko wanene, to in ya binciko shi fa?
Ragowar da take mu'amula da su fa? Wa ya san adadinsu?
Duk da cewa be ganta ra'ayil ainun ba amma ya yi amannar
da tana ha'intarsa, to yanzu meyc abin yi? wane mataki ya
kamata ya dauka?
Sa'ad abokinsa ne da suka tashi tun kuruciya sun
aminta da juna Abdulzahir mutum ne me zurfin ciki zai yi
wuya ka ji abin dake cikinsa amma a yau sai ya kasa rike
abin dake cikinsa ya gama zayyane mishi komai tare da
neman ma fita bisa yakinin dayake da shi ba zai taba ba shi
shawara mara amfani ba. sa'ad ya yi shiru yana nazari
tabbas ba sau daya ba ya sha jin rade-radi makamancin
haka amma da yake ba gani ya yi da idanunshi ba sai ya bar
komai a cikinsa, dadin dadawa da yake Hanifa yarinya се
ime siffar mutanen kirki ga kammala a tare da ita to amma
yau duk ya kau kasancewar ya jiyo daga bakin da ba zai
karya ba to amma fa daga shi Abdul din har shi kansa babu
wandh ya yi amannar ya kama ta dumu-dumu ma'ana
ra'ayul ainun (abin daka gan shi kuru-kuru) shawarata a
garc ka Abdul mu kawar da komai gefe guda tun da duk
wannan abu da muke magana a kai zargi ne da gani har kai
babu wanda zai ba da shedar idanunshi ya gane mishi abin
dayake zargi, ko a shari'ance ba ka taba tabbatarwa da me
lefi le finshi ba tare da kwararrun hujjoji ba ko kuma na cсе
shedu. Abumafi kyau mu bar awnnan magana a tsakaninmu
kar ma mu daga ta wani ya ji, mu mika lamarin ga Rabbil
Izzati da ya ganar da mu gaskiya a duk inda take. Sa'annan
ka kara kulawa gami da taka tsantsan ga duk wani motsinta
ina ga wannan shi ne mafita.
Abdul ya girgiza kansa sa'ad ba fa sharri na yi mata
ba... ya katse shi amma dai idanunka be ganc maka zahirin
abin dakake zargi ba ya dafe kai gami da runtse ido, Hanifa
kin cuce ni kin min karan tsaye a rayuwata duk da son da
nake miki kin cuce ni! kin cuce ni!! Kin tozarta ni hakika
ni kam ba zan taba tozarta ki ba.
Rayuwar ta yi mata ba dadi, gidan ya yi mata kunci
ta shiga damuwa mara misaltuwa dangin mijinta dai daman
ba wani ziyartarta suke ba saboda karan tsanar da suka dora
mata, kannenta kuma ba kasafai suke zuwa ba saboda
matsin babansu. Kullum ita ke nan cikin zaman kadaici me
gidanta ya yi fushi da ita fushi me tsanani, a wannan lokaci
sai ta samu kanta da ra'ayin bude wayoyinta kamar hadin
baki sakwannin da Mas'ud ya turo mata ta hanyar text
message da ke ajiye a na'urar adana sakwanni suka shiga
shigowa daya bayan daya, tun daga ranar da lamarin ya
faru har kawo yanzu duk dai jaddada soyayyarsa ne a gare
ta tare da tabbatar mata yana tare da ita a kowane hali a
kowane irin yanayi.
Tun tana karantawa har idanunta ya gajiya, a dai-dai
lokacin ne kiraye-kirayen Mas'ud ya cika wayoyinta
tamkar yana da masaniyar bude wayar. To fa ya kira ta fi
sau a kirga amma ta ki dagawa ko kadan ba ta so zuciyarta
ta kara rinjayarta. Tana son Mas'ud ko kadan ba za ta kasa
kaucewa bukatarsa ba mutukar suka yi ido biyu akwai ani
abu ne da take fatan kasancewa tare da shi irinsa. A zatonta
و
zai gaji ya Kyale ta ama da alaına ba shi da niyyar yin haka
tana yur surin kashewa yayinko ya shigo daga Mas'ud inda
vake hafa ta da gınnan zetin Allah ta saurere hi ko da na
minti faya ne. A dai-da: lokacin da ye yi caliing dinta.
Uhin Mas'ud ina jin ka. Ta ce da shi sai da ya vi wani irin
gwaron numrashi da har sai da yn isirga mata har cikin
jikirta Hanife mme ya sa za kiyı mia haka? Me ya ai za ki
guje ni bayan kin san a duniya babe macen da nake so da
Kauna nake kuma fatan mallakarta irin ki? Me va sa za ki
yi Rokaria toshe duk wata hanyar da zan gk Why
Hanifa?
Mas ud ka yi hakuri ka kyale rayuwata ta huta ka bi
ka jagula min tunanina me yasa ba za mu yihakurı da juna.
ba? a dalilin ka mijina na fushi da ni mara iyaka shin dn
Allah da ya lasa wannan abu ya kake gani? Ya tari
numfashinta mutukar sonki yake da gaskıya ba zai taba
tozarta ki ba bare har ya fasa wannan sirri, mu bar wannan
ma abin duba a maganarki shi ne fushin da kika ce mijinki
ya yi da ke to meye abin damuwa? Ca nake irin wannan
damar muke jira kina ganin daga nan ba zai hakura ba ne
ya sahula miki domin daman ssshihigi ya yi mana amma
smata ba ta shi ba ce, Hanifa ba ta da wani miji face Mas'ud
finta
Hannif aki tausayawa zuciyata ki tallafi rayuwata.
ha zan iya rayuwa ba tare da ke ba kin zame mini tamkar
ini da tsoka. Mas'ud ka yihakuri mu hakura da juna ba zan
iva rabuwa da Abdul ba ko rabuwar ce ma mu yi ta ta dadi
domin ya kyautata min va kaunace ni.... Ya katse ta d
cewa duk kaunar da zai gwada miki kin san da sanin ba za ta ko kai daya bisa goman wadda nake ıniki ba. mata nawa
10
na ki? Mata nawa na yasar duk a dalilinki Hanifa? Na nemi
na saba da kowa duk dai a domin Hanifa, me ya sa kike
neman guje min Hanifa ke kadai nake so ke kanki kin san
haka...
Be gushe ba yana me baibaye ta da irin matsanancis:
son da yake mata gami da kwadaitar da ita irin
ni'imtacciyar rayuwar da za su shiga da zarar sun mallaki
junansu. Abu mafi a'ala ta san hanyar da za ta bi ta subuto
ta dawo hannunshi ma'ana su yi aure.
Cikin sanyin murya ta ce, Are you sure Mas'ud?
Kina shakka ne? wane buri nake da shi da ya wuce ki zama
mallakina Hanifa? Hankalinta ya gushe zuciyarta ta shiga
ayyana mata abubuwa da- dama. Ka ba ni lokaci zanyi
shawara da zuciyata Mas'ud. Is okey, domin na san
zuciyarki za ta yi miki zabin 'Ni' Mas'ud mutukar za ta
kwatanta adalci. To fa kwanyar Hanifa ta dau aiki, zuciya
ta shiga aikin nata, ta saka wancan ta saka wannan. Тa
yanke duk wata alaka dake tsakaninta da ma'su ta rungumi
mijinta koko ta rabu da mijinta ma'ana ta kashe aurenta ta
koma ga mallakin zuciyarta Mas'ud? A'a ko alamar babu
na zabe cikin dayan biyun kamar yadda ba ta fata ta rabud
a kowannen su. Tana daraja Abdul tana girmama shi
hakika yana da mutukar muhummanci a gare ta to amma
'So' fa? Hakika yana ga ms'ud shi kadai take wa son da ba
ta iya hada shi da wani. Abu mafi muhimmanci ta ci gaba
da zama bisa tubalin da ta ginawa kanta ma'ana dai ta сі
gaba da ha'initar mijinta ta hanyar kasancewa da Ma'sud.
ZUCIYA BA TA DA KASHI take hankalinta ya
gushe tunanina ya 6ace ilmi da baiwa da basirar da Allah
ya yi mata duk suka kasa amfani a wannan lokaci saboda
11
kawai idanuinta ya rufe zuciyarta ta makance ta raja'a ga
son duk abin data ayyana mata. 'SON ZUCIYA' 6acin ta.
(Ubangiji ka fisshe mu daga son zukatanmu, ka ba mu iko
da aikata kyakkyawa ka hane mu da aikata mummuna,
amin summa amin.)
Zuciyarta ta shiga tuna mata irin ni'imtacciyar
rayuwar da suke gudanarwa ita'da tauraronta, to yaushe ma
za ta yi saken da zai subuce mata bayan ko shi kansa
megidanta ba ya iya yi mata yadda Mas'ud din yake mata.
Zuciyarta ta shiga tunasar da ita dan haka ta yi amannar
dari bisa dari tana Kaunar Mas'ud ko da kankanin lokaci ba
ta kaunar ya subuce mata.
Ga'Mas'ud dai ba haka ya so ba, to anma da babu
ai gwamma ba dadi, sun kimtsa sun hada gurin da za su
hadu to sai dai me? Da wane ido za ta dubi Abdul
ballantana har ta nemi izanin fita yanzu dai ba kamar da ba
ne dole ta yi taka-tsantsan ba re ta ce za ta yi satar fita.
Karon farko ta ji haushin Abdul har cikin ranta ko da yake
a baya ma ta ji rini wannan tsanar tashi to amma rashin
tozarta tan da ya yi sai ya shafe komai.
Dai-dai misalin karfe tara na dare ta fuskanci Abdul
ya gama duk abin daya saba yi a irin wannan lokaci wato
kama daga wanka nafilfilu har zuwa ga cin abinci wannan
kam al'adarsa ce a kowanne lokaci sai dai wannan karon ba
ta zaton ya ci abincin saboda kauracewa cin duk wani abu
da ta girka da ya yi, ta hade ta kimtsa cikin sleeping dress,
violet colour (ruwan hoda-hoda kenan) wadda take
bayyanar da surar. jikin bil'adama. Ta mutsike jikinta da
Al'oud nola hade da ward taif. Daga bisani ta feshe ilahirin
jikinta da body spray gami da turaren shafawa na Burj Al12
Haramain. Haka nan kayan jikinta ta bi ko ina ta feshe su
da turaren Marvia, gucci Envy haxe da Sotto - Voce.
Hatta da fuskarta sai da ta gyara ta ta murtsike ta da
powder nature Essehnce wadda aka yi ta da ganyen
Aloevcra. Tana gab da shiga sashinsa ne tsoro da fargaba
ya kamata shin da wane idon za ta dube shi ne? to sai dai ba
karmain karfin hali ta yi ba da ta sakai ciki. Yana zaune a
kan rest chair ya kwantar da bayansa jikin kujerar yayin da
kanshi kedage a sama yana kallon ceiling a lokaci guda
kuma yana karkada kafafu da alama yayi nisa a tunanin da
yake domin be ji shigowarta ba sai sautin maganarta da ya
jiyo. "Abdul..." ya dago ba tare da ya ce mata uffan ba. ya
bi ta da kallo irin kallon nan na kurulal sai kuma ya dauke
kansa yana me girgiza kai.
Tsugunawa ta yi gabanshi gami da dafa masangalin
kujerar da yake, "Please Abdul ka tausaya ka afuwanta min
na san na yi kuskure to amma ina me fatan kar ka zargi
komai a ranka, abin dakake tunani sam ba haka ba ne.
Please Abdul ka afuwanta min." Ta sunkui da kai kamar
me shirin kuka.
Ya kalle ta sama da kasa yarinya karama na shirin
raina masa hankali a lokaci guda kuma ya tuna da maganar
sa'ad, lalali kam zargi ne tun da be gan ta kuru-kuru ba, to
amma ko ma meye abin data yi sam be dace ba yaya za a yi
ta shigo masa da kato cikin gida cikin kuma tsakiyar dare.
Ya dada tamke fuska, duk abin dabawa ya ga zai fisshe shi
a rayuwa ba sai ya aiwatar ba komai kake dai akwai Sarki
Allah da ba za ka iya foye mishi komai ba, kima daina 6ata
bakinki wajen ba ni hakuri ni babu abin dakika yi min
komai kika daukarwa kanki dai-dai ne. ni dai ina me dada
13
ba ka hafuri wannan matakin da ka dauka ba zan iya
jurarsa Fa, ka manta da komas Abdul mu dawo normal. A
lokarn da take kokarin k wantowa jikinsa ya nıke gami da
numi da hannunsa, "Mi" Ya girgiza kai ba dai ni ba
kasancewa da fasıki ba." daga haka be ake cewa komai ba
ya ina ya bar mata dakin. Ba ta dai yi fushi ba a ko da
yaushe ta dinga bin shi tana ban baki a memakon ya yi abin
datake so wato hakuri sat ya dinga nuna kyamatarta ma
yake wannan abu kam ya kora mata rat ita ma la yi fushi
mai yawa ta fita barkarза.
Sanzu a hankali zuciyarsi:i ta lafa har kullum neman
zabin Ubangiji yake wato kasancewar su tare ko kuma
rabuwarsu to ya dai barwa Ubangiji zabin komai. Tabbas
yanzu idan ya furta ya ce ya sake ta za a nemi sanin ba'ai
ko ko zai fadi abin dindaunShi be gane mishi hakikatan
ba? ko ma ba don haka ba har abada ba zai taba tozarta ta
ba don albarkacin zuri'ar dake tsakaninsu.
Al'amarin Hanifa kuwa sai abin daya yi gaba ta fita
harkar Abdulzahir ta fita sabgarsa kwarai da gaske to a kan
me mea za ta tsaya bata lokacinta a banza. Abin
dazuciyarta ke so wannan kam babu me iya hana ta.
Rayuwa ta ci gaba da gara musu yadda suke so
dunivar ta yi musu dadi yanzu kam ba ta shayin komai
domin Abdulzahir ya zame mata tamkar alakakai, neman
hanyar rabuwa da shi akwai take ba ta ko tausayawa zuri'ar
da ke tsakaninsu duniyarta kawai take ci, yayin da
masoyinta yake faranta mata yadda da take muradi lallai
gaskiyarsa da ya ce a duk duniyar nan shi ya fi dacewa da
ita, ba ta dada gasgata hakan ba irin a wannan lokaci ta ci
gaba dai da aiki da duk abin dazuciyarta ta umarce ta
14
Hakika duk mutumin da be fi karfin zuciyarshi ba yana
tare da wanala, Ubangiji ka ba mu ikon fin karfin
zukatanmu. amin.).
Ba tun yau ba mali akasarin dangin mijinta suke
yamadidi da zancen magana ta dinga yaduwa tamkar wutar
daji, wanda ma be sani ba a wannan karon yana da
masaniya to tura dai ta kai bango ma'ana za su fuskanci
dan uwansu da wannan batu tunda shi wutar so ya rufe
masa idanunsa ya kaswa gane abind a su da suke a gefe
suka gano. To sai dai a lokacin ne shi ma kusan komai ya
kusa ya warawre masa illa me ya gan su ra'ayi! ainun ne
har yanzu be ba amma a iya bınci ken da ya yi ya tabbatar
abin dayake zargi gaskiya ne ya sha dana mata tarko tana
ketarewa.
Soha yarinya ce da take mutukar son Mas'ud so
mara misaltuwa a duniya ba ta da burin da ya wuce ta
mallake shi to amma ina shi be san ma tana yi ba, domin ba
ta gabansa duk da yakinin son da ya san tana yi masa shi
dai kawai Hanifansa yake so duk da cewa ba za ta nunawa
so han da konai ba to amma dai ba wannan ce a gabansa
ba, bar zuciya da abin daTake so.
Soha yarinya ce da ta tashi cikin gata mara amfani
gatan da ya illatar da rayuwarta take kuma cin duniyarta
yadda take so, irin rayuwar da ta so su yi da Mas'ud ke nan
tun bayan bijircewa aurenta da ya yi to amma hakan ta
faskara a dalilin Hanifansa kadai yake so, ita kadai yake
fatan kasancewa da ita muddin ransa Hukunci na karshe da
ta zartar shi ne za ta tona asirin abin dake akwai
tsakaninsa da Hanifa tun da ba abin daba ta sani ba wannan
ne kadai da zai sa ta yi ramakon takaicin da ya kunsa mata.
15
a
Ta gama shirya ta inda za ta bullo musu duk motsin da suke
yi a wannan lokaci a kan da nuna yakc.
Tafe yake a mota yana wani irin tuki na fitar
hankali