inda Allah ya
taimake ta tuni ya yi bacci. Ta yisaurin kashewa amma
kafin minti daya ya kara yin calling. Cikin sanda ta bar
72
dakin ta nufi dakinta ta sa key ta rufe sannan ta daga
wayar, abin da ta fara ewa shi ne Mas'ud ka yi hakuri kar
ka kashen aurena muna tare da mijinia ka dinga yi min
waya. Allah ne kadia ya san yadda yaji kalamanta amma
dai ya daurewa zuciyarsa
Ya fara magana a sanyaye cikin tattausan harshe har
dai ya gama kashe mata jiki ta ba shi attention dinta sossai
ya dada jaddada irin Kaunar da yake mata tare da rfayyace
mata ainihin dalilinn da ya sa ya daina yi mata waya da
yanke duk wata dangantaka da ke tsakaninsu a baya ya kara
da cewa duk da irin rike alkawarin da na yin shi ne za ki
saka min da haka, ki tuna fa irin kaunar da nake miki. Ta
rasa abin da za ta ce masa yanzu kam ya wanek kansa daga
zargin da take masa a da tana ganin kamar daman
yaudararta ya yi anzu ikam tun daga ranar da ta sake
ganinshi ta kasa tsaida zuciyarta wuri guda domin so da
Kaunarsa ne ya dawo sabo fil a zuciyarta. Ta ce to. yanzu
ya kake sona yi? ka san dai abinda yake kaina.
Ya ce, yauwa abin da nake son ji daga gare ki ke
nan, in kin amince gobe mu hadu a Price Hotel sai mu
tattauna. Ta ce kai nan akwai hatsari zuwana wajen ka san
wajen hada-hadar jama'a ne. ya ce, To shi ke nan mu hadu
a Guest House din Abba, kin san ya mallaka min wajen
babu em zuwa wajen, kin ga wajen zai yi sirri ko? Ta ce, E
ya kwatanta mata wajen da lokacin da za su hadu.
Kashegari kamar yadda suka yi alkawari ta kintsa
sai kuma ta rasa yadda za tayi ta fita. A karon farko ta yi
mishi karyar za ta je Barkar wata 'yar ajinsu da ta haihu.
Ya ce ta tsaya a yi magariba sai ya kai ta don yana da
uzurin da zai yi a lokacin sai ta nuna masa gwanda ta je
73
Γ
yanzu kar dare ya yi sai ya sa Driver ya kai ta. in a wm
samunta ne ta je ita daya amma ta san ba zai yiwu ba tun da
ba shiga motar haya take ba ballantana ta fakaice da hakan.
Ya ba ta naira dubu biyu ta bawa maijego. Suna tafe a titin
ta rasa dabarar da za tayi wa Driber ita dai ba abin ya kai la
har can ba har dai dabara ta fado mata ta ce ya kai ta gidan
wata Kawarta da ke Hotoro. Bayan ya kai ta ta ce ya je ya
dawo dan daukar ta. Tana isa gidan suka gaisa da Asma u
matar gidan ke nan bayan sun dan taba hira ta ce za ta je
unguwa in Driver ya zo daukar ta ya jria ta.
Daga nan ta sake shiga mota zuwa mahadar tasu.
Inama! Inama! Inama ba ta je ba.
Yana tsaye a harabar gidan yana tsumayinta ai ko
yana hango ta zuciyarshi ta yi mishi kal kamar ya taro ta sai
dai ya dake saboda maigadin da ke wajen duk da dai Buzu
ne ba kuma hausa yake ji ba amma dai ai mutum ne. Bayan
sun shiga kayataccen sitting room ya maid a kofa ya kulle
A rasa inda zai sa ta dan farin ciki ya kawo mata wancan ya
kawo mata wancan har sai da ta ce ya isa, sannan ya zauna
suka gaisa ya kunan musu TV sanyin AC da kamshin
freshner ke ta tashi a dakin.
Mas'ud ya ce. "Wace shawara kika yanke mana.?
Ta dan sunkuyar da kai kamar me nazarin wani abu.
"Gaskiya na hanga na hango ban gano mańa mafita ba." va
girgiza kai,"A ganinki ko? Ni kam ian ganin abu mafi
sauki ki kashe aurenki ki zona aure ki domin ni ne na fi
dacewa da ke." Nan ma ta girgiza kai, wannan sam ba zai
yiwu ba. Me ya sa? Na san ko da wasa Abdul ba zai rabu
da ni ba, ni na san irin son da yake min... ya katse ta a
hasale to na ji ai ba sai kin gayamin yana son ki ba amma
74
kin san dai be fi ni son ki ba. Ta yi murmushi, To ni dai ina
gaya maka sannan abu na biyu ko da hakan ta faru ivayena
da shi kansa za sunemi sanindalilin hakan, kana ganın zan
ce musu na ce ina so ya sake ni ne dar na aure ka? Kasan
dai halin Malam sarai kan akida ballantana wannan ma na
san ya sabawa sharia.
Ya ce, to na ji ga hanya ta biyu abin da nake nufi
ian sonmu ci gaba da gudanar da rayuwarmu tamkar miji da
mata. Ta zaro ido ban gane ba? abin nufi za m u ci gaba da
gudanar da rayuwarmu tamkar yadda kuke yi da mijinki illa
dai za mu tsarawa kawunanmu lokutan da ya dace mu
hadu. Cikin tsoro ta ce, Kai Mas'ud rufan asiri. Ya lumshe
ido shi ya sa nake gayamiki ba kaunata kike ba in kina so
na ba za ki ki duk abinda nake so ba. haba Hanifa ki
tausaya min mana, mata nawa ne suka tallata kansu gare ni
amma ba sa gabana. Ya matso daf da ita suna jin hucin
junansu ya ci gaba da yi mata dadadan kalamai.
Ita kanta ta san Mas'ud shi ya fi dacewa da ita
hakika tana son sa tana dai kokarin danne zuciyarta ne
kawai. Ta dinga kiyasta kyawun sura da Allah ya yi masa
har ta dinga kamanta shid a Abdul tana kwatanta irin
rayuwar jin dadin da za su shirya wa junansu mutukar suka
kasance tare. Wayyo Allah! Ina ma Mas'ud shi en a
matsayn mijina da dunaiyr nan babu wanda ya fi ni sa'a,
amına aynzu ma ba ta baci ba za mku ci gaba da gudanar
da rayuwarmu tamkar miji da mata, za mu yi kokarin duk
hanyar da za mku bi mu boye sirrinmu (sun mance da
Allah na ganinsu) kai hakika yanzu ne zan more rayuwa da
abin sona abin kaunata. Abin da Hanifa ta dinga ayyanawa
zuciyarta ke nan, dukkaninsu sun san dumbin zunubin
75
za su kwasarwa kawunansu amıma da yake idonsu ya rufe
sun bi son zuciyoyinsu da son ransu Shefan kuma ya dada
ingiza su har suka amince da wannan mummunar alaka da
suka kulla a tsakaninsu msuamman Hanifa da take da
fumbin ilmin addini amma ta kasa aiki da shi lokaci daya
tunaninta ya sauya zuciyarta ta runjaye ta suka bi
SHARRIN ZUCIYARSU wanda duk mutumin da ya biye
mata za ta kai shi ta baro.
Abu uku ke yawo da dan'adam mutukar ya fi
karfinsu to sai ya godewa Ubangiji. Na daya ZUCIYA.
zuciyarka za ta dinga ayyana maka son wani abu ko da ko
marar kyau ne. Na biyu RUHI ma'ana son rai, ranka zai
dinga azalzalarka da son duk abin da yake so komai
muninsa. Na uku SHAIDA, Shaidfan zai dinga angiza ka a
kan munanan ayyuka ba zai taba umartarka da aikata
kyakkyawa ba. duk mutumin da ya biyc wa wadannan
abubuwa guda uku hakika yana tare da wahala dan haka
'yan uwa inu dage mu yi yaki da wannan abubuwa guda
uku.
Sannu a hankali ya dinga hilatarta har ta kai su ga
direwa a gado. Gaba daya jikkunansu 'sun yi nisa da son
aikata abinda zukatansu suka umarce su da yi nan da nan
suka shiga aikata masha'a. Wa'iyazu billah. Tarbiyayr da
aka yi shekara da shekaru iyayansu na gina su a kai
zuciyarsu ta rusa. Sai misalin karfe bakwai da rabi suka
rabu da juna. Shi ma din ba da son ransu ba. gaba dayansu
suun tisnci kansu a wata duniayr da ba su taba zato ba.
bayans un kimtsa sun fito falo nan ma a ka sake gudanar da
wata sabuwar rayuwar tamkar su cinye junansu.
76
Sai misalin Karfe takwas da rabi ta isa gidan
Asma'u. ta iske tuni Driver ya gaji da zaman jiranta ya tafi
ya yi zaton ko ta zarce gida. Abin ka da wacce ba ta saba
ba nan da nan ta kadu sai tara da rabi ta isa gida ta tarar da
Abdulzahir a harabar gida yana yi wa Isa Driver fafa. Yana
ganinta sai ya dakata ya bi ta da kallo. Lokacin da ya shiga
ciki ya tambaye ta me ya tsayar da ita haka sai ta tsattsara
shi da yake mutum ne me halin ko in kula take ya share
zaneen komai ya shige kenan.
Cikin dare suna kwance suna aiwatar da rayuwar
aure amma kwata-kwata ta sakar mishi jiki tamkar ba ita
ba a haka dai ya lallaba ta. A nata bangaren sai ta ke jin shi
tamkar ba namiji ba idan ta kwatanta shi da mas'ud saboda
Shaidan ya gama Kawata mata zuciya a daran ma dai
Mas'ud bai bar ta ba sai da ya Kara yo mata waya. Ta
lallaba ta bar fakin da yake ta fahimei bacci yake, kusan
kwana suka yi suna hira yana kara kashe mata jiki da
daddafan kalamansa har ta kai da kusna kullum sai ya kira
ta a waya. Alaka mai karfi ta Kulu a tsakaninsu, duk da
matsancin son karatunta sai da ya raunana domin karatun
ma ya amanto rabi da rabi a kullum ta fita zuwa makaranta
rabin lokacinta yana karatu rabi kuma na Mas'ud ne, Ka ida
ne kusan kullum sai ta ziyarce shi ilal da zarar lokacin da za
a zo faukarta yayi ta kan yi kokarin ta dawo school. Ba za
ka taba cewa wani abu an faruwa da ita ba saboda ko da
can Hanifa yarinya ee me tsananin wayo da taka tsantsan
balalntana yanzu da ta soma gogewa da duniyanci. Sun yi
jarrabawarsu ta karshen shekara. Daga shi ne kuma za su
shiga zango na karshe amma ba ta yi abin kirki a Exam din
77
ba da yake abu ne na kudi take Mas'ud ya shiga ya lita
sunanta ya fito eikin jerin wadanda suka ci exam.
Huwailat ta yi mamaki don tuni ta saddakar Kawar
tata ba za ta kai labari ba. tanalura da ita kwata-kawta tt
watsar da karatu za ta zo school din amma karatun ba ya
gabanta ta rasa me yake damkunta gaba daya ta sauya
tamkar ba ita ce Hanifan da ta sani ba.
Sannan a hankali dangantakarsu ta dada yin karfi
har ta kai ga ko ba ta da lecture sai ta san dabarar da tayı
suka hadu, Karya kuwa tini suka Kulla Kawance da ita.
Driver na ajiye ta da zarar ya bar wajen Mas'ud zai zo ya
dauke ta kana shi zai dawo da ita school din duk dai suna
yi a boye ne dan ko harabar school din ba ta bari ya shigo.
Akwai ranar da ta yi wani irin ciwon ciki har ta kasa fita sa
da suka yi kwana uku ba su ga juan ba ana ukun ne suka
hadu a school duk da ta sha gargadarsa ya daina zuwa
nemanta school. Sun nutsa cikin shaukin kaunar junansu
sai kawai suka ga mutum a kansu sun dan kadu sai kuma
suka ga ashe Huwailat ce. Ta tsaya Kerere a kansu fuskarta
a murtuke babu alamun fara'a a tare da ita. Mas'ud ya
washe baki don tun da ya zo ba su hadu ba. A'a Huwailat
ce ashe rai kan ga rai?" Ba tare da fara`a ba ta ce, Kwarai
kawu. Zai ja ta da hira ta yi masa fuska sai ya ja bakinsa ya
yi shiru. Yana mamakinta tmakar ba Huwailat da ya sani ba
wace suke wasa da dariya har ta ishe shi da surutu. Ta kalli
Hanifa ta ce, in kin gama abin da kika ga zai fisshe ki kya
taho aji Malam ya shiga. Tayi gaba abinta. Jikinsu ya yi
sanyi daga shi har ita ransa ya dan sosu da abin da ta yi
masa amma da ya tuna matsayin da suke sai ya ga be ga
lefinta ba. ya kalli Hanifa ya ce, kina ganin ba matsala ta yi
78
murmsuhin karfin hali tare da cewa babu komar in dan huw
Suka yi sallama ya tafi. Sar dai fa tana tunanin ya kamata su sake shi
vanzu da Zakryya ce ta gan ta da ta kade har ganyenta munР АРиГ
givat sone ya ımakantar da ita tunanin hakan
A bangaren Huwailat abın ya mata wo halin da ta
Kawarta a cıki tuntini take zargın hakan amma da yake zato ne
kawar da shr a zuciyarta. Ta yı tunanin ko ta sanar da mahartanta halın
da take ciki sai ta ga wannan ba shi ne mafita ba ta yanke shawIP
mata nasiha ko Alah zai sa ta gane ko da ta zo tana yi mata nasthat
ta fuskanci jin ta kawai take wanda ya yi nisa ba ya jin kira ba t
ba haka take sa ta a gaba a duk lokacin da suke tare tana nusar da ita
hakika in wani ne ya gaya mata Hanifa za ta aiakta haka ba za ta uha
yarda ba saboda sanin halinta kai daga karshe dai sai da suka yi baraınbaram. Tun daga lokacin alakarsu tayi rani ita Huwailat ce ke daurewa
ma ta yi mata magana a ganin Hanifa duk wanda zai kawo mata sukar
Mas'ud ko ya nemi raba su wannan kam makiyinta ne dan haka ta i.ta
ta lavin makiyanta
A duk lokacin da Abdulzahir ba ya garı ran nan kam kam
salah a gurinta sabuwar duniya sike barewa dare kadia ke raba su. daidai da dan cikinta ba ta tunawa da shi mutukar suna tare shi k
yaron ya san maharfiyarshi ta sauya ba kamar da ba da a ko yaush
ynaa kasancewa tare da ita.
In ko aka ce Abdul na gari ji take kamar an sa ta a keji dan ma
da yake me wayo ce ba za ta taba nuna inasa wani abu ba abubuv ar da
take masa a da babu abin da ta fasa duk wani abu da ta an zai kyautota
masa shi take yi a bangare daya ne ta rage shi shi ne fangaran
kwanciya, ko kadna ba ta Kaunar ya kusance ta. in ma hakan ya lau tг
kan sakar mkishi wuka da nama Tun ranar da ta fara kasaneowatae d
Mas'ud ta ji babu wani namiji da take fatan kasancewa tare da shi fh.
Mas'ud dinta
Shi kansa Abdul duk da rashin kulawarshi sai da ya fahimei
hakan, dan haka ya kara Kaimi wajen kyautata mata a iya tunaninsa be
ga abin da ya rage ta da shi ba a da in zai yi tafiya yawanci tare suhe
tatiya in dai tana cikin hutu yanzu ko wannan ya zama tarihi ko da tana
cikin hutu ne ba ta amincewa su je
79
W/akiyya ta zo kamar yadda ta saba ba ta yi mata
sai dai wannan akron ta lura fuskarta,na cikin
NABAN tHT PAEk Vdulzahir ya shigo falon tana ganinshi ta skai fuska
ata ya tambayı mutanen gida zai fita ta ce yaya daman gurinka na Yave ar ga n A'a daman ina son magana, da kai ne Ya ce fafi
mana waye bakonki a nan? Hanifa dai tuni ta gane nufin ta dan haka ta bar musu falon
/
Bayan fitarta Zakiyya ta fara cewa, daman yaya ba wani abu
ne ya sa na zo ba illa dan in fitar da kai wani hadari da na ga kana
Kokarin fafawa, ko na ce ana Kokarin jefa ka. Ya dada tatara hankalinsa gare ta uhm ina jin ki. Ta ci gaba da cewa, a gaskiya yaya ba
za mu ga wani abu da zai cutar da kai ba mu Kyale wallahi yaya ka ji na
rantse matarka na ha intarka, ma'ana tana mu'amula da wani namijin alhali tana da aure a kanta in kuma bak.. Be bari ta Karasa ba ya
kawomata wani irin wawan duka ji kake jib-jib yana jibgarta har sai da ya ga ta fadi ya ci gaba da fada. shegiyar yarinya zaki zo ki yi wa 'yar mutane sharri dan kawai ba kwa Kaunarta, ai daman ina sane da duk irin Kiyavvar da kuke mata to wallahi hir dinki in dai a kan Hanifa
ne zan bata da kowa duk me son zumunci da ni dole ya kaunaci abinda
nake so. Ba ke ba ma duk wani da yake Kin ta munafikar banza fita ki
ba ni waje kar ki sake zuwa gidana in dai ba ki sauya wannan
mummunan halin da kika dauka ba. haka ya rako ta har waje yana fafa.
Duk wannan abin da ya faru a kunnen Hanifa don ta
dawo daukar key din dakinta ta tarar Zakiyya na gaya mishi da
tari ba Karamin kaduwa ta yi ba dan ta san asirin boye ya fito fili
amna sai ta ji akasin haka. Hakika ta jinjina irin Kaunar
damegidan nata ke mata ina ma yadda yake son ta ita ma haka
take Kaunarsa kai da da hali da ta tursasa zuciyarta ta hakura da
Mas'ud tare da yanke duk wata alaka da ke tsakaninsu. Zuciyarta
ta rinjaye ta ta kasa controlling dinta tana ganin har abada ba sa
ta daina son Mas'ud ba, ba za ta iya rayuwa ba tare da shi ba (mu
kam muna iya cewa wannan so ya zama makahon so domin ya
kasa nusar da ita dai-daitacciyar hanya ya nusar da ita zuwa ga
80
karkaatacciya wacce ba za ta amfana mata da komai ba face
halaka).
Ta yi mamakin yadda aka yi Zakiyya ta samu labarım
duk da boye-foyen da suke ko da yake makiyinka babu abin da
ba zai yi ba mutukar ya san zai tagayyara ka, sai dai ta mance
yanzu kiwon mutum ake ba na dabba ba.
Takaicin dukan da ta sha gurin yayanta gami da rashin
samun nasara. A da tana ganin da zarar ta sanar da shi zai
fatattake ta amma ina sai uban duka da ta ci, takaicin hakan ya sa
ta fasa kwai a zuri'ar gidansu nan da nan zance ya gama zagaye
dangi wasu sun yarda wasu ko ba su yarda ba suna ganin kamar
kiyayyar da ake mata ne ya sa aka kulal mata wannan sharrin.
tun daga lokacin mutukar Hanifa ta je wani taro na dangin
mijinta sai ta ji ana yada mata habaici a hankali a hankali ta
soma fuskantar zancen ta tabbatar Zakiyya ce za ta fesa mkusu
wannan dalili ya sa ta daina zuaw duk wani taro a bangaren
dangin mijinta har shi ma ya fahimci hakan ya nuna kin
amincewarsa.
Ita ko ta ce Kiyayyar da suke gwada mata ce ta isa
kullum ta je wani taro sai sun ci mata mutumei. Ya ko karbi
uzurinta shi kansa ya san da yawancin danginsa ba sa son ta don
haka ya dada kullatarsu har ya yi alkawarin saka Kafar wando
daya da duk wanda ya nemi takurawa matarsa, a wannan
fangaren kam ta samu kwanciyar hankali surutn da suke yi su je
su kara ta ita ba ya gabanta ta kudurcewa ranta babu wanda ya
isa ya raba ta da masoyinta ko da kuwa wanda ya ajiye ta ne
damuwarta daya yadda a ko yaushe suke cikin kunbiya-kunbiya
ma'ana ba su da 'yancin kansu ko da sun kadaice ne zuciyarsu
ba ta iya nutsuwa sukan kasance cikin fargaba. Takan yi mmakin
hakan tare da jin haushin maigidanta domin duk shi ya janyo
mata wannan matsala ga shi tana ji tana gani suna saawa
mahalicci amma ta kasa dainawa.
81
Sun kammala jarrabawarsu ta karshe ba tare da ta tabuka
komai ba ta kuma yi zaton za ta samu abin arziki a tattare da
result din nata ba, kai hasali ma karatun tuni ya bar kanta. Abin
da ta sawa ranta kawai take yi. Huwailat ta yi fafan tayi nasihar
ta mai da hankali wajen karatu ganin shi ne last exam finsu
amma a banza har ta hakura ta zuba mata ido mamakin yadda
farat faya halayyarta ta sauya. Kai ita kam in dai haka ake son
sai ta ce Allah ya tsare ta da shi domin wannan son shi ne son da
zai kai ka ga halaka. Ta nuna mata hakan ta ki ta gane.
da Yanzu dai karatu ya kare sai zaman gida haduwarsu
Mas'ud ta raunana sai dai a ko yaushe suna tare a waya wanm
loacin ma a gaban Abdulzahir za ta amsa wayarsa dan rainin
hankali amma ba za ta taba bari ya fuskanci da wanda take waya
ba. Yanzu kam wuyanta ya isa yanka. Sannan a hankali zance ya
soma baza gari da yake daman in abin sharri ka aikata yanzu ka
shi a bakin wanda ba ka zata ba ma, in ko na alheri ne wanı
makocinka ma ba zai ji ba.
ji
Rayuwa kam tana gara musu yadda suke sol. Wata rana
sun kasance a tare sun dulmiya cikin masha`a bayan sun nutsu.
Tana kwance a kan Kirjinsa yana wasa da gashin kanta zuciyarsu
ta yi musu fes. Suna cikin wani matsanancin farin ciki yana
shasshafa ta ya ce kin san abin da ke damuna Hanifa? Sai ka
fada. Ya ci gaba da cewa, a ganina lokaci ya yi fa ya yi da kama
ta ki rabud a wannan kallagaggenk mijin naki. Ta harare shi ba
na son wulakanci mijin nawa ne kallagagge. Sorry na daina
manfuata fan lele. Ta ce akwai dan lelen da ya fi ka? Suka yi
murmushi. To kin gane abin da nake gaya miki ko ki duba ki ga
yadda ko yaushe muke maleji ba muda wani 'yancin kanmu. Na
gane abin da kake nufi amsar dana ba ka a baya ita ce har yanzu.
Ya runtse ido ni fa ina tsoron kar wata rana ki guje ni. Ta ce har
abada suka ci gaba da farantawa juna rai daga bisani suka kimtsa
ya dauke ta dan kai ta gida.
82
Sun zo nesa kadan da gida ya taka birki ya rike hannayenta ya danka mata wasu makudan kudi ta kalle shi na
mey? Ya ce naki ne ko kin san tun da muka fara kasancewa tare
ba ki taba faranta min rai irin yau ba, wannan tukuici ne. Ta yi
murmushi gami da ajiye mishi kudin a gefensa, ka san soyayyar
da nake maka ba don kudi ba ne, kai bari ka ji ka ti karfin komai
a gare ni. Ya girgiza kai yana me gasgata ta ya lalubı harshenta
nan ma sun dade suna mutsittsika juna sannan ya sake ta ya
karasa daf da gidan suka yi sallama ya tali kamar an ce daga
kanki sai hango Abdulzahir ta yi a harabar gidan yana kallonsu.
Da yake get din a bude yake ba karamin kaduwa ta yi ba kamar
ta zura da gudu haka dai ta dake ta karasa. Fuskarshi a faure ya
ce. ke daga ina kike?" wai me kike nuti ne? me ya sa yanzu kike
sonkoyank yawo ne? waye kuma ya sauke ki?
Wannan tambayar ta karshe ita ta fi kafa ta ita ba abin ta
ce Direban kawarta ne kamar yadda ta tsara ba zai ce me ya
kawo ta gaban mota, kai sai yanzu ta ga rashin dabararta ko da
yake ba ta yi zaton za ta tarar da shi a gida ba.
Cikin dabara ba tare da ya fahimci rudewarta ba ta ce
daga gidansu Huwailat take. Ba ta same ta ba har sai da ta jira ta
dawo hakan ya sa ta yi dare shi ne Babansu ya uamrci Yayan
Huwailan ya kawo ta. Sa'arta daya da ya san da tafiyar illa dai
bai san karya ta kutsa masa ba. ya ce shi ke nan amma ko dan
gaba kar ki sake shiga motar wani. Meye amfanin wayar
hannunki da ba za ki yi kirana ba? shin wai mka meye dlailinki
na fita ba tare da Driver ba? kin san dai na tsani shiga motar haya
ko? Ta ce ka yi hakuri ba zan kuma ba. ya ce shi ke nan amma ki
kula ko dan gaba. Suka rankaya cikin gidan Walid na ganinsu ya
taho cikin murna ya dafe iyayansa don yaron ya zama marayan
Karfi da yaji, shi Abdul ba mazuanin gari ba uwa kuma a ko da
yaushe ta tafi nata sha'anin. Wannan abin da ya faru a kunnen
Malam Idi maigadi ya yi mamakin yadda megdan nasa ya kasa
83
fahimtar:halin matan:tasa gaushi har:su na waje suka lahimta
lallirkan ya.ci a nada masa Sarkin sokwaye.
Amman ya samu hutun Karshen shekara ya nuto gida
cukes daadokin ganin 'yan uwa da abokan arziki. In ka cire
iyavansa babu wanda yake son gani irin abokinshi amininshi
rabonsa da shi tun kafin ya tafi.
Ai ko yana dira ya samu labarin mummunan halin da
abokin nasa ke ciki ta hannun abokannsu ya samu labarin. Da
tari ya dauka kage ne sai da ya dada bincikawa ya tabbatar da
hakan ne. ko a mafarki bai taba tsammanin zai aikata haka ba
don ko zamanin samartakarsu yan mata ma ba su dame shi ba
kai har tsiya suke masa yana iya cewa Hanifa ita ce yarinyar da
ya fara saurara. Ya nufi gidan abokin nashi har yazu zuciyarshi
na cike da shakku. Abin da idanunshi ya fara gane mashi lokacin
daaya riske shi a dakinsa shi ya dada tababtar mishi da abin da
yake shakku a kai. Ya iske shi ne yana waya da ita ya fahimci
hakan ne ta yadda ya ke kiran sunanta gai kuma hotunanta nan a
barbaje a gadonsa, wasu ma ya kifa su kan kirjinsa da yake
kwance yake kan gado. Ko kadan be san wani ya shigo ba
saboda ya tafi wata duniyar har zuwa lokacin da ya kammala
sannan ya ankara da shi. baki ya bude cike da mamaki ya bud
hannu dan su rungume juna amma sai ya ga yana girgiza masa
kai hawaye na fita daga idanunsa.
Da sauri ya tashi yana tambayarsa laliya? Ya dakatar da
shi da hannu dakata Mas'ud wallahi ni babu abın da za ka ce
min, hakika ka ba ni mamaki ka kuma bata wayonka ka rasa
wanda a ka yi soyayya da shi sai matar wani, shin