kayatacciyar kwålliya ta yi ba taa
salalma da mahaifiyarta umma za ta shiga makota a yi mata
kitso sai ta jiwani yaro ya shigo ya ce ana sallamá da ita,
abin ya ba ta mamaki ita ba zance take yi ba hasali ma babu
namijin da take saurara tun da ta san mutukar Malam ya
amince da nutsuwarsa zai ba shi iznin ya fito ne ita kuma
abin da ta tsana ke nan saboda burinta na yin ilmi me zurli
wannan dalili yasa ta kin saurarar kowa duk da ta san
karatun da take yi ma ba a son ran mahaifinta ne, tana iya
cewa Allah ne kadai ya kadarto za ta yi amıma ban da haka
da tuni tana dakinta Kila ma da tarin 'ya'ya kamar yadda ya
faruda sauran 'yan uwanta. U'mma ta ce ana miki magana
kin tsaya sororo da ke ki sallami yaron mutane. Ba tare da
ta kalli mahaifiyarta ba ta ce ka ce ba ta fita zance. Umna
ta tabe baki gami da harararta daman tasan amsar da za la
bayar ke nan ita kam abin yana damunta yarinya kamar
wannan a ce har yanzu ba ta saurarar samari a ko da yaush
tana shakkun dangane da al'amarin tata, ta kan yi
16
yar
zaotn ko aljani ne ya auri 'yar tata da ba ta son saurarar
samari. Hanifa na kula da kallon daumman ta yi mata ta yi
sauri ta shige dakinta kitson ma ta ce ta fasa dan kar ta fita
ta hadu da me sallamar.
Ta kara jiyo maganar yaron yana cewa wai dan
Allah ta daure ta je mutumin da ya dauko ta daga bata ne
ran nan ya zo ya duba ta ne. ai da sauri ta fito daga dakin ta
zari takalımi har ta kai ga bakin sro ta ji Umma na cewa ke
kanki daya kuwa?" ta tsaya sooro sai kuma ta kalli kanta a
nan ta gane ba mayafi a jikinta. Ta yi saurin koma wa ciki
Kannanta Nasiba da Nusaiba hade da Umma suna yi mata
dariya. Ta dade a dakin sannan ta leko ta ce Umma dan
Allah ki bawa Nasiba ta kai mishi tabarma. Wa fa? Wanda
yake salama. Da wa? Kai umma wallahi kin gane. Cikin jin
dadi ta ce to ai na san halinki ne na sani ko ba za ki fita ba
nan da nan ta sa a ka kai masa sbauwar tabarma hade da
ruwan sanyi a sabon kwanun sha. Ba ta bukatar saya kaya
sai 'yar kwaskwarima da ta dada yi ta yafa yelon mayafi sai
da ta fakaici idon Umma sannan ta fita saboda kunya da
take ji.
Ta isa soron ta ga ba kowa sai ta dan leka waje ta
hango shi ya jingina damota sai tai ciki yana ganin ta ya
biyo bayanta. Ta dan rakuße geffe daya ta gaishe shi cikin
nutsuwa. Ya amsa cikin sakin fuska ya ce, yaya mun same
ku lafiya?" ta ce lafiya lau. Ya ce kin ji ni shiru ko wallahi
tun ranar da muka rabu Abbana ya aike ni Abuja sai a daran
jiya na dawo, na so na zo tun a jiyan sai na ga dare ya yi,
ina fatan ban yi lefi ba. kanta na sunkuye ta ce, Laifin me?
Haka za ki ce ashe ke ba ki yi kewata ba, ni ina can ian ta
tunaninki ashe ke tuni ma kin mance da ni ko? ta girgiza
17
kai haka ne man ga shi ko sunana ba ki nemi ki sani ba, ni
da na damu da ke ai tuni na nemi sanin sunan naki. Ta ce to
ka yi hakuri ka gaya min sunan naka. Sai da na roka
Pl;ease a gafarce ni ya dnayi murmushi ya ce sunarа
Mas'ud Khalil ina zaune a unguwar gadon kaya ina fatan
kin ganc? Ta ce, E ya ce kin san wani abu? Ta girgiza ka
mamana da kannena duk sun ce a gaishe ki. Ta zaro ido
ina suka snani har za su ce a gaishe ni? Ya yi murmush
kina shakka ne? to ai gani na yi ba su sanni ba. Ya girgiza
kai lallai ba ki san irin matsayin da kike da shi a zuciyalą
ba wallahi tun ranar da na gan ki na sanar da su ai ni na
samu matar aure. Gaba dayansu ba ki ga yadda suka y
farin ciki ba musamman kanwata Fauziyya dan wallah
kuna yanayi da ita haske kawai za ta nuna miki ke kuma k
fita tsayi ashekaru ma na san za ku yi sa'annin juna ton
dai kin ji abin da ke zuciyata kauna ce nake miki tsakani d
Allah yaya naki ra'ayin yake a game da ni.?"
Ta yi shiru ba ta ce komai ba ya kara tambayar
ita dai ta rasa amsar da za ta ba shi domin wannan dabas
yake da sauran samarinta, kai da dukanin wani namiji m
(amma fa a wajenta) tun farkon ganin ta da shi ta ji ya tsay
mata a zuciya tana son sa tana kaunarsa yadda baii za
misaltu ba abin da ba ta taba ato ba wato soyayar wani d
namiji a zuciyarta a kusa haka a yadda ta tsarawa zuciyanu
sai ta kammala karatunta ta zama cikakkiyar Malama
makaranta sai ga shi ta tsinci kanta dumu-dumu cika
Kaunarsa. Ya ce ba ki ce komai ba.
Kanta na sunkuye ta ce ka ba ni lokaci tukum. Bali
amince ba ke nan? A'a ni dai kai min wannan alfarmar. Y
ce to shi ke nan yaushe kike ganin zan dawo? Ta da
18
fuskarta ai ni ba na zance. Kamar yaya fa? Ina nufin Malam
ba ya barin mu fita ba tare da an nemi izininsa ba. ban
fahimta ba fa, ina nufin sai ka nemi izinin Malam idan ya
amince shi ke nkan ko yaushe ka iya zuwa. Ya yi murmushi
shi ke nan in dan wannan ne ba matsala hakan kuma ya
dada taabtar min na yi dacen kamialrm ace 'yar manyan
mutane, ko shari'a ma ta yarda ka fara neman iznin
mahaifin yarinya tukun. Yawancin hirar shi yake yi ya
fuskanci har yanzu ta ki sakin jiki da shi ya bkuaci zai tafi
ya miko mata rafar naira hamsin (5,00) amma ta ki karba
ya dauka irin abin nan ne na Malam Bahaushe amma sai ya
a da gaske take, ba yanda bai yi ta karba ba ta ki da ya
bukaci sanin dalili sai ta nuna amsa mahaifitna zai yi fada.
Bai dada yin mamaki ba sai da ya sa a ka kirawo Kannanta
su Nusaiba ya ba su nasu kudin amma fafur suka ki karba,
dole ya hakura ya tafi yana tunanin irin kyakkyawar
tarbiyyar da yaran suka samu.
Kamar aydda al'adar gidan Malam Sa'ad take
mutukar kana nemar 'yarsa sai ka fara neman izininsa shi
kuma zai yi bincike a kanka da ma iyayenka in ya ga
mutanen kwarai ne shi ke nan ya ba ka izini in ya samu
akasin haka ya kan fito karara ya ba ka hakuri ka nemi
wata. Jama'a da dama na yaba halayyar Malam Sa'ad da
ma na iyalansa. A daran ranar wakilan Mas'ud suka zo
nemaawa dansu izninf ara neman auren 'y arsa. Malam ya
yi farin ciki da hakan bayan ya yi dogon bincike dangane
da Mas'ud da iyayansa ya tabbatar mutanen kwarai ne ya
ba su izini.
Bayan kwana uku Mas'ud da yammacin ranar
asabar ya dira gidansu Hanifa bayan tsawon mintuna ta fito
19
sanye cikin ghana Wax ta lillibe kanta da wani dan yalolon
mayafi ta gaishe shi a kunya ce kamar yadad ta saba
tambaye ta mutanen gida tare da isar da sakon Mamans
da kannanshi a cikin gida kuma Umna ta bayar da kunu
zazi me sanyi hade da gashasshen kifi a kawo masa. Yara
suka gaishe shi cikin ladabi ya dinga jan su da hira gami
yi musu tambayoyi dangane da karatunsu ya gamsu da
fahimtarsu daga bisani suka mike za su tafi ya su gaishe
Umına. Ya miko musu leda cike da kayan zaki suka
karba zanebensu daya Malam ko Umma za su yi fada sh
kuma da ya fi su sai ya ce ai yanzu mun zama daya ni m
ai yayanku ne tun da zan auri yayarku kun ga Malam ba za
yi fada ba tund a ya san ni ma fansa ne sannans uka karba
Bayan fieewarsu ta ce ka sha kunun mana. Ya co
wane kunu ban ji matsayina ba gurin Princess. Taу
murmushi sunan da ka sa min ke nan? Ayce kwarai kuw
domin ke ce gim iya sarauniyar zuciyata. Ke ce dai ha
yanzu ban san abind a ke zuciyarki ba dan haka ke nak
jira. Ta dna yi jum saboda nauyinsa da take ji da kyar dai
daure ta ce ni mana amince kin amince da me?" sai ta kal
shi ki fada man. Dakyar dai ta cije kunayrta ta fada
amince da kaunarsa a zuciyarta.
Ya skai wani gwauron nufinashi gami da godiya
Ubangiji har ya ba ta dariya ya ce, dariya ma kike min ki
san Allah tun daga ranar da na bar nan ba na cikin nutsuw
ina ta zulumina msar da za ki ba ni ina tunanin in na samu
akasin hakan ban san yanda zan sa raina ba, ke kila ma
zautu saboda kaunarki. Ta ce, da da ba ka ganni ba fa? D
ban gan ki ba kika ce kin ga kin ba wa kanki amsa ke nau
yanzu kam tun ranar da Allah ya fora idona akanki Allab
20
па
ya dora min so da kaunarki a zuciyata. Ya ci gaba da
bayyana mata irin kaunar da yake mata har dai magariba ta
kawo kai suka yisallama tare da alkawarin zai kawo mata
Kanwarsa. Tana isa gida yabayar da kaya ak awo mata ya yi
saurin tashin motarsa dan kar ma a daow masa da shi. Ta
kaiwa umma kayan suka duba suka ga cosmeties ne hade
da kayan zaki sai wata 'yar guntuwar takarda da ya yi
rubutu kamar haka.
My Princess,
"Da fatan kin isa gida lafiya ga kaya nan babu yawa
ki yi hakuri abinka da students ki gaishe min da Umma da
Malam..
Your Husband M. KHalil
Da Malam ya zo a ka nuna masa kayan sai da ya yi
fadan me ya sa ta karba ya gargade ta kar ta kara karba ta
rike mutuncinta a karshe ya sanyawa kayan albarka. Da
dai ta ga komai ya kankama sai ta zayyanewa Kawarta
kuma aminiayrta Huwailat bayan shegantakar da ta yi mata
a karshe ta sawa lamarin albarka.
Kamar yadda ya yi mata alkawari ya kawo mata
Kanwarsa Fauziyya yarinya me hankali da nutsuwa, hakika
ta yaba da zabin da yayanta ya yi ta kuma yaba da
hankalinta da karamcinta ta tabatar da maganar yayanta da
ya ce suna kama da ita ga shi kusan tsararta ce dangane da
karatu ma duk suna mataki daya wato form five nan da nan
suka zama kawayen juna kusan duk karshen week
Fauziyya na hanyar zuwa gidansu Hanifa ita ce dai ba ta
21
taba zuwa ba a dalilin gidan surukanta ne. Kawarta ta yarda da uzurin nata.
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah har ta kai sun
samu kimanin watanni shida da haduwarsu a dan tsukin
wannan lokacin sun dafa fahimtar juna sun shaku kwarai
da gaske kowanne na kokarin nunawa dan uwansa Kaunar da yake masa duk wanda ya kalli yadda suke gudanar da
soyayarsu dole su burge ka cikin hankali da n utsuwa ba
tare da sun kaucewa Ubangiji ba. Tun tana far-dar da shi
ganin banbancin da yake tsakaninsu tun da ta fahimci dan
masu hali ne sabanin ita da sai dai godiyar Ubangiji har dai
ta fahimci kaunarta yake da zuciya daya ga shi ta fahime
nutuin ne me saukin kaı dan tuni gidansu ya zama tamkar
nasu in dai ya zo mutukar Umma na nan sai ya shiga ya gaishe ta, tun tana jin nauyinsa har ta saki jiki da shi sukank
dan taba hira. Shi ko Malam ya mayar da shi tamkar
mahaifinshi yana sakewa ya yi hira da shi sosai, a yawancin
lokuta tare za ka iske su suna cin abinci in har ya kai dare
ke nan.
Haka nan kannanta su Nusaiba sun shaku da shi kai
yawancin danginsu sun san da soyayar dake tsakaninsu
haka a bangaren Mas'ud abin har ya zarta nata bangaren a
dalilin tsananin kaunar da iyayansa suke masa kai da ma
sauran 'yan uwansa muna iya cewa halinsa ne ya janyo
masa haka domin akwai shi da sanin darajar mutane da
girman na gaba da shi, iyayanshi da sauran Kannanshi kai
dama sauran danginsa kowa ya yi na'am da zabinsa burinsu
Allah ya kawo ranar bikin. Mama mahaifirshi har kyautuka
take wa Hanifa kama datga sarkoki zuwa cosmetics da dai
22
sauran su, ita kanta Hanifa tana ayyanawa ranta ta yi sa'ar surukai masu Kaunar ta.
Dangane da kyaututtukan da yake mata har sai da
Malam ya yi masa magana ya daina shi zai ba shi 'yarsa ne
dan Allah dan kuma mutumcinsa da na iyayansa duk da
haka dai jefi-jefi yakan yi mata alheri duk da kasancewarsa
dalibi hakika shi kansa ya san ya dace da macen kwaria,
me son sa da gaskiya, ba wai don abin hannunsa ba, abin
ya yi karanci a wannan zamanin ke nan, inda idon
'yammata ya bude da shegen son abin duniya ba su ba ma
hatta da iyayansu kan dauki mace a matsayin jari, sam ba
shi da fargaba ko kokwanto dangane da son da take masa
burinsa daya ya kamımala karatunsa a yi auransu.
a
***** ***** *****
Mas'ud Khalil haifaffan unguwar Gadon Kaya ne
cikin birnin Kano shi ne da na farko gurin mahaifansa yana
da kanne ukuk Nasir, Nazir, sai autarsu Fauziyya.
Mahaifinshi Alh. Ibrahim Khalil (Wanda suke cewa Abba)
tsohon ma'aikacin gwamnati ne ya rike mayan mukamai
har daga baya ya yi ritaya ya shiga har kokin kasuwanci
yana shigo da motoci daga Republic of Benin (Cotonou)
yana sayar da su a kasar nan yana da gidajen sai da motoci
akalla guda hudu. Mahaifiyarshi kuma sunanta Haj. Saratu
suna ce mata Mama. Fara kyakkyawa ga kyan hali da
girmama bako. Duk da kasancewarsu masu wadata ba su da
wulakanci ba su daukan kansu wani abu ba daga ita har
mai gidanta ga su da taimakon na Kasa da su. Wannan
kyawawan halayan nas 'ya'yansu duk sung ado shi.
23
Sun tarbiyyanci 'ya'yansu yadda ya dace dan haka
yaran suka tashi da ingantaciyar tarbiyya. Mas'ud fan
kimanin shekara ashirin da hudu wankan tarwada
kyakyawa da shi, ba shi da wata makusa a jikinsa ya yi
karatunsa tun daga primary har zuwa University ya
kammala Degree a fanninsa Engineering a halin yanzu yana
yin bautar kasa ne. Sun hadu da abokinsa Ammar tun
zamanin yana secondary.
Hanifa kuma sai mu ce ita A bangaren ma
haifaffiyar jihar Kano ce cikin unguwar 'Yar Maishikafi
mahaifinta Malam Sa'ad da mahaifiyarta H. Hadiza
dukansu 'yan usulin Knao ne wanda tushensu ya samo asali
daga garin Kiru, dukansu yan dangi ne gaba da baya.
wadanda suka samu kyakyawan usuli Allah ya azurta su da
'ya'ya har guda biyar dukansu mata babbar ita ce Ummu
Salama sai Ummahani sai Hanifa, Nusaiba da- Nasiba
yayyant abiyu dukkansu an musu aure tun suna 'yan
shekara goma sha hudu. Iyakar karatunsu primary domin
wannan al'adar Malam ce da yarsa ta cika shekara goma
sha uku zuwa sha hudu zai aurar da ita ga wanda ya zabа
mata ko kadan ba shi da ra'ayin `yarsa ta yi makarantar
boko primary dinima fannin Arabi suke yi ilmin addini
kam wannan ba a maganarsa domin duk cikin 'ya'yansa
babu wanda be sauke ba hatta da kananan sun ksua
hattamawa mutum ne me gudun wulakanci dan haka
yadage wajen nemawa iyalinsa fan abin da za su'da sauran
hidindimun yau da gobe. Mutun ne me tsananin kula da
tarbiyyar iyalinsa ko kadan ba ya Kaunar ya ga sun yi wani
abu da zai janyo musu abin kunya dan haka da wuya ka ga
224
yaransa ko da a kofar gida ne in ka gan su a waje za su
makaranta ne ko wani aike me muhimmanci.
Sai dai fa duk da wannan tsananin nasa mutum ne
me son jan iyalinsa a jiki ya shaku da 'ya'yansa Kwarai da
gaske sai dai duk da haka duk lokacin da suka yi wani
kuskure ba ya raga musu. Sana'arsa shi ne sayar da
yadiddika da kananan atamfofi (Super Print) a kasuwar
Kurmi a kullum ya kan fita misalin karfe takwas na safe
sai Karfe biyar yake dawowa idan an yi sallar isha'I yakan
zauna da faliibansa wanda galibinsu magidanta ne hade da
dattijai a nan kofar gidansa yana karantar da su ilmina
ddini. domin Allah ya hore masa ilmi sai misalin karfe
goma zai shiga gida ba za ka kara ganinshi a waje ba in dai ba wani uzuri ba sai kashegrar mutum ne da ya san darajar
mutane hade da makwabta. Mutanen unguwarsu suna jin dadin zama da shi sukan yi kokarin yin koyi da kyawawan halayenshi musamman yadda yake kulad a tarbiyyar iyalinshi.
Hanifa 'yar kimanin shekara goma sha biyar
doguwa me kyan jiki ba ta da wani matsanancin kyau. Wanan tarwada ce idanunta matsakaita masu kyawun gani hancinta dogo siriri bakinta madaidaici haka nan ga shin kanta ma babu laifi abu faya da za ka so ka yi ta gani a
jikinta shi ne Allah ya yi mata baiwar jiki mai kyau irin jikin nan ne da ke boye shckaru, ita kanta ta san Allah ya yi
mata baiwar jiki me kyau msuamman in ta yi la'akari da yadda Kawayenta kai da saurna jama'a ke tanka mata. Tana makarantar yammata ta Sani Mainagge tana SS II. A
kullum ta Allah da misalin karfe biyu da rabi takan tafi Islaniyya wato shahararriyar makarantar nan Gwadabe
25
Maitasa wadda take daf da gidansu. Da dadadre kuma takan
je makarantar dare a nan lungusnu kafin ta kwanta bacci
takan kara daukar karatu gurin mahaifinta dan haka Hanifa
Allah ya hore mata sanin iilmin addini. Babban burinta shi
ne ta zama cikakiyar Malamar makaranta ta koyar kamar
yadda a ka koyar da ita. Sai dai ta san abu ne me wuya
mahaifinta ya kyale ta ta tafi higher insititution, secondary
din ma da yaya ya bar ta sai da aka sha wuya kafin ya bar
ta shi ma din da taimakon wan mahaifinsa sannan ya bar ta.
Dadin dadawa a lokacin da ta kammala primary ba ta fi
shekara goma ba ga ta da karamin jiki musamınan da ya
lura yarinya ce me hazaka dan har headmaster dinsu sai da
ya zo ya aroke shi ya bar ta ta ci gaba da karatu ya kuna
lura duk da karancin shekarunta yarinya ce me nutsuwa
wannan dalili yasa shi ya kyale ta. Ya dai kudurcewa ransa
ne da zarar ta tasa zai cire ta ya zaba mata miji ya aurar
daita har dai t akai zuwa aji uku ya so ya cire ta ya aurar da.
ita tun a lokacin msuamman da yake akwai masu neman
auranta amma sai ya sauya tunani domin ya lura tana
mtukuar son karatun ga shi Allah ya ba ta basira.
Wata rana ya yi kiranta ya yi mata nasiha ta ci gaba
da rike mutuncinta ya amince ta ci gaba da karatunta har
alah ya kawo mata wanda take so daga nan ne fa zai aurar
da ita ba wani abu ne ya sa shi yin haka ba ilal tsaanins on
ta da yake don duk cikin 'yia'yansa ba wanda yake so irin
ta babu kuma wanda ya fi yi masa biyayya kamar ta ya yi kuma la'akari da sauyawar zamani. Tsananin farin cikin da. ta yi ba zai misaltui ba ko a mafarki ba ta taba tsammanin zai amince ba, a zatonta karatutna ya zo karshe. Ta yi shirin rungumar duk wanda mahaifinta ya zaba mata dan haka ta 26
yi alkawari ga mahaifinta za ta guji yin duk wani abu da
zai tagfa mutumcinta tun daga wannan lokacin ta dada
dagewa da karatunta, tana ganin nan gaba ma zai amince ta
je har Higher Institution ko da wasa ba ta taba saurarar
saurayi ba da sunan zacne kozuwa suka yi ta kan ba su
hakuri ta kwan da sanin hakan abin da zai janyo mata har
dai zuwa ranar da Allah ya haſa ta da Mas'ud in da gaba
faya tunaninta ya sauya.
Sun samu kimanin shekara daya suna gudanar da
tsaftatacciyar soyayyarsu mai cike da so da kaunar junansu,
saboda shakuwa ya game jikinsu har ta kai ba sa iya yin
cikakken. 48 hours ba tare da sun ga juna ba. Soyayayrsu ta
zama abar kwatance ga 'yammata da samari da ma
al'ummar unguwanninsu. A wannan lokacin tuni ya
kammala hidimar Kasa yana aiki a kamfanin samar da
hasken wutar lantarki na kasa.
Ana daf da fara maganar aurensu Alh. Khalil ya
nema mishi Admission a kasar Japan domin yin mastering
Degree dinsa, saboda wani buri da yake da shi a zuciyarsa.
Mas'ud ya yi mutukar farin ciki domin babu abin da ya ke
so irin ya ga ya zama cikakken Engincer a fannin KereKere, amma a wani bangaren an zuciyarsa yana mutukar
bakin cikin rabuwa da gimbiayrsa na tsawon wani lokaci
amma da ya tuna kokacin da zai Kare karatunsa dai-dai
lokacin ne ita ma za ta kammala dan haka yake ganin
komai ya zo dai-dai ke nan. Musamman in ya tuna nisantar
tasu zai ba ta kwarin gwiwar tunkarar final exam da ke
gabanta.
Ba Karamin kaduwa ta yi ba da ta ji tafiyar gani
take shi ke nan da ya je can zai samu wata ya mance da ita
27
sat da kyar ya shawo kanta ya yi alkawarin zai dinga hugw
mata waya duk Kashen sati. Ya je har gidan babbar aminiyarta Huwailat ya danka mata amanarta.
Kiraye-kirayen salar da ya cika mata kunne sli ya
dawo da ita daga dogon tunanin da take yi muna iya cea kusan kwana ta yi tana kuka.
Sai da tayi kusan sati ba ta jin dadin jikinta ta san
kuma abin da ya haddasa mata ciwon dole ta dinga tursaa
zucıyarta don ta rage tunanin masoyinta. Ta ci gaba da
karatunta yadda ta saba, Kawancensu da Fauziyya ya c
gaba da gudana. Kamar yadda ya yi alkawari duk karshen
sati yakan bugo mata waya ta hannun abokinshi Ammar,
haka nan yakan aiko mata da kudi da `yan kayan ciyc-ciye
duk ta hannun Ammar ta sha fada masa ya daina wahalar
da kansa amma ya ki dole ta hakura take karba, a gaskiva
tana iya cewa ganin juna ne kawai da ba sa yi amma a ko
yaushe suna tare a waya, dan har ta kai duk bayan kwana
biyu sai ya yi kiranta yana me dada jaddada soyayyarsa а
gare ta. Fatansa a ko yaushe ya kammala karatunsa ya
dawo su yi aure.
Watansa goma cif da tafiya Hanifa suka fara final
exam sun fara da WAEC daga baya suka rubuta NECO.
Suka kammála jarrabawarsu cikin nasara tare da fatan
sanmun kyakkyawan sakamako. Ranar da suka rubuta
jarrabawarsu ta Karshe Mas'ud ya yo waya ta sanar da shi
ya yi murna Kwarai da gaske tare da yi mataalheri a Karshe
ya ce ta jirayi gift dinksa ya sanar da ita saura wata biyu su
kammala. Malam da umma duk sun mata fatan alheri a
Rarshe ya ce karatu ya Kare sai aure ko ta yi dariya cikin
jinn kunya. Cikin dare ma tana jiyo su suna tattauanwa
28
dangane da maganar aurenta. Tana ta mamakin wannan
dokin da suke tamkar ba su taba aurarda ya ba sai a kanta.
Awannan shekarar ne Nusaiba ta shiga secondary Nasiba
kuma sai shekara mai zuwa.
Kwanaki ba wuya game sauran nufmashi har ga shi
an yi kimanin wata shida da kammala karatunta amma babu
Mas'ud babu dalilinsa ba ma rashin dawowarsa ne ya fi
dainunta ba ilal rashin bugo mata waya da sam ya daina yi,
rabon da ta ji shi a waya an yi wata hudu ko biyar ko
sakon gaisuwa babu, ga shi dai Ammar zai zo kamar yadda
ya saba amıma ko sau daya bai taba yi mata maganarsa ba,
ita ma sai ta share dan kar ya ga ta damu da shi da yawa,
kai abu dai ya ci gaba tun tana tunanin ko ba shi da lafiya
ne har ta daina tunanin hakan don suna yawan haduwa da
Fauziyya ba ta taba ce mata haka ba hasali ma sukan yi
hirarsa sosai tare da hirar bikinsu saboda gaba daya a ka
shriya za a yi bikinsu har dai ta fara tunanin ko ya samu
wata ya mance da ita ne nan ma ta kan yi saurin akwar da
wannan tunanin dan ko a mafarki ba ta fatan hakan ta faru
kai abu dai ya dagule mata ta kasa sanar da kowa halinda
suke ciki ilal dai ana yawan tambayar ta me ya same ta
saboda ramar da ta yi. Tunani ko ba a maganarsa, hakika ta
shiga cikin daımuwa ko da a mafarki ba ta kaunar ya subuce
mata ita duk ba wannan ne ya fi damunta ba illa matsa mata
da iyayanta suka fara yi dangane da auranta, su gani suke
kamar lefinta ne. rannan kwatsam Fauziyya ta zo mata da
labarin aurenta sati biyu masu zuwa a dalilin wanda zai
aure ta ya matsa a yi bikin saboda shi ba mazaunin kasar ba
ne. 29
Gabanta ne ya fadi me ke nan hakan ke nufi tun da
ta san tare a ka shirya za a yi aurensu kamar ta ce ya
maganar nasu auren? Ya maganar yayanta? Wane hali yake
ciki yanzu?' shin ya mance da alkawarin da ya yi ne? kai
da dai tambayoyi masu yawa amma sai ta kasa sanar da ita
musamman in ta tuna banbanci da ke tsakaninsu kar su ga
zalamarsu ko su yi tunanin wani abu dan ko ita Fauziyyan
ba ta san abin da ke gudana da Yayan nata ba. ta 'danne
zuciyarta ba tare da ta bari ta fahimci wani abu ba ta yi
mata fatan alehri daga nan suka fara shirye-shiryen biki.
Sati biyu na zagayowa aka sha shagalin biki ango
ya dauke amaryarsa suka barkasar abind a ya dada kwantar
mata da hankali shi ne yadda a lokacin bikin dangin
Mas'ud da ma mahaifiyarsa suka dinga haba-haba da ita
duk inda ta shiga sai nuna ta ake.
Huwailat