me
Mas'ud din ya fi Abdul? Karewa ma in wani kyan Mas'ud
ke rudarki kin san Abdul ya zarta shi nesa ba kusa ba sai
dai ya nuna masa hasken fata, mutumci, karamci shi ma ba
daga nan ba ga shi shi ma ya fito daga tushe me kayu ian
ganin ki share wani Mas'ud daga zuciyarki ki rungumi
abd....." Ta katse ta da cewa Malama na ji ya isa haka ai ba
sai kin kushe shi ba za ki tusa min wani ra'ayi na daban,
banza mara rike alkawari wai yau ke kike kushe Mas'ud
duk da amanar da ya danka miki duk kuma da amincin da
ke tsakaninku.
Ta ce ko me a ki ce sai dai ki ce gaskiya ce duk inda
ta zo dole a fade ta. Tsawon kwana biyu Huwailat tana
mata nasiha har zuciyarta ta so ma karkata ta kan yi tunanin
maganganun iyayanta musamman ini ta tuna irin
gwagwarmayar da suka sha wajen dawainiyar su amma a
ce yau rana tsaka za ta bijire musu ta kwan da sanin cewa
44
duk gidansu ba wanda ya samu wannan damar sai ita, dole
ta hakurewa zuciyarta Mas'ud ta tabbatar Allah ne bai yi
nufin aurensu ba, tun da shi kansa Abdul din ba wai tana
jin kinsa a zuciyarta ba ne ilal dai dan tuni ta sawa
zuciyarta kaunar Mas'ud ne ainma in ba haka ba ai shi ma
ba shi da makusa a yawancin lokuta yakan burge ta har ta
dinga jin da ba dan kaunar Mas'ud da ta mamaye zuciyarta
ba da shi ne namiji na farko da za ta kaunata amma duk
dahakan babu lefi takan ji kaunarsa a zuciyarta duk da dai
ba za ta iya kwatanta shi da Mas'ud ba.
A daran ta nemi gafarar iyayenta tare da amincewa
da auren Abdul sukayi farin cikitare da yi mata fatan
alheri gami da nusar da ita martabar aure da umartar ta da
ta yi wa mijinta biyayya.
A da ta kudurce in suka hadu za ta goge shi tas kan
hada ta da ya yi da iyayanta amma fa babban abin da ya fi
ba ta haushi da shi shi ne yadda ya zo ya raba ta da
masoyinta. Cikin dan. kankanin lokacisa ka tsaida lkacin
aure wata biyu masu zuwa.
BA RI MU JE WAYE AABDULZAHIR.
bdulzahir haifaffan garin kano ne cikin ugnuwar
Yola, mahaifinshi Alh. Nasir yana da mata hudu
da 'yaya ishirind, ahudu, mahaifiyarshi Haj.
Maryam ita ce ta uku a gurin mahaitinsu babbar uwar
gidan tana da 'yaya goma me bi mata 'ya'ya bakwai sai
mahaifiyar Abdulme 'ya'ya hudu, Maijidda ita ce ta farko
sannan Abdul sai alkassim sannan auta Zakiyya. Amaryar
kuma an da 'ya'ya uku. Alh. Nasir irin attajiran nan ne na
45
kawai za ka kalla ka tabbatar da hakan. da. Yanayin gidan
Duk da dai yanzu sai rufin asiri yawancin 'ya'yansu
ma'aiaktan gwamnati ne wasu kuma suna taba kasuwanci.
Abdulzahir ya yi karatunsa daga primary zuwa
University, fan kasuwa ne yana shigo da kaya daga
Rasashen Asiya zuwa gida Najeriya yana da rufin asirinsa
dai-dai misali, dan kusan duk 'yayan gidansu ya fi wadata.
A tin shekaru hudu da suka shige soyayya me karfi ta
kuillu tsakaninsa da 'yar aminin babansa na kud da kud
wato Aysa. Duk dangunansu ba wanda be san da soyayar
da ke tsakaninsu ba. abu har yakai ga maganar aure, tun
kimanin shekara daya ba ya lokacin da aka sa auresu ya yi
amma saboda be kammala katafaren ginin da yake ba dole
aka dage bikin. Tana zaman tsimayinshi dan a bangaren
amarya da danginta tuni sun gama tanadinsu ango kawai
ake jira.
Kwatsam dare daya ya sauya tunaninshi a kan Aysa
tun sa'ar da ya hadu da Hanifa ya yi kokarin ya danne
zuciyarsa ya yakice ta amma da ya jewa mahaifinsa bsai
sauyin da ya samu fafur Alh. Nasir ya ki kai da ma ilahirin
danginshi hata da gun mahaifyiarshi be samu goyonbaya ba
kowannensu na ganin zai 6ata dadaddan zumuncin dake
tsakanin gidajen biyu.
Da kayr da sidin goshi ya shawo kan mahaifinshi
tare da mahaifiyarsa suka amince shi ma fin a dalilin baban
Aysan ne ya rokar mishi domin zuwa ya yi ya marairaice
mishi tare da nuna mishi Allah ne be nufi yin aurensa da
'yarsa ba amma ba wai dan ba ya son ta ba ya nunamishi
tana nan a matsayin 'yar uwarshi taımkar yadda kannanshi
suke a gare shi da yake Alh. Dattijon kirki ne sai ya karbi
46
uzurinsa tare da addu'ar alah ya yi wa 'yar tasa zabi na
gari. Duk da dai an kai ruwa rana kafin Alh. Nasir ya
amince kusan ilahirin danginsu in ka cire mahaifiyarsa
babu wanda ya yi na'am da wannan aure a ganinsu wannan
cin amana ne, musamman da yake suna sane da tsawon
lokacin da Aysa ta tsaya tana jiranshi. Babu wacce abin ya
fi bakantawa rai irin Zakiyya saboda a duniya ba ta da wata
aminiya da ta wuce Aysa. Tun kan ta ga matar da yayan
nata ya zaba a madadin aminiyarta ta ji ta tsane ta duk da
matsaancin kaunar yayanta da take yi da son duk abin da
yake so duk cikin yayyanta babu wanda ta fi kauna irin sa
wannan akromn kam sun raba hanya.
Lokacin da Aysa ta samu wanann mummunan
labari ba karamin rudewa ta yi ba, ba ta taba tsammanin zai
yimata haka ba ta yi kuka har ta gaji a karshe ta hakura tare
da fatan Allah ya saka mata a bisa cin amanar da ya yi
mata a ganinta dama can yaudararta yake yi.
A bangaren Abdul kuwa shi kansa ya san bai
kyautawa Aysa ba amma ya ya iyawa zuciyarsa tun ranar
da Allah ya hada shi da Hanifa ya samu kansa da mancewa
da duk wata mace da ke duniya mutukar ba Hanifa ba.
fatansa a ko yaushe ta zama mallakin zuciyarsa duk da dai
ita ma Aysan ba baya ba ce wajen kyau amma a gaskiya ba
a ka kwatanta da Hanifa ba, musamman ta kirar jiki. Ya yi kokarin ya danne zuciyarshi ko su biyu ne ya hada ya aura
ama ina zuciyarsa ta yi nisa da begen Hanifa a karshe ya yi
mata wasika tare da tausasan kalamai yana me neman
afuwarta yarubtua mata cheque na makudan kudi amma da
aka kai mata ko budewa ba ta yi ba ta dawo mishi da
47
sakonsa daga bisani ma ta bar garin ta koma Zariya gurn
ngin mahaifinta.
Ya rage saura sati daya a fara bikin Abdulzahir da
Hanifa Abdul ya dauki Zakiyya Kanwarsa zuwa gurin
amarya duk da dai tia-ba ta so ba saboda ba za ta iya ce
masa ba za ta ba ya sa ta bi shi. tun da suka isa kofar gidan
ta yi tsaki gami da takaicin ashe ma 'yar Malam Shehu
(wato 'yar talaka) ya kwaso musu, ko kadna ba ta kaunar
yin wata mu'amula da talakawa. A kyankyame ta shiga
gidan tana alla-alla ta ga wace sarauniayr kyan ce yayan
nata ya rufe ido ya yimusu wannanr ashin kirkin. Ta isa
tsakar gidan tana sallama kamar ba ta son yin maganar.
Hanifa na daki ta jiyo sallamar ta fito ai ko suka yi
kicibus suna kallon-kallo na wani lokaci, Hanifa ta ga bain
ya yi yawa ta ce Malama lafiya kin shgo gidan mtupane
kint saya kikam? Zakiyya ta bi ta da wani wulakantaccen
kallo domin ta san ita ce wace yayanta ya kwaso tuntuni ya
a ce ta gane ita ce ta jin cikakken sunanta gurin yayanta
kai dama hotunanta da ta gani gurinsa, hotunan sun yi
masifar kyau dan haka ba ta taba kawowa ita ba ce. Cikin
a ta ce daman ke ce wace yayanmu ya kwaso mana? Kai
amna yaya Abdul bai san me ya rude shi da ke ba yanzu
dman a kanki ne ya guji kawata? Kai Allah ya kyauta wa
Yaya. ya rasa wace zai waso mana sai 'yar matsiyata
makwadaita dan na sna kwadayi ne ya kai ki ga son sa. Та
yhi tsaki ta fice.
Hanifa ta bi ta da kallo cikin takaici da tsananin
mamaki ba ta taba zaton Abdul ya hada iri da irin wannan
yarinyar mara mutumci koda ya ce mata zai kawo. mata
Kanwarsa ko a mafarki ba ta yi zaton ita ba ce.
48
Ko da Zakiyya ta fita sai ta ce masa ai Hanifan ba ta
nan ya yi mamakin hakan musamman da yake ya sanar da
ita zuwansu suna tafe yana ta koda gimbiyar tasa gurin
kanwarsa tare da kwarzanta kyawawan halayenta. Shi ko
be san haushinsa take ji ba tamkar ta shake shi.
An yi Kasaitaccen biki yadda ya dace duk da a
6angaren amarya zuciyarta na cike da matsanancin bakin
ciki, ta san shi ke nan har abada sun yi banwakna da
masoyinta Mas'ud. Abin da ya dada ba ta mamaki shi ne
yadda mahaifiyar Mas'ud suka halarci bikin tare da
gagarimar gudummawa haka mahaifinshi da shi aka daura
auren don shi ne ya kasance waliyyinta ma.
An kai amarya kayataccen gidanta dake Sultan
Road har jama'a suka watse tana cikin kuka. Kusan tund a
aka fara bikin cikin kuka take sai dai na yau ne ya tsananta
ba wai dan rabuwa da iyaye ba ma a'a illa dan tunanin
tsohun masoyinta shi ke nan ta san sun rabu ke nan har
abada.
Misalin karfe goma na dare ango ya shigo ya iske ta
tana kuka ya yi lallashin duniya amma ta ki yin shiru, kai a
takaice dai a haka suka kwana yana aikin lallashi sai da
suka yi kusan sati a haka kullum da daddare kuka har Allah
ya taimake shi ya samu hadin kanta a cikin daran ya dinga
godiya ga Ubangiji da ya yi mishi kyauta da salihar mace
domin ya same ta cikakkiyar mace.
Sati biyu cur suka yi suna shan amarci ar daga
bisani ya ci gaba da harkokinsa ita ma ta ci gaba da zuwa
school. Duk wani abu da ya san zai kyautata mata si yake
yi yana tsananin nuna kulawarsa a gare ta ta yadda koо
tafiya ya yi yakan kirawo ta waya akai-akai dan ya ji
44
lafiyarta. Ita kanta ta san Abdul na son ta yana kaunarta
fiye da yadda ta zato a baya. Ga shi ta yaba dakyawawan
halayensa, ita ma sai ta dinga kokarin yakice Mas'ud a
zuciyarta tare da kokarin cusa mijinta ama ikon Aah
zuciyarta ta ik yadda ta yakice Mas'ud daga gare ta. Haka
ta y ta fama har alalh ya taimake ta ta kawar da Mas'np
gefe daya ba wai ta daina kaanrsa ba ne ilal dai ta kawar da
shi ne gefe daya tare da kokarin cusa Abdul a gurinsa ita
dai ta san har abada ba za ta daina kaunar Mas'ud ba amma
tun da Allah be kadarto mijinta ba ne dole ta hakura ta
rungumi mijinta.
Sannu a hankali har Allah ya taimake ta so da
kaunar mijinta ya ratsa jikinta burinta a ko yaushe ta
faranta mishi tare da kokarin yin duk wani abu da zai
bukata kama daga 6angaren kwanciya har zuwa mu'amular
yau da kullum haka bangaren abinci daman ga ta gwana ce
musamman da ta fahimci be cika son abinci me nauyi ba.
haka nan ya fi so nau'in abincin Larabawa.
Haka nan fangaren 'yan uwanshi tana bakin
kokarinta wajan kyautata musu duk da dai ita da kanta ta
san ba ta karbu ba gurin dangin mijinta musamıman
tsagerun kannansa in da ta godewa Allah iyayan mijinta na
Kaunarta kauna kuma ta hakika, dan daga hajiayr zua
Alhajin kowanne haba-haba yake da ita, wannan dalili ya sa
ba ta damu ba sosai kowa zai ki ta ma da sauki.
Ta ci gaba da kokarin kyautata musu tare da fatan
Allah ya sa su fahimci juna, ita kuwa ta rasa dalilin da ya sa
suka tsane ta. Haka nan in abokanan mijinta ne suka zo
ftakan karbe su cikin karamci a takaice dai muna iya cewa
taa bakin kokarinta wajankyautatawa maigidanta shi da
50
kansa ya sna da hakan har ya kan yi mamakin yadda farat
daya ta hakura da tsohon saurayinta ta rungume shi hannu
bibbiyu tare da yin biyayya a gare shi, wannan dalili ya sa
ba ya shayin kashe mata konawa ne duk abin daya gani ya
san za ta yi sha'awarsa sai ya sai mata.
Yau ranar asabar tana gida babu school ta hada
lafiyayyen abinci wato Labanise Rice hade da Kidney
soup, Chips & Baked Beans hade da Sardine-Omellete, a
bangaren drinks kuma ta yi Carrot Drink.
Karfe biyu narana tana zaune a ffalo ta hade cikin atamfa
Super Holland, zuwan Abdul kawai take jira don ka'idarsa
ce mutukar yana gari a gida yake cin abinci ba ya yarda ya
ci a waje, saboda ta gama sangarta shi da daddadan
girkinta, daman ga shi da son cink dadi sai Alah ya taimake
shi ya yi katari da macen da ta iya abinici, har biyu da rabi
ta gota be dawo ba, ta kishhingida kwata-kwata a 'yan
kwanakin nan ba ta jind adin jikinta daga zazzabi sai ciwon
kai. Misalin karfe uku ya iske ta a haka bacci ya dauke ta
ya tsaya a kanta ya kare mata kallo shi da kansa ya san ya
morewa mata. Ya dan shafi gefen kumatunta amma ko
motsi ba ta yi ba sai ya shiga yi mata susar tsutsa a tafin
kafarta abinda ya san ba ta so. Nan da nan ko ta tashi ta
rike hannusna shi kuma yana yi mata dariya ta kalli agogo
ta dan bata rai sai yanzu za ka dawo? Tun dazu ina ta
zaman jiranka har yunwa ta sani bacci. Ya ce sorry my
Dear, mota ce t ayi mint siya a hanya kin san da tuni na
karaso, ni ma kina raina. Tun lokacin da na ga loakini cin
abincinmu ya yi na san kuma halinki ba za ki ci ba sai kin
jira ni. Ya ja hannunta zuwa Dining table yana bude
kwanukan abincin kamshi ya cika mishi hanci ya girgiza
51
kai tare da yaba mata kamar yadda ya saba ya shiga ba ta a
baki har sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya fara cin nasa,
sai kuma ya ga ta dafe kai ya ce lafiya? Ba komai. Ba
komai.? Ya dan taba kanta ya ji shi zafi rau ya yi saurin
sakin spoon ya tallafe ta zuwa cinyarsa ya ce me yake
damunki ne? ta ce kai ne yake min ciwo sai dan zazzabi da
nake ji. Tsam ya tashi ya koma daga falo ya zauna bisa
carpet ya dora ta a cinyarsa ya shiga shasshafa mata ruwa
yana yi mata sannu ita ko ta daďa shagwaggwabewa har da
dan kuka.
A haka Huwaila ta iske su za ta juya ya ce shigo
mana yau gida ba lafiya. Ta karaso a tsorace lafiya? Me ya
faru?" ya nuno Hanifa ga ta nan ba ta da lafiya ba ki ga
yaddda ta fada ba? ta dan girgiza kai, to Allah ya kyauta,
kun je asibiti ne? a'a ai yanzu an dawo na iske ta a haka,
amma shi ne ka ce har ta rame daga cutar kwana daya ko
yini daya ma zan ce, na san ma ba na raba dayan biyu kila
juna biyu ke gare ta: Ya ce meye kuma juna biyu? Ta yi
dariya ganin yadda ya rude kai ko ka fi kowa sani ta fada
tana dariya ya dan bata rai Allah Huwaila ba ki da kirki
matar tawa tana cuta ki dinga wannan dariya.
Hanifa ta ce Abdul kyale ta ta karaci tsiyarta tashi
ka kai toilet amai ke taso min. da sauri ya sungume ta zuwa
toilet. Kashegari suka je asibiti sakamakon da aka gaya
musu ya sa su farin ciki, wato ciki ke gare ta na wata biyu
gaba dayansu haka Alah ya yi su da son yara a cikin satin
Abdul yana da tafiya kasar South Korea amma saboda
laulayin da take fama da shi sai ya janye tafiyar haka ya
shiga tarairayarta, ita kuna tana shagwaggwabe masa da
yake irin cikin nan ne me laulayi be samu lafiya ba sai da
52
cikin ya kai wata biyar sannan ta fita daga laulayin duk da
hakan dai ya kan talalfa mata da wasu abubuwan ga shi dai
suna da masuaiki har biyu amma sam ba ta yarda su yi
wame gidanta abinci tia ce takan daure ta yi.
Lokacin da cikinta ya cika wata tara gaba dayan
duk wata tafiya sai ya dakatar da ita, fatansa a ko yaushe
Allah ya sauke ta lafiya. Tana shirin shiga wata na goma
Allah ya taimake ta ta haifi sankacecen saurayi me kama da
ubansa sak, ba karamin farin ciki Abdulzahir ya yi ba.
Ranar suna ta zagyao yaro ya ci sunan Kakansa wato
nasir.an yi kayataccen suna na gani na fada haka nan
kayan da ya hado mata tamkar na lefe babu lefi dangin
Abdul sun zo in ka cire Zakiyya don daf da za ta haihu sai
da suka yi kaca-kaca a dalilin izgilanci da wulakanci da
take zuwa har gia ta yi mata. A ranar dai da abin ya ishe ta
ta wanek ta tas duk abin da ke tsakaninsu ba ta taba fadawa
Abdul ba.
lyayan Hanifa su ma sun yi bakin kokarinsu don
har gara sai da uska yi mata, sun ji dadin aydda ta kwantar
da hankalinta ta rungumi mijinta shi ma kuma Abdul ya
san ya yi sa'ar surukai ya fauke su tamkar iyayansa, ko
yaushe cikin yi musu hidima yake.
So da kauna gami da fahintar juna ya dada
wanzuwa a tsakaninsu duk wanda ya je gidan sai ya fito
yana me sha'awar yadda ma'auratan suke gudanar da
rayuwarus cikin tsananin kaunar junansu. Abdulzahir har
mamaki yake yi ashe Hanifa za ta kaunace shi haka ganin
yadda ta sawa ranta kaunar tsohon saurayinta.
A bangaranta ita ma tana mamakin yadda yake tarairayarta gami da shagwaba ta. Ita dai tana iya cewa
53
matsalarta daya wato dangin miji gabanta har faduwa yake
yi ta ji ya ce za su gidansu don ta san ba za ta je ta dawo ba
tare da ranta ya baci ba, ballantana a ce ana wani taron suna
ko biki har ta ji ta dawo a darare take wulakanci ko sai
wanda ta gani, a gurin hajiyar Abdul ne kawai take samun
karbar arziki, dan dai-dai da 'yan dakinsu Abdul din ba
Kaunarta suke ba, In ka cire kaninshi Alkasim wannan kam
tasu ta zo daya shi kuma ba mazauni ba ne, habaici ma
kadia ya ishe ta.
Ita dai kam da da hali da ta ce da Abdul ya
sauwwake mata halartar duk wani taro na 6angaren
danginsa amma ta san ba za ta iya ba don zai bukaci sanin
dalili, ita kuma ba za ta so ta hada shid a 'yan wuanshi ba
ko dan- kar ta Kara yini wani bakin jinin. Tun da ba ta da
tabbacin ko yana sane da irin kiyayayr da suke gwada
mata. A nan 6angaran kam tana iya cewa Abdul ya fadi
don kwata-kwat aba shi da kula tana iya cewa mutum ne
me sakaci da yawa amma in ban da wannan ba ta ga abin ki
a halayyarsa ba. hakika tana son sa tana son halayyarsa.
Hakika idan ka san Hanifa a 'yan shekarun baya
idan ka gan ta a yanzu ba za ka shaida ta ba, ta kara kyau
nesa ba kusa ba ta yi haske ta yi 'yar kiba irin ta hutun nan
da ganinta ka san tana cikin daula cikin kuma kwanciyar
hankali. A bangaren ci da sha babu abin da ta rasa, kai hatta
da iyayanta irin hidimar da. yake musu ta isa. Nasir wanda
ake wa lakabi da Walid ya zama abin so a tsaknain
iyayansa barin Abdul don in yana gari a ko yaushe suna
tare da yaron, ko makaranta za ta je tun da ya fara shan
madara shi yake renonsa haka nan in yana gari shi yake kai
ta school ya fauko ta sai dai in yana dawani uzurin ne za
54
sa Driver ya dauko ta, in kuma ba ya gari ne akwai Driver
da yake kai ta ya dauko ta ya zuwa yanzu shekara daya ya
rage ta kammala NCE dinta.
***** ***** *****
Da misalin karfe hudu na yamınacin ranar asabar
Mas'ud ya dira a filin jrigin sama na Malam Aminu Kamo,
sanye yake da bakar coat ya tsuke wuyansa da neck tie ya
kafa bakin glass a idonsa da ka gan shi ka ga dan hutu.
Yanayin faşar jikinsa kadai ma ya sai ya tabbatar maka da
hakan. Yana saukowa daga step din jrigi ya nufi
mahaifinshi da suka zo taryarsa, suka rungume juna cikin
tsananin farin ciki daga bisani ya gaggaisa da sauran
kannenshi suka shiga mota suka rankaya zuwa gida. Aabu
daya ke yawo a kwakwalwarshi, abu daya ke da burin gani,
abu daya yake fatan kasancewa tare da shi har illa
Masha'allahu. Abu daya yake da burin ya malake shi, shi
kadai a duniyar nan, wato sarauniyar zuciyarsa HANIFA.
Suna tafe a motar suna hira amma shi jin su kawai yake
tuni zuciyarshi ta tafi ga sahibarsa yana ayyana irin fairn
cikin da za ta yi da yadda zai gan ta saboda zuwan bazatan
da ya yi mata.
Sun isa gida ya tarar da Mamanshi tana zaman jiran
isowarsa ai ko ya kankame ta cike da farin ciki, bayan
tsawon lokacin da aka dauka al'ummar gidan suna masu
nuna fairn cikin dawowar dan lelen gidan Mas'ud ya isa
turakar mahaifinshi ya iske shi a falo kan kujera ya zube a
kasa ya dada kwasar gaisuwa daga bisani ya ce Abba ga
55
1
result din ka gani da fatan wannan zai sanyayar maka da
zuciya a kan Gacin ran da na sanya ka. Alh. Khalil ya karba
cike da dokin ganin abin da ke ciki, ai ko yana gama
duabwa ya yi godiya ga Ubangiji kana ya yabawa dan nasa
saboda fitar da shi kunyar da ya yi. Be taba tsammanin zai
samu Good Result haka ba, ya kasa boye farinc ikins ahar
sai da ya bayyana masa tare dayi masa addu'ar fatan alheri.
Cikin jin dadi Mas'ud ya ci gaba da godewa
Mahaifinsa bisa jajircewar da ya yi har ya kai ga wannan
matsayi. Cikin jin kunya ya ce, Abba shi ke nan komai ya
shige ko? Kuskuren da na yi a baya a yafe ınin, dan haka
nake sake neman yardarka na ci gaba da neman yarinyar
da nake so. Ya yi murınushi sannan ay ce, Haba Mas'ud ai
komai ya shige sai dai a kiyayi gaba kowae yarinya ce kake
nema ka sanar da ni da zarar kun dai-daita mu je nenan
maka aurenta.
Yana shafa kai tare da sunkuyar da kai ya ce, Abba
ai yarinyar dai da ka san ina nema ce 'yar wajen Malam
Sa'ad, tuni mun fuskanci junanmu, aynzu abin da ka ga ya
dace sai a aiwatar. Mas'ud na jiran ya ji abin da mahaifinsa
zai e amma sai ya ji shi dif kamar an dauke wuta ya yi
kasake kamar me tunanin wani abu da ya ga an dau tsawon
lokaci sai ya ce, Abba ya na ga ka yi shiru? Ya dna yi
firgigit alamar tunani yake sannan ya ce, shi ke nan yanzu
dai je ka ka huta ba tare daya kawo komai ba ya yi sallama
da shi ya nufi gurin mahaifiyarsa.
Ya iske ta a Dining Holl ana ta jejjera masa
kwanukan abinci da aka girka masa. Ta tare shi da farin
ciki a'a har kun gama gaisawa da Alhajin sai ka je ka dan
56
watsa ruwa ga baincin nan ka ci domin yau da kaina na yi
maka duk irin kalar abincin da kake so.
Ya yi murmushi kai mama na gode, kina shagwa6a
ni da yawa amma bari na je wata'yar unguwa yanzu zan
daow. Haba daga dawowarka ko ina ne ka hakura ka htua
tukun. Mamaki yi hakuri Mama gurin haniffa za ni aynzu
zan dawo. Wace Hanifa?" ya dan zaro ido haba Mama kar
dai a ce kin mance ta? Sai a lokacin ta tuan ta ji gabanta ya
buga dam da karfi sosai.
Be kula da yanayin da take ciki ba ya fita da fan
sauri mama bari in sauri in je ko na dawo da wuri.
Lokacin da ya isa gidansu Hanifa ba kowa a wajen
ya jima yana neman wanda zai masa iso sai Allah ma ya
taimake shi Malam Sa'ad dawowarsa ke nandaga kasuwa.
Yana shirin shiga gida da sauri yafito daga motar ya tarye
shi, Malam na jin muryar ya shaida Mas'ud ne, nan da nan
ya juyo ciek da farin ciki yana a'a yau bakini turai ne a
garin namu? Ya bude musu shagon dake makale a kofar
gidan, bayan gaisawar da suka yi suka shiga tambayar
lafiyar juna gmai da yar taba hira. Sun jima a shagon har
Mas'ud ya Kosa babu abinda yake burin gani irin sahibarsa
ga shi yana jini nauyin Malam balalntaa ya saya turo masa
ita. shi kuma ya kasa faukar haske da dai ya ga bain ba na
Karau ba ne sai ya danne 'yar kunyarsa ya ce, Malam ko za
a samu yaron da zai kirawon ita. Wa ke nan?" Malam ya
tambaya. Abin ya fan ba shi mamaki, amma dai ya се.
Hanifa man. Hanifa kuma? E Malam ko ta yi tafiya ne? nan
da nan fuskar Malam ta saya mamaki ya kama shi dan shu
ko kadan be yi tsammanin ba shid a labarin ta I aure ba, ya
57
higa girgiza kai ya rasa yadda zai yi ya sanar da shi har dai
Mas'ud ya tsargu ya shiga tambayarsa lafiya.
Da dai Malam ayn gaba mafita ilal ya gaya mishi
gaskiyar lamarin duk da ya san yaron zai kadu amma boye
gaşkıyar babu abind a zai haifar. Ya yi ta maza ya zayyane
mıshı abin da ya faru ya kara da yi mishi nasiha. Ga
Mas'ud kuwa muna iya cewa suman zaune ya yi don
komtosi yakasa yi har Malam ya dan tsorata sai da ya fan
girgiza shi sannan ya dawo hayyacinsa kana ya dau lamarin
kamar a mafarki ya Rkara nanata tambayarsa ga Malam don
a turo masa Hanifa amsar nan dai da bai fatan ji ita ya sake
ji. Take ya dimauce ya shiga sambatu kai har ta kai shi da
zub da hawaye, shi dai Malam sai aikin lallashi yake yi
amma tamkar yana tira shi har Umma dake cikin gida ta
jiyo hayaniya