ta leko ai yana ganin ta ita ma ya dire mata
tare da neman tainakonta.
Da kyar da sidin goshi suka lallaba shi ya tafi tare
da alkawarin za a kawo mishi Hanifa har gida. Motar da ya
zo da ita ma ba su bari ya tuka ta ba dan sun fuskanci ba a
hayyacinsa yake ba. Yana isa gida ya iske Abbanshi tare da
mama wanda daman suke zaman jiran ko ta kwana, aiko ya
rushe musu da kuka yana zantuttuka tamkar tabab6e. Cikin
kuka ya ce, Abba kuna gani wani ya kwacen Hanifa to
wallahi ba zan iya rayuwa ba mutukar babu ita, da na san
haka zan zo in tarar da ban tafi karo karatun ba. Abba duk
kai ka janyo da ka katse min duk wata alaka da ke
tsakaninmu da hakan ba ta faru ba.
Mama ce ta daka masa tsawa kai ya isa ba ma son
sakarci a kan mace za ka zo kana gayawa mahaifinka
magana dan shirmen banza, daman can Allah be yi
58
matarka ba ce amma da ko shekara nawa ka yi in matarka
ce za ka zo ka tarar da ita. Abba ya ce ba fada za ki yi
mishi ba lallashinsa za ki yi. Ya dube shi ka yi hakuri ban
yi haka dan na raba ku ba ilal dan ka mai da hankali ka yi
karatui wallahi mukan mu mun ji zancen auren ne kamar
daga sama lokacin kwanaki biyu ya rage a yi auren, dan
haka muka mai da lamarin ga Rabbil Izzati, domin mun san
daman Allah be kadartomatarka ba ce, ga mahaifiyarka nan
ita ce sheda. Haka dai suka din ga lallashinsa gami da ba
shi baki anma a gurinsa duk a banza, tuni tunaninsa ya tafi
ta hanyar da zai bi ya kwato masoyiyasa ko ta halin kika
ne. abincin da aka tanadar masa ko ta kansu be bi ba duk da
matsananciyar yunwar da yake ji ya kulle kansa a daki ya
rasa abin da ke masa dadi ina ma a ce be dawo ba ya tarar
da wannan bakin labarin haka yake ayyanawa ransa.
Kwana biyu ya yi yana zaune a gida babu inda ya je
shi dai ga shi nan ne kawai nan da nan ya fita hayaycinsa
don ko bacci ba ya iya yi a daran kwana na-uku ne ya kasa
zaune ya kasa kwance so da kaunar Hanifa shi ke amsa
murkususu a zuciya ya baza hotunanta yana kallo tun yana
kukan zuci har ya fito fili yana yi tare da bubbuga hannunsa
a bango. Misalin karfe ukun dare Alh. Khalil da mama suka
dinga jiyo sautin kuka a dakin Mas'ud cikin hanzari suka
isa suka iske shi ya kifa kai yana kuik kashirban ba sai an
gaya musu e dalilin kukan ba ko dan ganin hotunanta da ke
zube suka tsuguna daf da shi suna aikin lallashinsa a da sun
yi fushi da shi ne sun kyale shi ganin sun mishi nasiha ya
hakura ya rungumi kaddara ya ki amma yanzu suna ganini
abin ya wuce wasa, dan da alama nema yake ya zauta da
kansa a kank soyayyar mace. Kwana suka yi a kansa suna
59
lallashinsa tard:da tottofe shi da addu'a har suka samu ya yi
bacci.
Tun bayan tawowarnmaslduadanga gidan Malam
Sa'ad Malam damatarsa Umma suka shiga damwua ganin
halinda dan mutane ya shiga har dai a kwana na hudu
Malam ya yanke shawarar zuwa gidansu lokacin da ya isa
gidan ya tarar da Alh. Khalil suka gaisa cikin karamci daga
bisani ya gangaro zuwa abin daya kawo shi. Abin da ya ji
daga bakin Alh. Khalil bai mishi dadi ba domin ya tabatar
mishi tunr anar da Mas'ud ya dira kasar ya fita hayyacinsa
sun dade suna tattauanwa daga bisani suka zarce dakin
Mas'ud halin da suka tarar da shi kam abin ya girgiza
Malam Sa'ad.
Ya shiga lallashinsa gami da yi mishi nasiha amma
a banza, shi kam abu daya yake bukata shi ne ya mallaki
Hanifansa ko ta halin kaka a duk lokacin da Malam ya zo
yakan roke shi ya raba auran 'yar tasa ya zo ya aura masa
ta, shi kam ya san ba abu ne me yiwuwa ba ko a
Musulunci ma be halatta ba. abu ku lum sai gaba yake yi
sai sam batu yake yi kamar taba6be da dai suka ga haka sai
suka sa a ka dinga yi masa saukar Alkur'ani mai girma.
gami da addu'a kusan kullum Malam yakan zo duba shi
gaını da yi mishi nasiha har dai Allah ya ganar da shi ya
hakura ya fauwala Ubangiji, iyayansa sun ji dadin hakan.
Suka yi mishi alkawarin duk yarinyar da ya ga ta yi masa
ya zo ya fada za su nema masa aurenta. Cikin dan
kankanin lokaci ya mai da ramarshi komai nashi ya koma
normal illa har yanzu radadin kaunar Hanifa na zuciyarsa
ne sai dai yakan yi kokarin kawar da ita tunda ya san ta yi
60
mishi nisa, shi da ita kam sai dai gaisuwar mutumci, kai in
dan ta shi ne ma sai ya ce kar Allah ya kara hada su har
karshen rayuwarsa. shikansa ya san duk ranar da Allah ya
hada su be san yadda zai yi ba, shin wane hali zai tsinci
kansa ya ga matar da ya fi so fiye da komai a matsayin
mallakin wani.
Tun bayan barin Mas'ud gida Najeriya ya kasa
mai da hankallinsa kan abin da ya kai shi so da kauna
gami da tunanin abar kaunarsa Hanifa ya sa shi kasa
maid a hankali ya yi karatu, karatun nasa sai ya zama
rabi da rabi a yawancin lokuta lokacin da y kamata a се
yana karatu amma sai ka iske shi makale da waya suna
ganawa da sahibarsa, ko kuma ya baje hotunanta ya
tsudnuam cikin tunaninta gami da ayyanawa ransa irin
kasaitacciyar soyayar da za su yi da zarar sun yi aure.
Abokananshi sun sha yi mishi fadan ya mai da
hankali wajen karatui amma a banza, ai ko shekara na
zagayowa ya samu mummunan kayi shi da kansa be yi
mamakin hakan ba be kuma wani damu sosai ba sai mna
farin ciki dayake yi ai dawo ya ga abar kaunarsa duk da
sanın makudan kudin da mahaifinshi ke kashewa a kan
karatun, tunaninsa ya sauya ne lokacin da Abbansa ya
samun labarin abin da ya faru. Ransa ya yi mummunan
baci saboda tuni sun gama shiryawa da abokanansa tare
da hadin gwiwar kamfanin Honda da ke Kasar Japan za
su bude Branch na kamfanin za su dinga shigo da Spare
parts 61
A nan gida Najeriya
idna za a dinga hada su a kamfanin. Mas'ud na cikin
jerin mutanen da za su ci gajiyar abin ta hanyar samun
mukami me girma mutukar ya fito da kyakyawan
sakamako yadda ake bukata ko kadan Alh. Khalil be
taba zaton zai ba shi kunya ba ya san ya yarda da
hazikancin dan nasa sai ga shi ya yi mishi ba zata abin da
ka iya sa ya rasa wannan babban matsayi. Hankalin Alh.
Khalil ya tashi ya yi wa dan nasa fata-fata saboda zaton
ko ya tsaya shashanci ne ya sa shi samun wannan
mummunan kayi. daga bisani ne ya samu labarin abin da
ya sa shi kasa mai da hankali ya yi karatu. Take ya buga
mishi waya ya sanar da shi ya san halin da yake ciki tare
da alkawarin mtuukar ya Kara saurarar Hanifa ko ya
bugomata waya be yafe masa ba. da sharadin sai ya
kammala karatunsa sa ci gaba da gudanar da soyayyarsu.
Kai dokar ta yi kamari har ta kai da ya shafi duk wani
wanda yake mu'amala da shi hatta da gidansu sai da ya
katse duk wata alaka dake tsakani, fatanshi ya tsaya ya
vi karatu ya samu abin da ake bukata in ba haka ba yana
ji yana gani damar za ta subuce masa inda Allah ya
taimake shi ma an fage bude kamfanin zuwa shekara me
zuwa saboda wasu dalilai.
Wannan dalili shi ne musababbin katse duk wata
alaka da ke tsaknain Mas'ud da Hanifa, duk da haka
yana rike da alkawarin da ke tsakaninsu har dai zuwa
ranar da ya kammala karatunsu da gagarimar nasara shi
kansa be yi zaton zai samu good result haka bal. Allah62
Allah yake ya dawo ya nunawa mahaifinshi sakamakon
don ya san zai yi farin ciki tare da fatan mallaka mishi
abar kaunarshi. Kwatsam kuma sai ya dawo ya tarar da
wannan mummunan labari da ba zai taba mancewa ba.
An bude kamfani cikin nasara Mas'ud shi nc a
mataki na uku a duk fadin kamfanin. Cikin fan kankanin
lokaci ya dukufa aiki ba dare ba rana. Nan da nan suka
soma samun ci gaba sannu a hankali kamfanin na
karbuwa. Babu wanda ya fi farin ciki irin Alh. Khalil da
man kokadna ba ya jin danshi wajen dagewa da juriya
gami da kwatanta gaskiya da rikon amana. Fatansa daya
ya fito da mata ya yi aure ko ya zama cikakken mutum.
A bangaren Mas'ud shi ma muna iya cewa yana jin
dadin yadda yake gudanar da iakinsa babu abin da ya sa
a gaba irin aikinsa wannan ya sa duk ya kawar da wani
tuani da kunci dake zuciyarsa.
Ranar alhamis biyar ga wtan takwas na shekara ta
dubu biyu da biyu ranar da ta zamantotushenf aruwar
mummunar rayuwar da masoyan suka tsinci kansu a ciki
da misalin karfe biyar na yamma Mas'ud ya hade cikin
coat ruwan makuba wace ta yi masifar yi masa kyau da
ka gan shi ka ga matashi me ji da kansa ya isa
makarantar F.C.E. don ziyarar wani abokinshi da suka yi
karatu tare tun farkon dawowarsa yake so ya ziyarce shi
Allah bai yi ba sai a yau. Ya dade a harabar makarantar
yana nazarin wanda zai samu ya tambayi inda abokin
nashi yake. Yana ankare da yadda yammata ke kai kawo
ta gabanshi suna karairaya tuni kuma ya gano manufarsu.
63
amna shi ko a jikinsa dan ba a gabansa suke ba, kamar
ane daga kanka ya hango ta zaune a gindin wata
ısya kanta na sunkuye tana nazarinwa su littattafa.
Tana sanye da wani danyen voil, jikinta rufe da wani
yalwataccen mayafi duk da fuskarta na sunkuye hakan be
sa ya kasa sheda ta ba. Shi dai be san yadda aka yi ba ya
samu kansa ne a tsaye a kanta ya fan jima yana kallon ta
har daga bisani jikinta ya ba ta akwai mutum a kanta.
Dagowar da za ta yi ba sai ta yi arba da fuskar mutumin
da ta fidda ran sake ganinsa ba. Ta saki baki galala cike
da mamaki shi ma din kallon mamaki yake mata sun
dade a haka sannan ya yi karfin hali ya ce, "Hanifa."
Cikin raunananniyar murya. Ta dan bude baki za ta yi
magana sai ta fasa ta runtse idonta gami da ciek baki ya
kara matsowa daf da ita yana kiran sunanta ta bude ido
tana kallon shi kawai hawaye na zubo mata. Kome kuma
ta tuan sai ta yi zumbur ta mike gami da kwasar
littattafanta har tana zubar da wani ta yi saurin barin
wajen ganin haka shi ma ya bi ta yana kiran ta sai da
suka dangane da bakin titin Kabuga sannan ta tsaya.
Tana ganin mota ta tsaya ta shiga ba,tare da ta sanar da
me tasin inda za ta ba. Yana tambyar inda za ta ta ce mu
je zuwa, shi ko da ya fita ya tashi motar har suka kai
junction din Tal'udu ba ta san idna kanta yake ba shi ko
dan tasi mikewa yake kamar yadda ta umarta sai da suka
kai ga karshen titin daf da kasuwar kwari ke nan sannan
ta farga da inda suke. Ta uamrce shi ya karya kwana
zuwa Nassarawa G.R.A. kan titin Sultan.
64
Tana isa gida daki ta shige ta kulle kanta don ba
ta bukatar hayaniya ta fada gado ita dai sai ji ta yi tana
kuka har da shessheka ta kasa tantance dalilin da ya sa ta
kuka, nan da nan zazzabi ya rufe ta lokacin da
Abdulzahir ya dawo gida ya tarar da ita-cikinw annan
hali take ya rude ya shiga tarairayarta yadda ya saba duk
da kin amincewar da ta yi sai da ya kai ta asibiti cikin
daran haka ya kwana yana jinyarta, ko kadna ba ya
kaunar duk waniabu da zai taba masa mata. Ga- Hanifa
ko kwana ta yi cike da tunani barkatai, ta yi da ka ce ma
ba ta je school a ranar ba ballantana ta ga abin da zai
tayar mata da hankali, kai hasali ma ba ta taba sanin
Mas'ud ya dawo ba ballantana ta sa ran ganin shi.
A bangaren Mas'ud kuwa yadda ya natsa a bakin
titi yana me mamakin abin da ta yi masa sai kuma daga
baya ya tuna ashe fa wai tana da aure ba ya raba dayan
biyu dalilind a ya sa ta yi amsa haka ke nan. Ya juya a
sanyaye sai kumak kunyar mutane ta kama shi ganin
yadda suka zubo masa namujiya kai shi yana iya cewa
ma bai sna yadda-aka yi ya biyo ta har bakin titi ba duk
da tazarar da ke tsakani daga cikin makarantar zuwa
bakin titin haka dai ya Karasa ya dauki motarsa batare da
ya tuna makasudin zuwansa makarantar ba.
Misalin karfe biyui na dare ya kasa bacci
idanunsa a bude suke ko ko a rufe ne abu daya suke gane
masa wato Hanifa. Ya dinga tunano rayuwar da uska yi a
baya da ke nan ta zama rabon wani ashe daman ba
kaunarsa take ba kilama tuni ita ta mance da shi kai shi
65
Σ
ma gwada ya mance da ita ya shafe ta daga babin
rayuwarsa gaba daya. Me zai da mayaudari kokari yake
ya cire ta a ransa amma ina zuciyarsa ta kasa yarda da
hakan. Yana ganin har abada ba zai iya daina son ta ba.
ya dinga tunano yadda ya ga ta kara kyau ta zama
cikakkiyar mace ko da can ba baya ba ce ballantana
yanzu da take cikin hutu ya dinga tunano kyakyawan
jikinta shi ke nan ya zama rabon wani. "Kai ina
impossible." Ya fada da karfi a yayin daya mike yana
zagaye dakinsa kuma ya jingina da bango ya rufe
idanunsa yana kiyasta irin rayuwar jin dadin da za su
gudanar da zarar ya mallake ta. "Kai ko ta halin kaka
Hanifa sai ta dawo gare ni, ni ne nake son ta nake
kaunarta nake son duk wani abu da take kauna." Ya
debo hotunanta yabaje yana kallo sai ta dinga yimishi
gizo yana ganin akmar ita e sai ya je gare ta sai kuma ya ji ba ita ba ce zuciyarshi ta ci gaba da azalzalarshi da
Kaunar Hanifa tare da kwadaita mishi ni'iamr dake gare
ta ya kudure ko ta wace hanya ce sai ya malalke ta.
ZUCIYA BA TA DA KASHI, Ubangiji ka fisshe
mu sharrin zukatanmu, domin shi kam ya kasa daurewa
zuciyarsa abin da take so take kuma angiza shi. Shi ne
yake kusantar shi.
Kashegari ya nufi F.C.E. dai-dai idna ya gan ta na
nan ya nfua amma ko me kama da ita be gani ba. ya dade
yana gararambar neman ta duk wanda ya tambaya sai ya
ce be san ta ba daman ga ta ba gwanar shiga jama'a ba.
ya dau tsawon lokaci a school dini amma be same ta ba
66
haka ya dinga yi har tsawon kwana uku. A kwana na ukun ne ya tuna da abokisna Isma'il wanda a dalilin
zuwa wajenshi ne ya gnao abin da ya dagula masa lissafi
tare da taimakon wani Malami ya sada shi da inda yake
Ya iske shi a office dinsa Isma`il ya yi farin ciki da ganin
abokinsa, suka rungume juna cike da farini ciki. Bayan
tsawon lokaci da suka dauka suna hira isma'il ya
fuskanci abokin nasa ya dulmiya wata duniya ya dan
daki kafafarsa ya ce, Kai fa tsiyata da kai ke nan, da ka
zauna ba ka da wani aikin yi sai tunanin wa ta ke ne?
Halima ko Hanifa?
Mas'ud ya dago kai cikin mamaki ya a ka yi ka
ganc? Ka mance zaman mu na Japan ke nan? Shin ba ni
nake maka fadan ka rage tunanin ta ba? ka mai da kai ga
abin da ya kawo ka? Shin akwai wanda zai zauna da kai
na tsaown awa daya ma ba tare da ya sa matsayinta a
zuciyarka ba. Ka san ko yanzu ma ita na zo nema. Ban
gane ba, kana nufin Hanifan? Ita fa. Me ya sa ba za ka je
gida ka same ta ba? ka san wasu matan ba su cika son
saurayi ya zo wurinsu a school ba.
Mas'ud ya yi shiru yana nazarin amsar da zai ba
shi ya san tsattsauran ra'ayinsa da arar ya ji a halin yanzu
tana da aure ba zai ba shi goyon baya ba, dan haka ya
dora shi da cewa sun dan samu sabani ne ko ya je gidan
ba za ta fito ba. ya dinga kwatata mishi ita har dai Allah
ya sa ya gane ta. An ci sa'a yana daukarsu darasin
turanci ya yi mamaki don be taba tsammanin ita ce
Hanifan da abokinshi ya mato mata ba. Ya kuma yaba da
67
zaðin abokin nashi don a ko yaushe za ka gan ta cikin
shiga ta kammala ga ta da hazaka wajen karatu shi a da
va yi tsammanin tana da aure, saboda tsabar kamewarta
a nan ya tabbatar masa kwananta uku rabon da ya ga ta
zo school. Ya karbi nambar wayarshi da zarar ta zo zai
sanar da shi.
A gida yake a office ne kai a ko ina ne Hanifa ke
zuciyarshi a ko yasuhe fatansa ya sake sanya ta a
idanunsa ko zuciyarsa ta yi relief daga azalzalarsa da
take yi kullum ya je school fin sai Isma'il ya ce ba ta zo
ba har yake shawartarsa ya jarrabawa zuwa gidan nasu
ko za ta fito shi dai ya amsa da to, saboda idanshi ya rufe
da wutar begenta har ya fara tuannin bin shawararsa.
Cikin dabara ya samu su Nusaiba a school dinsu ya nuna
kamar ya zo duba su ne ya dinga jan su da hira har ya
samu abinda yake son ji ba tare da sun fahimci komai ba.
Be sha wahala ba wajen gane gidan haka zai
zauna na tsawon awanni yana jiran ya ga fitowarta har
dai ran nan Allah ya sa ya dace ya hango ta gilashin
mtar da take ciki hannutan rike da wani dan karamin
yaro gefenta wani kyakyawan mutum ne wanda ya
tabbatar mijinta ne. da alama unguwa za su. Ta gefensa
suka zo suka shige ba tare da ta gan. shi ba. wani
masifaffen kishi ya turnuke shi sai dai a wani bangaren
zuciyarshi ta yi sanyi tun da ta ga abin da take bege.
Sai da akai sati guda cur da haduwarsu sannan
Hanifa ta fra zuwa makaranta ba wani abu da take
zulumi ilal nna gudun ta kara haduwa da Mas'ud, tana
68
tsoron zuciyarta don a wannan kwanakin da ta yi fiye da rabinsu ya ta`allaka a kan tunkanin tsohon masoyinita.
duk da kokarin da take na ta yakice shi ko kadan ba ta fatan sake ganinshi.
Abin da take gudun kuwa shi ya faru, ko cikakken
sa'a daya ba ta yi da zuwa makarantar ba suna tarc da
Huwailat aka aiko kiranta daga office dini Lecturer dinsu
me daukarsu darasin turanci. Ammaki ya kama ta amma
da ta tuna Malaminta ne kila wani abin ne ya faru
dangane da harkar karatunta ta dada suturce jikinta
sannan ta isa office din. Mamaki ya kama ta ganin wanda
ta tarar a tare da Malaminsu. Ta dada daure fuska ta
gaida shi tare da cewa Malam an ce kana kira na? Isma'il
ya dan yi murmushi kwarai ni na aika a kirawo ki amma
ga me son ganin naki nan. Ya sa kai ya fita dan ya ba su
waje. Ta bi Malamin da kallo, a da yana daya daga cikin
Malaman da take ganin kimarsu saboda kamewarsa
amma a yau kam ya zub da duk wata kima da take zaton
yana da ita, in banda rashin mutumci me zai sa tana da
aure ya kirawo gurin wani ko ko me ya dauke ta ne?
Mas'ud ya dan gyara murya ya ce, "Ki zauna man
Hanifa." Ta juyo da fuskarta gami da galla mishi wata
harara ta nuno shi da yatsa, Ka ga Malam ka fita hanya ta
ko ba ka san da igiyar wani a kaina ba? ko kana
tsammanin ni 'yar iska ce? Ya ce haba Hanifa ni kike
gayawa wannan maganar, ki yi min alfarma daya ki
saurari abin da zan gaya miki....." be karasa ba ta katse
shi a hasale, me zan ji daga gare ka yaudara ko sabа
69
alkawari? To ka ga ka fita hanyata ka gane ko? Ta fice
abinta shi ko ya bi taa kallo ya kasa yin katabus jikinsa
ya yi sanyi wai yau Hanifanshi ke yi mishi haka.
Abhinda ya fi ba shi mamaki kalamanta na karshe in har
shi be ce mata ta karya alkawari gami da yaudararsa ba
ai ko be kamata ita ta ce masa haka ba. Ya kifa kai a
table din dake gabansa sai kawai ya samu kansa da zub
da hawayc. A kan mace ya zub da hawaye sau ba a dadi
lallai ya kamata mu kira shi da ragon maza.
Kai haka dai ya dinga nacin kiranta har na tsawon
kwanaki amma sam ta ki zuwa da abin ya ishe shi ya tafi
har department dinsu ya yi sa'ar ya tarar da ita a gindin
bishiyar da ya fara ganinta wąnnan karon ma ita kadai ce
tana dago fuskarta ta yi arba da shi tsaye a kanta ai ko ta
tsora ta jikinta har dan rawa yake yi ba dan komai ba sai
dan yanzun nan ta fito daga hall. Bayan sun gama daukar
darasi saboda irin habaice-habaicen da Zakiyya ke mata
ya sa ta fitowa ko kadan ba ta son ta biye mata ko dan
darajar yayanta amma da ba dan haka ba da kullum sai
sun yi fada, ita kam ta rasa dalilin wannan kiyayya da
take gwada mata, abin tsautsayi yanzu kuma a ce ta zo ta
gan ta da wani namijin ai kuma sai abin da ta kitsa mata.
Cikin sanyayiyar muryarshi ya ce, "Hanifa ni kike wa
haka ko? Yau ni kike gudu ko? Kin mance da kaunar da
ke tsakaninmu?" cikint soro ta ce, "Dan Allah ka yi
hakuri ka rabu da ni na gaya maka ina da aure." Ya ji
wani abu ya tokare mi shi zuciya, ko kadan ba ya so ya ji
wannan kalmar ta fito daga bakinta. Cikin fushi ya danki
70
hannunta ba ya tunanin jama'ar da ke kai kawo a wajen ya ce ko ki bi ni mu je office din isma'il ko kuma mu yi
ta zama har wanann dan iskan mijin naki ya zo ya tarar da mu a haka don na san abin da kike tsoro ke nan ko?
Gaba daya ta gama kaduwa babu abin da take
tsoro irin Zakiyya ta leko ko ta fito ta gan su a haka ba
tare da wata shawara ba ta bi shi. Suna shiga offic din ya
tura kofar ya saki hannuta ya kifa kansa a bango yana
fidda wani irin nishi ita kuma tana tsuguen ta kfia kai a
kan gwiwarta tana kuka. Sun dade a haka sannan ya zo
ya tsuguna daf da ita ya sa hannu ya dago fuskarta tana
kokarin kwacewa ya rike hannayenta ya yi zaman
dirshan a gabanta ya dora kanta a kan kafadunsa kana ya
dora fuskarsa a kan bayanta, ta ji wani abu yarr ya ratsa
jini da tsoka hade da gangar jikinta haka kawai sai ta
samu kanta da kasa janyewa daga gare shi sai ma wani
sabon kuka da ta saka.
Sun dade a haka sannan ya dago fuskarta ya sa
handkerchief ya goge mata hawayen da ya 6ata mata
fuska. Ya rike mat ahannu gam ya fara magana а
sanyaye. "Hanifa me ya sa za ki yi min haka? me ya sa
za ki auri wani ba ni ba? kin san iriin matsananciyar
Kaunar da nake mik? Ke kanki na san ni kadia kike so to
me ya a za ki auri wani bani ba wallahi ba zan iya
rayuwa ba tare da ke ba, ke kanki kin san da haka shin
ina alkawarin damuka yi wa juna." Ya dada kankame
hannayenta.
Ita kanta jikinta ya yi sanyi ta kasa aiwatar da komai
hakika abin da ya fada gaskiya ne shi kadai take so duk
wanda za ta so a bayanta yake to amma ya za ta yi?
Ya kara cewa, kin yi shiru ko kin daina sona ne?
anya kuwa daman can kina yi min pure love? Wallahi in
har ba kya kaunata gwanda mutuwata da wannan rayuwa.
Ta sa hannu ta toshe masa baki hade da girgiza masa kai
muryarta na rawa ta ce, "Mas'ud ka san ina son ka ian
Kaunarka illa wani lamari da Ulbangiji ya aartar a kanmu.
Ka yi ahkuri wallahi har abada ba zan daina son ka ba,
amıma yanzu ka ga ba yanda zan yi tun da da aur....."Ba ta
Karasa ba ya katse ta, "Ba na son wannan maganar, ki dai je
ki yi nazari ki samo mana mafita na ba ki daga nan zuwa
kwana biyu.
Tana komawa gida ta tarar da Abdulzahir har ya
dawo. Ta dauke kai kamar ba ta gan shi ba. gaba daya
haushinsa take ji domin shi ne y ai musu katanga tsakaninta
da mutumin da ta fi kauna fiye da kowa, shi kansa ya lura
da sauyi da ya gani a tare da ita, da ya tamlbaye ta dalili sai
ta ce kanta ke ciwo ai ko ya shiga tarairayarta kamar yadda
ya saba be san gaba daya haushinsa take ji ba.
Misalin karfe daya na dare wayarta ta yi kara, ta
duba ta ga ba ta san nambar ba kamar kar ta dauak ai dai ta
danna cikin muryar me yin bacci ta ce, "Hello, hello
waye.?" A daya bangaran aka amsa da cewa, "bacci kike
ko Hanifa? Ni ko ga shi tuanninki ya hana ni sakat." Ai da
jin mruayr ta shaida Mas'ud ne take ta dan yi kara saboda
tsoro dan suna kwance ne tare da Abdulzahir