ta zo ta sanar da ita result ya fito suka je
suka amso babu laifi result ya yi kyau ta samu 3 credits 2
pass 1 Distinction a 6angaren WAEC ke nan a NECO kuwa
ta samu fiye da haka.
Gabanta na faduwa saboda sanin abinda zai je ya
dawo tsakaninta da mahaifinta ta dai daure ta iske shi a
falosna yana lazimi sai da t abari ya kammala ta russuna ta
gaishe shi daga bisani ta mika mashi resutl din nata gami
da yi mishi bayanin kowanne dalla-dala. Ya karba yana mai
nuna farin cikinsa da yaba mata kan kokarin da tayi. Ta
dan rissinar da kanta ta ce Malam daman wata alfarma na
zo nema. Ya yi murmushi fadi ummata wace alfarma ce na
yi miki mutukar ba ta fi karfinia ba (da yake ainihin
Sunanta sunan mahaifiyarsa ne, an sakaya ne ake ce mata
lanifa). 30
Ta ji kwarin giwa, Daman Malam dangane da
karatuna ne nake neman yardarka na ci gaba da
karatuna..... ba ta karasa ba ya daka mata tsawa ya ce, kina
hauka ne?" kin san abin da kike fada? Wane irin akratu
kuma? Duk wanda kika yi bai ishe ki ba, ko dan kin ga na
kyale ki wato kin girma kin yi ilmin da za ki juya ni ke nan,
to bari ki ji na zuba miki ido ne na ga gudun ruwanki da an
yi zance sai ki ce ya kusa dawowa to shin shi zai yi jiranki
ko ko ke za ki yi jirans,a ni na soma tsinkewa da zancen
yaron nan, ca nake kin ce shekara daya zai yi ga shi har
yana shirin yin ta biyu. Ca nake tare aka ce za a hada bikin
da na kanwarsa ba ga shi ita har an yi nata, so kike ni na vi
ta zuba miki ido ina kallonki, to bari ki ji na ba ki nan da
wata uku ko ki fito da wani wanda kike so ko kuma na aura
miki wani kamar yadda na yi wa sauran 'yan uwanki.
Tana kuka ta ce dan Allah Malam ka yi ahkuri ka
ga ni ma ba laifina ba ne shi ma kuma akwai uzurin da ya
dakatar da shi ya ce karshen shekarar nan zai dawo. (Ta yi
wannan karyar ne dan ta kare Mas'ud ko da wasa ba ta
fatan wani abin da zai kawo matsala a tsakaninsu). Ta shis
yi mishi daddin baki da yake ita gwanar iya magana ce
Allah ya yi mata wannan abiwar kam a ci gaba da cewa, shi
ya sa nake neman yardarka na.ci gaba da karatuna a
maimakon zaman haka. Allah yana dawo da shi shi ke nan
na hakura sai kazartar da duk abinda va dace. Wallahi
Malam ka san ina kaunar ka ina gudun bacin ranka ba zan
yi duk abin da zai zubar mana da martaba ko mutumeinmu
ba, jikinsa ya yi sanyi ya ce shi ke nan ki ba ni lokaci zan yi
tunani. 31
Ba a fi sati biyu ba ya ba ta izinin ci gaba da
karatunta duk da an kai ruwa rana kafin Umma ta amincе a
cikin wata daya ta gama yin duk abin da ya dace dace
dangane da karatunta ta faca zuwa makarantar da ta dade
da burin shigarta wato F.C.E. Kano. Da yake ra'ayinsu ya
zo daya da Huwailat sai ya zamanto suna department daya
ne bangaren Education tana karantar English/Sos.
A wannan lokaci ne Ammar ya tafi Rasar South
Africa kamfanin da yake wa aiki ne ya tura shị can har gida
ya zo suka yi sallama ta kara tabbatarwa shi ke nan ta dada
nisa da Mas'ud a ko da yaushe takan yi tsammanin zai
bugo mata waya to ga shi wanda yake sada ta da shi ya tafi
abin mamaki har zuwa lokacin da zai tafi yana sake nanata
mata ta rike alkawarin abokinshi. Ta dai fahimci ba wanda
ya fuskanci abind ake tsakaninsu ga rashin Fauziyya wace
sukan yi hirar yayanta da shi ta fan ji sanyi abu dai ya dada
cabe inata, dan ma a ko da yaushe Huwailat na kwantar
mata da hankali tare da nuna mata kila akwai uzuirin da ya
tsaida shi dan daga baya ta zayyane mata duk abin da ke
gudana a tsakaninsu.
Sannu-sannu suna karatu har suka kai zangon
karshe na shekarar sun yi jarrabawa an musu hutun karshen
shekara. Wata ranar Asabar da yamma ta yi wanka ta nemi
iznin mahaifiayrta za ta je shopping centre. Ta kimtsa cikin
atamfa 'yar Koddebuwa ruwan kasa dinkin me sharp ne ya
fito mata da ainihin surar jikinta ilal dai ta yafa yalwataccen
mayafi, takalmi da jaka bakake hakika kayank sun yi mata
kyau domin ita bain a jikinta ne duk munin kaya in ta sa shi
sai sun yi mata kyau. Ga shi Malam ba da gana nan ba
wajen wadata iyalinsa in ka ga sutturun da suke sa wa sai
32
ka yi zaton 'ya'yan masu hali ne haka nan ta fannin abinci dama karatunsu.
Ta sai Sahad Store ta nufi bangaren cosmetics ta shiga zabo tsadaddun turarruka da yake Alah ya yi ta da
son kamshi. Turare komai tsadarsa mutukar a ya yiimata takan siye shi, hakika takan dada yin kewar Mas'ud domin
tun da ya fahimci ita ma'abociyar son kamshi ce yakan siyo
mata tsadaddun turaruka masu kamshi babu turaran da ta fi
so irin (Pleasures). A duk lokacin da zai kawo mata turaren
yakan hado mata da shi. Yakan ce mata Hanifa babu wani
kamshin turarc da na fi so irin 'Pleasure' saboda haka nake
so a ko da yaushe ki dauwama cikin kamshinsa kamkar
yadda a ko yaushe shi ne abin shafawata. Wannan dalili ya
sa ba wani turaren da ta fi so irin sa.
Ta yi sa'a ta same shi a store din cikin hanzari ta
debi guda biyu amma kuma da ta duba kudin dake jiki sai
ta ga kudin da ke jakarta ko guda daya ba zai sai mata ba.
tayi mamakin tsadar turaren. Ta ayyanawa ranta lallai ba
karamin kudi Mas'ud yake kashe mata ba a bangaran turare
ma kawai. Tana ajiye turaran da zummar ta samu me dan
saukin kudi ta siya sai ta ji magana daga bayanta ana cewa,
"Haba 'yamınata ya za ki ajiye wannan daddadan
turaran.?" Ba ta ce komai ba dai ta ci gaba da abin da ke
gabanta. Ya Kara matsowa daf da ita tare da daukar turaren.
Ya kalle ta ya ce a gaskiya kar ki wuce wannan turaran duk
wadannan babu me dadin kamshin kamar sa. Ta jiyo ta ga
wannan sarkin ancin ai ko idonta ya yi karo da wani dan
kyakykawan matashi ta rasa me za ta ce masa domin ya za
a yi ta sanar da shi kudinta ne ya yi short.
33
Sai ta daure fuska na gode. Da tayin da ka yi min
Malaım amına ba nid a ra'ayinshi. Ya yi murınushi gamid a
zura hannu cikin aljihu ya tsare ta da itokin ga ko duk
wadannan babu turaren da ya dace da ke irin wannan.
Ni kuma ba ni da ra'ayinsa yaya ke nan? Ta fada
cike da kosawa da surutun nasa. Ya yi murmushi mai da
wukar amma na san kin fada ne kawai alhalin ba haka abin
yakc a zuciyarki ba koba haka ba? mamaki ya kam ta sai
kuma ya ce na fahimci haka ne ta yanayin kamshin turaren
da ya ke fita daga gare ki ai ko ta tuan kafin ta fito ta feshe
dan ragowar da ya yi mata saura. Ya ce ko na yi karya ne?*
ta kalle shi tsawon dakikoki sai kuma ta dauke kanta ta yi
bangaren maya-mayai tana zaba, a nan ma gwana ce, akwai
ta da son mai me kamshi be gaji ba dai ya sake bin ta bari
in taya ki zabar man ko.
Ya dauko dan karamin kwando ya dinga diban duk
wanda ya zo hannunsa yana zubawa har sai da kwandon ya
cika. Ta kai hannu za ta dau wani may a dai-dai lokacin shi
ma ya kai hannunsa yana kokarın dauka. Sai ji suka yi
kowanne ya dauki hannun ſan uwansa ba tare da sun sani
ba. Tayi saurin janye hannunta har ta ba shi dariya ya се
kamar wanda zai cinye ki. Ta yi gaba za ta shige ya ce ga
ajiyarki. Ta kalli tulin maya-mayan ta kada kai za ta yi
gaba yà dan tari gabanta ko ba ki ji ba ne. na saka? Kwarai
kuaw to ka rike abinka na gode. Ya ce Allah sai kin karba.
Ta rike baki ta na mamakinsa sai kuma dariya ta kubисе
mata. Ta ce, yau na ga ikon Allah, dan Allah Malam ka
kyale ni. Ya ce in kina son na kyale ki sai kin karbа. Та
fan ratse ta gefe ta shige shi ma ya bi bayanta suka jera
tamkar ango da amarya. Ma'aikatan store din suka bi su da
34
allo cike da sha'awar wannan jaririyar soyayyar. AnAn zo
vajen biyan kudi akai total din abin da ta siya aka zuba a
cda za ta ba da kuddin aka ce Oga ya biya. Ta san wanda
ke nufi dan haka ta ki yadda da ta ga sun ki karbar kudin
ai ta hakura ta fita. Tana fita ya bi bayanta ya iske ta a
arabar kantin ya sha gabanta ya tsaya yana murmushi ya
e, 'Yan mata za mu rabu ba ki gayan sunanki ba. ta ce
Malam ka yi hakuri sanin sunana ba shi da wani amfani a
are ka, a ganin ki ko? To ni sunana Abdulzahir ba Malam
ba. Malam din nan ta fita daga bakinki, kin gane ko. Тa
kalel shi akwai ya ce kin san Allah in ba ki gaya n ba za mu
i ta tsayuwa a nan. Tabbatar zancensa haka ne dan da
lama irin mutanen nan ne masu shegen naci dabara ta fado
nata tace sunana Bilkisu. Ya ce, to Malama bilkisu zo na
kai ki gida ko. Ta ce a'a na gode ni Malamar nan ta fita
daga bakinka bilkisu nake. Ya gyada kai to shi ke nan a yi
min afuwa bisimilla mu je in kai ki ko? Ta ce yanzu kai
kana ganin ya dace daga ganin mutum sai na shig amotarsa,
wa ya sani ma ko dan.... Ta kasa karasa maganarsawa ya
kwashe da dariya bari na karasa mi ko dna yankan kai ne
ko? Amıma kuma ko yankan kai nake ina ga kanki ba zai
tsada ba ko? Ta dan runtse ido sakamakon kunya da ta
kama ta ya ce shi ke nan na yadda da uzurinki bari na
samo miki taxi. Kan ta yi magana ya isa bakin titi har ya
tsaida mota. Tana nazarin wace karyar za ta yi mishi tun da
ta san titi kawai za tą tsallaka ta karya kwanar unguwarsu
amma da ta tuna hakan zai ba shi damar sanin ainihin
hakikanin sanin unguwarsu sai ta bi shi a hakan. Tа се
masa tana unguwar Aisami sai da ya ga shigar ta motar
mnan ya bude but din motar ya zuba tarin wasu kaya a
35
cikin ledodi sannan ya mikawa Driver 500 kudin mota
mutumin ya karba cike da mamaki abin da be fi a ba shi
#50 ba sai ya shiga yi masa godiya yaa dan leko jikin
window ya ce masa ka fa kular min da mata kar wani abu
ya same ta. Cikin hanzari ya ce to yallabai Allah dai ya
saka da alheri. Sai da ya ga bacewar motar sannan ya shiga
tasa ya tashe ta ya tafi.
Suna zuwa dai-dai kofar gidansu ta tsaida dan tasi
din nan ya kalle ta cikin fargaba tamkara wace ta ke shirin
kwace kudin ya ce ba kin ce unguwar Aisami zan kai ki ba.
ta yi murmushi saboda ta karanci abin da ke zuciyarsa
sannan ta ce ba wani abu ka sauke ni a nan na fasa zuwa
can din da sauri ya fito ya firfito mata da kayan da ke but
din sai da ta ga kulewar me motar ta dan waiwaiga ta ga ba
me bin ta sannan ta shiga gida. Bayan ta yi salah ta shiga
bubbude kayan. Mamaki ya kamata ganin tsadaddun
turarukan da maya-mayan da ke ciki, ta jinjinawa wannan
mutum wanda ta yi masa lakabi dama wayo domin ta san
ya zuba adashin da ba zai dawo ba, ko kuma ta ce ya zuba
a bankin asara. Ta san ba ta yadda za a yi ya gano inda
take. Ban da ma shirme daga haduwa da mutum ka kashe
masa wannan makudan kudi ita kam ta san Allah ne ya
kashe ya ba ta, ko da wasa ba ta nunaawa mahaifiyarta
kayan ba dan ma kar wani abu ya biyo baya.
Kashegari da yamma aka aiko ana sallama da ita.
amma ta ki fita abin mamaki mutumin be yi zuciya ba sau hudu yana sake turowa ta je na karshen ne ya hada ta da
girman Ubangiji ta je. To sannan ne ta fita ta ga wannan
wane uban 'yan nacin ne. Tana isa soro ta iske wani kyakkyawan saurayi a tsaye ya sha hartin da wando na
36
Galila Kamshin turare sai tashi yake a jikinsa. Ta dan kalle
shi tana nazarin ina ta taba ganin wannan kyakkyawar
fuskar, amma ta kasa tuanwa. Ta dan rakube daga jikin
bango ta gaishe shi a mutum ce ya amsa tare da jin dadin
haka. Ta dan yi shiru tana satar kallonsa don gaskiya ya
burge ta ba ta taba zaton za ta ga bakin mutum me kyau
haka ba. ya dan yi gyaran murya har ta dan ji kunya ta
kama ta. Bilkisu ya kika zo gida?
Yana fadar haka ta gano ko waye ta rufe fuskarta da
tafukan hannunta tana dariya. Ya ce ya kika rufe ido? Ka yi
hakuri dan Allah. Da kika yi min me? Ni dai na ce ka yi
hakuri na yi lefi. Nli ba ki yi min lefin komai ba, ba ka
hakura bha ke nan? Gaskiya ban hakura ba domin kin
wahalar da ni da yawa, kin san tun jiya nake nemanki? Ta
ce a yi dai hakurin dai. Ya kura mata ido ta yi saurin kawar
da nata shi ke nan na hakura amma kar ki kara,. Ta daga
masa kai. Ya ce ta ina zan fara ne bilkisu? Au haka za ka ce
ba ka hakuran ba ke nan? Ya yi murmushi to shike nan na
gyara Hanifa. Ya ci gaba da cewa, a gaskiya Hanifa tun da
Allah ya sa na gan ki kaunarki ta shiga zuciyata kauna ta
fisabilillahi daga ni har ke dai mun mallaki hankalin
kanmu, in dai Allah ya sa in amince a shirye nake na aure
ki amına ban san abin da yake zuciyarki ba ni dai kin ji
abin da ke zuciyata.
Ta fan yi shiru na wani lokaci sannan ta ce, Hakika
na gode da kaunar da ka gwadan ni ma kuma ina kaunarka
kamar yadda addinin mu na Islama ya uamrce mu damu
kaunaci junanmu sai dai kuma inda a ka samu akaisn ni ian
da wanda nake so hasali ma mun yi alkawarin aure a
tsaknainmu dan haka nake ba ka hakuri da ka je ka samu
37
kika ce ma? Ni na mance, ki macne da shi. ta harare shi, in
mance da shi fa ka ce ya yi dariya, to a yi min afuwa amma
abin da kike nufi ni ba shi nake nufi ba, to me nake nufi?
A'a mu bar dai zancen. Ya shiga marairaice mata har dai ta
ce ya ba ta lokaci za ta yi tunani, a kai sun dade su na hira
har ya gangaro kankaratunta ya ce shi ma kanwarshi tana
FCE a department din da take a karshe dai suka yi sallama.
Tana shiga gida a ka biyo ta da tulin kaya mamaki
ya kama ta tana ayyanawa ranta wannan mutumin Kila
kudin ne suke masa kaikayi ganin yadda yake facaka da su.
Ta sota mayar amsa da kayan amma kafin a gama shigo da
kayan tuni har ya tafi duk da haka ta kudurce in ya dawo za
ta mayar masa da kayansa da ta nunawa mahaifiyarta kayan
fada ta hau ta da shi daman kuma abin da ta zata ke nan.
Kwana uku a tsakanin Abdulzahir ya dawo ita har
ga Allah ta mance da shi ta mance da sun taba haduwa da
shi domin Mas'ud dinta kadia take so shi kadai ke
zuciyarta a ko da yaushe kai ita ko sunan mutumin ma ba
ta rike ba domin ba shi ne a gabanta ba.
Lokacin da ta fita suka gaisa ya bkuaci jina msarsa
sai ta diririce don maganar da suka yi ma a nan ta bar ta ba
ta sake tuanwa ba sai a yanzu sai ta tsinci bakinta ta furta
amincewa bukatarsa ba tare da ta shiryawa fadar hakan ba.
shi ko dadi ya cika zuciyarsa yana ganin nan gaba zai iya
shawo kanta. Har ta kai duk bayan kwana uku sai ya zo. A
hankali a hankali suka soma sabo cikin dan kankanin
lokaci suka shaku duk da ba wata maganar soyaya a
tsakaninsu har ta kại ga duk al'ummar gidansu sun saba da
shi musamman ansiba da Nusaiba har gidan yayyanta sai da ta kai shi amma kuma ta kasa bayyanawa kowa matsayinsa
39
a gare ta. Hutunsu ya kare suka koam suka ci gaba da
karatunsu a kulluma ddu'arta Allah ya karkato da Mas'ud
gare ta. Ya dawo suyi aurensu kamar yadda suka shirya.
Yawan zuwan da Abdulzahir yake gidansu har ya sa
suka saba da Huwailat don saboda nisan da ke tsakanin
unguwarsu 'Yankaba da makarantarsu ya sa ta dawo wa
gidansu Hanifa sai week end take koamwa gida. Sabo mai
karfi ya shiga tskaninsu. Ta kan yi mamakin abin da kawar
tata ta gaya mata dangane da alakar da ke tsakaninta da
Abdulzahir ita kam tana kallon su ne kawai, ta tabbata su
kansu zukatansu sun aksa amincewa da hakan balalntana
ita.
A duk fadin dinsu babu wanda 'yan department
Hanifa ta tsana ko kuma muc e ta tsani halayyarta irin wata
Zakiyya nasir. Yarinya ce me mutukar jiji da kai, da son
nuna isa kowa kuma ya yarda da halayayr ta ce girman kai,
dan haka ba sa shiri ko kadan. Kafin ta fahimce ta, ta kan yi
mata magana amma sai ta share ko ta amsa a dakile har dai
ta fahimce ta ita ma ta shiga share ta musamman da ta
fahimci ta raina mata kura ne tund a ta fahimęi yawancin
wadanda take hurda da su 'ya'yan amsu kudi ne. a koda
yaushe ka gan su su biyu. Wato ita da Aysa wace ta kasa
fahimtar kawarta ce ko'yar uwarta ce domin shakuwar
tasu ta kai inda ta kai, sai dai abin mamaki sam halin
Zakiyya da Aysa ba daya ba ne. Aysa akwai saukin kai ga
ta da karamci duk da ita ma da alama 'yar masu halin ce
sukan dan gaisa da Hanifa ko dayake lefin Zakiyya ya so
ya shafe ta tana ganin duk ‘ya'yan masu hali fadin ran tsiya
ne da su, wannan dalili ya sa in ba ta kure ba ba ta yi mata
magana. 40
kwata ba Nu shirya mata ba dan haka kan Galibai ya fи
A want yanme an ytmunn test waeee kwatienll d vake Zakiyya yarinya ce me mastiar kokari nai Лунн и bukact taimakonta duk da itu me ba baya by ce bn Zaklyya
Rudundune
ta
da
rattabo
niyyar
mata amsoshin tamboyin a paper t
akardar ta fadin
ta eilla wa Aужи дbin auisayi NAİ idon invigilator dat-dui kan cinyar Hanita a dar-dal lokacin
faa paper ya budn
yu
kai
ya
kan Hanifa yu Karaso daf da tt yu
wanda ga abin dake ciki ya kalli Hanita
ya eillo jikinta
mikr,
fikinta
ke Bari ya ee, na kama ki sat ki nuna wanda
Nitm na tawa tu shijga ba shi hakuri amma ya Ki ya ma Kwace takardarta ya soke ta ya umarce ta da ta fita ta tabbatar kalli Zakıyyn ta ga
da ta yi asmar waman test din. Ta
ta janyo ta fauke kanta kammar ba tu sitn abin da
Aysa mata ba, haushi ya dacla kama ta ta kurna kalli
San Hanifan ti pa gaban daya ta rude ta yt sranda kawai tun da ta
kanta. ta gane ita a kai niyyar jefawa abin ya facda
ko dan
Hanifu
mutumein
ta ayyanawa
da zuciyarta ba za ta nuna Aysa ba ta ke gwada mata ummm ya zama dole ta nuna Zakiyya ko dan albarkacin izgilancin da take gwada
shayin
mata. Ba ma wai don abin da ta janyo mata ba, ba tare da komau ba ta nuna ta duk da dai da fari ta so ta musn wannan
ya
abu da ya faru shi ya janyo suka fadi a subject din sai shekara mn zuwa su maimaita wannan hukuncind a
aka
sassauci
yi musu ke nan a matsayin Malamin ya yi musu ke nan.
Tun daga lokacin gaa mai tsanani ta dada shiga tsakaninsu daman kuma tuntuni Zakiyya na jin haushin Hanifa saboda kafin zuwanta ita da wata 'yar kabilar Ibo su suka fi kowa Kokari a ajinsu amma da zuwan Hanifa ta
41
doke su a 6angaren Hanifa abin da ya fi ba t ahaushi shi ne Zakiyya yadda ta dauki gaba da ita duk da sanin cewa ita
ta janyo mata wanan abu dan haka take ganin ita ba ta ji haushinta ba sai ita ce za ta dau gaba da kiyayya ta dora
mata, gaba dayansu daga ita har Aysan ta hada ta watsar da
su kallo ma ba su ishe ta ba.
Hanifa da Abdulzahir sun samu kimanin watanni
bakwai suna tare a duk lokacin da ya bijiro mata da
maganar soyayya ta kan datse shi shi kuma ya ci gaba
dajuriya don ya san me nema yana tare da samu har kuma
wannan lokacin babu Mas'ud babu labarinsa. A 'yan
kwanakin nan Abdulzahir ya matsa mata dangane da
maganar aurensu, ya kan nuina mata wanda take tsananin
kaunar da yana son ta yadda take son shi ai da tuni ya dawo
sunyi auren. Da yake zancen duniya ba ya buya tuni yia
samu labarin abin da ke wakana saboda haka yake kara
karfafa gwiwa kila rabonsa ce a duk lokacin da ya yi mata
complain a kan hakajn takan ji haushinsa tana ganin yand
so ya yi mata fatan tsiya ne, dan kwanaki har fada suka yi a
kan ya ce yana ganin yaudrar ta kawai yake yi shi ya sa ya
ki dawowa sai daga baya suka shirya.
Yau ranar juma'a bayan an yi sallar isha'I Malam
ya yi kiran Hanifa zuwa falosna ta iske umma a ciki tana
ganin haka jikint aya yi sanyi ta samu gefe ta zauna. Bayan
'yan nasihar da ya yi mata ya sanar da ita iyayan
Abdulzahir ne suka zo neman aurenta, shi ne ya kirawo ta
ya ji ra'yainta. Wai ai ji ta yi kamar an soka mata mashi a
kirji a diririce ta ce Malam me ka ce? Ya ce abin da
kunnanki ya jiye miki. Bakinta na rawa ta ce dan Allah
Malam ka yi ahkuri shini ka mance da maganar Mas'ud ne?
42
ya ce na mance sai yanzu da kika tuna min fitsararriya, to
bari ki ji tuni na share maganar wannan yaron daga zuciyata na edai kyale ki ne har Allah ya fito miki da wani
wanda na yaba da nutsuawrsa ga shi ko Allah ya amsa
addu'ata ni da kaina na yi bincick na tabbatar da yaron
nagari ne ya fito daga uzri`a tsatatacciya ni yanzu ba wai ra'ayinki nake nema ba na kiraow ki ne in fita hakkinki na
sanar da ke in kuma kin ki wallahi wallahi kin ji na rantse
zan ahda ki da duk wanda na yi ra'ayi daman dan na yi
alkawari zan ba ki zabinki ne amma tun da kina son yawo
da hankalina zan yi maganinki.
Cikin kuka ta ce dan Allah Malam a aika gidan su
Mas'ud din a ji abin da iyayansa za su ce 'wallahi Malam na
sna yana so na..... ba ta karasa ba umma ta daki bakinta
cikin fada ta ce, to fitsararriya tun da kin fi mu sanin abin
da ya kamata sai ki gaya mana abin da ya kamace mu mu
yi, in ban da ma shashanci kin taßa ganin inda mace ke
jiran namiji ko ko kin taba ganin inda iyayan mace ke zuwa
neman aurenta ga dangin mijinta? Wato sai mu
kwadayayyu ko. Su iyayan nasa inda da gaske suke ai ko
da baya nan sa iya zuwa su zartar da wata magana me
kwari, shin wa kika ga ya zo?" ni ina ganin Malam kai
kake mata sako-sako, shin ta fi 'yan uwanta ne ko ko su sun
fi ki ladabi da biyayya ne? daman ni tuntuni na tsani
karatun nan na ce ka aurar da ita tuntuni ka ki kai kana
ganin yarinya ce me ladabi to ga irin karatun taurin kan da
ta yi yo mana nan, kai fada dai sosai har sai a Malam ya
dakatar da ita, a karshe a ka ba ta zabi ko Abdulzahir ko
kuma ya hada ta da duk wanda ya ga dama.
43
Da da daddare ita da Huwailat suna daki Huwailat
na kwantar mata da hankali duk abind a ake ciki ta sani ta
shiga yi mata nasiha da ta bi iyayanta cikin kuka Hanifa ta
ce wallahi Huwaila ba wani abu ya fi dagan hankali ba irin
haliln da Mas'ud zai riski kansa mutukar ya zo ya tarar na
yi aure, kin san dai irin kaunar da muke wa juanmu, ni na fi
tausaya masa fiye da kaina, shin yaya zan yi da alkawarin
da muka daukarwa junanmu? Ta ce a gaskiya Hanifa kin
kasa tsayawa gaskiya kin san dai Malam ko umma ke ko
mu nan kawayenki babu wanda ya taba sukar Mas'ud a
baya, tun da ko kika a kowa na ba ki shawara ki hakura da
Mas'ud ki rungumi Abdul a gaskiya ina ganin kamar
yaudrar ki yake yi inba jhaka ba ya za a yi ya kyale ki ba
wani bayani ko shi ko iyayansa, ni in ban da abinki da