An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ZUGIYA BА
TA DA KASHI
NA
ZAINABJKABIR BIROMAN
(Mrs. Sunus Sani Briscoe
ZUCIYA BA TA DA
KASHI
TOOS
1
NA
utzduok s I y botap
ZAINAB KABIR BIROMAN
(MRS. SUNUSU SANI BRUSCOE)
Copyright Zainab Kabir Biroman
Hakkin Mallaka (M) Zainab Kabir Biroman
AN FARA BUGAWA
2007
Printed By Al'amin Bookshop
Printing& Publishing Company
ИДМОRIB R156 S/Titin Mandawari
nurikano State
G.S.M. 08044114269
2
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) me kowa me komai. tsira da aminci su tabbata ga manzon Annabi Mohd. (S.A.W).
Ha, kullum ina me dada godewa mahaifana tare da illahirin zuri'armu baki daya "ISA MEKARA MISKI FAMILY" dama faukacin zuri'armu da ke unguwar ZANGON BAREBARI cikin Birnin kano dama daukacin
'yan uwa na nesa da ke tushenmu na usuli a can Jahar
Barno (MAI DUGURI) Ubangiji ka sa da fuskokin mu da alkhairi.
SADAUKARWA
Wannan Sadauakrwar ta ku ce masoyana masoya littattafai
na wadan da na gansu da wadan da muke zumunci da su ta
waya, kai da ma wadan da ban taba gani ba Alkhairin Allah
ya isar muku bani da bakin da zan iya gode muku fata na Ubangii ya sada fuskokinmu cikin JANNATUL
FIRDAUSI (Amin).
TUKWICI
Ga 'yata ta kaina diyar mutanen Jos, (nabila Sadi bala Jos,)
Allah ya raya mana ke bisa turbar Islama, ya kuma bar
mamanki sadiya kabir Biroman tare da Angon Karni Mohd.
Sadi bala Jos.
Haka kuma, Tukwici ne dai ga dana na kaina:-
Mohd. Sabi'u Daura kai ma Allah ya bar mamanka
Maryam Kabir Biroman tare da Angonta Sabi'u Daura.
3
BAN MANCE DA KU BА
Murjanatu Dr. Sa'ad Usman (Sakrin jere) yar muta
Isaduna garin 'yan boko, 'yar da ta san girma da mutuneı.
rame da:-
Maryam Kaka yale (CCommissioner of Education) Borno
State, yarinya me tushen usuli Diyar Ma'abota Karamci da
girma, taken ku ke nan mutanen Maiduguri.
GARGADI
Ban yi wannan littafi domin wani ko wata ba, ban
kuma yadda a yi amfani da shi ta kowace siga ba ba tare da
izinin marubuciyar ba.
BUGAWA A NA'URA
Mubarak Ahmad Kurawa
Yolawa Computers& Communications
Email: almubrak@yahoo.com
G.S.M: 08025475907,064936815
4
TUSHEN LABARI'
Sohuwa ce 'yar kimanin shekara saba'in da foriya. Twankan tarwafa kyakkyawa da kyaı diri. Da gani ka
san zamanin kuruciyarta ba karamar kyakkyawar a
zo a gani ba ce. A gefenta dalibai ne ke zagaye da ita galibi
matan aure to sai dai akwai tsirarun masu Karancin shekaru
(matasa) a yau darasin nasu ya ta'allaka ne a bisa illolin
da SON ZUCIYA ke haifarwa. Tsohuwa lya ta ci gaba da
yi musu bayani tare da karanto musu hujjoji daga Alkur'ani
mai girma hade da Hadisan Manzo (S.A.W).
"Mu yi kokari mu tsarkake zukatanımu kada mu bari
ta rinjaye mu abin da ka kai mu ga halaka, hakika zuciya za
ta iya kai mu ga aikata munanan ayyuka. Ya 'yan uwana
Musulmi ZUCIYA BA TA DA KASHI, mu yi kokarin
karya ta a duk lokaci da ta yi kokairn kai mu ga halaka.
Saboda Allah abu nawa ne zukatanmu kan ingiza mu ga
aikatawa? Galibi abu ne marasa kyau a yawancin lokuta ba
za ka taba samun nutsuwa ba ba tare da aiwatar da abin da
take so ba, bijirewa hakan ko sai mai karfin imani da ya yi
kokarin yaki da zuciyarsa har ya zamanto me iya lankwasa
ta.
Son zuciya dai bacinta duk wanda ya biye mata
hakika yana tattare da wahala, in ba ka yi da gaske ba
zuciya na iya kai ka ga samun makoma mara amfani duniya
da lahira. Shin ina ribar rayuwar? Me zai hana mu yi
kokarin karkata zukatanmu ta hanyar dora ta bisa turbar
gaskiva?"
Tsohuwa lya ta numfasa gami da runtse ido sannan
ta ciza lebe alamar tunano wani abu me faci, nan da nan ta
fita hayyacinta ta shiga kukan zuci salar da ta tuna da illar
da zuciya ta yi mata. Abadan abidina ba za ta taba mance
da musibar da zuciya ta sanya ta a ciki ba, ba za ta tabą
gushewa ba har sai tana me bakin ciki gami da nadamar
halin da zuciya ta sanya ta a ciki ba muddin rai za la
dauwama ne cikin neman gafarar Ubangiji domin shi ne
Gafurur-Rahim.
Tun tana kukan zuci har ba ta san sa'ar da ya kwace
inata ba ta shiga rera kuka me tsuma zuciya irin kukan nan
ne me nuni da al'amun nadama a tattare da bawa. Halin da
tsohuwa Iya ke kasancewa a ciki ke nan a duk sa'ar da ta
tuan da hakan.
Ba faya ba, ba biyu ba ilahirin daliban da ke zagaye
da tsohuwa Iya sun sha riskarta cikin wannan hali a du
lokacin da ta suka riske ta cikin wannan hali sukan shiga
damuwa gami da neman dalili. "Wannan sirri ne tsakanina
da Mahalicci." Amsar da take ba su ke nan a duk lokacin da
suka nemi sanin dalili, to sai dai a yau tsohuwa Iya ta lura
da halin da dalibanta ke ciki kusan ya fina ko yaushe. Sun
shiga damuwar halin da take ciki kwarai da gaske.
Cikin tausasshiyar murya me ban tausayi tsohuwa
lya ta ci gaba da cewa, "Abadan abidin ban taba zaton
akwai wata rana da zan iya tona wani sirri dake adanea
zuciyata ba wanda ZUCIYAR ce dai ta yi silar faruwar
hakan. Muddun rai ba zan taba mance da wannan abu ba, to
sai dai adana wannan sirrin ab shi ne mafita ba, a yau ya
zama dole na bayyana muku wannan abu da ke adanea
zuciyata, ko dan al'umımata ta fafaka ta ilmanta daga illolin
6
da bin son zucıya ke haifarwa. Hakika duk mutumin da
yake so ya wanye da duniya lafiya to ya yi Kokarini Kauracewa abin da zuciya ke so mutukar ba na alheri ba ne.
Ya 'yan uwana Musulmi! kar fa mu manee
ZUCIYA BA TA DA KASHI. To yaya Dan'adam me jini
da tsoka, bargo da kashi, halitta mafi daraja cikin halittun
Ubangiji zai kaskantar da kansa ya zub da kima da darajar
da Ubangiji va yi masa ya soyu ga son zuciya har ta kai ka
ga sabawa ko bijircewa Mahaliccinka.
Ku yi duba ku nutsu da kyau, ku tattara hikima da
basira gami da hankalin da Ubangiji ya buwace mana (abin
da ya banbanta mu da Dabba) a bisa wannan labari nawa da
nake son ba ku, abin da ya faru ya kuma gudana tsawon
shekaru masu yawa da suka gabata.
7
***** ***** *****
Vana tsugune a soron gidansu kan 'yar karamar kujeraa Tta tsuguna ta hada kai da gwiwa idanunta cike da
hawaye wanda suke barazanar zubowa, duniyar ta yi
mata zafi dalilin rabwua da masovinta. Mas'ud da ke
geenta a tsaye hannunsa a saye cikin aljihun wandonsa ya
tsura mata idanu ko kafan ko da wasa ba ya kaunar ya a
ranta a bace ballantana har ta kai ga zubda hawaye, j ikinsa
a sanyaye ya taso daf da ita ya tsuguna a gabanta ya sa
hannu da zummar ya dago fuskarta sai kuma ya tuna
haramcin hakan dan haka ya sauke hannayensa muryarshi a
sanyaye ya ce. "Hanifa ki daina kuka wannan tafiyar da zan
yi ba ita ce rabuwarmu ba shekara daya kamar kwana daya
ce, in dai muna da saurna numfashi, duk kin bi kin damu
kanki har kina neman ki sa na karaya, kin san ko kadan ba
na Kaunar na bacin ranki. Da ina da iko ba zan yarda iniyi
wannan tafiya ba sai tare da ke. To kin san ko a al'adan ce
ma bai dae ba ballantana a Addinance. Tun farko na nemi
amincewarki a faura mana aure kin ki kin ce sai kin gama
karatunki wannan tafiyar wata dama ce nuka samu domin
mu tsaya mu fuskanci abin da ke gabanımu ko ma samu
kyakkyawan sakamako, kin ga lokacin da zan dawo lokacin
kin karasa karatunki da na dawo sai a sha biki ko ba haka
ba Princess.?" Ya fada yana murmushi. Ita kanta kalaman
nasa sun mata dadi domin ta tabbata Mas'ud na mutukar
Kaunarta abin da take zato ba mai yiwuwa ba ne a gare shi,
duk da haka dai sai ta ce, "Ka gane ko Mas'ud ni ba war
tafiyar ce ba na so ba, a'a tunanina daya kar ka je ka hadfu
8
da jajayen fata ka sanuya tunaninka a kaina, mka ana ka yaudare ni. Ni ina nan ina jiran ka kai kana can ka kama Wata.... Ya katse ta da cewa haba dai Hanifa ki daina
wannan zan ce ke ko a mafakri kar ki yi zaton haka za ta faru har abada, ke kadai nake so ba zan taba yaudararki ba
soyayarki a gare ni a jinina take, domin ta wannan Gangaran ma ni ke nake ji. na san mata zuciyar ku raunanniya ce kar wani ya zo ya kwace min ke." Tana
girgiza kai ta ce, "haba Allah ya sauwake. ni wane namiji
ma na ta6a saurara in ba kai ba, kai kanka shaida ne ba
kuma na tunanin ko nan gaba wani da namiji zai ja hankalina." Ya ce ke dai um um. Ta ce Allah kuwa alkawari fa. Ta ce Alalh na dauka ya sha kunu sosai scriously. Ta girgiza kai ya fito da wata farar takarda ya mika mata hade da biro ya ce ga shi nan ki rubuta promise da kika dauka ni ma zan rubuta.
Ta sa fan kyakkyawan hannunta ta yi rubutu kamar haka. “Ni Hanifa Sa'ad na yi alkawari ba ni da wani miji a
rayuwata sai masoyina Mas'ud Khalil." Ya karba ya karanta yana murmushi shi ma ya rubuta kamar yadda ta rubuta kana ya ce bari in zan tali Ammar sai ya shigo ya sa hannu sai ya zame mana shaida kuma duk wanda ya saba wannan alkawari a hukunta shi. ta ce har yanzu kana shakku a kaina ke nan? Ya ce a'a ba haka ba ne shaida ce dai. Ta harare shi ta ce ka ji da shi da majidashidako suka yi dariya a lokaci faya.
Tsawon lokacin da suka fauka kowa na kokarın jadedada
alkawarin
Kaunarshi ga fan uwansa tare da dada jaddada da suka dauka. Misalin Karfe goma da rabi na dare Ammar ya leko zauren yana hararar abokin nasa ya сe
kai dan iskanci sai ka bar ni a waje sanyi yana ta ka dadin
ce ko ka mance ka bar mutum a waje? Ko da yake ku
kun hadu mancewa kuke da kowa sai kanku. Mas'ud y
kalle shi ya ce, fadi kanka tsaye ka san Allah wallahi na
mance tare muke ko da yake laifinka ne kai na ce ka shigo
ka ki, wai ka shigo dga baya ga shi nan da ka ga uwar ban
ka shigo. Ya ce madam ba ma gana ko? Zai dai tafi ya bar
ni tare da ke. Tayi murmushi ta ce, "to ai kai ne ba kaj
mana sallamar kirki ba daga zuwa ka fara yi wa mutum
fada. Ya ce, Au haka ne ba ki ga laifinsa ba na shanya ni da
ya yi a waje sai na wa za ki gani?" to ai ka san so so ne
anma son kai ya fi. Ya ce shi ek nan zan rama ne. ta ce to
ka I ahkuri amıma kar ka kuma yi mashi fada. Sun dan taba
hira sannan Mas'ud ya danka amanar masoyiyarsa ga
abokinsa amininshi Ammar shi kuma ya yi alkawarin rike
ta da gaskiya, ya nuna mata duk abin da take bukata ta sa a
kirawo mata Ammar ta sanar da shi ita dai ta amsa ne
kawai amıma ko akfan ta san ba a yi musu tarbiyya da haka
ba, ta san hakan na iya rage mata daraja a idonsa kai da ma
abokin nasa.
Ya ce in Allah ya kai shi lafiya zai neme ta a wuvan
Ammar kai da ma duk lokacin da yake bukatar zantawa d
ita. Da zai talī aka ftowa da Ammar takardar da alKawarin
da suka dauka ya sa hannu a matsyain me yin shaida duk
dai sun sha tsiya kafin ya sa hannun. In a son ran Mas'u
ne ta yi mishi rkaiya kashegari zuwa Airport amma ya sa
ba abu ne me yiwuwa ba saboda tsananin mahaifinta ba
taba bari ba, ya san halinta ita ma ba za ta taba zuwa ba ya
san ta akwai ta da kawaici da kunya dole ya hakura suka i
sallama. 10
Misalin Karfe goma sha biyu na dare Hanifa ta kasa
bacci tunanin masoyinta kawai take yi wannan tafiyar da
zai yi gani take kamar shi ke nan sun rabu, a hankali a
hankali ta gangaro farkon haduwarsu kimanin shekara daya
ke nan.
Da misalin karfe tara da rbai na daren ranar alhamis
Hanifa na tsaye a gefen titin Bata tana jiran motar da za ta
kai ta bakin asibitin Murtala wanda daga nan za ta shiga
motar Unguwarsu ta kai kimanin minti talatin tana jinra
Hiace domin tana mutukar tsoron shiga tadi musamman
cikinw anann daren amma motocin kamar hadin baki babu
su in ma Hiace din ta zo za ka tarar a cike take ta gama
gajiya likis ga tsananin tsoron da yake kama ta ganin
jama'a sun soma dauke sahu. Ba abin da ta fi t soro ma irin
fadan mahaifinta domin ya tsani su kai magariba ma a waje
ballantana wannan uban dare da ta kai ga ba mkota ba
alamar ta ilal dai motocin gida da suke gilmawa jeti-jeli. Tafiya tsaknain bata zuwa unguwarsu Mandawari cikin
titin 'yar Mai Shinkafi tafiya ce mai tazara balantana ta ce
za ta tafi a Kasa. Ba nisan tafiyar take ji ba ilal awannın da
za ta kara batawa kafin ta kai gida dan haka take ganin
gwanda ta jirkitna ko Allah zai kawo mata mota ta shiga ko
ta isa gida da wuri.
Ta tuno makasudin fitar ta da har ta yi wannan dare
da yammacin ranar ne kimanin Karte bivar ta baro gıdansu
zuwa gidan Kawarta ko ma mu ce ammiyarta wato
Huwailat domin sun shaku tun farkon shigar ta secondary
suke tare kimanin shekara biayr ke nan dalilin zuwa gidan
nasu da ke `Yankaba shi ne dan ta dubo jikin aminiyar tata
saboda rashin lafiyar da ta sha fama da ita duk da dai ta je
"
ta tarar da ita jikin nata da sauki har ta yi alkawarin za ta je
school sati me zuwa, a tsaminaninta awanni biyu ya isa ta
je ta dawo sai ga shi ba ta isa gidan ba sai kimanin Karfe
shida da mintina, ta so ta jiyo tun a lokacin sai uınmi babar
Huwailat ta bukaci ta zauna driver ya dawo ya kai ta ba za
ta iya musa mata ba saboda girmanta da take gani ta zauna
amına ba dan ta so ba har sai da ta kai karfe takwas da rabi
sannan driver ya dawo ba tare da motabha domin ta lalace
masa a hanyarsa ta zuwa gidan dole uimmin ta Kyale ta ta
taho. Ta kai kimanin minti ishirin kafin ta samumotar bata
kan ta iso bata tara ta yi, ta yi tsayuwar akalla minti talatin.
Ta yi ajiayr zuciya gami da tsakin jin haushin rashin samun
mota
Ba tare da ta lura ba sai ji ta yi ana fan jan gyalenta
a razane ta waiwaya sai ta ga wani matashi ne da alama a
buge yake. Ta daure fuska lafiya Malam cikin magana ta
mashaya ya ce lafiyar ke nan yana son magana da ita ne. ta
yi tsaki dai-dai lokacin wani me mota ya zo shigewa har ya
yi gaba sai kuma ya yo ribas ya juyo, ita dai ba ta zata ba
sai gani ta yimutum uku sun sa ta a tsakiya dag ganinsu ka
san ba na zabe. Ta dada tsorata ga titin ba mutane sai jefijefi wasu kan shige ta rasa yadda za ta yi tana neman
hanyar tsira sai ta ga wani matashi daga cikinmotar ya fito
ya nufo shi ya tsaya daf da su ya ce ku lafiya k uka tsare
yarinyar mutane? Suka ce lafiyar ke nan ka tafi ka ba mu
waje. Ya yi ya yi su bar ta ta tafi suka ki ya tabbatar dai ba
yadda zai yi da su domin ko da kKarfin tuwo ya-ce zai Rwace
ta ba zai iya ba sai ya sauya dabara ya ce ya zaro naira dari
biyar guda uku ya ce ga wannan a sha lemo nan da nan
suka karba suna kare ka Oga suka tafi abinsu. Ta yi ajiyar
12
zuciya domin gaba faya ta gama rufewa ban da Allah ya kawo wannan mutumin ya cece ta da ya za ta yi? ta san komai yana iya faruwa. Ya kalle ta ya ce ki yi hakuri al'umma ce ta lalace sai dai addu'a. ta ce uhm kanta na sunkuye ko za ki zo mu je in rage miki hanya? Ta girgiza
kai na gode ma da wannan taimakon da ka yi min. kina
ganin na tafi na bar ki a wannan wajen ki dubi yanayin
wajen fa bai kamata a ce yarinya me mutumei kamar ki ta Isaya wajen nan cikin wannan daran ba, ki zo mu tafi ba
zan cuce ki ba har ga Allah na yi niyyar taimaka miki ne.
Ta ga dai ba wata mafita ila ta bi shi ita kanta ta san hatsari
ne zamanta a wannan wajen kuma ko ba haka ba mutumin bai mata kama da mutanen banza ba.
Tafe suke cikin motar tana zaune a gefensa. Tunda
ta shiga ta sunkuyar da kanta tana tunanin fadan da za ta je
ta tarar a gurin mahaifinta, abin da ta tsana ita kam gwanda
ya dake ta da fadain da zai mata, ba ita ba ma Ummanta
ma ta janyo mata. Ya kalle ta ta gefen ido ya ga hawaye na digar mata ya ce, "Ki daina kuka aikin ga ba abin da suka
yi miki ko.?" Ta ce, "e." ya ce, "to me ya sa ki kuka?" abin maki sai ta samu kanta eda zayyana nasa abind a ke
zuciyarta, wato halin da za ta riski mahaifinta a ciki. Ya ce,
"E to aikin ga baban naki yana da gaskiya domin duk uban
kwarai dole ya tarbiyyanci'ya'yansa yadda ya dace, amma Insha Allahu babu abin da zai maki." Sun kawo dai-dai
Mandawari ya ce wace kwanar za mu bi? Ta nuna masa kwanar gidan Aminu Ado, haka suka dinga tafiya tana nuna mishi hanya har suka kaow unguwarsu Yar Maishinkafi
duk da cikin dare ne hakika ya yaba da tsarin unguwar tamkar ba cikin gari ba. Tuntini yana mutukar son unguwar
13
domin ya san unguwa ce me dadaddan tarihi, Allah ne ba
sa ya taba zuwa ba sai wannan karon. Sun zo daf da kofar
gidan ya yi parkign ta kai hannu za ta bude kofar sai la ja
doguwar ajiyar zuciya gami da rufe idonta a rude ya ce
lafiya? Ta kale shi akwai ta ce Malam wato Babanta da ta
hango a tsaye a kofar gidansu ya girgiza kaiaay ce ba
komai ki je ni na san abin da zan ce masa. Tana zuwa daidai kofar gidansu ta sa kafa za ta shiga ciki sai ji ta yi ya
daka mata tsawa ba shiri ta juyo jikinta na rawa ta tsuguna
ganink Malam a fusace ya ce dan Ubanki daga ina kike?
Bakinta na rawa ta fara ba shi amsa cikin in ina be fahimci
abin da take nufi ba har mutumin ya karaso. Ya kalle shi
fuskarsa daure ganin haka shi kuma ya dan rankwafa
Alhaji barka da dare. Ya daure ya amsa illa dai fuskarsa na
daure.
Ya kalle ta ya ce, tashi ki shiga ciki mutuniyar
banza. Da sauri ta mike har tana kokarin kifawa duk dai
nutumin yana kallo yana tsugune ya fara yi wa Malam din
bayani, dan dai ya fitar da ita daga zargi har karya sai da ya
Kara sai a nan Malam ya saki fuskarsa yace, to to na
fahimta ka sna duniyar ce ba gaskiya kana kula ma ya aka
cika ballantana ka yi sako-sako shi yaro ai sai da lura kana
yi kana sa shi a hanya. Al'ummar ce ta gurbace yanzun nan
sai a bata maka yaro a cuce ka. Na gode maka ka ji yaro
Allah ya yi albarka, me ye sunanka ne.?" Cikin ladabi ya
ce, Mkas'ud. Daga nan dai suka yis allaına ya rako shi har
gindin mota yana yi masa godiya, daman shi abin da ya fi
Gata masa rai ganin ta da ya yi da wani namiji a cikin mota
daya kuma cikin wannan dare shi ne dalilin dada fusatarshi,
ko da ya shiga gida bai mata fadan da ta zata ba illa dai ya
14
a
yi mata nasihar ta dada kula da kanta gami da kame kanta
da tsayawa matsayinda Allah ya ajive ta, a karshe ya
gargade ta in dai magariba ta kawo kai kowace unguwa ce
dinga hakura da ita. Ita ma umman nata ta dada jan
kunnenta domin gaba daya daga ita har maigidan nata
mutane ne masu kula da tarbiyyar 'ya'yansu gami da
kokarin kaucewa duk wani abu da zai taba mutuncinsu, ko
su ko 'ya'yansu, ko kuma wani abu da zai janyo musu abin
kunya a idon jama'a don haka ya ransu sun tashi cikin
ingantacciyar tarbiyya.
Ranar litnin Hanifa da Huwailat sun hadu a school
ta shiga ba ta labarin abin da ya faru bayan tawowarta daga
gidansu ta ce ki ce Allah ne ya kiyaye ki wallahi kuwa dan
da ba dan mutumin ba ban san yadda zan yi ba, ba ki gan
shi ba kyakkyawa da shi ga shi da kirki. Ta shiga koda shi
Huwailat ta ce, to ni kina ta zuba ba ki gaya min sunansa
ba. ta ru nutse ido gami da dan tsaki kin san Allah sam ban
san sunansa ba. abin b haushi ma ba ki ji aydda na damu an
sake ganinsa ba ga shi ban san sunansa ba ballantana na san
inda yake. Ta ce me ya sa kika damu ki sake ganinsa?" ni
kaina ba na ce ga dalili ba haka kawai na riski kaina da son
sake ganinmutumin.
To ko dai sonsa kike?" Ta kalle ta da sauri, Kai
haba dai daga na fadi haka sai ki nemi ki yi min sharri. Ta
yi dariya, sannan ta ce, dole ne yi zaton haka tun da na san
halinki na kin kula samari ko kin mance irin mitar da nake
sha a kanki in kin ganni da wani guy din ke ni ba ma zato
nake ba na tabbata wannan mutumin ko wanene Kaunarsa
kike yi zan so na ga wannan me sa ar, lallai yau su Afiya za
sha labari. Daga yau dai kin bi sawunmu baba zancen vi
15
mana mita. Ta shiga yi mata shegantaka kala-kala daman a
ta gwanar surutu.
Ita dai Hanifa ta yi shiru tana nazarin maganganutan
wanda da alama zancenta gaskiya ne dan a daran jiya ma
kasa bacci ta yi saboda tunaninmutumin. Tana dago kanta
da zummar yi wa Huwailat wata tambaya sai ta hango
ayarin yan group finsu wato su Afiya Ado, Rashida Tata.
Binta Mukhtar da dai saurnasu da sauri ta bar wajen dan ta
san in ta sake suka iske ta kashinta ya bushe a kodayaushe
ita ke musu mitar kula samari.
Kashegari da yamma ta kitmsa jikinta cikin atamfa
Charas yeluwa da ratsin kroe kayan sun amshe ta ta fito fes
abinta duk da ba wata