hana ku fuskanci juna.
"Yarinyar nan tana kaunar ka Waheed ka san ni
abokinka ne kana dan uwanka ba zan taba tura ka ga
abin da zai cutar da kai ba."
Maganganun nashi sun dade suna tasiri a
zuciyarshi, kwana da yini yana tunanin abu daya, anya
kuwa yarinyar nan za ta so shi har ma ta kaunace shi
musamman idan ya yi la'akari da irin abubuwan da suka
wakana? Tiryan-tiryan ya dinga tunano musabbabin
rikicinsu, kana babban abin daya dada hura wutar tsana a
tsakaninsu, lallai kam shi ma da nashi lafin, kai shi nema
ummul aba'isi, dole ne yarinyar ta tsane shi har ma ta rike
shi a matsayin gagarumin makiyinta, to amma ita ma akwai
abubuwan da ta yi mishi, kai na rashin kyautawa duk
dahakan ya share ya nemi su fahimci junansu su zauna
lafiya, to amma ta turje har zuwa lokacin da ya gama
yanke kauna da ita samakon cin amanar da ta yi mishi,
babu zancen sulhu a tsakaninsu.
A ko da yaushe takan kasance cikin damuwa da
rashin sanin takamaiman matsayinta a zuciyar mijinta.
Yayin da wutar kaunarshi ke azalzalar ta ga dukakn alamu
Sameer din ya kasa samun kan abokinsa, ta la'akari da
yadda yake mata kwane-kwane ta riga ta fahimta yana
kokarin 6oye zahirin abin dake wakana a tsakaninsa da
74
ZAINAB KABIR BIROMAN
wane irin zama ka yi da yarinyar nan? Shin menene ba ta gani ba daga gare ka? Tsana da tsangwama da nuna halin ko in kula duk kai ne amma a hakan ta jure ta yi hakurin
zama da kai har ma ka sanya ta cikin damuwa sakamakon halin da kake ciki, in har ka amince ta nuna
sha'awar ta taimaka....
"In kuma ban amince ba fa?" Ya tambaye shi.
Kallon shi yake ba shi da niyyar tanka masa, ya ci
gaba da fada, "In har sai yarinyar nan ce za ta yi silar
fitar da ni daga wajen nan to in dauwama a wajen nan, ka
je ka shaida mata tun da kai dan sako ne." fada yake
gami da fadar zafafan kalamai a gare ta da shi kansa
Sameer din.
Shiru ya yi har ya yi ya gama be fusata ba, ya bi
shi sannu a hankali, daman shi ba ma'abocin fushi ba ne
da kuma cewa shi ya fi kowa sanin matsalar. Kwantar da
harshe ya yi yana yi masa nasiha gami da jan hankalinsa
a kan kyawawan lafuzza. Shi daman gwani ne wajen
tsara magana, bai gushe ba har sai da ya tankwarar da
zuciyarshi.
Ya ci gaba, "Na sani cewa Heedaya ta saba maka,
to amma mu dauka cewa kowane bawa ajizi ne Allah (S.W.T) ne kadai ba ya kuskure don haka sai mu yi mata
afuwa mu manta da abin da ya gudana. Abu daya ne nake so ka fahimta a wannan lokaci yarinyar nan tana yi maka kauna ta hakikatan, ba na jin in ba ta kaunarka za
ta shiga wannan halinda take ciki, ta damu ainun fiye da zatonka. Ka san lamarin Ubangiji babu abin da bai iyawa
73
ME GARI YA WAYA? 3
shi mai iko ne a kan komai a kuma lokacin da ya so, don
haka ba abin mamaki ba ne ganin ta riski kanta a wannan
hali. Kamar yadda ka sani ne kiyayya ta kan juye ta
zama soyayya, ko da yake ko can baya ban taba daukar
junanku a matsayin makiyan juna ba face dai wani dalili
da ya hana ku fuskanci juna.
"Yarinyar nan tana kaunar ka Waheed ka san ni
abokinka ne kana dan uwanka ba zan taba tura ka ga
abin da zai cutar da kai ba."
Maganganun nashi sun dade suna tasiri a
zuciyarshi, kwana da yini yana tunanin abu daya, anya
kuwa yarinyar nan za ta so shi har ma ta kaunace shi
musamman idan ya yi la'akari da irin abubuwan da suka
wakana? Tiryan-tiryan ya dinga tunano musabbabin
rikicinsu, kana babban abin daya dada hura wutar tsana a
tsakaninsu, lallai kam shi ma da nashi lafin, kai shi nema
ummul aba'isi, dole ne yarinyar ta tsane shi har ma ta rike
shi a matsayin gagarumin makiyinta, to amma ita ma akwai
abubuwan da ta yi mishi, kai na rashin kyautawa duk
dahakan ya share ya nemi su fahimci junansu su zauna
lafiya, to anma ta turje har zuwa lokacin da ya gama
yanke kauna da ita samakon cin amanar da ta yi mishi,
babu zancen sulhu a tsakaninsu.
A ko da yaushe takan kasance cikin damuwa da
rashin sanin takamaiman matsayinta a zuciyar mijinta.
Yayin da wutar kaunarshi ke azalzalar ta ga dukakn alamu
Sameer din ya kasa samun kan abokinsa, ta la'akari da
yadda yake mata kwane-kwane ta riga ta fahimta yana
Kokarin boye zahirin abin dake wakana a tsakaninsa da
74
ZAINAB KABIR BIROMAN
abokinsa. Tabbas ta riga ta sani ta tafka babban kuskure, kuskuren da ba lallai ne ya iya afuwanta mata ba.
Damuwar da take ciki da kuma rashin kwanciyar
hankali ya yi musabbabin tayar mata da ciwonta na asthma.
Wasa-wasa sai da ciwo ya kai ta kasa, ciwo kam ya
tasarımata kwarai da gaske bar ma wani lokacin
numfashinta yakan yi kokarin daukewa. Kai bai ma taba
tayar mata irin haka. Kai ba ka ce za ta tashi ba idan ya
motsa mata. Numfashi ne kan yi kokarin tsayawa cak, to sai dai duk da hakan babu wani kulawar da take samu daga
gurin mahaifinta, kai lallai kam Dadin nata ya yi fushi
ainun daita. Inda take dan samun kulawar ma bai wuce
gurin mahaifiyarta ba.
Wannan hali da ta shiga ya sa iyayen mijinta da 'yan uwansa shiga halin damuwa a ganin su ko menene ya
samu yarinyar mutane dansu ne musabbabin hakan.
Tun bayan da ya samu labarin rashin lafiyar matarshi daga wajen abokinshi ya shiga cikin damuwa,, shi kansa Sameer din ya sauya masa, tamkar ma ya fi damuwa da halin da take ciki fiye da shi abokinsa. Kai abubuwan suka taru suka yi masa yawa.
Abin kamar bai dame shi ba, abin mamaki lamarin
sai ya tsaye mishi, duk ta inda ya yi kokarin kau da abin a
zuciyarsa lamarin ya ci tura. A cikin kwanaki biyu sai da ya
tare
dada
da
sauyawa damuwa da fargaba suka dada bayyana a
shi.
Anya ko bai yaudari zuciyarshi ba idan har ya ce babu kaunar yarinyar a tare da shi abin dakake so shi kake damuwa da shi. Ya shiga damuwa a kan rashin lafiyar nan hakikatan, wanda yake fan samun labarin daga gare shi ya
75
ME GARI YA WAYA? З
dauke sahunsa, ko daman mahaifinsa da 'yan uwansa babu
mai zuwa inda yake,a bisa kashedin da ya yi musu domin
fushi kam ya yi da shi ainun. Galibin wafanda suke zuwa
gurinsa bai wuce surukinsa Abbansa da kuma abokinsa
kana danuwansa ba sai kuma wadanda ba a rasa ba
sakamakon dalilai na tsaro.
Zahirin gaskiya ya gama gano ta ya kuma gasgata
zatonsa so kam yana yi wa yarinyar saura dame ya sadu da
ita domin neman afuwarta, duk da cewa ya san lokaci ya
riga ya kure, ba shi da tabbas ga rayuwarshi ya kan tuna da
kalaman Samcer din, "Idan yarinyar mutane ta mutu shi ke
nan sai ka vi yadda kake so ka zauna ka mike kafa a
duniyar da babu afuwa a cikin 'ya'yanta."
A yau Sameer din ya zo yana neman afuwarsa.
"Nayi kuskure Sameer, na yarda na aminta da Kaunar
yarinyar nan a tare da ni ka taimaka ka sada ni da ita, ko na
sami sassauci a zuciyata duk da na san lokaci ya riga ya
Kure mana.
Daina fadin haka da yardar Allah mu ne da nasara.
domin ni na san abokina ba zai aikata wannan mummunan
aiki ba, kai dai abin da nake so ka gane, mu dauka cewa
jarabta ce ta Ubangiji da babu wanda ya isa ketare mata.
mu yi fatan kuma kaffara ce da shiriya a gare mu.
ABIN DA KA KI....
Vanas Zanayin da ta gan shi ya yi matukar itsorata ta ya rame ya
kode kai ya ma fita hayyacinsa, sai tarin Kasumba
kawai da ke fuskarsa. Kallon-kalo suka tsaya yi hawaye ne
76
ZAINAB KABIR BIROMAN
kawai ta ji ya zubo mata ganin yadda mijinta ya lalace kai ba ka çe shi ne gayen nan mai ji da kansa ba, (Rayuwa ke
nan mai kaskantar da Bawa a lokacin da ya daga kai ya ce shi wani ne), a yau alfahari da nasaba gami da tarin dukiya
ba su amfana maşa komai ba tun da sun gaza fitar da shi daga kangin rayuwar da ya fada. A yau ga shi dai bạ shi da
tabbas ga rayuwar da ake fangima da isa a cikinta.
Ya dago ta yana lallashinta, "Ki yi hakuri kowane
bawa akwai irin jarabtar da Allah yake masa, wannan ba
wani abu ba ne face jarabta ta Ubangiji, amma wallahi ina
nai rantsuwa da girman Ubangiji ban aikata wannan laifi b.
Bai Karasa ba ta rufe bakinsa, "Ko baka rantse da
girman Allah ba ni na san Abdul wannan ba halinka ba ne,
ban taba amincewa zuciyata za ka aikata wannan laifin ba,
haba kisa, hakkin rai ai ba abin wasa ba ne. bayan Allah ne
da kansa ya hane mu. Abin da nake so da kai ka amince ka
ba mu hadin kai da yardar Allah za mu iya bakin
kokarinmu wajen tabbatar da gaskiya."
"A'a." kai ya kada mata, "Ban cancanci haka ba
daga gare ki. haba! Mutumin da ya musugna.miki ya kuntata miki ya yi miki babara illa za ki ceci rayuwarsa, ni
na san na zalunce ki Heedaya na kuma san wannan abin
kike duba har kika kasa afuwanta min a yayin zamanmu. Ki yi hakuri ki je kawai komai ya faru da ni dai-dai ne. Abin da nake rokonki kawai ki afuwanta min...." nan ma bai
karasa ba ta datse shi, "ya isa Abdul ka bar tuna baya, ka bar tunawa da abin da ya shige sai dai mu roki gafarar Ubangijin ma kuma ina mai kaskantar da kaina tare da
neman gafarar kurakuran da na aiwatar maka. Hakika ban
77
ME CARI YA WAYA?
kyautamäka ba, ban kumarikemartibarida aure ya bamu
ba saitdaitda izinin Ubangijithäkan ba zai kara faruwaiba.
kuma 4ka fahimta a otkin shaanin rayuwarmu akwai
wadanda sükaso-su gurbata mana, sukaškuma thafa imu
husuma. ammasina yiaka:rantsuwa(dasgirman Allahotun
da mike in bayan abin da yasgudana attsakaninmu ban:taba
ko shaiawar eikata zinaba iballantana tharva kai ga faukar
ciki, abin man ya tsaye mia zuc...
Shi ma datse tan yayi,Na fähimta ki bar damun
kanki kin san rashin sani ba abinida be sawa, amma iko ya
kike nimime shaida. Heedayaına soskitun da ga ranar da
Allah ya fara dora idona a kanki, Allah shine shaidata а
kan hakan, don haka ina ımaittabbatar miki ina miki kauna
ta gaskiya. (Iko sai Allah, dama Hausawa na cewa,Duk
abin da ka kiovatanana zaka zoikaso shi.")
Duk wani hadin kai du süke bukata ya ba su. harna
tana ganin abin zai zo musu da sauki sakamakon bayanan
da-suka da suka samu daga gare shi,tbabu wanivabu da ya
Goye mata daga abubuwan da suka wakana:a tsakaninsa da
Tahir da kuma marigayiya Farida.
Daki-daki ta tsara yadda:aikin nasu zai wakana tare
da tallafin abokiyar aikinta Barrister Maijidda Sharif. Cikin
nutsuwa da hankali suke bin komai, sannu a hankali-sai ga
shi-sunata samun masara sun kammala ida duk bayanan da
zai taimaka musu.
Tashin farko Tahir ya wayi gari da takardar
sammaci. Bayan sauye sauye da aka samu na daga
bangaren wanda ake (tuhuma ((Waheed) da kuma sabon
wanda ake tuhumar (Tahir) køtunta ci gaba da sauraron
Karar a bangarensu Tahir da na su Lauyar haka nan a
78
ZAINAB KABIR BIROMAN
bangaren Waheed din matarsa ke tsaya masa abin da ya yi
mutukar bakanta ran Tahir tare da daukar alwashin ganin
bayansu ta kowacce fuska, dan haka babu zancen
tausayawa aljihunsa.
Shari'ar dai na ci gaba da wakana kowane bangare
na kokarin ganin cewa shi ya yi nasara, a nata bangaren
Barrister Heedaya ta dage ta kuma fito da tsantsar baiwar
da Allah ya ba ta wajen kokarin kare mijinta abin da ya
dada jan hankalin masu kallo to sai dai a can daya barin
Barrister Tinibu shi ma na baje kolin basirar daAllah ya yi
masa musamman ko dan kasancewarsa sanannen Lauva ne
da ya kware a fagen aikinsa, don hakà wani bangare mali
rinjaye ke danganta nasarar a gare su, yayin da kalilan ne
ke musu hasashen samun nasara to sai dai fa abin na
kokarin juyewa, idan muka yi la'akari da zaman da kotun
ta yi na baya bayan nan, irin kwararan hujjoji da bayanan
da Barrister Heedaya Sa'ad ta bayar..
A yau ma kotun ta dage zamanta har zuwa ishirin
da hudu ga watan yuli, wató makwanni uku masu zuwa. Ta
fito da kwarin gwiwa da jin nasara a tare da su. Tana jin
wani irin farin ciki a zuciyarta ganin'nesa ta kusa zuwa
kusa da yardar Allah. Mutum ta gani kawai a gabanta a
lokacin da take shirin shiga motarta a cikin harabar kotun,
kallon-kallo suka yi sai akwai ta ja tsaki da niyyar barin
wajen. gabanta ya dada sha, hannayensa na sanye a cikin
aljihun wandonsa babu wani alamun damuwa a tare da sti.
magana yake yana mai karkada kafafunsa, "Sweety
Heedaya na zo ne in dafajan hankalinki kamar ki kamar
matsayinki bai kyau tu ki tsaya bata lokacinki a kan abin da
ba ki da nasara a cikinsa. A kan kuma mutumin dabai ma
79
ME GARI YA WAYA? 3
sankina yi ba, domin ba ke ce a gabanslhi ba. Ya kamata ki
gane kirtsaya ki fuskanoi mai Raunarki mai sonki. Heedaya
ba zantaba daina somki ba...."
A nanıta katse shi;."Ni kuma ina kin ka Tahir kuma
ba zanmdaina Rimkaibai" Tsakimta dada ja, "Asararre kawai
dai baiu sam martaban aurc ba" Kila in ban da suna cikin
hurumin kotun da tuni ya aiwatar mata da abin dà ba ta zata
baıganin yadda ya fusatar
Tana shirim tasliim motarr ya yi hanzarin rike
sitiyarim motar,. rankwafo da: fuska ya yi,. "Kin riga kin
makaro yacuya Rivavarki da soyayarki a gare ni ba su dà
wani ta ah h na sani kawai dole ne in
emma ah da yakg zuciyata, don haka sai ki shirya ki
kuma kimta dhik, sa in da muka yr karon batta, ina fatan
kim fahumta
Nemi Kashi Na 4 Wanda Suka Fito Tare Da Nas3
Taku
Zainab Kabir Biroman
Mtss Sunusi Sani
80
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels