An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ME GARI YA WAYA?
NA ZAINAB KABIR BIROMAN
MRS. SUNISU BRISCOE)
ME GARI YA WAYA? 3
GABATARWA
Assalamu Alaikum Warahmatullab!
odiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) da ya ba ni ikon G
kammala wannan labari, duk da cewa mutane da
yawa sun yi korafi wajen rashin fitowar littafin a
kan lokaci, wannan ya faru ne sakamakon halin da na
tsinci kaina. Da yawa dai daga cikinmu muna sane da tarin
matsalolin da ke tattare ga mace mai juna biyu, alal hakika
wannan dalili ne ya hana ni kammala labarin a kan kari, ko
da yake akalla na rubuta kaso daya bisa biyun labarin a
lokacin da nake rubuta kashi na daya da na biyu (1&2) sai
kuma na sami kaina cikin wannan yanayi wanda ya tilasta
ni ajiye alkalamina har zuwa lokacin da Ubangiji ya sauke
ni lafiya.
Ko da yake a tsarina nakan kammala rubuta labari
tun daga farko har zuwa karshe kafin ma na fara bayarwa a
buga a na`ura mai kwakwalwa (Typesetting) in ban da
littafin SAKAYYA (wanda tun ainihi ban yi nufin rubuta
kashi na biyunshi ba) sai kuma wannan 'ME GARI YA
WAYA 3' da Allah bai ba ni ikon kammalawa ba a lokaci,
saboda dalilan da na bayyana a baya.
Ko bayan da na haihu na ci gaba da fuskantar rashin
samun isasshen loakcin da zan yi rubutu, domin rubutu abu
ne da yake bukatar lokaci da nutsuwa mutukar kana
bukatar rubutun mai inganci da zai amfanar da al'umma.
Ga shi kuma 'RAINO' ba abu ne mai sauki ba musamman
da yake akwai hidindimu da yawa a kaina da ya hada da
kula tarbiyyar yara da hidindimunsu da kuma uwa uba
6
ZAINAB KABIR BIROMAN
maigida. Ba ya ga sauran hidindimun nawa na kaina da
kuma hutun da nake bukata a matsayina na yar'adam. ko
da masu karin magana kan ce "Rai Dangin Goro ne....".
Don haka nake neman afuwar masu karatu a bisa
jinkirin da wannan littafi ya yi duk da cewa ni da kaina na
ba ku fi ni son ya fito a kan lokaci ba, domin samun damar
isar da sakon da nake fatan isar da shi ga al'umma yadda ya
dace. Wannan kuma burin kowane marubuci ne idan da za
ka bincika a bisa jinkirin wasu daga cikin littattafai za ka
iske akwai uzurin da ya tsai da shi, don haka nake nasiha ga
'yan uwa a bar bin mu da kausasan kalamai a duk lokacin
da muka yi kuskure ko jinkirin fitar da littafi, me yiwuwa
muna da uzurinmu, alal misali a kan rashin fitowar wannan
littafi akwai wadanda za su rubuto maka sako ta hanyar
Text Message da zafafan kalamai wasu ma na cin fuska.
to sun mance cewa Allah (S.W.T) ne kadai dauwamamme
wanda hikima, basira da ma komai nashi ba su da iyaka ba
kuma sa karewa. In haka ne kuwa dole wata rana ko mun
ki ko mun so za mu gajiya mu daina rubutun ma baki dayansa sai dai fatan Allah ya sa al'umma ta amfana daga abin da muka bari.
A karshe nake fatan Ubangiji ya sa mu amfana daga cikin darussan da ke da amfani cikin wannan labari, haka
kuma Ubangiji ya sa mu guji wadanda suke marar sa kyawu, Allah ya hada mu cikin ladan abin da muka rubuta
bisa siradil mustakim, ya kuma yafe mana abin da na rubuta shi bisa kuskure.
Sai mun hadu a sabon littafin girke-girke da na yi masa lakabi da ‘KAYAТATTUN GIRKE-GIRKE'. Da kuma sabon littafina da zai fita idan Allah ya ba ni ikon
7
ME GARI YA WAYA?3
kammala shi wanda na yi masa lakabi da RAYUWARMU
A YAU.
'Rayuwarmu A Yau' Labari ne da yake magana a
kan akidar nan ta ‘JARI HUJJA`, ma'ana sai kana da shi
kake mutum ake kuma yi da kai, akidar da ta yi tasiri a
zukatan mafi rinjayen al'ummar wannan zamani da kuma
hanyoyin da za a bi domin magance wannan matsaloli. A
hannu daya kuma ya tabo tsagwaron talauci da al'umma ke
fama da shi a wannan yanayi da muke ciki. Anya kuwa ka
taba karanta labarin da aka ta6o tsantsar talauci irin haka?
Zainab Kabir Biroman
Mrs Sunusi Sani
Al-Ahad, 2 R/Thani, 1430AH.
Sunday 29/3/2009
Ma'assalam!
Ga Kadan daga Cikin Littafin
RAYUWARMU A YAU
awowarta ke nan daga makaranta cikin wahala gami D
da azabar yunwa da kishirwa. Zubewa ta yi a tsakar
dakin Innarta. "Inna ruwa me sayi, Inna kishi nake ji
tun a kan hanya." Innar ta dube ta cikin tausayawa tare da
fadın, "Yau cikin hikimar Ubangiji ko wanda za mu jika
makoshi babu shi, babu na famfon da Bature ya sabar
mana, rijiyoyi kuma sun gama kafewa har ta kai rijiyar da
take dauke da daruruwan shekaru wanda za ki ga ruwa bai
taba janyewa daga gare ta ba yau ta kafe a wannan yanayi
8
ZAINAB KABIR BIROMAN
maigida. Ba ya ga sauran hidindimun nawa na kaina da kuma hutun da nake bukata a matsayina na 'yar'adam. ku
da masu karin magana kan ce "Rai Dangin Goro ne....". Don haka nake neman afuwar masu karatu a bisa
jinkirin da wannan littafi ya yi duk da cewa ni da kaina na
ba ku fi ni son ya fito a kan lokaci ba, domin samun damar
isar da sakon da nake fatan isar da shi ga al'umma yadda ya
dace. Wannan kuma burin kowane marubuci ne idan da za
ka bincika a bisa jinkirin wasu daga cikin littattafai za ka
iske akwai uzurin da ya tsai da shi, don haka nake nasiha ga
'yan uwa a bar bin mu da kausasan kalamai a duk lokacin
da muka yi kuskure ko jinkirin fitar da littafi, me yiwuwa
muna da uzurinmu, alal misali a kan rashin fitowar wannan
littafi akwai wadanda za su rubuto maka sako ta hangar
Text Message da zafafan kalamai wasu ma na cin fuska.
to sun mance cewa Allah (S.W.T) ne kafai dauwamamme
wanda hikima, basira da ma komai nashi ba su da iyaka ba
kuma sa karewa. In haka ne kuwa dole wata rana ko mun
ki ko mun so za mu gajiya mu daina rubutun ma baki dayansa sai dai fatan Allah ya sa al'umma ta amfana daga abin da muka bari.
A karshe nake fatan Ubangiji ya sa mu amfana daga cikin darussan da ke da amfani cikin wannan labari, haka
kuma Ubangiji ya sa mu guji wadanda suke marar sa kyawu, Allah ya hada mu cikin ladan abin da muka rubuta
bisa siradil mustakim, ya kuma yafe mana abin da na rubuta shi bisa kuskure.
Sai mun hadu a sabon littafin girke-girke da na yi
masa lakabi da 'KАYATATTUN GIRKE-GIRKE'. Da kuma sabon littafina da zai fita idan Allah ya ba ni ikon
7
ME GARI YA WAYA? 3
kammala shi wanda na yi masa lakabi da RAYUWARMU
A YAU.
'Rayuwarmu A Yau' Labari ne da yake magana a
kan akidar nan ta 'JARI HUJJA', ma'ana sai kana da sh
kake mutum ake kuma yi da kai, akidar da ta yi tasiri a
zukatan mafi rinjayen al'ummar wannan zamani da kuma
hanyoyin da za a bi domin magance wannan matsaloli. A
hannu daya kuma ya taßo tsagwaron talauci da al'umma ke
fama da shi a wannan yanayi da muke ciki. Anya kuwa ka
taba karanta labarin da aka tabo tsantsar talauci irin haka?
Zainab Kabir Biroman
Mrs Sunusi Sani
Al-Ahad, 2 R/Thani, 1430AH.
Sunday 29/3/2009
Ma'assalam!
Ga Kadan daga Cikin Littafin
RAYUWARMU A YAU
awowarta ke nan daga makaranta cikin wahala gami D
da azabar yunwa da kishirwa. Zubewa ta yi a tsakar
dakin Innarta. "Inna ruwa me sayi, Inna kishi nake ji
tun a kan hanya." Innar ta dube ta cikin tausayawa tare da
fadin, "Yau cikin hikimar Ubangiji ko wanda za mu jika
makoshi babu shi, babu na famfon da Bature ya sabar
mana, rijiyoyi kuma sun gama kafewa har ta kai rijiyar da
take dauke da daruruwan shekaru wanda za ki ga ruwa bai
taba janyewa daga gare ta ba yau ta kafe a wannan yanayi
8
ZAINAB KABIR BIROMAN
da muke ciki da tarin laifukan al'ummar wannan zamani ya yi yawa a cikinta."
"Inna babu ruwan da zan sha ke nan?"
"To ya za a yi Nana Safiyya? Ba ni da ko silan da
zan iya sama mana ruwan sha, wanda muka dogara da shi
din ma (na rijiya) a yau an wayi gari babu shi. "Abinci fa Inna?"
Sunkui da kai ta yi saboda nauyi da kunyar diyar
tata, ba ta da shi ba ta da mai bata hatta da dan aikatau din
da take samu (Surfe) dif kamar hadin baki babu inda ta
samu, don haka ta yi hakuri ta zubawa sarautar Allah ido.
Nana Safiyya ta fahimci abin da Innar ke nufi, hannu ta sa
ta dafe cikinita tana dan numfarfashi na wahala da azabar
yunwa, ba kanta take ji ba, kananun Kannenta ta fi
tausayawa, domin in sabo ne ya ci a ce ta saba da yunwa.
Inna Halima ta yi jugum hawaye ne kawai ke zubo
mata tare da kaicon halayyar al'ummar wannan zamani da
babu tausayi ko tausayawa a mafi yawa daga cikin
'ya'yanta. RAYUWARMU A YAU haka ta koma? Mutane
sun daina kyauta, sun daina sadaka, sun daina fitar da hakkin Allah
Zainab Kabir Biroman
Mrs Sunusi Sani
9
ME GARI YA WAYA? 3
TSUNTSUN DA YA JA RUWA
ayewar garin Asabar iyalan gidan General WAbdallah usman suka wayi gari cikin mummunan
tashin hankali, a dangane da bakin labarin da ya
riske su. Kafarsa dayakan daya yana karkada su, ya zagaya
falon ya fi sau a kirga, har daga bisani ya sami waje ya
zauna cikin mummunan bacin rai, ya kalli mai dakinsa
Hajiya Fatima, magana yake cikin faga murya, "Bari ki je
babu wani dan iskan yaron da ya isa ja minmasifa
balltantana ya zubar min da kima da mutumcina a idanun
jama'a, dan haka daga rana irin ta yau ina bayyana miki ni
Abdullahi na tsame hannuna daga 6angaren Abdulwaheed,
ya je ya yi duk abinda yake ganin dai-dai ne a wurinsa ba
shi kadai na haifa ba ballantana ya haddasa min da tashin
hankali." Ya kada kai, "Na yafe shi ya je can ya aiwatar da
duk wacce za ta fisshe shi.
"Kisan kai! Haba wannan takadarancin har ina
haka? To ba a gidana ba babu kuma wanda ya isa ya shigo
nin da zaluncin cikin gida."
Kanta na duke kuka take faman yi da wanne za ta ji
ne? me ya sa shi General yake haka? Hannunka ai ba ya
rubewa ka yanke ka yar. Wannan kawai ibtila'I ne da ya
afkawa dan nasu, domin kuwa ba halinsa ba ne. Kai ita ba
ta ima amince zai aikata wannan ta'addancin ba.
Daga shi sai Hajiya Kaltum a falon. kowannensu
oike da damuwa a tattare da shi, ta dube shi jikinta duk а
sanyaye fuskarta akwai yanayin alhini a cikinta, Alhaji
10
ZAINAB KABIR BIROMAN
lamarin nan fa abin dubawa ne, anya kuwa yaron nan zai
aikata wannan aiki? Kisan rai ba fa abin wasa ba ne, Alhaji
a dai duba lamarin nan." Hannayensa na kan kumat
yana dogon nazari zuciyarsa na kissima masa abubuwa da
yawa, ya dubi mai ſakinsa, "ni ma tunanin da nake yi ke
nan, toamma inda gardamar take wace hujjar za ki kawo da
zai karyata kwararrun shaidun da aka bayyanar? Waye ya
yi kisan idan ba shi ba ne? to duk ma mu bar wannan, abin
ta'ajibin shi ne, meye gamin shi da yarinyar da ake tuhumar
sa da kashe ta har suka kebe a wani kebantaccen wuri?"
Ta yi saurin tarar nufamshinsa, kai dai Alhaji duk
wani tone-tone ma a bar shi, makiyinka a duk inda yake
yana tare da kai ya kuma san ta inda duk zai bi ya kassara
ka. Ta ci gaba da bambami, haba Alhaji kai ko ka ki ka
gane halin dan'adam ne, mutumin da ya nuna ba ya
kaunarka shin meye ba zai yi wa zuri'arka ba? ya soma
fahimtar inda ta sa gaba, hannu ya sa ya dakatar da ita, Ya
isa Kaltum je ki kawai ki bar ni da abin da ya ishe ni. Au
haka za ka ce? Ko da yake na lura gaskiya ce ba ka cika son
ta ba saboda an riga an gama da kai.
Illahirin jikinta ya yi mata tsami yana yi mata ciwo
dai-dai da kafafunta ta kasa motsawa, inda ya bar ta har
yanzun a nan take duka kam ta ci shi, dukan da ko jakar gidanka ba za ka iya yi wa shi ba (A tunaninta) ai ko ya da kowa kansa balbalin bala'i, komai yake takama da shi komai yake gadara da shi a wannan karon ba za su amfana
masa komai ba, aure ne dai kam ya kare a tsakaninsu sai kuma an bi mata hakkinta domin ita ba jakar gidansu ba ce. konai wuya komai runtsi karshen zamansu ya zo ko da za
a sa ta a turmi a kirba ba za ta ci gaba da zama a gidansa
11
ME GARI YA WAYA? 3
ba ta tsani mutumin ta tsane shi ba za ta taba kaunatar shi
bа. Nа yтmata illoli da yawa.
Zamansu kam ya zo karshe, ko da can din ma an
tursasa ta ne, yanzu kam babu wanda ya isa ya Kara tursasa
ta kan abin da ba ta kauna, kai ba za ta taba ma kaunatar
shi ba kamar yadda ta san haka yake a gurin shi in ban da
haka dan menene zai je yana yi mata kazafi yana kuma
vayata ta a duniya saboda kawai tsana da kiyayya? To
amma me? Gaba daya ta kasa motsa jikinta saboda
dumamar da jikinta ya yi, duka kam ta sha shi tamkar a
hannun masu wasan tamaula, (abin ka da 'yar shagwaba)
Kuka kawai ta saka takaicinta mugun mutumin ya dawo ya
riske ta a gidansa gidan da ya sha yi mata gorinsa, ba ta
neman agajin kowa ballantana ta nemi agajin har ma a nemi
bata mata budget, hukunci kam ta riga ta gama yankewa
kanta.
Wasa-wasa sai ga shi ta WAYI GARI a gidan
mugun mutumin kamar yadda ta lakanta masa, ya dawo be
dawo ba ba ta sani ba, ba ta ma damu ta sani din ba. Cikin
karfin hali tayi kemai ta kimtsa yunwa da jiri na dibar ta
amma haka ta daure ta shiga harhada kayanta. Ruwan
gidan mutumin ba ta kaunar ta dandana ballantana har ta yi
tunanin breakfast, duk da cewa rabon da wani abu ya shiga
cikinta tun da yammacin jiya, duk da kasancewar ita ba
ma'abociyar cin abincin da yawa ba ce, to amma dai ta
galabaita.
Ta gama kimtsa kayanta ta fito babban falon gidan
da zummar kiran Peter domin ya fitar mata da kayanta
akwati guda. Jiri ne kawai ta ji yana diban ta, kamar za ta
yi kasa Allah ya taimaka ta yi saurin fadawa kan kujera, ta
12
ZAINAB KABIR BIROMAN
dade a haka hannunta dafe da saman goshinta, mutumin so
yake ya kashe ta da ranta, tabbas ya kamata ta yi wani
yunkuri don ceton rayuwarta.
Sallama ta jiyo a lokacin da take yunkurin kwantar
da kanta jikin hannun kujerar saboda hajijiyar da gaba daya
garin yake mata. Sun dan jima suna sallamar, lallai kam ba
lau ba sai kawai suka kunno kai. Hafya Eatima ce tare da
Inna Asabe abokiyar zaman mahaifiyar maigidanta. Kallo
daya ta yi mata ta yi masifar ba ta tausayi, kila tana alhinin
rashin dawowar maigidanta ne tun daren jiya, tunanin
Hajiya Fatima ke nan.
Wani irin abu ne ta ji ya tsaye mata a zuci, tana
mutukar ganin girman dattijuwar ta cancanci hakan, domin
tana da halin dattijantakar, to amma fa a wannan akron
babu wani sauran kara bare alkunya. Sam-sam ba za ta taba
yarda da wani lallashi ko ban baki ba idan ma shi ne ya
kawo su.
Cikin karfin hali ta danne damuwarta ta tarye su.
tana yunkurin tashi amma ta kasa. Da sauri ta dakatar da
ita, yi zamanki 'yata ai mu ba baki ba ne saboda lura da
yanayin ta. Ta rissina ta gaishe su ba yabo ba fallasa, domin
wannan karon ba za taba yarda a lallashe ta a kware ta a
kuma tafi abar ta da mugun mutumin. Ita kanta Hajiyan
talura da sauyin, to sai dai ta dangana da rashin ganin
maigidanta tun a safiyar jiya. Kanta na sunkuye ta rasa ta
cewa, kai wannan yaro bai kyauta musu ba, tausayin
yarinyar duk ya bi ya baibaye su.
Inna Asaben ce ta yi karfin hali ta fara da yi mata
nasiha a bisa karbar kaddara mai kyau da marar kyau, duk
da kasancewar ta dattijuwa amma kuma mace ce mai juriya
13
ME GARI YA WAYA? 3
da kuma kadaita Allah. Cikin karfin hali Hajiya Fatima ta
ci gaba da yi mata bayani, ni na san wani ibtila'l ne ya
afkawa yaron nan amma na yarda da nagartarsa ko daya
ban yarda da zai aikata wannan aiki ba. ba ta dai fahimce su
ba, cike da alamun rashin fahimta ta ce, "Momy." Kamar
yadda 'ya'yanta suke ce mata, "Ban fahimta ba, menene ya
faru ne Momy?" tambayar ta yi mata tsauri ta yi kuma yi
mata nauyi haka dai ta yi kokarin fahimtar da ita a gajarce.
Zumbur ta mike ta dafe kirji tare da fadin "Kisa!
Kisan kai!! Kai ta shiga kadawa yayin da gidan ya ci gaba
da juya mata, ko kafin su tarye ta tuni ta yi kasa ta fadi
Kasa sumammiya.
Misalin karfe hudu da 'yan mintuna na yammaci ta
farka da kyar take iya bude idanunta tana iya shaida
wadanda suke wajen. Mahaifiyarta ce tare da dadinta sai
kuma Momy Fatima da wasu da ba za ta iya kiyayewa ba,
ba da jimawa ba bacci ya dada sace ta. Sai misalin karfe
taran dare da wasu 'yan mintuna ta farka, sai a sannan ta
dawo cikin hayyacinta. Ba ta ma bari an gane ta farka din
ba ta runtse idanunta cikin matsanancin hali da takaici,
bakin cikin duniyar nan kam ya kare akanta, an cuce ta an
gama cutar ta baki daya, yau ita ce mai auren mai daukan
rayukan al'umma? Dole kuma a kira ta da matarsa. Tarihi
ya riga ya tabbatar da hakan, hakika an gama da rayuwarta.
Tabbas lamarin ya dake ta ya buge ta, kai ya ma
bugi zuciyarta baki daya, ta shiga bawa kanta amsa, meyс
abin manaki? Meye abin damuwa? Mutumin nan fa babu
abinda ba zai aikata ba in ma da abin da ya fi wannan ta
san shi mai iya aikatawa ne, ba shi da tausayi, ba shi da
halin kirki, maketaci ne mai bakar aniya, Allah ne ma ya
14
ZAINAB KABIR BIROMAN
cece ta ya bayyana da ta'addancinsa ko iyayensu sa hankalta su raba tsakaninsu, muddun ba haka ba kuwa suna iya zuwa su iske gawar ta a gidansa, wannan ba wani abu ba ne mutumin da ba ya kaunarka babu abin da ba zai iya aikata maka ba.
Cuta ce an cuce ta an gama da rayuwarta tun da an hada ta da maketacin mutum, me yawan zalunci, aka raba ta da abin kaunar ta saboda kawai ba a Kaunarsa aka Kakaba masa wani lefin aka 6ata zuri'arsu aka kira su da
marassa tarbiyya ga shi tun kan GARI YA WAYE an soma
fahimtar wayemarar tarbiyyar, akwai rashin tarbiyyar da ta
wuce daukan rayukan jama'a? wa ya san iya adadin wadanda ya kashe? Sai Allah sai kuma yanzu da ya toni
asirinsa. Hawaye suka shiga zubo mata, kai! An gaıma da
rayuwarta, an kuma gama a tagayyara ta a idanun jama'a bayan tagayyarar da ya yi mata da ta fi komai illa, ta tsane
shi ta tsane shi, ko da tsiya ko da arziki sai an raba tsakaninsu, azzalumi mai daukan rayukan jama'a. Momy Fatima ce ta fara ankara da ita da sauri ta yo
kanta, hado ta ta yi da jikinta tana lallashinta gami da share
mata hawaye, ki yi hakuri 'yata mun sani ba karamin tashin hankali ba ne wannan amma ki yi hakuri da sannu Allah zai fito miki da mijinki lafiya. Abdul dana ne ni na haife shi na san dabi'unsa ko da wasa ba zai taba iya kwatanta aikata haka ba, ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki da yardar Allah mijinki zai dawo gare ki. Karon farko taji dattijuwar ta fara sure mata saboda son kai da rashin adalci, mutum ya yi kisan kai ya aikata wannan dungumemen lefi a rika fatan ya fito har ma ana rokon
15
ME GARI YA WAYA? З
Ubangiji, ai shi Ubangiji adali ne ba ya zalunci, ya fada
cikin littafi mai tsarki.
a
Hajiya Fatima na aikin lallashi Inna Asabe ma na yi,
a hannu guda Mamanta na yi to amma duk a banza
takaicinta guda wata sabuwar da take shirin bullowa na
take gaskiya kiri-kiri da idanunsu, har ma ake mata fatan
sake kasancewa tare da mutumin.
Tun zuwan ta asibitin General Abdallah,
Ambassador Sa'ad da kuma kannen mijinta ke sakaraftun
duba ta, haka nan Hajiya Kaltum a nan take yini ita ko
Hajiya Fatima a nan take kwana. To sai dai ba ta wani dade
ba kwanaki uku likita ya sallame ta. Karfin ciwon nata
yunwa ce da kuma damuwa. Sai kuma ciwon ta na asthma
da ya tashi wanda daman damuwa na daya daga cikin abin
da ke assasa ciwon.
General din ne da kansa ya bukaci a tafi da ita can
gidansa. Tana ji tana gani aka yi mata wannan karfa-karfar.
Kuka kawai take ita dai ba haka ta so ba to amma General
din gaba daya ya kasa ya tsare, shi mutum ne mai kwarjini
da ba ka iya musanta abin da ya bukata. To amma abin da
ya dada tausasar da zuciyarta, be wuce wanda ake abina
domin shi tashi ta riga ta kare, menene ma za ta damu
kanta?
Hajia Kaltum da Ambassador Sa'ad ba su wani
nuna damuwarsu ba a bisa hukuncin da General ya zartar,
domin sun yaba da kulawar da ake bawa 'yarsu.
Hajiya Fatima na iya bakin kokarinta wajen
kyautata wa surukarta tare da febe mata kewa, haka nan
kannen mijinta, daki guda aka ware mata a nan sashen
16
ZAINAB KABIR BIROMAN
Hajiyar, ko da yake yawancin lokuta suna tare da su lubuna in dai ba sun je makaranta ba.
yanayin rayuwar dai kam sam babu dadi a gare ta, an kuntata ta an takure ta saboda kawai a cuce ta da kuma
cewa wani ya jaza mata wanin ma makiyin ta da yake kokarin tagayyara rayuwarta.
Zaune take a falon Hajiya Fatima Momin na ci gaba da ba ta baki tare da kwantar da hankalinta, jinta take amma abin da take tunani sam ba haka nan ba ne a gurin ta, meye damuwarta a ciki? Ya shckara dubu ma ba damuwarta ba
ce, hakkinta ne ya fada mishi yayi nufin tozarta ta sai kuma
abin ya juye kansa.
Sallama ya yi ya shigo ya gaishe da Hajiyan cikin girmamawa ita ma Heedayan suka gaisa ya dada russunawa Momy a ci gaba dai da yi mana addu'a muna nan muna
bakin kokarinmu da yardar Allah, Allah zai bayyanar da gaskiya, domin na san dan uwana ba zai taba aikata
wannan aikin ba, ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki
Momy komai yayi zafi maganinsa Allah.
Akwai yanayin damuwa a tattare da ita ta shiga fadin, "To Sameer me za mu yi in ba hakurin ba? hakuri
kam ya zama dole, addu`a dai ba za