Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
ta sani ta kuma gama gano ba wani abu ba ne yake damun diyarta face rashin TARBIYYA da dukkanin su suka gaza sauke wannan nauyi da Allah (S.W.T) ya dora musu. Ranar 20/6/2001 kotun ta kara zama, an fafata a tsakanin Lauyan gwamnati da Lauyan wanda ake tuhuma duk da babu alamun nasara a 6angaren wanda ake tuhumar sakamakon kwararrun hujjojin da Lauyan gwamnati ya 31 ME GARI YA WAYA? 3 bayar. An Kara daga sauraron Karar zuwa goma sha hudu ga wata mai zuwa. Yanayinshi kadai za ka kalla ka san yana cikin damuwa marar misaltuwa yayi baki ya rame, haka nan ga w ata kasunba da ya tara, kai ya fita daga matashin nan dan gaye dan Kwalisa, Kafafunsa da hannavensa sakale da ankwa ba ya iya kwakkwaran motsi ba tare da ka ji karar sarkar ba. Takaici da bakin ciki suka dada sarke zuciyarshi a yayin da aka zo fita da shi daukacin jama'ar da ke wajen hankalinsu ya karkata a kansa da wadanda abin ya shafa da wadanda kallo ne kawai ya kawo su, domin ganin yadda shari`ar za ta kaya, saboda sanin matsayin mahaifin yaron, shinz a a aiwatar da adalci ne ko kaka? Russunar da kai ya yi a lokacin da aka zo gilmawa da shi gaban surikinshi, abokanshi da ma kanne da 'yan uwanshi. Kowannen su sunkuyar da kai ya yi babu mai iya tanka mishi sai ko surikinshi da ya yi karfin halin dafa kafadarshi tare da girgiza mishi kai alamar karfafa mishi gwiwa. Hawaye ne kawai ya ji yana zubo mishi sa ilin da jami an tsaro suka iza kafadarshi. Kanshi na hade da gwiwarsa tunani ne fal a zuciyarsa, "Kisan kai? Yau shi Waheed ake tuhuma da wannan laifi, wane abu ne ya fi wannan?" Ko da wasa ko daa mafarki ne tunaninshi bai taba ba shi ya aikata wannan laifi ba. shin wa ya kashe wannan baiwar Allah? Waye ya hada mishi wannan kullalliyar? Da wace hujjar zai kare kansa? Babu sai fa Sarki Allah da ya halicce shi. A yau ya jawa iyayensa dama danginsa baki daya abin kunya, wai tun farko me ya kai shi tsunduma kanshi cikin wannan kazamar rayuwa? Meye gamin gaminsa da mace a cikin 32 e ZAINAB KABIR BIROMAN Otel? In dai ba shashanci ba. Kai laifukansa sun yi yawa, ya zalunci kansa ya zalunci iyayensa, 'yan uwansa. masoyansa da ma matarsa. Tunaninsa ya tsaya cak! Sai lokacin da ya tuno irin rabuwar da suka yi. Daya bayan daya abubuwan da suka wakana ya dinga bijiro mishi, har kawo zargin da ya yi wa matarshi, rabuwar baram-baram din da suka yi, kawo zuwa kiran da marigayiyar ta yi mishi a waya. To a lokacin ne hankali da tunani suka fara dawowa jikinsa, kwakwalwarshi ta shiga aiki, ta shiga cajin duk abin da ya wakana, tsoro da fargaba suka fara kama shi, anya kuwa yarinyar nan za ta aikata wannan aiki ciki ciki fa ba abin wasa ba ne, duk da dai yana da shakku a kan lamarinta da Tahir to amma fa akwai ayoyin tambaya a cikin lamarin nan, to sai dai hotunan da ya gan su tarwatse duk wani tunaninsa a dangane da al'amuran matarsa da babban abokin gabarshi ya fadi lokacin da yake tsinkayo gargadin da Tahir ya yi mishi na karshe tare da alwashin da ya dauka a kansa musamman a kan marigayiya. Ya yi masa abubuwa da dama ya kuma san haka dan haka zai iya yin komai a kansa, shi kansa ya san ba shi da matsala a kan kowa da Farida sai fa Tahir. Wannan ma hujja ce mai karfi, to amma anya komai rashin imanin Tahir zai iya daukan rai dungurungum? Tambayar ta yi mishi tsauri ya kasa lalubo mahadinta. Zahirin gaskiya rayuwar da yake a gidan kason rayuwa ce ta kaskanci kamar dai shi kamar matsayinsa domin mahaifinshi ya yi fushi da shi ya kuna hana duk wani nashi shiga cikin lamarinsa sai fa surikinsa da mahaifin abokinsa su ke iya bakin kokarinsu. 33 ME GARI YA WAYA? 3 Shari'a ake tafkawa to amma babu wani alamun nasara a bangarensu Waheed. Kishingide take a kan kujerar hutu (resting chair) tana amsa wayar masoyinta Tahir ya ci gaba, kina ji na ko Heedaya, ni ban ga dalilin da zai sa har yanzu ki zauna da Kallagaggiyar igiyar mutumin nan ba, Heedaya wannan ai babbar tawaya ce a tare da ni da ke baki daya. Mutumin da ya yi kisan rai meye amfanin zama da shi? shawarata a gare ki ki yi kokarin duk yadda za ki yi a datse igiyoyin nan, tun kan GARI YA WAYE miki. In ba haka ba wata rana za a wayi gari sai dai a tsinci gawarki a gidan maketacin mutumin nan wanda bai dauki rai a bakin komai ba. ki tuna fa tsana da kiyayya ce a tsakaninku, me kike tunanin zai iya wakana nan gaba? kowa fa ya san matsananciyar soyayyar da yake tsakaninsa da Farida amma yau ga hukuncin da ya zartar mata, wannan ma fa abin dubawa ne Heedaya. Zuyciyarta ta dada kawowa wuya. Ita dai ba ta ce tana kishinsa ba to amma ko can baya tana mutukar jin zafin ta gan shi da wata, sai dai ko ta danne. Cikin yanayin dauwa ta shiga fadin, Tahir na fi ka damuwa da halin da nake ciki ba don komai ba ko dan in zo in mallaki abin Kaunata, zabin raina, anma wani batu can nasa ni bai dame ni ba, domin ban ga abin da ya hada ni da shi ba, igiyoyina kawai nake wa takaici idan har su dinne ake ganin kullin da ya hada tsakaninmu to za kwa su sha mamaki, domin dunivar nan da fadi take ba kuma wai lallai sai a nan ne za mu iya rayuwarmu ba. Wannan batu naki haka yake sweet heart. To fa ya dada ingizo ta tare da famfa ta. Tana jin ko dama wanene za su iya raba hannun riga in dai a kan masoyinta Tahir ne. 34 ZAINAB KABIR BIROMAN A kan hanyarta ta fita daga sassan mamanta suka yi kacibus. Ja ta yi ta tsaya tana yi mata wani irin duba na kaskanci, shi dan talaka duk inda yake sai ya nuna hafamarsa da babakerensa, har meye a hanyar sai an nemi handame ta baki daya ne duk da fadinta? Ko ko a tunaninki kin yi nasarar raba ni da zabin raina kin cusa rayuwata cikin kunci da wahala shi ke nan za ki mike kafa ki wala? Kai ta girgiza mata, A'a ba haka ba ne. Za ki gwammace zama cikin kuntataccen gidan da kika fito ne. Da kyau Heedaya gaskiya ne batunki. Cewar Hajiya Kaltun. Ta ci gaba, Na'ima ko? Ta fada kamar mai shakkun sunan nata. Kin debo ruwan dafa kanki tun da burinku ya cika na ruguza farin cikin rayuwar 'yata, to bari ki ji ta nuno ta da yatsa, inda ba ku bar ta ta zauan gidan aurenta ba haka nan ke ma ba ko za ki yi zaman gidan ubanta ba. Sakato suka bar ta a tsaye kamar wacce aka zarewa laka, a lokaci daya 'ya da uwa sun ci zarafinta a bisa abu guda sai dai kowacce da ma'auninta, ma'ana da inda ta dosa ta kuma fahimta to amma dukkaninsu ta hada ta mikawa Sarki Allah, ta kai kokenta gare shi domin shi ne kadai wanda zai iya share mata hawayenta. Cin zarafi kam wadannan bayin Allah suna yi mata da ita da tsoffinta duk da cewa a mafi yawan lokaci ta fi dora laifin gurin tsoffinta, domin su suka jaza mata wannan halin da take ciki, sun kuma kasa sanin ciwonta da damuwarta su kawai abin duniya kawai suka sani, kullum cikin karyar da kai suke a gurin maigidanta. Ya dauka ya ba su shi ke nan fakat! ta kare, aure ne dai na jari hujja aka yi ko ko auren 35 ME GARI YA WAYA? 3 son zuciya, ko kuma ta kira shi da na kwađayi kamar yadda kishiyar tata takan goranta mata. Yau ma dai kamar ko vaushe suna tare da Tahir a harabar gidansu wanda take jin dan shakkun ba ya nan (mahaifinta) Momy Kaltum kuwa kamar yadda ta sani ba ta isa hana ta abin da ta dora zucıyarta a kai ba. Tahir din dai kullum yana nuna damuwarshi a kanta yayin da ita kuma ta ce ta ninninka shi idan muka vi la'akari da irin tataburzar da take da iyayenta duk dai a kan Tahir. A wannan lokaci damuwarta ta soma raguwa saboda farin cikin da masoyinta yake sa ta da dadadan kalamansa na yaudara (eh yaudara mana mace da aurenta kana bibiyarta). A ko da yaushe yakan yi kokarin nuna mata farin cikin da za ta shiga muddun ta kasance a Karkashinsa tare da nuna mata babu wanda ya dace da Heedaya face Tahir dinta. Sun shagala a haka sallamar mutum kawai suka ji a kansu, kallon biyu ahu suka yi wa junansu yayin da ita kuma ta kau da kai daga gare shi. Ranshi ya yi mummunan 6aci fuskarshi a faure ya hada hannayenshi ta baya yana dan karkada kafa kai ka cе: wani soja ne yake fareti, ya dube shi a iya sanina dukkanin mu musulmai ne muna kuma bin tsari da dokokin islama sat do me za ka tsare matar mutane kana magana da ita? Meye dalili? Yana busa sigari cikin nishadi ya shiga ba shi amsa, dalilin be wuce cewa daman can Heedaya malalkina се zabina ce son raina ce ka ga ko babu abin da zai hana ni mallakar ta ta kowane hali, kowane irin yanayi haka а kowane irin bigire take, ballantana a irin yanayin da ake 36 ZAINAB KABIR BIROMAN ciki na shafe babin tsohon abokin hamayya daga doron kasa. Ya dube shi gami da fesar da hayakin da ya kunsa a bakinsa. So ina fatan na ba ka amsa dai-dai da tambayarka? Cikin matsanancin bacin rai ya mayar mishi da raddi, lallai kam ban taba sanin cewa kai jaki ne dan jakai ba sai yau, haka kuma sai a yau din na tabbatar da cewa gadon iskanci da alfasha tanbarin gidanku ne, in ban da haka mace da aurenta ka dinga bibiyar ta? A'a Sameer ban da fa cin mutumci, me ya kawo batun iyaye a nan? Cewar Heedaya. Hannu ya sa ya dakatar da ita, kyale ni da shi sweet heart in ba shi amsa dai-dai da irin tasa. Ya fuskance shi ya ci gaba cikin yanayin nuna rashin damuwa ya shiga fadin, ai ko kana burge ni abokina daman na san ka da saurin fahimta, ka ga ko banza ma danbanza ba, jaki ba, da har zan kasa iya rike kambun gidanmu, ka san jaki ba ya iya rike abin da ya gudana ko da na kankanin lokaci, ba shi kuma da kishi balle har ya iya rike tambarin gidansu. Abu daya nake so ka gane, na riga na gayawa abokinka, ina jin kai shaida ne be isa ya ja da ni Tahir El- Hussein ba. Ya nuna kanshi da yatsa, ballantana har ya malake abin da raina ke so. Na cimma burina ko ko ban cimma burina ba? Wannan amsar ba na bukatar ta daga gare ka a yanzu, na bari ka yi tunani da kaifin basirar nan taka ka gano meye amsar tambaya ta. Daga haka be kara cewa komai ba ya sa kai ya shiga mota ya tashe ta tare da yi mata nuni da hannu wato yana nan dawowa. Juyawa ta yi za ta tafi ya yi saurin shan gabanta yana wani tsuma ji yake kamar ya wanke mata fuska amma 37 ME GARI YA WAYA? 3 dai ya daure maganganu yake cikin bacin rai, ban tabа sanin halinki ke nan ba, ban taba sanin za ki yi haka ba. haba Heedaya? Da aurenki ki dinga sauraron wani katon banza, haba me za a yi da rayuwa irin ta su Tahir? Meye ne a gurin Tahir din nan da yake yaudarar ki? Bawan Allah yana can cikin musiba ke ko kina nan da wannan dan iskan babu abin da ya shalle ki, to ki sani Allah yana kallon ki yana kuma kallon iyakokinsa da kike ketawa. Dakatar da shi ta yi ya ishe ka, ya ishe ka Sameer ba za ka zo kana gaya minmagana a kan mutumin da ba komai ba ne a gurina face gagarumin makiyina da ya rusa farin cikin rayuwata, ya keta alfarmata. Dan haka ka ji ka kuma sani ba na son shi ba zan so shi ba bakuma zan taba sons hi ba dan haka ka shawarci abokinka da ya sahale min in kuma ya ki shi ne a wahale domin babu me iyaraba tsakanina da Tahir, Tahir shi ne zabina shinekuma zabin raina babume iya hana ni Raunar shi. Bari ma ka ji abokinka ya sake ni kar ya sake ni duk daya ne a gurina, aure ne ni da shi ya kare. Me za ayi da zama da maketaci mai daukar rayukan jama'a.... Kauuuuuuu! Ya sakar mata mari. Shi da kansa bai san san da ya aiwatar da wannan hukunci ba. ya sa hannu ya nuno ta da yatsa bakinshi har wani rawa yake, abokina! Abokina!! Be yi kisan kai ba ba na shakku ko kokwanto har abada ba zai taba aiwatar da wannan hukunci ba, domin ba tarbiyyarmu ba ce, ba a tarbiyyance mu da haka ba, wallahi karya ne! karya ne!! karya ne!!! ya dinga nanata haka. Mai hakuri daman an ce bai iya fushi ba, ya ci gaba. ko ki yarda ko kar ki yadda ko ki so ko kar ki so ba kowane ya aiwatar da wannan danyen hukunci ba face masoyin da 38 5 ZAINAB KABIR BIROMAN kike ikirari, wallahi! Wallahi!! Tahir yana da hannu a kisan Farida na dade ina zargin haka amma a yau na dfa tabbatar da hakan. Shi ma ya figi mota ya fice cikin fus.. Ya kasa bacci ya kasa ko runtsawa ne duk da tsalelend aren da ya tsala acin rai da tunani barkatai ne kawai a zuciyarshi wane irin kiyayya ne yarinyar nan take wa abokinshi? Me ya yi zafi haka? Maganganunta sun tsaya mishi a kahon zuci, “..... ba za ka zo kana gaya min magana a kan mutumin da ba komai ba ne a gurina face gagarumin makiya da ya rusa farin cikin rayuwata ya keta alfarmata, dan haka ka ji ka kuma sani ba na son shi ba zan so shi ba ba kuma zan taba son shi ba....." Ya rasa ta wacce siga zai kalli wadannan kausasan maganganu, ba tun yau ba dai ya san tana yawan furta kalmar nan ta ki ga abokinshi to amma be taba fahimtar me hakan ke nufi ba sai fa a yau din nan. "....Ya keta alfarmata...." To wannan ce fa ya kasa sanin ma'anarta. Kai matan ma dai meye amfaninsu meye amfanin aurensu? Wannan masifa har ina? Ya dada goge su daga cikin kundin rayuwarsa in dai har haka lamarinsu yake ya yi nazari da kyau a can baya... a ko da yaushe yana tausar abokinshi tare da nuna mishi kuskuren fahimtar da ya yi wa yarinyar, ashe ko gaskiya ne ba ta kaunar tashi. Har kawo yanzu da yake gidan kaso, a duk lokacin da ya je yakan tausar da abokinshi a duk lokacin da ya sako batunta. Sameer ya dau aniyar duk mutumin da ya kullawa dan'uwanshi kuma abokinshi wannan makarkashiyar da yardar Allah sai ya binciko shi. Shì dai ba Lauya ba ne amma yana nan yana neman taimakon Ubangiji. 39 ME GARI YA WAYA? 3 Ko ana hamaza-hamata babu mai iya mayar da ita gidan maketacin mutumin, idan ma har ya fito (ba ta san me ya sa ba ita kanta ta kasa yarda zai iya aikata wannan mummunan aiki) to amma ko ma meye ko ma me yake ciki be dame ta ba, barin yanzu da abokinshi ya kara dagula komai, a kan me karatan banza za su dinga nadar ta? ya mare ta ba daya ba biyu ba yau ma kuma dan wani raini abin har ya kai ga abokinshi ya taba lafiyar jikinta. Ko da yake tun farkon haduwarsu da haka a ka fara da kuma hakan take fatan a kare, domin duk wani kima da darajar Sameer da take gani a yau ta kau, har shi ne zai dubi tsabar idanutan ya yi wa masoyinta wannan sharri ai kuwa ya debor uwan dafa kansa, wane shi wane ja da rabin ranta? Al'amarin ahalin gidan General Abdallah kuwa sun kasance cikin rashin walwala da sukuni hatta da shi kansa General din da ya tsame hannunsa daga dan nasa a baki ne dai kawai, amma a zuci shi ya san abin da yake ji, bare kuma Momy Fatima da aka ce da da uwa sai Allah, balle ma dai irin dan da ake sokamar Abdulwaheed. Haka abin yake a gurin yan uwansa komai da komai na dawainiyar iyali babu abin da suka gaza a ko da yaushe cikin aike da sakonni suke gidan Ambassador Sa'ad duk da ccewa ya nuna rashin son hakan, amma suka ce wajibinsu ne. Duk abin da suke yi ba ya burge ta ba ma ya gaban ta, domin ta soma fahimtar su suke dada tame kullun da ke tsakaninsu da dansu, saboda kawai tsabar son kai da kuma son a cusguna rayuwarta. Dan haka ne ma kanne kai da ma iyayen mijin suka daina ganin fuskarta a tunaninsu be wuce halin da mai gidanta ke ciki ba ne, don haka suka kara ganin kimar ta da 40 ZAINAB KABIR BIROMAN darajarta. Ga Hajiya Kaltum ko ta san ba haka ba ne babu dai yadda za ka yi da dan yaune (wani ba). Suna zaune a falon Ambassador gaba daya da yaranshi ya duba bai ga Na'ima ba ko yaranta.. Kai ina Na'ima ne? ku je ku kira ta. Ya umarci fa'iza mai biyewa Heedaya. Kamar dai ko yaushe cikin rashin ladabi da tarbiyya sakon Ambassador ya isa gare ta, ta yane kanta da mayafin abayar da yake jikinta ta riko hannun yaranta suka isa falon Ambassador,ta sami gefe ta zauna gami da gaisar da Ambassador. Yana dariya ya fara, "Ke Na'ima wace iri ce ne ki dinga zama a kasa kina wani dar-dar ke da gidanki kin kasa sakewa, haba Na'ima shekara nawa? Ta tabe bakinta, yo munafurci fa?. Cewar Hajiya Kaltum. Be ji ta ba ya ci gaba, taso maza ga mazauni ki zauna. Ya nuna mata kujerar da ke kusa da shi. har ga Allah a dararen take a dararen ma ta zauna kai jikinta ma har karkarwa yake inda za ka kula da ita, ta gama tsorata da abokiyar zamanta bare kuma 'ya'yanta da suka mayar da ita tamkar wata bola. To fa Hajiya Kaltum ta hade rai sakamakon wani shisshigewar da maigidan yake yi a kan sha'anin Na'ima, dan ma meye zai dinga tsomo musu ita cikin sha'aninsu? Kowa na fadin albarkacin bakinsa, amma ban da Na'ima Mabruka kuwa tuni ta dare cinyar Hajiya Kaltum sai mahaifiyarta kiriniyarta take tana sakewa da ita fiye ma da a dalilin ita 'yar fari ce. Tana ta furuntunta Hajiyan take kuma na biye mata yayin da ita kuma mardiyya da kan a rungume dada a jikin fa'iza tana ta tsotsar hannunta abin lokuta tausar da zuciyar Na'ima ke nan a yawancin musamman in sun kunno mata, har ga Allah Hajiya 41 ME GARI YA WAYA? 3 Kaltum da 'yayanta ba daga nan ba wajen son 'ya'yanta ita ce dai ba ta san me ya sa suka tsane ta ba. Daya bayan daya kowanne yana fadar abin da yake bukata Ambassador na ba shi an zo bangaren kudaden da aka nema na party da za su yi a school na zangon karshen shekara (third term) dukkansu babu wandwa be rubanya ba hatta da fiddausi 'yar Karamar cikinsu ta dauki wannan akida tsaf ta mahaifiyarsu bare manyan, halayyar Hajiya Kaltum ke nan a duk lokacin da aka bukaci wani abu a school ne ko ko na sha'anin yau da gobe to fa sai ta rubanya a haka har 'ya'yanta suka tashi da wannan akida in fa ka cire Heedaya. Tana daga kishingide tana karanta novel ta fago gami da kannawa kannenta harara, nawa kuka ce a bayar? Ba na ga takardun naku ba duka-duka kudin naku gaba daya ina jin total dinshi dubu goma sha biyu da naira dari biyar ne shi ne za ku wani dubu talatin ko menene? Harara ta galla mata to ina ruwan ki uwar katsalandan koma nawa ne ba mahaifinsu ba ne wa suke da shi da ya wuce shi? ko akwai wanda za su je su roka bayan shi ne? Dan karamin tsaki ta ja wanda ya riga ya shige makoshinta ta kau da kai kawai, ba tun yau ba ta san wannan akida ce ta mahaifiyarsu kiri-kiri za ta su su danfari mahaifinsu abin naira goma sai a ce na talatin ne har dai ta yi wayo ta daina saboda tana son mahaifinta fiye da zaton mutun. Don haka a fili take cewa Hajiya Kaltum ce tsanin ruguza tarbiyyar 'ya'yanta. Da budar bakin Ambassador sai cewa ya yi, gaskiya ne Kaltum wa suke da shi da ya fi ni? Zan yi kaico idan na ji cewa kun fita kuna roko ko daukar abin da ba na ku ba 42 ZAINAB KABIR BIROMAN hayan ko babu abin da na rage ku, ku fada sai me da me kuma? Hajiya Kaltum ta ji dadini hakan yayin da Aunty Na'ima ke ganin baiken Ambassador ha yarinya karama ta fi shi tsinkayen abin da shi ya kasa tsınkayowa lallai kam laifin ba na Hajiya Kaltum ba ne kadai. ***** ***** ***** Idanunshi a rufe yake amma ba bacci yake yi ba tsabar tunanin sa-in-sar da ta shiga tsakaninshi da Tahir a kwanakin baya, har ya gangaro zuwa ga ziyarar da ya kaiwa abokinsa kafin sa'insarsu da Tahir,. a Kamar yadda ya saba saba yaya kaiwa abokinshi ziyara. tausayi da kaunar abokin nashi ya gama cika zuciyarsa. gaba daya ya sauya ya fita hayyacinsa babu alamun nasara tare da su har yanzu a kila wa kala yake. Kai! Wannan duniyar abar tsoro ce a yau Waheed ne ya fita hayyacinsa ya ma fitar da rai da rayuwar baki dayanta. Babbar damuwar shi mahaifinshi da ya yi mishi komai a rayuwa amma a yau ga da abin da ya sakanta mishi babu wata hujjar da zai ga laifinsa wai don ya yi fushi da shi. “Babbar damuwata a yau shi ne yankan kaunar da yarinyar nan tà yi min." Ya kada kai, "Hakika ta cuce ni ba zan taba yafe yankan kaunar da ta yi min ba. "Ban fahimta ba." Sameer din ya fada duk da ya san da wacce yake. Karon farko ya ji yana sha'awar bayyanawa abokinshi sirrinsa ko ya wuta daga kuncin da zuciyarsa ke masa kasancewar ya aminta da shi. Tiryan-tiryan ya labarta mishi har kawo lokacin da aka iske shi da gawa a kan cikinsa. Ya yi kasake yana 43 ME GARI YA WAYA? 3 sauraronsa lamarin nasu akwai sarkakiya a cikinsa, tabbas kwai wani abu da yake zargi yake kuma da tabbatar da cewa hakan nc. Ya fuskance shi a tunaninka ka ga alamun ciki a tare da matarka?ko ko akwai shaida na zahiri da zai tabbatarmaka da hakan tana gudana a tsakaninisu ma'ana ka gan su ra'ayul ainu? Hotunan ma da na gaya maka wanman ai duk sun isa shaida, bayan wasu hujjojin da nake da su a dangane da dangantakarsu. Ban yarda ba wannan duk ba za su zama hujja a gare ka ba, ba kuma su isa shaida ba, ka dai tsangwami yarinyar mutane ne kawai har ba ka iya duban gaskiya. Mе zai hana ka tsaya ka yi tunani da hankalinka ka gano gaskiyar lamarin nan. Yarinyar nan ko ya take kai ne ka fi kowa sani, lalatacciya ce, kintsattsiya ce wannan duk amsar a hanmunka suke. Cikin Gacin rai ya dubi abokinshi, na fahimta ka kasa fahimta ta duk tsawown shekarun da muka yi, tun Curuciyarmu ka san sharri ko karya ba halina ba ne, dan me zan batawa kaina lokaci wajen yi wa yarinyar mutane sharmi? Gaskiya ne na tsane ta, ta tsane ni sai me? Baya ya jrya mishi ya yi kwanciyarshi. Hannu ya sa ya share hawayen da ya zubo mishi, tsinkayen abokinshi ya zama gaskiya ke nan? Yana ganin fada yake ashe ko haka ne yarinyar ba ta kaunar sa, kai yarinyar ta ba shi mamaki, ba haka nan ya dauke ta ba, 1o sai dai duk da haka ya yarda da kiyayya a tsakaninsu, to amma alowai makarkashiya a kasa. Ko ma meye kanshi ya shiga cikin duhu. Tahir maketaci mugun mutum har abin yardane? ga ta ga Tahir sun zuba masu ido. ZAINAB KABIR BIROMAN Ambassador Sa'ad ya gama fahimtar wanda yake ingiza yarshi har ta kasa yi mishi biyayya, a lokacin da ya zo shiga sashen mahaifiyarta ya tsinkaye ta a daki tana amsa waya ta hanyar lasifika (handsfree). Radau yana jin irin ingiza mai kantun da yake yi wa yarshi, rashin da'ar da yake shiryo mata kala-kala duk dan ta bujire masa. Saboda takaici bai iya jin karashen tabargazar da yake shiryowa diyarshi ba ya juya rai a 6ace. Lallai kowacce wace zai rufe ido ya ci zarafin ba ma wai Tahir din ba har shi kansa mahaifin ansa duk da mutumcin da ke tsakaninsu. Ba zai yiwu ba ya 6ata tarbiyyar 'yayanshi shi ma a nemi bata mishi tarbiyyar tashi diyar, tun ainihi ya tsani yaron ko ko ya ce ya tsani ta'adunshi, bare irin yanzun ma da suka yi kaurin suna wajen ta'annati da 'yayan jama'a. Tunaninshi tuni ta hakura da hatsabibin yaron tun kashedin da ya yi mata, bai sani ba a nan cikin kuryar gidanshi ake dada rusa tarbiyyar fiyarshi. Kai tir da cellular (wayar zamani) duk da ita ne ake kulla mishi wannan sharri kala-kala. Ya taki rashin sa'a Dr. El-Hussein baya: gari ya je can kasar Switzerland, a bangaren abin da ya shafi aikinsa: Bastare da bata lokaci ba ya nufi wurin da yake tunanin zai sami yaron wato ofishinsa, domin ya gargade shi gami da ja mishi kunne wanda yake ganin shi ne na karshe. ME GARI YA WAYA? Kafarsa daya kan daya yana dan karkada su bayan daya kwantar da

Chapter 3 of 6