haife ba ta isa ta tsawatar ba, yanzu matsawa yara, ita kuma da yake mai tsananin
59
ME GARI YA WAYA? 3
son yaran ce sai ta biye mishi suka ci gaba da sangarta
yaran ba tare da sauke nauyin da Allah (S.W.T) ya dora
musu ba.
Kwanaki biyu tana wannan nazari ta cimam
Ambassador a turakarsa tayi mishi duk abin da ya dace
sannan ta soko mishi da batun diyarshi, ni ko Alhaji ko
wane irin laifi yarinyar nan ta yi maka ai sai a afuwanta
mata, ba ka tausayawa halin da take ciki ne? haba-ban yi
tsammanin haka za ta shiga tsakaninka da yaranka ba....
Katse ta yayi gami da 6ata rai, "Kaltum abin da
yarinyar nan ta yi min ba na jin zan yafe mata nan kusa, irin
dai abin da ya faru a lokacin aurenta duk ba sai na yi miki
bayani ba amma a ce duk ba ta hakura ta saduda ba ta cі
gaba da bibiyar yaron nan marar tarbiyya (Tahir). Haba
wane irin zub da mutumci ne haka ko ko in ce wace irin
rashin tarbiyya ce haka?
A nan ta datse shi, "Yauwa Alhaji abin da nake so
ka fahimta ke nan. Tambayar da ya kamata tuntuni ka yi wa
kanka ke nan, rashin tarbiyya! Kana ganin ka ba ta
ingantacciyar tarbiyyar da ta kamata dan musulmi ya
samu?"
Cikin fusata ya ce, "Wace irin tambaya ce
wannan?"
Та сe, "A'a kwantar da hankalinka Alhaji ka tsaya
tsam ka yi nazari da kyau, lillahi warasulihi kana ganin ka
ba ta tarbiyyar da ta dace?" Ta muskuta, Alhaji mu cire duk
wani son zuciya mu kuma yi wa yarinyar nan adalci, duk
abin da ya faru ta fayyace min ta kuma gane kuskurenta
kuskuren da mu ya kamata mu nusar da ita kazalika ta
kuma nemi afuwarınu, to saboda Allah dan meye ba za mu
60
ZAINAB KABIR BIROMAN
afuwanta mata ba bayan ko ma menene mu ne sila. Eh! Da mun tsaya mun kau da son rai mun ba ta tarbiyyar da ta dace tun kan GARI YA WAYE da ba mu riske kawunanmu
cikin wannan yanayi ba. Yanzu kam da GARI YA WAYE
mana sai dai kaiwa mu dukufa wajen lalubo bakin zaren." Bayani fa take ta sakar masa ta ko ina ba tare kuma da ta
tsame kanta ba cikin masu daukar alhakin wannan kuskure
ba.
To fa Ambassador ya yi shiru ya yi zuru sai zufa ke
feso masa, hakika akwai kamshin gaskiya a maganganun
matarsa.
Kwana daya, biyu, uku kai har tsawonsati guda
Ambassador bai ce da diyarsa komai ba a wannan yammaci
ne ya dawo daga ofis yana zaune yana hutawa a falonshi ta
yi salama ta shigo ta yi fari ta rame akwai yanayin rashin kwanciyar hankali a tare da ita duk da cewa ta dan warware
daga rashin lafiyar da ta yi. Kanta na duke kamar ko yaushe
ta shiga neman afuwar mahaifinta cikin kyakkyawan lafazi
tare da nuna nadamarta, tuni zuciyarshi ta gama karaya, kauna da tausayin diyar tashi ya gama mamaye zuciyarshi,
musamman tun lokacin da ya gama gano nashi kuskuren, gaskiya da sun bata ingantacciyar tarbiyyar da duk haka ba
ta faru ba, ainma dai dan ya hora ta ya kuma dada sa ta a
saiti sai ya dake ya ki nuna damuwarsa a kanta duk da har
cikin zuciyarsa ba ya jin dadin halin da yake ganin ta a ciki.
To amma babbar damuwarshi halin da yaron yake ciki da kuma rashin sanin makomarsa, zahirin gaskiya ya san'yarsa ta gwadawa yaron halin rashin da’a a kan idonsu ma wane bore ne ba ta yi ba.
61
ME GARIYA WAYA? 3
Fuskarshi a daure babu alamun walwala a tare da
shi ya shiga fadin, "Zan iya goge wadannan kura-kuran da
kika tafka ne tare da goge shi a zuciyata a ranar da Allah ya
fito da mijinki kika kuma nemi afuwar irin rashin da'ar da
kika aiwatar mishi, ina jin wannan ne kadai zai iya kankare
mikin da kika dasa min a cikin zuciyata. Daga haka bai
Kara cewa komai ba ya tashi ya shige daki.
a
Ta sami dan sassauci a zuciyarta, tun lokacin da dad
dinta ya bayyana mata abin da ke zuciyarsa akalla yanzu
yana amsa gaisuwarta duk da dai babu wani sakin fuska
tare da shi ahalin yanzu tunanin ta ya fi karkata ne a kan
mijinta, to amma kunya da kuma tunanin fuskar da zai kalle
ta da shi shi ya fi damunta, tabbas ta sani ba ta kyauta ta
masa ba a iya żamansu, watanni dai-dai har bakwai yana
daure a gidan kaso dai-daid a rana daya ba ta taba tunanin
ziyartar shi ba, anya ko ta kyauta?
Ai ido ba mudu ba a ka ce ya san. kima, ko ma
menene ya zama dole ta kawar da kunyarta da ma duk wani
shakku ta fuskanci mijinta. Mutum daya ne ya fado mata
wanda take ganin shi kadai ne zai iya yi mata jagora
(sameer) to ko shi din ma tana shakku gami da kunyar
tunkararsa musamman idan ta yi la'akari da abin da ya
gudana a kwanakin baya. Abu na farko da ta fara yi shi ne
fuskantar Sarki mabuwayi maigirma da daukaka, addu'arta
a ko yaushe Allah ya kubutar mata da maigidanta ya kuma
daidaita tsakaninsu.
Karo na biyu ke nan tana taka rashin sa'a tare da
barwa baba mai gadin sallahu gurin aminin mijin nata,
sakon ba ya isa gare shi ne ko ko menene? Ba ta da wata
hanyar da za ta sadu da shi face dai ido-da-ido din.
62
ZAINAB KABIR BIROMAN
Ba ta gaji ba dai, da sanyin safiya ta isa gidan, sun gaisa tun kanta tambaye shi yake shaida mata wannan
karon ta taki sa’a. ta fito da kwarin gwiwa daga cikin motar bayan da ta gaisar da baba maigadin. dattijon kirki mai iya rike mutumein kansa ba kamar nasu sakaran maigadin ba,
tana so ta tambaye shi rashin isar da sakon ta ga Samcer din, tana kuma shakkun hakan. Zuciyarta ma sai ta fi
karkata ga sakon ya isa gare shi ya ki dai zuwa ne kawai ko
don yana jin haushinta ko kuma ma ya riga ya yi fushi da
ita, in tai la'akari da abin da ya gudana a kwanakin baya. A
nan jikinta ya yi sanyi, rashin kyautawa kam ta yi shi, to
amma babu gudu babu ja da baya daga abin da ta yi niyya, don haka ta yi shirin daukar duk wani laifi da za a dora
mata.
Sashen Hajiya Hindatu (Mahaifiyar Samir) ta nufa a
babbabn falon nata ta riske su, Sameer din da kuma mahaifiyarsa. Da fara'a ta karbe ta, "A'a Heedaya ce a
gidan namu?" Ni ce Momy ta fada gami da russunawa
Momy ina kwana? Lafiya lau Heedaya. Ta janyo ta taso, Zauna mana sai ka ce wata bakuwa, ya mutanen gida da Alhajin? Kowa lafiya Momy sun ce ma a gaishe ku. To
madalla haka ake so. Ta sauya zancen ki ci gaba da hakuri
da yardar Allah gaskiya za ta yi halinta nan ba da jimawa ba, mu dai kam mun shaida fanmu ba zai aikata wannan
mummunan aiki ba. Abdul mutumin kirki ne da ne na kwarai, dan haka ki kwantar da hankalinki ki ci gaba da jajircewa da hakurin nan da aka san ki wata rana sai labari. Kanta na duke tana sauraron nasihar gami da ambaton kyawawan halayyar maigidan nata.
63
ME GARI YA WAYA? 3
a
Jikinta ya dada sanyaya. wai me ya sa ne ta kasa
gane hakan tuntuni ne sai yanzu da lokaci ya riga ya kurc?
Na gode Momy. Ta fada a sanyaye. Ta kai dubanta gare shi
kansa na wani 6arin tamkar ma be san da wata halitta
wurin ba, ina kwana Sameer. Ta fada cikin raunanniyar
murya. Da alama ma bai son amsa gaisuwar ganin yadda ya
amsa a gajarce fuskarshi babu yabo babu fallasa kai ka ce
ba shi ne Sameer din nan mai barkwanci ba.
Shiru-shiru babu wanda ya ce da wani Rala tsawon
wani lokaci, fuskantar wani abu ta yi ko kuwa, mikewa ta
yi bari in duba kitchen na sama miki wani abin. A ladabce
ta ce, a'a Momy dama kin bar shi na riga na yi break na
fito. Uhim a yi haka bari dai ini je din. In ba so kike su o'oh
a tuhume ni da kasa bawa matarsu abinci ba. Murmushi ta
yi gami da sunkuyar da kai, shi ma murmushin ya yi to sai
dai da fitarta annurin fuskarsa ya 6ace. Shiru dai be ce mata
ba ita ma ba ta ce masa ba, kai ya yi ma kamar be san da
mutum a gabansa ba. Bai fasa daga abin da yake ba ya
kamımala tsaf daga karin kumallon da yake.
Da gasken dai bai san da itan ba, yunkurawa ya yi
da niyyar tashi cikin rawar murya ta ce, "Sameer ba ka ji
sakona bane gurin baba maigadi? Wane sako fa? Ya dube
ta. Ina ce ya gaya maka sau biyu ina zuwa nemanka har ma
na nemi alfarmar ya turo ka tun da muna ta samun sabani.
Kada kai ya yi, Auwoooo! Ina ce wani sako ne na daban.
A kaikaice ya dan dube ta rashin zuwa na na da nasaba da
rashin samun sukuni samakon wani babban gibi da ya shafi
rayuwata, abu mai matukar mahimımanci a gare ni da ma
duk wani mai kaunata. Sa kai ya yi sosai zai fita da sauri ta
ce. Dan Allah ka saurare ni Sameer abin da ke tafe ni da ke
64
ZAINAB KABIR BIROMAN
nan. Kamar ta sha gabansa saboda gudunkada ya subuce
mata a ganint a shi ne kadai mutumin da zai iya sada ta da
abin kaunar ta kana tauraron zuciyarta.
Agogon da ke hannunsa ya duba, kada kai ya yi ya
kuma kada kai, lokaci ya kure be sake ko duban ta ba ya tafi abinsa, tana Samcer, Sameer amma ko ya waigo ya
dube ta. wani irin abu ta ji ya tsaya mata a zuci, ta dade a
hakan har ma ba ta san san da hawaye ke zubo mata ba a
haka Hajiya Hindatu ta riske ta. A'a ya kuma haka
Heedaya? Ke da muke yaba miki wajen dakiya da hakuri, haba kar ki dada samu cikin damuwa mana.
Hannu ta sa ta share hawayen da ke zubo mata,
yauwa ki kwantar da hankalinki kin ji, shi mai gaskiya yana
tare da Allah. Mikewa ta yi na gode Momy bari na wuce.
Damota kika zo ne dan na ga fitar Sameer ay ce kun riga
kun yi salama ko? Eh Momy. Da na san ba jimawa za ki yi
ba ai da ya kai ki gida. ba komai Momy tare da driver
muke.
Tafiya take da kafafunta ba ta ko sha'awar shiga
motar domin direban daya kawo ta ta sallame shi tun kafin
shigar ta gidan. Da me za taji ne? me ya sa Sameere zai yi
mata haka? Me ya sa zai kasa yi mata hanzari? Shi ne kadai
mutumin da take ganin zai iya yi mata jagora, me yasa zai yi mata haka? a lokacin da take mutukar bukatar
taimakonsa, a lokacin da take matukar so da kaunar
abokinsa da nadamar abin da ta yi masa, so da kaunar da ta
ke jin zai iya fasa kahon zuciyarta. Duk inda ta kai ga son
su hadu da Sameer abin ya ci tura karara ya guje mata ya
ma mai da ita kamar wata sauna, ba ta yi fushi ba ba ta
kuma gajiya ba ta ci gaba da bibiyarsa.
65
ME GARI YA WAYA? 3
A yau dai sai ta yi mai gaba daya ta cimma sa a
ofis, karyarsa dai ya ce zai wulakanta ta a gaban jama'a,
dole ne ya mutumta ta ya kuma darajata ta in dai kaunar da
yakewa abokinshi ta domin Allah ce.
Ba ta ko saurari sakatariya ba da ta sha yi mata
shamaki, ko don rashin sanin matsayinta ne? ko ko wani
dalili ne na daban?
Kusan a lokaci guda suka shiga da sakatariyar.
Sakatariyar na wani irin huci tamkar ta fisgo ta a tunaninta
ire-iren 'yammatan da suke mu'amala da su ne tana
matukar kishi da jin zafin hakan, ita kadai ya cancanta a so
ta duk da ta fuskanci ba ta ciak wani daďa shi da kasa ba.
Yana zaune kan daya daga cikin kujerun da ke
ofishi a gabansa faffadan teburi ne mai dauke da tarin
takardu da alama aikin ya cunkushe mishi ko ko ba ya
ra'ayi ne? kanshi ya dago da zummar ganin abind ake
wakana a lokacin da Sera diyar Baburawa ke kokarin janyo
kafadunta, tsawa ya daka mata, ke wace irin sakarai ce ne?
in ce ko kanki ya motsu ne? kallon shi ta yi, da ke nake? Ya
tambaye ta. Cikin yaran nasara take shaida masa keta dokar
ofishin nasu da ta yi (shigowa ba bisa ka'ida ba) shin ba ki
san wace ce ba ne? kai ta kada. Shi ne za ki nunawa mutane
halin rashin da'a. Ya ja dogon tsaki, maza kama gaban ki
ba bukatar ganinki a nan.
Rufo kofar da ta yi ya yi dai-dai da fuskantar junan
su, ya rasa me zai çe mata sai kawai ya kau da kai, ita ma
kau da kan ta yi gami da tame fuska.
"Duk wani kuskure da dan'adam ya yi ya kuma
gano hakan har ma yake kokarin neman afuwa ya kamata a
tsaya a saurare shi a fahimce shiba wai a dinga guje masa
66
ZAINAB KABIR BIROMAN
ba. Kuskure ne na san na yi na kuma fahimta don haka ne nake neman tallafi daga gare ka ka sada ni da abokinka na nemi afuwarsa harma na bayyana mishi radadin kaunarsa da ke zuciy..."
Datse ta ya yi cikin fusata ya juyo ya dube ta, "me kike nufi ne? me hakan ke nuſi ne? ko kuwa makuwa kika yi-ne? to idan makuwa kika yi ki tsaya da kyau ki fahimta Sameer ne aboki kana dan uwa, masoyi ga mutumin da kika sha bayyana rashin kaunarsa a zuciyarki, wannan kalamai naki tamkar tatsuniya na dauke su, ya kamata ki rufe da kurunkus shi ke nan ta kare."
Numfasawa ta yi da niyyar magana, katse ta ya yi da hannu gami da kadamata kai, “ki yi hakuri ba ki da wani
abu da za ki gaya min, kun hada kai ke da saurayinki
domin kai shi ga halaka ya tafi ya bar muku duniyar ku sha kuruminku. A'a ya girgiza kai burinku ba mai yiwuwa ba
ne za mu yi iya bakin kokarinmu wajen tabbatar da gaskiya."
Hawaye ne ya zubo mata a lokacin da ta kama murfin kofar da niyyar fita, "Kazafi ko zargi kuskure ne wannan na ji na kuma saurari duk abin da ka ce sai dai bai zama dole na aminta ba, ka tsaya ka fahimta ko kada ka fahimta, ka aminta ko kada ka aminta wannan duk daya ne abin da na furta shi ne a zuciyata ba gudu ba ja da baya daga kaunar dan uwanka, ruwanka ne ka yi duk yadda za ka
dai
sasanta
daya mu, ruwanka ne kuma ka bijirewa hakan, kauna ce aminci ma daya ne, in dai aminci da kaunar nan gaskiya ne."
Kwakwalwarsa ta gama hautsinewa da kalaman yarinyar, tsawon yinin ranar zuciyarshi sai kai kawo take a
67
ME GARI YA WAYA? 3
tuanninsa ba wani ne ya jazawa dan uwansa wannan halin
da yake ciki ba face ita matarsa, ta kuma zo ta guje masa
har ma take sauraron mutumin da yake da yakinin shi ne
silar faruwar wannan lamari ga dan uwan nasa. Meye
dalilinta na dawowa daga rakiyar tasa? Me ya hado su? To
sai dai duk wannan tunani nasa yana rugujewa a lokacin da
ya hango kalamanta na karshe, gaskiya ne "Kauna da
aminci daya ne... in dai kauna da amincin nan domin Allah
ake yin su..." Wannan ya share ya kuma tunkude duk wani
zargi da ke zuciyarsa. Kuskure ne kam ya tabbatar da babu
wanda ba shi da irin nasa (wato a tsakanin ma'auratan).
Kwanaki hudu a tsakani yana nazarin abin yi, fushi
ta yi ko menene har yanzu dai ba ta sake ce masa komai ba,
bayan ko ita ta san abin da ke zuciyarta na daga kunci da
rashin sukuni. Duniyar ta rikice mata har ma ta rasa tudun
dafawa, ko ina ba dadi, ga fargaba da tsoron da ya cika
zuciyarta na hakkin mijinta muddin shi ko ita suka fuskanci
Ubangijinsu a wannan hali da suke ciki ba ma kamar ita,
hakika ta kasance daga masu hasara domin ta kasa yi wa
mijinta da aljannarta take karkashinsa biyayya.
Har cikin gidan ya shiga sashen Ambassador sun
gaisa tare da alhinin halin da ake ciki, sun jima suna
tattauna matsalar da ke gabansu, a kokarin da suke na
samun kwararren mai kariya (lawyer) da zai ci gaba da
kariya ga Waheed. Ba su gamsu da aikin da mai kariyar da
yake kare shi a halin yanzu ba, ganin yadda ake ta samun
nasara a kansu duk da kasancewarsa kwararre ne a wannan
fanni. Bayan sun gama tattaunawar ne ya tura a ka kirawo
Heedaya kamar yadda shi Sameer din ya bukata.
68
ZAINAB KABIR BIROMAN
Ta shigo rike da hannun mardiyya jikinta sakaye da yalwataccen hijabi, russuna wa ta yi ta amsa kiran mahaifinta kamar dai ko yaushe tana fuskantar rashin fuska daga mahaifinta tamkar ba dad din nan nata da yake shagwabata ba, har ma shi Sameer din ya fuskanci haka ya mike suka yi musabaha domin daman fitar yake harama.
Tana rike da hannun mardiyya ta gaishe shi, babu
wata fara'a tare da ita. Akwai yanayin damuwa da
fargaba a tare da ita bayan ramar da ta yi ba ta kara ce
masa komai ba illa sunkuyar da kai, yanayinta ya ba shi
tausayi, kai sai ya ji wani iri ma a zuciyarshi tare da
tuhumar kansa na rashina dalcin da ya gwada mata, ai
mace daman mai rauni ce.
Na zo ne domin neman afuwarki a bisa rashin
kyautawar dana yi miki, bayan ko Allah ne kadai ba ya
yini kuskure, don haka ina mai ba ki hakuri da kuma
alkawarin tallafa miki gwargwadon hali domin sabinta tsakanin da dan'uwana.
Wata irin ajiyar zuciya ta saki, na gode Sameer
abin da tun farko ya kamata ka yi ke nan ba ka yi fushi
da ni ba, na rasa yadda zan yi da rayuwata Sameer. rayiuwata na cikin wani irin kalubale ko ina babu dadi,
uhm shin yaya zanyi da hakkin dan'uwanka a bisa kuskuren da na tafka? Ka taimaka min Sameer ya fahimce ni na tuba na gane kuskurena, ba na fatan kara kwatanta abin da ya gudana. Na yi mishi ba dai-dai ba ni
na sani, shin ya za a yi mutumin da ka yi wa irin haka ka
nuna mishi kiyayya karara ya tsaya ya fahimci tsantsar kaunar da kake masa, kauna mai tsafta, kaunar da babu
69
ME GARI YAS WAYA? 3
algus a cikinta. Wallahi ina rantsuwa da Sarkin da ya
halicce ni ina kaunar dan uwanka da zuciya sahiliya,
hakika na dade ina jin wannan abin a zuciyata amma
shedan da sharrin zuciya sai su rinjaye ni. Ina neman
tallafinka Sameer ka taimaka ya fahimce ni, domin na
san kauna da amincin da ke tsakaninku. Ka taimaka min
mahaifana fushi suke da ni duk dai a kan hakan, kai
kanka ka fahimci hakan. Na rasa sukuni na rasa jin dadin
zuciyata Abdulwaheed kadai nake so, shi ka fai nake
kaunata a zuciya da gangar jiki baki daya, haka na kuma
fahimci shi kadai ne mutumin da yake kaunata da
gaskiya, ka mance da baya Sameer ka taimaka min.
Bai tari numfashinta ba har sai da ya bari ta
amayar abin da ke zuciyarta. Nasiha yake mata bayan da
ya gama kwantar mata da hankali da kuma nuna mata
martabar aure da sakamakon duk wanda ya wulakanta
sunnar ma'aiki. Ya ci gaba, "Don haka ina fatan hakan
ba za ta sake faruwa ba duk da cewa na san kowa ba zai
rasa nashi dan kuskuren ba, to amma zahirin gaskiya
kuskuren ya fi ta'allaka ne a kanki domin ke ce karama
ke kuma kike karkashinsa, to don menene za ki kasa yi
masa biyayya? Har ma ki dinga kebancewa da wani
namijin da ba muharraminki ba? wannan kuskure ne.
wannan kadai ya ishe ku gaba dayanku afkawa akan
musibar da za ku rasa kanta, aure sunna ce ta Ma'aiki bai
kamata a yi wasa da ita ba, har ma a wulakanta shi, abin
da ya gudana a baya ai ya ci a ce ya wuce sai kuma
kokarin shimfida managarciyar rayuwa, amma duk ku
70
ZAINAB KABIR BIROMAN
kuka ce a'a kuka kasa yi wa junanku afuwa, to yau dai ga ki a durkusite kina begensa a lokacin da shi kuma yake fuskantar hukuncin barin duniar dungurungum."
Kuka ta saka, dakatar a ita yu yi. "A'ah ba kuka za ki sa ba, ku kuka jawa kanku da aurenki saboda Allah
ki dinga sauraron wani kato to yau ga abir da kika janyo
masa, dominn ba na kokonto dar'uw a zai taбa aikata wannan mummunan aiki ba faee sn lahir."
Da sauri ta dube shi, “Kai na ka yı hasashen
haka?" ta ci gaba, "gaskiya ne ni kaina na dade ina hasashen haka har zuwa lokacin da wasu dalilai suka sa
na dáda gasgata haka." Ta dada tattara hankalinta,
"Sameer zan sa rigar aiki domin karyata zargin da ake yi
wa mijina domin ni kaina na yi imanin Abdul ba zai aiksta wannan ta'addanci ba. Abin da nake so da kai ka
yi kokarin sada ni da shi, ya tsaya ya fahimce ni domin ko meye ya ta'allaka ne a bisa goyon bayan da ya ba mu, domin in har ba mu fahimci junanmu ba ma iya samun nakasu. Abdul ya yi fushin da ni ni na san haka, sakamakon shaidan da ‘yan kanzaginsa da suka shiga tsakanin mu, musamman da yake akwai abin da ya gudana a tsakaninmu a ranar da abin zai faru, na san
wannan kadai ya isa ya rike ni, ni da kaina sai daga baya
ne na soma gano bakin zaren.
Kamar yadda ya alkawarta karo na uku ke nan yana ziyartarsa duk dai a kokarinsa na sulhutan su amma
ya tsaya ma ya saurare shi koya fahimce shi ina. Duk da cewa ganin nashi ba abu ne mai sauki ba da kuma rashin
71
ME GARI YA WAYA? 3
isasshen lokaci. Duk wata kafiya da tarin kai da yake
tunanin zai fuskanta abin ya fice gaban haka.
Daya bayan daya yakan kasance cikin tunanin
nau'in zaman da suka yi da yarinyar da irin rashin
ladabin da ta nuna masa, da kuma tsantsar kiyayyar da
suka gwadawa junansu, abu na karshe mafi kuma muni
matarsa da cikin wani wanin ma babban makiyinsa. Cuta
kam yarinyar ta riga ta yi mas ababu zancen afuwa a
tsakaninsu.
Yanayinshi kawai za ka kalla da zai tabbatar
maka da cewa ba ya cikin kwanciyar hankali, ya yi baki
ya rame ga kasumbar da ta cika fuskarsa, kai ba ka ce
Waheed din nan ne dan kwalisa ba.cikin sanyi-sanyi
amma akwai yanayin bacin rai a ciki yake yin furucinsa,
na vi mamakin haka daga gare ka ba, a matsayinka na
Kina dan'uwana, amma kake kokarin raina min
tunanina, a zatonka na sauya ne daga bigiren da nake,
yarinyar nan ta cuce ni ta kuma gwada min kiyayya ba
tun yau ba amma kuma kake kokarin mai da ni kamar
wanda bai san ciwon kansa ba, kaunar ganin ta ba na son
yi, ballantana har ka yi kokarin sada ni da ita. Ta cuce ni,
ta cuce ni, ta yi min babban gibi a rayuwata. Tahir!
Heedaya! Ba don komai zan so in fito ba, ba don jin
dadin wata rayuwa ba sai domin in dandana muku gubar
da kuka dasa min a zuciyata.
Katse shi ya yi, "Haba malam ka dinga adalci a
cikin lamarinka mana, shin in har Heedaya na da laifi kai
ba ka da shi ne? kai ne fa babba kai ne kuma jagora,
72
ZAINAB KABIR BIROMAN
wane irin zama ka yi da yarinyar nan? Shin menene ba ta
gani ba daga gare ka? Tsana da tsangwama da nuna halin
ko in kula duk kai ne amma a hakan ta jure ta yi hakurin
zama da kai har ma ka sanya ta cikin damuwa
sakamakon halin da kake ciki, in har ka amince ta nuna
sha'awar ta taimaka...."
"In kuma ban amince ba fa?" Ya tambaye shi.
Kallon shi yake ba shi da niyyar tanka masa, ya ci
gaba da fada, "In har sai yarinyar nan ce za ta yi silar
fitar da ni daga wajen nan to in dauwama a wajen nan, ka
je ka shaida mata tun da kai dan sako ne." fada yake
gami da fadar zafafan kalamai a gare ta da shi kansa
Sameer din.
Shiru ya yi har ya yi ya gama be fusata ba, ya bi
shi sannu a hankali, daman shi ba ma'abocin fushi ba ne
da kuma cewa shi ya fi kowa sanin matsalar. Kwantar da
harshe ya yi yana yi masa nasiha gami da jan hankalinsa
a kan kyawawan lafuzza. Shi daman gwani ne wajen
tsara magana, bai gushe ba har sai da ya tankwarar da
zuciyarshi.
Ya ci gaba, "Na sani cewa Heedaya ta saba maka,
to amma mu dauka cewa kowane bawa ajizi ne Allah
(S.W.T) ne kadai ba ya kuskure don haka sai mu yi mata
afuwa mu manta da abin da ya gudana. Abu daya ne
nake so ka fahimta a wannan lokaci yarinyar nan tana yi
maka kauna ta hakikatan, ba na jin in ba ta kaunarka za
ta shiga wannan halinda take ciki, ta damu ainun fiye da
zatonka. Ka san lamarin Ubangiji babu abin da bai iyawa
73
ME GARI YA WAYA? 3
shi mai iko ne a kan komai a kuma lokacin da ya so, don
haka ba abin mamaki ba ne ganin ta riski kanta a wannan
hali. Kamar yadda ka sani ne kiyayya ta kan juye ta
zama soyayya, ko da yake ko can bava ban taba daukar
junanku a matsayin makiyan juna ba lace dai wani dalili
da ya