bayanshi jikin kujerar me dauke da tayoyi
45
ME GARI YA WAYA? 3
uku, karkada kafafun nashi da yake shi ya bawa kujcrar
damar yin motsi tana dan jujjuya shi cike da nishadi da
kwanciyar hankali a hannu daya kuma yana busa sigari
cikin sigar kwarancewa da tsotsarta yayin da yake fitar da
hayaki cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ranshi a bace ya ci gaba da yi mishi kashedi gami
da jan kunne a kan ya fita harkar 'yarshi. lyakacin
kufuluwa wannan karon Ambassador Sa'ad ya kai dan
haka yake dankara mishi magana iya son ransa.
Ya ci gaba, "Yaron banza mara da'a masu lalata
tarbiyyar yaran mutane, in ban da rashin tarbiyya yarinya
da aurenta ka dinga bibiyarta kana hure mata kunne saboda
iyayenku sun kasa ba ku tarbiyyar da ta dace, har kuke
yunkurin lalata tarbiyyar yaran mutane?"
Yana jin shi yana sauraren shi niyyarshi ya yi ya
gama domin ya ji dadin mayar mishi da raddi, ko kusa ko
alama babu batun girmamawa a tsakaninsu domin shi ne
ummul aba'isin raba tsakaninshi da diyarshi don haka babu
batun ragayya a tsakaninsu, ya riga ya gama shirya mishi a
duk irin yadda ya zo masa.
A dai-dai lokacin da ya fara mayar mishi da raddi a
dai-dai kuma lokacin ne Heedaya ta iso domin cika
alkawarin da suka yi na haduwa a dai-dai lokacin a nan
ofishin nasa. Ja ta yi ta tsaya cak a lokacin da ta tsinkayo
kalaman masoyin nata.
Tahir din ya ci gaba da cewa, "A'a Ambassador
kada son kai da rashin adalci ya makantar dakai har ma ka
kasa hango laifinka a bisa tarbiyyar da ka kasa baiwa diyar
taka, ko da yake an ce laifi tudu ne...." Eh mana! In ban da
haka akwai rashin tarbiyyar da ya wuce macen aure da
46
ZAINAB KABIR BIROMAN
aurenta tana bibiyar wani can daban? uhm! Ambassador
akwai rashin tarbiyyar da ya wuce wannan? Shin ma meye
laifin Tahir a bisa amsa tayin abin da aka tallata masa?"
Tun kan ya karasa ya zaburo kamar ya rarume shi.
hannu ya sa ya dakatar da shi, "A'a Ambassador babu
batun duka a tsakaninmu, kamar yadda babu batun wata
ragayya da zan maka, tayi diyarka ta yi min na kuma amsa
tayin da aka yi min sai menene kuma?" ya ci gaba da
karkada kafafunshi gami da zukar sigarin da ke hannunsa
tare da huro hayakin da ke fita daga bakinsa cikin nishadi.
Ya dube shi cikin raini sannan ya ci gaba da cewa,
"Don haka ka kwantar da hankalinka Ambassador da zarar
na gama cin moriyar gangar ya da kwauren ba wani abin
wuyaba ne a gare ni, ko da yake kila da ka ba ni diyar taka
cikin daraja da mutumci da na yi jumurin rike kwauren har
na tsayin wani lokaci mai yawa.
Ya gama kaiwa bango, zuciyarsa ta gama kufula,
mari kawai ya sakar masa yana fadin, "Dan iskan yaro
marar mutumci da tarbiyya, ai ban san rashin tarbiyyar taka
ya kai haka ba."
Ai bai ko gama sauke hannunsa ba ya ji saukar mari daga yaron da bai fice dan cikinsa ba. Cike da mamaki da al'ajabi ya dube shi yayin da Tahir din yake a tsaye kikam
yana jiran wani hukuncin da zai kara zartar mishi, domin
samun damar daukar fansa.
Cikin abin da bai wuce dakika biyar ba ta faso dakin cikin wani irin rudani, kai tamkar ba a hayyacinta take ba, kansa kawai ta yo tamkar zakanyar da take cikin yunwa yayin da ta hango abin farautar ta mari ta sakar
masa ta kara sakar masa kai tamkar ta haukace, gaba daya
47
ME GARI YA WAYA? З
dukansa kawai take ta ko ina. "Na tsane ka, na tsane ka
Tahir, mahaitin nawa ka yi wa wannan wulakancin? Marar
mutumoi marar da'a da tarbiyya. Na tsane ka, na tsaneka
wallahi sai na ga bayanka."
Sai kuma ta zabura ta yi kan mahaifinta yayin da ta
zube akasan Kafafunsa tana neman afuwa, "Please Dady
please... please.... Ka yafe min ni na janyo maka ka yafe
min Dady....." Cikin tsanaki ya zare kafafunsa daga gare ta
ya dube ta da wani irin duba mai wuyar sha'ani, kai kawai
ya kada, "Ko menene ya same ni ko menene ya faru da ni
ke ce sila, abin da kawai zan ce inda kuka janyo a ka yi min
wannan Kasancin ke ma Allah ya baki dan da zai janyo
miki mafiyin wannan." Da fadin haka ya sa kai ya fice
vayin da ta ke dada neman gafararsa amma ko sauraron ta
be yi ba.
Kanshi ta juyo ta yo kansa cikin wani irin kujnar rai
yayin da ta rarumi katon teburin da ke gabanta amma ko
kafin ta ikai gare shi ya yi wuf ya cafke ta. Cikin
yandaramın kalamansa ya shiga fadin, "Please Heedaya.
plcase... me ya faru da ke ne dawo nutsuwarki Tahir dinki
ne masoyi mai son cikar burinki."
1
"Na tsane ka na tsane ka Tahir har abada ba ni da
makiyin da ya wuce kai jahili, dakiki da bai san martabar
iyayensa ba ballantana ma wasu." Hannu ya sa ya toshe
bakinta. "Daina fadar haka sweet heart, ba da son raina na
fadawa Dad wadannan maganganun ba har da ta kai da na
kai hannu jikinsa, na rasa yadda zan yi da raina ne. Dad har
yanzu ya kasa fahimtar irin azababben son da nake miki a
kulluyaumin shi yake kawo mana tangarda a cikin
lamaninmu. Ya za a yi ina ganin abu ya zo gangara kuma
48
ZAINAB KABIR BIROMAN
yana dada shirin raba tsakaninmu. Please.. Heedaya ki tuna da irin matsanancin son da nake miki, shekara nawa zuciyata ta kasa samun nutsuwa saboda rashinki, ina som ki Heedaya son da ban san iya adadinsa ba ki manta ki kyale Dad da ma duk wani wanda. kike ganim zai kawo mana tangarda ki zo gare ni Heedaya saboda kaunar da nake miki.
Fisgewa ta yi daga rukon da ya yi mata, hannu ta sa ta nuno shi da yatsa cikin matsanancin. bacim rai, "Mayaudari mai lalata tarbiyyar yaran jamaa, ka ji ka san ka kuma. fahinta, daga rana irin ta yau yaudararrun
kalamanka sun bar tasiri a gare ni na soka a cikin rashin
sani, yanzu kam na gode Allah da ya fahimtar da ni ya kuma kare ni daga sharrinka.
Ta juya: da niyar barin ofis din tana fadin, "Har abada ba na fatan Ubangiji. ya kara nuna min wannan
mummunar fuskar taka da tafi komai muni a gare ni.. Ni da kai haita-haihata Tahir, domin na tsane ka na tsane ka tsana
marar iyaka, ina kuma mai nadamar son da na yi maka a
cikin rashin sani." Daga yadda take furucin za ka san har zuci abin da take fadi haka ne.
Yana: ban hakurin amma duk a banza ko ta saurare
shi da gasken dai tafiyar za ta yi ta bar shi, tafiyar da ya yi imanin katse duk wata huda da ke tsakaninsu abadanabidina. Tana gab da kaiwa bakin kofa zuciyarshi ta shiga raya mishi, "Haba kai wane irin sakarai ne shekara da shekaru kana bibiyar yarinya tare da hidimta mata duk dam ka
maka
lallaba ta ka sami biyan bukatarka amma dare daya ta yi kwalelenka?"
ME GARI YA WAYA? 3
Haba bai san sanda wani karfi ya zo mishi ba cikin
matsanancin zafin nama ya fisgo ta jikinsa gami da
hankada kofar da kafafunsa da yake irin mai bamewar nan
ce nan da nan ta Game. Ta dube shi a tsorace yayin da shi
kuma yake kokarin hado ta da jikinsa, gaba daya ta firgice
idanunsa ya kada ya fita hayyacinsa babu komai a
idanunshi face tsabar rashin mutumci, kai gaba daya ma ya
sauya daga Tahir din da ta sani ya koma tamkar irin villain
(mugun mutum) din nan na American Films da take yawan
gani a cikin fina-finansu. Kokarin fisgewa daga gare shi
take yi, tana magana bakinta har karkarwa yake yi tana
fadin, "Na shiga uku, menene haka? Ka sake ni na ce ko an
gaya maka ina daya daga cikin yaran da suke siyar
damutumcinsu? Sake ni bakin mugu, azzalumi marar
tausayi."
Dariyar keta ya saka, "To da meсссе се? Кe da a
tunaninki meye marabar ki da yaran da kike ikirarin 'yan
iska ne? in ma akwai bambancin be wuce wannan ba." А
yayin da ya yi nuni da hannunsa. Ya ci gaba, "A yau pin
nan kuma zan kawar da shi sai in ga da mai kuma za a yi
tunkahon, tun da ina ne ban sani ba in ban da shi din?"
Ai ko karya kake macuci, dan iska kawai." Ta
fada yayin da take kokarin kwace kanta.
Dariyar ya dada sakawa, "Gaskiyarki yarinyar, ai
ko kin shigo hannun dan iskan da ba zai iya rangwanta
miki ba, sai dai fa kada ki mance yarinya iska ba ta da da
sai dai,fa 'ya'ya da yawa.
ta
"Karya kake." Ta mayar mishi da raddi.
"A'a gaskiya ne mana in ban da 'yar iska wacce ba
san mutumcin kanta ba balle na nauyin da yake kanta
50
ZAINAB KABIR BIROMAN
(aure) yaushe za ta dinga bibiyar wani katon banza can daban? Kina ganin yarinyar kirki za ta yi haka? Shin meye bakona a gurınki Heedaya in ban da wannan abun da a yau nake shirin kawar da shi."
Kuka ta saka, “Allah ya isa tsakanina da kai Tahir. ka cuce ni ban sani ba ashe kai tentirin dan iska ne mai lalata yaran jama'a." Sakinta yayi-a lokacin da ya watsa
wasu kwayoyi a bakinsa ya kora da wani abu da ma iya
cewa ruwa ne. Cike da nishadi ya cc, "A'ah kio se i, meye kuma wani bakon abu a gurinki in ban da shi waraen din." Cafka ya dada kawo mata yayin da take dada yoget
nesanta kanta da shi taku yake cikin nutsuwa da nmy yar cimmata. Gaba daya yanayinsa kamanninsa kai dama komai nashi ya canja kamanninsa ya koma kamar na wani rukakken dankwaya.
Kuka ta saka gami da neman afuwarsa. Dariya yake, Haba yarinya duk shekarun dana 6ata a kanki kina nufin su
tafi a banza? Haba yarinya, ni wane irin sakarai ne ko kina nufin in dau na damo (hakuri) in bar wa wancan sakaran abin da na dade ina tattalinsa ina kuma burin na mallaka a
yi min kwalelenka? Ta kowane fuska na kosa amma ina sharewa, to ba fa sharewar na yi ba ina nan ina jiran rana irin ta yau din nanne da zan wuce gajiyar abin da na yi shekara da shekaru ina dakonsa. Kan ta ankara ya rarume ta ya nufi cikin kuryar ofis din da ita, ME GARI YA WAYA? Tana kuka tana kururuwa amma ko ya kula musamman da yake ya ma fita hayaycinsa. To ko fita hayyacin nasa da ya yi ne sai fa zance rututu yana kwance kullin da suka kullawa mijinta.
51
ME GARI YA WAYA? 3
Ba tun yau ba tun farkon rikicinsu har kawo wannan
Kullalliyar da suka Kula masa da ba mai iya fitar da shi sai
ko Sarki Allah mai kowa mai komai, Sarkin da babu abin
da ya gagare shi. Cikin maye ne ko meye ya ci gaba da
fadin, sai kuma da komai yayi clcar mun rufe babin wancan
dakikin mutumin wannan old man din zai kuma wani kawo
mana cikas, ai Karyarshi ta sha karya dan haka na nuna
mishi ba komai ba ne, bai kuma isa hana abin da ni Tahir
na vi nufin aiwatarwa ba.
Ita dai kuka take tana Kokarin neman mafita, ko
dayake tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, to amma
a zahirin gaskiya za ka tausaya wa halin da take ciki. Kuka
take da kururuwa. Shi ke man ita rayuwarta a haka za ta
Kare? Wai shin ane ya janyo umata wannan masifar ne? wane
irin WAYEWAR GARI ranar ta yi mata ne? sunan Allah
kawai take ambata domin shi kadai ne Sarkin da zai iya
kawo mata agaji ya fitar da ita daga wannan musibar da
take ciki. Allah ya agaje ta wani inin Karfi ya zo mata cikin
matsanancin zafin nama ta rarumi kwalbar da ya gama kora
wasu kwayoyi da su ta rotsa a tsakiyar kansa, iba ta hakura
ba ragowar da ta yi saura a hannunta ta caka a tsakiyar
goshinsa. Ya yi taga-taga kamar zai fadi amma ya yi karfin
hali ya dada kawo mata raruma jikita ne kawai yake
makyarkyata tana tsaye tana shirin ganin ikon Allah amına
ina ko kafin ya kawo gare ta jini ta tsakiyar ka ta goshi ya
gama wanke masa fuska haka ya dinga reto yana layi har
zuwa sand a ya zube Kasa babu ko alamun motsi a tare da
sti
Ba za ta iya tabbatar da irin yanayin da ta isa gida
ba, a nude, a kidime ta har ofishin. Zazzabi ne, ciwon kai
ZAINAB KABIR BIROMAN
ne kai da ma meye ne ya dirar mata, ko ko tsabar tsoro ne
da razana? Ta dinga karkarwa tana makyarkyata, haka ta
kudundune cikin kuryar gadonta.
Tahir ya cuce ta ya gama da rayuwarta duk irin
soyayyar da yake gwada mata ashe ta karya ce? Wane irin
rashin sa'a ne da ita a rayuwa haka? Ta saba da iyayenta.
'yan uwanta kai da ma duk wani me kaunarta duk dai a kan
mutumin da take hangen mai kaunarta ne ashe ba baka ba
ne? ta bijirewa iyayenta duk dai a domin sa yau ga abın da
mutumin da take hange mai kaunarta ne wanda ta yi shirin
fito-na-fito da duk wanda ya kalubalance shi ya yi wa ba
ma ita ba mahaifinta, tabbas Tahir ba shi da fa a ba shi da
tarbiyya, sam bai cancanci zamantowa abokin rayuwarta ba
kamar yadda take bege a baya ashe ba haka ba ne, shin
ME GARI YA WAYA ne a tsakaninta da Tahir?
Tsoro ya dada kama ta bayan da ta tunano da
mijinta da kuma halin da yake ciki, wai duk a domin ta aka
Kula masa wannan makarkashiyar, laifi mafi girma, bawan
Allah bai ji bai gani ba. Wai shin ma meye dalilin tsana da
kiyayyar da ta gwada mishi a iya zamansu? Laift laifi ne
amma in aka yi dubayya laifinta ya shallake nashi ko banza
ya sunkuyar da kai domin neman sulhu amma ta nuna
hakan ba mai yiwuwa ba ne, dan menene ba zai kyale ta
ba? koma menene ai ita ta jawa kanta, ina ita ina fada da
namiji har ta dinga kokarin daukar fansa a gare shi? anya
yarinya mai tarbiyya za ta aikata haka? Gaskiya ne, gaskiyar Tahir da ya nuna ba fa shi ne kadai marar tarbiyyar ba, ina wata tarbiyya take a wajenta?
Ta shallake mijinta na sunna har ta tafi gurin wani
kato? Katon da ba ta ganin kowa da daraja face shi? To yau
53
ME GARI YA WAYA? 3
ga abin da ya yi mata da kuma abin da ya WAYI GARI a
tsakaninsu.
Ta cusgunawa mijinta ta bata mishi ta gwada mishi
halayyar rashin da'a duk dai a domin shi amma ya ya iya
da ita haka ya ci gaba da hakurin zama da ita, bai hana ta ci
ba bare sha kai ba za ta iya tuna wani abu na kyautatawa ba
da ta aiwatar mishi a iya zamansu. Kuka ya ci karfinta
lokacin da ta tunano sharrin da Tahir din ya kula nasa duk
dan ya bata tsakaninsu, in har soyayyar da yake mata ta
Allah ce zai yi mata wannan mummunan kazafi? Ciki!
Cikin ma da aurenka dole Waheed ya harzuka ya fusata ya
dankara mata duk irin maganganun da suka zo masa.
Tabbas sai bango ya tsage Kadangare ke samun
wurin shiga, hakika ba ta da wani abu da za ta-kare kanta.
Shin ta yaya ma za a yi ya amince mata bayan abubuwan da
idanunshi suka sha gane masa? Hakika ta cuci rayuwarta ta
jefa kanta cikin wata irin rayuwa me wuyar sha'ani, а
yanzu ne ta soma hango tarin illolin da t ayi wa rayuwarta
wai duk da sunan wayewa. To sai dai duk babbar
damuwarta a halin yanzu bai wuce mahaifinta da
maigidanta ba. da wane idon za ta fuskance su? Anya dad
dinta ya cancanci irin wannan sakamakon da ta janyo
masa? wane mahaluki ne zai iya fitar da mai gidanta daga
wannan kullalliyar? Shi ke nan shi da ita sai dai a DarusSalam. Wayyo wani abu ta ji ya soki kahon zuciyarta, so da
Kaunarshi da kuma tsabar tausayinshi ya soki kahon
zuciyarta.
Tana jin a zuciyarta tana yi mishi waniin so da baki
ba zai iya fadarshi ba, to sai dai kuma anya ba ta riga ta
makaro ba? anya kuwa ba ta yi nadama a lokacin da ba ta
54
ZAINAB KABIR BIROMAN
da wani anfani ba? mutunin da yake fuskantar hukuncin kisa. Kirjinta ne ta ji yana yi mata wani irin suya a lokacin da numfashinta yake shirin kai kawo sai shessheka take, alamun ciwonta na asthma yana gab da tashi. Sunkuye take gaban mahaifinta tana neman afuwarsa cikin kyawawan lafuzza da nuna nadamarta. In
dutse yanka magana to kuwa ma iya cewa Dad din nata ya tanka mata. Ficewa ya yi ya bar dakin yayin da abin ya daurewa Hajiya Kaltum kai.
Kan mahaifiyarta ta yi tana kuka, "Momi ki roka
min Dady ya afuwantamin bisa abin da na jaza masa, ko na
sami sassaucin zuciyata." Kuka take tana dada rokar ta. lallashinta take yi, "ki yi hakuri daina kuka, kukannan babu kyau. Wai shin me ya faru ne? wane abu kika yi wa Dadin
naki haka? Menene Heedaya? Tambaya take amma ba
amsa sai faman kuka take. Kai abu kamar wasa sai ga shi
an shafe makwanni biyu tana neman afuwar dadintaba tare dako ya saurare ta ba.
Yau ma durkushe take gaban Ambassador, fadi take, "na tuba na roke ka Dady ka yafe min ka afuwanta min, Insah Allahu za ka tarar da ni mai biyayya a gare ka a
dukkanin abin da ka umarce ni ko menene. Dady na sani ni ce mujaza don haka nake neman afuwarka, wallahi har abada babu ni babu shi (Tahir) kuma zan kasance mai biyayya a gare ka Dady."
Tsawa ya daka mata, "Bace min da gani, daga nan har duniya ta nade na ba ki izininki je ki aiwatar da duk abin da zuciyarki ta shriya miki. Ina gargadinki kada ki kuskura ki kara zuwar min da wani batu ko ma menene in dai ya yi miki ki jeki aiwatar, ni Sa'adu ban isa da ke ba
55
ME GARI YA WAYA? 3
ballantana in tsawatar miki a bisa wani abu da zuciyarki ta
riga ta kitsa miki.
Kuka ta saka yayin da Momy Kaltum ta tashi rai a
Бace, "A'a Alhaji wai duk me ya yi zafi ne? me yarinyar
nan ta yi maka ne ka dauki zafi da ita haka? Ko ma menene
yaro ba mai kuskure ba ne? illa iyaka a tsawatar masa ni
ban ga dalili da zai sa ka tsangwami yarinyar nan ba."
Tsawa ya daka mata, "Yi min shiru, daman na dade
da fuskantar ke kike dada lalata yarinyar nan take wa
mutane iya shegen da ta ga dama, in ban da haka na isa na
yanke hukunci har wani ya ce a'a saboda tsabar raini da
wulakanci? Wane irin rashin da'a ne yarinyar ba ta gwada
min ba? to bari ki ji kau da kara ba wani abu ne mai wuya
ba a gare ni, dukkanin ku zan iya sallama ku domin
rayuwar ba ta zame min dole sai da ku ba."
Cike da alamun mamaki ta dube shi, “A'a Alhaji sai
yanzu na fahimci inda ka dosa ka ce dai 'yan ba ni na iya
sun shiga sun fita suтuma sami biyan bukata. Ta kwalla
Kara, "Oh ni Karum 'ya za a raba da ubanta saboda tsabar
ketą da hassada." Wani kallo ya sakar mata haka dai, abin
da kika sanı ke nan asiri, asiri, magani, magani, get out, ku
fice ku ba ni waje. Ya fada cikin fusata: Hannu ta sa ta dafe
kirjinta yayin da ta shiga wani irin shassheka, zubewa
kawai ta yi a nan cikin matsanancin hali
Kwanaki shida ke nan da kwanciyarta ciwonta na
asthma ya tasar mata sosai amma abin mamaki har wannan
lokacin babu alamun kulawa ko damuwa daga wurin
Ambassador kai dai-dai da rana daya bai nuna alamun ya
san halin da take ciki ba ballantana har ya tauşaya wa
halinda take ciki. Wannan abu ya dada kona zuciyar Hajiya
56
ZAINAB KABIR BIROMAN
Kaltum lallai kam ‘yan ba ni na iya sun shiga sun fita har sun sami biyan bukatar raba tsakanin da da mahaifi. Don
haka Aunty Na'ima ta gwammace matsin da take ciki a
baya a bisa dai halin da take ciki a yanzu, cin mutumci da wulakanci babu wanda ba ta gani ba, gori da habaice- habaice kuwa tamkar ita ko iyayenta suka zo da talauci duniyar, to sai dai a duk halin da ta tsinci kanta ta kan yi hakuri gami da mika lamuranta ga Ubangiji.
Kwance take a cikin tsakiyar gadon mamanta,
tunani barkatai ya addabi zuciyarta, wai yau dadinta da yake mutukar kaunarta ne ya yi shakulaton Gangaro da ita,
be damu da ganin halin da take ciki ba ballantana ya tausayamata, ko da yake ta cancanci hakan, ko ma menene
ita ta jawo har Dad dinta mai kaunarta ya yi fushi da ita
haka. A wani 6angaren zuciyarta na mai dada nuna mata
kuskuren da ta aikatawa mijinta wanda aljananrta take karkashinsa. So da kaunarsa gami da rashin sanin makomarsa su suka fi addabar ta, wadannan batutuwa sus uka hadu suka cunkushe zuciyarta.
Ta kai hannu ta goge hawayen da suke zubo mata a
dai-dai lokacin daMomy Kaltum ta shigo. Kallonta ta yi cike da tausayawa ta dade a hakan sai kuma ta ja ta zauna gefen gadon da take kwance.
Cikin yanayin kuka ta shiga fadin, "Momy kin ki ki yi wani abu a kai, kin kyale Dady sai fushi yake d ani, ki taimaka min Momy ki roka min gafarar Dadyi ban taba tsammanin Dady zai juyan baya haka ba."
Kada kai ta yi cikin bacin rai, "Sai ya juya miki
mana tun da 'yan ba ni na iya sun shiga sun fita sun raba
57
ME GARI YA WAYAP 3
tsakaninku, ba tun yau ba irin abin da nake nuna muku ke
nan. Nime za a yi da kishiya.ne?"
Tarar numfashinta ita yi don fahimtar da ita, don ta
fuskanci Momin tata ta yi wa lamarin bahaguwar fahimta,
kai irin.cusgunawar da ake wa abokiyar zaman mahaifiyar
tasu ya isa haka. Cikin kwantar damurya ta shiga zayyane
mata abin da ke akwai ta kara da cewa, "Don haka Momy
ina rokon ki bar zargin Aunty Na'ima wallahi ayanzu ne
ma na dada fuskantar Aunty Na'ima sam ba ta da wani
mugun nufi a tare damu. Ni babban abin da ya fi damuna
bai wuce inin shamin da Tahir ya yi min ba a gurin Dady
wanda na san shi yake hange har ya kasa saurarona balle yа
tausayawa halinda nake ciki, Allah shi ne shaidata babu
wani abu da ya taba shiga tsakanina da shi ba kamar yadda
shi Dady yake zato a zuciyarsa, ba. Momy da mai zan ji
ne? ga Dadyna na fushi da ni, mijina ban san a wane hali
yake ciki ba, wallahi mom tun da abin nan ya faru nake
nadamar rashin ibiyayyar da na gwada muku, na yi nadama
amma kuma Dady ya kasa fahimtar haka, wallahi Momy
ina son duk wani abu da kuke so kamar yadda a yanzu a
shirye nake na karbi duk wani hukunci da kuka zartar min.
Kuka ta saka, "Momy ki rokar min gafara gurin
Dad ina son mijina wallahi kuskure ne na san na yi shi
Mom."
Jikinta ya yi matukar sanyi har ma ta kasa furta
wani abu sai faman kada kai take yi. Ta yi karfin hali ta се,
"Lallai kam Heedaya dole dad dinki ya yi fushi da ke, ai ni
ban san abin da ya faru ke nan ba, wannan yaro kam ya
tabbata marar da'a, ko da yake ko meye ke kika jawo
58
ZAINAB KABIR BIROMAN
daman ni tun farko Allah ya sani ba na son yaron nan, to ba yadda za mu yi da ke ne Heedaya....
Ta katse ta cikin yanayin kuka, "A'a Mom akwai yadad za ku yi da ni man ku ne dai kika kasa nunamin haka. Momy ku yi hakuri ku gatarce ni amma ni na San na rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwata wato INGANTACCIYAR TARBIYYA, kila Momy da na sami tarbiyya kamar yadda addini ya tanadar da am fuskanci kaina cikin wannan yanayi ba. Duk abin da make so Mom shi fa nake yi ni kam ban so a ce haka rayuwata ta kasance ba. Ba ni da abin da zan ce Mom sai dai in ce ku yate min
abubuwan da na yi muku, hakika sai yanzu ne nake kaа gano halin rashin da'ar da na gwada muku ba daya ba ba biyu ba Mom an sha goranta min rashin tarbiyya da ke gare ni ina ganin cin zarafi ne ashe ko da gasken na rasa wannan babban inajingini na rayuwa.
Hajiya Kaltum dai ta rasa katabus sai zufa take gogewa, maganganun yarinyar sun yi matukar tasiri a
zuciyarta, ba fa tun yau ne ake nusar da ita a kan sakaci da tarbiyyar da suke wa yayansu ba amma duk ta sa auduga ta toshe kunnuwanta ta ki gaskiya. Nasiyar yayarta ke nan a
ko da yaushe amma saboda ita wata daban ce ta kasa fahinta, so da kaunar da take wa "yayanta ya makantar da ita komai. Lallai kam wannan ba gata ba ne face yin karan tsaye ga tarbiyyar 'ya'yanta. To sai dai duk da haka zahirin gaskiya Mamanin ba a kanta ya tsaya ba har ma da maigidanta kai shi ne ma da daukan alhakin kaso mafi tsoka na daga tabanbarewar yaran musamman ma 'yar lele
ya
Heedaya
ce ta
cika
da ko ita da ta