mu gajiya ba da sannu Allah zai bayyanar da gaskiyar magana. Ta dan numfasa, damuwata daya ce Sameer yadda Abbanku ya tsame hannunsa daga sha'anin yaron nan kana ganin tun da abinnan ya faru wane katabus ya yi? Hasali ma gaba daya ya zare hannunshi daga kan yaron nan, ina aka taba haka? Ai naka-naka ne ba ka da yadda za ka yi da shi, amma ji halin ko in kulan da ya nuna a kan yaron nan, sabida Allah ya kyauta ke nan?
17
ME GARI YA WAYA? 3
Momy a dai kara hakuri, kin san hakurin shi zai sa
a kau da komai a daina duban komai ma, kuma ma Momy
duk abin da ya dace dadin ya yi ga Abba nan (mahaifinsa)
da Abba Sa'ad (mahaifin Heedaya) na yi ki kawntar da
hankalinki kawai Momy da yardar Allah komai zai daidaita. Duk abin da suke tajna jin su ba ta dai tanka musu ba
tunaninta kawai tsabar rashin adalcin da ake son gwadawa,
rai rai ne kowa kuma na son abinsa.
Momy ta dade da tashi a wajen ba ta ce mishi
komai ba shi ma kuma haka yana dai nazarin abin da zai
gaya mata. Ya numfaa sannan ya dube ta, "Ya kamata ki
tsaya ki fahimci halayyar mijinki, ki san abin da zai aikata
da wadanda ba zai aikata ba. A tsawon zaman da kuka yi
na shekara da ‘yan watanni ai ya ci a ce kin fahimce shi,
dan haka saurin yanke hukunci banaki ba ne, kada garin
hanzari ki zalunci bawan Allah ki yi duba a maganata da
kyau. Shi dai Sameer shi kadai ya san ra'ayinta, saboda
sanin irin zaman da suka yi.
Ta dan muskuta gami da bata rai, ya kamata bawa
ya dinga adalci a duk lokacin da ya tashi aiwatar da wani
hukunci, kada son kai da son zuciya ya kai shi ga barin
hanyar Allah, gaskiya daya ce, duk wanda ya aikata wani
abu na barna ya kamata a zartar mishi da hukunci dai-dai
da laifinsa, babu batun dubayya ko sanayya a tsarin zartar
da hukunci, idan ma duk muka cire wannan meye gaminsa
da 'ya mace? Macen da ba muharramarsa ba a kuma guri
kefantacce? Gurin da galibi aikata 6arna ake a cikinsa.
Wannan ma kadai ai babban laifi ne don haka babu wani
hanzari da za ka kawo min, ka ma kyale ni da wannan
maganar baki daya. Babin mutumin kam na gama da shi ya
18
ZAINAB KABIR BIROMAN
fito kar ya fito be dame ni ba wannan ba a gabana yake ba lokaci kawai nake jira, lokaci na cika ina jin ko an ki ko an
so dole a tsahirta min.
Ya fahince ta dan haka ya fusata ya mike yana
gargaya mata maganganu shi ma ko ta ki ko ta so idan
Allah ya yi nufin fitarsa ba me iya dakatarwa ita ba komai
ba ce ba kuma ta isa yin komai a kai ba. Ba ta ko daga kai
ta dube shi ba babu me hana ta iya amayar da zahirin abin
da ke cikinta, tsuntun da ya ja ruwa ai daman shi ruwa kan doka.
***** ***** *****
Yana takure a cikin cell aka yo mishi izinin fitowa
dakin da ake ganawa damasu laifin. Kafafunshi da
hannunshi daure da ankwa. Kai ya russunar gami da jin wani matsanancin kunya bayan da ya yi arba da surukinsa
tare da Abbansa (Dr. Salim Ibrahim) yana kokarin
russsunawa ya gaishe su amma babu halin haka kawai sai ya sunkui da kansa hawaye na zubo mishi. Abba na yi kuskure na aikata ba dai-dai ba, don Allah Abba ku afuwanta min, amma wallahi ba ni na aiakta wannan laifi ba, ya ma za a yi na aikata kisan kai? Hakkin rai ai ba abin wasa ba ne Abba. Sai kawai ya saka kuka. abba ku nemar min gafara gurin Dady na san yayi fushi da ni Abba. Ba haka ba ne. Dr. Salim ya fada. Dadinka ya yi tafiya ne.... ya datse shi, "A'ah Abba kada ka kare shi ni na san Dady ya yi fushi da ni ne na kuma cancanci hakan." Ambassador a'ad ya shiga lallashina, ka yi hakuri Abdul ka kwantar da hankalinka da yardar Allah za ka fita
19
ME GARI YA WAYA? 3
daga wannan waje. Kai dai abin da nake so shi ne ka tsaya
a kan magana daya tun daka hakikance ka kuma rantse
mana da girman mahaliccinmu ba ka aikata wannan laifi
ba, to komai ya zo da auki, Insha Allahu Rabbi kamar ka
fita daga wajen nan ka gama.
***** ***** *****
Zaune yake ya yi zugum abin duniya ya taru ya yi
mishi zafi, yana jin yanayin rayuwar ya canja mishi, zaman
kadaicin ya ishe shi, tun tasowarsu kwanciyar bacci kawai
ke raba su a yau kuma ga ibtila'in da ya afkawa abokinsa
kana dan uwansa, ya damu ainuni har yanzun yana da
shakkun lefin da ake tuhumar abokin nasa to sai dai wacce
hiujjar zai yi tunkaho da ita a bisa kararrun shaidun da aka
bayyana?
***** ***** *****
Ta kassasnce cikin jmatsanancin hali, duniyar ta bi
ta yi mata kunci, an bi an takure ta haka siddan kuma a kan
mutumin da ya nuna karara a ya kaunarta, ba kuma ta
kaunar shi, in ban da rashin adalci a tsahirta mata mana ta
je ta auri zabinta abin kaunar ta Tahir mai so da kaunar ta.
mutumin da zai iya yin komai a domin ta (Lallai kam).
Kamar yana da masaniyar tunaninsa take a lokacin
sai jin wayarshi tayi sai da ta kullo dakin ta tabbatar ta sami
isasshen tsaro annan ta amsa wayar ba ta ce komai ba sai
kawai ambata sunanshi da ta yi cikin mutuwar jiki. Ya dan
gyara murya, "Heedaya." Ya kira sunanta. "Ina jin ka
20
ZAINAB KABIR BIROMAN
Tahir." Ta kara fada a sanyaye. "Ya kuma muka ji da
wannan fargaba?" uhm ta ce mishi. Ya ci gaba, "To Allah
ya kiyayc gaba, ina taso in kira to amma ina ta shakkun
halin da kike ciki dan ban san a wane yanayi kike ba. Ban
fahimce ka ba? ina nufin damuwar da kike ciki a bisa
wannan abu da maigidanki ya aikata na rahin kyautatawa
kin san fa mata da miji sai allah. Mtsss, ta ja dogon tsaki,
amma ko in wannan dalili ne ya sa ka kasa kira na ka
yaudari kanka. Haba! Kama cuce ni wallahi, meye gamingamina da wannan maketacin mutumin, mutumin da ba ya
kauna ta ko muskala zarratin, to me zai sa na wahalar da
kaina a kansa, Allah ma ya sauwake ya je can ya karata ko
menene shi ya jawa kansa.
Gaskiya ne Heedaya, mutumin nan ba shi da halin
kirki na riga na san halinshi, ina iya cewa a cikin
halayyarsa sam babu na zabe tun farko kuma irin abin da
na guje miki ke nan don mutumin nan babu abin da ba zai
iya aikatawa ba, yanzu saboda Allah ME GARI YA
WAYA? Haka kawai ana neman je fa kicin masifa.
"ME GARI YA WAYAR masa dai, ni kam da
alheri zai waye mini. Ta bashi amsa cikin fada-fada.
Gaskiya ne fatana ke nan Heedaya. To sai dai ya kamata ki
fahimtar da Dad, domin ya yi wani abu a kai dan gudun
kada a kuntata rayuwarki, na ji an ce kina ma can gidansu mijin naki dalilin ke nan ma da na yi hakkun kiranki, ban
ani ba ko kina ra'ayin mijin naki, da har kika iya tsallake gidan iyayenki kika koma nasu.
Maganar ta fan yi mata ciwo, ita marar zuciya сe?
To amma ai da gaskiyarsa meye alfanun zamanta a gidan
21
ME GARI'YA WAYA? 3
ko ko suna tunanin ko da tsautsayi ya gifta ya fito za ta
Kara komawa auronsane? Never. Ta ambata hakan.
Ambassador Saladi tarc da Dr. Salim Ibrahim suna
bakin kokarinu wajen kashe wutar rikicin tun kafin a kai
gaba. To sai dai abin mamakin duk wata hanya da za su bi
za swiske ta a kulle take babu wata mashiga lamarin kam
da ban mamaki kamar su dai din nan a yauma suna tare da
D C.O. Akwai tsanayya a tsakaninsu, dan haka suke
ayyana komai zai zo da sauki amma ina!
D.C.O. ya dube shi da girmamawa, "Yallabai kun
san babu abin da za ku nema a gurina ku rasa, mutukar ina
da damar hakan, amma abin takaicin shi ne duk wata hanya
da na san zan bia kashe case din nan na yi bakin Kokarina
a kai, amna abin takaicin na rasa yadda aka yi har case din
nan ya je State CID. a yanzu haka an yi reporting komai a
ranar uku ga watan gobe za a fara aiwatar da shari'a a can
Higher Court da ke titin gidan Zoo."
Dr. Salim ransa a bacc ya shiga fadin, "Amıma ina
mamaki fa, ya za a yi kana babba a wajen nan har case din
nan ya fita daga arkashin ikonka ba tane da ka sani ba da
mamakifa.
Ambassador ne ya shiga kokarin kwantar nishi da
hankali, "Ko ma mcyc dai ai ita gaskiya daya take. anukan
mumasu sonakamanta adalci ne, a je a yi shari'ar ai ga fili
man ga anai doki. Ambasador akwai wata a kasa. Yes. Ya
kada kai ina tabbutaumaka da haka. ewar Dr. Salim.
A rana ta darko da kotu ta zauna an fara gabatar da
laifin da ake tuhumar wanda ake zargi da aikatawa wato
lefin kisan kai tarc da kwararan hujjoji daga bakin
inspoctor da makarrabansa. Hujjojin masu kam ababan
ZAINAB KABIR BIROMAN
dubawa ne abin da ya yi mutukar tafiyar da hankalin ma- kallo gami da wadanda abin ya shafa a wannan zama na farko, masoya da 'yan uwan Abdulwaheed sun tash da
sanyin giwa, zahirin gaskiya babu wata hujja da za ku vi
tunanin kaworta da za ta share wannan. Abin duniya dai ba
ya buya musamman kam a wannan zamanin kan kа сe
kwabo labari ya gama watsuwa tamkar wutar daji, masA
taya su alhini na yi masu farin ciki ma na yi haka dai
alumımar murta ke a wannan zamanin. Kafofin yada labarai
une suka fara yaryada wannan labari. To fa abin ce-ce-kuce ya samu a gurin al'umma, musamman masu ana ar banza (Sa Ido).
Wannan rana kam ba ta wanye wa General
Abdallah da alkhairi ba, kar ka tona ka ji zuciyarshi
wannan yaro ya gama zubar mishi da kima da mutumci a
gurin al'umma, ya kuma gama kunyata hi a idanun jama'a,
a yau dan cikinsa ya jaza mishi wannan abin kunyar? Haka
nan abin yake gurin Hajiya Fatima da sauran 'yan uwanshi babu wani me sauran kuzari, damuwa kam suna cikinta, to sai dai ga Heedaya ba haka ba ne damuwarta be wuce shirin kuntatan da ake shirin Kara yi ba duk dan a raba ta da mai kaunar ta, abin da kan sa mutane suke tsamınanin tunanin damuwar halin da mijinta yake take yi bayan ko ba haka ba ne.
Tana zaune a falon kafafunta daya kan daya sai faman karkada su take, yau kam za ta ci kaniyar yarinyar gara ta nuna mata ta san abin da take aiwatarwa a kan zuri'arta, kamar yadda aminai da 6ata garin malamai
zancensu.
marasa tsoron Allah suka haida mata ta kuma yi amanna da
23
ME GARI YA WAYA? 3
Ta shigo jiki a sanyaye ko dan sanin kiran da wuya
ya wanye da alheri. Cikin ladabi ta sami waje daga Kasan
carpet ta zauna bayan ko ga 'ya'yanta nan dfare-dare kan
kujera. Shiru ba ta ce mata komai ba tana yi mata wani
kallon banza. Ta yi karfin hali, Hajiya an ce kina kira na
ko? Tambayata kike? Saboda ni sa'arki ce? To bari ki ji ko
mahaifiyar da ta tsuguna ta haife ki ba tsarar yi na ba ce
don haka ki shiga taitayinki. Ta ci gaba cikin daure fuska A
dangane da kiran da nake miki bude kunnuwanki da kyau
ki saurare ni, Kullun nan da kika kulla ke da iyayenki kika
saka surikina cikin masifa to ku je ku kwance shi tun kan
DARE YA YI muku kafin GARI YA WAYE.
Muddun ba haka ba kuwa zaman gidan nan sai ya
gagare ki ke duniyar ma baki dayanta, domin zan kulla
miki irin kullin da kika kullawa mijin 'yata, duk dan ku
jefa ni da zuri'arta cikin musiba, to karyarku ta sha karya.
idan har kun kwana a tafe, to mu asubanci muka yi. Tа
fahimce ta kuma fahimci inda ta dosa. Hawaye ne kawai ya
shiga zubo mata, ba ta yi kokarin tare su ba saboda bakin
ciki da takaici, wannan wane irin daukan hakkine haka?
Lallai hakika matar nan ba ta kaunar ta tun da har za ta iya
dunguma mata wannan dungumemen aiki, da mutumin da
ya rasa imaninsa ne kawai zai iya aiwatar da shi, ita kam
me ta yi wa wannan baiwar Allah ne haka?
Fa'iz da fa'iza da kuma fiddausi kannen Heedaya
duk suna falon ba su dai fahimci me mahaifiyar tasu take
nufi ba, abin da kawai suka sani Aunty Na'iman ba ta
kaunar su ba kuma ta kaunatar mahaifiyarsu, dan haka suke
kallon ta kuma suka rike ta da wannan matsayi a duk cikin
su babu me shiga huruminta. 24
ZAINAB KABIR BIROMAN
Tsangwama da kyara kam Na'ima tana han shi a
wannan gida, har ma ya zamo mata da gwanda yanayin
zamansu na da da ba ruwan wani da wani, duk da cewa shi
ma yana damun ta to amna gwamma shi ko banza ta kan
dan tsira da mutumcinta, sabanin yanzu da cin zarafinta da
ma na iyayenta bawani abu ba ne.
Hazika ce, makaranciyar alkur'ani dan haka a duk
lokacin da wata musiba ta same ta ta kan kasance cikin
karanta litttafin Allah mai tsarki tare da neman sauki daga
gare shi, abin da ba ta yarda ba faya ne, takai kukanta gurin
wani abin halitta face Sarki Allah me kowa me komai.
A duk daren duniya sukan shafe tsawon lokaci suna
tare da Tahir a waya a kullu yaumin yakan kara nuna mata
fifikon son da yake mata tare da dada ingiza ta a dangane
da bijirewa iyayenta muddun suka kafe suka nace suka ki
raba auren nan.
Yau ma kamar ko yaushe ya kira ta a waya, sai dai
fa yau hirar bamai dadi ba ce, tuntuni ya fara yi mata
wannan korafin, yanayin yadda yake maganar daga ji ka an
ba cikin dadın rai yake ba, ya ci gaba da korafi, haba
Heedaya na fahimci wasa kawai kike da hankalina, amına
ba wai kina nufin ki fito ki aure ni bane, son da kike
ikirarin kina yi min a baki ya tsaya, in ba haka ba zaman
me kike yi ne har yanzu idan har kin nuna da gaske kike ba
dole su sahale miki ba. Ko ko an taba ci gaba da aure da
matacce ne? ke kaai dai na gane mijinki kike so shi ya sa
kike yi min wannan wulakancin, ki daina ma yaudara ta da
wasu kalamai wanda ba haka ba ne a zuciyarki.
Lallashinsa take haba Tahir me ya sa za ka yi min
haka ne? kada ka zarge ni a kan hakan, da ka san kokarin
25
ME GARI YA WAYA? 3
da nake mana da ba ka yi min wannan zargi ba, haba dan
Allah ya kake so in yi ne?muryarta ta raunana alamun za ta
yi kuka, nan da nan hankalinshi ya tashi, sam ba ya kaunar
Gacin ranta ya na son Heedaya so marar iyaka. Ya shiga
lallashinta shi ke nan na fahimta, abin da kawai nake so da
ke komai runtsi ki dage ki cije a cikin satin nan takardarki
ta zo hannunki ki rabu da kallagaggen mutumin nan da aka
kakaba miki, mutumin da ba ya kaunar ka zai iya yin
komai fa a kanka.
Wannan kalma ta Tahir kam ta tsaya a zuciyarta,
lallai mutumin da ba ya kaunar ka zai iya yin komai a
kanka, kai kila ma wata rana a WAYI GARI babu ita a
duniyar kai Allah ne ma ya cece ta a hannunsa. Mutumin da
ya aikata kisan kai meye kuma ma ba zai iya ba? wannan
huduba kam ta Tahir ta shige ta, to sai dai ta rasa ta inda za
ta bullowa surukan nata, halin karamci da dattako kam sun
gwada mata suna kuma kan gwada mata, kai kila da da hali
ko kuda ba za su bari ya taba ta ba saboda so da kaunar da
suke mata. Wannan abu kam ya yi mata kiki-kаkа.
Hanya daya da take hange take kuma ganin tafi
sauki, shi ne ta yi duk yadda za tayi ia koma gidan
mahaifinta, ta bar zama a gidan mahaifan mutumin da ya
gwada mata kiyayya. Kai haba! sai ka ce wata mara zuciya
ma, ai ya zama dole ta bar gidan, in ya so ta san yadda za ta
yi ta karbi takardarta ko ta tuntubi iyayenta su kwance
wannan kulli da suka kulla ko kuwa ma ta je can gidan
kason da kanta ta kar6i takardarta, tun da ta san ba abu ne
me yiwuwa ba ta tunkari mahaifan ta da wannan magana,
ga dukkan alamu sun daina kaunar ta, sun daina son farin
cikinta, tun da har suke kaunar makiyinta. Kai ko da tsiya
26
ZAINAB KABIR BIROMAN
ko da arziki zama da kaddararren mutumin ya kare, ba ta
fatan ta riski kanta a nai yi mishi takaba. Takaba? T
tambayi kanta ta kuma kara nanata kalmar.
Gabanta ne ta ji ya fadi, wani irin tsoro ya tsuiga
mata, abin da ba ta gane ba shin takabar da ta ambata ce ta
bata tsoro ko komutumin da za a yi wa takabar. Karon
farko ta ji dama dai ya fito din in ya so kowa ya kama
gabansa. Ta rasa hanyar da za ta bi ta tunkari Momy Fatima
bare fa General a kan batun komawar ta gidansu.
A 'yan kwanakin nan ta kasance cikin rashin kuzari
ta kasance a kwance a koda yaushe babu wani kuzari a tare
da ita, daga haka sai ciwonta ya tashi, sannu a hankali sai
ga shi ta fita hayyacinta ta fada ta rame, abin kam ya soma
bawa Momy Fatima tsoro duk da kokarin da suke wen
samin warakarta akwai likitansu da yake zuwa ya duba ta.
Suna tare da General ta tunkare shid a maganar a
zahirin gaskiya Alhaji ina ganin mu mayar da yarinyar nan
gaban iyayenta, ni dai na tsora ta da larurar nan ta yarinyar
nan. Wani lokacin fa in ciwon ya tashi tamkar numfashinta
zai fice. Alhaji ina tsoron kada yarinyar mutane ta mace mana shin da wane ido za mu dubi idanun mahaifinta ko ko
me ka gani Alhaji?
Cikin fusata ya ba ta amsa, Tun da kin gama yanke hukunci ai sai ki dauke ta ki kai ta. Ya dada fusata wannan ai rashin tunani ne in da yaron nan ya kunyata ni a idanun jama'a
haka ba
haka
ne.
ke ma kike so ki kunyata ni? A'a Alhaji ba
fahimta
ya yi saurin datse ta, haka ne mana, na dai
kunnuna
bakinku daya da yaron nan tun da farko dama
iya raba
auren
ba kwa ra'ayin auren nan, to ki ji ki sani babu me nan mutukar yaron nan yana doron duniya.
27
ME GARI YA WAYA? 3
Momy Fatima ta kasance cikin tsaka me wuya tana cikın
tsoro da fargabar halin da yarinyar take ciki da kuma
tausaya mata a hannun da ya kuma Gencral din ya kasa
fahimtar ta.
Ga Heedaya dabara ta soma kure mata General din
ya ki ya ba da kai Momy Fatima kam ta san ta riga ta yadda
da lambonta a kulluyaumin Tahir cikin shirya mata
sabuwar dabara yake, likitan nasu tuni ya riga ya gama siye
shi dan haka dan kansa ya shawarei General a mai da
yarinyar gaban iyayenta ko tafi samun nutsuwa a halin
yanzu tsananin damuwar da take ciki ka iya haddasa mata
wani ciwon ciki har da ciwon ta na asthma da Gacin ran da
take ciki yake tayar mata da shi.
Kanta na sunkuve a falon General din tare da
Momy Fatima ya fara yi mata nasiha gami da ban baki, ya
ci gaba ki ci gaba da hakuri mijinki zai fito da yardar Allah
ba dan kowa na shiga maganar nan ba sai don ke, don haka
ki kwantar da hankalinki ki yi hakuri ki ci gaba da
jajircewa da addu'a ki bar damun zuciyarki kada wani
ciwon ya zo ya shige ki yanzu abin da nake so dina kin
kimtsa ga su Abdulwahab can su je su kai ki gida ki dan yi
musu kwana biyu a can, sai dai ba na so inji kina
cikindamuwar nan. Ungowannan karbi ki rike a hannunki.
Ya mike mata rafar 'yan naira dari biyar.
Sai ta ji wani irin, kai sai ta ji ma ba dadi jikinta ya
yi sanyi ta rasa ma me za ta ce sai kuka. Kuka?
Subhanallah! ba ki ji nasihar da na yi miki ba ne Heedaya
latlashi yake ita ma Momy Fatiman lallashi take.
Kuka take har ta je daki, cak ta tsaya da kukan
wayin da ta tuna da planning dinsu da Tahir wannan fa
28
ZAINAB KABIR BIROMAN
tamkar wani mataki ne na farko, a kokarin cimma burinsu da suke. Take zuciyarta ta saki duk wani kunci da damuwa
ya bar ta zuciyarta ta ware har ya zamo ba waniburi da take da shi da ya wuce ta auri masoyinta Tahir.
Abdulwahab din ne ya kai ta gida suka yi bankwana
cikin juyayi. Tabbas har ga Allah ta ji babu dadi a lokacin
rabuwar ta da ahalin gidansu mijinta to amma idan ta
tunano da masoyinta sai ta ji komai ma ya wuce. Karon
farko ta isa gidansu tun bayan faruwar lamarin.
ICE TUN YANA DANYE AKE TANKWARA SHI
S
un yi mutukar mamakin ganin ta har ma shi
Ambassador ya kasa boye damuwarsa, ummina in ce
ko lafiya? Murmushi ta yi, Dad ko na koma ne? na ce haka
ummina, shigo mana. Ta gaishe sulkamar dai yadda ta saba.
Derere ta yi a kan kujera babu wani batun russunawa, ko da yake babu lefinta haka aka koya mata. Tambayar dai ya fi
so ta amsa mata, Me ya faru ne na gan ki a gidan nan
Ummina? Wannan kayan kuma na inenene?
Idanunta ya dan yi rau-rau, Dady na komo gidan
mahaifina ne na gaji da zaman wucin gadi. Dady tun da farkona gaya muku iba na son mutumin nan, ba na son sa Dady, ni dai kam na gaji da wannan zama Dady ka vi magana su ba ni takardata ni kam ba na Kara komawa gurin
mutumin nan ko da ya fito.
Dady ni ban san me yasa tun farko ka hana ni zabina ba a gaskiya mutukar ba ka amincewa zabina ba ba
zan kara auren kowa a duniyar nan ba, Tahir shi ne zabina shi ne ra'ayina Dady.
29
ME GARI YA WAYA? 3
Sautin mari ne kawai kake ji ya fito daga fuskarta.
Ya nuno ta da tafin hannunshi, “Kin ci uwaki ke da Tahir
din, ashe yarinyar nan ba ki da hankali da aure a kanki kike
wannan rashin hankalin? To bari ki ji ke da wannan fan
banzan yaron har abada in ya so in mutuwa za ki yi ki mutu
sakaryar yarinya kawai."
Kuka ta dada sakawa, Wayyo Dady. na bani na
lalace, wallahi in ba ka amincewa aurena da Tahir ba zan
iya bin uwa duniya. Ni wallahi Tahir nake so ba zan iya son
kowa ba bayan shi. Na tsani mutumin na da kuka hada ni
da shi na tsane shi. bugu ya kawo mata. Ka ji yarinyar
banza, ashe ba ki da kunya? Yarinyar banza marar tarbiyya,
iyayenki kike gayawa wadannan maganganu saboda rashin
tarbiyva?
Bambami yake yana fada yayin da ita kuma take ci
gaba da kuka har da kururuwa. Ita kam Hajiya Kaltum ta
rasa ta cewa. Ta yi zugum ranta in ya yi dubu ya bacі,
domin ita ma din ta tsawatar amima yarinyar ta gwada mata
ba ta isa ba. Lallai kam yau ga ranar nan da ake jiye mata
ake kuma hanga mata ake kuma kokarin nusar da ita tun
kan GARI YA WAYE yanzu kam da GARI YA WAYE
mata ba su da yadda za su yi da ita, dama masu karin
magana na cewa, "Ice tun yana danye ake tankwara shi."
Abin duniya ya taru ya yi mata zafi ji take tamkar
daga turirin wuta ta fito ta fada garwashin wuta, sakamakon
shiga tsakanin ta da masoyinta da dad dinta ya kudurci yi.
Tana son Tahir tana yi mishi wani irin so da ba shi da
yaka. don haka tana jin cewa da ko waye za ta iya sabawa
in dai a kan Tahir ne. Tahir ne zabin ranta don haka shi ne
kadai mutumin da za ta iya soyayya da shi.
30
ZAINAB KABIR BIROMAN
A ko da yaushe babu wani sassauci a tare da ita.
tsana da kiyayyar mutumin ce a zuciyarta don haka a ko da yaushe cikin bujurcewa iyayenta take. Wannan abu kam na damun Ambassador.
Yana zaune ya yi zugun tare da mai dakinsa, cikin
yanayin bacin rai yake magana, "Ni kam na rasa wannan
hali irin na yarinyar nan, kafiya da taurin kai kamar me. Ka
haifi abu a cikinka amma ba ka isa ka tankwara shi ba, ina
sane da cewa a iya zamanta da yaron nan babų wani zaman
jin dadi da kwanciyar hankali a tsakaninsu, kullum cikin
aiwatar mishid a rashin kirki take mu ke nan kullum a tafe
wajen sulhu. Meye ba a yi wa yarinyar nan ba? meye take
bukata wanda na gaza yi mata? amma a ce yaro ya kafe a
kan ra'ayinsa ba zai bi abin da ka dora shi a kai ba. wannan
wane irin rashin albarka ne na yaran zamanin nan?"
Ta yi saurin datse shi, "A'a kar ka kai ga yi wa
yarinya baki mana, wannan abu sai dai mu yi addu'a
kawai."
A zahirin gaskiya Hajiya Kaltum ta soma fahimtar gaskiya face dai king askiya da son kai da ya rufe mata
idanu a ganinta wannan duk wata makarkashiya ce da abokiyar zamanta take kullowa diyarta ta karkashin kasa (sihiri) bayan ko ta riga