ya samu ya iso wurinta. Tauraruwa ta yi murna ta
kuma yi murmushi sannan ta yi tambaya ko shi Muhammadul
Ziyara ya je ga likitan nashi? Aka gaya mata ai ya riga ya gan shi,
kuma har ya yi masa irin aikin nan na ban mamaki, kuma a
wannan lokacin ma shi Muhammadul Ziyara yana iya tashi. To
saboda haka sai ta ba Muhammadul Ziyara tasbaha wadda ta ke a
ladaninta akwai hotonta.
Da ta ba wannan dan taliki wannan carbi sai ta gaya masa
kowane lokaci yake son ya sami dukiya in ya iso cikin taurari, to
sai ya nuna wa Lagwai-Lagwai wannan tasbaha, to za su kai shi
har wurinta. Ya yi murna kuma daga nan sai shi da wanda ya
kawo shi suka yi godiya suka tashi don su yi haramar tafiya gida.
Tauraruwa kuwa sai ta tambaye su don me ba su dauki 'yan
sandunan zinare da lu'u lu'u ba don ta tabbata za su iya amfani da
su lokacin da suka isa duniyarsu.
Nan da nan fa sai suka je suka daďdauki sanduna bibbiyu
na su wadannan karafa da ta gaya musu. Suka yi sallama da
Tauraruwa sannan suka yi godiya, suka je bakin kofa su
wadannan Lagwai-Lagwai suka taru suka bude musu kofa, suka
fita don su je su shiga jirgi su tafi gida.
50
Tauraruwa Mai Wutsiya
Suna isa wurin jirgin nan kuwa sai suka tarar da
wadannan 'yan mutane sun baibaye jirginsu, suna jira wai ko a ba
su abinci, ko kuma su huda jirgin su ga abin da za a tafi da shi,
don su suna takama da hakoransu babu abin da ba ya hudawa.
Nan take sai Muhammadul Sama ya ce da su da ma ya kawo
musu goronsu, ai abin da yake jira shi ne ya gama abin da yake yi
ne da Sarauniyarsu. Ya shiga cikin wannan jirgi ya dauko abincin
nan da suka dauko daga wani gida a daji kafin su fara wannan
tafiya tasu zuwa taurari. Ko da suka ba su wadannan LagwaiLagwai abinci sai suka sami damar ajiye kayayyakinsu a jikin
jirgin nan nasu, sannan kuma suka tashi sama ba da jirgin ba,
suka je wata tauraruwa da ke kusa da wannan inda shi
Muhammadul. Sama ya nuna wa Muhammadul Ziyara wurin da
ita Tauraruwa ke hutawa.
Watau shi wannan wuri cike ya ke da kanshi iri-iri kuma
ga.wani wuri kamar an shimfida wundi, to amma sai daukar ido
yake yi da wadansu launi-launi iri-iri, kuma ga wadansu matasai
dunkulallu, kuma kewayayyu masu taushin gaske ga mazurara,
watau. inda aka yi musammman don saboda ruwa ya rika
tsirarowa ta hanyoyi iri-iri don ya ba mutum sha'awa. Kuma ga
ainihin su siffar taurari sun kewaye shi wannan dan lambu mai
mazurara; ga kuma inda aka yi musamman don saboda ruwa ya
rika tsirarowa ta hanyoyi iri-iri don ya ba mutum sha'awa, ga
kuma ruwa na gudu a cikin wani dan karamin kogi wanda shi
kuma an yi shi da wadansu duwatsu ne farare masu kyalli da ban
sha awa: Wurin nan dai in mutum ya tsaya ya ce zai yi kallon shi
ne, sai har ya 6ace. Ita Tauraruwa ta ji labarin ga bakin da suka yi
sallama da ita can sun shiga wurin hutawarta. Saboda haka sai
suka sake tashi suka nufi ainihin inda jirginsu ya ke, kuma
Muhammadul Sama ya yi wa Muhammadul Ziyara alkawarin
cewa in sun sake komowa taurari zai kai shi sauran duk wuraren
alatun wannan yar talika.
Kafin su je su/shiga wannan jirgi nasu karfe daya saura
minti ashirin ta yi. Kuma karfe daya na yi wannan jirgi zai tashi
don ya koma Kasa. Suka dai shiga wannan jirgi nasu ganin haske
tangaran amma sun san kasa in sun sauka babu abin da za su gani
sai, duhu, domin wannan lokacin duniya dare ake yi. Bayan sun
shiga sai suka janyo tsaninsu sannan suka yi wa Lagwai-Lagwai
51
Tauraruwa Mai Wutsiya
sallama suka janyo kofarsu suka rufe, sannan suka shirya kamar
yadda suka saba. Suka dubi agogon nan nasu na cikin jirgin sai
suka ga sauran dakika goma sha uku su tashi. Daga nan ta hanyar
akwatin karbar maganarsu, sai suka ji ana tambayar su ko sun
shirya? To da tambayar ne fa sai Muhammadul Sama ya tuna
dadin kallon dazu ya sa sun mance da kayan da suka samu
tsaraba daga taurari. Nan da nan sai ya dauki abin magana ya ce
ba su shirya ba, suna bukatar minti biyar. To ya yi sa'a ya ji an cсе
an yarda. To daga nan sai ya yi maza ya bude kofa ya jefa tsani,
sannan ya sauka yana mika wa Muhammadul Ziyara ma'adanan
nan dai-dai da dai-dai, shi kuma Muhammadul Ziyara yana adana
su. Nan da nan da gama shigar da dukkan wadannan ma'adanai
sai Muhammadul Sama ya shiga wannan jirgi ya janye tsani,
sannan ya kintsa kamar yadda ya kamata.
saura dakika goma sha
a
Lokaci ya sake yi, watau ya rage
biyu sai aka tambaye su ko sun shirya, suka ce sun shirya
wannan lokacin. Saboda haka sai suka sake jin ana kirga kamar
yadda aka yi kafin su tashi, ana cewa sifili suka ji su sun tashi cul
daga birnin Taurari kuma garin Lagwai-Lagwai. Suka juya suka
lula suka yi kasa, mai zayyana na ta aikinsa yana ta zayyana
musu inda suka fuskanta. Can kuwa sai suka ga ainihin shi đan
dakin nan na kusa da inda suka tashi, kuma ga mutanen nan guda
biyu. Nan fa Muhammadul Ziyara ya yi hamdala da ya ga ga su
sun komo kasa lafiya, kuma sun narko wani niki-nikin kaya na
zinariya da lu'ulu'u. Can sai suka ji jirgin nan ya tsaya da
gindinsa. Ana bude musu kofa, to kafin su fita sai Muhammadul
Ziyara ya shiga tunanin yadda za su yi su fitar da wadannan
dukiya tasu, tun da ya san nauyinsu ba zai yi daidai da yadda su
ke a kan taurari ba.
SHAGALIN KOMOWA DAGA TAURARI
Ko da saukowar su, sai shi Muhammadul Sama ya yi
nuni ga wadannan mutane biyu, suka kuwa dauko wata mota da
ke tsaye a kusa, sannan suka zo aka tara mutane hudu kafin su iya
ciro wadannan sanduna na zinare da lu'ulu'u. Sannan da suka
zaro su duka sai suka saka su cikin motar nan suka lullube su da
wadannan tsummokarai suka shiga motar suka kama hanya suka
nufi birnin Sukarta inda ya ke akwai masu sayen irin wadannan
52
Tauraruwa Mai Wutsiya
ma'adanai suna amfani da su, kuma suna sayar wa ga wadansu
masana'antu, wadanda suke yin kere-kere da su.
Muhammadul Sama sai ya ba Muhammadul Ziyara wani
dan kullin zinare da ya kunso a cikin hankicinsa lokacin da su ke
a taurari. Ya kuma ce masa ya tafi gida za a kawo masa motarsa
ta kansa da direba wanda zai koya masa, tare da kudin da aka
samu na wannan kaya da suka samo daga taurari.
Muhammadul Ziyara ya yi godiya ga Muhammadul
Sama, sannan ya tashi sama shi ma kamar tsuntsu ya nufi gidansa
don ya je ya gaya wa jama'a cewa ya dawo daga taurari. Ko da
isar Muhammadul Ziyara bayan garin Karinda sai ya sauka ya
Karasa a kasa. Da shigarsa gari sai ya hango benen da ya sa a gina
wa mahaifinsa, abin ya ba shi sha'awa, sannan kuma ya gamu da
jama'a da yawa wadanda suka shiga rufa masa baya suna yi masa
barka da zuwa.
Bayan ya isa gida dukkan mutane sun samu sun yi masa
barka da zuwa, sai kuma da daddare aka ji ana aikin hanya. Ko da
Muhammadul Ziyara ya fita ya kama hanya, sai ya tarar ashe
mutanen Muhammadul Sama ne suke yin aikin hanya don saboda
har an riga an sayo masa wata zungureriyar mota, kuma ga
wadannan kudi da aka ba shi labari cikin wannan mota shake.
Abin ma ba don ya riga ya gogu da wuyar duniya da kuma ganin
arziki da dukiya ba, da watakila ya haukace. Aka yi ta aikin nan
har aka kai Karinda, watau garin su Muhammadul Ziyara, sannan
aka karasa har zuwa kofar gidansu da can wajen tsakar dare. Aka
ba Muhammadul Ziyara motarsa da direba da kuma wannan
dimbin dukiya da ya samo lokacin da ya tafi taurari.
Muhammadul Ziyara, ko kuma mu kira shi Kilba, tun da
yanzu ya dawo gida, tun da su sun san shi da wannan suna ne
kawai, ya sa aka shiga da kayan nan cikin gidan mahaifinsa,
watau Malam Musku, aka zuba su a wani bangajejen daki. Shi
kuma Kilba sai ya zo ya sami direba mai koya masa mota dare da
rana don ya samu ya rika 'yan kasuwancin, tun da ya riga ya sami
jari. Kuma shi ba mutum ne malalaci ba, bugu da kari ma shi
dukiyarsa ba ya same ta a cikin ruwan sanyi ne ba.
Kilba na cikin wannan koyon mota ne, sai wata rana ya
tuna da yarinyar nan tasa, watau Bintun Sarauta. Sai kuma ya
tuna shi banda ita babu wadda yake so a duniyar Allah, kuma ga
53
Tauraruwa Mai Wutsiya
shi a gidansa an matsa masa wai sai ya auri wata 'yar'uwarsa,
watau dai a yi musu auren zumunta, wanda wadansu mutane kan
kira, bata zumunta, watau idan bai yi dadi ba. To shi wannan dan
taliki sai ya cije ya kuma gaya wa tsohonsa cewa shi babu yadda
za a yi ya auri wata yarinya a wannan kauye nasu, tun da bai saba
da ko daya ba, sai dai a hankali ya sami wadda yake so.
Nan fa mutane suka shiga aikin nasu, sai zagin sa suke yi
suna cewa wai ai wannan yaron tun da ya ga ya yi arziki ba ya
ganin kowa da gashi, da ma me ake da arzikin dan matsiyaci? Kai
tun suna yi ba ya ji, har dai abin ya kai ga kunnensa. To amma shi
Kilba bai daina irin alherin da yake yiwa jama'a ba, ko da ya ke
an ce komai kirkin mutum ba ya kosar da jama'a. An ce kuma shi
dan Adam kayan Allah ne, ana kayansa yana kayan wani. To shi
dai Kilba bai matsa wa kansa ba, abin da ya ga dama shi yake yi
wa jama'a. Kuma ba ya wulakanta kowa, to amma kuma shi ba
ya yarda da raini, don kuwa in mutum na so ya rike kansa, to ba
ya zama wawa kowa ya raina shi.
Rannan dai sai surutun mutanen Karinda ya dami Kilba
na maganar aure, tun da har sai da aka shiga kawo masa sadakar
karfi da yaji, sai shi ko ya gudu don shi ya tabbata ba zai sami
zaman lafiya da yarinyar ba, tun da shi dai ba son ta yake yi ba.
Kuma ita din an kawo ta ne kawai don saboda kudi, in da bai sai
da ransa ya tafi taurari ba, har ya sami irin wannan dukiya ba, to
babu wani wanda zai san da wani taliki wai shi Kilba, ballantana
ma har a ba shi sadakar cikakkiyar budurwa. Da kuwa haka ta
faru ne, sai ya tafi gun Muhammadul Sama wanda ya dauke shi
suka tafi can birnin Malala kuma suka zama manema auren
wannan Sarauniya ta Malala.
Ko da isarsu babban birnin nan, sai suka tarar da ita
wannan yarinya har ta shirya musu abinci mai dadi sosai, da
sauran dukkan alatu, kamar su raye-raye da za a yi da kuma
wasanni da za a yi don baki. Da suka tambaye ta yadda aka yi har
ta san suna zuwa, sai ta yi dariya ta ce shi Muhammadul Sama
ba'a yake yi yadda har zai yi wannan tambaya tun da ya san
madubin garin Malala wanda in Sarauniya ta duba za ta ga
abubuwan da za su faru gare ta daga ranar da ta duba har zuwa
kwana bakwai.
54
Tauraruwa Mai Wutsiya
Kuma ta kara da tambayar Kilba ko ba ta tarbe shi ba
ranar da ya fara zuwa cikin birninsu? Bintun Sarauta dai ta yi
musu liyafa mafificiya, kuma tana ta duban Muhammadul Ziyara
da tunanin cewa lallai ya taho da wata magana mai haskaka
zuciya. Can fa Muhammadul Sama ya gaya wa Bintul Sarauta sun
fa zo neman aure ne. Ita kuma sai murna ta kashe ta, to amma sai
ta dan yi murmushi kawai ta tambaye su, ko neman auren wace
yarinya suka zo? Nan ne fa shi gogan ya bara, ya ce, a'a ai su sun
zo neman auren wadda suke magana da ita ne a wannan lokacin.
Sai kuwa ta ce ta yi murna, ai tuntuni take bukatar wannan abu,
kuma ita abin da take so kawai a ba ta kawunan kura uku
wadanda za su zamo su ne kamar sadakinta.
Kilba ko da jin cewa ita wannan mata babu abin da take
sha'awa sai kawunan kuraye uku, sai dariya ta kama shi, kuma ya
gaya wa Bintul Sarauta ta tashi su tafi tare da ita don a kashe
wadannan kuraye a idanunta ta gani, sannan a daura musu aure.
Suka kuwa tashi su uku, suka fita daga cikin wannan birni na
cikin ruwa, suka hawo tudu sannan suka nufi wani kungurmin
daji. Ko da fara tafiyarsu cikin wannan kasurgumin daji, sai suka
fara haduwa da mesa. To amma sai mesar ta kauce ta yi ta kanta,
can sai biri, shi kuma ya yi nasa wuri, suna dai ta haduwa da
namun daji iri-iri, sai can suka ci karo da kan mutum da kafafuwa
an cinye gangar jiki. Ko da ganin wannan alama kuwa sai Kilba
ya ce lallai wannan shegiyar na kusa da wannan wuri, wai ita har
cinye gangar jikin dan'uwanmu ta bar wa mai daji kai da kafa ko
shi ma ya dan dandana.
Abu fa ya ba yarinyar nan da Muhammadul Sama dariya,
suna kuwa cikin dariya sai ga kura ta garzayo a guje tana zawu.
Shi kuma Kilba babu abin da ya yi sai ya bi ta a guje, ya je ya
kama ta, sannan fa suka shiga murda dambe, suka yi ta murda
damben nan. Kilba na kayar da kura, kura na ramawa. Har dai can
Kilba ya samu ya yanke kan wannan kura ya kai wa Bintul
Sarauta, sannan ya gaya mata cewa wai a cikin wannan kurar
akwai 'ya'ya biyu saboda haka nan idan ya fede kurar ya fito da
'ya'yan nan da ransu, to zai yanke ya bai wa yarinyar nan sauran
kawunan biyu. Yarinya ta ce ko da ya ke dai ita ba ta bukaci a yi
haka ba, to amma duk da haka idan zai iya fito da su da rai to sai
ya aikata haka din.
55
Tauraruwa Mai Wutsiya
Kilba ya fara wannan aiki ke nan sai fa wadansu kurayen
guda biyu suka tasar wa taronsu, shi ma Muhammadul Sama da
ya ke dan kallo ne, sai nasa aikin ya same shi. Ita kuma yarinya
sai ta gudu tana neman hawa sama. Can fa Kilba da Muhammadul
Sama suka samu suka ci karfin wadannan kuraye, suka kashe su,
sannan suka kunshe kawunan uku na kuraye, suka daure suka
shiga neman Bintul Sarauta. Can kuwa sai suka gan ta a sama ta
kame duk ta cika da tsoro. Kuma ko da jin motsinsu sai ta fado
don tana tsammanin kura ce ta biyo ta. Da suka gan ta sai suka
dauke ta suka kai ta bakin rafi suka dan yayyafa mata ruwa ta
farfado, sannan suka koma ainihin birninta da wadannan
kawunan kuraye guda uku, suka ba ta domin cikon alkawari.
Sannan suka ce wa yarinyar nan a wannan lokacin suna neman ta
da ta yarda da a daura musu aure da Muhammadul Ziyara.
Da gama wannan bayani, sai yarinyar nan ta gaya musu
su tafi garin su Kilba, watau Karinda su ba da labarin wannan
aure, kuma su gaya wa jama'a su taru a kofar gidan Sarkin
Karinda da karfe goma sha biyu na dare don saboda daura auren.
Kilba da maigidansa sai suka tashi suka tafi daga birnin Ruwa
suka komo doron kasa, sannan suka shiga mota suka nufi Karinda
inda da isarsu suka shaida wa Sarkin garin cewa ga irin abubuwan
da aka shirya game da bikin Kilba. Nan da nan kuwa sai aka sa
Sankira ya bi gari yana ta shela cewa za a yi bikin shahararren
mutumin nan Alhajin Taurari a kofar gidan Sarki.
Gari fa duk sai ya dauka cewa, "To ga irin tsiyar nan yaro
ana ba shi sadaka amma yana tsallakewa, to ga shi za a yi daurin
aure da tsakar dare a maimakon da safe ko da Azahar. Watakila
ma aljana ce." Wadansu kuma suka ce ai daga sama zai yi auren,
wadansu kuma sun zuba ido kawai don su ga irin abin da zai faru.
Da tsakar dare kuwa sai Kilba ya ci ado, sannan kuma
abokanensa su ma suka hallara don su kai shi gidan Sarki. Can sai
Muhammadul Sama ya iso wurin Kilba, suka tafi gaba daya da
sauran jama'a, suka dunguma sai fada. Ko da isarsu da karfe
goma sha biyu daidai, sai ga iyayen amarya sun isa wannan gari.
Sarkin ya tarbe su, aka zauna aka daura auren Kilba da na
Summu'atu wanda ya ke shi ne sunan yarinyar na sosai. Da aka
gama daura aure, sai mutanen gari suka shiga nasu shagulgula,
sannan kuma iyayen amarya suka ba da sanarwa cewa za su yi
56
Tauraruwa Mai Wutsiya
musu gida a kusa da ganuwar Karinda. Sarkin garin nan ya yarda,
sannan sai kawai aka dinga jin ana keta iska ta sama sai ji kake
ana ta kakkafa dakuna. To kafin a yi haka dai sai ga kantamemen
gida ya tashi a bayan wannan ganuwa, ga lambuna da itatuwa
kamar an halicce su a cikin wannan gidan. Ga lantarki ya kama
radau wanda shi kansa su mutanen Karinda dai-dai ne suka taba
gani. Sannan kuma a cikin wannan gida ga abubuwa kamar su
famfo, su gadaje masu lilo, su fanka, su gadaje shiryayyu masu
shimfidu iri-iri, da dai sauran irin abubuwa da akan samu a gida
wanda ya cika gida ko a birni.
Gidan nan fa na dutse wanda ya ke shi ne na farko a
Karinda sai ya karfewa benen Malam Musku 'yan kallo. A
wannan dare dukkan garin Karinda ya tashi, babba da yaro, mace
da namiji, Sarki da talaka duk aka tafi ana ta kallo har gari ya
waye. Su kuwa su Kilba da matarsa suna ciki suna shan shagalinsu.
Kilba fa sai ya zamo rikakken mai arziki a kasar nan
tasu, duk ya bar samari 'yan'uwansa suna cizon lebe suna tunanin
me ya sa su ma ba su tagaza wani abu ba? Shi ya sa ma watakila
masu hikima sukan ce wai, "Da rashin tayi akan bar araha."
57
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels