kawai
sai jijiyoyi su hade. Da ma duk inda aka gutsura, sai ka ga jini ya
makale a jikin gundulmin, ba ya gangarewa kasa.
To bayan an gama wadannan aikace-aikace ne sai aka ce
Muhammadul Ziyara ya kwanta a wani gado don a karasa aikin.
Da ya kwanta sai aka kawo wata katuwar kwalba aka ajiye kusa
da shi, aka kuma kawo wadansu bututu sirara na roba aka
sassarkafa masa. Aka ce ya rufe idanunsa, ya rufe, aka tsaga
hannayensa guda biyu a daidai inda magudanar jini ta ke, aka
sassa wadannan bututan roba, to fa a wannan lokacin ne
Muhammadul Ziyara ya sami allura mai sa barci daga wurin
wannan likita. Ko da aka yi masa allurar nan sai ya shiga barci.
Sannan kuma da yin barcinsa sai likitan nan ya shirya yadda duk
jinin Muhammadul Ziyara zai kwararo ya koma cikin kwalbar
nan. Aka kuwa kwashe manya-manyan kwalabe biyu masu kama
da tulun ruwa, na jinin dan talikin nan.
Likitan nan da ya sami wannan jini sai ya zuba wa jinin
wadansu ruwan magunguna a ciki, sannan ya kawo wani irin
garin magani fari ya zuba, ya dai yi 'yan hade-hadensa ya gama,
sannan ya je ya mayar wa da Muhammadul Ziyara jininsa duka.
Ko da mayar da jinin nan nasa sai ya farka, ya tashi ya zauna ya ji
kuma kamar shi kansa ba shi da lafiya, wannan lokacin ne fa
likitan ya gane lallai shi wannan dan taliki ya sha wuya, saboda
haka sai ya je ya kai masa ruwan zafi ya sha, sannan kuma ya yi
masa allura mai sa karfin jiki.
Bayan wannan allurar kuma sai ya yi masa wata mai
kashe tabbai, ana yi masa wannan allura mai kashe tabbai sai ya
ga dukkan tabban da ke jikinsa hatta wadanda ya yi lokacin yana
40
Tauraruwa Mai Wutsiya
dan mitsitsi sun shafe, sai ya koma kamar wanda aka haifa a yau.
Muhammadul Ziyara sai ya tashi a kan gadon da aka yi masa aiki
ya je ya zauna wajen da Likitan nan ya ke. Likitan ya gaishe shi
sannan ya gaya masa cewa lallai bayan kwana bakwai babu wani
abu da zai gagare shi, kuma komai ya ga ana yi shi ma in ya so ya
yi, saboda haka babu abin da ya kamace shi sai ya samu ya nufi
hanyar garinsu ya sami hutu na ko da kwana shida. To daga
lokacin dukkan abin da ya so sai ya yi, kuma a cikin lokacin da yake hutawa ne zai san cewa lallai shi wannan garambawul da
aka yi masa ya yi daidai. Kuma dukkan man da aka sa in ya jika,
to shi ke nan sai ya shiga sha'aninsa.
Muhammadul Ziyara sai ya yi godiya kuma ya yi sallama
da wannan likita ya kama hanyar garinsu, yana mai mamakin abin
da zai faru idan wannan garambawul ya zauna sosai a cikin
jikinsa. Can kuma sai ya ji ma ai ko mene ne dai, to ai ya riga ya
gama ainihin abubuwan da suka kamata, kuma abubuwan da suka
rage masa kawai su ne zuwa gida ya ga mutanen garinsu da kuma
zuwa taurari. Maganar dawowa ko oho, shi dai in ya samu ya kai
ga biyan bukata, to ko me ya faru ya riga ya yi namiji a wannan duniya mai wuyar kamawa.
Muhammadul Ziyara na cikin tafiya sai ya hango wata
'yar bukka a gabansa. Gabanta kuma ga rijiya ga guga ga kuma dan gora, saboda haka ma sai ya ga cewa to me ya kamace shi in
ba ya yi maza ya je ya dauki wannan gugan ya debo ruwa a
rijiyar nan ya kuma zuba a cikin goran nan ya yi alwala kuma ya yi Salla ba? Nan da nan kuwa ya isa gindin wannan rijiya, ya
debo ruwa ya yi alwala, sannan ya yi Salla. To ko da gama Sallar,
sai ya ga ya kamata ya yi sallama a rumfar nan ya yi wa mai
wurin nan godiya, tun da ya haka rijiya, sannan ya ajiye irin wadannan abubuwan don amfanin jama'a.
Ko da ya yi sallama sai wani dan tsoho ya leko ya ce,
"A'a yaya ne dan samari, ko lafiya?" Sai kuwa yaron ya gaya
masa cewa shi yana neman hanyar Karinda ne, kuma sai ya ga
guga da sauran abubuwa har ya yi Salla, shi ne kuma ya yi zaton
lallai akwai mutum a wannan daki har kuma ya yi sallama don ya
gode masa.
Abin ya bai wa tsohon nan sha'awa na irin hankalin
wannan yaro har kuma ya yi mamakin irin son addininsa, saboda
41
Tauraruwa Mai Wutsiya
haka ne ma har ya sawa Muhammadul Ziyara albarka, kuma ya
kawo dukiya mai yawa ya ba shi, sannan ya ba shi mutane guda
uku suka taya shi daukar kayan nan, kuma ya ce su wadannan
mutanen za su kai shi har Karinda, watau garinsu.
Muhammadul Ziyara tare da mutanen nan guda uku sai
suka dauki kaya suka fara tafiya, suka kuwa yi ta yin sauri har
suka fada kan wata shahararriyar hanya wadda za ta kai su
Karinda. Suna fadowa wannan hanya kuwa sai Muhammadul
Ziyara ya gane hanyar kauyensu kuma sai ya shige gaba suka yi
ta tafiya, har suka kusa da wannan garin. A lokacin da suka kusa
da garin nan na su Muhammadul Ziyara wanda shi a garinsu an
san shi ne da Kilba, sai ya ce su wadannan mutane uku su je su
shiga Karinda su tambayo masa baffan Kilba wanda ya bar garin
tare da Kolin Koliyo, in an nuna musu shi, sai su ba shi wannan
kaya sannan su gaya wa baffan nasa cewa shi Kilba yana tafe.
Mutanen nan suka kama hanya suka isa gari, shi kuwa suka bar
shi nan yana zaune a gindin wata 'yar bishiya.
YA JE SALLAMA GARINSU
Ko da shigar mutanen nan cikin garin Karinda da kaya
niki-niki, sai mutane suka fara kallon su, wadansu kuma sai nuna
su ake yi da baki ana ta mamakin daga ina irin wannan kaya ya
fito? Wadansu irin 'yan karambanin nan sai cewa suke yi,
"Sannunku, ai ga hanyar gidan Sarkin nan." Su kuwa sai su kyale
su kawai. Can suka hadu da wani yaro dan saurayi wanda
shekarunsa za su yi kamar Kilba suka ce da shi, “Sannu samari,
don Allah ko ka san Kilba na Kolin Koliyo?" Sai wannan saurayi
ya ce, "Kai ku kyale wannan yaron banza wanda ya dauki ransa
ya makala ga abin da ba ya yiwuwa, ai ma yanzu mun san ya riga
ya mutu domin yanzu 'yan yara kanana ma ba za su san shi ba, ku
yi dai gaba ku tambayi Musku tsohonsa, tun da yana da jakuna
watakila zai iya daukar muku kayan naku." Su wadannan mutane
sai mamaki ya kama su, suka dai yi shiru da bakinsu saboda irin
wadannan maganganun banza da wannan saurayi ya fada.
Ba su yi nisa kwarai ba kuwa sai suka gamu da wani dan
tsoho yana saye da shudiyar riga rike da carbi yana ja. Yana
kuma tafe a dudduke, sai suka gaishe shi. Nan da nan kuwa ya
amsa yana mai fara'a kuma ya tambaye su ko su baki ne. Suka ce
42
Tauraruwa Mai Wutsiya
haka ya ke su baki ne, sai kuma suka tsaya shiru dukkan su, shi
yana mamakin su na sun gaishe shi, su kuma suna mamakin
yadda ya tambaye su ko su baki ne. Can sai ya ce, "Ai ba don ku
baki ba ne na san da ban sami gaisuwa daga gare ku ba, domin
mutanen garin nan sun mai da ni wani wawa, wai na rude, dana
ya bi wani aljani ya mutu ni kuwa ina nan ina ta yi masa addu'a
ya dawo lafiya. Abin dai sai hakuri su mutanen yanzu domin in
banda shakiyanci ba abin da suka tsare, babu tsayuwa da
sakankancewa da ikon Allah, sannan kuma lalaci da sharri da
rashin tausayi da son abu ya yi musu yawa. Sai dai Allah
Ubangiji ya kiyaye bayinsa."
Mutanen nan sai tausayi da al'ajabi ya lullube su, suka
dai yi kokarin sakaya wannan tunani da ya sarke zuciyarsu, suka
tambayi wannan tsohon ko ya san Musku mahaifin Kilba? Sai
kuwa tsohon nan ya ce, "Ai ni ne Musku." Ya kara da tambayar
su ko lafiya suke neman sa? Sai suka ce ai lafiya lau, sai dai ya
juya su tafi gida domin dansa Kilba shi ya aiko su, kuma ya ce a
gaya masa yana isowa an jima.
Musku fa dadi ya kashe shi, murna ta kama shi, nan take
ya yi godiya ga Ubangiji Madaukakin Sarki, sannan ba tare da
nuna wata razana ko gigicewa ba, sai ya juya yana jan carbinsa
suka nufi gidansa, yana mai imani ga Ubangiji da hakkakewa da
cewa kyakkyawar aniya ko yaushe takan sami hanya mai kyau.
Suka isa gida, aka shiga da kaya gida aka kuma sanar da mutanen
gida cewa Kilba yana zuwa. Aka kawo wa wadannan mutane
tabarma suka zauna, sannan aka shiga shirin yin abinci don baki.
Musku kuwa sai ya zauna a zaure yana hira da wadannan baki.
Shi kuma Kilba lokacin da aka bar shi a wajen garin nan
ashe ya kira Kolin Koliyo don ya zayyana masa ainihin irin abin
da ya faru kuma da irin abin da ya samo a hanya. Kolin Koliyo ya
ba shi zinaren nan da ya karba a daji lokacin da ya koma daga
sama, don kila zai so ya yi tsaraba da su. Sannan ya gaya wa
Kilba cewa su wadannan kayan yana iya amfani da su.
Bayan sun gama zancensu, sai Kolin Koliyo ko kuma
Muhammadul Sama ya gaya wa yaron nan cewa bayan kwana
biyar ya yi sallama da mutanen garinsu ya kuma tafi ya same shi
a bayan gari da yamma don su je su yi tafiyarsu. Kilba ya yi
murna da abin da Kolin Koliyo ya gaya masa, ya yi godiya
43
Tauraruwa Mai Wutsiya
sannan kowannensu ya kama gabansa. Kolin Koliyo ya bace, shi
kuma Kilba ya kama hanya ta shiga garinsu.
Ko da Kilba ya shiga garin nan nasu kuwa sai mutane na
ta mamakin ko ainihin Kilba ne ko kuma wani ne. Wadansu sai
su zo su tambaye shi don dai su ji kwakwaf, wadansu kuma sai su
yi ta kallon sa suna mamaki, wadansu kuwa sai su tuno da
lokacin da ya janyo musu aljani mai sunduki, sai su ce, "To Allah
ya kiyaye, ga wannan hatsabibin yaro kuma ya komo." Wadansu
kuma sai su sake duban sa su ga irin kayan da ya sa, sai su ce,
"Lallai wannan inda ya tafi din nan ba tafiyar tsiya ya yi ba. Mu
kuwa har da muna tsammanin ya mutu." Har sukan kara da cewa,
"Da mutum zai dage a yi tafiya ta neman dukiya ai ka ga da abin
ya fi mutum ya zauna jagwab a gida, yana neman na fura a wurin
wadanda suka dage suka yi aikinsu." Kai duk garin dai sai surutai
za ka dinga ji iri-iri. Shi kuwa Kilba kafin ya kai gida mutane sun
shiga rakiyarsa, abin ma ko kunya mutanen ba su da ita, da ana ta
zagin tsohonsa, to ga shi kuma yanzu sai yabon sa ake yi da
kwarzanta kokarinsa don a je a sami dan abin karyawa a wurinsa.
Yaron nan wato Kilba ya isa gida ya tarar da mutanen nan da
suka daukar masa kaya na zaune tare da tsohonsa. Ya dakata
tukuna ya gaishe da tsohonsa, sannan ya sallami wadannan
mutane da suka rako shi, suka yi tafiyarsu. Daga nan sai ya ce wa
sauran jama'a su koma tukuna yana so ya je ya yi wanka sannan
can bayan magariba in ya gama Salla, sai jama'a su zo domin su
gaisa.
A lokacin da kowa ya watse, sai manyan 'yan sana'ar
kawai aka bari, wato masu roko, su ne suka nace har da aka so a
kafa kida, to amma sai ya ce shi ba ya son kowa ya dame shi.
Kilba fa ya shiga gida mahaifiyarsa da dai sauran jama'ar gida
duk suka zo suka sake ganin sa don kuwa ya yi wani girma
saboda dadewa da ya yi rabonsa da wannan gari.
Bayan Kilba ya natsa sarai, sannan ya sami damar gaya
wa mahaifinsa ainihin abin da ya faru, mahaifin nasa kuma ya yi
masa godiya saboda dauriya da ya yi don ya sami abin da yake so,
kuma ya yi masa fatan ci gaba da dauriya, kuzari kuma da samun
amfanin abin da yake yi.
Kilba sai ya yi ta kyauta da riguna da zannuwa da
kayayyaki iri-iri, sannan kuma aka shiga gina wa mahaifin nasa
44
Tauraruwa Mai Wutsiya
wadansu soraye har ma da bene. Idan ko aka gama wannan ginin
to Malam Musku shi zai zamo mutum na farko da ya yi bene
wannan gari na Karinda.
a
A garin nan aka yi ta harka ana jin dadin kwazon wannan
dan saurayi, kuma har wadansu yara masu tasowa suka kuduri
aniyar ba za a bar su a baya ba wajen neman ilimi da sauran hulda
daban-daban na duniya. Kilba sai ya yi kwana biyar a kauyen nan
nasu, kuma ran na biyar din da zai tafi ya raba wa iyayensa
sauran dukiyarsa da ta rage, ya gaya musu cewa shi ba ya bukatar
ko kadan daga cikin ta don saboda babu wanda ya san abin da zai
samo a wannan fitar tasa.
Iyayen nan nasa suka kuwa cika da farin ciki, suka kuma
yi masa fatan alheri a kan dukkan abin da zai yi suka kuma yi
masa fatan dawowa lafiya. Kilba ya zagaya abinsa ya fita daga
garin nan ba tare da sanin jama'a ba, ya je inda ya kamata da ya
sami Kolin Koliyo, to amma sai ya tuna ya mance da zoben nan
da yarinyar nan tasa Bintun Sarauta ta ba shi, kuma yana bukatar
daukowa amma ga lokaci ya kure. To kamar wasa sai ya mika
hannunsa wejen fuskar gidan nan nasu, sai kuwa ga zobe ya zo.
Nan fa sai ya shiga tunani, ya ga cewa lallai watakila aikin nan da
likitan nan ya yi masa shi ya sa shi a irin wannan madaukakin
hali.
SUN TAFI ZUWA TAURARI
Ko da gama gane cewa aikin likitan nan ya yi, sai
Muhammadul Sama ya bullo ya kuma kece da dariya, sannan ya
ce wa Muhammadul Ziyara ko da shi yana tsammanin ba tare da
an yi masa aikin nan ba zai iya zuwa taurari? Muhammadul
Ziyara sai ya yi murmushi kawai kuma ya gaishe da
Muhammadul Sama kamar yadda ya saba. Daga nan ne fa sai
suka tashi sama, suka je suka sauka a wani gida kuma a cikin
dokar daji inda suka shiga gidan suka tarar da abinci a shirye.
Suka ci, sannan suka dauki wadansu wadanda aka sa su a cikin
wani irin kwano mai kyakkyawan murfi, suka fita abinsu. Da
suka fita kuma sai suka tarar da wani fili babba, kuma a gefe ga
wani daki, sannan a cikin wannan filin ga wani katon jirgi kamar
na sama, to amma shi wannan jirgin ba shi da fikafikai, kuma
kafafunsa kamar kibiya su ke, guda biyu daga wajen gindin. Wato
45
Tauraruwa Mai Wutsiya
kamar daga wajen inda dan tozon nan na bayan jirgin sama ya ke
ke nan.
Ko da saukarsu a wannan wuri, sai wadansu mutane biyu
suka fīto daga wurin suka gaishe su, sannan ne shi Muhammadul
Sama ya ce, "Karfe biyar to a lokacin kuwa wajen karfe hudu da
kwata ne, to ko da ya ce karfe biyar din nan, sai shỉ Muhammadul
Ziyara ya ga wadannan mutane sun nufi wani katon agogo wanda
ke tsaye da Kafarsa a kan kasa sun gyara hannuwan agogon sun sa
shi kan karfe biyar daidai.
To a wannan lokacin fa wani an shirya lokacin tashin
wannan jirgi ke nan wanda zai ga ainihin taurari. Daga lokacin
kuma sai shi Muhammadul Sama ya kama hannun Muhammadul
Ziyara suka je suka shiga cikin wannan abu mai kama da roka da
wata 'yar kofa Karama kuma wadda suka kama suka rufe.
Shi wannan daki yana kulle ne dukkansa yadda babu
iskar da za ta shiga, to saboda haka ne ma shi Muhammadul Sama
ya dauki wata irin 'yar jaka mai robobi da suka haďu da jikin
wannan jirgin ya saka a hancinsa ya daure, ya kuma nuna wa
Muhammadul Ziyara ainihin nasa abin shakar iskar. Ko da suka
daddaura wadannan abubuwa, sai kuma suka nemi kujera suka
zauna. Sannan kuma suka ajiye abincin nan nasu a cikin wata 'yar
kwasfa inda yake ko kwai aka ajiye ga alama ba zai fashe ba,
ballantana abinci.
Su kujerun guda biyu ne kawai a cikin wannan injin din,
kuma suna duban juna. Watakila don masu tafiya su rika samu
suna dan ganin juna ne. To a cikin wannan injin din har ila yau
akwai wani agogo daga can kolin wannan daki, kuma wannan
lokaci da suka riga suka shiga har suka zauna, lokaci ya nuna
karfe biyar saura minti ashirin da biyar ne. To da karfe biyar ta yi
kuwa wannan inji zai tashi don ya kama hanyarsa ta zuwa taurari.
Ainihin shi agogon da suka baro a waje shi ke aikata motsin
wannan injin din. A cikin shi wannan injin akwai wadansu injina
masu nuna irin motsin da wannan jirgin yake yi, kuma akwai
wadansu akwatunan magana da su mutane biyu, da suke kasa,
sannan akwai wadansu akwatuna na zayyana. Watau masu nuna
hoton inda jirgin nan ya nufa ta amfani da haske mai amfani da
karfin lantarki. Akwai kuma tsani guda daya a irin wanda a kan
nade din nan. Sannan ana iya ganin cikin wannan wuri ta amfani
46
Tauraruwa Mai Wutsiya
da lantarki, ko kuma ta bude sakata ta daya wadda 'yar
kankanuwa ce. Bayan ita akwai wata roba mai kaurin gaske
wadda ta jikinta ne ake iya ganin waje in ana cikin shi wannan
jirgin.
Su Muhammadul Ziyara na cikin zama a cikin wannan
jirgin sai suka ji an ce, "KU SHIRYA." Ko da jin haka kuwa sai
Muhammadul Sama ya kama wadansu 'yan igiyoyi na damara ya
daura a jikinsa, sannan kuma ya ce wa abokin tafiyarsa shi ma ya
faura a jikinsa sannan kuma ya ce ya daura, suka faura suka
natsa. Sannan suka duba agogo saura dakika goma sha daya, sai
can kuma ta akwatin nan nasu na karbar sako, sai suka ji ana
kirga kamar haka, "Tara! Takwas! Bakwai! Shida! Biyar! Hudu!
Uku! Biyu! Daya! Sifiri!" To da zarar fadin sifiri din nan sai
kawai suka ji sun yi sama cul!! Kamar an harba kibiya. Daga
waje kuwa inda suka tashin sai ka ce an yi gobarar gidan mai, sai
hayaki kawai suka bari na tashi bul,bul yana ta yawo a kan
wadansu kafafu inda shi wannan inji ke sauka.
Su kuma mutanen nan biyu sai suka koma suka sake tura
agogon nan suka kai shi kan karfe daya, sannan suka dauki waya
suka buga wa su 'yan Kolin Koliyon nan da suka harba su, ba da
daďewa ba cewa wannan jirgi nasu zai juyo ya komo kan kasa da
karfe daya na dare daidai. To da shi Muhammadul Koli ya ji abin
da aka ce sai ya ce wa Muhammadul Ziyara, za su yi 'yar tafiya
zuwa cikin taurari na 'yan awoyi kadan kawai don saboda shi
wannan jirgin ba ya iya wuce kamar awa takwas rabonsa da
doron kasa, kuma za su isa taurari kafin wannan lokacin da awa
guda.
Shi wannan inji sai cillawa yake yi kamar walkiya,
wadannan su kuma sai ganin irin abubuwan da suke wucewa suke
yi ta cikin zayyanar da ke cikin wannan jirgi nasu. Suna ganin
gizagizai da kankara wani lokaci, sai kuma sararin sama. Shi
wannan inji nasu na cikin tafiya sai suka fara hango taurari,
saboda haka shi Muhammadul Ziyara sai ya fara nutsawa don
saboda ya ga abin da ya yi ta neman gani tun tuni, kuma a
wannan rana ga shi ya fara hango su kuma zai shiga cikin su,
watakila ma ya sami wani abu a cikin su.
Suna nan dai cikin wannan jirgi nasu har suka ji ya tsaya
da gindinsa a kasa watau su wadannan kibiyoyi da ke gindin
47
Tauraruwa Mai Wutsiya
jirgin sun kafu a kan wata tauraruwa, suka duba kuma sai suka ga
wadansu irin mutane marasa Kashi, watau dukkan su ba su da
wata alamar kashi a jikinsu kuma ga su 'yan kanana kamar
'ya'yan tumaki, sai kuwa suka daina kallon ita wannan zayyana
din, suka kama kofa suka bude, suka kuma sa tsanin nan ya fada
kan ita wannan tauraruwa. Sannan suka kawo madubin ido masu
duhu suka sa don saboda ita wannan tauraruwar wai tana kusa da
rana fiye da duniya.
Ko da saukarsu a kan wannan tauraruwa sai suka ga ashe
katon wuri ne da kuma mutane masu zama a wurin. Shi
Muhammadul Ziyara wannan wuri bako ne a wurinsa, to amma
shi Muhammadul Sama da ma dan gida ne, saboda haka sai ya
kama tafiya kawai a kan irin wannan ta6o na zinare, sai shi kuma
Muhammadul Ziyara ya bi shi. To sai dai kuma shi ainihin
wannan wuri kafuwar shi da girman shi bai yi daidai da na duniya
ba, saboda haka sai suna jin su kamar karmami ne, wani lokacin
ma sai sun tashi sama. To shi Muhammadul Ziyara ainihin a nan
ne ya san aikin nan da likitan nan ya yi masa abu ne amintacce
kuma mai amfani a gare shi da taurari.
Ita wannan tauraruwa da suka sauka a kan ta sunanta
Auriya, kuma katuwar tauraruwa ce cikin taurari, saboda haka ne
shi ainihin Muhammadul Sama ya sauka a wannan tauraruwa.
Kuma ita wannan Auriya din tana da wadansu duwatsu guda
hudu bakake a kowace kwana tata, watau Gabas, Yamma, Kudu
da Arewa. Wannan kuwa shi ya sa akan hango taurari sun ba da
wadansu 'yan kusassari guda hudu, dalilin shi ne, dukkan kasar
wurin gwal ne, watau zinare, kuma akwai duwatsu hudu wadanda
su ke bakake ne, to idan rana ta haska tauraruwar, sai zinaren nan
ya ba da fal, mu kuma da mu ke a nan duniya sai mu hango
kyallin wannan dusa ta zinare da dan baki-bakin wadannan
duwatsu. Su Muhammadul Sama sai suka yi ta tafiya har suka kai
daya daga cikin wadannan duwatsu. Ko da isarsu sai suka fara
ganin mutanen nan Kanana marasa kashi, suna zuwa suna kama
musu jiki. Shi Muhammadul Sama ya riga ya saba, to amma shi
Muhammadul Ziyara sai duka abin yana ba shi tsoro, don saboda
yana cikin tafiya sai ya ga wani dan mutum ya saukar masa a
gaba lagwai, sannan can ya ji wani karami ya hau masa hula da
dai sauran irin su.
48
Tauraruwa Mai Wutsiya
Suna cikin gwagwarmaya da wafannan 'yan mutane wadanda sunansu, ko kuma mu ce kabilarsu ita ce LagwaiLagwai, sai suka iso kofar wannan katon dutse inda suka ga su
mutanen nan dai suna gadi. To amma ko da ganin Muhammadul
Sama sai suka dauko wani zandareren makulli suka shiga kikikikin bude kofa. Da budewar su sai kuma ma fi yawansu suka
dafe murfin, suka samu suka bude kofar. Ko da jawo kofar sai suka ga wadansu mutane biyu, kuma sun fito da wata irin hula mai kama da tauraro, suka bincika ko suna son ganin Tauraruwa
ne? Suka ce, "I.", har Muhammadul Sama ya fada wa wadannan
cewa shi ne ya iso tare da bakonsa.
Nan da nan sai wadannan mutane suka yi ciki suka fito
suka ce wai an ce su shiga. Suka shiga wani tankamemen daki,
sannan kuma aka rufe wannan gangamemiyar kofa ta karfe. Suka
nufi inda ita tauraruwa ta ke don su yi gaisuwa.
Ita wannan Tauraruwa wata 'yar tsohuwa ce wadda ita ce
ke da wannan garin, kuma duk wadannan mutane mayakanta ne, kuma ta yi wannan gida ne a cikin dutse, ta amfani da hakoran mutanenta ne. Ita ke ciyar da su kuma a yi musu komai da suke
so. Ko da matar nan ta hango bakin nan nata sai ta kori dukkan Lagwai-Lagwai da ke wannan dakin suka fita, suka shiga wani dan Karamin daki da ke cikin shi wannan din. Ko da suka isa
wurinta sai ta tashi ta yi musu barka da zuwa, sannan ta tambaye
su koTSRES sun sha wuya a hanya?
Muhammadul Sama ya gaya mata cewa ba su sha wuyar komai ba, to amma ya kawo bakonsa wanda tun tuni yake ta fatan Allah ya kawo shi taurari. Saboda haka ne ma ya ce to bari ya jawo shi wurin ainihin uwar taurari, kuma mai taurari, wadda saboda hasken dukiyarta da ta ajijjiye a cikin wadannan taurari ne aka sa wa ainihin su taurarin sunanta. Kuma ita ta ci gaba da
sarautar dukkan wadannan taurari da suke gani.
Muhammadul Ziyara ya yi mamaki kwarai na irin
wannan dukiya da wannan mata take da ita, domin ainihin a
wannan dakin hatta gadon da matar nan ke zaune a kai an yi shi
ne da zinare da lu'ulu'u, sannan kuma ko'ina a dakin sai hasken
wadannan karafa masu daraja kake gani suna jingine kawai
kamar ba a son su.
49
Tauraruwa Mai Wutsiya
Ita tauraruwa mace ce mai kama da 'yan Adam, tun da ita
tana da Kashinta ba kamar sauran jama'arta ba, kuma akwai wata
mata wadda suke tare, wadda take kamar ita ce ke yi mata abinci,
ko kuma sauran ayyuka da za su bukaci sauri don saboda su
Lagwai-Lagwai kowa ya san ba za su iya yin saurin girki ba. Duk
daben dakin matar nan zinare ne, sai ado da aka yi masa da
lu'ulu'u da azurfa, saboda haka mutum wanda ya ke daga kasa,
bayan ba shi da nauyin kirki, sai kuma ya yi kokari ya daddaga
don saboda kada ya fadi. Sai kuma su hauren giwa su kuma an yi
ado da su. To amma su wadannan duk lokacin da ake bukatar su
sai kawai a aika kamar irin mutanen nan Lagwai-Lagwai kan kasa
watan duniya inda za su sami giwa su far mata da cizo sai sun ga
sun kashe ta, sannan su yanke hauren su kai wa uwargijiyarsu,
watau Tauraruwa.
Bayan shi Muhammadul Sama ya bari sun natsa sai ya
gaya wa ita wannan Sarauniya cewa wannan da ya kawo ya zo ne
ya gaishe ta kuma ya sami albarka don saboda ya sha wuya
kwarai kafin