karamin daki, har ila
yau da na bahaya. Sai ya kunna fitila, ya yi alwala, sannan ya fita
ya koma ainihin dakinsa inda ya sami darduma ya shimfida ya yi
ta yin salloli, don shi dai kansa bai san ainihin ko wane lokaci ne
ba kuma ya dade rabonsa da yin Salla, sai dai ya yi iyakar yadda yake tsammani ake bin sa, ya yi roko ga Ubangijin talikai, sannan
ya tashi ya cire rigunansa. To amma ya bar wando da singileti,
takalmansa kuma ya goge su fyas yadda ba za su bata gadon ba. Ya dauko mayafi ya rufa ya kwanta shiru yana jiran barci ya dauke shi. To amma yana kwance din nan sai tunawa yake yi da
zancen nan na Muhammadul Sama inda ya ce da shi banda barcin
babu gaira babu dalili. To a dalilin haka ne ma ya ki cire takalmansa, yadda ko da wani abu zai faru cikin lokacin da ya ke
barcin nan, to zai iya tabuka wani abu daidai gwargwado. Shi
yana ta wannan tunani da sauran irinsu, gari kuwa ya yi tsit, babu
kukan tsuntsu babu na namun daji. Ainihin su kifi kuma da dukkan namun ruwa da ke karkashin wannan gari, ko dai ba su
da ikon yin wata mummunar kara, ko kuma a'a ita wannan shiyya
an yi ta ne yadda za a yi abin fake ruwa a karkashin ruwan nan a
ji shi a cikin wannan gari mai kama da birnin 'yan ruwa. Dakin nan da wannan dan taliki ya ke wato kamar a ce mutumin da ke Sakkwato ne ya tashi a cikin watan Mayu ya tafi
Jos, watau lardin Kuza inda yake akwai sanyi mai dan karen dadi,
to haka ni dai nake tsammanin shi yaron nan ya ji. Domin kuwa mutumin da ya ke busasshen dakin kauye ya zamo ya sami daki
19
Tauraruwa Mai Wutsiya
mai injin sanyayawa, to ai lallai ka tabbata wannan mutum yana
shan lagwada, bugu da kari kuma shi wannan mutum yana
tsakiyar ruwa ne, inda lallai kowa ya san a irin wannan wuri sai
fitila dare da rana. Bayan dukkan irin wannan alatu, ga kuma
dakin nan yana kanshin turare, wanda in mutum dai ya ci abinci
ya koshi ya ji kanshinsa, to lallai zai sake iya zama har sa'a goma
sha biyar bai sake kulawa da ya ci abinci ba domin kara koshin da
wannan turaren yake yi saboda kanshi. Sannan kuma sai ya sa
mutum ya rika wani irin rawar kai saboda lallai shi kansa ya san
ya sa turare na gari, ba na garari ba, irin wanda mutum zai sa ya
dan yi kusa da kai kanshin ya nashe ka, ka ji kamar ka zub da dan
abincin da ka dan ci.
Ga wata fitila kuma mai dan karen haske wadda tilas
kowa ya gan ka ya gan ka cikin ni'ima, domin ita kanta fitilar don
kyalli har ta fi fari, fari. Ta taga kuma idan mutum ya leka sai ya
hangi inda fitilar nan ta haska ruwa, ruwan kuma yana tafiya a
hankali kamar mutum ya je ya ce tsaya in taba ka sannan ka
wuce. Ga shi kuma shi wannan ruwan kamar an za6o shi ne
sannan aka kwararo shi wannan shiyyar saboda kyansa.
Muhammadul Ziyara na cikin kwanciya a cikin irin
wannan ni'ima sai can ya ji kamar an bude kofa, sai kuwa ya
farka, to amma bai bude idanunsa da 'wuri-wuri ba sai dai ya yi
lamo yana jiran ya ji abin da zai faru kuma, sai kuwa ya ga
ainihin Sarauniyar Birnin Malala ce ta shigo. Tana tafiya da kafar
nan tata kamar ba kasa take takawa ba, ga kayan da ta sa
wadannan korra da suka dace da ita. Ga fuskar nan babu hoda, to
amma ko makaho da zai shafa ya san ta kyakkyawa ce, mai
kyakkyawar kira, kuma idan da mutum zai lura sai ya ga a'a babu
irin ciye-ciyen mala'iku din nan a fuskar, babu 'ya'yan yayyaba,
babu tabo, kai fuskar dai kamar bayan gautan yalo, wanda ya
gawurta, kuma ya nuna din nan, watau wanda bayansa sulisuli ne.
Bintun Sarauta ta ratsa dakin nan tana tafe jikinta na
sheki ta isa gadon nan da wannan yaro ke barci, ta dan lamushe
zaninta daga wajen guiwoyinta ta zauna kyamas a kan gado, tun
da da ma ita ba jiki take da shi irin rugaggen nan ba. To amma
kuma ba ramammiya ba ce, ta dago 'yan hannayen nan nata, ga
su farare fat, kamar tun da Allah ya yi su ba su taba datti ba, ko
ma in ce kamar tun da aka haife ta, ba su taba yin ko da zufa ba
20
Tauraruwa Mai Wutsiya
balle su yi wata uwar dauda. Ta kuwa kama yaron nan ta shiga
waka tana cewa, "Raina ya canza, raina ya yi fari kuma ni kaina
na canza, sabon jin dadin ya zo mini, duka saboda masoyina.
To yanzu wane ne masoyina, in ba bako mai bakon suna
ba, wayyo ni kaina, zuciyata ta kamu kamuwa irin ta soyayya, to
ko shi bako ya zam ya sami bakuntata a cikin zuciyarsa, shi ne
abin da ke damuna."
Nan ne fa yarinya ta kai ga wannan wuri sai shi yaron ya
mike, shi ma da rana tsaka ya koyi yin waka. Ba gadon uwa balle
na uba, ya shiga cewa, "Yau ni na yi tarihi na kaina game da zuciyata, na yi matukar rudewa bisa wannan siffa taki, kuma
soyayya a gare ki ta rigaya ta yi saiwa, ta girma kuma ni kawai
abin ne da bakunta, sai dai a daure da halinmu na yanzu." Sai
kuwa yarinya ta yi ta mamakin yadda wannan yaro ya iya waka
har ta yi masa tambaya ko a ina ne ya koyi waka? Shi kuwa sai ya
ce mata ai ba wani koyo ya yi ba, a'a, ainihin kawai da jin tana
waka sai ya ji duk tsigar jikinsa ta tashi, ko da ta kai baitinta
kuma, sai kawai ya ji ya kama ci gaba da wakar. Yarinya ta ce masa to tun da shi ma yana da zuciya mai
kamar tata, a nan sai yaron ya yi wuf ya ce, "A'a, mene ne na
wani damuwa? Ai ni ina son ki ne kamar in cire kwakwalwata in
mika miki, tun da ya ke ko da ma da na fara ganin ki babu
tunanin komai a cikin kwakwalwata banda tunanin ki." Ita kuma
sai ta yi dan murmushi ta ce, "To kai bawan Allah idan ka ciro kwakwalwarka ka miko mini, to ni yaya zan yi ke nan a duniyar
nan ta Allah? Tun da ni duk lokacin da ka yi tunani na sai na ji shi
a cikin zuciyata, kuma na ji dan karen dadi. Kai dai yanzu abin da nake so da kai, duk lokacin da kake bukatar ganina, ga wannan zobe, ka sa shi a hannunka. Da ka cire shi daga hannunka, to zai
zamo sarewa. To sai ka busa, za ka gan ni na zo a duk inda ka ke."
Yaro zai karbi zoben sai kuwa ta dube shi ta yi murmushi
ta ce, "Haba amintaccen sahibina, bari mana in sa maka zoben ko
na rika tunawa da na sa maka zobe in ji dan sanyi-sanyi ko ba ka
nan." Sai kuwa ya ce da ita, "Ki yi hakuri ya abar kaunata, kin
san ina son ki, so mai dalili, kuma ina kaunar dukkan abin da kike
so, don na san a cikin soyayya babu kafar ki, ko kuma cuta."
21
Tauraruwa Mai Wutsiya
Yarinyar nan ta sa masa zobe, ta kama hannun nan da ta
sa wa zoben ta rungume, kuma ta sunbace shi. Can sai suka zauna
shiru sai kuwa ta ce wa yaron nan, "To sai ka kwanta ka huta sai
wani lokaci kuma mun sadu." Da ta gama magana sai ta shafa
hannunta na dama a kan fuskarsa, ya yi kamar zai yi magana
amma ina, sai barci ya fyauce shi, ita kuma ta tashi ta tafi fadarta
tana mai matukar tunani a kan yaron nan masoyinta.
Jimawa kadan sai Muhammadul Ziyara ya farka firgigi
daga barcin da yake yi. Ko da farkawarsa kuwa sai ya ji murya
irin ta Muhammadul Koli ta ce, "To Muhammadul Ziyara ga
lokacin da za ka sake kutsawa fagen fama inda za mu gwada ka
kafin ka sami biyan bukatarka." Yaron nan sai ya yi kokari ya
yunkura, don ya sauka daga kan gadon ya dauki 'yar rigarsa da
kuma sauran 'yan kayayyakinsa, to amma sai ya lura ashe ma ba
lokacin neman wadansu riguna ba ne. Ai ma a lokaci ko da
wando ne mutum ba shi da shi a jiki bai kamata ya tashi yana
neman shi ba. Dalili kuwa shi ne, da zarar kare maganar mutumin
nan, watau Kolin Koliyo, sai fa abu ya sake juyewa. Wuri sai ya
yi fayau kawai, dukkan kayayyakin da ke cikin wannan dakin ya
zamo babu komai sai kawai gadon nan da shimfidun da ya ke a
kai, da kuma shi Muhammadul Ziyara na kwance lamo a kan shi.
Babu daki balle a yi zancen su madubi, dabe, da dai dukkan
sauran abubuwa.
To, ko ina su ke? Shi ya yi tunani, to amma yana cikin
tunanin nan sai kuwa ya ga af, to shin ina daki da kayan daki
suka tafi ne, ko kuwa shi ne yake tafiya? Ko kuma dakin ne ya
kunshi Muhammadul Ziayara da gadonsa? Yaro ya lura ashe yana
kan gado mai tashi ne. Ga shi a kwance a kan gado, shi kuma
gadon da ya ke a kasansa akwai wani dan karamin inji wanda
yake taimakonsa tashi. To ko fa shi Kolin Koliyo ne ya ta da injin
din, ko kuma gadon mai aiki yadda ya so ne, shi ne abin da
Ziyara bai sani ba? Sai dai ya ci gaba da dudduba abubuwa
kawai. Amma wani abin ban mamaki kuma shi ne, ta yaya ne aka
yi ainihin shi wannan kinkimemen gado na hawan mutum biyu ya
fito ta wannan daki wanda 'yar kofarsa kankanuwa ce?
Kafin in ci gaba da bayanin irin wannan wuri da wannan
yaro ya kutsa, sai in tuno da wata 'yar magana da nakan ji, watau,
"Sama tantan, kasa tantan, tsakiya sarautar Allah." To a nan shi
22
Tauraruwa Mai Wutsiya
mutum da ne yanzu ake, "Sama wayam, kasa wayam, tsakiya
gadonsa, ko kuma mu ce Muhammadul Zaiyara a kan gadonsa"
To ai kuwa abin dai da kamar wuya gurguwa da auren nesa,
yaron nan in ya daga kansa sama ba ya iya ganin komai, haka
kuma in ya sunkuyar da kansa kasa, kuma in ma ya yi ta duban
kasa babu abin da zai faru sai jiri ya kama shi. In kuwa ya fadi, to
ina za shi ke nan? Ga Kasan babu kasa da ake takama da ita,
kuma ga iska mai dan karen sanyi sai busawa take yi, kuma don
tsananin sanyinta har tana karkada dan yaron. To abu dai babu
kama hannun yaro. Shi dai abin da ya yi shi ne ya dauki mayafi
tafkeke ya lullube jikinsa da shi. Can jim kadan ya fara tunanin
cewa wai yana jin yunwa, sai ya ga wani ringimemen tsauni
kamar rabin mil daga kansa, ya kuwa rufe idanunsa nan da nan,
sannan ya sake budewa. To amma ko da budewarsa ta biyu, sai
ya ga ainihin gadon nan ya nufi wajen tsaunin nan da shi, shi
kuma tsaunin sai karar yiwowa kasa-kasa yake yi. Yaron nan fa
ya rude, ya shiga yi wa gado kaimi da takalminsa kamar yana kan
jaki ko doki, amma ina! Ai shi wannan gado ya rigaya ya dukufa
ga zuwa inda ya nufa.
Yaron nan sai ya sake rufe idanunsa, to amma wannan
budewar da zai yi sai ya ga tsaunin nan ya kara sama, to da ya
kara sama kuma sai ya kama wuta, sannan ya sake yiwowa kasa,
abin dai gwanin ban al'ajabi, ga su a sararin Allah, babu kasa
balle a gudu. Shi ba rafi ke kasa ba, balle a ce a fada alabarshi a
haye da iyo. Abin na yi ne, sai yaro ya nisa, ya kuma shiga tunani
na ainihin yadda zai yi da wannan alakakai. Can sai ya tuna
zamansa a birnin Malala, ya kuma tuna da masoyiyarsa, ya ga
wayyo watakila ga shi ya kusa halaka, kuma shi bai gan ta ba. To
haka shi sha'anin so ya ke, ku dubi irin wannan hadari da dan
talikin nan ke ciki, to amma maimakon ya yi tunanin yadda zai
fita sai yana tunanin ainihin yarinyar da yake so. Can sai ya duba
zoben da yarinyar ta ba shi, ya nisa, kamar zai yi kuka, ya fitar da
rai a rayuwarsa. To can sai ya tuna da sunan da aka rada masa,
kuma da abin da Bintun Sarauta ta gaya masa game da asirin da
ke cikin kowane suna da shi Muhammadul Sunaye ya rada.
Nan take da tunawarsa sai ya daga kai sama ya dubi
tsaunin nan mai cin wuta ya kuwa kwala wa kansa kira, watau ya
ce, "Muhammadul Ziyara!"
23
Tauraruwa Mai Wutsiya
Sai kuwa ya ji amsa-kuwwa ta amsa masa kuwwar da ya
yi. Can kuwa a saman shi daga daya fuskar sai ya ga rafi makeke
ya tinkari wannan tsauni. To amma wani abin mamakin shi ne
kuma, ko da yake ga kogi ana gani, kuma har ya zo ya wuce ta
kan shi wannan dan taliki, ama duk da haka ruwa ko da kamar
kwayar zarra bai digo masa ba. Kuma ga shi ko ana ganin sa yana
ta kwarara. Wannan abu da yawa ya ke, shi dai zurfin ruwan nan
ya yi kamar ya shanye dukkan wannan tsauni maí cin wuta. To
saboda haka ne shi wannan yaron ya yi tsammanin cewa lallai
watakila wannan kogi shi ne zai kashe wannan wuta. Ai kuwa da
abin da aka yi ke nan, can sai kogin nan ya je ya auka wa wannan
tsauni. To me ka yi tsammani zai faru? Ka san ko garwashin wuta
aka watsa wa ruwa yakan yi kara cuu-u-u! To balle wannan
dingimemen dutse da kogi, sakamakon abin dai to shi ne babban
rugugi wanda ya hadu da kakkauran hayaki wanda ya turnuke
wannan kewayen wurin.
Yaron nan bai yi wata-wata ba, sai ya sake kiran sunan
nan nasa. Ya kuwa yi sa'a, gadon nan ya sake tashi da shi ya
shilla da shi ya yi sama, suka tsallake wannan tsauni. To da
tsallake wannan ne fa sai yaro ya hango wani gida na karfe yana
yawo a sama, da wadansu wayoyi sun lelleko daga cikinsa ga
wadansu karafa kuma sun fito daga samansa sun lula sun yi sama,
da suka dada yin kusa sai ya ji karar wani inji wanda bai taba jin
irinsa ba. A zuciyarsa sai ya ce, "Oho, komai dai ya zo ya wuce,
tun da na fice daga mummunar kuna, da rashin samun kabari, to
ai ni komai ya yi!
AN SA SHI AIKIN INJI
Gadon nan fa sai kawai ya nufi wajen gidan nan na karfe
da yaro. Kuma yana kai shi wurin sai ya ajiye shi a kan wata 'yar
farfajiya, kuma kafin ka ce kwabo sai wannan gado ya басе.
Yaron nan ya tabbata cewa shi wannan gado watau ya riga ya
gama aikinsa ke nan, kuma yanzu sai ya yi damara ya shirya tsaf.
Ya jira kuma ya ga irín abin da zai yi gwagwarmaya da shi
wannan wurin. Can yana cikin wannan irin tunanin, sai kuwa ya
wata fitila ja ta yi fal, ta kuma mutu. Sai can kuma ta sake
walkawa, sai ya ce. 'To yau kuma aikin nawa da gama na uku
babu ko da hutu sai in shiga na hudu? To amma ai ba komai, ai ni
ga
24
a
Tauraruwa Mai Wutsiya
ba zama na zo yi a wannan wuri ba, saboda haka bari in farka
daga wannan rarumi nawa, in gama abubuwan da suke gabana.
Wannan fitila ja kafin a yi haka sai ta face, wata kofa ta
bude, sai kuwa wadansu mutane suka fito cikin wadansu
kayayyaki na karfe su biyu, kayansu iri daya. Kuma dukkan su
suna rike da wadansu wayoyi a hannayensu na dama da na hagu.
Sannan kuma a bayansu ga wadansu irin jakunkuna na karfe sun
goya. Fuskokinsu duk a rufe, kuma ko tafin hannayensu duk sun
rufe su da safa ta roba, a daidai inda ya kamata hancinsu ya leko
sai wadansu wayoyi masu rufe da roba suka leko don su ba su
damar samun shakar iska. Ko da fitowar wadannan mutane sai
Muhammadul Ziyara ya dube su da kyau, kuma dai-dai, ya nisa,
to amma bai ce komai ba. Sai can kuma ya ji magana kamar ta
mutane, to amma ta surka da wata 'yar kara kamar dai daga
rediyo take fitowa. Abin da ya ji an ce kuwa shi ne, "Kai samari,
ka keta mana haddin kasa, saboda haka sai ka biyo wadannan
ma'aikata biyu ku zo cikin wannan gida domin a yanke maka
hukunci. Ko ka fara yin gwale-gwalen da za a sara maka."
Yaron nan, nan da nan ya tashi ya wuce gaba, wadannan
mutane biyu kuma suka bi shi, kamar ba mutane ba, sai tafiya
suke yi kamar wadanda su ke a sankare, su ba sa magana. Suna
jin abin da ake cewa, ba sa waige sai juyi, kuma su ba sa tausayi
ga mutum a kan dukkan aikin da aka sa su. Suka shiga wannan
gida, shi wannan yato babu abin da ya fara karo da shi sai
wadansu manya-manyan kwalabe cike da magunguna, da
wadansu dogayen tebura wadanda aka rufe samansu da wata irin
shimfida mai kama da siminti. To amma shi wannan yana kyalli
kuma yana da wadansu jefin baki-baki a jikinsa. Sai kuma
wadansu bututu tsukakku masu wani dan mariki, irin wadannan
kuwa akwai kamar talatin, sai kuma wadansu famfuna masu 'yan
Kananan daro a kasansu. Ga kuma wadansu 'yan kayayyaki dai
na karfe masu kama da jiragen sama. To daga can karshen dakin
da suka fara shiga sai ya ga wata siffa kamar ta mutum, sai dai
wannan baki ne, kirin kuma, babu alamar fuska ko wani abu, sai
dai kawai wata waya da ta fito wajen bakin mutumin. Daga
wannan siffar ce fa ya ji magana ta fito inda ya ji an ce, "Tsaya
nan!"
25
Tauraruwa Mai Wutsiya
Nan kuma ya ji kamar an kafe shi, sai kuma aka ci gaba
da cewa, "Ku wuce da shi daki na takwas." To a lokacin kuwa
suna daki na daya ne, inda ya ke babu komai sai kawai wadansu
`yan tarkacen kwalaben magunguna, saboda haka suka kama
hanya suka shiga faki na biyu, wanda shi kuma babu komai sai
ainihin kayan alatu kawai. Dabensa dai na katako ne wanda aka
shafe da mai, sai kyalli yake yi, ga wata irin shimfida mai dan
karen tsada da taushi an baje ta. A kowace kwana daga cikin
kwanoni hudu na wannan daki kuwa akwai wata irin bindiga
wadda ke hade da lantarki. Kuma da mutum ya shiga wannan
wuri ba tare da izini ba su wadannan bindigogin ba wai sai an
harba su ba, a'a, da kansu za su shiga harbin mutum. Watau su
wadannan bindigogin sun zamo masu aiki da kansu ke nan.
Akwai kuma wadansu 'yan kujeru wadanda su ke a kewaye da
wani teburin abinci da ke tsakiyar dakin, su kuma kowannensu
yana da wata waya wadda ta hadu da ita daga Karkashin
shimfidar da ke dakin, kuma idan mutum bai lura ba, to babu
yadda za a yi ya iya fahimtar cewa akwai waya da ta hadu da
wadannan kujeru.
Su ainihin wadannan kujerun kuwa an ce idan mutum yа
zauna kansu yana iya mutuwa ta fizgar lantarki.
Suka wuce daki na biyu, suka nufi na uku, inda suka tarar
da wadansu irin tsuntsaye manya-manya, masu gashin zinare, su
kuma wadannan kewaye su aka yi da wata 'yar katanga gajeriya
wadda ta kawo wa mutum kirji. An kuma shirya ta yadda duk
abin da ya tabi katangar, idan dai ba an riga an cire hade-haden
da aka yi ba ne, to in dai har ya fi wannan tsuntsun girma, to ka
tabbata zai ji an yi wurgi da shi. Da an yi wurgi da shi kuwa zai je
rijiyar same 'yar tsidau. Wato a saman fakin akwai wani lungu
inda cikinsa duk kaifafan masu ne, kuma zamowarsa kamar rijiya,
to amma a sama, shi ya sa aka sa mata suna rijiyar sama. Kuma
saboda wadannan tsinukan masu, sai ana kiranta 'yar tsidau, to
tuntube dadin gushi, kuma mutumin da ya gama sokuwa a rijiyar
saman nan in ya zo fadowa ba fa zai fado a kan daße ne ba. A'a
zai wuce kai tsaye ta wata kofa da takan bude da kanta ya yi kasa
iska ta wajajjaga sauran jikinsa.
Da suka wuce daki na uku kuma sai daki na huďu inda
banda macizai da duwu (bakar kunama) babu komai. Su kuma
26
Tauraruwa Mai Wutsiya
ne yanzu ake, "Sama wayam, kasa wayam, tsakiya mutum da
gadonsa, ko kuma mu ce Muhammadul Zaiyara a kan gadonsa"
To ai kuwa abin dai da kamar wuya gurguwa da auren nesa,
yaron nan in ya daga kansa sama ba ya iya ganin komai, haka
kuma in ya sunkuyar da kansa kasa, kuma in ma ya yi ta duban
kasa babu abin da zai faru sai jiri ya kama shi. In kuwa ya fadi, to
ina za shi ke nan? Ga kasan babu kasa da ake takama da ita,
kuma ga iska mai dan karen sanyi sai busawa take yi, kuma don
tsananin sanyinta har tana karkada dan yaron. To abu dai babu
kama hannun yaro. Shi dai abin da ya yi shi ne ya dauki mayafi
tafkeke ya lulluße jikinsa da shi. Can jim kadan ya fara tunanin
cewa wai yana jin yunwa, sai ya ga wani ringimemen tsauni
kamar rabin mil daga kansa, ya kuwa rufe idanunsa nan da nan,
sannan ya sake budewa. To amma ko da budewarsa ta biyu, sai
ya ga ainihin gadon nan ya nufi wajen tsaunin nan da shi, shi
kuma tsaunin sai karar yiwowa kasa-kasa yake yi. Yaron nan fa
ya rude, ya shiga yi wa gado kaimi da takalminsa kamar yana kan
jaki ko doki, amma ina! Ai shi wannan gado ya rigaya ya dukufa
ga zuwa inda ya nufa.
Yaron nan sai ya sake rufe idanunsa, to amma wannan
budewar da zai yi sai ya ga tsaunin nan ya kara sama, to da ya
kara sama kuma sai ya kama wuta, sannan ya sake yiwowa kasa,
abin dai gwanin ban al'ajabi, ga su a sararin Allah, babu kasa
balle a gudu. Shi ba rafi ke kasa ba, balle a ce a fada alabarshi a
haye da iyo. Abin na yi ne, sai yaro ya nisa, ya kuma shiga tunani
na ainihin yadda zai yi da wannan alakakai. Can sai ya tuna
zamansa a birnin Malala, ya kuma tuna da masoyiyarsa, ya ga
wayyo watakila ga shi ya kusa halaka, kuma shi bai gan ta ba. To
haka shi sha'anin so ya ke, ku dubi irin wannan hadari da dan
talikin nan ke ciki, to amma maimakon ya yi tunanin yadda zai
fita sai yana tunanin ainihin yarinyar da yake so. Can sai ya duba
zoben da yarinyar ta ba shi, ya nisa, kamar zai yi kuka, ya fitar da
rai a rayuwarsa. To can sai ya tuna da sunan da aka rada masa,
kuma da abin da Bintun Sarauta ta gaya masa game da asirin da
ke cikin kowane suna da shi Muhammadul Sunaye ya rada.
Nan take da tunawarsa sai ya daga kai sama ya dubi
tsaunin nan mai cin wuta ya kuwa kwala wa kansa kira, watau ya
ce, "Muhammadul Ziyara!"
23
Tauraruwa Mai Wutsiya
Sai kuwa ya ji amsa-kuwwa ta amsa masa kuwwar da ya
yi. Can kuwa a saman shi daga daya fuskar sai ya ga rafi makeke
ya tinkari wannan tsauni. To amma wani abin mamakin shi ne
kuma, ko da yake ga kogi ana gani, kuma har ya zo ya wuce ta
kan shi wannan dan taliki, atma duk da haka ruwa ko da kamar
Kwayar zarra bai digo masa ba. Kuma ga shi ko ana ganin sa yana
ta kwarara. Wannan abu da yawa ya ke, shi dai zurfin ruwan nan
ya yi kamar ya shanye dukkan wannan tsauni maí cin wuta. To
saboda haka ne shi wannan yaron ya yi tsammanin cewa lallai
watakila wannan kogi shi ne zai kashe wannan wuta. Ai kuwa da
abin da aka yi ke nan, can sai kogin nan ya je ya auka wa wannan
tsauni. To me ka yi tsammani zai faru? Ka san ko garwashin wuta
aka watsa wa ruwa yakari yi kara cuu-u-u! To balle wannan
dingimemen dutse da kogi, sakamakon abin dai to shi ne babban
rugugi wanda ya hadu da kakkauran hayaki wanda ya turnuke
wannan kewayen wurin.
Yaron nan bai yi wata-wata ba, sai ya sake kiran sunan
nan nasa. Ya kuwa yi sa'a, gadon nan ya sake tashi da shi ya
shilla da shi ya yi sartta, suka tsallake wannan tsauni. To da
tsallake wannan ne fa sai yaro ya hango wani gida na karfe yana
yawo a sama, da wadansu wayoyi sun lelleko daga cikinsa ga
wadansu karafa kuma sun fito daga samansa sun lula sun yi sama,
da suka dada yin kusa sai ya ji karar wani inji wanda bai taba jin
irinsa ba. A zuciyarsa sai ya ce, "Oho, komai dai ya zo ya wuce,
tun da na fice daga mummunar kuna, da rashin samun kabari, to
ai ni komai ya yi!
AN SA SHI AIKIN INJI
Gadon nan fa sai kawai ya nufi wajen gidan nan na karfe
da yaro. Kuma yana kai shi wurin sai ya ajiye shi a kan wata 'yar
farfajiya, kuma kafin ka ce kwabo sai wannan gado ya бace.
Yaron nan ya tabbata cewa shi wannan gado watau ya riga ya
gama aikinsa ke nan, kuma yanzu sai ya yi damara ya shirya tsaf.
Ya jira kuma ya ga irín abin da zai yi gwagwarmaya da shi a
wannan wurin. Can yana cikin wannan irin tunanin, sai kuwa ya
ga wata fitila ja ta