farka ya gan shi a dan
ragaitaccen gadonsa da ya yi, ga kuma biri yana yi masa 'yan
kararraki irin na dariya. Sai ya sauko daga wannan gado nasa,
suka kama hannu da wannan biri, suka nufi wajen kogi domin
yaron ya samu ya wanke fuskarsa, ko ya ji dan dadi-dadi. A
lokacin da suke tafiyar ne ya yi tunanin cewa lallai ungulu ta
koma gidanta na tsamiya. Shi da da zai tashi daga barci ya je ya
yi wanka a cikin wani dan tafki na karfe da ruwan zafi sai ya
zamo ya koma har ya fi jin dadi lokacin da ya ke kauyensu. Shi
da birin nan suka tafi bakin rafi, Muhammadul Ziyara ya wanke
fuska, ya yi alwala kuma ya yi Salla. Ko da yake lokacin da birin
nan ya ga yaro na Salla, sai shi ma ya shiga kafa goshinsa a kasa
duk lokacin da ya ga ya yi sujada. Yaro dai ya gama Salla, ya yi
'yan addu'o'insa, sannan suka tashi shi da biri suka tafi neman na
kalaci.
34
Tauraruwa Mai Wutsiya
gaskiya. Ainihin abin da mutum ya samu damar yi shi ne kadai
gaskiyar.
Yaron nan dai ya yi ta mafarke-mafarke yana ta kuma
shara barci a wannan gindin itaciya har rana ta zo ta cim masa a
inda yake kwance, rana ta fara gasa shi ya farka firgigi da
tsammanin ko yana kan gado ne yana kwance. To amma sai ya ga
ashe ba haka ba ne, yau yana kwance ne a cikin ciyawa, kuma ko
darajar tabarma babu balle a ce ya sami gado. Yunwa ta fara
kama wannan dan taliki kuma a wannan daji babu abin da ya
mallaka banda zinare din nan da aka ba shi tsaraba wanda kuma
shi yana ganin ba shi da wani amfani tun da ya ke ma a wannan
lokacin da karin waina suka ba shi da ya fi masa wannan tarin
dukiyar wadda ba ta amfani wajen ci, in dai ba birni mutum ya isa
ba. Kuma a wannan lokacin bai san Gabas ko Yamma ba, kuma
ko da ya sani din ina za shi? Babu alamun gida a gabansa ko
bayansa, saboda haka sai duk abin ya dame shi. Kuma ya rasa
ainihin abin da yake ciki.
Ana cikin haka din ne sai ya ji an runtse masa ido daga
bayansa, ko da jin haka kuwa, wa kake tsammanin shi zai zata a
zuciyarsa? A'a, wa kuwa banda yarinyar nan da ya gamu da ita a
birnin Malala, to amma ko da aka sakar masa fuska, ya juya da
murmushi don ya ga yarinyar nan, ina, sai ya ga Kolin Koliyo ne.
To duk da haka dai an ce da babu wawa gara da wawa, balle shi
wannan ma ya wuce gaban wawa sai dai dodo. Gama dodo shi ne
aka ce ba a yi masa magana gadangadan sai dai ko raďa.
Yaron nan sai ya gaishe da Muhammadul Sama, shi kuma
ya amsa yana mai farin ciki da irin kwazon da yaron nan ya nuna
masa, har kuma ya ce zai yi wa yaron nan albishir. To ko kafin
Kolin Koliyo ya yi wa wannan yaro albishir, sai yaron nan ya tare
shi ya mika masa ainihin kwayoyin zinaren nan da ya samu daga
inda ya fito, aikin gwaji na hudu.
Kolin Koliyo ya karba ya yi murna da kwazon wannan
yaro kuma ya yaba nagartarsa da kuma gaskiyarsa. Ya sa masa
albarka, sannan ya ce masa, "To saboda wannan abu da aka yi ina
so in yi maka wani adalci, watau ko da yake yanzu ne za ka shiga
aiki na biyar, to amma in ka tuna ka taba zuwa cikin tsakar dare
ka gaishe ni, wata rana da na fito daga cikin wata 'yar tauraruwa
mai wutsiya. Har na samu na ba ka wata 'yar kwalba." Yaron nan
31
Tauraruwa Mai Wutsiya
ya ce masa, "I, haka ne." Ya kuma tsaya tsai, yana sauraron yadda
shi wannan mutum zai karasa zancensa. Kolin Koliyo ya ce, "To
na mayar da wannan gamuwa da ka yi da ni ta tarihi, muhimmiya,
kuma na mayar da wannan aikin gwajinka na daya wanda ya
mayar da yawan ayyukan gwada ka da aka yi zuwa biyar. Yanzu
kana cikin na shida. Da ka gama wannan kuma sai shirin na
bakwai kuma na Karshe ke nan."
Yaron nan fa murna ta kashe shi, yana jin yunwa da,
amma kuma sai har ya mance ma da wannan yunwa da yake ji
don saboda ya ji cewa sauran aiki daya kawai ya rage a gabansa
maimakon biyu, kuma da ya gama zai kai ga samun cikon
burinsa.
Muhammadul Sama, sai dai ya 6ace ya bar Muhammadul
Ziyara da murnarsa. Muhammadul Ziyara sai ya shiga yawo a
cikin dajin nan yana tafe yana waka don saboda murnar irin
wannan labari da Kolin Koliyo ya ba shi. Yana tafe ya wuce
wannan itaciya, ya taka wannan busasshen ganye ya wuce, ya
tsunki wannan furen yana kallo, ya ta da wannan tsuntsu, ya
tsallake wannan rami. Ya dauki 'yar wannan tsakuwa ya yi jifa da
ita, kai yaron nan dai yana ta ayyuka iri-iri, har ya kai wata 'yar
korama wadda ta ke cike da ruwa, kuma shi wannan ruwan shar
da shi, kamar babu abin da ya taba shiga cikinsa. Yaron nan ya ji
a lokacin jikinsa ya fara danko, saboda haka nan sai ya tuttube
kayansa ya ajiye a bakin rafin nan, shi kuma ya zamo daga shi sai
dan kamfai, ya yi kuwa tsalle ya fada cikin ruwan nan, tinjim!!
Da ya fada ya yi ta wanka ya guggurje daudar da ke jikinsa, ya
goge hakora. Ya wanke kansa, ya dai fito fyas, babu dauda a
jikinsa.
Ya gama wanka ke nan kuma yana shirin ya fito ya dauki
wandonsa ya sa, ya je ya sake hutawa tun da rana ta kusa faduwa,
sai ya ga wani biri ya je har ya dauke kayansa, ya sa wando, ya
kafa hula. Kuma yana kokawar sa rigar yaron nan, to amma ta ki
sawuwa, sai Muhammadul Ziyara ya yi nitso cikin ruwa ya bullo
ta gaban rafin nan ya fita daga cikin rafin a hankali sannan ya
mamayi birin nan don ya kwace kayansa, sai kuwa ya ji wani
birin ya yi kuka. Shi kuwa biri mai wando ko da jin kukan
dan'uwansa, sai ya tabbata babu lafiya kare ya sha taba, sai ya yar
da rigar nan ya yanka a na kare, yaron nan kuma ya danna ya bi
32
Tauraruwa Mai Wutsiya
shi. To abin ka da abin da ba sabo ba, sai shi birin nan wandonsa
ya kwance kuma tun dama ya yi masa yawa, sai kuwa wandon ya
tadiye biri, sai gani kake biri na faduwar 'yan bori, sai ya fadı ya
tashi, ya kuma sake faduwa. Shi kuma yaro sai bin sa yake kamar
wadanda ke wasan 6uya. Ya waska nan ya garzaya can, sauran
birai kuma sai suka taru suna dan kugi kamar suna ta dariyar irin
abin da birin nan da yaro suke yi. Da kyar dai daga karshe yaron
nan ya samu ya sha kan shi wannan biri ya kama shi ya zare
wandonsa ya kuma koma ya dauki hularsa da rigarsa ya sa.
Su birai din sai suka kuma zamo sun shaku da yaron nan,
kowane lokaci sai ka gan shi cikin dajin nan tare da a kalla biri
daya. Yaro yana ta garari a wannan daji har dare ya yi, ya ga
cewa lallai ya kamata ya sami wuri ya kwanta, ko ya hutar da
kasusuwansa. A wannan lokaci sai ya ga biri ya hau sama ya
kwanta a cikin wani dan amaku watau shi birin nan ya sami
tsakanin reshe da reshe ya yi wani dan gado inda zai iya mike bayansa.
To ko da wannan yaro ya ga wannan abu sai shi ma ya се
toai lallai shi ma ba a bar shi a baya ba wajen irin wannan alatu
na daji. Sai ya nemo 'yan siraran itatuwa guda biyu, ya kuma tayo
kalgo ya zo ya sami wata itaciya mai wadansu rassa guda biyu
wadanda ya ga alamar cewa lallai 'yar tazarar da ke tsakanin
wadannan rassa za si iya daukar tsawonsa. Saboda haka kuwa sai
ya sami wadannan siraran itatuwa guda biyu, ya daura daya ta
wannan sashi na wannan reshe, daya kuma a daya bari. Ya koma daya reshen, ya kama karshen kowadanne siraran itatuwan nan ya
tamke su da kyau a jikinsa, yadda watau idan mutum ya koma
waje daya zai ga kamar an daura igiyar wanki ne, to amma guda biyu, dukkan su suna daure da rassa biyu kuma da 'yar tazara a
tsakaninsu, yadda inda za a cike tazarar ta tsakaninsu za a iya
kwanciya ba tare da damuwa ba, sai dai ko in mutum mai mugun
barci ne.
Da yaron nan ya koma da baya ya ga cewa komai ya yi,
sai ya je ya samo kalgo da yawa ya zo ya yi ta hada wadannan
danyun kiraren itatuwa yana daurewa datsan-datsan, har ya cike
tsakankanin reshe, da kuma tsakanin karamin itacen nan da
dan'uwansa. Abin ya tashi gwanin kyau, kuma kai da gani ka ga
gadon lilo irin wanda aka yi shi ta hikima, da dabara daga wajen
33
Tauraruwa Mai Wutsiya
birai. To bayan da gado ya samu sai kuma ya je ya samo
ganyayyaki masu taushi ya zo ya barbaza su a kan wannan gado
nasa da ya yi, sannan kuma ya zo ya kwanta ya sami rurumi.
A wannan ranar dai ya gode wa biran nan saboda agajinsa
da suka yi da samun gadon barci. Ya kuwa yi ta sharar barcinsa
ba tare da wani abu ya dame shi ba. To yaron nan ya yi ta barci
har gari ya waye, har birai suka farka, sannan rana ta fara
washewa da irin dan shudi-shudin nan nata na sheki, kuma iska
tana dan busawa a hankali yadda kowa da kowa zai ji dadinta.
Itatuwa da ganyayyaki sai busawa suke yi a hankali suna rangaji.
Abin dai gwanin ban sha'awa. To amma yaron nan duk bai farka
ya'ga irin wannan ni'ima ta kyakkyawar safiya a daji ba. A
maimakon haka ma sai ya shiga mafarkin wai ga shi an sa shi a
daki mai kunama za a ta da inji, to ita kunamar ta yi kokarin ta
gudu, amma sai wani ya zo ya rike ta abin kuwa ya zo a dace
lokacin da wani ya rike a cikin mafarkin nan sai kuma birin nan
da ya taba dauke masa wando ya sa, ya zo ya kama shi. Nan take
kuwa Muhammadul Ziyara ya kwalla ihu kuma ya zabura daga
kan gadon nan nasa, ya ma yi sa'a ne, da ya tuntsura kasa, kuma
babu shakka da ya ji ciwo, domin irin surkukiyar da ke karkashin
wannan itaciya sai wanda ya gani.
Ko da farkawarsa sai abin ya ba shi mamaki kuma da
kunya saboda irin wannan abu da ya farka ya gani, shi yana
tsammanin za a kashe shi ne sai ya farka ya gan shi a dan
ragaitaccen gadonsa da ya yi, ga kuma biri yana yi masa 'yan
kararraki irin na dariya. Sai ya sauko daga wannan gado nasa,
suka kama hannu da wannan biri, suka nufi wajen kogi domin
yaron ya samu ya wanke fuskarsa, ko ya ji dan dadi-dadi. A
lokacin da suke tafiyar ne ya yi tunanin cewa lallai ungulu ta
koma gidanta na tsamiya. Shi da da zai tashi daga barci ya je ya
yi wanka a cikin wani dan tafki na karfe da ruwan zafi sai ya
zamo ya koma har ya fi jin dadi lokacin da ya ke kauyensu Shi
da birin nan suka tafi bakin rafi, Muhammadul Ziyara ya wanke
fuska, ya yi alwala kuma ya yi Salla. Ko da yake lokacin da birin
nan ya ga yaro na Salla, sai shi ma ya shiga kafa goshinsa a Rasa
duk lokacin da ya ga ya yi sujada. Yaro dai ya gama Salla, ya yi
'yan addu'o'insa, sannan suka tashi shi da biri suka tafi neman na
kalaci.
34
Tauraruwa Mai Wutsiya
Suna cikin tafiya a cikin daji sai suka yi kicibis da zaki,
biri ya hau sama, shi kuma yaro ya shiga gudu, zaki ya ce masa
ga shi nan bisa kansa kuwa. To amma kafin zakin nan ya cim
masa, har ya samu ya haye sama, kuma da taimakon wadansu
dogayen igiyoyi da birai suka daura a wannan daji a jikin itatuwa,
sai yaron ya sami abin tafiya. Ya sami igiya daya ya dafe mata,
ita kuma ta yi shillo da shi ta kai shi gun wata, ya dinga yin haka
nan har ya kai inda yake so. Can kuwa sai ya cim ma birin nan
wanda har ya rigaya ya samo musu ayaba, da gwandar daji da
kuma kade domin su karya.
Yaro ya sauka daga sama, suka kama abincin nan nasu da
ci har sai da suka kusa karewa sannan ya ce kai, amma dai ku
biran nan kuna da wayo, don Allah dubi yadda kuka daura
igoyoyin nan don jin dadin tafiyarku. Shi kam ya mance ma cewa
shi biri ba ya magana, sai dai watakila yana ji, ya kuwa dubi biri
sai ya ga biri ba abin da yake yi sai cin abinci da yin 'yan
kararraki irin na birai. A lokacin ne kuma ya gane cewa lallai shi
ba abin da yake yi sai santi. Ya yi wa kansa dariya sannan da suka
gama cin abinci sai suka tashi, sai shi birin nan ya kama hannun
Muhammadul Ziyara ya shiga neman cire zoben da ke hannunsa.
A wannan lokacin ne fa yaron nan ya tuna da cewa
yarinyar nan ta gaya masa cewa a duk lokacin da yake son ganin
ta idan ya cire zobe nan, to zoben zai zamo sarewa kuma da ya
busa zai gan ta ta garzayo zuwa wurinsa. Sai kawai ya shiga
kogin tunani, ya ga kuma tun da suka rabu bai sake saduwa da ita
ba, sai nan da nan ya fizge hannunsa daga gun birin nan, ya kuma
kama hannunsa mai zoben nan yana tunanin ko ya kira yarinyar
nan su gana.
Ko da cire zoben nan daga hannunsa sai ya ga zoben ya
zama sarewa mai kyan gaske, ga wurin hurawarsa har da kumfar
zinare, kuma daga kasan wurin hurawar ga hoton ita yarinyar nan.
Ko da ganin hoton nan na Bintun Sarauta sai ya mato, ya tuna da
irin abin da ya wakana lokacin yana birninta, ya lumshe idanu
kuma ya bude sannan ya rungumi wannan sarewa a kirjinsa, sai
ya kama ita wannan sarewar da busa.
Ko da fara busa sarewar, sai kuwa wurin nan nasu ya fara
badewa da kanshi, kuma abubuwan mamaki suka fara wakana,
tun da na san za ku yarda da ni idan na gaya muku cewa ainihin
35
Tauraruwa Mai Wutsiya
wannan yarinya ta Muhammadul Ziyara wadda ta ke daga wani
birni sihirtacce kuma mai fifiko a kan sauran birane, ba za ta zo
eikin wannan daji da wannan yaro ya ke ba batare da wafansu
alamu na karama ba ko da za ta iya zuwa ta zauna cikin wannan
sunkurun. To daya daga cikin wadannan alamu da nake magana
kuwa su ne, watau wannan kanshin, kuma bayan wannan kanshin
sai kawai ruwan kogin nan ya shiga sauyawa yana wani sheki,
tare da dan kadawa kamar shi kan sa yana jin dadin ita wannan
sarewa kuma yana rawa da sautinta, ko kuma yana murna saboda
wani abu muhimmi, ko kuma wadansu masoya za su hadu a
gabansa.
Can yaro na cikin busarsa sai ya hango yarinyar nan
watau Bintun Sarauta ta bullo daga wani dan loko tana takawa
dai-dai, kuma ga wadansu mata guda biyu sun yiwo mata rakiya
kamar yadda aka saba. Ko da ya hango yarinyar nan tasa sai kuwa
ya daina busa ya shafa a guje domin ya je ya taryi wannan
masoyiya tasa. To amma ko da daina busar nan, sai kuma ita
yarinya ta 6ace. Mamaki ya kama yaron nan, sannan kuma shi
birin nan da ya ke tare da shi ya yi ta 'yan tsalle-tsalle na nuna
mamakin abin da ya faru.
Muhammadul Ziyara sai ya sake kama yin busa da sauri
da sauri ko ya ga yarinyar nan ta dawo. To sai kuwa ya sake yin
busar nan cikin sa'a, domin a wannan lokacin ko da za ta bullo
sai ta bullo masa a daidai gabansa. Nan da nan kuwa ya yi wuf ya
kama hannun wannnan masoyiya tasa, sannan ita kuma da kanta
ta kwace sarewar wadda ta zama zobe, sannan ta mayar wa yaron
nan da zoben a hannunsa.
Nan fa masoyan nan biyu suka hadu suna kallon juna,
kowa ya yi zugudum sai kallon kowa yake, to sai can yaron ya ce
da Bintun Sarauta shi fa ya kira ta ne kawai ba wai don yana cikin
wata wahala ko wata matsuwa ko kuma damuwa ba. To amma ya
ne shi yana son ya gan ta kawai, kuma tun da ya gan ta a
wannan lokaci, ta san yana nan shi kuma ya san tana nan. To shi a
wurinsa komai ya yi.
از
Ita kuwa sai ta ka da baki ta ce da shi ai ita tana
tsammanin cewa ya kira ta ne don ya gaya mata cewa ya riga ya
gama harkar da ke gabansa yadda za su iya samu su shirya ainihin
abin da ya kamace su. To a lokacin ne shi wannan yaro ya nuna
36
Tauraruwa Mai Wutsiya
mata cewa, ai ba laifi ne ya nemi ganin ta ba, tun da ya dade bai
gan ta ba, kuma shi a yanzu saura aiki daya kawai ya rage masa
ya yi nasara a kan wannan gwaji da aka sa shi.
Yarinya ta yi murmushi, ta kuma gode masa, kuma ta
gaya masa cewa ainihin ita da kanta ta so ta zo nan wurinsa
domin ta ga lafiyarsa, to amma saboda kunya shi ya sa ta ki zuwa.
Kuma ta yi murna kwarai da ganin cewa shi wannan yaro bai
mance da ita ba, yana nan lafiya. Bayan dai da suka gama 'yan
zantuttukansu, biri na zaune waje daya yana kallon su, sai kuma
suka yi sallama yarinyar nan ta 6ace, shi kuma Muhammadul
Ziyara ya kama hannun birin nan suka yi tafiyarsu cikin daji
domin ci gaba da yawace-yawacensu. Suna cikin haka ne fa, sai
suka ci karo da wani dan yaro karami a cikin wannan daji. Yaron
fari da shi kamar dan Bature, to amma da ganinsa a kusa-kusa,
kai da kanka ka san wannan ba yaro ba ne. Yana dai da gashi a
ka, ga gemu, ga saje, kuma ga idanun nan nasa kamar na mai
shekaru arba'in. To amma tsawonsa bai fi na yaro kankani fan
shekaru hudu ba.
Shi wannan mutum kuwa yana saye da babbar riga da
wando, da hula, da kuma wani rawani da ya kinkima kamar irin
na samarin alhazai. Shi mutumin ya bude idanunsa ko kiftawa ba
ya yi, kuma ya sha toka. Wannan irin halitta kuwa a cikin wannan
hali sai ya bai wa birin nan da ke tare da Muhammadul Ziyara
tsoro. Nan da nan kuma sai wannan birin ya tsere ya haye sama.
Shi yaron kuwa sai ya yi tunani ko mutum-mutumi ne, wadansu
mutane suka yi don su ba birai da ke wannan sashen gonaki tsoro,
ko da yake babu wadansu gonaki a wurin. Muhammaul Ziyara sai
ya tuge masa dan nadin da ya yi. Ko da tuge nadin nan kuwa sai
mutumin ya narke ya zama kamar ruwa, abin gwanin ban
mamaki. Kuma ko da zama ruwan nan nasa sai ruwan ya tafasa
ya zamo har ya yi zafi, da shi Muhammadul Ziyara ya harari irin
wadannan ayyuka da wannan aljani ke yi, sai aljanin ya yi shiri
ya zama hayaki ya tashi sama abinsa. Wannan kuwa sai ya sa
birin nan ya yi zaton cewa lallai hararar Muhammadul Ziyara ita
ta sa ruwan ya tafasa ya tashi sama.
Wannan abu ya faru kuma ke nan sai ga Muhammadul
Sama ya zo wurin Muhammadul Ziyara ya kama hannunsa suka
sheka a guje, da shekawar nan tasu a guje ba su tsaya ko'ina ba
37
Tauraruwa Mai Wutsiya
sai a wani fili inda ya ke babu itatuwa da yawa kamar inda suka
fito, to a nan ne fa suka tsaya, sannan Muhammadul Ziyara ya
tambayi Muhammadul Sama ko mene ne ya sa shi ya zo haka
cikin hanzari har ya kama hannunsa ya gudo da shi wannan wuri?
Sai kuwa Muhammadul Sama ya ce wa yaron nan ya dubi wani
abu ya fado daidai inda ya ke da, ya fashe da wata babbar kara
sannan dukkan itatuwan da ke wannan wuri sai ya kashe su,
sannan kuma wurin ya kama da wuta. Bayan ya ga haka ne sai ya
gode wa Muhammadul Sama. A wannan lokaci ne kuma shi ya
gaya masa cewa ai shi wannan da ya tube wa rawani, Muk
Sawuta ke nan, wanda shi ke sawa daji wuta babu gaira babu
dalili, kuma in ba don gudun da suka yi ba, lallai babu abin da zai
hana Muk Sawuta ya kone Muhammadul Ziyara.
Da wannan hayaki ya kwanta sai suka kama hanya suna
tafiya a cikin wannan daji, suna tafe suna tadi har suka kai ga
wata 'yar itaciya da ta fadi kuma ma ta shekara da faduwa, domin
har ta fara fari kwal irin na itatuwan nan da sukan zamo sai wuta.
Ko da suka isa ga wannan kututturen sai shi Muhammadul Ziyara
ya ce wa Muhammadul Sama yana jin yunwa kuma in ya yarda
yana son ya samo masa abinci, ko ya dan gasa hantarsa.
Muhammadul Sama kuwa sai ya tabi wannan kututture da ke
kwance da wata 'yar sanda da yake wasa da ita. Taba ta ke da
wuya sai kawai yaro ya ga an sassare wannan itaciya, an yi
katako da ita, an yi teburi, an yi kujeru guda biyu. Sannan an sa
mai an shafe su sai kyalli suke yi. Can sai aka kawo kyalle aka
rufe teburin nan, sannan fa tangarayen abinci suka dinga saukowa
daga sama. Ko da aka hada abinci tsaf, sai Muhammadul Sama ya
ce da yaron nan ya zauna don su ci abinci. Ya zauna, suka ci suka
gama, ga ruwa suka kurkure bakunansu, sannan suka tauna goro.
Bayan sun gama tas sun tashi, sai kuma tangarayen nan suka tashi
suka yi sama tare da hankicin rufe tebur da dukkan tarkacen kan
teburin.
GWAJIN KARSНЕ
Daga wannan wuri da suka gama cin abinci sai
Muhammadul Sama ya gaya wa Muhammadul Ziyara cewa to tun
da ya iya jure dukkan abubuwa shida da ya shiga cikinsu, lallai a
yanzu zai kai shi inda za a kwakkwance jikinsa a yi masa
38
Tauraruwa Mai Wutsiya
garambawul, tun da yake zafin kasa da na taurari ba ſaya ba ne.
Muhammadul Ziyara dai bai yi gardama ba, sai kawai ya ce, "To
madalla, ai sai ka kai ni, tun da aka ce in ka shiga garin 'yan gafi
kai ma lallai ka yi tsafta."
Da gama wannan shiri sai Muhammadul Ziyara ya kuma
dan kifta idanunsa, to ai fa kiftawar nan tasa ke da wuya, sai ya
kifto wa kansa. Domin da bude idanunsa sai kawai ya gan shi a
dakin wani likita katon gaske, wanda da ganin sa da ma sai ya yi
kamar ya san yana zuwa, sai kawai ya ji wannan Likita ya kirawo
sunansa ya kuma yi masa barka da zuwa.
Muhammadul Ziyara dai ya amsa, amma sai duk ganin
wadansu wukake masu kyalli, da wadansu masu motsi da kansu, da kuma wadansu almakasai masu daukar ido, suka sa hankalin
yaron nan ya tashi. Likitan nan sai ya yi murmushi ya kawo wani
dan irin ruwa a cikin karamin tambulan ya ba shi ya sha, ya zo
kuma ya yi masa allura a hannunsa na dama da na hagun, sannan
kuma ya yi masa a duwawu.
Shi dai Muhammadul Ziyara ya daure wa wadannan
allurai, ya yi fatan kuma watakila shi ke nan abin da za a yi masa,
to, amma ina? Ai wannan ma kamar ba'a ake yi, ko ma a ce ba a
ma fara komai ba. Can likita ya ce ya tube rigunansa dukkan su,
kuma ya hau wani gado wanda lantarki mai hasken gaske ya haska.
Muhammadul Ziyara ya yi dukkan yadda aka sa shi,
kuma shi wannan likita ya zo ya duba shi. Bayan da likita ya duba
shi ya ga yadda ya ke, sai ya ce masa ya tashi. Ya tashin, sannan
likitan nan ya tafi ya dauko wani irin mai, da wadansu sabulai
kamar an yi su da 6argo, sannan kuma ya dudduba kayayyakin
aikin nan nasa duka domin ya tabbata cewa kowace wuka tana
yanka yadda ya kamata, sannan kuma ya dudduba kowane
almakashi in yana iya yanka ba tare da wata wahala ba. Da likita
ya ga cewa komai ya yi daidai, sai ya ce wa Muhammadul Ziyara
ya je ya jingina. Ko da jinginarsa kuwa sai ya ji igiyar lantarki ta
kama shi kuma ta ratsa jikinsa, amma da ya duba bai ga komai ba.
Kirjin yaron nan fa sai ya fara dal-fal, amma shi ga shi
babu yadda zai yi, tun da gwaji na karshe ke nan, kuma watakila
mafi wuya. Tun da an ce aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi.
Likita sai ya zo ya dauki wata zundumemiyar wuka, ya huda
39
Tauraruwa Mai Wutsiya
eikin wannan saurayi, ya zaro hanji ya wanke da wani irin ruwa,
sannan kuma ya kawo wani mai ya goga, 'yar hanta kuma ya saka
a cikin wani dan kwano ya yanko mai tsarki, ya mai da cikin nan
cif ya dinke. Ya je kuma ya ta da wata vata 'yar wuta a wani murhu
mai amfani da iska, ya gasa hantar ya zo ya raba ta biyu, ya sake
tsaga kirjin Muhammadul Ziyara yana yanke kafafunsa da
hannayensa, ya je waje daya ya sa musu wadansu irin mai da
kuma wadansu jijiyoyi sannan kuma ya zo ya mayar masa da
Kafafuwansa da hannyensa. Su idanu da kunnuwa su ma ba su
tsira ba, su ma sai da aka cire su aka sa su a cikin wani ruwa aka
wanke, sannan aka mayar masa da su. Da an mayar da su