yi fal, ta kuma mutu. Sai can kuma ta sake
walkawa, sai ya ce. 'To yau kuma aikin nawa da gama na uku
babu ko da hutu sai in shiga na hudu? To amma ai ba komai, ai ni
24
Tauraruwa Mai Wutsiya
ba zama na zo yi a wannan wuri ba, saboda haka bari in farka
daga wannan rarumi nawa, in gama abubuwan da suke gabana.
Wannan fitila ja kafin a yi haka sai ta face, wata kofa ta bude, sai kuwa wadansu mutane suka fito cikin wadansu
kayayyaki na karfe su biyu, kayansu iri daya. Kuma dukkan su
suna rike da wadansu wayoyi a hannayensu na dama da na hagu.
Sannan kuma a bayansu ga wadansu irin jakunkuna na karfe sun
goya. Fuskokinsu duk a rufe, kuma ko tafin hannayensu duk sun
rufe su da safa ta roba, a daidai inda ya kamata hancinsu ya leko
sai wadansu wayoyi masu rufe da roba suka leko don su ba su
damar samun shakar iska. Ko da fitowar wadannan mutane sai
Muhammadul Ziyara ya dube su da kyau, kuma dai-dai, ya nisa,
to amma bai ce komai ba. Sai can kuma ya ji magana kamar ta
mutane, to amma ta surka da wata 'yar kara kamar dai daga rediyo take fitowa. Abin da ya ji an ce kuwa shi ne, "Kai samari,
ka keta mana haddin kasa, saboda haka sai ka biyo wadannan
ma'aikata biyu ku zo cikin wannan gida domin a yanke maka
hukunci. Ko ka fara yin gwale-gwalen da za a sara maka."
Yaron nan, nan da nan ya tashi ya wuce gaba, wadannan
mutane biyu kuma suka bi shi, kamar ba mutane ba, sai tafiya
suke yi kamar wadanda su ke a sankare, su ba sa magana. Suna jin abin da ake cewa, ba sa waige sai juyi, kuma su ba sa tausayi
ga mutum a kan dukkan aikin da aka sa su. Suka shiga wannan gida, shi wannan yaco babu abin da ya fara karo da shi sai
wadansu manya-manyan kwalabe cike da magunguna, da
wadansu dogayen tebura wadanda aka rufe samansu da wata irin
shimfida mai kama da siminti. To amma shi wannan yana kyalli kuma yana da wadansu jefin baki-baki a jikinsa. Sai kuma
wadansu bututu tsukakku masu wani dan mariki, irin wadannan
kuwa akwai kamar talatin, sai kuma wadansu famfuna masu 'yan
Kananan daro a kasansu. Ga kuma wadansu 'yan kayayyaki dai
na karfe masu kama da jiragen sama. To daga can karshen dakin
da suka fara shiga sai ya ga watą siffa kamar ta mutum, sai dai
wannan baki ne, kirin kuma, babu alamar fuska ko wani abu, sai
dai kawai wata waya da ța fito wajen bakin mutumin. Daga
wannan siffar ce fa ya ji magana ta fito inda ya ji an ce, "Tsaya
nan!"
25
Tauraruwa Mai Wutsiya
Nan kuma ya ji kamar an kafe shi, sai kuma aka ci gaba
da cewa, "Ku wuce da shi daki na takwas." To a lokacin kuwa
suna daki na daya ne, inda ya ke babu komai sai kawai wafansu
'yan tarkacen kwalaben magunguna, saboda haka suka kama
hanya suka shiga daki na biyu, wanda shi kuma babu komai sai
ainihin kayan alatu kawai. Dabensa dai na katako ne wanda aka
shafe da mai, sai kyalli yake yi, ga wata irin shimfida mai dan
karen tsada da taushi an baje ta. A kowace kwana daga cikin
kwanoni hudu na wannan daki kuwa akwai wata irin bindiga
wadda ke hade da lantarki. Kuma da mutum ya shiga wannan
wuri ba tare da izini ba su wadannan bindigogin ba wai sai an
harba su ba, a'a, da kansu za su shiga harbin mutum. Watau su
wadannan bindigogin sun zamo masu aiki da kansu ke nan.
Akwai kuma wadansu 'yan kujeru wadanda su ke a kewaye da
wani teburin abinci da ke tsakiyar dakin, su kuma kowannensu
yana da wata waya wadda ta hadu da ita daga karkashin
shimfidar da ke dakin, kuma idan mutum bai lura ba, to babu
yadda za a yi ya iya fahimtar cewa akwai waya da ta hadu da
wadannan kujeru.
Su ainihin wadannan kujerun kuwa an ce idan mutum ya
zauna kansu yana iya mutuwa ta fizgar lantarki.
Suka wuce daki na biyu, suka nufi na uku, inda suka tarar
da wadansu irin tsuntsaye manya-manya, masu gashin zinare, su
kuma wadannan kewaye su aka yi da wata 'yar katanga gajeriya
wadda ta kawo wa mutum kirji. An kuma shirya ta yadda duk
abin da ya ta6i katangar, idan dai ba an riga an cire hade-haden
da aka yi ba ne, to in dai har ya fi wannan tsuntsun girma, to ka
tabbata zai ji an yi wurgi da shi. Da an yi wurgi da shi kuwa zai je
rijiyar same 'yar tsidau. Wato a saman dakin akwai wani lungu
inda cikinsa duk kaifafan masu ne, kuma zamowarsa kamar rijiya,
to amma a sama, shi ya sa aka sa mata suna rijiyar sama. Kuma
saboda wadannan tsinukan masu, sai ana kiranta 'yar tsidau, to
tuntube dadin gushi, kuma mutumin da ya gama sokuwa a rijiyar
saman nan in ya zo fadowa ba fa zai fado a kan dabe ne ba. A'a
zai wuce kai tsaye ta wata kofa da takan bude da kanta ya yi kasa
iska ta wajajjaga sauran jikinsa.
Da suka wuce daki na uku kuma sai daki na huďu inda
banda macizai da duwu (bakar kunama) babu komai. Su kuma
26
Tauraruwa Mai Wutsiya
wadannan macizai ba wai na Allah Ta'ala ba ne, wadannan
macizan da duwun duka ainihin su, Sarkin wannan birnin ne ya
kago su da taimakon ma'aikatan kimiyyarsa. A dakin ne kuma
aka yi rubutu kamar haka: Alfaharin birnin Kage-Kage. To su
wadannan kunamai da macizai kowane daya a kalla ya fi girman
akuya, wato su kunamun ma ke nan, to amma ainihin macizan in
aka tara su tsibin kowane daya ya yi kamar girman bajimin sa.
Aikin su kunamun nan kuwa shi ne in aka sa dunkulen kasa a
bakinsu aka ta da injinansu, kuma aka koma aka sa kashin su
tsuntsayen nan na daki na uku a cikin kwayar idon su macizan
nan, to su kuma aka ta da injinansu, in kwayar idanun macizai
guda biyu suka haska dunkulen kasar da ke bakin kunamun, to sai
ka ga dunkulen kasar nan ya zama lu'ulu'u, wanda kowa ya san
abu ne ba mai karamin amfani ba.
Sannu a hankali kuma har suka iso daki na biyar, wannan
dakin kuwa babu komai sai irin kunamar nan da suka wuce a daki
na hudu. To amma wannan kunamar guda daya ce kurum, kuma
ita wannan kantareriya ce. Ta yi kamar girman irin kananan
motocin nan, to amma ita ba wai aikinta kamar na wadancan ne
ba. Ita kam da an ta da ita ko ka fi kowa, ba ka iya wuce ainihin
wannan daki, tun da samun ka za ta yi, ta murkushe, kuma ko
kana da bindiga, kowane irin makami ka rike, ba zai yi mata
komai ba.
Sai kuma daki na shida, wanda ya ke shi wani katon daki
ne cike da gadaje. A wannan lokacin kowane gado akwai mutum
yana barci, ko da yake dai ba wai maza ne duka ba, har da mata.
A lokacin ne ma ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, "Dubi wadansu ma'aikatan dare su da rana suke barci."
A wannan dakin banda su wadannan mutane da ke
kwance babu ainihin wani abin lura kuma, sai dai karar inji da ke
tasowa daga daki na gaba, sai ji kake rim-rim-rim!
Suka wuce zuwa daki na bakwai inda suka sami mutum
biyu suna gyare-gyaren injina, kuma suka ga wani injin ruwa mai
kusassari sai murdawa yake yi barkatai. A wannan dakin ne suka
raba suka shige kuma aka ce kada ya yi tari, in ba haka ba injin
zai murde shi, don duk wanda ya je wannan wuri babu izini, to sai
tari ya turnuke shi sannan wani inji ya hadiye shi.
27
Tauraruwa Mai Wutsiya
Sai kuma ga su tsundum a cikin daki na takwas inda wata
murya ta ce a kai wannan yaro. A dakin ne fa akwai wasu 'yan
dakuna har guda bakwai, kowane daki da inda yake iya tafiyarwa
cikin dakuna da suka keto. A nan ne kuma aka ba wannan yaro
wani irin abin sakawa a kunne. Sannan kuma aka kawo wani don
ya nuna masa yadda ake aiki da injinan nan, kuma aka sa shi ya
taba injin wurin, amma kafin ya ta da shi, sai da aka je ainihin
dakin ita kunamar, aka ajiye wani dan rago. To da ya tayar da
injin a kamar minti biyu, sai aka ce ya kashe ya kuma je ya ga
abin da wannan dan rago da aka kai wurin. Ko da ya je sai ya
tarar an mai da wannan naman dan rago lakai-lakai. Ko kuma ma
ya zamo kamar fatar ragon, in dai ba don kara tsawo da ta yi ba,
sannan sai aka dauka aka jefar da shi ta taga, iska ta sami nata.
Bayan da ya gama wannan aikin ne sai ya ce, "To mene ne
manufar wannan irin aiki da kuka yi wa wannan rago?" Sai kuwa
aka ba shi amsa cewa ai wato an yi wannan ne don shi kansa ya
sani cewa, in ya yi wasa ya bar wani 6era ya shigo wannan wuri,
bai yi masa haka nan ba, to shi ma ya tabbata babu abin da zai
same shi, illa irin wannan karshen. In ko ya zauna ya yi aiki
tsakani da Allah, to zai sami saki bayan an gafarta masa laifinsa
na kutsawa Kasarsu.
Muhammadul Ziyara nan ya kama aiki gadan-gadan tare
da amfani da injina ba ji ba gani. Dare da rana, safe da yamma,
sai dai kawai wani lokaci akan kawo masa abinci ya ci, sannan ya
ci gaba da aiki. Ga mai koya masa aiki, ga masu gadinsa. Haka
dan talikin nan ya dinga yi har kwana takwas, sannan shi wannan
mai garin ya kira shi don ya sallame shi saboda irin aiki mai kyau
da ya yi musu.
MUHAMMADUL ZIYARA YA KOMO
DAGA SAMANIYA
A lokacin da aka kira Muhammadul Ziyara don a sallame
shi, sai ya ga an hau da shi wani bene, inda ya je ya tarar da wani
mutum ya kinkime a kan wata kujera mai juyawa, duk inda
mutum ke so ya juya ta. Ko da shigarsu, mutumin na duban
sashen da ke duba kofar dakin ne, watau yana mai juya wa kofar
dakin nan baya. To sai kawai ya waskata kujerarsa ya juyo yana
duban kofa. Waje daya kuma ga wata 'yar kujera cike da kayan
28
Tauraruwa Mai Wutsiya
shaye-shaye iri-iri, kuma ga wafansu mata can waje daya suna
zaune suna jiran kowane irin umarni daga wannan Sarkin nasu.
Sai yaro ya shiga ya yi gaisuwa, ya nuna cewa kuma lallai ya ji
dadin zaman da ya yi da wannan masarauci tare da talakawansa,
kuma ya yi murna da irin ilimin da ya samu daga gare su.
A wannan lokaci ne fa sai wannan Sarki ya yi wuf ya
tuna da shashancinsa da ya sa ya nuna wa wannan yaro dukkan
dabarunsu, kuma sai ya yi tunani, ya dauko wani dan kuttu na
karfe wanda ya yi kama da karamar rediyon hannu. To amma shi
wannan Wayalis ne, watau wanda mutum zai iya magana da wani
wanda ya ke yana da ainihin irin wannan Wayalis din. Da shi
wannan Sarki ya yi mui da baki sai can yaron nan ya ji an bude
kofa daga bayansa ya ga wani ya shigo da wani abu kamar kokon
kai, amma na karfe da wata waya yana hade da jikin shi wannan
koko-kokon. Sai aka yi wuf aka sa wa wannan yaro a ka. Ko da
aka ta da injin sai idanun yaron nan suka yi burwai kamar wanda
ya suma, ko kuma za a cire wa rai. Bayan kamar dakika talatin da
ta da injin nan sai kawai yaron nan ya ji duk ya mance da dukkan
irin abin da ya sani a game da gidan nan da ya yi bauta na kamar
kwana takwas, abin kamar a mafarki, amma hankalinsa dai yana
nan tare da shi, saboda haka ainihin abin bai 6aci kwarai ba.
Sarkin nan ko da ya san abin da ya yi, sai ya yi wata 'yar
gajeriyar dariya irin ta keta. Sannan ya tambaye shi cewa me ya
yi a makon da ya wuce? Yaron nan kuwa sai ya ce, “Ai shi bai yi
komai ba banda hutu da barci.” A nan ne shi wannan Sarki ya san
cewa lallai wannan ya samu, kuma yanzu ba shi da sauran tsoro
na game da wannan yaro, yadda yake ba zai iya gayyato masa
komai ba, ko kuma kowa ba zai je inda ya ke cin duniyarsa ba.
To a wannan lokacin ne kuma ya tambayi yaron nan don
ya ji ko yana so ya koma birbishin kasa? Yaron ya ce, kwarai
kuwa wannan abu ne ai wanda yake so. To ainihin wannan Sarki
sai ya sa aka ba shi zinare cikin gwangwanin taba daya, kuma ya
ba shi riguna ya sa don saboda tun da gadon nan ya sauke shi
yana saye ne da wando da kuma wadansu 'yan takalma, da kuma
'yar tsumman singiletinsa. Bayan da ya sami wannan kaya kuma,
sai aka sa mutanen nan guda biyu da suka fara tarbo shi lokacin
da gadon nan ya fado da shi a kan wannan garin su mayar da shi
kasa. Da suka fita daga dakunan, wadannan mutane biyu sai suka
29
Tauraruwa Mai Wutsiya
kama hannun wannan yaro, sannan suka ta da injinsu suka tashi
sama, tare da wata 'yar kara mai dadi.
Bayan da suka yi sama ne sai can kuma suka sauko kasaKasa suka yi ta yin kasa har suka iso wajen hazo, suka keta shi.
Suka wuce suka yi ta yin kasa dai har suka fara hango wani sashe
na duniya mai itatuwa, ko ma mu ce dazuzzuka da ruwa. Kuma
ga shi ta zamo a kewaye sai ka ce wani dan wuri da aka shata,
amma kuwa sai ka ga duk zafin tafiyar mutum ba zai cim ma
wannan wuri da samaniya ta hadu da kasa ba.
Bayan da suka kusa kasa, sai mutanen nan suka karkata
kawunansu ta wajen hagu sai kuwa ya ji wata magana kamar daga
rediyo wadda ta ce ku ajiye shi ko a ruwa ko a dawa duka daya
ne. Bayan ya ji haka ne kuma, sai ya ga sun yi kasa sun nufi wani
kasurgumin daji da shi. Can sai ya ji su kaya-kaya cikin ganye,
suka yar da shi a wannan wuri, sannan suka sake matsa injinsu
suka sake ta shi suka nufi sararin samaniya. Shi dai sai ya daga
kai yana ta kallon wadannan mutane biyu, har suka bace masa.
A wannan lokaci kuma sai ya nisa ya kuma nemi gindin
itaciya, ya sami wani dan guntun itace ya gyaggyara wurin ko ya
sami dan sarari ya zauna, ya kishingida a kan tushiyar itaciyar
don neman ya sami barci, domin kuwa ya jima idanunsa ba sa
samun hutawa. Da kwanciyarsa kuwa sai barci ya share shi, ya
kuma dinga yi ba ji ba gani. Yana cikin barci ne fa, sai ya fara
mafarki wai ga shi ya tafi taurari, kuma ma har daga can wai ana
yi masa shirin zuwa wata inda zai sheke ayarsa, sannan kuma ya
ci karensa ba babbaka.
To duk dai a cikin mafarkin sai ya ji wai an ce da shi wai
yanzu ya soma aikinsa na shida ne, watau a irin gwaje-gwajen da
za a yi masa saura daya ke nan ya sami zuwa ga taurari. Kuma
burinsa ya cika ke nan game da irin abin da yake nema ya samu.
Har gogan naka ya ci gaba da tunawa da yarinyar nan da ya gamu
da ita a birnin Malala, kuma har ma wai ga su suna sheke ayarsu a
cikin birnin Taurari. To a wadansu lokuta in mutum ya yi
mafarki, sai ya tarar karya ne. To amma akwai wani lokaci da
mutum kan yi mafarki wanda ya ke kusa da gaskiya, domin ko da
zai zamo mutum ya yi mafarki, sannan kuma daga baya abin ya
zamo ya faru, to sai mutum ya ce mafarkinsa ya kusa zama
30
Tauraruwa Mai Wutsiya
gaskiya. Ainihin abin da mutum ya samu damar yi shi ne kadai
gaskiyar.
Yaron nan dai ya yi ta mafarke-mafarke yana ta kuma
shara barci a wannan gindin itaciya har rana ta zo ta cim masa a
inda yake kwance, rana ta fara gasa shi ya farka firgigi da
tsammanin ko yana kan gado ne yana kwance. To amma sai ya ga
ashe ba haka ba ne, yau yana kwance ne a cikin ciyawa, kuma ko
darajar tabarma babu balle a ce ya sami gado. Yunwa ta fara
kama wannan dan taliki kuma a wannan daji babu abin da ya
mallaka banda zinare din nan da aka ba shi tsaraba wanda kuma
shi yana ganin ba shi da wani amfani tun da ya ke ma a wannan
lokacin da karin waina suka ba shi da ya fi masa wannan tarin
dukiyar wadda ba ta amfani wajen ci, in dai ba birni mutum ya isa
ba. Kuma a wannan lokacin bai san Gabas ko Yamma ba, kuma
ko da ya sani din ina za shi? Babu alamun gida a gabansa ko
bayansa, saboda haka sai duk abin ya dame shi. Kuma ya rasa
ainihin abin da yake ciki.
Ana cikin haka din ne sai ya ji an runtse masa ido daga bayansa, ko da jin haka kuwa, wa kake tsammanin shi zai zata a
zuciyarsa? A'a, wa kuwa banda yarinyar nan da ya gamu da ita a
birnin Malala, to amma ko da aka sakar masa fuska, ya juya da
murmushi don ya ga yarinyar nan, ina, sai ya ga Kolin Koliyo ne.
To duk da haka dai an ce da babu wawa gara da wawa, balle shi
wannan ma ya wuce gaban wawa sai dai dodo. Gama dodo shi ne
aka ce ba a yi masa magana gadangadan sai dai ko rada.
ya
Yaron nan sai ya gaishe da Muhammadul Sama, shi kuma
amsa yana mai farin ciki da irin kwazon da yaron nan ya nuna
masa, har kuma ya ce zai yi wa yaron nan albishir. To ko kafin
Kolin Koliyo ya yi wa wannan yaro albishir, sai yaron nan ya tare
shi ya mika masa ainihin kwayoyin zinaren nan da ya samu daga inda ya fito, aikin gwaji na hudu.
Kolin Koliyo ya karba ya yi murna da kwazon wannan
yaro kuma ya yaba nagartarsa da kuma gaskiyarsa. Ya sa masa
albarka, sannan ya ce masa, "To saboda wannan abu da aka yi ina
so in yi maka wani adalci, watau ko da yake yanzu ne za ka shiga
aiki na biyar, to amma in ka tuna ka taba zuwa cikin tsakar dare
ka gaishe ni, wata rana da na fito daga cikin wata 'yar tauraruwa
mai wutsiya. Har na samu na ba ka wata 'yar kwalba." Yaron nan
31
Tauraruwa Mai Wutsiya
ya ce masa, "I, haka ne." Ya kuma tsaya tsai, yana sauraron yadda
shi wannan mutum zai karasa zancensa. Kolin Koliyo ya ce, "Tо
na mayar da wannan gamuwa da ka yi da ni ta tarihi, muhimmiya,
kuma na mayar da wannan aikin gwajinka na daya wanda ya
mayar da yawan ayyukan gwada ka da aka yi zuwa biyar. Yanzu
kana cikin na shida. Da ka gama wannan kuma sai shirin na
bakwai kuma na Karshe ke nan.
Yaron nan fa murna ta kashe shi, yana jin yunwa da,
amma kuma sai har ya mance ma da wannan yunwa da yake ji
don saboda ya ji cewa sauran aiki daya kawai ya rage a gabansa
maimakon biyu, kuma da ya gama zai kai ga samun cikon
burinsa.
Muhammadul Sama, sai dai ya 6ace ya bar Muhammadul
Ziyara da murnarsa. Muhammadul Ziyara sai ya shiga yawo а
cikin dajin nan yana tafe yana waka don saboda murnar irin
wannan labari da Kolin Koliyo ya ba shi. Yana tafe ya wuce
wannan itaciya, ya taka wannan busasshen ganye ya wuce, ya
tsunki wannan furen yana kallo, ya ta da wannan tsuntsu, ya
tsallake wannan rami. Ya dauki 'yar wannan tsakuwa ya yi jifa da
ita, kai yaron nan dai yana ta ayyuka iri-iri, har ya kai wata 'yar
korama wadda ta ke cike da ruwa, kuma shi wannan ruwan shar
da shi, kamar babu abin da ya taba shiga cikinsa. Yaron nan ya ji
a lokacin jikinsa ya fara danko, saboda haka nan sai ya tuttußе
kayansa ya ajiye a bakin rafin nan, shi kuma ya zamo daga shi sai
dan kamfai, ya yi kuwa tsalle ya fada cikin ruwan nan, tinjim!!
Da ya fada ya yi ta wanka ya guggurje daudar da ke jikinsa, ya
goge hakora. Ya wanke kansa, ya dai fito fyas, babu dauda a
jikinsa.
Ya gama wanka ke nan kuma yana shirin ya fito ya dauki
wandonsa ya sa, ya je ya sake hutawa tun da rana ta kusa faduwa,
sai ya ga wani biri ya je har ya dauke kayansa ya sa wando, ya
kafa hula. Kuma yana kokawar sa rigar yaron nan, to amma ta ki
sawuwa, sai Muhammadul Ziyara ya yi nitso cikin ruwa ya bullo
ta gaban rafin nan ya fita daga cikin rafin a hankali sannan ya
mamayi birin nan don ya kwace kayansa, sai kuwa ya ji wani
birin ya yi kuka. Shi kuwa biri mai wando ko da jin kukan
dan'uwansa, sai ya tabbata babu lafiya kare ya sha taba, sai ya yar
da rigar nan ya yanka a na kare, yaron nan kuma ya danna ya bi
32
Tauraruwa Mai Wutsiya
shi. To abin ka da abin da ba sabo ba, sai shi birin nan wandonsa
ya kwance kuma tun dama ya yi masa yawa, sai kuwa wandon ya
tadiye biri, sai gani kake biri na faduwar 'yan bori, sai ya fadi ya
tashi, ya kuma sake faduwa. Shi kuma yaro sai bin sa yake kamar
wadanda ke wasan buya. Ya waska nan ya garzaya can, sauran
birai kuma sai suka taru suna dan kugi kamar suna ta dariyar irin
abin da birin nan da yaro suke yi. Da kyar dai daga karshe yaron
nan ya samu ya sha kan shi wannan biri ya kama shi ya zare
wandonsa ya kuma koma ya dauki hularsa da rigarsa ya sa.
Su birai din sai suka kuma zamo sun shaku da yaron nan,
kowane lokaci sai ka gan shi cikin dajin nan tare da a kalla biri
daya. Yaro yana ta garari a wannan daji har dare ya yi, ya ga
cewa lallai ya kamata ya sami wuri ya kwanta, ko ya hutar da
kasusuwansa. A wannan lokaci sai ya ga biri ya hau sama ya
kwanta a cikin wani dan amaku watau shi birin nan ya sami
tsakanin reshe da reshe ya yi wani dan gado inda zai iya mike
bayansa.
To ko da wannan yaro ya ga wannan abu sai shi ma ya ce
toai lallai shi ma ba a bar shi a baya ba wajen irin wannan alatu
na daji. Sai ya nemo 'yan siraran itatuwa guda biyu, ya kuma tayo
kalgo ya zo ya sami wata itaciya mai wadansu rassa guda biyu
wadanda ya ga alamar cewa lallai 'yar tazarar da ke tsakanin
wadannan rassa za si iya daukar tsawonsa. Saboda haka kuwa sai
ya sami wadannan siraran itatuwa guda biyu, ya daura daya ta
wannan sashi na wannan reshe, daya kuma a daya 6ari. Ya koma
daya reshen, ya kama karshen kowadanne siraran itatuwan nan ya
tamke su da kyau a jikinsa, yadda watau idan mutum ya koma
waje daya zai ga kamar an daura igiyar wanki ne, to amma guda
biyu, dukkan su suna daure da rassa biyu kuma da 'yar tazara a
tsakaninsu, yadda inda za a cike tazarar ta tsakaninsu za a iya
kwanciya ba tare da damuwa ba, sai dai ko in mutum mai mugun
barci ne.
Da yaron nan ya koma da baya ya ga cewa komai ya yi,
sai ya je ya samo kalgo da yawa ya zo ya yi ta hada wadannan
danyun kiraren itatuwa yana daurewa datsan-datsan, har ya cike
tsakankanin reshe, da kuma tsakanin karamin itacen nan da
dan'uwansa. Abin ya tashi gwanin kyau, kuma kai da gani ka ga
gadon lilo irin wanda aka yi shi ta hikima, da dabara daga wajen
33
Tauraruwa Mai Wutsiya
birai. To bayan da gado ya samu sai kuma ya je ya samo
ganyayyaki masu taushi ya zo ya barbaza su a kan wannan gado
nasa da ya yi, sannan kuma ya zo ya kwanta ya sami rurumi.
A wannan ranar dai ya gode wa biran nan saboda agajinsa
da suka yi da samun gadon barci. Ya kuwa yi ta sharar barcinsa
ba tare da wani abu ya dame shi ba. To yaron nan ya yi ta barci
har gari ya waye, har birai suka farka, sannan rana ta fara
washewa da irin dan shudi-shudin nan nata na sheki, kuma iska
tana dan busawa a hankali yadda kowa da kowa zai ji dadinta.
Itatuwa da ganyayyaki sai busawa suke yi a hankali suna rangaji.
Abin dai gwanin ban sha'awa. To amma yaron nan duk bai farka
ya ga irin wannan ni'ima ta kyakkyawar safiya a daji ba. А
maimakon haka ma sai ya shiga mafarkin wai ga shi an sa shi a
daki mai kunama za a ta da inji, to ita kunamar ta yi kokarin ta
gudu, amma sai wani ya zo ya rike ta abin kuwa ya zo a dace
lokacin da wani ya rike a cikin mafarkin nan sai kuma birin nan
da ya taba dauke masa wando ya sa, ya zo ya kama shi. Nan take
kuwa Muhammadul Ziyara ya kwalla ihu kuma ya zabura daga
kan gadon nan nasa, ya ma yi sa'a ne, da ya tuntsura kasa, kuma
babu shakka da ya ji ciwo, domin irin surkukiyar da ke karkashin
wannan itaciya sai wanda ya gani.
Ko da farkawarsa sai abin ya ba shi mamaki kuma da
kunya saboda irin wannan abu da ya farka ya gani, shi yana
tsammanin za a kashe shi ne sai ya