ana zama a irin wadannan
kujeru ba, sai ya kura wa yarinya ido kawai. Ita kuwa sai ta yi
dariya, ta je ta kama hannuwansa ta zaunar da shi kan kujera,
sannan ta ce da shi, "Yau ne sunanka dan samari domin haka ne
na kawo ka fadata, na sa kuma Muhammadul Sunanye ya je ya
zabar maka suna mafi kyau da tsari."
9
Tauraruwa Mai Wutsiya
Yarinyar nan sai ta ci gaba da yi wa Kilba bayani cewa
shi Muhammadul Sunaye din nan yana da sunaye iri-iri, kuma
yana iya zabar wa mutum sunan da ya fi dacewa da shi, wanda
kuma ya ke cike da sa'a, yadda ya ke ko da mutum zai shiga cikin
wani hadari idan dai zai iya kiran wannan suna nasa, to ka ga
wani dan'uwansa wanda ke da sunan wanda kuma ya fi shi
fasaha, da lakanin abin, ya zo ya cece shi. Tana gama wannan
magana sai ta sake tafa hannayenta sau biyu, sai can ga 'yan mata
wadansu daban, sun zo sun durkusa, sai ta ce da su su tafi su
shirya musu abinci, da za su ci su biyu, watau ita da wannan yaro.
Yaron nan dai mamaki ya kama shi, sai kallon ta yake yi
don bai taba ganin namiji da mace suna cin abinci tare ba. To can
wata sai ta zo ta ce wa yariyar nan, "Ga ruwan can an shirya don
wannan bako namu mai martaba." Yarinya sai ta ce, "To, ai sai
ka tashi domin in kai ka wurin wanka ko ka yi wanka ka ji dan
dadi-dadi." Kilba ya mike suka kama tafiya a kan shimfidu har
suka kai wani dan karamin daki a can sakon shi wannan babban
dakin. Da kusantarsu da wurin kuwa, sai ya hangi wata yarinya
na tsaye cikin ladabi tana jiran su su isa, ta bude musu kofa. Da
isarsu kuwa sai ta bude kofa sannan ta koma waje daya ta tsaya.
Shi gogan naka ko da bude kofa sai ya nemi ya fara shigewa
daki, to sai ita wannan da ta bude dakin ta tsare shi, matar ta fara
shigewa tukuna sannan shi kuma ya shiga. Wannan kuwa ya ba
shi mamaki.
sa
yi Da fa shigarsu sai ya ce, "To mene ne dalilin da ya
kika fara wucewa gaba, sannan ni?" Sai wannan yarinya ta
murmushi, ta ce da shi, "To ai ka san kai namiji ne ko?" Ya ce,
"I." Sai ta ce, “To ai ka san kowane lokaci ya kamata namiji da ya
ke shi yana da mazakuta a jikinsa ya rika lura ya ga ko'ina aka je
matarsa ce ké gaba, ko kuma akalla matar da suke tare da ita, ta
wuce wurin lafiya, kafin shi ya wuce. Dalili ke nan kuwa mu nan
muka saba mu ga najimi ya rika tabbatarwa matarsa ta wuce kofa
kafin shi ya shige.
Yaro ya yi murna da jin wannan bayani maí faranta
zuciya tare da annuri da wadansu kalmai kuma masu neman
bayani. To amma duk da haka bai nemi bayanin komai ba, tun da
ya gan shi cikin wani dan daki da wani katon daro cike da ruwa,
ga kuma madubi a waje daya a jikin bango, ga soso ga sabulu. Ga
10
Tauraruwa Mai Wutsiya
wani katon kyalle wanda ya ji cewa wai ana kiran shi tawul,
watau abin tsane ruwa bayan mutum ya yi wanka. Yarinyar nan ta
ce da shi ya tube ya shiga ruwa ya yi wanka, in ya fito ya goge
jikinsa da tawul. Ta kuma buda masa wani wuri kamar kabod
inda ya ga riguna, da wanduna, da huluna iri-iri, ta ce in ya gama
ya fece kansa, ya kuma sa rigunan da yake so, sannan ya sa
takalma, da dai dukkan abin da yake so ya sa. Kuma idan ya ji bai
gane wani abu ba daga cikin abubuwan sai ya matsa wani dan
kullutu da ke jikin bango. Sannan sai ta fita, ta sakaya masa kofa,
ta ce, 'Sai ka fito.'
Dan Kolin-Koliyo sai ya tube 'yan tsummokaransa, ya
zubar a kasa, ya fada tsundun cikin daron nan, yana ganin kamar kududdufi ne. To shi bai san ruwan zafi ne ba, ai kuwa sai nan da
nan ya zabura ya kwada ihu, ya kuwa tashi, ya shiga matsa dan kullutun nan da aka nuna masa. Shi bai san ashe Kararrawa се
yake matsawa ba. Yarinya nan da nan ta je a guje, duk tana ta
mamakin ko me ya faru.
Ko da shigowarta sai ta ga mutum a tube, ta yi mamaki,
kuma nan da nan sai ya ji ta ce, "A'uzu Billahi. To nan da nan shi
kuma sai ya ji 'yar kunya, ko da yake da ma ya riga ya suturta gabansa, sai dai ya ji kunyar kauyancinsa ne kawai, sai ya ce mata, "Shin wannan ruwan haka ya ke da zafi?" Sai ta amsa masa
ta ce, "Ai haka ya ke, mun ga ka fito cikin sanyi, shi ya sa muka
ga cewar ruwan zafi zai fi kyau. Ai sai ka kokarta haka nan ka ji ko ka iya yi." Kilba ya ce, "To ai ni da ma so nake in ga haske a
dakin domin ko da kika fita sai na ga duk fitilun dakin sun dushe,
amma yanzu da kika shigo sai dakin ya cika da annuri ga haske
ga ni'ima.'
Yarinya dai sai ta yi murmushin nan nata mai sa yaro ya
manta cewa ya yi na Sauna, ya yi karo da itaciya, don saboda
manta kansa da ya yi don tunaninta. Nan kuma ta sake sallama da
yaron, ta ce masa sai ya fito ke nan. Yaro fa ya shiga wanka.
Yana ta tunani, ya fara jin ainihin yarinyar nan dai ta fara shiga
masa cikin kashin ransa. Wani wajen kuma yana tunanin ga shi
wai za a sake rada masa suna, sai ka ce wani jinjiri. Ga shi kuma
shi har yanzu yana so ya isa ga taurari, to kaka-tsara-kaka, goma
da goma sai dan gata. Karo da karo sài rago, ba a sanin rago
kuma sai an kara, saboda haka ya ce zuciyarsa 'shi kam ya dage
11
Tauraruwa Mai Wutsiya
wa wannan niyya tasa ta cim ma taurari, kuma ko ta yaya ya yi
niyya kuma za shi.
Yaro dai ya gama wanka tsaf, har da dan shasshafa mai,
da fece kai, ya tabbata dai ya fito fyas. To amma me, abinka da
bakauye, duk da kayayyakin da aka nuna masa ya kidime sai ya
daura tawul, ya kifo sauran aka, ya fito wai shi ya sa wata riga ta
burgewa. Nan take kafin ya fita sai da ya duba madubi ya ga
kansa har ya ce, "Lallai yau zan burge in cashe." Ba shakka zai
burge amma ba wai don rigar tawul ba. To yana cikin wannan
shirmen ke nan sai ya ji an kwankwasa kofa a hankali watau abin
kamar an kada wata 'yar ganga mai zaki, sai ya tabbatar yarinyar
nan ce, sai kuwa ya ce, 'Shigo! Sai ta shigo ta yi masa barka da
gama wanka. Ta bude dan kabod din nan kuma ta ce masa ya
zabi kayan da zai sa, To shi kuma da ragon azanci maimakon ya
ce a'a, ita ta zabar masa, sai ya je ya shiga daukowa. To ainihi
kuwa shi cikin kabod din da sashen kayan mata da na maza, a
maimakon ya fara dauko wando, sai ya tsallake ya dauko tofi
mai kyalli da daukar ido. Nan da nan sai ya ji yarinya ta
kyalkyace da dariya. Kamar ya sani sai ya yi maza ya yar da
tofin, sai ta ce masa, "Ai ga wajen kayan maza nan." To a lokacin
ne fa shi wannan yaro ya dauko bakin wando, bakar shat da jar
kwat, da kuma jar hula, sai dai ta ga lallai bai saba sa kayayyakin
ba, sai ta ce, "Bari dai in dauko maka."
Ta dauko masa farar kwala da shat, ta mayar da bakar, ta
dauko masa bakar kwat ta mayar da jar, sannan ta dauko farar
hula ta mayar da jar. Dan samari fa nan take ya ci adonsa ya yi
tsaf ya je ya duba a madubi, sai ya kyalkyace da dariya saboda
tunawa da ya yi lokacin da ya cukumude da tawul ya je yana
duba madubi wai shi ya burge. Yarinyar nan sai ta kamo
hannunsa suka fita daga dakin, suna tafe tana rausaya tana dan
dubansa da wutsiyar ido.
Daga nan sai Yarinyar nan ta nufi da shi wajen cin abinci
inda suka tafi suka zauna a tebur. Aka kawo kayayyakin abinci
kamar su inabi, dabino, gwanda, lemo, ayaba, da kek, da miya
wadda akan sha ta da ludayi kawai, da masa irin wadda a kan ci
da miya wata dabam, da hanta, da madara da ti, da kuma wasu
irin 'yan hankici na takarda, da kuma burodi da man shanu mai
12
Tauraruwa Mai Wutsiya
gishiri, Watau irin daskararren nan wanda a kan shafa a jikin
burodi don a ci.
To yau fa ake yin ta, yau ga wanda zai zare hannu ya
wanke shi ya sa shi cikin debi da kanka, ya warba a baki, ya cire
idon daddawa ya yar waje daya, ya ci gaba da cin abincinsa, har
ma wani lokaci idan an yi rafkanuwa wani dan kuda ya fada a yi
nama da shi. Tun da ya ke ainihin shi wannan yaro a gidansu
yakan sha lami ne, ranar ko da za a yi miya mai nama lallai ranar
za a yi gayya a gidansu tun da za ta zamo rana ce ta musamman.
Yau ga shi Allah ya kawo shi inda zai ci abinci ba ma a kan
tabarma ba, a'a wai a kan tebur, kuma ba da hannu ba, a'a wai da
wadansu cokula masu yatsu da kuma wadansu iri-iri har da wuka.
To ka san kai da kanka ainihin wurin ma zai ba mutum tsoro balle
irin wannan shirgi na abinci da aka kawo.
Yarinyar nan fa sai ta ce da yaro ai za su fara taruwa don
a raďa masa suna. Nan da nan kuma sai ta dauki cokali ta shiga
shan miya, sai shi kuma ya shiga kallon ta galau, kamar wanda ya
ga ana saran mutum, shi kuwa ba shi da karfin hanawa. Domin
shi wannan yaro banda a wannan rana bai taba ganin ana shan
miya haka nan tsirarta ba. Yarinya ta dube shi ta yi murmushi ta
ce, "Ai sai ka dauki abin da kake so ka yi ta ci don yanzu ba mu
da lokacin 6atawa." Yaron nan ya dauki ayaba ya saka a baki da
bawon da komai. Yarinya kuwa ta dube shi ta ga ya 6ata rai
saboda yana jin zaki-zaki da daci-daci, shi kuwa bai sakankance
da irin wannan abincin nata ba, har ya shiga tunannin ko ma guba
ce aka zuba masa cikin wani abu mai zaki.
Yarinya dai ta ga shi wannan dan taliki bai gane wa irin
wannan harka ba, saboda haka sai ta kawo gutsuren waina da
miya ta hada ta ci, shi kuma ya gani, saboda haka nan sai shi ma
ya dauki wainar yana ci. To sannan ne ya ji dan dama-dama, daga
nan kuma komai zai ci sai ya dakata sai ya ga ainihin abin da ta yi
sannan ya yi. Ko da yake shi inda duk ake sa cokali, ko cokali
mai yatsu, shi hannu yake sawa, domin tun da ya ke bai taba rike
ainihin koshiya ta itace ba, balle cokali ko kuma wata uwa wai
cokali mai yatsu. A haka nan dai aka kokarta har aka samu aka
gama cin abincin, daga karshe kuma ya dauki abin goge hannu,
watau irin 'yar takardar nan da akan yi amfani da ita don kare
datti a riga, ya nemi ya tsoma ta a miya domin ya foye shi, shi ma
13
Tauraruwa Mai Wutsiya
cikin ciki. Nan da nan sai yarinya ta agaji yankin nan ta nuna
masa amfaninsa. Da aka gama sarai sai aka kawo wa wannan yaro
ruwa ya wanke hannayensa, wata yarinya kuma ta kawo wani
tawul a cikin tire na azurfa aka goge wa Dan Kolin Koliyo hannu.
Ko da gama goge wa gogan naka hannu sai ya dubi rigarsa da
kyau don ya ga ko miya ta zuba a jiki. To ya yi sa'a dai miya ba
ta zubar masa ba ko dis.
Da suka tashi daga kan wannan teburi na cin abinci sai
suka je suka shiga wani lambu na fulawa da furannin kallo iri-iri.
Suka je, suka zauna a kan wani gado wanda aka kafa shi mai lilo,
yaron nan ya hau gadon yana mai mamaki da taʼajibin irin yadda
dan Adam ya yi ya kago yadda aka yi wannan irin gado mai đan
karen dadin hawa. Suna nan zaune a cikin lambu sai ya ji ana ta
hura kakaki da bigila irin na sarauta, ya duba haka sai ya hango
mutanen da suke wannan aiki a kan benayen fadar nan wadda
samanta ruwa ne, kasanta ruwa, Kudu da Yamma Gabas da
Arewa duk ruwa ne, ya kare wannan fadar dungum dinta.
'Yan mata na gama busarsu sai ya fara ganin jama'a ana
ta tafiya ana shiga ainihin katuwar farfajiyar nan da suka fada ciki
lokacin da yarinya ta shafe masa fuska da hankici. Su dai suna
zaune a wannan wuri yarinya ba ta cewa komai, sai fuskarta ke
sheki kawai, shi kuwa wannan yaron ko da dan hakin wurin, ba
shi sha'awa da mamaki yake yi. Can kuma sai ga shanu an kawo
guda biyu, daya fari, daya kuma mai fari da ja da kuma baki, aka
tsayar da su aka ce shi wannan yaro ya je ya tabi kowanne daga
cikinsu domin kuwa da su ne za a rada masa suna. Yaron ya je ya
yi kamar yadda aka umarce shi ya yi. Sannan aka tafi aka yanka
shanun aka fede su, aka cire hantar kowanne, sai aka gasa aka
yanka aka kai wa yaro da yarinya suka ci. Aka kawo lemon
kwalba aka ba su a cikin wani dan kofi da ake zuba irin
wadannan shaya-shayen.
Lokacin da suka gama dura dan wannan lemon nasu sai
ga wani mutum ya iso musu kamar daga sama shi da matarsa. Shi
mutumin nan wani kosasshe ne, yana saye da fararen kaya, amma
da damara ta fata baka, yana sanye da wata hula da ta yi kama da
roka ko kuma jirgin sama a kansa. Ita matar tasa kuma tana sanye
da wadansu 'yan kayayyaki masu launin sararin sama, kuma da
14
Tauraruwa Mai Wutsiya
takalma masu tsini, ga kuma hula ita ma ta sa irin ta wannan mijin
nata.
Ko da isowarsu sai shi wannan mutumi ya dan duka irin
na ban girma ya ce, "Bintun Sarauta yau ga ni na zo wajen shirin
namu, kuma ina tsammanin shi Muhammadul Suna ya riga ya
shirya." Sai Bintun Sarauta ta amsa ta ce, "Na yi murna da jin
haka kuma ina tsammanin yanzu an gama shirya mana komai.'
Ta ci gaba da tambayar yaron nan cikin murmushi ta ce, "Ko ka
san wannan mutumin?" Sai yaro ya kada kai da nunin kamar ya
san shi, to amma bai ce komai ba. Sai ta ce, "Wannan shi ne
Muhammadul Sama, kuma waccan ita ce Bintun Sama, watau
matarsa, ina fata in ka gan su wata rana za ka iya shaida su?" Sai
yaron ya ce, "Haka ne in dai ban shaida wannan yanzu ba, to nan
gaba kuwa zan shaida su dukkan su, kuma na yi murna da saduwa
da su."
Shi yaro yana ganin aihinin shi wannan mutum shi ne
Kolin Koliyo, duk da haka dai bai ce komai ba sai ya ja bakinsa
ya tsuke kawai. Bintun Sama sai ta ce, "To yanzu me ake jira?"
To in gaya maka kafin ta rufe baki sai ga 'yan mata biyu sun iso,
sun rusuna, sun ce, wai fada ta hadu, kuma su kawai ake jira. Sai
fa 'yan matan nan biyu da suka zo suka ja musu gora, amma fa ba
ta makafi ba, irin ta masu ido, kuma masu gata ko a masu idon.
Da shigar wannan kungiya cikin fada sai kowa da kowa ya mike
kuma dukkan ilahirin wadanda wannan ayari ya tarar a cikin
wannan fada bayan da ya mike sai da ya sunkuyar da fuskarsa
don saboda tsananin girmamawa. Su hudun nan sai suka wuce ta
tsakiyar mutanen da suka yi dafifi a kan gefen dama da hagu na
wannan shirgegen daki. Su kuma wadannan mata da suka yi
rakiya sai suka je bayan kujerar da wadannan za su zauna suka
dauki mafitai suka shiga aikinsu, watau yi wa wadannan mutane
masu martaba a wannan gari na cikin tsakiyar ruwa fifita. Yaron
nan kuwa sai ya kalli nan, ya kalli can, ya ce wannan a zuciyarsa,
ya ce wancan, har ya kiyasta a zuciyarsa cewa, to, ya shiga kasa
saura kuma ya hau sama gun taurari in ma da sarari gun wata.
Da wadannan suka zauna, sai kuwa sauran jama'a duka
suka zauna, sai kuma kowa ya yi tsit yana jiran ya ji irin jawabin
da Bintun Sarauta za ta yi. To amma kafin ta yi magana, sai da shi
Muhammadul Sama ya tashi ya ce, "Ko da yake na sani ainihin
15
Tauraruwa Mai Wutsiya
Mai Martaba Bintun Sarauta, kuma Sarauniyar Birnin Malala, za
ta so yin magana saboda babban bako da muka yi, to amma na ga
kafin ta ce wani abu zan kira mawaka da makada su dan kada
mana ganga, don kowa ya dan ji dadin da mai martaba za ta ji. To
amma kafin in kira su masu kida da waka zan fara nuna wa
jama'ar Malala cewa mu ne na sama, kuma mu ne na ruwa, a
yanzu da ya ke fadar tana da girma, ga ta tankamemiya, kuma
akwai fili a sama, to zan yi iyo a sama, don kowa ya ganar wa
idanunsa ya san mu ba wasa muke yi ba.
Nan take sai shi wannan dan taliki ya mika hannayensa
biyu sama ya yi wata 'yar dariya. To in gaya maka kuwa abin
gwanin ban mamaki, kafin kiftawa da Bisimilla sai Muhammadul
Sama ya yi sama, ko kuma mu ce Muhammadul Koli ya yi koli,
don kuwa ita yarinyar nan ta ce sama ne, don kada wannan yaro
ya gane cewa wannan ainihin Kolin Koliyo ne. Jama'a sai tafi ake
yi, ana cewa, "Lallai na Koli, gaishe ka! Naka shi ne na farko shi
ne kuma na sama!" 'Yan yara kuwa sai suka rude sai gani suke
kamar zai fado musu a ka. Tsofaffi kuwa sai mai da tarihi ake yi
ana cewa ai wane ne dan wane, jikan wane, mai abu kaza da kaza.
Bayan shi wannan Muhammadul Koli ya gama shawagi a sama,
ya kusan saukowa sai ya sako irin kyastun nan da akan kyasta shi
ya kama wuta, ya ba da launi iri-iri, ya kuma haskaka wuri. Nan
ne fa wuri ya kara dagulewa, sai kirari ake yi masa, ana cewa mai
taurari a hannu, wata ma nasu ne.
To a nan ne kuma kai wannan soko watau dan Kolin
Koliyo ya yi shirme, ya shafa a guje. To, abin ka da bakauye, shi
ma sai ya fita a guje. Ya garzaya ke nan sai shi Muhammadul
Koli ya fado daidai gabansa ya rike shi. Abin dai ya zamo kamar
ya je ne ya tare shi. Aka yi ta tafa wa wadannan mutane gaba
daya. Su kuwa su Bintun Koli da Sarauniyar Malala sai
murmushi kawai suke dokawa. Can su wadannan mazan suka
dawo suka zauna lafiya abinsu. Tafi ya lafa, can kuma zance ya yi
sauki, sai Muhammadul Koli wanda ya ke kamar Wazirin garin
ne ya tashi ya ce, "To jama'a mun yi murna da wannan dan taro
da aka yi, kuma yanzu za mu kira shahararren mawakin nan namu
watau Muhammadul Waka da kuma sahibarsa Bintun Waka su
fito tare da 'yan kada gangunansu, su rera mana wakoki irin
16
Tauraruwa Mai Wutsiya
wafanda za mu san lallai yau muna nishadi kuma muna yi wa
babban bako barka da sauka.
Da gama maganarsa sai ya zauna, jama'a duka aka sake
fashewa da sowa tare da tafi. Ana tafin nan da sowa, masu
ganguna na fitowa, masu siriki suka fara ziza busa, kuma masu
ganga suka shiga fan kwankwasa ta kwas, kwas, kwas. To a nan
fa wuri ya sake yin tsit kowa na jiran ya ga sarautar Allah, kuma
sarautar ganga, da siriki da kuma Muhammadul Waka da Bintun
Wake. Abin na yi ne, masu ganga fa suka fara doka ta, ga busa,
ga kuma wadansu suna tafi lokaci-lokaci. Wuri ya rude, dattijai
suka fara kada kafa, limamai na girgiza kai, sannan yara na kada
gindi, kowa dai kidan nan ya soma tsima shi. Kuma kowa babu
abin da yake jira sai ya jin irin wakar da za a yi.
Sarauniyar Malala kuwa sai idanunta kawai suka yi rau
rau suka kuma cika da annuri da hikima, kuma sai ta rika kallon
masu kida tana duban shi wannan yaro watau Kilba. To amma
ina! Shi gogan naka sai yi yake kamar ya tashi ya carke da rawa,
kallo kuwa kamar an sa kugiya ana jan idanuwansa an kafa su ga
masu kidan. Can kuma ana cikin wannan kida sai mai ganga ya yi
zarya ya yi kamar zai fita fage. Ya matse gangarsa da kyau ya
kuma kada ta, sai kowa idanunsa suka bude, kowa ya san cewa
lallai ba kawai ba, wannan irin ziyara, da makadin nan ya yi, sai
kuwa aka ji wata murya mai dan karen zaki da dadi ga zalaka, ta yi wata 'yar waka mai dadi da sanyaya zuciya.
Kowa ya duba haka sai ya ga ashe ainihin Bintun Waka
ce ta fara rera irin wakokinta, can kuma Muhammadul Waka shi
kuma sai ya fito da nasa salon, yana rawa yana waka, ita kuma
tana rawa tana kada kuturi tana kuma kada mama. Kai abin dai da
ban sha'awa, kowa sai dadi ya kashe shi. To daga nan kuma sai
aka gama waka, sannan ne kuma sai ga wani tsoho ya shigo fada
da dogon gemunsa duk ya yi fari, kuma yana yafe da wani irin
tafkeken farin mayafi, kuma ga tasbi ya rataya a wuyansa. A
hannunsa kuma ya riko turaren wuta wanda zai yi amfani da shi
wurin radin suna. A bayansa kuma wadansu samari ne da 'yan
mata ke biye da shi. Kowannensu da turaren wuta da furanni а
hannunsa, suka zo tsakiyar wannan tafkekiyar fada suka zauna,
suka sa wannan turaren wuta da tsohon nan ya dauko a tsakiya.
Wato suka yi wa turaren wutar zobe, kamar yadda zobe kan
17
Tauraruwa Mai Wutsiya
kewaye dan yatsa. Can kuma aka kawo wadansu kwalaben
turaren manya-manya aka ajiye su waje daya, sai malamin nan,
wato Muhammadul Suna, ya je ya kira shi wannan yaro bako,
Kilba. Da ya je, aka zaunar da shi a tsakiyar mutanen nan da suka
kawo turaren wuta. Malamin ya yi 'yan wadansu addu'o'i sannan
aka kara turaren wuta a cikin turarurrukan nan na turaren wuta.
Hayaki ya tashi, aka kawo wadannan turare kuma aka yi ta
yayyafa wa Kilba. Malami kuwa, sai addu'a yake yi, can sai aka
ga wani haske mai karfin gaske ya haskaka wurin fal kamar
walkiya. Kowa sai gabansa ya fadi. To amma da ganin wannan
haske mai kyallin gaske sai jama'a suka ji an ce, “Allah ya raya
Muhammadul Ziyara! Amin!"
Nan da nan sai shi malamin nan da 'yan mukarrabansa
suka bace. Shi kuma Muhammadul Ziyara wato Kilba sai ya gan
shi kawai shi daya babu kowa. Babu dai masu rada masa suna,
babu 'yan kida, babu 'yan kallo dukkansu. Babu su Muhammadul
Koli, hasali dai babu kowa. Kai sam ma a dakin da ya ke da ba a
gan shi ba yanzu, ya gan shi ne kawai a wani daki karami wanda
a cikinsa akwai gado babba guda daya, gadon kuwa da
shimfidunsa da komai, ga madubi dogo irin wanda mutum zai ga
dukkan jikinsa in ya ga dama, da kuma wata kofa 'yar karama
wadda za ta kai mutum zuwa wurin wanka da bayan gida.
To me wannan dan taliki ya iya illa banda ya san na yi?
Ko dai ya yi barci ko kuma ya nemi yin kikikin fita daga wannan
daki. To amma idan ya nemi fita ma ina za shi? Ga shi kuma duk
ya gaji, saboda haka sai ya ce to, tun da ya kammala da gwaji na
biyu ai ya kamata ya kwanta ya huta wa dan tsumman ransa. A
lokacin ne kuma sai ya hau gado ya kwanta, amma ya rufe ido zai
yi barci ke nan sai ya ji Kolin Koliyo ya ce, "I to ka sami suna
yanzu ina fata ka yi matukar murna!"
MUHAMMADUL ZIYARA YA HAU
GADO MAI TASHI
To bayan da Ubangidan Muhammadul Ziyara, watau
Muhammadul Koli ya yi masa murnar rada suna, sai ya ce da shi
ai ya kamata ya kwanta, ya huta don kuwa ya dade yana wahala a
wannan rana. To amma fa ya ci gaba da tuna masa cewa wannan
lokaci ba na sake ba ne, saboda haka kada ya yi ta barci na babu
18
Tauraruwa Mai Wutsiya
gaira babu dalili, domin kuwa dukkan ſaukacin mutumin da yake
son kansa da arziki, da kuma ainihin rufin asiri, to, ba ya tare wa
barci. Domin me, mutum na cikin barci ne ake iya zuwa a kashe
shi, ko wani muhimmin rabo ya wuce shi. Ya ci gaba da cewa ba
wai yana nufin ko kada yaron nan ya yi barci ne ba, a'a wato da
dai mutum ya yi dan barci nadari, to, sai ya farka ya shiga yin
abin da yake tafe da shi. Domin kuwa ya sani cewa lokaci ba abu
ne mai jiran Sarki ba, balle bafade. Duniya kuwa babu wanda ya
zo domin ya zauna a cikinta.
Yaron nan ya ji duk abin da wannan dan taliki ya fada
kuma kafin a yi haka sai ya ga wannan mutumin ya bace. A
wannan lokaci sai yaron nan ya tashi daga kan gadon nan ya je ya
shiga dakin nan na wanka inda ya ga akwai daron nan wanda ya
taba wanka a cikinsa, da kuma wani dan