Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TAURARUWA MAT WUTSIYA UMARU A. DEMВО HAUSABOOK.COM Tauraruwa Mai Wutsiya Ümaru A. Dembo NNPC Tauraruwa Mai Wutsiya Mallaka (M) Copyright © Umaru Dcmbo 1967 An fara bugawa a 1967 An sake bugawa a 1977, 1978, 2013 ISBN: 978-978-169-153-0 Ba a yarda a buga wannan littafin ko kuma a sarrafa shi ta kowace irin hanya ba matukar ba da rubutaccen izinin mawallafan littafin ba. All rights reserved. No part of this publication may be reproduced or tansmitted in any form or by any means, without permission. PIRACY IS A CRIMINAL OFFENCЕ! Under the Copyright Art (Cap. 68, Laws Amendment Decree No. 98 of 1992 and the Copyright (Amendment) decree 1999 piracy is criminal offence equivalent to criminal theft. Both the Company and the Nigerian Copyright Commission will pursue legal action against any offender caught producing, selling or buying pirated books. Under the criminal code the punishment for piracy can include imprisonment. The Company will also pursue any offender for damages in a civil suit. SATAR FASAIHА ВАВВAN LAIFI NE! A karkashin dokar hakkin mallaka mai lamba ta 68, da kuma gyaran da aka yi mata a karkashin dokar mulkin soja ta 1992 da 1999 mai lamba ta 98, ta nuna cewar satar fasaha babban laifi ne wanda ya yi daidai da satar dukiya. Saboda haka, hukumar da ke kula da hakkin mallaka ta Nijeriya tare da wannan Kamfani, za su gurfanar da duk wanda aka samu yana bugawa ko sayarwa ko kuma sayen littafan da aka buga ta bayan fage. Daga cikin irin hukuncin da aka tanada ga ire-iren wadannan laifuffuka sun hada har da dauri. Kuma wannan Kamfani ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen gurfanar da mai laifi don neman hakkinsa bisa tsarin doka. NNPC Published by Northern Nigerian Publishing Company Limited Gaskiya Building P. O. Box 412, Zaria. Tel: 069-332087 www.nnpchausa.com Printed by: AMANA PRINTING & ADVERT. LTD. Tel: 08034251810 1 Tauraruwa Mai Wutsiya TAURARUWA MAI WUTSIYA A wani dan kauye da ake kira Karinda, an taba yin wani hatsabibin yaro da ake kira Kilba wanda kowane lokaci ba tadin da yake yi a cikin tsararrakinsa sai na taurari. Idan suna magana da yara ba abin da za ka ji Kilba na cewa sai, "Allah ya sa in je wurin taurari, ni dai ina son su." Ana nan fa Kilba abin nasa sai dada habaka yake yi, har ya zama bayan yara sun gama wasa da daddare, sai shi ya zauna a waje yana ta kalle-kallen taurari, kuma ba ya barin wurin wasan sai bayan karfe goma sha biyu ko ma karfe biyu na dare. Kowace rana kuma sai ya zama sai 'yan'uwansa sun sha wahalar jan sa zuwa gida, don saboda sun san halin gogan nasu, muddin suka bar shi a waje, to shi babu abin da ya shalle shi, sai kawai ya kwana abinsa a wajen. Wata rana da daddare bayan yara sun ga Kilba ya garzaya da gudu ya nufi wajen da wata tauraruwa mai wutsiya ta yi zarya, sai can bayan an dan jima kadan suka gan shi ya komo musu yana rike da wata kwalba 'yar kankanuwa mai kyalli, kuma tana ba da launi iri-iri. ’Yan'uwansa sai suka tambaye shi inda ya sami ita wannan kwalba mai ban sha'awa, ga kyau ga daukar ido, to amma shi wannan yaro babu abin da ya ce wa 'yan'wansa sai wai shi dai Allah ya karfi rokonsa kuma har ya hada shi da wani wai shi Malamin Sama. Har kuma can yaron nan ya ci gaba da gaya wa yaran nan cewa wai shi wannan Malami sunansa Kolin Koliyo. Yara dai abin ya ba su mamaki kowa sai ya yi sumuisumui ya kutsa gidansu ya shiga ba da labarin irin wannan abin al'ajabi da takadarancin da Kilba ya yi. Kowa ya ji wannan labari sai ya ce, "To ai da ma haka ne, in mutum ya ce hatsabibanci zai yi, ai ya gamu da gamonsa, ga shi nan ai ya gamu da aljannu sun fara ba shi siddabarunsu." Ran nan da gari ya waye, sai Sarkin Karinda ya sami labarin cewa ai Kilba ya sami lu'ulu’u, saboda haka ya ga babu abin da zai yi sai ya aika a kira Kilba. Da aka kira Kilba, sai ya tambaye shi, "Ina kwalba mai kyallin nan da aka ce ka tsinta?" Kilba kuwa sai ya kawo wannan kwalba ya mika wa Sarki. Sarkin ya duba ya ga lallai shi wannan abin da ke cikin kwalbar nan lu'u lu'u ne, ya san kuma da an kai shi birnin Sukarta, wani birni da ke kusa da su, zai samu ya canke kudinsa ba tare da ka-ce-na-ce ba. 2 Tauraruwa Mai Wutsiya Sarki sai ya tura aka kira iyayen Kilba, ko da isowarsu sai ya gaya musu ya karbi kwalba daga hannun dansu Kilba za a ba Di'o ya kai Sukarta inda za a yi amfani da ita. Iyayen Kilba ba su yi ko gardama ba, amma Kilba sai ya ce shi sai a ba shi abarsa. Sarki sai ya yi kunnen uwar shegu da yaro, har ya tashi zai shiga gida, tun bai kai ga daga duddugensa ba, sai kawai ya ji yaro na cewa, "Kolin! Kolin!! Koliyo!!!" Yana karewa sai kuwa aka ji wani rugugi mai karar gaske. Walkiya kuma ta ratsa fadar wal! Sai ga wani sunduki ya fado a gaban yaro. Mutanen fada suka rude, wadansu suka ranta a na kare, wadansu suka suma, wadansu suka shiga rawar jiki da kururuwa. Sarki kuwa ya kama cunar rigarsa ya jefa a kansa tare da tuge rawanin gaba daya don tsoro. Wani mutum kuma ya fito cikin wannan sunduki mai haske da falfali, shi hasken sundukin ne ma ya sa jama'a suka rude, har suka yi ta ayyuka iri-iri don firgici. Shi sundukin, bayan haske da falfali, ya yi kama da jirgin sama irin namu na yanzu, sai dai shi ba shi da fikafikai da kafafuwa, kuma jikinsa lallausa ne kamar audugar rimi, shi ba shi da kofa, ba shi da nauyi kuma a tsakiyarsa akwai wata siffa mai kama da tauraro wadda take ba da haske iri-iri, watau kamar yadda ake kunna lantarki a kashe. To, amma wannan idan ka ga ja yanzu, sai ka ga shudi, sai fari, kai da sauran launuka iri-iri. Wannan haske da yake bayarwa launi-launi kuwa yakan ratsa zauren Sarki ya fantsama wa garin haskensa. Gari kuma duka sai ya rude saboda wannan haske, sai sallallami ake ta yi, wadansu na haka kasa don su shiga. Wadansu kuwa sai kida da waka suke yi, wai suna yi wa Sarkin Aljannu maraba don ya kyale su, wadansu nan take suka yi kaura daga garin. Wadansu kuwa sai amai da gudawa suke yi wanda har ya kusa kai su ga bingirewa. In kun tuna, Sarki da sauran jama'a da ke zauren Sarki sun yi kamar sun mutu saboda tsoro, to amma shi yaron nan sai ya durkusa ya sake cewa, "Kolin! Kolin!! Koliyo!!!" Sai mutumin da ya fito daga sunduki ya ce, Dana! Mene ne?" Sai yaro ya ce, "Ajiyarka da ka ba ni a hannuna cę, yake neman ya canza." Sai Kolin Koliyo ya ce, "Bar su, duk wanda ya yi wasa ya sha wuya, ko ma ya halaka, don darajarka na kyale su." To daga lokacin nan sai Kolin Koliyo ya dauki kwalbarsa wadda Sarki ya ajiye a dabe, lokacin da sunduki ya fada zaure, ya 3 Tauraruwa Mai Wutsiya kama hannun Kilba suka fita abinsu sannan kuma sundukin nan da Kolin Koliyo ya zo a cikinsa ya tashi sama cil, kamar kibiya. Can sai Sarki ya tashi ya leka waje ya ga bai ga Kolin Koliyo ba, bai kuma ji rugugin sunduki ba, sai ya koma zaure ya tattashi jama'a don ya fara ba su labarin jaruntakarsa, don yana tsammani dukkansu sun sume ne lokacin da sundukin ya fado. Ya fara ba da labari ke nan sai wani ya katse masa hanzari ya ce ai ya gan shi rawani ya sarke shi har fuskarsa ma ba a gani. Sarki kuwa sai ya ce, ai wannan lokacin da wani mutum mai ja kamar garwashin wuta ya ce masa ya daina kallonsa, shi kuma ya ga ba abin da zai yi sai cika umarni, ko kuma ya sha wuya. Da aka gama dan tattauna maganar dai sama-sama kuma cikin tsoro, sai Sarki ya shige gida sauran jama'a kuma suka fita don su tafi gidajensu. Ko da suka fita, sai suka yi ta karo da mutane wadanda suka haka rami suka shiga, ko kuma suka yi amai har suka gaji. Suka tattaimaki irin wadannan jama'a da arashin cewa, "Dodon ya tafi.", sannan suka isa gidajensu. Su wadanda suka firfito daga rami da sauran dai masu ayyuka iri-iri duk sai aka shige gida, garin ya zamo kamar an kafa dokar ta бaci. Mutane a cikin gida, bayan sun kulle kofa sai ka ji ana cewa mu kuma mutanen wannan gari, Allah ya hada mu da alakakai. Wadansu kuwa sai su yi shiru da bakinsu don saboda tsoro, kada su ambaci sunan Kolin Koliyo ko na Kilba, su jawo wa kansu. Lokacin da Kolin Koliyo kuwa suka fita da Kilba, sai suka tafi wani dan daji a bayan gari. Da suka isa dajin, sai Kolin Koliyo ya ce wa Kilba zai tafi da shi wurin taurari, to, amma zai gwada shi tukuna, in ya ga ya ji tsoro, to sai ya dada goguwa tukuna. Idan kuwa bai ji tsoro ba, to sai ya kai shi zuwa ga taurari, domin kuwa sai an gwada akan san na kwarai. Kilba ya yarda da gwajin da za a yi masa, ya kuma tabbatar da cewa ba wani abin da zai firgita shi. Kolin Koliyo ya ce, to shi zai tafi, amma Kilba zai ga abubuwan mamaki guda bakwai, kafin ya bace, kuma sai ya nuna wa Kilba wata 'yar itaciya. 4 Tauraruwa Mai Wutsiya ITACIYAR KALGO Kilba na duban itaciyar da Kolin Koliyo ya nuna masa, wadda 'yar kankanuwar itaciyar kalgo ce, da ganyayyakinta lafalafa, ga furanni masu fari da kasa-Kasa har da 'yan Kananan kwari na bin su suna shan kanshi, ga sauyoyinta guda uku sun bullo a kasa, ga 'yan ciyayi koraye shar sun gewaye itaciyar su kuma ba masu tsawo kwarai ba, kai komai dai na itaciyar gwanin ban sha'awa. Amma da kallon ta a wannan lokacin sai komai ya canza kwata-kwata. Jikin itaciya sai ya zama baki wulik, wadansu 'yan fararen tsakuwoyi kuma suka kakkafu a jikinta, itaciyar kuma sai mikewa take yi sama zalala kamar ana jan ta, tana kuwa yin kauri gaba daya. Ganyenta suna zama kawuna irin na mutane, gangunan jiki kuwa ba a ganin su, kawunan kuma bakake ne, hakora farare, wadansu na mata, wadansu na maza, wadansu kawunan da kitso, wadansu da shamfo. Wadansu da aski, wadansu da ciko, rassan kuma sai suka zamo cinyoyin al'umma. Yaro ya tsaya cif, yana ganin sarautar Allah. A kasan itacen sai hannuwa suke ta yin adabo maimakon ciyayi da ke wurin a da. Hannáyen wadansu farare, wadansu bakake, wadansu jajaye. Jijiyoyin nan kuwa guda uku na itaciyar nan sai suka zama kirjinan mutane, ga awazu ana gani, amma babu ciki ko wuya. Kilba dai duk da haka ko motsi bai yi ba, sai ya dubi nan ya dubi can, da ya dan kifta idanu, ya ci gaba da kallon wani wuri. Da Kilba ya gama ganin kawuna na barka da zuwa, hannaye na adabo, rassa na zama cinya, jijiyoyin itace na zama kirjuna, ciyayi na zama hannaye, abubuwa suka dagule, wuri ya rude da hargowa, sai ya yi dariya ya ce, "Kolin! Kolin! Koliyo!" Sai kuwa duk wadannan abubuwa suka bace, itaciya ta komo yadda ta ke. Kolin Koliyo kuma ya fito ya ce, "Da kyau dana. Daya ke nan, haka nake so namijin maza!" Kilba sai ya ji karfi a jikinsa, sannan ya waiga ya ce wa Kolin Koliyo, "To yanzu me ya kamata ka rada mini suna, tun da ya ke yanzu ni na san zan iya zuwa can kasarku ta taurari? Ga shi ni yanzu ba ni da suna kamar naku, kuma ni duk wani abin tsoro gani nake sassauka ne, to amma yanzu ai bai kamata a ce na isa garin taurari amma ba ni da suna irin na burgewa, ko kuma in ce irin na 'yan taurari ba, sai irin na 'yan Adam kawai." 5 Tauraruwa Mai Wutsiya To ana wata ga wata, ana dara kuma ga dare ya yi, ana yawon La'asariyya ga ruwa ya zubo, 'yan biri sai a ware a shafa a guje, ko kuma wanki ya бaci. Kolin Koliyo sai ya dubi yaro ya yi masa kururuwa, yaro ya gigice, amma bai nuna masa cewa ya ji tsoro ba, ko da yake dai ya jin. Domin ko kai ne ke tsaye kamar mil biyar daga wannan wuri da su Kolin Koliyo su ke, za ka ji wannan kara wadda ta yi kama da ta aladen dawa, ta ma fi ta aladen dawa, ta yi kama da ta garkunan 6aunan da aka zo harbin su suka rude suna ta kuka. To amma abin ya wuce misali domin kuwa idan da karar ce kawai, to da kowa ya ji dadi, kuma ba zai ko duba ba balle ya firgita. To amma abin shi ne kasa sai ta yi wani dan girgiza, iska ta taso gadangadan, itatuwa suka nemi tugewa don iska. Gari ya rufe, kura kuma ta tashi, wuri ya dagule, babu komai sai ainihin alamun halaka da hadari. Kafin ka ce kwabo hadari ya hadu yá kankama kamar irin hadarin nan na bakin dare da wani lokaci akan yi a watan Agusta a wadansu sassa na Nijeriya, kai abin dai kamar mafarki. Kai yaro, kana so a rada maka suna, to, ga shi an rada maka wahala, da bakin duhu da matsananciyar iska kawai kake ji. To, can kafin a yi haka ko labarin da Kolin Koliyo yake bayarwa ba a ji, sai kuma ruwa ya goce, sai walkiya sai tsawarwaki kake ji wata na bin wata. Ga iska ba a daina ta ba, ji kake wu-u-u-u!! Kugin iska. Yaron nan iska sai fataki take ta yi da shi, tana ina aka saka, ta dauke shi daga kan wannan itaciya ta jefa shi a kan waccan, ta dora shi kan matattun namun daji, ta cire shi zuwa ga masu rai, kai shi dai ko dan karfin da zai samu ya dan ciccije ba shi da shi. Saboda haka sai dai ya zuba wa sarautar Allah idanu, ya ga inda iskar nan za ta gama da shi. Can cikin wajejjewa da shi sai a gabansa kawai ga mesa ta bude baki tana so ta kama dan talikin nan, to amma ina! Iska sai ta yi fatali da ita, shi kuma ya ji an jefa shi daidai inda ita wancan mesa ta ke a da. To a yanzu ne abin ya soma sauki har yaron nan ya samu ya bude idanunsa ya waiga, sai kuwa ya ga wani rafi mai fadin gaske ya taso gadangadan babu abin da ruwan rafin nan ke yi illa ya cinye dukkan abin da ke gabansa ya zama ruwa. To abin ne da wuya, kai ba abin yaron ya tashi ya shafa a guje ba, domin ainihin shi wannan ruwan da ya nufo wurin yaron nan yana gudu ne a kan kimanin mil goma sha 6 Tauraruwa Mai Wutsiya biyar a cikin minti daya. To kuma da a ce wannan rafi ba a hakan nan yake gudu ba, ita ainihin mesar nan da iska ta tunkude tana gaban yaron ne, kuma babu hankoron da mesar ke yi irin ta sami na kalaci. Shi dai abin duk ya dagule masa, sai dai saukin abin da ya zama komai zuwa yake yi ya wuce, kuma bayan wuya sai dadi. Mutuwa kuma ai kowa ya sani sai Allah ya yi, saboda haka sai ya zabi ruwa ya cinye shi, tun da ma ya tuna cewa lokacin da ya ke gida shi da sauran yara 'yan'uwansa sukan ce wai dukkan wanda ruwa ya ci shi, to yana da rabo a lahira. Oh! Lallai wannan yaro da cijewa ya ke, tun da dukkan irin wadannan ayyuka da ya gani bai yi ihu ko kururuwa irin na mata ba, ko sowa, ko wani irin firgici da dai zai nuna ya ji tsoro. To amma fa wa ke gane mini kirjin wannan dan yaro? Sai bugawa yake yi, das-dadas-das-dkhdkh. Duk da haka dai shi yana tsammanin cewa da ya samu ya shige cikin ruwan nan, to zai sami sa’ida, ya kuma sami suna, to amma ina? YAU NE SUNANKA DAN SAMARI Ko da ruwa ya zo ya shafe wurin nan da wannan yaro mai azaliyyar ganin taurari ya ke, sai fa ruwan nan ya shanye shi. To ko da ruwa ya cinye yaron nan sai ya yi tunanin cewa, "Ahaf ai tun da ya ke da sauran raina na iya ruwa a kauyenmu inda nake haye rafin Kululu." Sai ya yi wuf ya shiga iyo, to amma ina? Ya wantsala hannunsa na dama ke nan ya dauko na hagun zai yarba sai ya ga wata yarinya sharbebiya a gabansa, wuf shi kuwa sai ya dauki hannunsa ya shafe fuskarsa don ya tabbatar da cewa a'a ba mafarki yake yi ba. Ya ga har yanzu dai yana ganin wannan kyakkyawar yarinya, kai shi dai bai yarda ba sai ya ce ko 'yar ruwa ce wannan kuma Allah ya hada shi da ita? Sai ya sa hannu ya koda wa kansa mari, ya kuma marin kansa sai ya ga dai yarinyar nan tana nan. Sai ya ce, "Bari kawai watakila ba mafarki ba ne, amma ko me ake ciki bari in yi kumajin kura komai ta fanjama, fanjam, in koda wa wannan yarinyar mari." Ko da gama tunaninsa, bai yi wata-wata ba sai kawai ya yi iyo ya nufi wurin yarinyar nan, ko da isarsa kuwa babu abin da ya yi sai ya koda wa yarinyar nan mari. Allah Sarki, da ya sani da bai yi wannan mari ba. Domin kuwa bayan ya yi marin ne, sai ya ga yarinyar nan hawaye na 7 Tauraruwa Mai Wutsiya zuba daga idanunta, ko da yake a cikin ruwa ne, to, amma kafin a yi haka sai ya ga hawayenta ya taru waje daya, da ya yi yawa kuma sai ya zama hankici sai ta ce masa, "Ya kai wannan dan kyakkyawan saurayi, wannan hankici ka share mini hawayena ko na ji dan sanyi-sanyi a zuciyata." Yaro fa a lokacin ya dauki hankicin nan, yawu na zuba a cikin ruwa don saboda mamakin yadda wannan yarinya mai mafificin kyau za ta ce masa ya share hawaye ko ta dan ji sanyi. Ita dai wannan yarinya fara ce sal, ga dai idanunta dara-dara, ga gashin kai, ga ta kuma kamar mutum ya leka, ya duba fuskarsa, ga farinsu kamar ba a sa musu tsaki a ciki, ko kuma ba a yin tauna da su. Ga ta kuma ta daura kayayyaki masu ruwan shudi da 'yan adon zinare a gefensu. Rigar da ta sa kuwa ta kama ta tsaf, ga maman nan nata ya cika kirji, kuma ya yi mata daidai wa daida, yadda har ya kara ingiza wannan yaro cikin tunanin ko a wace irin halitta ita wannan yarinya ta ke. Ga girar nan tata ta fito ziyat kamar an ce tsaya in dan ja miki ita da gazal, da idanun nan nata suka yi rau rau, sai duka abin ya kara zamowa fyas domin kuwa sun yi wani dan shudi-shudi, haka kuma suka kara mata kyau. Ita kuwa ta daura wani zani wanda ya dan rufe mata kafa, to, amma saboda ruwa ya dan karkada shi. Yarinyar nan ta gaji da jiran yaron nan don ya share mata hawaye da hankicin nan, har kuma ta yi gudun ko me zai same shi, sai ta ce, "To, bawan Allah ai sai ka rufe bakinka." Sai kuma ta kama hannunsa mai hankici ta share fuskarta, ta kuma share masa tasa. Ko da ta share masa fuska, sai ga su tare a cikin wani tafkeken gida. Shi tun da ya ke bai taba ganin kamar wannan dandasheshen gini ba. Ga daben cikin dakin da su ke an yi shi da wadansu irin duwatsu farare masu ban sha'awa ga shi kuma daben an zo an rufe shi da wata irin shimfida mai dan karen kyau da taushi. Ga fitilu, sai ka rantse kamar masu lantarki sun yafe wa mai gidan biyan kudin lantarki, ga su iri-iri, launi-launi ga wadansu irin furanni na kallo an saka su a cikin wani irin kofi na zinariya mai ban sha'awa da ke kan tebur. Can kuma ga irin kujerun nan na roba wadansu masu lilo, wadansu masu kewayawa da kansu, wadansu masu lollotsawa da mutum, duka dai yaro sai kallo yake yi kamar yadda ya kammata. Yarinya sai mamakin yaro take yi, yaro kuma yana mammakin ita yarinya, ga kuma irin wannan wuri da suka shiga 8 Tauraruwa Mai Wutsiya mai kama da wanda ba za a taba samun irinsa a duniya ba. Suna cikin tafiya sai ya duba daga dama, sai ya ga ganguna da kayan busa, da dai kayayyaki irin na kida wadanda ake yin kida, a yi nishadi. Ya duba kuma daga hagu sai ya ga wata yarinya ta sheko, ta durkusa, ta yi musu barka da zuwa. Ita yarinyar da ke tare da shi Kilba sai ta amsa, to amma shi gogan naka Dan Kolin Koliyo ko amsawa bai iya yi ba, shi dai ya sa idanu kawai ya ga inda ita wannan yarinya za ta kai shi. Abin na da wuya a wurin shi Kilba don sai ya tuna da cewa, shi ya fito can wani dan kauye ne inda ya ke banda 'yan dakunan ciyawa ko soraye babu abin da suka sani. Yanzu ga shi cikin irin wannan alatu, to ai ka ga ma sai ya shiga tunanin a'a cewa ko a nan ne taurari su ke, tun da aininhin su dai ba su da lantarki a garinsu, balle a ce ko zai gane da wadansu abubuwa irin wadannan. Can sun kusa Karshen wannan daki da su ke ciki, sai ya ga ita wannan yarinyar da ya mara ta tsaya cik, ta yi tafi biyu raf-raf, sai kuwa ya ga wafansu 'yan mata biyu sun zo, sun ce da ita, "Me kike so ya uwargijiyarmu?" Sai ta ce a shirya wa wannan ruwan wanka, kuma in ya gama a shirya raye-raye da sauran abin da ya kamata na bako. Yau za a rada masa suna, saboda haka sai a je a fada wa Muhammadul Sunaye ya nutsa cikin shirin sunayensa, ya samo suna da zai dace da dan saurayin nan kyakkyawa. 'Yan matan nan suka amsa, suka kuma kama hanya don su cika umarni. Shi kuwa sai ya shiga tunani a zuciyansa cewa, "Watau cewa da na yi ina son suna shi ne har aka kawo ni wannan wuri domin a rada mini sunan?" Yana tafiya yana wannan tunani har suka kai ga wadansu kujeru guda biyu, ita ta zauna, shi kuwa bai san sun kawo wurin ba, har ya ci karo da kujerar ya fadi, to ko da ya fadin ma sai ya yi na kayen malami da ya samu kaye daga jaka, ya ce ko da ma nan zai yi Salla. Sai kawai yaro ya zauna ya mimmike kafansa wai shi ya sami shimfida. Shi kam bai ma san cewa

Chapter 1 of 7