abin da mutane suka gaza
ganewa,har ina tunaninna yi
SADAUKARWAr burina ga mutane don na
tsira da mutuncina. To amma na kasa jure
hakan, ina fatan na yi auren da zan samu
nutsuwa وو
Alhaji Mande ya murgina kai yana fadin.
"Ban ki ta taka ba, amma hujjar ida
99
mutane za su dubeka da ita na ke nema...o
Alhaji Atiku ya ce.
NAJNOOR113
SADAUKARWA-I
"Tunda ka gaza fahimta ta, bari na fada maka matsalolin da na ke samu da matana, ba
wai don ina alfahari ni mai gaskiya ba ne, zan
fada maka sirrina ne don ka zamo adali a cikin
lamarin da mutane ke zargina da shi".
A nan ya kwashe masadukkan
matsalolin da suka raba shi da matansa yá fada
masa, daga karshe ya dora da cewa.
"Na sanya wa raina na hakura da aure
akan wannan dalili tunda haka Allah Ya tsaro
min, amma da ya ke ba ni ke tsarawa kaina
rayuwa ba shi yasa na hakura da abin da
Ubangijina ya tsara min, kuma ina zuba wa
sarautar Allah ido".
Alhaji Mande ya yi shiru cikin nazarin
maganganun "Alhaji Atiku, hakika yaji
kamshin gaskiya a maganar tasa, domin duk
wanda zai yi mu'amala da shi zai tabbatar shi
akili ne, bare kuma ga iyalansa sai dai da ya ke
akwai wasu mazan da a waje suke muminai a
cikin gida azzalumai, shi yasa ba lallai ne a
yarda da hujjar da zaj bayar ba.
NAJNOOR 114
K
SADAUKARWA-1
ce.
Bayan wani dan lokaci, Alhaji Mande ya
"Na gamsu da bayaninka, na tabbata
kuma idan da rai da rabo, Allah zai amshi
bukatunka Ya baka mace wadda ka ke muradi...
Hakika Zahra'u yarinya ce mai tarbiyya da
kamun kai, wadda duk fadin unguwar nan zan
iya rantse maka babu wadda za ta kamo ko da
sawun kafarta ne.
Mahaifinta Malam Audu mai almajirai ya
tsayu tsayuwar tsayin daka wajen tarbiyyar
yaransa, shi yasa duk wanda zai dube ta zai
dauka matar aure ce, na yi mamaki matuka kai
da ka ganta ka sanya wa ranka ba ta da aure.
ban san abin da Allah ke nufi da hakan ba, wata
kila kai ne abokin rayuwarta... Lallai idan ka
samu nasarar auren Zahra'u zai yi wahala ka
samu wata 6araka daga gareta, sai dai idan daga
gareka ne matsalar za ta kunno kai"
Alhaji Atiku ya ji wani sanyi-sanyi ya
ratsa zuciyarsa da ya ji ba ta da aure,. fuskarsa ta
yalwatu da murmushi, ya сe.
NAJNOOR-115
SADAUKARWA-1
"Wanda ke son zuwa hajji a ka ce an biya
masa umra zai yi wasa ne da damar da ya
samu? Ai sam hakan ba mai yiyuwa ba ne, shin
yanzu me ye abin yi?"
Maganarsa ta karshe ta ba wa Alhaji
Mande dariya, ya ce.
"Abin yi ai ya rage gare ka, wai tsohuwa
ta auri jikanta".
Su duka suka yi dariya, sannan Alhaji
Atiku ya cе.
"Maganar gaskiya na yarda da
maganarka na cewar ta samu tarbiyya a
gidansu, amma duk da haka zan Kara lokaci
kafin na je gare ta, ka kara bincikawa ko a wani
wajen ne ka ji ba ta da wata matsala, ban so na
yi gaggawa na aureta na same ta da wata
matsalar a dawo ana cewa halina ne, duk da ban
isa na tsallakewa hakan ba idan Allah Ya
tsara.
Alhaji Mande ya ce da shi.
"Ba ni da shakku akan duk wani bincike
da zan kuma yi zai haifar da alkhairi, sai dai
kamar yadda ka ce din zan sake bincikawa ko
NAJNOOR 116
SADAUKARWA-1
don gudun kada na shugabancin lamarin na
dawo ina da na sani"
Alhaji Atiku ya ce.
"Ba ma fatan hakan ta kasance, kullum
fatanmu idan muka yi niyyar alkhairi Allah Ya
tallaba mana mu ga alkhairin a ciki... Tana
makarantar boko?"
Alhaji Mande ya ce.
"Eh to, kwanaki na ji an ce ta gama
sakandire, wanda shi ma abin ya ba wa kowa
mamaki ganin duk 'ya'yan Malam Audu ba sa
karatun boko sai akan Zahra'u... Ban sani ba ko
za ta ci gaba... kai ba na tunanin ma za ta ci
gaban"
Alhaji Atiku ya jinjina kai cike da farin
ciki, ya ce.
"Na ji dadin hakan, don wani lokaci
karatun mace idan ya wuce sakandire ana
samun matsala, duk da dai wasu rashin zurfin
karatun ma na haifar da wata matsalar, fatan dai
Allah Ya sa ba ta da tsayayye".
Alhaji Mande ya ce.
NAJNOOR 117
SADAUKARWA-I
"To wannan ne ban sani ba, don ko tana
da shi, ka'idar Malam Audu yaransa ba sa
zancen dare, kuma ba a kofar gida suke hira ba,
bare wani ma ya gansu
Alhaji Atiku ya sake jinjina kai, ya ce.
"Wallahi tun yanzu ma na soma samun
nutsuwa akan lamarin, ina ganin kamar kakata
ce ta yanke saka".
Suka sake yin dariya su duka, Alhaji
Mande na shirin yin magana Hafiz suka iso
bakin motar shi da abokinsa Habib.
z "Yauwa Hafiz, kwara da ka dawo, dama
mun gama kai na ke jira"
Inji Alhaji Atiku yayin da suke kokarin
fitowa daga motar shi da Alhaji Mande.
Habib ya rusuna ya gaishė da su, sannan
Alhaji Atiku ya takawa Alhaji Mande zuwa
kofar gidansa. Sun shiga motar, Hafiz ya dubi
Habib ya ce. A th
"To abokina, sai ka shigo goben ko, don
Allah ka cika alkawari
Habib yana dariya ya се!
NAJNOOR118
SADAUKARWA-1
lafiya
"Kada ka damu, Allah Ya sauke ku
Ya ce, "Amin", Sannan ya tayar da motar
suka soma tafiya:
Alhaji Atiku da farin cikinsa ya kasa
boyuwa ya dubi Hafiz ya ce.
"Rage sautin kira'ar nan na baka wani
albishir
Cike da dokin jin abin da ya sanya
mahaifin nasa farin ciki ya kai hannu ya kashe
rediyon ma gaba daya, tare da tattara
nutsuwarsa zuwa ga mahaifin nasa, ya се.
"Ina jinka Abba, daga ganin yanayin
fuskarka akwai dadadan albishir a tare da kai"
Alhaji Atiku ya kara yalwata fuskarsa da
murmushi ya ce.
"Auren dai zan Kara"
Yanayin fuskar Hafiz ta sauya zuwa
yanayin tuhuma da kuma tausayi, ya lura
idanun mahaifin nasa sun rufe yin auren shi ne
kwanciyar hankalinsa, dazun fa da suka taho ya
ke masa zancen zai kara aure, shi bai dauki
maganar gaske ba ganin yadda lamurran suka
NAJNOOR 119
SADAUKARWA-I
kasance, sai ya dauka zuwa yanzu din dai zai
iya hakura, ashe da gasken ya ke, ko dai dama
neman auren ne suka zo yi gidan Alhaji Mande
ba maganar fili ce ta kawo su ba?
"Wata yarinya ce na gani daga dukkan
alamu ta fito daga gidan mutunci, kuma
ganinta kawai da na yi sau daya jikina ya ba
ni ita ce macen da na ke mafarkin samu, don
haka na tuntubi Alhaji Mande ya ke sanar da
ni tarbiyyar gidansu din dai irin wacce na ke
so ce... To yanzu mun aje magana da shi zai
Kara bincikawa don kar ai aikin da na sani".
Jin hakan ya sanyaya wa Hafiz rai, don
ya yi tunanin addu'arsu ce Allah Ya karba ya
hada mahaifin nasa da irin macen da ya ke
fatan samu, sai dai kamar yadda shi mahaifin
nasa ya fada, matan ba tukwane ba ne bare a
kwankwasa a ji wacce ta fi kwari, daga
ganinta cikin lullubi sai a ce ta gari ce?
Amma kuma ai ya ce masa Alhaji Mande ya
tabbatar masa da ingancin tarbiyyar gidan su
yarinyar, wanda a saninsa Alhaji Mande
NAJNOOR 120
SADAUKARWA-1
kamilin mutum ne mai yakana, zai yi wuya ya
fadi abin da babu shi a bayyane.
Cike da farin ciki ya ce.
"Kai amma zan fi kowa farin ciki idan
har a ka same ta da kyawawan halayen da ake
fata, ina kuma goyon bayanka dari-bisa-dari
akan haka, Allah Ya tabbatar man da abinda
ya fi zama alkhairi".
garı
Alhaji Atiku ya ce da shi.
"Amin, kai ma Allah Ya ba ka mace ta
وون
Murmushi Hafiz ya yi, tukunna ya сe.
"Gaskiya zan fada maka Abba, sati
biyu da suka wuce na hadu da wata mata a
wajen aikina, tana da nutsuwa da kamun kai,
sai dai matsalar da na ke tunani ita ce, na
fuskanci kamar matar aure ce, don tana da
kamewa irin ta matan aure, sannan wani
وو namiji ne ya ke kawo ta
Alhaji Atiku ya yi dariya sosai, ya сe.
"Kamun gafiyar baidu ke nan, kai
kanka ka ce kana ganin matar aure ce, to don
NAJNOOR 121
Π
SADAUKARWA1
i
me za ka sanya zuciyarka a ragayar da ba za
ka iya fita ba?"
Ι
と
a
g
n
ha
ni
SC
ka
:
ya
ha
fal
na
kv
ga
Ar
tat
ya
Shiru Hafiz ya yi, kuma fuskarsa ba ta
gushe daga murmushin da ya ke yi ba, don
mahaifinsa shi ne abokin shawararsa, ya kasa
hakuri ne ya boye masa ya ga kwara ya fada
masa wata kila zai taya shi da addu'a Allah
Ya cire masa sonta.
Alhaji Atiku ya ci gaba da cewa.
"Wata kila kuma ba matar auren ba се,
kamewa ce irin ta gidan kwarai wadda ake
son kowacce mace ta same ta, don haka sai ka
dage da addu'a idan ba matar auren ba се
kuma alkhairi ce a gare ka Allah Ya ba ka ita,
ni ma zan ci gaba da yi maka addu'ar da na ke
maka ta fatan samun abokiyar zama
managarciya"
Ya ji dadi ainun à ransa, shi dama ya
san mahaifinsa mai karfafa masa gwiwa ne
akan duk wani abu na alkhairi, yа сe.
"Amin Abba, kuma gobe idan Allah Ya
kaimu zan bincika na gano shin matar auren
NAJNG
SADAUKARWA-1
ce ko ba ta da aure. Idan tana da aure zan
rungumi hakuri, har Allah Ya zaba min mai
kyawawan halaye kwatankwacin wanda na ga
ta siffantu da su. Idan kuma ba ta da aure, to
fa zan ce maka na samu.
sb s) Kunya ta sa ya kasa karasawa, sai shi
Alhaji Atikun ne ya ce.
sb Ka samu mata ko? Daina jin kunya,
kai abokina ne kuma dana ne".
Haka suka iso gida cike da jin dadi da
nishadi, musamman Hafiz da ya ke ganin
lokaci ya zo na farin ciki a gidan nasu. Suna
tsayawa da motar Alhaji Atiku ya fito ya
shiga cikin gida, yayin da shi kuma Hafiz ya IHNAGU
ja motar zuwa wani wajen.
nimoSai da ya zo kwanciya ne tunanin ya
sha masa kai, wato tunanin Fadimatu, shi kam
zai yi ittifakin son da ya kewa Fadima kusan
ya fi wanda ya ke wa Rufa'atu duk da kuwa
ita ce wadda suka dade kuma ya fara so a
rayuwarsa, sai dai shi so ya gaji haka, shiga
NAJNOOR 123
SADAUKARWA-1
ya ke ya kurda inda duk mutum bai yi
tumaninsa ba, don haka ba zai yi jayayya
cewar Fadiima ta yi masa shigar burgu ba.
Takaicinsa daya rashin tabbas da ke t
dawainiya da lamarin nasu, hakika yana cikin
a taraddadin tabbatuwar Fadima wadda ba ta da
aure, domin alamomi sun bayyana kansu na
n cewar ita din mai auren ce, amma duk da
h kokarin da ya yi na ganin ya taushi zuciyarsa
n ta hakura da son matar wani hakan ya ci tura,
S don haka ya sanya wa ransa hakuri da
k kaddarar da ta zo masa, mai kyau ko mara
kyau.
y Fata da burinsa ta zamo mallaki a gare
ha shi, musamman don ta maye masa guraben
fa filayen da ya rasa na cikon farin ciki a
n zuciyarsa da rayuwarsa gaba daya, domin
k kowane dan Adam ba shi da kwanciyar
ga
A
ta
ya
hankali muddin bai dace da matar aure ta gari
ba, wadda za ta iya ba wa 'yalyansa tarbiyyar
kwarai mai nagarta,
NAJ 124
SADAUKARWA-I
Kuskure daya ne ya ke ganin ya tafka,
na saurin sanarwa mahaifinsa lamarin, anya
bai yi kuskure ba? Koda ya ke ai dama ya
sanar masa yana tunanin tana da aure. Da
haka dai ya samu baccin ranar ya dauke shi.
Washegari da ya je kamfani yana zaune
a ofis dinsa, zuciyarsa ta azalzale shi ya fito
harabar kamfanin don ganin ko zai gam-dakatar da ganin Fadima. Bai wani jinkiri ko
tsayawa shawarar yin ko barin ba, kai tsaye ya
fito harabar ya tsaya a jikin motarsa.
Kamar ko yaushe bai fi mintina goma
da tsayuwa ba ta danno kai, wannan karon
abin ya ba shi matukar mamaki, domin ita
kadai ya gani tạ shigo cikin harabar kamfanin
sabanin kowace rana da namiji ne ya ke
kawota akan mashin dinsa.
Tafiya ta ke cikin nutsuwa ba ta ko
duban gefenta, illa gabanta inda ta ke takawa
ke nan. Ya shiga tunanin me ya hana matashin
ya kawota a yau kamar yadda ya saba?
NAJNOOR 125
k
is
n
b
a
g
n
h
n
S
R
:
ya
h
fa
ni
SADAUKARWA-1
Amsar da ta gaza samuwa ke nan a gare
shi, illa binta da kallon kawai da ya dinga yi
har ta kusa shigewa ta gefensa, ga dukkan
alamu ba ta lura da wanzuwarsa a gurin ba,
babu mamaki domin ai ba ta cikin yanayin da
za ta iya lura da shi din. Mace mai tafiya tana
waige-waige ita ce ta ke ganin kowa har idan
a ka yi katari da marasa kamun kai ko kuma
masu irin surutun nan, sukan kasa tsallakewa
kula wanda suka gani koda kuwa ba ya cikin
irin mutanen da ya kamata su kula a lokacin,
ma'ana wadanda kula su ko rashinta ba ya
amfanarsu da komai.
Zuciyarsa ta ayyana masa kawai ya
tanka mata, wani tunanin. kuma da ya yi na
rashin dacewar hakan ya hana shi.
Har dai ta shige ajin da suke daukada
k karatun yana tsayc sagale da baki, abin da ya
lura da shi, kullum tana sauya kayan da ke g
A jikinta, hijabi dai ce kamar ba zasu wuce guda
ta
y
biyu wadanda ta ke da su ba, tunda shi dai a
iya saninsa da ita hijabai biyu ne ya ke
126
SADAUKARWA-I
ganinta da su, idan ta saka wannan yau, bayan
kwana biyu ko uku sai ta sauya.
Hakan yana bayyanar da rashin wadatar
arziki da suke fama da shi. Haka a bangaren
kayan da ke jikin nata ma dai ana gane rashin
da suke da shi, domin kusan kayan duk sun
koke, hatta da takalman kafarta da yá nacewa
ganinsu sau biyu ya lura akwai karancin
babun dai a tare da ita. Sai dai duk wannan
bai zamo nakasu ko wata madogara da za ta
rage karfin sonta da kaunarta da ko yaushe
suke kara cushe masa zuciya.
Bayan dan gajeran lokaci da ya dauka a
gurin, ya nufi ofis dinsa ya zauna, hakika yau
yana muradin tattaunawa da Fadima, sai dai
ya rasa azancin da zai yi amfani da shi,
hanyar da ya ke da ita ta zuwa ajin nasu yayin
da lokacin daukarsu, karatu a darasinsa, to ga
shi ba shi ne ya ke daukar nasu a yanzu ba.
Har dai tsayin mintina ashirin yana
zaune a cikin wannan yanayi, zuwa can sai ga
wayar Habib ta shigo wayarsa. Hannunsa har
NAJNGOR 127
SADAUKARWA-1
rawa ya ke wajen dauka, ya kara ya kunnensa
yana fadin.
"Haba Habib wallahi ka ba ni mamaki,
har sai yaushe ne za ka sauya halinka ne na
rashin cika alkawari? Na dubi tsayin lokacin
da ka dauka kana wannan halayyar, tun fa
muna sakandire a ce duk lokacin da ka ce za
ka zo guri ba za ka zo ba? Yanzu me kake
nufi da ka kira ni?
Daga can bangaren Habib ya yi dariya
ya ce.
"Dadina da kai azarbasi da rashin
hakuri. To ga ni nan cikin harabar
kamfaninka, dama kira na yi na ji kana ofis
ne, don ban ga motarka a harabar ba".
Ya ce, "Da wannan an tura, tsohon
banza biko ya ce in ba a mayar masa ba ina
wa dana riko
Suka yi dariya su duka, yayin da Habib
ya kashe wayar ya nufo ofis din Hafiz. Yana
zama ya mika masa hannu suka yi musabiha,
Hafiz ya dora da fadin.
NAJNOOR 128
SADAUKARU'A-
"Haba ai na dauka halin za ka yi min,
ka san a duniya babu abin da na tsana irin mu
yi alkawari da mutum zai zo ko za mu hadu
da shi lokaci kaza ya ki zuwa da wuri, sai na
ji kamar na makure shi ya mutu don tsananin
bakin ciki”
Habib ya yi dariya ya сс.
"Kai kuma ga ka da bakar zuciya ba,
sai ka ce za ka ba wa mutum wani abu".
Bayan sun gaisa ne, Habib ya ce.
"To ka ce na zo game da matsalar da ke
damun zuciyarka, wadda har ta ke hana maka
bacci, shin wace matsala ce? Nai san dai a
rayuwa babu abin da ke wahalar da kai irin
biro da takarda, idan akwai abu na biyu da za
a dorar to kuwa na'ura mai kwalwa ce... Shin
mene ne labari? Ko kuwa da gaske ne labarin
da na ke samu na cewar ka samu wata
budurwa 'yar Katsinawa masu asirin gado ta
sarkafe maka zuciya da nau'in asirin nasu?"
An famo masa inda ya ke masa kaikayi,
don har yanzu idan za a ambaci Rufa'atu ko
NAJNOOR 129
☐
1
1
S
y
ha
fe
na
a
SADAUKARWA-1
wani labari da ya shafe ta yana jin kaunarta na
nukurkusar masa zuciya. a Gangare daya
Kuma yasan Habib ba shi da masaniya game
da mu'amalar da ya yi da Rufa'atu har kawo
rabuwarsu, tunda ba wani shahararren
haduwa suke yi ba, abokai ne dai wanda
makaranta ce jigon haduwarsu, kuma ana
mutumta juna da karrama uzurorin juna, shi
yasa duk lokacin da suka hadu sai ka dauka
suna tare ne koda yaushe.
Murmushin karfin hali Hafiz ya yi, ya
Ce meb
"Ko daya ba ma akan 'yar Katsinawa la
ba ce, wata jarabawa ce la same ni Habib na
rasa yadda zan yi da zuciya ta wadda ta ke
azalzalata da kuma tunzurani fadawa tarkon
halaka
Bis Habib yaa dan call fito da idanu waje yana
kallonsa cikin rashin fahimta, ya cе.
"Ban gane tarkon halaka ba? Ina
takawa da zuhudun da nasan ka da su Hafiz?
Subhanallah. kai kuwa me ya kaika barin
NAJNOOR 130
SADAUKARWA-/
zuciyarka kusanci da shaidan la'anannc har
ya ke kissima maka shiga hurumin da ba na
halak ba?"
Hafiz ya cije laßbansa cike da jin zafin
abin da zuciyarsa ke raya masa game da matar
da har lokacin ba shi da tartibin sanin
makomar rayuwarta, ya се.
"Na rasa yadda zan yi ne Habib, da ina
da iko da zuciyata da ba a kawo yanzu ina
tare da wannan gambon da ya gama nakasa
min rayuwa ba, har na iya kiranka domin
kawai na furta maka... Habib wallahi
rayuwata tana cikin hadari akan SOYAYYA!
وو Ná tabbatar ni ba mai sa'a ba ne...
Da sauri Habib ya katse shi da cewa.
"Ashe ka san gaibu tunda har ka
tabbatar ne ba hasashė kake ba?"
Hafiz ya girgiza kansa, yana fadin.
"Ba nufina ke nan na sanin gaibu ba,
abin da ya faru da ni ne a baya akan budurwar
da ka samu labarin na yi mu'amala da ita 'yar
Katsina, da kuma wannan da zuciyata ta kamu
NAJNOOR 131
SADAUKARUA-1
da tşananin sonta shi ne yasa ni wannan
magana
Bai boyewa Habib komai ba, ya sanar
masa duk yadda, lamarin ya kasance na
tsakaninsa da Fadima, amma bai ba shi
labarin dalilin rabuwarsa da Rufalatu, wadda
mahaifinsa yasa ya rabu da ita ba, domin yana
ganin wannan sirrin gidansu ne wanda bai
kamata ya bayyana shi ga wani ba.
(Kuma haka din ne, ya kamata 'yan
uwa mu kasance masu zurfin ciki, ba komai
ne ya kamata mu fadawa aboki ba, gudun
mummunar shawara, musamman abin da ya
shafi umarnin mahaifa, shaidan ya fi rinjayar
zuciyar mutane ga bijirewa umarni. Allah Ya
sa mu dace da rayuwa ta gari mai inganci,
ameen).
Da ya kare ba shi labarin, Habib ya
girjgiza kansa ya çe.
"Gaskiya ni kaina na jiujinawa sakacin
da ka yi wa zuciyarka haka har shaidan ya
makwabtace ta tana bijiro maka son wadda ba
NAJNOOR 132
SADAUKARWA-1
ta dace da ka so ba, haba wannan wane irin
al'amari nc mai kama da almara, daga ganin
-mace sai ka nace lallai ita kake so bayan
kuma kana tunanin tana da aure, tunda har ga
shi mijin nata ne ma ke kawo ta?
Wallahi ka ba ni haushi da takaici
Hafiz, kuma da na san haka ne da ba zan zo
gare ka ba... Sai dai tun da shawarata ka
nema, gaskiya ba zan ja ka da nisa ba, ina
shawartarka da ka hakura ka janye daga son
matar mutane, ka rarrashi zuciyarka ko da ta
ki ba ka hadin kai ka tursasata gujewa fadawa
halaka..."
Tun kafin ya Karasa Hafiz ya runtse
idanunşa yana jin wani abu na yi masa yawo a
kirji, ya rasa yadda zai kwatanta yadda ya ke
jin Fadima a ransa.
Lokaci, daya kuma ya ji ya cika da jin
haushin Habib wanda ya ke ikirarin ya rabu
da Fadima, domin a ganinsa duk wanda ya ke
neman ya ba shi shawarar rabuwa da ita ba
'mai sonsa ba ne, ina ma laifi a ba shi shawarar
NAJNOOR 133
SADAUKARWA-I
yadda zai same ta a matsayin matarsa ko da ta
kasance matar wani ba wai a ce masa ya
hakura da ita har abada ba.
Suka yi shiru na tsayin wani lokaci,
kafin daga bisani Habib ya katse shirun nasu
da cewa.
"Wannan ita ce kadai shawarar da na ke
ganin ta dace na ba ka, idan ka ji ke nan, idan
kuma ka nace har ka kai kanka fadawa tarkon
matar aure sai mu ce Allah Ya fidda A'i daga
rogo, don tun kafin aje ake shawara kuma an
baka"
Hafiz ya ce, "To na gode Habib
Habib ya yunkura ya се.
"Ni bari na wuce".
Shi ma Hafiz ya yunkura yana fadin.
"Mu je na taka maka".
Suka fito daga cikin ofis din zuwa
harabar kamfanin, dai-dai lokacin da suka
kusa kaiwa ga mota ne Hafiz ya hango
Fadima ta fito daga cikin ajin da suke
NAJNOOR 134
SADAUKARWA-1
daukada karatu. Gabansa ne ya sake yankcwa
ya fadi, murya kasa-kasa ya ce da Habib.
"Ka ganta nan ta fito"
Habib ya juya a hankali ya kai dubansa
ga Fadima, yana fadin.
"Ba ka dai daddara ba ke nan?"
Hafiz ya yi shiru bai ba shi amsa ba,
ganin Fadima din ta kusa isowa inda suke, shi
ma sai bai sake cewa komai ba, ya shiga
kokarin bude murfin kofar motar.
"Yallabai barka da war haka"
Ta fada bayan ta dan rusuna.
Ya amsa mata cikin kulawa.
"Yauwa Fadima, ya ya karatu?"
Ta ce, "Alhamdu lillah". Sannan ta dora
da fadin
Haba malam Habibu idan ba yakimai
ya kawo gaba?"
Da sauri Habib ya juyo yana dubanta,
shi dama tun da ya ji, muryarta ya yi, tunanin
ya isan mai muryar. amma hankalinsa bai
kawo ita ba ce, ya cey
SAJNOORS135
SADAUKARWA-I
"Batula dama ke ce?"
Kai tsaye ta ce masa.
"Au kana nufin ba ka gane ni ba?"
Ya сc, "Та ya za a yi na gane ki kina
sanye da al'adar taki, kuma kin san ni ba nace
wa mace kallo na ke ba barc na shaida ki ta
farad daya".
Hafiz dai sun saka shi rudani, wato ma
Habib ya santa shi yasa ya ke ba shi shawarar
ya rabu da ita? Ko kuwa mene ne manufarsa
akan haka? Shin matar auren ce ko kuwa?
• Fadima ta ce, "Ai ko dai, amma na
dauka Yaya Isma'il ya fada maka a nan na ke
training din computer?"
Yà girgiza kai yana fadin.
"Wallahi ban sani ba, maganar ba ta
hada mu ba... Ina ya ke ne ko ba shi ke kawo
ki ba?"
Ta ce, "Shi ke kawo ni, yau ya tashi
yana fama da matsanancin ciwon kai ne shi
yasa bai samu kawo ni ba, yanzu ma sauri na
ke na koma gidan na ga ya jikinsa
NAJNOOR136
SADAUKARWA-I
Habib ya ce, "Ah to mu je mana na
ajiye ki, tunda ni ma gidan na nufa".
Ta ce, "Ai kuwa na gode, Allah Ya saka
da alkhairi"
Hafiz dai bin su ya ke da kallo, har
Habib ya bude mata mazaunin gaba daga
gefen direba ta shiga, shi ma ya shiga, sannan
ya samu bakin magana.
"Mutumin zan shigo unguwarku da
yamma"
Habib ya dan harare shi eikin sigar
wasa. Ya сё.
"Kurugus! Tatsuniyar ta kare ba sai, ka
shigo ba".
Hafiz na niyyar sake tofawa, Habib ya
zuge gilashin moțarsa, sannan ya tayar suka
fice yaná yi wa Hafiz dariya ta cikin motar.
Mamaki, da kuma alajabi suka lullube
zuciyar Hafiz, a yau dai ya samu saukin zafin
rudanin da ya ke ciki a game da Fadima,
domin idan har shi mai fahimta ne a cikin
zantukan da ya ji Habib da Fadima din sụn
NAJNOOR 137
SADAUKARWA-1
tattauna zai iya tantance matsayin da ya
kamata a dorata a kai.
Tabbas ba matar aure ba ce, kuma
wanda ya ke kawota yayanta ne mai lakabin
YAYA ISMA'IL, idon haka ne kayansa sun
tsinke a gindin kaba ke nan? Karin hasashen
nasarar tasa ma da Habib ya kasance ya san
ta, wata kila ma unguwarsu daya, ko kuma
'yar uwarsa ce.
A şanin da ya yi wa Habib adali ne, mai
kuma taimakon abokansa a tun zamanin
rayuwarsu ta makaranta, ya san zai yi wahala
ya kife masa ciki bai taimaka masa ya mallaki
Fadima a matsayin matar aurensa farin cikin
rayuwarsa ba.
A haka Hafiz ya wanzu cikin farin ciki
tsayin yinin wannan ranar, da yammaci lis ya
dauki hanyar gidan su Habib.
Sai dai ya taki sa'a, domin Habib din ba
ya gida, da ya kira wayarsa yana dauka ya ce.
"Dama mun yi da kai za ka zo ne?"
Hafiz yana dariya ya се.
NAJNOOR 138
SADAUKARWA-I
"Kar mu yi haka da kai mutunina, na fa
ce maka zan shigo da yamma ko?"
"Amma me na ce maka? Ina ce na се
tatsuniyar ta kare ko? Fadima da kake gani
matar aŭre ce, matar abokina ce don haka sai
ka sa hakuri ka kuma kiyaye, don zan iya
daukar kowane mataki a kanka don kiyaye
hakkin auren abokina..."
Daram! Gabansa ya sake yankewa ya
fadi, wannan wane irin lamari ne haka, komai
ya ke ganin nasara sai kuma hakan ya sha
ruwa? Yanayin da Habib ya yi maganar a
wannan lokaci ya nuna sam ba ya cikin
annashuwa, kamar ma ransa a бace ya ke,
wanda hakan ke tabbatar masa da lallai
maganar tasa hakan ta ke, Fadima matar aure
ce!
Saboda haka murya a raunane ya ce.
"Yanzu don Allah kana ina? Wallahi
ina son ganinka".
NAJNOOR 139
SADAUKARWA-1
Habib ya ce, "Gaskiya babu dama, ka yi
hakuri idan na samu lokaci zan zo har inda
kake da kaina".
Hafiz ya sake marairaicewa kamar zai
yi kuka, ya ce.
"Don Allah kada ka yi min haka
abokina, sanin kanka ne ina cikin wani irin
rudani, wanda ya kamata a ce na samu masu
tausar zuciyata don samun maslaha ga
...rayuwata وو
Habib ya katse shi.
"Tunda har ka san kana cikin rudanin,
ai abu ne mai sauki ka cire kanka a ciki,
domin mutumin da bai san yana cikin rudani
ba shi ake hangowa rudanin har ai tunanin
hanyar da za a bi a cire shi..."
Shi ma Hafiz din ya tare shi da cewa.
"Na lura abokina ka dauka da zafi,
Allah Ya huci zuciyarka, idan dai Fadima ce
na hakura da ita har abada..."
Habib ya sake tare shi.
NAJNOOR 140
SADAUKARWA-I
"Ba ma sai ka kuma ganinta a kamfanin
naka ba sannan za ka nacewa sonta?"
Kafin ma ya ce wani abu tuni Habib din
ya kashe wayar, Hafiz ya yi zugudi ya ma
rasa mai ya ke masa dadi a duniya.
Ya dauki tsayin lokaci zaunc a mota
yana' tunanin abin yi, kafin daga bisani ya ja
dogon tsaki ya ce.
"ZUCIYA DA SHAIDAN! Allah ka
raba mu da sharrinsu!"
Ya tayar da motar ya sa kai zuwa gida.
*** *** ***
Abu kamar wasa, Hafiz ya daina ganin
Fadima a kamfaninsa tsayin kwanaki hudu.
Abin ya ba shi mamaki matuka, duk da dai a
bangare daya bai kamata ya yi mamakin
hakan ba, tunda Habib ya sanar masa cewar
ba za ta kuma zuwa ba.
Lallai yanzu ya tabbatar ya aikata
babbar katobara, me ma