tana gasa shi.
Yana kallon matashin da akalla zai kai
shekaru talatin ko fin haka ya ciro waya ya
kara a kunne, ba ya jin abin da ya ke fada
saboda akwai 'yar tazara tsakaninsu. Bai wani
jima yana wayar ba, ya ga wannan mata mai
sanye da nikab ta fito, ta iso wajen matashin
ta rusuna ta gaishe shi, sannan ya ga matashin
ya tayar da mashin din ta hau baya suka bar
harabar gurin.
Mamaki ya kama shi, kar dai a ce
wannan shi ne mijinta? Lallai ya dace mata
mai kaifin kwalwa, sai dai ita ta dace sa miji
NAJNOOR 85
SADAUKARWAtalaka fitik! Abin da ya ayyana a ransa ke nan.
Dama haka rayuwa ta ke, wani za ka same shi
da kaifin kwalwa amma sai rashi ya tauye
masa damar da ya ke da ita.
Bayan sallar isha'i ne Larab ya zo
gidan, suka nufi asibiti shi da' Hafiz.
Yanayin da ya tarar da Bintu ta ba shi
tausayi, don duk ta rame saboda yarinya ce
mai kumari amma ciwo ya ramar da ita.
Tausayin yarinyar ya kama shi, ko me ya ke
damunta haka har ciwon zuciya ya kamata?
Larab abokinsa ne, tare suka yi
sakandire har jami'a, don haka akwai
shakuwa tsakaninsu. Duk gidan su Larab ba
wanda bai san shakuwar da ke tsakanin Hafiz
da Bintu ba, domin tun tana yarinya idan zai
zo gidan yana taho mata da alawa,
kasancewarta yarinya mai son kayan zaki, shi LTELA
yasa da zarar Hafiz ya zo gidan da gudu za ta
nufe shi.
Yadda ya ke zuwa gidan yasa kowa ya
sanshi, suna kuma girmama shi, don duk
NAJNOOR 86
SADAUKARWA-1
Kannen Larab da Yaya suke kiran Hafiz
wannan koyarwa ce ta gidan, karami bai isa
ya kira sunan babba gatsal ba.
Yanayin shakuwar da ke tsakanin Hafiz
da Bintu ba yana nufin soyayya ba, don shi
bai dauke ta a matsayin macen da zai so ba,
duk da ba wani muni ne da ita ba, bai dai taба
jin haka a ransa ba, haka ba wanda ya taba
hasashen haka a tsakaninsu, ita ma a gare ta
(Bintu) babu watą alama ta soyayya da ta ke
duban Hafiz da ita, sai dai sun shaku ainun.
Lokacin da suka zo asibitin bacci Bintu
ta ke, amma kafin su tashi tafiya ta farka, tana
yin tozali da Hafiz fuskarta ta yalwatu da
fara'a, ta се.
"Haba Yaya Hafiz ai na dauka sai na
mutu za ka zo shan gumba?"
Ya yi murmushi ya ce.
"Hmm, na yi tafiya ne, ban ma san ba
ki da lafiya ba sai dazun Larab ya ke fada
min... Ya karfin jiki?
Ta ce, "Da sauki".
NAJNOOR 87
SADAUKARWA-|
Ya ce, "To Allah Ya kara afuwa, amma
ya kamata ki rage sanya wa kanki pressure da
yawa, koda-ya ke na ga alama sai an cire ki
daga makarantar nan tunda na lura ita ke
haifar miki da tunani har ga shi hakan ta soma
faruwa da ke"
Ta yi takaitaccen murmushi, ta ceuh
"Yaya karatun ne da wuya wallahi, ga
shi kuma ina so
Ya ce, "Duk da haka sai ki rage, saboda
lafiyarki".
abin?"
Ta maida dubanta ga Umma ta ce.
"Umma Yaya Larab ya kawo min
Umman tana murmushi ra ce
"Ai ga shi nan gabanki ba sai ki
tambaye shi ba?"
Larab ya ce, "Wane abu kuma?""
Bintu ta ce, "Zogalan ko?
Ya auna mata harara, ya ce:
"An ki a kawo, sai ka ce wani ci ta ke".
Ta dan sobare baki, ta ce.
NAJNOOR 88
SADAUKARWA-1
"Shi ke nan na ma daina cin komai"
Larab ya ce, "Yo wa kika yi wa? Ina ce
cikinki za ki kai"
Hafiz ya yi dariya ya се.
"Hmm Bintu rigima, yau kuma an
koma cin zogala?"
Ta juyo da ba wa maganarsa
muhimmànci ta ce.
"Likita ne fa ya ce na yawaita cin
zogala, yana kara jini da lafiya a jikin dan
Adam"
Hafiz ya ce, "To shi ke nan, bari gobe
zan kawo miki, kyale wannan man din ya
cika latsi da yawa i nsa
Sun dan jima asibitin sannan suka taho.
***
Bayan kwana biyu zuciyar Hafiz ta dan
yi sauki daga damuwar da ya ke ciki.,vibBm
Ya shigo falon gidan da niyyar ya
amshi abinci, tsautsayi kawai sai idanunsa
NAJNOORA89
SADAUKARWA-1
suka hango masa Hamdiyya ta ci kwalar
Alhaji Atiku cike da masifa, tana cewa.
"An fada maka ni ma irin matan da ka
saba' aura ne? To wallahi ni na fi karfin duk
wani iskancinka, rubuta min takarda ta na ce"
Hankalin Hafiz ya tashi ainun, duka
kwana nawa da yin auren har an soma
wannan artabu?
Alhaji Atiku ya ce.
"Ba zan ce da ke komai ba, don na lura
hauka da rashin tarbiyya suna tattare da ke"
Kamar ya watsa mata ruwan zafi, ta
sake dakumar rigarsa.
"Idan ba ka san ni mahaukaciya ba ce,
yanzu za ka sani, rubuta na ce maka!"
Takaici ya ishi Hafiz bai san lokacin da
ya karasa gurin da hanzari ba, ya dauke
Hamdiyya da wani gigitaccen mari, wanda ya
yi sanadiyyar daukewar kuzarinta.
Alhaji Atiku ya dubi Hafiz ya ce.
"Wa ya sanya ka?"
NAJNOOR 90
1-0.04 002 SADAUKARWA-I
si sast Kansa ya rusunanikasa ya kasa cewa
omaiAlbaji Atiku ya ci gaha da gowabnua
kent sBanasyoi kanashiga sabgar da ba laka
svieA BviigH idub 661-6t uliA ijsdIA
Kafin Alhaji Atiku ya gama fadan abin
da ya ke son fada, tuni" HamdiyyaMa rarumo
aniufarantida i kel|saman lebur la rotsawa
AMhajiAtiku a ka, men da nat goshinsalya
fashe, jini ya soma zuba. uensbiy
s uikin tsananin bacin rai da zafin nama
Hafiz va damko ta ya oi gaba da duka, Hajjya
Asiyanda ke labe tun da a ka fara rigimar tana
ganin ta'adin da Hamdiywalla yiaya Alhaji
sAtikuta fito dansauridanudigurin Alhaji
lAtikunyayin da shiikuma Hafiz ya oirgaba da
dukan Hamdiyya har suka fito harabar giden,
tana ihu da kururuwar neman taimakowowsh
nevsy Maigadi da ke zaunqaken benoi ya taso
a rikice yan kokarin Kwatar Hamdiyyardaga
schannun Hafinushiurkumas yanellciv gaba da
dukanta.isz isd sn sd ijimsa nimerodвг пілвг
.swo2 sb sdisd sy sm udsH
SONAJNQ0821491
SADAUKARWA-I
Da kyar maigadin ya kwace ta tana ta
kundumawa Hafiz ashar. ya juya ya koma
cikin gida. Lokacin tuni jini ya yi wa fuskar
Alhaji Atiku fata-fata, ya dubi Hajiya Asiya
ya ce.
"Mu je asibiti".
Suka fito da Alhaji Atikun su duka
ukun, lokacin tuni Hamdiyya ta gane hanyar
gidansu.
Suna zuwa asibitin suka samu a ka
karbe su, don ba karamin buguwa goshin nasa
ya yi ba sai da a ka yi masa dinki sannan a ka
ba shi gado ya huta zuwa anjima.
Karfe biyar na yamma-suka dawo gida,
suka tarar da yayyen Hamdiyya maza guda
uku da mata biyu suna zaman jiran
dawowarsu.
Suna ganin dirin motar, Hamza yayan
Hamdiyya ya taso da sauri, ya ce.
"Wallahi ka ba mu kunya, ba mu taba
sanin sahoramin namiji ba ne kai sai yanzu!.
Habu ma ya karba da cewa.
NAJNOOR 92
SADAUKARWA-I
"Ka dake ta, katon danka ya daketa?
Ina ba zai yiwu ba".
Alhaji Atiku ya yi murmushin vakaici,
bai ce da su komai ba. Hafiz ya се.
"Wata kila makafi ne ku'shi yasa kuka
gaza ganin abin da ya ke goshinsa! To ku yi
abin da zaku yi".
Sa'uma ta ce, "Kana nufin Hamdiy ya
ce ta fasa masa goshi? Ina wannan zuki ta
malle ce, ina Hamdiyya ta ke da karfin da za
ta yi kokawa da katti biyu irinku? Kun dai ji
kunya".
cc.
Alhaji Atiku ya nuna musu hanya, ya
"Ku fice min daga gida"
Lauwali ya ce, "Takardarta za ka ba
وو.
mu, kuma ka saurari sammaci
Alhaji Atiku ya ce, "Idan an je kotun na
bayar".
Ya sa kai zuwa cikin gida, su Hafiz
suka bi bayansa, yayin da suka bar dangin
Hamdiyya suna ta bambamin bala'insu.
NAJNOOR 93
SADAUKARWA-1
Wannan shi ne karshen auren Alhaji
Atiku da Hamdiyya, auren da duka-duka bai
kulla sati biyu ba, ai fa masu jini a farce suka
samu abin fada, wai lallai Alhaji Atiku
NAMIJIN ZARA ne, tunda ga shi wannan
auren ma ko tsawo bai yi ba har ya saki
ámaryar. Shi kam yana mamakin yadda
mutane ba sa yi masa adalci, duk lokacin da
sakin aure ya faru tsakaninsa da matansa shi
ake ba wa laifin, bayan an ce idan an ciza a
hura.
Yanzu ita Hamdiyya daga ta ce tana
bukatar kudi za ta yi kasuwanci ya ce, bai
amince da ta yi kasuwanci ba. Ta koma ta ce
tana so ta ci gaba da karatu, shi ma ya ce bai
amince ba.
Shi ke nan abin da ya jawo tashin
fitinar, wai dama ya aureta ne dan ya
takurawa rayuwarta ya tauye mata hakki, to
ita ba ta daga cikin matan da maza suke
rainawa wayo, idan bai sani ba ya sani tana
NAJNOOR94
SADAUKARWA-I
cikin kungiyoyin mata masu karc hakkin.
mata, don haka ita ba za a takura mata ba.
Abin ya ba shi mamaki, ya zauna yana
mata nasiha don su samu daidaito, amma fir
yarinyar nan ta ki fahimtarsa, ta ce, alo tsiya
alo danja sai ya barta ta yi yadda ta ke so,
kuma tunda tana da matsayi a kungiyoyinsu
na kare hakkin mata dole ya amince da yin
taro a gidan.
Shi kuma ya ce bazai yiwu ba, shi ya ke
aurenta dole ta bi dokokin da ya kafa.
To a nan me ye laifinsa? Amma saboda
rashin adalci na wasu mutanen sun ara sun
yafa wai halinsa ne auri-saki! To bai damu ba,
su ci gaba, aure ne dama ya sanyawa ransa
daga wannan zai hakura, ya kuma hakuran
insha Allah.
Hafiz ya fi kowa tausayin mahaifinsa,
halin da ya ke ciki yana damunsa ainun, sai
dai ya zasu yi da kudirar Ubangiji?
Yau ma kamar kullum a kan idanunsa
Matashin nan ya sauke dalibar akan mashin
NAJNOOR 95
SADAUKARWA-1
dinsa, tun kwanaki biyu da suka wuce Hafiz
ya tsirarwa kansa wata al'ada, da zarar ya
shigo gurin bayan ya shiga ofis ya ajiye
abubuwan da ya zo da su, zai fito waje ya
tsaya gurin motarsa yana kallon masu shiga
da fice a kamfanin.
Abin da kullum ya ke ba shi sha awa
bai wuce wadannan ma'aurata ba, domin suna
táfiyar da rayuwarsu cikin sauki, idan za ta
gaishe da matashin ka'ida ne sai ta rusuna,
haka idan za ta hau mashin abin gwanin
sha'awa don tana ba wa addini hakkinsa
wajen baza hijabinta gudun kada wani ya ga
tsiraicinsa.
Allah Ya sa ni bada wata manufa ya ke
kallonsu ba, sai don burge shi da suke. Lallai
talaka yana dace da mace, ina ma shi ne ya
dace da samun wannan mace haka?
To yau din ma yana tsayen ya ga ta
sauka daga kan mashin din, shi kuma ya buga
ya fice daga harabar gurin. A hankali ta ke
takunta har ta iso gab da inda Hafiz ya ke, ta
NAJNOOR 96
SADAUKARU'A-I
dan rusuna ta gaishe shi. Cike da jin dadin
yadda ta ke girmamashi ya amsa mata,
wannan halinta ne idan har za ta ganshi za ta
rusuna ta gaishe shi a matsayinsa na
malaminta.
Bayan ya amsa gaisuwar ta mikc za ta
wuce, yа се..
"Am ba ki ji ba".
Ta tsaya ba tare da ta juyo ba.
Ya ce, "Kin karbi handout din wajena
י"?kuwa
Ta dan juyo kadan, idanunta cikin
nikab ta се.
"Ban karba ba Yallaбai".
Ya ce, "Ko me yasa?"
Ta ce, "Zan karba ne".
Sai ya ji tausayinta ya kama shi, wata
kila ba su da karfin siya ne, karatun ma ya
lura karfin hali ne kawai irin na talaka mai
dogon buri, ba don haka ba ina za su sami
kudi har naira dubu ashirin na rajista?
NAJNOOR 97
SADAUKARWA-1
Ya ce, "To shi ke nan, idan na shigo
zan taho miki da shi".
Duk da a cikin nikab ta ke, hakan bai
hana ya gano firgitarta ba, shi ma sai ya ji
haushin kansa, me ya kai shi shiga shirgin
matar aure?
Ta ce, "Yallabai ka barshi, na gode"
Ya tamke fuska tare da kawar da kai daga dubanta, da kuma kokarin gotar da zuciyarta zuwa tunanin da bai dace ba, ya ce.
"Tsarin gurin nan ne, mukan ba wa. dalibai masu kokari tallafi ba da wata manufa ba, don haka zan shigo miki da shi".
Ta сe, "To na gode Yallabai".
Bai ce komai ba, ta wuce shi, ya dan juyo a hikimance yana binta da kallo har ta shige ajin da suke daukar darasin.
Duka daliban ba su wuce su sha takwas ba, amma yadda ya lura yarinyar ba ta mu'amala da kowa, hakan na matukar burge
Hafiz, yana son mace mai shariya domin irinsu sukan kula da mu'amala da mutanen da
NAJNOOR 98
SADAUKARWA-1
a
Iכ
ba su dace da su ba. mace mai karadi an fi
samun munanan halaye a gare ta.
a
د
כ
n
지
Lokacin da ya shiga ajin nasu, tana
zaune a mazaunin da ta saba zama, kanta a
sunkuye da alama wani abu ta ke dubawa. Ya
dube ta a nazarce sannan ya maida dubansa ga
sauran daliban da ke cikin ajin.
Bayan ya gabatar musu da darasin da
zasu gudanar a ranar, ya mike a hankali yana
takawa tarc da duba kowanne benci har ya
kawo kan inda ta ke zaune. Ba ta dago da kai
ba, sai ya zagaya ta bayanta yana kallon abin
da ta ke dubawa, wani littafi ne na koyon
computer, ya jinjina kai, wato ta mallaki ma
wasu littattafan bayan handouf?
A hankali ya koma can gaban allon,
sannan ya сe.
"Ina ganin gobe za mu fara pratical tunda kuna cikin mako na biyu da farawa, ina
fatan kun haddace duk abin da a ka koyar da ku?"
Gaba daya suka hada baki suka ce.
NAJNOOR 99
"Insha Allah yallabai".
SADAUKARWA-J
Ya lura ban da ita a ka yi magana, abin
sai ya dan taba masa zuciya, ba wai ya ji
haushin kin tankawarta ba ne, a'a a ganinsa
ya yi jam'i akalla tunda ita ma tana cikin
daliban ta amsa, koda ya ke kanta a kasa ya
ke bai sani ba ko ta amsa a cikin lullubin nata.
Ya jinjina kai, yana cije lebe ya ce.
"Da kyau"
Ya zauna yana duba record din sunayen
da a ka ba shi, sannan ya ce.
dinka"
"Ina Usman Hassan?"
Matashin ya mike tsaye ya ce.
"Ga ni nan yallabai",
Ya ce, "Yauwa, zo ka karbi handout
Ya mika masa.
"Ina Fadima Malam Abdullahi?"
Ya fada yana mai zare idanu ya ga ta
taso, tsam ya ga ta taso din kuwa cikin
takunta na tafiyar hawainiya ta iso gabanshi ta
rusuna yayin karbar, hakan ya kara burge shi,
NAJNOOR 100
SADAUKARWA-1
duk da kokarin da ya ke na kwabar zuciyarshi
da ta ke son kissima masa burgewar matar a
gare shi hakan ya ci tura, shi kam aiki ya
same shi, don bai san irin yadda zai kwatanta
shigar burgun da ta yi wa zuciyarsa.
Kafin ya sakar mata, sai da ya yi jim
kamar ba zai ba ta ba, har ta dan dago kai
idanunsu suka hadu. Tsau! Ya ji wani abu ya
ratsa bargo da kashinsa, lokaci daya kuma ya
ji gabansa ya yanke ya fadi, don haka ba shiri
ya sakar mata, ta juya ta koma inda ta ke
zaune, shi kuma ya zauna yana nazarin
takardun dake gabansa.
Daga karshe ya tattara yanasa-yanasa
ya yi musu sallama ya fice.
Yana zaune a ofis dinsa hankalinsa
gaba daya ya rabu da jikinsa. Fadima ta tsaye
masa a rai, abin da ke kular da shi yadda ya
kasa sarrafa żuciyarsa ta daina siffanta masa
taswirrar matar da ya ke tunanin matar aure
ce. Sai ma azalzala shi da ta ke yi, wai ya
samu matar aure!
NAJNOOR 101
SADAUKARWA-1
Da tunani ya yi masa yawa, sai ya
dauki makullin motarsa ya bar kamfanin gaba
daya, bisa matakin da ya ke son daukarwa
kansa tunda zuciyarsa ta ki amince masa
daina tunanin Fadima, gwara ya bar kamfanin
wata kila zai kubuta daga fadawa tarkon
halaka.
*** ***
Tafe suke cikin mota Hafiz da Alhaji
Atiku zasu je gidan Alhaji Mande akan
maganar takardun gidan da Alhaji Atikun ya
siya a wajensa.
Hafiz ke tukin motar, shi kuma mahaifin
nasa yana zaune a daya 6angaren, babu mai
magana a cikinsu, kusan kowa da tunanin da ya
ke. A gare shi (Alhaji Atiku) har yanzu yana
tausayin halin da dan nasa ya ke ciki na rashin
Rufa'atu, a ganinsa wannan shi ne dalilin da ya
sa har yau Hafiz ya ke cikin rashin walwala ba
kamar can baya ba.
Yayin da shi kuma Hafiz zuciyarsa ta ki
nutsuwa da tunanin Fadima, tun ranar da ya ba
NAJNOOR 102
SADAUKARWAta handout ya ke kokarin gocewa ko da
kallonta; bare kuma kintatar lokacin da mijin
nata zai kawota kamfanin, amma hakan ya
faskara, ta ki fice masa.
Dalilin haka ya shiga damuwa ainu, ko
baccin kirki ba ya yi, da ya ga hakan na neman
zame masa babbar matsala sai ya tsiri duk dare
zai yi alwala ya yi nafila, bayan ya sallame sai
ya kama karatun alkur'ani don gusar da shaidan
daga makotaka da zuciyarsa.
To yana samun sukunin yin bacci idan ya
yi haka, da zarar gari ya waye ya je kamfanin
ne ta dinga zuwar masa a cikin tunaninsa, da
fatan ganinta a zahiri.
Tunaninta yana matukar tasiri a gare shi,
duk da haka ya kan takura kansa ko da
zuciyarsa na azalzalarsa ya fito daga ofis din
don ganin isowarta cikin kamfanin yakan ki bin
umarnin. Haka dole ya samu Yusha'u ya karbе
shi daga darasin da ya ke daukarsu, har zuwa
practical da suke yi ya daina don dai ya daina
ganinta har Allah Ya sa ta kammala ta bar
kamfanin.
NAJNOOR 103
au
ay
an
ail
at
SADAUKARWA-1
Yau da safe da tsautsayi ya sa suka hadu,
yana shigowa kamfanin su 'ma suna shigowa,
don haka kafin ya gama tsayar da motarsa inda
ya dace tuni ta iso gareshi tana jiran ya bude
kofar ya fito.
Da farko ya yi nufin shareta, to amma
tunawa da ya yi matsayin mace da darajarta har
ta iso don ta gaishe shi bai dace ya watsa mata
kasa a ido ba, wannan ya sa ya bude kofar ya
zuro kafafunsa waje ba tare da ya fito ba. Ta
gaishe shi a mutumce, sannan ta wuce gaba.
To tun bayan tafiyarta sai ta fama mishi
tabon mikin kaunarta da ke nukurkusar
zuciyarsa, ya yarda haduwarsa da ita wata
jarabawa ce da Ubangiji Ya ke nufinsa da ita,
bayan ya tsallake siradin Rufa'atu' na yin
biyayya ga mahaifinsa yanzu kuma ya fada
tarkon halaka?
Haka ya baro kamfanin cike da damuwa,
yinin ma dai duk a damuwa ya yi shi, har
lokacin da Alhaji Atiku ya kira shi a waya
cewar ya zo su je gidan Alhaji Manden, har
NAJNOOR 104
SADAUKARWA-1
kawo yanzu da suke tafiyar hankalinsa bai
kwanta ba.
Alhaji Atiku ya juyo da dubansa kadan
ya kalle shi, ya girgiza kai, tukunna ya ce.
"Jiya Kawunka Isma'il ya ke ba ni wata
shawara, wai me zai hana a hada aurenka da
'yar wajensa Nusaiba?"
Da sauri Hafiz ya dago kai, don maganar
ta daki zuciyarsa, ina shi ina Nusaiba? Cike da
tsananin mamaki ya ce.
"Nusaiba kuma Abba?"
Alhaji Atiku ya yi murmushi, ya cе.
"Ni ma abin da na gani ke nan, ana
gudun gara a fada gidan zago, don dai ban san
kai naka ra'ayin ba ne, kar na zartar da
hukuncin da zan dawo ina da na sani, na so
matuka na nuna masa rashin amincewata a
lokacin, amma na bari na ji ra'ayinka”
Girgiza kai Hafiz ya yi, ya ce.
"A'a Abba, ni kam bana son auren
Nusaiba, saboda ina da labarinta tsab ba ta da
nutsuwa, shi yasa ko gidan na je ba na kulata
duk da yawan shisshige min da ta ke yi".
NAJNOOR 105
SADAUKARWA-1
Alhaji Atiku ya tsura masa ido, cike da
dai tausayin ya ce.
"To shi ke nan haka za ka zauna babu
lokaci?"
Hafiz ya ce, "A'a, lokaci kam ai zai zo
ko Abba?"
Ya ce, "To Allah ya kawo mana shi,
amma na kosa matuka na ga ka yi aure Hafiz,
domin aurenka yana daga cikin burace-buracen
da na ke wa kaina tanadi".
Shiru bai tanka ba, yayin da Alhaji
Atikun ya ci gaba da cewa.
"Duk da cewa ba a gaggawa ga lamarin
aure, amma don Allah ka sanya wa ranka za ka yi aure a wannan shekarar, kar don wannan
matsalar da ta faru ka će ba za ka yi aure ba..."
Da sauri Hafiz ya katse shi.
"Ina! Wallahi ko daya Abba ban taba
sanyawa raina wannan abin da ya faru a takurar
da za ta sanya ni kin sunnar ma'aiki ba, ai Kaddara ce tunda na san na dace da mahaifin
kwarai bana shakku akan duk wani hukuncinka.
Duk abin da ka zartar a gare ni dai-dai ne,
NAJNOOR 106
SADAUKARWA-I
fatana kullum Allah Ya Kara raunanar min da
zuciya na yi biyayya a gare ka, kar shaidan ya
samu nasara a gare ni ko yaya ta ke kuwa".
ce.
Ya ji dadin wannan furuci na Hafiz, ya
"Yauwa dana, haka na ke so, Allah Yai
maka zabi na alkhairi, ni ma ina nan ina addu'a
Allah ya ba ni wata macen mafi alkhairi a gare
ni, don na kasa tauye zuciyata ga lamarin aure".
Hafiz ya sake waigowa ya dube shi,
amma sai bai tanka ba, akalla don ya ce yana
son ya sake wani auren ba aibu ba ne idan a ka
yi la'akarin da halin da ya ke ciki, to amma shi
ke nan haka za a kare, da wannan ta fita sai
wannan ta shigo?
Dai-dai lokacin suka isa kofar gidan
Alhaji Mande, Hafiz ya tsayar da motar a inda
ya dace, sannan suka fito su duka biyun daga
cikin motar. Alhaji Atiku ya ciro wayarsa ya
kira Alhaji Mande ya sanar da shi sun iso.
Babu 6ata lokaci Alhaji Mande ya fito
yana murmushi ya tare su, suka gaisa, sannan
ya ce.
NAJNOOR 107
SADAUKARWA-1
"Bismilla, mu shiga daga ciki mana"
Alhaji Atiku ya ce, "A'a ba sai mun
shiga ba, mu tsaya a nan ma ya isa
Alhaji Mande ya ce.
"Haba dai, sai ka ce gidan bakonka ne?"
Alhaji Atiku ya yi dariya ya ce.
"Ko ba bakona ba ne, ka san ni mai laifi
ne, na kwana biyu ban zo na duba Anboy ba,
don haka idan muka shiga ya ganni rigima се
kawai zai saka min".
Alhaji Mande shi ma ya yi dariyar, ya ce.
"Kamar kuwa ka sani, jiya-jiyan nan ya
ke min rigimar wai sai na kai shi gidanka..."
Hafiz ya dubi mahaifin nasa ya ce.
"Abba, bari na duba wani abokina nan
kafin ku gama, ai babu wata matsala ko?"
Alhaji Atiku ya juyo yana dubansa.
"Nan din ma kana da abokai ke nan?"
Murmushi kawai Hafiz ya yi ba tare da
ya tanka ba. Alhaji Atiku ya ce.
"Babu matsala, sai ka hanzarta, don ba
daďewa za mu yi ba".
NAJNOOR 108
وو
ne.
SADAUKARWA-1
Ya ce, "To, da ya ke ma ba nisa nan baya
Ya tafi, su kuma suka shiga cikin motar
suka soma tattauna abin da ya hada su. Suna
cikin tattaunawar ne kamar an ce daga idonka,
Alhaji Atiku ya hango wata matashiya tana
tafiya sanye da koriyar atamfa, ta saka hijabi da
ya wuce gwiwarta. Kallo daya ya yi wa
matashiyar zuciyarsa ta buga, har hakan ya yi
sanadin yin shirunsa daga maganar da ya ke.
Alhaji Mande ya bi shi da kallon
mamaki, bai tanka masa ba har sai da
matashiyar ta face wa ganinsu, sannan ya tabo
shi yana fadi.
cе.
"Ya ya dai Alhaji?"
Alhaji Atiku ya sauke ajiyar zuciya, ya
"Wannan yarinyar ce ta burge ni, daga
ganinta 'yar gidan manyan mutane се".
Alhaji Mande ya yi dariya.ya ce.
"Ka ji ka da wani shirme sai ka ce
karamin yaro, shin daga ganin sarkin fawa sai
miya ta yi zaki? Ka sani ko matar aure ce?"
NAJNOOR 109
1
d
SADAUKARWA-I
syed nAlhaji Atikuyugigiza kar ya seY "Na san ma ba matar auren ba се
Tsloru Alhaji Mandeya Gwl ve ) Y
ВП? Ме yasa ka ce hakauee smor ekua
snobAlhaji Atiku ya cck Gu ettst nidio
snsi Jikina ne ya bani ka san matar aurel ko
da ganinta za ka iya ganewanol sb ovnse svitst
AlhajiMande ya yi dariyajsosai ya.ce.s
"Wannan hasashenka ke nan, amma idan
yarinya ta samu tarbiyya daga gidan kwarai ba
lallai ne ka lantance matar aure ce ko akasin
haka ba sd szsm skus) isd ikamsm
odsiAlhaji Atiku ya ce/ 988 :61 evidastem
"Duk da haka, yanayin da naji a jikina
ya ba ni ba ta da aureiisdlA isb aY G
Alhaji Mandayacey ulA isdlA
"Wato maganar dai da ake fada za ta
Labbata Tip atac syni
Cikin yanayin tuhuma Alhaji Atiku ya cсe
da shi. 00 εν σxiτch iv sy əbasM jediA
ייף 9Wace magana ke nад? i К"
in ewlhalMnde Ya sauya fuskaimdagä
yanayin dariya daraya ya cod inse o SIREN İN BI BYim
SADAUKARWA-1
"Da ake cewa kai namijin zara ne, da ka
ga mace ba ka da kwanciyar hankali sai ka kaita
gidanka. Da kuma ta shiga ba ta cika shekara za
ka saketa ka rido wata".
Iya Bacin rai Alhaji Atiku ya shiga.
fuskarsa a tamke ya ce.
"Amma ka ba ni mamaki Alhaji Mande
da ka yi min wannan fassarar".
Alhaji Mande da ya lura ransa ya бaci,
sai ya ji bai ji dadin fitowar furucin ba, ya
karyar da kai cikin yanayi na rarrashi ya ce.
"Ba ni na yi maka wannan fassarar ba,
mutane ne ke fada, kuma da na tsaya na bi
kanun abin, sai na ga kamar suna da gaskiya
Shiru na tsayin mintoci ya gilma a
tsakaninsu, kafin daga bisani Alhaji Atiku ya
magantu da cewa.
"Wata kila maganar ne ba ta taba hada
mu da kai ba, amma wallahi ka ji na rantse
maka duk lokacin da zan yi aure ba ni da
kwanciyar hankali, saboda gudun irin
wadannan maganganun da ake fada a kaina, to
abu ne babu yadda ka iya, idan Allah Ya rubuto
NAJNOOR 111
SADAUKARWA-1
sai ka auri mace ka sake ta ko ba laifin komai
sai hakan ta faru, bare kuma ni da dalilai
mabanbanta ke sa wa na saki mata. Ban taba
auren wata mace da niyyar wani lokaci na sake
ta ba, illa idan na aureta sai mutuwa ka raba,
amma da ya ke haka Allah Ya kaddara min
babu yadda zan yi, su kuma mutane 'yan
ba'ni'na'iya da babu ruwansu da rayuwarka su
bi su tsangwame ni. Shin me ye laifina a kai?"
Alhaji Mande ya ce.
"Ko ba ka da laifi dole a dora maka laifi,
domin kowa ya sani mata hakuri ake da su,
bare kai. da ka ga jiya ka ga yau, izuwa yanzu
ya dace a ce ka tsaya ka nutsu ka fuskanci
alkibla daya. Idan har an ce ba don ka so ka ke
sakin auren matanka ba, da wace hujja mutane
za su yarda da hakan? Kar fa ka manta ba a kan
mace daya ko biyu hakan ta faru ba, sai a се
koda yaushe laifin matan ne?"
Alhaji Atiku ya ce.
"Ba za ka gane ba ne, kaddara ba yadda
ba ta zuwar wa Bawa, duk kuma wayo ko
hikimarsa bai isa ya tsallake mata ba, facele
NAJNOÓR 112
SADAUKARWA-1
Allah Ya iyakance masa. Wannan auren na
Hamdiyya da na yi, shi ne na sawa raina ba zan
kuma wani, auren ba ko don.na gujewa
wadannan Kananan maganganun, ba don Allah
Ya haramta min ba, to amma kullum zuciyata
tana muradin na auri mace wadda zan ji dadin
aurenta,
Yau sama da shekaru ashirin da takwas
ke nan, tun bayan rasuwar marigayiya Halima,
har kawo yanzu bani da kwanciyar hankali akan
rayuwar aurena, shin don me ba zai so samun
kwançiyar hankali ga rayuwar aurena ba kamar
yadda kowane namiji ya ke samu?
Wannan shi ne