Rufratti ba ta dace da
kaibäsaboda máhaifinta ba matumin kirki ba
ne. muddin ka atri 'yarsa sai ka yi nadanma.
Don haka a matsayina na mahaitinka ha
ké neman alfarma ka yi hakuri da yarinyar nan
kanemi 'yar gidan mutunci. Ka "var gidan dan
Ta'adda ba, don ka dace da auren voasali mai
nagarta".
Wani irin zazzafan gumi tsattsah
wa Hafiz. va ji tamkar zuciyarsa za ta buда йс
don tsinanin prdani da tashin hankati
Wanhan lamari va fi kanma da mafarki. a
ce wai ya rabii da Rufa átu duk da cewa ba yu
jayayya Ko kadan datmäbaifinsa kuma ya san
dak hukuncin dalya y
L: E:
domin har kallüm yaha alfatari da mahaitinsa
'mutum-ne mai FIUKUNCI DA GASKIYA. ba
ya yanke BAHAGON HUKUNCT. sa ai bai
san yadda zad kwatanitad lkamarin ba..
NAINOOR
SADAUKARWA-I
ccwa.
Alhaji Atiku ya girgiza kai,ya ci gaba da
"Na sani kan son yarinyar nan, to amma
hakan da za ka yi min yana matsayin
SADAUKARWA a garc ni, muddin ka yi min
hakan zai faranta min rai, na kuma gamsu da
irin biyayyarka a gare ni. Ka daure ka hakura
da ita, aurenku sam bai dace ba ko a musuļunce
shari'a ba ta amince da shi ba"
Murya a matukar kasalce Hafiz ya сe,..
"Ba komai Abba na sani ba za ka tabа
hanani abin da zai zamo alkhairi a gare ni ba.
haka ba na fatao na samu, wata rana wadda za
ka
kuwa son da na ke wa abin ya zarce mizani
matsawar hakan bai shiga hakkin shari'a ba.
Saboda haka ina mai farin cikin zuwan
wannan rana da ka ba ni umani aka rabew
da abin da na ke so. Wallahi na hakura da
Rufa'atu har abada, idan dai har hakanszai
zamo cika umarninka da kuma sanya ka farin
ciki, sai me kuma kake bukata da ni Abba
NAJNOAOR
2
1
Di
53
い
نا
k
SADAUKARWA-1
Tausayi sosai ya kama Aklhaji Atiku, sai
dai hakan shi ne abu mafi dacewa a gare su
gaba daya. Ya ce da shi.
"Yauwa dana, dama na san kai da ne mai
biyayya da yarda da kaddara. Allah Ya shige
maka gaba akan komai naka. Ya yi maka zabi
da mace ta gari wadda za ka yi farin ciki da
ita".
Hafiz ya ce, "Amin".
Suka dan yi shiru na wani lokaci, can
Alhaji Atiku ya ce.
"Ka ci gaba da addu'a da maida
lamarinka ga Ubangiji bayan haka ka nutsu
sosai wajen duban macen da za ka aura, saboda
wannan lokacin matsalar da ta fi yawa ke nan,
namiji ya ga mace rumi-rumi kamar mutuniyar
kirki, sai ya aure ta ya ci karo da tarin
matsaloli, ko da dai ba ga matan kadai matsalar
ta tsaya ba, har mazan ma akwai bara-gurbi a
cikinsu, Allah dai Ya zaba wa kowa abokin
rayuwa na gari".
Shiru dai Hafiz ya yi, zafi da radadi kawai ke dawainiya da zuciyarsa, ya kasa cewa
NAJNOOR 59
SADAUKARWA-1
komai har sai da mahaifin nasa ya gama
maganganunsa ya ba shi izinin ya tashi.
Ranar sam bai samu nutsuwa ba,
damuwa ta yi masa yawa, ga ta umarnin da a ka
ba shi ga kuma wayar Rufa'atu da har lokacin
ya kasa samu. Ya tabbatar zuwa yanzu tana
cikin irin halin da ya ke ciki, wata kila hakan ne
sanadin da ya sa ta kashe wayarta.
Allah Sarki, so kayan wahala! So
mabudin tashin hankali, so tarkon rashin
nutsuwa da sukuni. Duk wanda ya dace da
takobin so na gari ya more.
Rufa'atu ta zamo mai SADAUKARWA
a gare shi, domin ba karamin kokari ta yi wajen
mallaka masa sonta duk da cewa kafin, shi
akwai wanda ya riga shi kafa harsashin a
zuciyarta, sài dai yadda ta nuna masa kulawa ya
sa ya gane ba karamin kokari ta yi ba na sama
masa muhalli a zuciyarta.
Ya yarda ya kuma amince rabuwarsu na
tattare da kaddararsu da ba su taba tsammanin
fitowarta ta wannan siga ba.
NAJNOOR 60
SADAUKARWA-1
Karfe sha biyu na dare, amma bacfci ya
ki zuwar masa. Shekaran jiya a dai-dai wannan
lokacin ya kasa bacci ne cike da dokin gari ya
waye aje katsina nemar masa auren Rufa'atu.
Jiya ya kasa bacci saboda ya kosa gari ya waye
ya ji sakamakon zuwa Katsinan.
Yau ga shi ya kasa bacci saboda alhini da
jimamin rabuwa da Rufa'atu sanyin idaniyarsa.
Ba wai yana son musanta tabbatuwar umarnin
da mahaifinsa ya ba shi na rabuwa da Rufa'atu
ba, damuwarsa daya ta sigar da zai cireta a
cikin zuciyarsa har ya saka wata wadda za ta
maye gurbinta.
Wannan ya fi komai damunsa da daga
masa hankali ainun.
Dareń wannan rana ma bai samu bacci ba
sai bayan sallar asuba.
Misalin karfe sha daya da rabi na safe
yana cikin ofis dinsa ya dora kansa a saman
tebur, shi kansa bai san tunanin da zai canko ya
ce shi ne mafi rinjaye daga cikin tunanukansa
ba.
NAJNOOR 61
SADAUKARWA-1
Wayarsa ta yi kara, ya duba fuskar wayar
ya ga bakuwar lamba ce, ya ja gajeran tsaki
yana mai kallon wayar har kiran ya katse wani
ya sake shigowa.
Ya ki dagawa har sai da ya ga an nacewa
kiran, sannan cike da kosawa da kuma takaicin
yadda a ka dame shi da kiran, ya sa hannu ya
dau wayar ya latsa ok tare da karawa a kunne.
Cikin yanayi na tashin hankali da matsanancin
firgici ta ke magana.
"Hafiz wai don Allah me ya ke faruwa,
tun shekaran jiya na kasa samun nutsuwa, ko ka
fasa aurena ne?"
Zuciyarsa ta kare ainun da jin muryar
Rufa'atu a raunane, shi ma a raunanen da kuma
nuna nasa tashin hankalin ya zarce nata, ya ce.
"Ina wayarki ne kika kirani da wata
lambar?"
Ta ce, "Daddy ya karbe ta, hakan ma ya
kara min tashin hankali... Don Allah kada ka
boye min komai, kai ka ce ka fasa aurena ko
kuwa Daddy ne ya ce ba za ka aure ni ba?"
NAJNOOR 62
SADAUKARWA-/
Yacc. "Maganar ba ta waya ba ce. ki
bari zan shigo Katsinan sai mu tattauna
Ta C"Ni kam na ga ta kaina! Daga jin
abin da ka fada na gane akwai babbar matsala...
Idan dai daga gare ka matsalar ta ke, ka zaluncс
ni! Ka yaudare ni! Da ka raba ni da son
kowannc da namiji bayan ka san ba aurena za
ka yi ba!"
Ta karashe maganar lokacin da kuka ya
ci karfinta.
Ya cc, "Kada ki min wannan mummunan
zaton. Sanin kanki ne KE CE MURADINAА.
ban taba soyayya ba sai a kanki bare na iya
Та сс. "Кa daina ba ni hakuri, domin na
san an min babbar ilfar da tábonta ba ya
goguwa.
På tare da td jita Cewarsd Ba ta kášhe
wayar. Ya kira har kusan sau uku, sai a na
cikon hudun ne ta dauka, shi ma kukan ta ke
kashirban. Abin da ya sake dagula masa
lissafi ke nan, dama abin da ya ke gudu shigar
NAJNOOR 63
C
기
k
E
SADAUKARWA-1
Rufa'atu cikin damuwa, ga shi kuma ta shiga
din. Muryarsa a sanyayс ya сс.
"Don Allah ki nutsu ki saurare ni. sanin
kanki ne babu bawan daya isa ya gujewa
kaddara, ki, fauki duk abin da ya faru a
matsayin kaddara... Kuma fa har yanzu akwai
sauran dama a gare mu... Ki dai yi hakuri na
zo din"
CC.
Ta sassauta kukanta, ta cc.
"Shi ke nan, yaushe za ka zo?"
Ya dan yı jim na wani lokci. tukunna ya
"GGobe ko jibi insha Allah
Тa сс. To Allan Ya kawo ka laliya
Ya cc. "Amin
Bayan ya kashe wayar. jigum ya sake yi
vana nazarin maganganun da suka tattauna da
mahaifinsa. da kuma hanyar da zai billowa
Rufa'atu ta aminta cecar kaddara ce dukkan
abin da ya gudana a tsakaninsu.
NAJNOOR 64
SADAUKARWA-1
Yana cikin wannan hali na damuwa
Fahad mai kula da sabbin dalibai ya shigo.
Bayan sun gaisa, Fahad ya ce.
"Yallabai jiya wani mutum ya zo ya
sayawa wata forn, wai sun zabi zuwa da safe.
Ya cike form din har ya maido gobe za ta fara
zuwa.
Hafiz ya ce, "To ba matsala, amma
gobe zan yi tafiya, Badaru ne zai wakilce ni
ya gabatar musu da darasin".
Fahad ya ce, "Shi ke nan Yallabai, na
kai form din hannun Joseph ko da za ka
bukata; duk an saka hannu saura naka"
Ya ce, "Sai na dawo na duba"
NAJNOOR 65
KATSINA
SADAUKARWA-1
ashegari, misalin Karfe daya Wna rana Hafiz ya iso birnin
Katsina. Kai tsaye otel ya nufa
ya kama daki kamar yadda ya saba a duk
zuwan da zai yi idan har zai kwana a garin
tunda ba shi da wanda ya sani.
Bayan ya kama dakin, ya huta ya nemi
lambar Rufa'atu bai samu ba, sai ya gwada ta
Zubaida, ya ci sa'a wayar tata a kunne ta ke.
Suka gaisa tukunna ya tambaye ta.
"Ina mutumiyar?"
Zubaida ta ce da shi.
"Tana gidansu ba ta da lafiya, tun jiya
zazzabi mai zafi ya rufe ta, amma dazun na
shiga dubata da sauki sosai".
Ya ce, "Eyya, Allah Ya ba ta lafiya".
Ta ce, "Amin".
Ya ce, "Ko za ki taimaka ki sanar mata
na iso?"
a
e
Та се, "Ва komai, bari na je"
NAJNOOR 99
SADAUKARWA-1
Ya kashe wayar. Jim kadan ta kira shi,
amma bai dauka ba, ya bi kiran nata. Muryar
Rufa'atu ya ji.
"Da fatan ka iso lafiya?" cewarta.
Ya ce, "Alhamdu lillahi, ya kufan jikin?"
Tа сe, "Da sauki".
Ya ce, "To, Allah ya kara lafiya
Ta ce, "Amin".
Ya ce, "Yanzu zan zo ya ke nan?"
Та се, "Sai dai mu hadu gidan su
Zubaida".
Bai tambaye ta dalili ba, domin ya san
zuwa lokacin mahaifanta sun shaka da yawa,
komai ma yana iya faruwa. Ya ce.
"To sai na iso".
Yana gama wayar, ya shirya tsaf ya nufi
unguwar tasu. A kofar gidan su Zubaida ya
tsayar da motar, sannan ya kira wayar Zubaida
ya sanar musu ya iso.
Jim kadan suka fito ita da Zubaidan.
Kallo daya ya yi wa fuskar Rufa'atu ta ba shi
matsanancin tausayi, domin duk yadda ya ke
ganin ya rame ta fi shi rama. Lallai ba abin da
NAJNOOR 67
SADAUKARWA-/
ya fi rabuwa da masoyi zafi a lokacin da ake
muradin kasancewa da juna, ga dai su yadda
lamarin ya zo musu, suna so da kaunar juna
kamar sa hadiye kansu don so, amma wani
dalili zai raba su.
Cikin sanyin murya Rufa'atu ta gaishe
shi. Zubaida ta dube su, sai ta ji sun burge ta,
yadda yanayin kowannensu ya sauya. Hakikа
sun kasance masoyan juna na hakika. Daga
shekaran jiya da ta ji abin da ke faruwa, zuwa
yau ta jinjina lamarin matuka, musamman ta fi
tausayin kawarta da ta yi zurfi sosai akan son
Hafiz, duk da bangare daya ba ta ga laifin
Rufa'atun ba don ta nacewa zuciyarta son
Hafiz, domin ya kai matsayin da ko wacce
mace za ta zo shi. Zubaida ta ce.
"To, ni bari na koma ciki sai ku yi sauri,
kin dai san abin da Ummi ta ce kafin ki samu ki
fito daga gida".
Rufa atu ta yi murmushin yake ba tare da
ta ce komai ba. Zubaida ta shige cikin gidansu.
NAJNOOR68
SADAUKARWA-1
Haiz ya sauke gwauron numfashi,
idanunsa akan fuskar Rufa'atu da ta sunkuyar
da nata kan kasa cike da fargaba. Ya ce.
"Dago kai ki dube ni mana, magana na
ke so mu yi da ke ta fahimtar juna”.
Ba ta bi umarninsa ba abin da ba ta taба
yi ba ke nan tsawon lokacin da suka kwashe
suna mu'amala. Ya ci gaba da cewa.
"Ban taba tunanin akwai ranar da bacin
rai zai yi tasiri ya shafi mu'amalolin rayuwarki
ta yau da kullum, wato ladabi da biyayya da
kika saba yi min su gaza samuwa... Shin yau
kina nufin za ki ki bin umarnina ne?"
Shiru ta yi, kuma ta ki dago kan ta dube
shi. Ya gyara tsayuwarshi tare da soka
hannayensa cikin aljihun rigarsa, ya ce.
"Shi ke nan, na gode... Amma na san kin
san matsayin mahaifa akan 'ya'yansu? Kin sani
cewa bijirewa umarnin mahaifa ba tare da ya
kaucewa shari'a ba baya haifar da da mai ido
tunda kina da ilimin islama? Idan har da yana
so ya gama da duniya lafiya, to ya yi biyayya
ga mahaifnsa, sai ya samu kyakkyawan karshe.
NAJNOOR 69
SADAUKARWA-I
Allah Ya sani ina tsoron bijirewa duk
wani abu da mahaifana suka umarce ni
matsawar bai sabawa mahaliccina ba, ba ni da
azancin da zan kare kaina ranar da na koma ga
mahaliccina bisa tubalin kin biyayya ga
mahaifana, saboda haka a wannan karon ma ina
so na yi biyayya".
Da sauri ta dago idanunta ta dube shi
cike da tsananin mamaki, ta ce.
"Dama matsalar daga gare-ka ne?"
Ya daga mata gira, sai ta mayar da kai ta
rusunar.
"Mahaifina ne ya ce ba zan aure ki ba"
A karo na biyu ta sake dago kai, suka
kalli juna sosai, sannan ya ci gaba da cewa.
"Ina sonki Rufa'atu, amma babu yadda
za mu yi tunda haka mahaifina ya tsara cewar
ba zan aure ki ba, dole mu yi hakuri da juna. Ba
zan boye miki ba duk abin da na ke so muddin
mahaifina ya nuna ba ya so, lallai kuwa na
hakura da shi komai tsananin son da na ke wa
abin... Ki yi hakuri ki kuma fahimce ni ba ni da
nufin yaudara a gare ki, ke ma kin san haka".
NAJNOOR 70
SADAUKARWA-1
Kwalla suka kawo mata, ta kasa cewa da
shi komai. Shi ma sai ya ji tamkar wutarsa ta
dauke, suka yi shiru su na tsayin wani lokci,
kowanne da abin da ya ke kissimawa a
zuciyarsa, zuwa can ta rausayar da kai cike da
nuna takaici da alhininta ta ce.
"Na gode wa Allah da hakan ta faru, ba
wai ina farin ciki ko murna ba ne na rasa ka, sai
dai ina farin ciki ne da Allah Ya hada ni da
masoyi managarci wanda ya san hakkin
iyayensa akansa. Idan da abin da zan iya kiran
wannan rana, to ba za ta wuce RANAR BAKIN
CIKI ba, domin ina ji a jikina wannan ita сe
ranar da na yi bankwana da farin ciki har
karshen rayuwata..."
Ya katse ta da sauri da cewa.
"Ki daina fadar haka, domin bawa bai
san abin da gobe za ta haifar ba... Kuma wani
rashin alkhairi ne, duk da cewa ni ma na san na
yi babban rashi amma sai mu taru.mu maida
komai ga mahaliccin mu, ya fi mu sanin abin da
ya 6oye game da faruwar wannan lamari".
Та се, "То".
NAJNOOR 71
SADAUKARWA-1
Ya ce, "Ranar da su Abba suka zo, ba a
sanar da ke komai ba?"
Ta girgiza kai, tana fadin:
"Ai lokacin ba ni gida, sai yamma lis na
shigo gidan, na tarar da Daddy a falo ransa a
bace, ko gaisuwata bai amsa ba, na nufi
hanyar dakina ya kirani, ya ce min na ba shi
wayata. Ina ba shi bai kuma saurarata ba, ya
mike ya bar falon, iya tambaya na yi wa
Ummi amma ba tà ba ni amsar abin da ya ke
faruwa ba, sai dai ita 'ma na fuskanci tana
cikin matsananciyar damuwa.
Sai a washegari ne wato shekaran jiya
ya ke ce min ba yanzu zai min aure ba, na
dauka matsalar daga gare shi ne, sai kuma
1A0
Ummi ta ke sanar min wai mahaifanka
Rananan mutane ne, hakan ya ruda ni na kasa
gano wa ke da gaskiya, ga shi ya amshe min
waya".
Ta yi shiru daga maganar da ta ke yi.
Hafiz ya ce, "Kaddara ce kawai ta faru,
don ni ma ban taba tsammanin zan samu
NAJNOOR 72
SADAUKARWA-I
wannan matsalar daga Abba ba, amma sai mu
yi fatan hakan ya zama alkhairi a gare mu...
Cikin raunanniyar murya ta се.
"Ina fargabar halin da zan shiga,
wallahi ban iya karya ko munafunci ba, duk
duniya babu namijin da na ji zuciyata na so da
kauna tamkarka"
Ya ce, "Na sani Rufa'atu, amma dole za
mu yi tawakkali duk kanmu fa musulmai ne,
kuma ke ma kin san a duniya babu macen da
na ke so sama da ke, biyayya ce kawai za mu
daure mu yi, idan da rabo kuma sai ki ga
Allah Ya kai mu wannan rana ta aurenmu.
Ta ce, "Hmm!"
Ya ce, "Kuma ina so ki sanya a ranki,
hana mu aure da a ka yi ba yana nufin ya
yanke mu'amala tsakaninmu ba, wallahi tun
daga yanzu na dauke ki a matsayin kanwata
wadda muka fito ciki daya, ina neman
wannan alfarmar a gare ki, ki dauki
mu'amalarmu a wannan bigire.
Ta girgiza kai, tana fadin.
NAJNOOR 73
SADAUKARWA-1
um isasAibakin alkalamilyaslriga ya Bushe,
yadda na ajiyeka a matsayin abokin rayuwata
bana tunânin akwai sanadin da zai sahya na
sauya maka matsayi a zuciyatatet sl"
lub .sdipnabinuda ota sfada va tabbataflsda
gaskiyarta, shi din ma Karfin hali nedya (yi ya
fadi haka, ba wai don har eikin zuciyarsa
shakan ne ba, ya sani idan a ka ce masoya za
su ihaduaizai wuyanba tb ylswatas halayya
wadda ta shafi soyayyar ba, idan kuwa häka
ne,syasvkamata su Kauracewa ganin juna
muddin suna son biyayya ga abinuda
mahaifansu saka bukataneшек вY рsllA
Ya ce, "Haka ne, to na gode amma ina
fatan idan na zo zakiad sK c.sY
BY MUKERufa atume kikea nan?” ទប្រ
nut idsMaganat Yayar Usmanla katse Hafiz
daga zancen darya ke. Dukkansu suka dube
shi yana tsaye Ryami füskarsh a turbunepya ci
igaba da dewal 0163 6 Ests W
"Wato da Daddy ya ah she wayarki' don
kada ki kira wannan Rarainin mutumih shi ne
ENAJNOOONLA14
SADAUKARWA-1
kuka yi mahada a nan ko? Me kuke nufi?
Wato tunda ba aurenki zai yi ba sai ya biyo ta
wannan hanyar domin ya lalata miki
rayuwa?"
Takaici ya lullube zuciyar Hafiz, tunda
ya ke a rayuwarsa bai taba jin magana mai
munin wannan ba, domin bai taba duban wata
mace da sunan lalata ba bare kuma Rufa'atu
wadda ya ke fatan ta zamo uwar 'ya'yansa,
sai dai ya san a yanayin da ake ciki ko wace
irin magana ce za su iya furtawa a gare shi,
don haka bai iya cewa komai ba illa bin
Usman din da kallo da ya ke. Kanta a rusune
ta ce.
"Ka yi hakuri Yaya Usman, ka yi min
alfarma bankwana muke da shi, kuma ka ga ai
ni ban san dalilin raba mu ba, sai yanzu da ya
zo ya ke sanar min".
Ya ce, "Amma ina ce da safe Abba ya
ce kada ya sake ganinki da shi?"
Hafiz ya dube ta, ashe ma har gargadi a
ka yi mata a kansa, amma ta boye masa?
NAJNOOR 75
SADAUKARWA-1
Та се, "Наka ne, ka dại yi hakuri don
Allah ka rufa min asiri".
Da ya ke mai zafin kai ne ainun. sai ya
nuna mata hanya, ya се.
"Bi nan"
Ta juyo da dubanta ga Hafiz muryarta
na bayyanar da sautin kukan da ya kasá
6oyuwa a cikinta, ta се.
"Hafiz SAI WATA RANA!"
Kasa cewa komai ya yi saboda raunin
da zuciyarsa ta yi, kadan ya rage shi ma
kwallan su zubo masa. Yana kallo Usman ya
tusa keyarta suka 6acewa layin.
Cikin sanyin jiki ya bude murfin motar
ya shiga ya zauna yana tunanin abin yi. A
kalla an kwashi mintina sun fi ashirin, can sai
ga Zubaida ta fito daga cikin gidansu.
Turus ta tsaya da ta hango Hafiz zaunc
a cikin mota shi kadai, gabanta ya shiga
_ faduwa, a haka ta karaso ta ce.
"Ya na ganka kai kadai, ina Rufa'atun
ne?"
NAJNOOR 76
SADAUKARWA-I
Bai boye mata komai ba, yana gama
sanar mata ta girgiza kai, ta cc.
"Lamarin nan yana da ſaure kai, amma
shawarar da zan baku, ku yi hakurí da juna,
ku kuma dage da addu'a da neman zabin
Allah. dama aure ya gaji haka, mawuyaci ne
ka ga an yi aure ba a fuskanci irin wadannan
matsalolin ba, wasu ma sai idan an yi aurcn
ne za ka ga ana ta tashin hankali
Ya ce, "Na gode Zubaida"
Suka vi Sallama ya tayar da motar ya
bar kofar gidan.
Yana, komawa otel (fin ya ji gaba daya
duniyar ta yi masa zafi, zaman garin ba shi da
wani amfani a gare shi, da ya zo da nufin ya
kwana, to amma yanzu ya san ko ya kwana
zai yi wuya ya sake ganin Rufa'atu don haka
ya yanke hukuncin kawai ya koma Bauchi.
NAJNOOR 77
BAUCHI
SADAUKARWA-1
ashin Rufa'atu ba Karamin-lamari R
ne ga Hafiz ba, domin sai, da
hakan ya shali al'amuran
rayuwarsa, walwalarsa ta ragu, hatta da gurin
aikinsa sai da ya yi masa Kaura, don tun da ya
dawo Katsina bai samu fita gurin aiki ba, har
tsayin mako guda.
Duk halin da ya ke ciki, mahaifinsa yana
lura da shi, sai dai babu wani tallafi da zai iya
yi masa, kuma bai tursashi akan ya daina
damuwa ba, don dama yasan hakan za la iya
faruwa. Sai dai ya so matuka ya ga dan nasa
cikin farin ciki, don haka ko da zai je Rasar
Dubai harkokinsa da kuma hado léfén aurensa
da zai kara ya ce da Hafiz ya shirya su'tafi tare.
Hafiz bai so taliyar balsai dai bå yakda
zai yi haka-ya daure ya aminees Cikin dan
lokaci Alhaji Atiku ya gama duk wasu shiry cshiryen da zai yi. Ranar asabar da yamma
jirginsu ya daga zuwa Dubai.
NAJNOOR 78
9
SADAUKARWA-1
Ba laifi Hafiz ya dan sami sukuni,
saboda koda yaushe ba shi da, lokacin
kadaicewa shi kadai, musamman ma Alhaji
Atiku ya kama musu daki daya, don ya kasance
koda yaushe suna tare, hakan ya hana masa
zaman kadaici bare tunani ya dame shi, duk da
dai a bangare daya idan ya runtse idanunsa da
nufin bacci yana hasko fuskar Rufa'atu.
Kwanansu biyar suka gamo duk abin da
zasu yi, hatta da kayayyakin da za a saka a
gidan da ake ginawa Hafiz sai da a ka siyo, duk
da dai shi Hafiz din bai san ana masa wani
sabon ginin ba, sai dai mamaki da ya ishe shi na
kayayyakin da ya ga ana ta jida, wani abin ma
bai ga amfanin sanya shi a gida ba, misali
colour room.
Bayan sallar juma'a suka iso Bauchi, sai
me? Tunanin Rufa'atu ya dawo masa sabo fil!
A satin a ka shiga hidimar auren Alhaji
Atiku, don haka ko da suka dawo din ma bain
samu şararin ofis ba, illa ya leka ya ga yadda
lamura ke gudana. Dabig Rs
NAJNOOR 79
SADAUKARWA-1
An daura aure lafiya, amarya ta tare a
gidan Alhaji Atiku, sai dai matsalar da a ka
soma cin karo da ita, sam amarya ba ta da
fara'a, sannan ga kyama shi yasa ma
washegarin da a ka kawota suka soma samun
matsala da Hajiya Asiya da ya ke ranar Hajiya
Asiya ta yi girki, ai kuwa Hamdiyya na fitowa
ta ga yadda ake gwamutsa kwanuka ta ce ina ba
da ita wannan kwamacalar ba.
Shi ke nan rigima ta tashi, Hamdiyya ta
ce, dama tana sane da labarin bakar kazantar da
Hajiya Asiya ta ke da ita, don haka ita ba ta
lamunta ba.
Hajiya Asiya na jin haka ta tada rigima
wai Alhaji Atiku ya gama tozartata a idon
amarya, ya rasa yadda zai shawo kan al'amarin,
ga dangin amarya sun zo, amma Hajiya Asiya
sai balbalin bala'i ta ke. Da abin ya sha masa
kai, sai ya ce ta shirya su je dubiya tunda dama
an kwantar da mahaifinta asibiti.
Da kyar dai ya samu ta shirya suka fice
daga gidan, a cikin mota ya ke mata bayanin shi
sam bai taba fadawa mace halin matarsa ta gida
NAJNOOR 80
SADAUKARWA-1
ba, halinta ne dai kowa ya sani, don haka sai ta
gyara.
Yau tunda sanyin safiya Hafiz ya ji babu
abin da ya ke muradi irin ya tafi ofis, ko dan ya
kwana biyu bai yi aiki ba ne.
Karfe tara na safe a ofis dinsa ta yi masa,
yana zaune yana ta dudduba takardu kafin
lokacin da zai shiga ba wa dalibansa darasi.
Lokacin na yi kuwa ya nufi ajin, yana
gabatar musu da darasin akan Hardwear,
hankalinsa ya kai ga wata daliba mai kokari na
ban mamaki, domin duk tambayar da ya yi
kafin wani ya bada amsa ta bayar.
Sanye ta ke da zumbuleliyar hijabi, ta
yane fuskarta da nikab, ya jinjina wa kwalwarta
irin bayanan da ta ke bayarwa sun yi shige da
na wadda ta ke da digiri a fannin na'ura mai
kwalwa. Har ya karashe yi musu darasin yana
cike da mamakin yarinyar.
Bayan ya gama musu darasin yana tsaye
jikin motarsa bayan ya dauko wasu takardu
daga cikin motar a ka kirashi a waya, don haka
NAJNOOR 81
S
f
И
Π
A
ta
da
SADAUKARWA
ya jingina da bayan motar yana amsa wayar,
abokinsa ne Larab.
Sun gaisa tukunna Larab din ya cе.
"Haba mutumina shi ke nan sai a ji ka
dif, ba ka ba labarinka?"
Hafiz ya yi dariya ya се.
"Amma dai ka an yi an iska, wato da ka
ji ni dif me ya hana ka kai ka tuntube ni?"
Larab ya ce, "Hmm dama haka za ka ce...
Muna fa asibiti"
Cikin yanayin damuwa Hafiz ya ce,
"Wa ke ba shi da lafiya?"
Larab ya ce. "Ya wuce sarauniyar ciwon
ce
Ha
laı gidanmu?""
wa "Ban gane ba, har sarauniyar ciwo gare
ku?" Inji Hafiz.
am
ga
sai
kai
an]
dag
sam
"Eh mana, ka san Bintu ta mayar da
asibiti dakin kwanciyarta, kafin ka ji wani dan
gidanmu ya kwanta asibiti sau daya ka ji Bintu
ta kwanta sau uku ko sau hudu
Hafiz ya ce, "Subhanallah, wai me ya ke
damunta ne? Idan babu sauki a fita da ita waje
NAJNOOR82
SADAUKARWA-1
mana, amma a bar yarinya da ciwo sai kuma ku
dameta da korafin ta cika rashin lafiya?"
Larab ya ja tsaki, tukunna ya ce.
"Hmm! Ka rabu da yarinyar nan daukar
buhun hatsi gare ta bayan ba ta da mai cinsa!"
Hafiz ya ce, "Wallahi ka kasancemai
adalci, babu fa mutumin da zai so a ce yana
kwanciya asibiti sai dole”.
Larab ya ce, "Ai duk abin da ya same ta
ita ta ja wa kanta....
Hafiz ya katse shi da cewa.
"Ban san yaushe ka koma haka ba, dama
mutum na sanya wa kansa ciwo?"
Ya ce, "Eh mana... Ka san wai meoke
damunta?"
"Sai ka fada". แฟ
kanta"
"Hmm wai ciwon zuciya ne!
A rikice Hafiz ya ce.
"Ciwon zuciya fa ka ce?"
"Eh mana, ka ga kuwa ita ta jawa
"Yanzu kuna wane asibiti ne?"
NAJNOOR 83
12052
SADAUKARWA
Ya ce. "Muna nan El-Noor Clinic, amma
yanzu zan je gida, a nan na ke wuni Umma la
kwana da ita".
Hafiz ya cc, "Shi ke nan, idan ka dawо
anjima sai mu je na dubata, dan Allah ka yi
mata sannu da jiki kafin na zo, ni ma mun je
Dubai ne da Abba ga kuma hidimar biki da
muka sha".
Da sauri Larab ya ce masa.
"Biki? Ba dai ka yi aure ba mu sani ba?
Lallai da ka cika mara mutunci
Hafiz ya yi dariya, ya сё.
"Ai kuwa amarya na nan a gidana, sai ka
zo shan man shanu ko?"
Larab ya ce, "Dan Allah tsaya, da gaske
kake ko da wasa?"
Jin yadda ya yi maganar yasa ya tabbatar
lallai ya yi tunanin da'gaske yä ke, ya ce.
"Kai wasa na ke maka, Abba ne ya kara
aure, yau sati daya ke nan".
Larab ya ce, "Duk da haka dai ba ka
kyauta ba, ai yadda muke da kai ya dace ka
sanar min"
N. 84
SADAUKARWA-1
Hafiz ya ce, "Ka ga sai anjiman idan ka
zo... Ka gaishe min da Umma".
Ya kashe wayar dai-dai lokacin da ya
ga wani matashi mai kama da malamai ya
tsaya da mashin dinsa. Sanye ya ke da
dogayen kaya, da hula a kansa, kana kallonsa
ka san yana fama da talauci, don shi kansa
mashin din da ya ke a kai ya tsufa da yawa,
haka kayan ma yadi ne duk ya yi fari alamar
rana