da ta amince lokaci daya
sakamakon kwarjinin da ya yi mata, duk da
cewa tana da saurayi amma yanayin karatu da
ya tafi kasar waje ya yi wa soyayyar ta su karan
tsaye, har ya kasance ta fuskanci ba auren'ne a
gabansa ba, karatu shi ne ya saka a gabansa, ga
shi ita kuma a tsarin mahaifinta da ta kammala
diploma ya ce zai ayrar da ita.
Saboda haka Hafiz ya samu muhalli a
zuciyarta, dama ita soyayya tamkar shuka ce
wadda idan ana ban ruwa nan da nan za ta
mike, to haka idan saurayi na kulawa da
budurwarsa ta hanyar kiranta a waya ko zuwa
inda ta ke za ta shaku da shi, har ta ji ta amince
masa dari bisa dari.
Wannan ya sa ba a dauki tsawon lokaci
ba. Hafiz ya mamaye duk wani gurbi na
soyayya da ke cikin zuciyarta.
Zuwansa na farko a garin Katsina
Zubaida na ganinsa ta ce, wai suna matukar
kama da juna, dan ita da farko ma ta 'fauka
yayan Rufa'atun ne.
NAJNOOR 28
SADAUKARWA-1
Haka zuwansa na biyu da ya shiga gaishe
da mahaifiyarta, ita ma ta ga wannan kamanni,
har abin ya dinga ba ta mamaki da tsoro.
Shi ma a nasa bangaren duk wanda ya
dubi hotunanta sai ya ce suna kama.
Soyayya ce suka gina bisa gaskiya da
amana, ga shi dama kowanne da kyakkyawar
niyya ya ke son dan uwansa.
A daren sam bai sami bacci ba sai bayan
ya gabatar da sallar asuba a masallacin da ke
layinsu, kai tsaye ya dawo sasshensa yana
mamakin yadda a ka yi Abbansa bai je
masallaci yau ba, tunda ya sąba a can
masallacin suke haduwa, idan an gama sallar
sai su dawo tare. Amma yau shi kadai ya dawo,
bai san abin da ya hana Abban zuwa ba.
Kafin ya shigo sashen nasa tuni har bacci
ya ci karfinsa, saboda haka yana shigowa ya
maida kofa ya rufe, ya wuce zuwa bedroom
dinsa ya zube akan gado ya soma kwasar
ramakon baccinsa da bai yi ba a daren jiya.
Karfe takwas na safe su Alhaji Umar
yayyen mahaifinsa sun dira a gidan, har sun
NAJNOOR29
SADAUKARWA-1
"Idan ya dawo kya fada masa mun tafi,
kuma ya yi kokarin ciro kudin nan kafin mu
dawo, dan mutanen sun nuna suna bukatarsu
yau, Alhaji Mande zai zo sai ya ba shi".
Та се, "То Alhaji. Allah Ya kai ku lafiya,
Ya dawo da ku lafiya".
Gaba daya suka amsa mata da, "Ameen"
Sannan suka fito harabar gidan suka hau
motar Alhaji Atiku, dama da ita suka tsara za su
yi tafiyar, don haka mashina suka hawo suka zo
gidan nasa da ke Buzoye Road.
Su uku ne, shi kansa Alhaji Atikun, sai
Alhaji Umar, da Alhaji Abubakar wanda ya ke
kanin marigayiya Halima.
Suna tafe suna hirarsu cikin nishadi har
suka isa Kano, sannan suka dau hanyar birnin
Katsina.
Firgigit! Kamar wanda a ka kwarawa
ruwan sanyi haka Hafiz ya farka daga
nauyayyen baccinsa. Babu abin da ya soma da
shi illa kai dubansa ga agogon da ke makale a
jikin bango wadda ta nuna masa karfe sha biyu
saura mintoci takwas.
NAJNOOR 31
SADAUKARIVA-1
Gabansa ya yi mummunan faduwa, ya yi
mamaki matuka da ya kai wannan lokacin a
kwance, domin ya san yasaka alarm tun kafin
ya tafi sallar asuba, akan karfe tara ya tashe shi.
Ya kai hannunsa da sauri ya dau wayarsa
ya duba, 22missed calls ya tarar a fuskar wayar,
goma sha takwas duk daga mahaifinsa ne!
Zumbur ya mike tsaye ya cire pyajames
din ya zura doguwar jallabiya sannan ya tunkari
cikin gidan ba tare da ya kurkure baki ba, yana fargabar shanyawar da ya yi wa mahaifan nasa, har kawo wannan lokacin.
Tun kafin ya karasa isa cikin falon Hajiya Asiya ta soma yi masa dariya.
"Makararren ango, ko kuma na ce ango
mai boyo saboda kunya”.
Babu walwala a fuskarsa ya ce.
"Suna ina ne?"
Тa сe, "Ayya! Ai yanzu idan ba su kai
Katsinan ba, ko shakka babu sun wuce Kano".
Hannu ya dora a kai.
"Me yasa Abba ya yi min haka?"
NAJNOOR 32
SADAUKARWA-1
Ta сс. "Ya yi maka haka ko ka yi wa
kanka? Tun fa safe ya ke kiran wayarka ka ki
dauka, na je kuma bangarenka iya bugu ba а
same ka ba, ka san da za ku tafi da wuri ka
kama hanya ka yi ficewarka yawonka, idan ba
za ka je ba ai bai kamata ka ce masa za...
Ya katse ta cikin gimshira da zancenta.
"Ni fa Anti babu inda na je"
Ta dube shi cike da mamaki.
"Babu inda ka je amma saboda Allah
kana ji ina buga kofa ka ki budewa?"
Ya ce. "Wallahi bacci ne mai nauyi ya
dauke ni, kasancewar jiya sam ban samu na
runtsa ba”.
Ta jinjina kai.
"Cab! To ai sai ka dauki hanya, ko kuma
ka bari sai wani lokacin, yau dai an sha da kai”
Ta karashe maganar cikin dariya, ba shi
da zabi ko damar tsayawa ci gaba da
saurarenta, sai kawai ya koma dakinsa ya
dokawa Abban nasa kira. Yana dauka ya ce,
"Dan Allah Abba ka yi hakuri, wallahi
bacci ne ya kwashe ni shi yasa ban ji karar
NAJNOOR 33
SADAUKARWA-1
kiranka ba... Yanzu kuna ina ne? Welcome to
Katsina? Shi ke nan Allah ya dawo da ku
lafiya".
Ya kashe wayar, sannan ya lalubo lambar
Rufa'atu ya ce.
"Am sorry Sweety ga su Abba nan sun
iso, ni ban samu zuwa ba saboda wani dalili".
Ta yi dariya kafin ta се.
"Ni dama na san wasa kake ba zuwa za
ka yi ba, shi yasa ma ban kawo zuwan naka a
raina ba”.
Jin ta fadi haka ga kuma matsalar da ka
samu sai ya bi ta a hakan.
"Yanzu yaushe kile da bukatar ganina?"
Ta ce, "Yanzu".
Ya yi dariya ya ce
"Yanzu kam'ta wuce sai dai gaba".
Та се, "Тo duk lokacin da ka samu sarari
ina maraba da zuwanka"
وو
Ya ce, "Ina nan zuwa cikin satin nan"
99
Та се, "То, sai ka zo"
Ya ce, "Babu wata kalma da zan samu
sai wannan?"
NAJNOOR 34
SADAUKARWA-1
Dariya ta yi, murya a nutse ta ce.
"Ai na gama magana tunda na yi maka
addu'ar Allah Ya kawo ka lafiya ko?"
Shi ma ya narke murya, ya cc.
"Na ki wayon, idan zaki zage ki zage
malama, yau kalamai na ke so masu sanyaya
zuciya da sanya nishadi".
Та се. "Тabdi! Ashe kuwa kunnuwanka
za su kurumce?"
Ya ce, "Yo tun yaushe an ce da kuturu ka
gama da duniya lafiya? Ai ina tabbatar miki tun
daga lokacin da kunnuwana suka soma jin
amon muryarki suka kurumce, muryarki ce
kadai ke tasiri a cikinsu
Ta ce. "Hmm, ni dai sai ka iso"
Ya cc. "Au kora ta ma kike? To shi ke
nan. sai na iso din"
Ya kashe wayar yana mai cizon yatsa
akan rashin zuwanshi Katsina, ya so matuka ya
yi tozali da abar Kaunarsa akalla hakan ya
wanke masa mikin rashin ganinta da ke
damunsa tsayin makonni uku.
NAJNOOR 35
SADAUKARWA-1
KATSINAN DIKKО
arfe sha biyu dai-dai na rana su KAlhaji Atiku süka iso welcome
to katsina da ke sabon garin
Dandagoró. Bayanm Alhaji Atiku ya gama
waya da Haliz ya juya bangaren Alhaji Umar
yana murmushi, ya се.
"Mutuminka ne, wai bacci ya yi shi yasa
ya makara".
Alhaji Umar ya ce. "Ai kwanda haka...
Yanzu sai ka kira can gidan su yarinyar su ba
mu kwatańcen gidan".
Ba Gata lokaci kuwa Alhaji Atikuü ya kira
lambar, bugun farko ta shiga a ka kuma dauka.
Bayan sun gaisa ya fada musu unguwar
Goruba Road zá su nufa, da ya ke Alhaji Atiku
ya san binin na Katsina. don liaka ba su sami
matsala ba gurin gane kwata,nce.
Mustapha kanin Rufa'atu ya bude musu
falon baki, sannan ya yi musu jagoranci zuwa
cikin falon. Babu bata lokaci a ka soma gabatar
musu da kayan ciye-ciye da lashe-lashe irin dai
NAJNOOR 36
SADAUKARWA-1
karar nan ta mutanen Katsina babu wacce ba su
gani ba.
Tun a nan Alhaji Atiku ya soma
sakankancewa dansa ya yi dace da gidan
karamci. Sai da suka kammala da komai sannan
mazaje guda biyu suka shigo, malam Hamza da
Alhaji Shehu, dukkaninsu yayyun mahaifin
Rufa'atu ne.
Suka zazzauna a ka gaisa a mutumce,
tare da yi wa baki sannu da zuwa. Bayan haka
Malam Hamza ya dubi bakin cike da kulawa da
mutuntaka irin ta Katsinawan Asali, wanda ake
gane tun a fuskarsu, ya ce.
"Muna matukar farin ciki da zuwanku
gare mu da kyakkyawar manufa".
Alhaji Abubakar ya ce, "Babu komai".
Ya dubi Alhaji Atiku ya ce.
"Ya kamata mu gabatar da abin da ya
tara mu, saboda sha;anin nisa ko?"
Alhaji Shehu ya ce, "To bari mahaifin
yarinyar ya shigo"
Ya ciro waya ya kira Alhaji Nuhu, ya ce.
NAJNOOR 37
SADAUKARWA-1
karar nan ta mutanen Katsina babu wacce ba su
gani ba.
Tun a nan Alhaji Atiku ya soma
sakankancewa dansa ya yi dace da gidan
karamci. Sai da suka kammala da komai sannan
mazaje guda biyu suka shigo, malam Hamza da
Alhaji Shehu, dukkaninsu yayyun mahaifin
Rufa'atu ne.
Suka zazzauna a ka gaisa a mutumce,
tare da yi wa baki sannu da zuwa. Bayan haka
Malam Hamza ya dubi bakin cike da kulawa da
mutuntaka irin ta Katsinawan Asali, wanda ake
gane tun a fuskarsu, ya ce.
"Muna matukar farin ciki da zuwanku
gare mu da kyakkyawar manufa".
Alhaji Abubakar ya ce, "Babu komai".
Ya dubi Alhaji Atiku ya ce.
"Ya kamata mu gabatar da abin da ya
tara mu, saboda sha;anin nisa ko?"
Alhaji Shehu ya ce, "To bari mahaifin
yarinyar ya shigo".
Ya ciro waya ya kira Alhaji Nuhu, ya ce.
NAJNOOR 37
SADAUKARWA-1
sauri".
"Yauwa ka hanzarta dan Allah suna
Kamar dama a bakin kofa ya ke, sai ga
shi ya shigo sanye da danyar shadda Mali
Quality, dinkin tzarce daga hula har takalma da
shaddar duk green ne, abu ga farin mutum sai
kayan suka haska shi matuka.
Sallamar da ya yi ce ya sa dukkansu suka
dago kai suka dube su: Das! Gaban Alhaji
Atiku ya fadi, hakika bai manta wannan dan
ta'addar fuskar ba, wadda ta kasance mai
tsananin muni da munanawa. Dama yan a raye?
Tambayar da ya yi wa kansa ke nan, ya yin da
Alhaji Nuhu ya zauna fuskarsa dauke da fara'a,
kira ya ke.
"Sannunku da zuwa
Yawan fara'arsa ya sa su Alhaji Umar
nutsuwa da lallai sun dace da gidan mutunci,
shi kam Alhaji Atiku kallon fuskarsa kawai ya
ke yana tuhano wsu shekaru can da suka gabata
zamanin wanzuwar ta'addanci da rashin imani
irin na Alhaji Nuhu, sai bayan kammala
NAJNOOR38
SADAUKARWA-1
gaisuwar ne Alhaji Shehu ya dubi Alhaji Umar
ya ce.
"Muna so ku sake gabatar mana da
kanku".
Alhaji Umar ya nuna Alhaji Atiku, ya ce.
"Wannan shi ne mahaifin yaron
wajenmu, mu kuma yayyensa ne. Kamar yadda
kuka sani mun zo nemawa yaronmu mai suna
Hafizu auren yarinyar wajenku wadda ikon
Allah Ya hada su a can garinmu Bauchi".
fadin.
Alhaji Shchu ya gyara zamansa yana
"Haka lamarin Ubangiji ya ke, duk inda
mijin mace ya ke, to fa sai an hadu, misali akan
Rufa'atu wadda daga haihuwarta zuwa yanzu
mahaifinita ba ya son ta yi nisa da shi"
Ya juya ya dubi Malam Hamza, kamar
yana nemon shawarar abin da zai fada, y
gaba da cewa.
"To mun godewa Allah da ya kawo ku
gare mu da zummyr nemawa danku auren
'yarmu, sai, dai wani hanzari ba gudu ba, sanin
kanku ne bincike a cikin lamarin aure abu ne
NAJNOOR 39
SADAUKARWA-1
mai kyau, kuma koyi ne da sunnar ma'aiki, cika
sharadi ne daga cikin sharuddfan aure, wanda
mafi akasarin auren da a ka gina shi ba tare da
an yi bincike ba ya sake kasancewa da yinsa
gwamma ba a yi ba, domin za arika fuskantar
matsalolin da ba a san da su ba. To maganin a
yi kar a fara... ba wai ba mu yarda da
nagartarku ba ne, a'a abu ne mai kyau da ya
kamata a ce an yi".
Alhaji Abubakar ya ce, "Wannan ba
matsala ba ce, mu da mun zo ne mu tsayar da
magana sati biyu masu zuwa mu dawo a saka
rana, amma ba komai"
Malam Hamża ya ce, "Eh duk da haka ba
zai dakatar da komai ba, cikin-mako daya za
mu iya binciken duk da iya dace. idan mun
gamsu da binciken shike nan sai ku dawo a
ronar hakano saf mu eo kunja akasn
ku yi hakuri haka lamarin nema ya gada, dama
can Ubangiji ya rubuto ba rabonsa ba ce"
Alhaji Umar yana murmushi ya сс.
NAJNOOR 40
SADAUKARWA-I
"Wannan ba matsala ba ce, mu ma za mu
ji dadin hakan, kuma za mu yi alfahari da
binciken da za ku yi.
ya ce.
Alhaji Atiku ya ja ajiyar numfashi kafin
"Ina da uzuri".
Gaba dayansu suka bada nutsuwarsu gare
shi. Yayin da ya ci gaba da cewa.
"A cikinku waye mahaifin yarinyar,
wanda ya haife ta?"
ce.
Alh. Nuhu yana murmushi'ya ce.
"Ga ni nan, ni ne mahaifinta"
Alh. Atiku ya sake kafe shi da idanu, ya
"Ka yi hakuri da tambayoyin da zan
gabatar a gare ka".
"Kada ka damu, ai zan ji dadin hakan
dan komai da bincike ya fi tafiya daidai".
Ya fada cikin jin dadi.
Alhaji Atiku ya jinjina kai A alamun
gamsuwa da abinda ya fada, sannan ya ce.
"Da farko zan so sanin sunanka' da
asalinka".
NAJNOOR 41
SADAUKARWA-1
Babu wanda ya yi mamakin jin wannan
tambayar da ta fito daga bakinsa. Alhaji Nuhu
ya gyara żzama yana fadin.
"Sunana Alhaji Nuhu, ni haifaffen garin
Katsina ne a karamar hukumar Bakori".
Alh. Atiku ya cika da mamaki ga dai gari
daidai da yadda ya ke tsammani, amma a sunan
ne ya sha bamban da wanda ya yi zato, ya сe.
"Ka tabbata sunanka ke nan?"
Sai a ka shiga kallon-kallo tsakaninsu
cike da mamakin tambayar da ya yi.
"Ka yi hakuri da tambayata idan ta yi
maka tsauri. Na yi amfani da maganar da kuka
fada cewar zaku yi bincike shi ne nima na ke
son soma binciken a matsayina na mahaifin
yaron da zai auri 'yar wajenku". Inji shi.
"Ba wai na ji zafin tambayar ba ne
mamaki na yi da ka yi tababar sunan nawa,
amma ba komai gaskiyar ke nan
"Na gode, tambaya ta biyu da zan maka
ita ce, matanka nawa?"
"Haba Atiku wannan wace irin tambaya
ce?" Fadar Alhaji Usman.
NAKOG 42
SADAUKARWA-1
"Aa ku kyale shi, wallahi ban damu da
tambayoyin da ya ke min ba.!! matata daya tun
kuruciya har yanzu ita ce, muna da 'ya ya
shidda da ita"
Alh. Atiku ya jinjina kai, ya ce.
"Ina da sauran tambayoyin da ya kamatá
na yi maka, to amma yadda na ga kun dauki
lamarin ba zan iyá karasa sú bà, illá' ina ba ku
hakuri eewar ba yanzu zan yi wa yarona aure
ba. kada ku saurare shi, ku aurar da ita ga
wan
Dukkansu ransu ya baci da wannan
maganganu na Alhaji Atiku, musamman Alhaji
Nahu daaa le gi nin am sun shirvg di nes
mutunci. ba don haka ba sun san dansu Bai
tashi aure ba za su zo har inda suke da sunan za
stu zo neman aure?
L
st ke ian ba sai sun sanya ya saka ran
zuwansuneman auren ba?
Yayin da Alhaji Atiku yana gama fadar
atepre draz af thda yasaKan ya tice t a auknesif
ma ransua dagule yana kuma godiya ga Allah
ΝΑΙΝΟO1R43
S1DUKARUAI
da Ya samya da shi a ka zo Katsinan, don da zai
zame yu bar su Athaji. Gmar su zo. SaVga
rashin dacewar hakan, gar shi zuwan ya yi masa
rana. wata Kika da bai zo ba da an tatka ABIN
KUNYA da har duniya ta nade ba zai uanta
ba balle kuma yadda al Ummni za su dubi
lamarin.
Ya zauma a cikin motar yana goge gumin
da ya tsattsalo masa, lallai lamarin aure abu ne
ai girma, wanda da shi da mutuwa ne manyan
ababen tonon asiri. a gare shi tun wanican
lokacin bai kuma tsamamanin zai vi dozali da
Alhaji Nuhu ba. domin daga baya wani M/uriya
Ral shit Kanam
wani rabata ha znayt Nantarinahanyaraa
toshe darundum! Saboda dama meta dan
va ke tmanin zai kawo masa wani dabagi da aaa
rasewa tunda dadewa.
Cikin Bacdin rai Alhaji Nuhuya.cc.
"Na godewa Allah da Ya sa ban aurar da
Naa gndaка bа. do
hakan, da kuka vi Na nuna mana ku-Kanaman
SADAUK.IRWA-I
mutane nc. Sai dai ku sani danku ko shi ne
autan maza ba zan taba ba shi auren 'yata ba.
Kuma ku sanar masa kada tsatitsayi ya sa ya
tako gidan nan"
Fuuu! Shi ma ya fita yana huci, su Alhaji
Usman ba su da ta cewadomin sun san duk
abin da a ka yi musu Alhaji' Atiku ne ya ja
musų, wai na 'yan magana da suke cewa, duk
abin da ya sami shamuwa watan bakwai ne ya
ja mata. Tabbas su dai Alhaji Atiku bai kyauta
musu ba da ya maida su kananun mutane.
"Ku yi hakuri don Allah
Abin da suke ta fada ke nan, sannan:
suka fito daga dakin kowanne ya shiga motar
babu fara'a a fuskarsa.
Alhaji Abubakar gwanin zuciya shi ya
ja motar a matukar tunzure, shiru babu mai
ndgalia a cikusu hai sai ua suha kai Chalanci
sannan Alhaji Atiku ya ce.
"Don Allah 'yan uwana ku yi hakuri,
wallahi ban yi hakan da mummunan manufa
ba, illa dole tasa na san kuma idan har za ku
.i
NAJNOOR 45
SADAUKARWA-J
saurare ni za ku yarda da abin da na yi shi ne
dai-dai".
Alhaji Umar ya dube shi, ya ce.
"Takaicinmu daya, ko da a ce kana da
hujjar kamawa, amma me yasa ka amince mu
zo nema wa Hafiz aure? Ko kuwa dama kana
so ne duniya ta dube mu hr yanzu ba mutane
ne masu daraja a gare ka ba? Kana so ne ka yi
ramuwar gayya da sharri bayan kai da
bakinka ka ce ka yafe duk wani abu da a ka yi
maka?"
Girgiza kai ya soma yi, sannan ya ce.
"Wallahi ba haka ba ne Yaya, na yi
haka ne bisa babbar hujja. Hasalima kamar
yadda kuka sani mun zo garin nan da zummar
neman auren Hafiz gare su, hakan ne a zuciya
ta. Ban taba sanin wace ce Hafiz ya ke so a
zahiri ba sai a hoto da na ke ganinta, haka ban
san waye mahaifinta ba, ban bincika ba sai
yanzu da muka zo. Saboda ina ganin hankali
da kamalar Hafiz ba zai zabo 'yar kananan
NAJNOOR 46
TANAKAUN SADAUKARWA-1
mutane badya be zal autaindarda da
hakan a raina, nob ИОХИН ODAHа
UWSaboda haka ya kamata Kuy mitA?
dababu nujja ba zanyf hakatbam ub піжo
18msAlhaji Abubakar ba tarendaya fuyo a
yalec?Ysw ns2 sa msn s Οι πολκα emwAud
daтNA HUJJARSTA KENIAT
abulne ka gani bal yl maka baa
hakűffmu dawo sannan fu sah ya
Gillowa damatins ba wapkayiA
danyen hukuncin wanda kai Kafk
mun ji kunya matuka, Haba! Gaskiya Ka bata
maná, ka zubár mana da Rima da mCi"
sm s Cikin sanyin fhalya AlhjiAtiato
"Idan kuka saurarPuźdti
hujjar tawa" isd ssigtig 67 uliJA ijsdlA nilsd Cikin harrukä AlhajiUnarya e
noz issairecwarka ke kana da hujja? md
mw har yanzu ba mu sah hujjat Ba iSTEW nab
ne Rasa, ya eda win il ai awan im ad
"sd
NAJNOOR0014
SADAUKARWA-I
"Wallahi INA DA HUJJA, bana yanke
BAHAGON HUKUNCI don son rai...
Shekaru ashirin da takwas da suka wuce
lokacin da matsalolin nan suka faru har na
buce wa ganinku aiki ya kai ni karamar
hukumar Bakori, to a nan na san waye shi
wannan mutumin. Dan ta'adda ne na karshe,
idan kuna neman mutum mara imani da rashin
Isoron Allah da kun zo kansa kun gama...
Wallahi Atlah ne kadai ya san hatsabibancin
wannan mutumin...
Alhaji Umar ya katse shi da fadin.
:
"Jira na yi maka wata tambaya, idan shi
ba shi da halin kirki, dole ne duk zuri'arsa ma
ba su da halin kirki ne?"
Alhaji Atiku ya girgiza kai, ya ce. eint
"Ba dole ne ma a samu mai rashin halin
kirki a cikin zuri'arsa ba, amma dai mai son
dan Kwarai ya auri isassa. Duk uba na gari
yana fatan dansa ya auro 'yar mutunci, nasaba
ba Karamar rawa ta ke takawa a rayuwar aure
ba".
NAJNOOR 48
り
SADAUKARWA-1
Alhaji Umar ya sake magantuwa.
"Shi ke nan, sai ka san yadda za ka yi
da Hafiz, tunda kowa ya san irin son da ya ke
yi wa yarinyar nan".
Alhaji Aiku ya ce da shi.
"Ba na jin ta Hafiz, domin na san yaro
ne mai biyayya, yana son abin da na ke so.
Yana kuma kin wanda ba na so, don haka ba
na duban matsala ta wannan fannin
Su duka biyun suka се.
"To Allah Ya zaba mafi alkhairi"
Ya amsa musu.
"Ameen
NAJNOOR49
edash ua ad
BAUCHI
SADAUKARWA-1
un karfe hudu da rabi Hafiz ya Tdwo gida ya ke zaune a falo ba shi
da wani labari sai na 'har yanzu su
Abba ba su dawo ba'.
Dariya Hajiya Asiya ke yi masa, tana
cewa ya kara kiranshi a waya mana.
Ya ce, "Ina! Wallahi Aunty kunya na ke
ji, bana son na dinga nuna zakewata".
Ta dube shi cike da mamaki, ta ce.
"Au ashe kana jin kunyar? Ai na dauka
aboki ka dauki Abban naka?"
Ya ce. "Mhm Auntv ke nan
Ya mike ya koma sashensa.
Tun. bayan sallar la'asar ya ke neman
lambar Rufa'atu ammá bai same ta ba, haka su
Abbansa duk ya neme su amma dif! Hakan ya
sake daga hankalinsa, nutsuwa ta Kaurace masa
barin yanzu da ya ga har karfe tara na dare ta yi
ba su dawo ba.
Yana cikin wannan yanayi har misalin
karfe goma da rabi sannan ya sake shigowa
NAJNOOR 50
SADAUKARWA-1
falon gidan, Hajiya Asiya ya tarar a falo ita ma
zuwa lokacin ha.nkalinta a tashe ya ke.,.
Yana kallon yanayinta gwiwarsa ta dada
yin sanyi, cikin rashin kuzari ya zauna yaraf
Akan kujera, ya cc.
"Wai har yanzu ba su dawo ba?"
Ta ce, "Eh wallahi, ni har hankalina ya
soma tashi. Anya lafiya kuwa?"
Ya leme baki, ya ce.
"Abin da na ke fargaba ke nan kar a ce
wata matsala ce ta faru da su".
Haka suka zauna suna tattauna wannan
matsala. Mislin karfe sha daya suka ji dirin
motar Alhaji Atiku a harabar gidan.
Gaba dayansu suka sauke ajiyar
numfashi, sai yanżu suka samu nutsuwa. Suka
mike zuwa bakin kofa, zasu fita ke nan suka yi
kicifus da Alhaji Atiku yana foßarin shigewa
hakan ya sa suka kauce ya shigo, sannan suka
bi bayansa.
CC.
Ya zauna akan kujcra yana murmushi, ya
"Kun ji ni shiru sai yanzu ko?"
NAJNOOR 51
SADAUKARWA-1
Çikin kulawa Hajiya Asiya ta ce.
"Ai kuwa, tun la'asar muke zuba idanu,
amma shiru"
Ya ce, "Karfe goma muka shigo gari, na
biya sauke su Yaya ne a gidajensu, na taho
kuma a ka kirani a waya a ka shaida min
Hamdiyya (amaryar da zai aura) ba ta jin dadi
tun safe, shi yasa na biya na dubata".
Kamar ya watsawa Hajiya Asiya ruwan
zafi haka ta ji, wani irin tukuki ya tokare mata
makoshi, maimakon ya bari sai gobe ya je ya
dubata, amma shi ne ya je yanzu? Lallai namiji
sai a bar shi!
Nån da nan annurin fuskarta yo gushe ta
kasa cewa komai don takaici, tsam ta mike ta
nufi dakinta.
Su duka suka bi ta da kallo, sam Alhaji
Atiku bai yi mamakin hakan ba, ya san halin
mata da zafin kishi.
Har ta shige dakinta ba wandą ya nemi
dakatar da ita, sai bayan ta shige ne Alhaji
Aliku ya dubi agogon hannunsa, sannan ya
maido dubansa ga Hafiz ya ce.
NAJNOOR 52
SADAUKARWA-I
"Ya kamata ka je ka kwanta zuwa safe
sai a ka ji komai".
Hafiz ya sosa keya, ya so ya ji
sakamakon tafiyar, sai dai shi kansa ya san
lokaci ya ja, ya kamata ya ba wa mahaifin nasa
dama ya huta gajiya, ko ba komai ya tabbatar
da zuwan su Katsina, kuma a yadda ya ga
fuskar mahaifin nasa ya ga alamun nasara a
tattare da shi. Saböda haka sai ya yunkura ya
ce
"To Abba, Allah ya huta gajiya"
Alhaji Atiku ya dube shi cike da
tausavawa sahoda valsan irin matsanarcin son
da ya ke wa Rufatu, kasarce duk
mutumin da ya rabe shi ya san da wannan
kaifin son da ya ke wa Rufa'atu.
To amma ya za a yi, Kaddara ce wadda ta
riga fata, domin ya san hakam da ya yi shi ne
mafita a garc shi gudun aikata abin da za a
dawo ana da na sanin faruwarsa.
Ya ce. "Allah ya sa".
Haliz ya koma dakinsa. har lokacin dai
shiru bai samu wayar sanyin idaniyarsa ba.
NAJNOR 53
SADAUKARWA-1
Ita kanta Zubaida aminiyar Rufaʼatu ya
sha neman layinta bai samu ba.
Ya kammala abin da duk ya dace ya yi ya
kwanta, amma sam bacci ya Kauracewa
idanunsa, dokin wayewar gari da kuma farin
cikin tabbatuwar neman aurensa su ne suka
cushe masa zuciya.
Washegari bai samu sararin ganin Alhaji
tiku ba, sai bayan an gama sallar la'asar ya isko
shi a dakinsa yana duba wata jaridar
RANARMU.
Ya gaishe da shi. sannan ya saurara don
iin ahin da zai fada Shiruna wani lokaci va
Efta a isalise kadm Jaga bisant Athaj
Atiku ya ajiye jaridar akan desk din da ke
gabansa, ya dubi Hafiz ya ce.
"Kafin ua ce komai game da batun
zuwanni make matá
halayen da ake son musulmi ya kasançe da stt,
Na farko ya kasance mai nutso ga neman
ilimi. Ya kasance yana aiki da ilimin, da ya ke
da sii ta hany atgjewa abin da ya Zanto haram
a gare shi. Ya kuma kasance mai yarda da
NAJNOOR 54
•
SADAUKARWA-1
kaddara, domin kaddara tana daga cikin ababen
da kewa rayuwa tarnaki, shi yasa ake so mutum
ya kasance mai yarda da kaddara"
Jikin Hafiz ya yj sanyj sosai, nan da nan
tsoro ya shige shi, domin ya san banza ba ta kai
zomo kasuwa, hakika akwai wani al'amari da
ya faru a zuwansu Katsina. Tun yanzu har ya
soma tausayin kansa, saboda ya san soyayyar
Rufa'atu ba karamin kamu tà yi wa zuciyarsa
ba.
Yana tunanin ta ya zai iya rabuwa da
abar da ya ke so da kauna tsayin lokaci? Abin
kamar da wuya bera a sansanin kyanwoyi.
Sabed ka a teke ya soma addu'ar kar
lamarin yakasance na rabuwa da Rufa'atu ne.
Alhaji Atiku ya sake duban Hafiz cike da
tausayawa, ya ci gaba da cewa.
"Idan har ka kasance mai wadannan
abubuwa da na lissafa maka hakika za ka samu
rangwamen zogin zuciya a duk lokacin da wani
sha'ani` ya taso ka, Na sani kai yaro ne mai
dumbin biyayya, uunda na'ke da kai ban taба
cewa ka yi wani abu ko ka baii ka kasa bin
NAJK DOR 55
SADAUKARWA-1
umarnina ba, hakan yana matukar faranta min
rai, har na ke tunanin wane irin tallafi ya dace
na yi maka a duk lokacin da ka tashi aure.
Cikin hukuncin Ubangiji sai na gano
babu tallafin da kake bukata a gare ni, wanda
zai inganta rayuwarka sai na dage wajen tayaka
zaben matar aure, gudun kada ka shiga halin da
na ke shiga akan aure.
Falillahi hamdihi, mun je nema maka
aure a Katsina, abin ya matukar burge ni
saboda an karrama mu, sun nuna mana
halayensu na KATSINAWAN ASALI".
Wani sanyin dadi ya ziyarci zuciyar
Hafiz, wancan tunanin ya gushe. Ya ci gaba đ
cewa,
"Sai dai kamar yadda kullum na ke yi
maka addu'a Allah Ya zaba maka mace ta gari,
wadda zą ka yi alfahari da ita ta ba wa
'ya'yanka arbiyya ta gari, sai Allah Ya cika
min burina ya hana a yaudare mu a cusa mana
bara-gurbi a cikin kyakkyawan tsatsonmu.
Ka yi hakuri akan duk abin da zan fada
maka, dole ce tasa kwanan (uwar miji dakin
-NAJNOOR 56
SADAUKARH 1-1
amarya) gudun kar a auri racen da Za ka dawo
kana da na sani,
Maganar gaskiya