An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SadaukarwaNaja'atu Haruna Saleh
(Matar Nura Sada Nasimat KT)
SADAUKARWA-I
SADAUKARWA
NA
NAJNOOR
NAJA'ATU HARUNA SALE
(Matar Nura Sada Nasimat Kt)
NAJNOOR 1
SADAUKARWA-/
SHEKARAR BUGU
2015
GODIYA
Ina mika godiyata ga Ubangina.
mahaliccin kowa da komai, wanda Ya ba ni
dama da ikon rubuta wannan littafi nawa ba
don iyawata ba. sai don kudirarsa na
tabbatuwar rubutuna alkali a cikin al'umma.
GODIYA TA MUSAMMAN
Ga Mijina abin tinkahona. wanda ba
gajiya da bukatuna. ina fatan Allah Ubangiji Ya
saka masa da gidan aljanna Firdausi, Ya
daukaka, Ya kiyaye shi daga dukkan sharri,
Allahumma Amin.
SADAUKARWA
Wannan littai nawa SADAUKARWA
ne ga mahaifiyata Marigayiya Rukayya Na'iya,
ina fatan Allah Ya kai haske a kabarinta, Ya sa
aljanna Firdausi ce makomarta,
NAJNOOR 2
JINJINA GA:-
SADAUKARWA-I
Alhaji Haruna Sale (Abbana)
Alhaji Sada Isah Mani (Babana)
Alhaji Ibrahim Na'iya (Kawuna).
YABON GWANAYE
Makaranta littattafaina a duk inda ku ke,
bisa kokarin da ku ke yi na duba littafina, Allah
Ya saka muku da alkhairi. Ya bar kaunar da ke
tsakaninmuú har zuwa aljanna Firdausi, amin
MUN HADE HAR KULLUM
bomAisha: Wada Abdullahi (Jini da tsoka)
Maimuna Idris Sani Beli lN
As aids
ch Ten
Sadiya Garba Yakasai
Fauziyya D. Sulaiman
Ummulkhairi Kabir Aliyu
Khadija Sharubutu
Zulfa'u Jabir Abdullahi
Zulfa'a Aliyu Zango
A'isha Ali Dambatta
Farida Ado Gachi
NAJNOOR. 3
SADAUKARWAHauwa Abubakar Lawan Maiturare
Bilkisu Yusuf Ali
Nafisat Tasi'u Moh'd
Lu'ubatu Isah Lawan
Da sauransu, duk ina mana fatan alkhairi.
JINI DA TSOKА
Dana Kwallin Kwal Yusuf Nura Sada
(Faanah) Allah ya raya ka tare da sauran
'ya'yan musulmi bisa tafarki na gaskiya, amin.
KA CANCANCI YABO
Yahaya Mahi Bookshop, da ke wurin
'Yan Awaki, Bakin Kasuwar Kauran Namoda, Zamfara State.
TA'AZIYYA
Ga 'yan uwana musulmai wadanda
hatsarin rikicin addini ya rutsa da su suka rasa
rayukansu dakuma wadanda suka rasa
muhallansu da rashin nutsuwar zuciya. Allah ya
jikan rayukan da a ka rasa, Ya mayar da abin da
a ka rasa da mafi alkhairinSa, Ya zaunar da
Kasarmu lafiya, allahumma amin.
NAJNOOR
SADAUKARWA-1
TSOKACI
Don Allah ina son a tsaya a fahimce ni.
kar ai saurin yanke min hukunci kamar yadda
wasu suka soma yi akan tallar littafin kawai da
suka gani kafin ma su karanta, wasu har kafirta
ni suka dinga yi. To ina neman alfarma a yi
hakuri a kammala labarin sannan ai sharhi.
Baya da haka, ina rokon duk wanda ya
ga kuskure a cikin littafi na daya da na biyu
bayan wancan maganar da na fada na sakin
aure ga da uba ya aura, to a sanar min don
kiyayewa. Na gode.
GARGADI
Daukar wani Gangare na wannan littafi
ko sarrafa shi ta wata hanyar, laifi ne babba.
kuma hakan yana iya gurfanar da mu gaban
kuliya. Neman izinin marubuciyar shi ne abú
mafi dacewa da samun salama a tsakani.
NAJNOOR 5
SADAUKARWA-I
SADAUKARWA
BAUCНІ
gajiye likis ya shigo falon. A
saboda zirga-zirgar da ya sha, ga
yanayin garin yau an yi rana. Ya
zauna saman kujera tare da jan tsaki ganin
yadda falon ya ke kaca-kaca. komai a yashe
kuma a hargitse, Idan akwai abin da ke bata
masa rai bai wuce yadda mahaifinsa ya yi
rashin dace da matan aure ba.
Mata biyu ne yanzu a gradn. anina
kowacce da tata matsalar. Hajiya Suwaiba
masifa da ganin kyashi ke dawainiya da ita.
yayin da Hajiya Asiya ta ke muguwar kazama
ta kin Karawa. don haka gidan ya kasance
tamkar bola.
Shi kuma mahaifin nasa haushi da takaici
ya sanya ya ki daukar 'yan aiki, ya zuba musu
idanu ko wacce na sharafin gabanta.
Hajiya Asiya ta fito daga cikin fakin
baccinta, hannunta dauke da kofi da robar
NAJNOOR6
SADAUKARWA-1
SADAUKARWA BAUCHI
gajiye likis ya shigo falon, Asaboda zirga-zirgar da ya sha, ga
yanayin garin yau an yi rana. Ya
zauna saman kujera tarc da jan tsaki ganin
yadda falon ya ke kaca-kaca. komai a yashe
kuma a hargitse, Idan akwai abin da ke bata
masa rai bai wuce yadda mahaifinsa ya yi
rashin dace da matan aure ba.
Mata biyu ne yanzd a grudli. anima
kowacce da tata matsalar. Hajiya Suwaiba
masifa da ganin kyashi ke dawainiya da ita.
yayin da Hajiya Asiya ta ke muguwar kazama
ta kin Karawa. don haka gidan ya kasance
tamkar bola.
Shi kuma mahaitin nasa haushi da takaici
ya sanya ya ki daukar 'yan aiki. ya zuba musu
idanu ko wacce na sharafin gabanta.
Hajiya Asiya ta fito daga cikin dakin
baccinta, hannunta dauke da kofi da robar
NAJNOOR 6
SADAUKARWA
Ya ce. "Ba azarbabi ba ne, kuma ni ha
so na hada da kaina, zan li sanin kayan da suka
dace da ita tunda shi bai taba ganinta ba".
Hajiya Asiya ta hařarc shi, "Rasa kunya berianka".
dadi".
Ya sosa keya yana dariya, ya ce.
"Wai ina Anti Babba ne?"
Hajiya Asiya ta kyabe fuska kafin ta ce.
"Sun je asibiti ita da Alhaji, wai ba ta jin
Ya ce, "Allah Ya sauwake... Allah Anti
da gaske na ke. da me- da me zan siya?"
Sai ta dan yi murmushi. ta сс.
"Zan rubuta maka, amma da za ka bi
shawarata ka bari kawai Alhaji ya hafa maka,
dan ba ka san irin tanadin da ya yi maka ba".
Ya yi murmushi ya ce.
"Shi ke nan Anti; amma..."
Ta katsce shi da fadin.
"Ban sanka da musu ba, kullum ka
kasance mai barin wuka da nama a hannun
mahaifinka sai ka ga nasara a cikin lamuranka".
NAJNOOR 8
SADAUKARWA-1
madarar Amira Yoghort, ta fadada fuskarta da
murmushi yayin da ta yi tozali da HAFIZ zaune
akan kujera.
"A'a ango ka sha kamshi",
Ya yi/murmushin yake kafin ya се.
"Kai Anti tun yanzu?"
Tana Kokarin zama akan kujera ta ce.
"Ah to, sai yaushe? Ai ka zama ango
tunda gobe za a je nema maka aure, kuma Alhaji ya ce sati biyu bayan neman auren za a
saka rana wata uku, ka ga ke nan ka zama ango".
Wani sanyin dadi ya mamaye masa
zuciya, shi kam ya tabbatarwa kansa ba
Karamin so ya ke yi wa RUFAʼATU ba, haka
nan tun jiya zuwa yau ya ke cikin matsanancin
farin ciki duk saboda tabbatar dá zuwa nema
masa auren abar so da kaunarsa.
"Gaskiya kam Anti, yanzu ma zuwa na yi
ki fada min kayayyakin da zan zuba a lefe"
Ta ce, "To Sarkin azarbabi, ai Alhaji ne
ya ce zai je da kansa ya hado maka lefen".
NAJNOOR 7
SADAUKARWA-I
AN "Haba G Yaya Suwaiba, wannan wace irin
magana ce haka?"
Wata razananniyar tsawa ta daka mata,
MOLOdanunta RΝΩΝΗ a waje cikin yanayi na rashin mutunci
S02da dama jira na ke, ta се. SD
"Ina ruwanki? Wa ya saka ki a ciki? Kо
katsalandan din da diyan talakawa suka saba za IBT ENL ki yi min?"
Ita ma cikin daurarriyar fuska da maida
Karamar magana ta zama babba, ta ce.
"Ai dole na sanyo baki ko ba a kasa da ni ΠΕΥΙΕ 8/ ba, tunda kina neman haddasawa mijina bacin S
rai a ragowar kwanan da na yi miki alfarma... G DS
Maganar IKO kudi kuma da kike takama kuna da su,
ina sanar miki ko a mafarki ba na fatan na SNISX kasance cikin tsatson mahaifinki, wanda ku
kanku 'ya'yansa kuke hasahen kudin nasa na SR 99 SHA JINI ne....' S20
رز
Wata ashariya Hajiya Suwaiba ta lailayo
ta narkawa Hajiya Asiya, za ta ci gaba da
magana, Alhaji Atiku ya rigata fadin.
"Asiya kar na kuma jin bakinki, kin san
da wasu kudin ba tarbiyya kwara babu su".
NAJNOOR 10
SADAUKARWA-1
Abin da ya sake hasalar da Hajiya
Suwaiba ke nan, maimakon ta ci gaba da yi wa
Hajiya Asiya tijarar da ta tanadar mata, sai ta
koma ga Alhaji Atiku tana fadin.
"Oho dai! Duk da rashin tarbiyyar tamu a
haka a ka gani a ka kuma ce ana so har a ka
auro ni... Gidanka ne na ce ba zan zauna da
JUYA mara haihuwa ba, ehe!"
Hafiz da takaici gami da mamaki suka
gama kashe shi, ya cе.
"Anti dan Allah ki daina wannan
maganar, domin ni kaina na isa shaida a gare ki
cewar Abba yana haihuwa".
Ta auna masa harara, ta ce.
"Da kai sa'ana ne sai na maida maka
raddi. To ubanka shi ne abokin yina, idan kuma
ka nacewa tsoma min baki za ka sha mamaki".
Shiru ya yi bai kuma magana ba, a
saninsa mahaifinsa ya kasance mai aure-aure,
wanda suke rabuwa da matan a sanadiyya
daban-daban, amma bai taba jin wadda suka
rabu ta wannan sigar ba, idan har ta gaji da
zaman gidan sai ta wannan hanyar? Me ta ke
NAJNOOR 11
nufi? Ko tana nufin shi (Hafiz) ba halataccen
dan Alhaji Atiku ba ne?
Shi kansa sai ya ji fitarta a gidan ya fi
alkhairi, tunda har ta tsiro da wannan bakin
Kazafin!
Alhaji Atiku wanda takaici ya gama
lullube masa zuciya, ya nemi guri ya zauna
akan kujera, yana dubanta ya ce.
"Ke wallahi ba ki da hankali sam, ba ki
iya cin ribar zance ba. Bari to ki ji, dama ni na
cewa likitan ya ce miki ni ne bana haihuwa dan
na ga shin idan ni ne matsalar ta shafa za ki iya
zama da ni?
Sai ga shi tun kafin a je ko ina, na gane
ba son gaskiya kike min ba..."
Ta katse shi da cewa.
"Kana nufin zan so ka dan kudinka?"
Ta yi dariya har da buga cinya.
"Allah na tuba, ina abin ya ke? Ko ka
manta inda ka auro ni?"
Ya ce, "Kwarai kuwa. ban manta inda na
auro ki ba, wato gidan da a ka yaudare ni da
kyakkyawar fuska, mummunar zuciya! Ko ba
NAJNOOR 12
SADAUKARUA-I
nan kike nufi ba? Tunda na gano zaman da kike
da ni ba na gaskiya da amana ba ne, sai ki tafi
gidan naku na ske ki, saki daya".
Ta yi shewa ta sake bugun cinya.
"Ta fi nono fari".
Ta maida dubanta ga Hajiya Asiya, ta ce.
"Ke kuma makwacfaiciya, 'yar talakawa
ba sabun shan jar miya ba, sai ki yi ta zama
haihuwa ce ke da ita har abada, kina ji kina gani
bakin ciki zai sa ki yi mutuwar tsaус".
Hajiya Asiya ta fago idanu ta dubeta ta
cс.
"Na gode Allah da Ya sa na kasance mai
biyayya sau da kafa ga mijina. iya abin da zan
ce da ke kenan, sai kuma na yi miki Allah raka
taki goña!"
Tana sababi ta shiga dakis jim kadan ta
fito janye da jakarta ta fice daga falon.
Hajiya Asiya ta dubi Alhaji Atiku, ta ce.
"Alhaji ban so ka yanke hukunci cikin
fushi ba".
Ya ce, "To ai shi mutum ic
mai hangen Dala komai za ka za ka
NAJNOOR 13
SADAUKARWA-1
tabayi masa bajinta ba. dón haka sakin nata shi
ya fi dacewa, ko ba ki ji dan tsabar hauka ba
har cewa ta ke wai ba ni haihuwa. Shin idon
haka ne ta ya a ka yi na haifi Hafiz?"
Та се, "Hаka ne kam, Allah Ya kiyaye
gaba"
Ya amsa da, "Ameen"' Tare da maida
dubansa ga Hafiz da ya zuba tagumi, ya yi
murmushi.
"Manyan anguna ya a ka yi ne?"
Ya ja ajiyar zuciya tare da yin
murmushin karlin hali ba tare da ya ce komai
ba.
Alhaji Atiku ya ci gaba da cewa.
"Gobe kamar yanzu muna, can muna
tattaunawa da surukan naka
Murmushi ya sake yi. Alhaji Atikųu ya сс.
"To bayan sallar ishai ka zo ina son
ganinka, sai mu tsara yadda za mu yi taliyar.
Dzun mun hadu da iyayenka mun yi magan da
su, sai dai anjiman idan ka shigo"
SADAUKARWA-1
Saboda abin da ya faru ya san dole
mahaifinu nasa yana bukatar kasancewa shi
kadai. don haka ya се.
"Shi ke nan Abba... Anti dan Allah ai
mana dambu yau"
Та се. "Cab! Sai ka bari sai Rufa'atu ta
zo ita ce komai kurewar lokaci ba za ta damu
ba, za ta tsaya ta girka maka duk abin da kake
SO
Ya yi dariya yana sosa keya, ya san
zolayarsa ta ke son yi, don haka ya fice ba tare
da ya kuma magana ba.
Bayan sallar isha'i Alhaji Atiku da Hatiz
suna zaune a cikin daki suma cin tuwon
shinkafa da miyar agushi.
Wannan kyakkyawar al'ada 'ce da ke
tsakanin da dazuban. duk dare tare suke cin
abinci. hakan kuwa ya taka muhimmiyar rawa
wajen kara shakuwa da aminci. da iyye da
dama- za su dinga cin abinci tsakaninsu da
yaransu. lallai da an sami shakuwa ,ai yawa,
kuma hakan na matukar taimakawa ta sanin
wace irin rayuw yaronka ke yi.
NAMNOOR 15
SADAUKARWA-1
Sai da suka kammala cin abincin sannan
Alhaji Atiku ya dubi Hafiz yana murmushi, ya
сс.
"Na gode Allah, yau an wayi gari dana
ya isa aure, shi ma zai zama babban mutum"
Murmushi Hafiz ya yi, yay8in da Alhajin
ya ci gaba da cewa.
"Wannan babban abin farin ciki ne, ka
haifi yaron da yå ke son raya sunnar ma'aiki,
don haka ban san adadin farin cikina ba game
da wańnan kudiri naka.
Kamar yadda na fada maka dazun. mun
tattauna da mahaifanka gobe idan Allah Ya
kaimu za mu je Katsinan bisa jagorancinka duk
da akwai waya, za mu nema maka aure' sati
biyu mašu zuwa a sanya rana, ina so bikin ya
kasance watanni üku masu zuwa, ban sani ba
ko hakan ya yi maka?
Haliz ya dan dubi mahaifin nasa ya ce.
Ya yi Abba, ai duk hukuncin da ka
yanke daidai ne".
Alhaji Atiku ya ce. "Yauwa, na godewa
Allah da Ya ba ni da mai biyayya, na ba ka
NAJNOOR 16
SADAUKARWA-/
gidana da ke Shagari Road, sai ka zauna a can.
Allah Ya sa ka yi dace da abokiyar zama ta gari
ba irin matan da Allah Ya jarabce ni zama da su
ba".
Ya karashe maganar cikin yanayin rashin
jin dadi, sannan ya ci gaba da cewa.
"Wallahi Hafiz kullum ina takaicin
halayen natan da na ke aure, kowacce babu
wani hali na alkhairi, daga barauniya, sai
kazama da mai kawo min katti a cikin gida?
Allah Ya jikan marigayiya Halimatu
mahaifiyarka., har ta koma ga mahaliccinta ban
taba samunta da wani mummunan hali ba,
tunda na rasata na ke ta rashin dace da mata na
gari".
Hafiz ya ce, "Sai hakuri Abba".
Ya girgiza kai yana fadin.
"Ai hakurin na ke da su shi yasa kowaçe
na ke zama da halinta. Wallahi har fargaba na
ke na ce zan kara aure, to amma da ya ke har
yanzu ban dace da abokiyar zama ta gari ba shi
yasa bana iya hakuri, kullum fatana Allah Ya
NAJNOOR 17
SADAUKARWA-1
yanke min wannan wahalar, amma ba dan in so
ba na ke ta aure-aure...
Rannan fa ina ji cikin abokaina, wani da
ya ji an ce zan Kara wannan auren da zan yi,
yana buda baki sai cewa ya yi, wai na zama
NAMIJIN ZARA.
Maganar ta min ciwo, sai dai babu yadda
zan yi, na san dole a fadi haka, tunda ni kadai
na san dalilin aure-aure na.... Hafiz samun mace
ta gari shi ne farin cikin kowanne magidanci,
muddin ba ka da ce da mace ba baka da
kwanciyar hankali, kana dai ganin yadda
rayuwar gidan nan ta ke a wani irin bahagon
yanayi...Yanzu ka dubi irin tozarcin da Suwaiba
ta yi min, wane irin hakuri ne ban yi da
munanan halayenta ba? Wane irin karamci ne
ban yi mata ba? Amma da ya ke tana hangen
ban iya sauke bukatunta ba, sai ta 6illo da
wannan hanyar, ita a tunaninta ni ne bana
haihuwa, da ya ke kwalwar Kifi gare ta sai ta
rasa hango abin da a ka shirya mata, nan da nan
ta zurma a ramin da na, gina mata dan gano
hakikanin dalilin da ta ke zaune da ni.
SADAUKARWA-I
To duk ba wannan ne abin duba a gare ni ba, domin an ce mutuwar yawa kaka, idan
kuma hagu ta kiya sai a koma dama. Ma'ana
rashin dace da wasu matan da ban yi ba, ba zai
karya min gwiwar cewar ba ni da sa'ar aure ba.
zan yi wannan auren na yanzu da niyyar samun
dace, idan ita ma da tata illar sai na hakura har
zuwa wani lokaci"
Hakika Hafiz ya tausaya wa mahaifin
nasa, domin ya fi kowa sanin halin da ya ke
ciki, don haka ne ma kullum ya ke cikin taya
shi addu'a Allah Ya yaye masa wnnan jarabta
ta aure-aure.
Ba su rabu ba sai kusan sha faya saura,
dama idan suka zaun hira ba sa son rabuwa har
sai sun soma jin bacci. wand hakan shi ne abu
na Karshe da suke gudanarwa a tsakaninsu.
saboda Hafiz-ba zaman majalisa ya ke ba. bai
ma fiye yawan abokai ba, mahaitinsa shi ne
abokin hira da shawararsa. Ya fi gamsuwa da
zama da mahaifinsa akan kowa.
Suna rabuwa kai tsaye Gangarensa ya
nufa, ya yi wanka tare da sauya kayan jikinsa
NAJNOOR 19
SADAUKARWAzuwa Pyjames masu ruwan goro, sannan ya
kwanta akan gado ya janyo wayarsa fuskarsa
kunshe da murmushi ya kira hasken zuciyarsa
Rufa'atu.
Dukan farko kamar jira ta ke'ta dauka, ko
da ya ke jiran ma ta ke, tunda ya sabar musu
daidai wannan lokacin yana kiranta su sha hirar
su zuwa lokacin kwanciya.
"Amincin Allah Ya tabbata ga wannan
bawa mai tsinkaye da halin da. abokiyar
tagwaicinsa ta ke ciki na mararin son jin
muryarsa
Ya lumshe idanu cikin jin dadi, ya се.
"Ke ma amincin ya tabbata a gare ki, da
fatan yau din ta kasance rana mafi samar da
farin ciki a gare ki. kwatan-kwacin jajibirin
sallah".
Yayin da ta ke gyara kwançiyarta akan
nata gadon cikin farin ciki ta c.
"Fada ma Garnar baki, domin idan da
akwai ranar da ta fi jajibirin sallah samar da
farin ciki da dokin gari ya waye, to kuwa
wannan ce ranar. Ko ka san duk yinin yau ban
NAJNOOR 20
SADAUKARWA-1
yi bakin ciki ko daya ba? Ko fa bata min rai a
ka yi ba ya damuna, saboda farin cikin. gobe
kamar yanzu an gama tabbatar da neman
aurenmu... Ka ga kuwa dole farin ciki da
nishadi su mamaye komai nawa, tunda hakan
ya zamo cikin tanade-tanadena".
Kalamanta sun sake sanyaya masa rai,
koda ya ke tun ma lokacin da suka hadu da ita
ta zo bikin Kawarta wanda angon ya kasance
abokinsa, bai taba yin hira da ita ko da ta wucin
gadi ce ba tare da ta fitar da kalamai masu
sanyaya zuciya daga bakinsa ba. har hakan na
sanya shi tambayar, wai dama haka soyayya ta
ke ka samu mai sonka da gaskiya?
Kasancewarsa bai taba tsayuwa da kowdecL
mace da sunan soyayya ba. sai akan Rufa'atu.
wadda har ake cewa sun dace da juna matuka,
wai har kama suke da juna!
Tabbas ya yarda ya amince suna kama da
juna, wanda daga șhi har itan suka dauki hakan
a matsayin, maganar nan da Hausawa kan fada,
tun kafin zuwan mutum Allah Ya halicci matar
da ta dace da shi, kuma ya yi ittifakin
NAJNOOR 21
SADAUKARWA-1
tabbatuwar dacewar su a matsayin ma'aurata
tunda har ga shi dacewar tasu ta sa suna diban
kamanni da juna.
"Hellow! Bros kana tare da ni kuwa?"
Ta katse shirun da ya gilma a tsakaninsu.
Ya sauke numfashi kafin ya cе.
"Ina tare da ke mana".
Ta ce, "To lafiya na ji ka yi shiru?"
Ya ce, "Lafiya lau, dadin kalamanki ne
suka katse duk jijiyoyin samar da sautin
magana da ke jikina"
Ta yi dariva sosai. ta ce.
"Wallahi ba ka da dama Bros... Dan
Allah. kai wane irin yanayi ka samu kanka a
ciki?"
Ya cc. "Au kina tunanin za a 'samu
bambancin yanayi tsakanina. da ke? Ai duk
halin da kika tsinci kanki a ciki haka ni ma na
kasance, wata Kila za a samu bambanci ke
6acin rai da damuwa ne kawai ba ki yi ba, ni
kuwa yau ko gurin aiki ban je ba, hasalima
daga cikin gida sai dfakina, ko waya yau ban
NAJNOOR 22
SADAUKARWA-1
amsa ba, dan ma kar na samu wani abu da zai
yanke farin cikina. Kin san me ke damuna?"
Da sauri ta ce masa.
"Sai ka fada".
Ya ce, "Wallahi fargaba na ke, anya
Abbanki zai ba ni aurenki?"
Ta ce, "Ni ma wallahi da fargabar na.
yini, amma ba ta wannan ba, domin na san
Daddy ya amince da kai dari bisa dari, tunda
har ya bari idan ka zo na ke tsayawa da kai.
Amma me ya sa kake fargabar hakan?"
Ya cc, "Wai ina ganin nisan da ke
tsakanin Katsina da Bauchi, sai na ke ganin
kamar ba zai amince na kawo ki nan ba".
Ta ce, "Wallahi ko daya, domin shi ma
da farko ya jinjina nisan, amma sai ya ce yana
ganin dalilin haduwarmu ne ya sa ya amince
har na je Bauchin bikin Aisha, ka san tun da na
ke rayuwata Daddy bai taba barina na tsallake
Katsina ba bare har na kwana uwa duniya
kamar garin Bauchi".
NAJNOOR 23
SADAUKARWA-1
Ya 'ce, "Da wannan dan wannan, to
amma ke me ye dalilin kasancewarki cikin
fargaba?"
Ta ce, "Wallahi ban sani ba, ni dai na
wayi gari cikin yanayin farin ciki da nishadi,
amma kadan-kadan sai na ji gabana na faduwa,
da farko na dauka ko labarin wani mummunan
al'amari ne zai riske ni, to amma har kawo
yanzu da ban ji komai ba na fidda wannan
hasashen, sai na dauki hakan a matsayin dan za
a zo neman aurena ne, ka san abin ya zo ga
manya".
Ta Karashe magana cikin dariya, shi ma
dariyar ya ke, ya ce.
"Lallai kam manya! Me kika tanadar min
a goben?"
Ta ce, "Wai dan Allah da gaske kake da
kai za a zo Katsinan?"
Ya ce, "Y a wuce wai".
Та се, "Ai ni na dauka da wasa kake
domin abu ne da ba mun saba gani a nan ba a
zo neman aure da ango"
Ya yi dariya yana fadin.
1a
NAJNOOR 24
SADAUKARWA-/
"Ai ko da babu sha'anin nisa ni han
dauki hakan abin kunya ba, to me ye ma a cikin
ido ban da tsawurya?"
Tа ce, "Mhm, lallai kam".
Ya ce. "Dan Allah da gaske, me kika
tanadar min gobe?"
Та се, "Тo, tunda za ka zo ai sai ka bari
kawai ka gani, amm ni a gidan su Zubaida
Shchu zan zauna, ka ga ke nan a can za ka tarar
da ni".
Ya yi dariya yana fadin.
"Sarkin kunva ke nan. wato dan kada ki
gaida su Abba shi yasa za ki gudu ko? To duk
wayon amarya sai an sha manta. idan kina
tunanin wannan mafita ce, to hanya ce mara
bilewa, dan komai wayonki sai kin'gaishe da su
Abba".
Idanunta a waje tamkar tana a gabansa. ta
сC.
"Dan Allah rufa min asiri idan ba so kake
a karasa ce min mara kunya ba, yanzu ma ya ya
lafiyar. Giwa bare ta yi hauka? Cewa fa ake na
NAJNOOR 25
SADAUKARWA-1
cika tsaurin ido akan kawai ina amsa wayarka a
gaban kowa.
Rannan Ummi har cewa ta yi, wai ta
kosa a daura auren saboda ta lura kafin auren
sai ya kasance bana duban kowa da gashi... Dan
Allah Bros wane irin so ne na ke maka haka?
Anya kuwa ban fi ka zurmawa a cikin kogin
Kaunar junanmu ba?"
Ya ce. "Kan ki kika sani, kin san gwano
bai san warin-jikinsa ba sai na wani. don haka
babu mamaki dan kin yi wannan hasashen. Ni
dai abin da na sani ina vi miki matsananciyar
Kaunar da ba ta misaltuwa.
Kwanciyar hankalina da cikar burina ba
zstu wuce Allah ya mallaka min ke a matsayin
uwar dakina na tabbata a lokacin za ki fahimci
na fi kowa Kamarki.
Duk ranar då a ka ce na rasa ki kuwa. to
al'amari ne na Ubangiji amma na yi rashin
hazikar macen da duk namijin da ya yi sa'ar
samunta a matsayin uwar 'ya'ya ya haye, wata
Kil daga lokacin zan iya samun kaina cikin
kuncin rayuwa mara gushewa...
NAJNOOR 26
Cikin sanyin jiki ta ce.
SADAUKARWA-1
"Dan Allah ka daina fadar haka, insha
Allah mu rabon juna ne na har abada..."
"One minute remaining
Na'urar sadarwar ta sanar masa, wanda
shi bai ma san sun dauki lokaci mai tsayi haka
ba, domin ba kananan kudi ba ne a cikin wayar.
"Please sweet darling kudina sun kare,
sai na ce mu kwana lafiya".
Та се, "A'a bari na kira ka"
Ya ce, "A'a, sai dai mun iso goben"
Daidai lokacin ta ji dif alamar kudin sun
kare ko na flashing.
A hankali ya sauke wayar daga dodon
kunnensa zuwa gefensa. Ya maida kansa akan
filo idanunsa a lumshe yana jin kansa a wani
yanayi wanda ba shi misaltuwa. Sannu a
hankali ya soma tunano ranar da suka hadu da
Rufa'atu, ta zo garin Bauchi bikin kawarta
Aisha, tunda ya ke bai ta6a ganin wata 'ya
mace ya ji yana sonta farad daya ba sai akan
Rufa'atu.
NAJNOOR 27
1
a
1
R
R
SADAUKARWA-1
Cikin tsoro da rashin sabo ya gabatar da
kansa a gare ta, yayin