ki tsiri
haukan banza wai ke me kishi alhalin da baki damu da shi ba
baki taya shi ksihin kanki ba ta hanyar killace kanki haka
baki damu da kishin saba ta hanayar kyautata msa ta yadda
ba zai ga wata ya kyasa ba balle ya tafi nwman mata ba sai
kin ji zai karo wata ki shiga giggika dan tsabar kyashi da
bakin ciki dan wannan bakin ciki ne da kyashi ba kishi ba.
Don haka dan Allah yaran nan ku riki mazajenku da
kyau. Yayi murmushi yace kufa mata ku kuke haukan ku
Allah ya baku girma da daukakar da mu maza ba'a bamu ita ba, ko ya kace Abban yara? Malam ya na fada yana dariya 59
LUBABAН
ya kalli su Auwal da fahad yace sai wani takama kuke kuna
huhhura hanci ba kusan mu maza duk bayin mata bane ba
ama fa bayi masu matsayi tunda matan sune gatan mu a
rayuwa, kinga su mata suna gida a kwance mu fita muyi
noma muyi kwadago mu nemo mu kawo musu sai kuma
abinda sukaso zamuyi musu, kunga ai mun zama bayinsu
Fahad yai dariya yace malamai kuma suma zasu dinga mana
yai dariya yace bakun san girikin ma ai'adace ta bashi ba
addini ba sai dai al'adace mai girma tunda matan annabawa
sunyi amma ai ca akayi muciyar dashi mu shayar da su kuma
mu tufatar da su kunga duk abinda mukayi su mukewa bauta
sai dai kuma bayie masu matsayi tunda in munyo bautar dole
a lallashemu a kade masa kura, to in ba haka ba mu
shagwabe, gobe mu warke muki fita gaba daya falon aka sa
dariya.
Dan haka dan Allah mu kiyaye mu tsare kawunan mu
mu ringa dora rayuwar mu bisa ta farkin Ubangiji wato fadar
Allah da manzansa kamar yadda Allah ya shirya wa
muminan bayi kyakyawar rayuwa a cikin fadar sa Allah
(SWA). In kuka duba SURATUL NISA'I ZA KUGA
SURACE DA AKA SAUKAR DA ITA A GARIN
MADINA (MADANNIYA) TANA DA AYOYI DAR!
DA SABAʼIN DA SHIDA WACCE TAYI MAGANA
AKAN HAR KO KIN TSARA RAYUWAR DAN
ADAM KO INCE JAMA'A DA KUMA ALAKOKIN
DA SUKE TSAKANIN MUSULMAI A KAN KAN SU
WATO A TSAKANIN MUMUNAN BAYI KO KUMA
TSKANIN SU DA WATA AL'UMMAR.
Dan Allah mu kasance masu kiyayewa ga dukkan
a'amuran mu mu cire buri da sankai da san duniya gami
da son zuciya ita kuma sumayyar in sha Allahu za'aje
gidan iyayenta ko da da daddare ne a dawo da ita saboda
ba'a dacc a cc anyi fushi an rabu da su ba shi aure ba'a
60
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
masa haka tunda shima yana da rai, dan haka ba'a san
gagawar,mutuwar sa daga karshe kuma Abban yara na
gode kwarai da gaske Allah ya barmu tare, kai Fahad kayi
godiya an fa bamu 'ya sukutum wato Khadija in badda
gudun surutun jama'a ai da gobe harku za'a hada a daura
suren jibi mu tafi da 'yarmu ko) tunda kun kwace
Humaira nan ma dariya aka saka
Daga nan Auwal ya nis ayace malam nifa tun jiya na
saketa saki uku saboda catayi in ina kaunar Allah in
saketa daban sake ta bane tace, wai ina an haifeni da jini
kuma ina daraja iyayen na wa in saketa shine na saketan
dan in nuna mata cewa ni dan halak ne.
"Dama ka saketan amma kayi shiru tun farkon, cewar
mama. Malam yace aisha-aisha amma abin baiyi kyau ba
Abba kuwa shiru yayi ya kasa magana sai salati kawai da
yakeyi su Hajiya ne ma da ma da kuma kishiyar Hajiyar
suka dauki salatin mata farat Fahad yai yace Allah yasa
hakan shine yafi alkhari yayin da ya kawar da jimamin
gaba daya akace amin.
Daga nan malam ya ce ai, shi ke nan Auwalu kayiwa
kanka tunda ba a daurawa namijin da ya saki matarsa
aure, har sai tayi idda Dan haka musulunci ya koyar da
mu cikin sauri yace wallahi saki daya na mata. Dan kar'a
dawo da ita na ce uku ne kuma wallahi a tambayeta ta
kadarma tana gurinta, in haka ne kuwa na dawo da ita
gaba daya aka sa sariya yayin da shi kuma kunya duk ta
rufeshi cikin sauri ya tashi ya fice.
Dama ashe karya yakeyi? Cewar abba kai yaran
yanzu sai a barsu ai garama da ka masa haka malam
tunda ya dawo da ita sai aje a gaya musu in sunga dama su
dawo da ita.
61
LUBABАН
Da gari ya waye aka dauara auren Humaira da Auwal
su Fahad kuma aka musu baiko. Da yamma suka hada 'yar kwarya kwayar walima da daddare aka kai amarya
gidan ta tun yan ma akaje aka gayawa iayayen su
Sumayya cewar an janye sakin da akawa yar su amma
basu dawo da ita ba.
D
lokacin da aka kai amarya ba wata gayya akayi ta A
azo a gani ba daga humairar sai Khadija, Shafa'atu
sai kakanninta da kuma su Hajiya sai wasu
kawayenta su uku sai kuma yara irin su Maryam da
sauransu kafin karfe goman dare gida ya kaye daga
Humaira sai Khadija da Sháfa'atu. Tuni Humaira ta ware
suka kama hira suna cikin hirar ne suka Fahad da Auwal
da kuma wani dan Uwan su Auwal din mai suna Sadisu
amma ana kirasa Sadi shina ya biyo su ne saboda shafa,
saboda tunda ya ganta ya mutu a kanta a nan suka hadu
aka sha hira sai wajen sha dayan dare suka musu sallama
suka tafi Fahad ya dauki Khadija da marya Shafa'atu da
wasu yara su biyu 'yan uwan Sadin ne suka shiga motar
Sadin suna tafe suna hira har suka isa gida kowa cikin
farin ciki.
A washe gari su malam suka shirya suka koma gida
da direban su shi kuwa Fahad yace sai ya kara kwana biyu
nan ma shafa tace sai ta kara sa tafi tare kullum suna
gidan amare hakIka yadda su Auwal suke tafiyar da
junansu ba karamin burge Fahad suke yi ba.Suma bayan
kwama biyun suka koma zamfara, dukansu cike da farin
ciki da annashuwa yana isa zamfara ya hada kayansa ya
nufi abuja gurin aikinshi. 62
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
Amma sam Şumayya taki ta dawo dakinta wai ita
bazata zauna da Humaira ba da ya ji haka yace ta sha
zamanta babu lalle babu dole bayan sati biyu suka dauko
'ya'yan su rayuwa ta dawo sabuwa.
Akwai wani lokaci suna zaune suna hira Auwal
rungume da Humaira yace, Humaira gaskiya rashin ki
kusa dan ba karamin wahala na shaba, kuma rashin ki
kusa dani ya karamin sonki matuka a cikin zuciyata
kinsan kuwa Allah ne ya kiyayeni da yanzu na zama
rakakken mazinaci wallahi a duk sanda sha'awar ki ta
bijiro min sai in ga kamar inje in nemi mata kawai kona
dace in sami kamrki amm me? Sai sam in kasa saboda
tsannin imani." "hakika ka kyautata wa kanka wai sai
yaushe zaka dawo da Sumayya ne, ya saketa ya danja
baya yace da waike me yasa sai ana maganar kirki ki tsiro
mana da shirme dan Allah in ba so kike mu fataba ki bar
magana tunda aka je suka kI su dawo da ita ai ko sati
bakiyi ba a gidan nan na sake aika mata da takardar saki."
"wato kana nufin kayiwa Allah wayo kenan kace ka dawo
da ita saboda a maka aure, sai da ka auri matar ka saketa,
ato ai dai da zuciya Allah yake amfani, bada fadar
mutumba.
Amma wallahi yaya apple nake sonsciso to yanzu
yaya za'ayi ke nan dan yanzu dare yayi tayisdariya tace
dama shi bawa har yana da lokacin kansarkaimanta abinda
malam yace ba yace ku maza bayin mbane. Atorkada ka
kawo apple yau kaga tsiya, dan kuwa yai baskadal hutuа
gidan nan "wane irin hutu kike nufi kinsan shiuhutun kala
kala ne, ato zaka sani ne? ta fada tana dariya cikin shuri ya
zari doguwar rigar baccinshi yace a'a inamagáta zama
bari ina fita in nemo apple, duk inda yake, a'a ai ni sai
ince ranace ba dareba. 63
LUBABAН
BAYAN WATA SHIDA
a zagayo waccee ta ke cike da tarishin soyayyar T
Fahad da Khadija Sadi da Shafa'atu sai aka shiga
hada hadar daurin auren su da biki, baki daya
hakika bikin ya yi armashi yadda ya kamataya tabbas sai
yanzu fahad yasan yai aure, Khadija matarshi ta farko
kuwa aure ya gagara sai yawon wofi jeki gidan kawa fita
makota daga karshe ma sai yaji labari ta gudo kano dan
shirya film, a inda ta sami nata daukakar, dan kuwa kowa
ya santa.
Tabbas soyayyar Fahad da Khadija ta kayatar kuma
sun dace da juna watan ta uku a zamfara ya dauke
Matarshi sai abuja shafa kuwa dama ita tuni tayiwa
zamfara bye-bye dan kuwa tana garin Kano a binta.
Tazama yar Kano bayan shekara daya kowacceta
haife abinta, Khadija 'ya mace ta haifa shafa kuwa namiji.
Allah ya raya musu yaya yansu Sumayya kuwa sai addu'a
dan har yanzu ko mashin shini babu. Da alama dai
rayuwar 'yan matanci za'a kuma. A karasa tsufa haka.
To muhuta lafiya masu karatu bissalam al'hamdu
lillah. Allah yasa ya zamana anyi amfani da abinda
murubuciyar take san ganarwa Allah kuma yasa mu mata
mu gane cewa tabbas duk wanda yace namiji ubane zai
mutu imaraya tofa jahilar kalma ce mara tushe. In ma
banda abin kunya maza bayin mune sai fa yadda muka yi
sdasusamafa in miunt hada da hakuri, ladabi da biyayya,
kara,i karamci, kunya, kishin kai, kare hakkin da ya hau
kanmu, nuna soyayya ga maza jenmu. Yarku, Kanwarku,
yayarku, Kawarku Antinku LUBABAN
(Mrs Ado Dauda.) 64
1.- So Shu'umi 1-2-3
2- Ilham 1-2-3
3- Wanda Ya Daka Ta Bado 1-2
4- Malika 1-2-3
5- Yaya Ke Nan 1-2-3
6- Zargi
7- Sila
1-2-3
1-2
8- Wanda Yace Namiji Uba Ne... 1-2
Designed & Printed by. Lubabah Publishers
Phone 665532 Kanb.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels