ina sonki so na
gaskiya ba kuwa zan iya rabiuwa da ke ba. dan ki koma ga
wani. shi ramace yai kawai babu mama ma matarsace ta
ke bata masa rai dan da ya sami to gari da tuni ya manta
dake, ke kanki ki kalle ni a lokain da ina tare da Khadija
ba duk na rame ba aboda fargabar tunnarta ba? to
yanzufa kiduba kiga irin kibar da nayi saboda ına tare da
masoyiyata ke kina tunanin rana tsaka zan iya hakuri
dake.
Danine na rabu da ke ina ganin mutuwa ma zanyi ba
rama ba, ko kuwa in koma dan tsince tsincen bola, na
ababbta daga ke harshi baku gama fuskantar meye so ba,
dan haka banga abinda za rabani da ke ba sai dainana
auran maza biyu to in kuwa ba haka ba kima gaya masa
tun wuri ya hakura, dan rabuwa ta dake abin ba zaiyi kyau
ba.
Duk maganganun da yake yi babu ala min annuri a
fuskarsa ya daure fuskar nan tamau shi a dole da gaske
yake ita kuwa in badda faduwar gaba babu-abinda takeyi,
hakIka ta tabbatar wa kanta akwai sauran magana a gaba
to amman anya kuwa zata iya zama da kishiya can wata
zuciyar tacc ató ki dai tuna da 'yaʻyanki da tarbiyyarsu, ki
kuma tuna da illar raba 'ya 'ya in badda dole uwarmu
daya ubanmu daya ai yafi uwarınu daya uba kowa da
nashi, ta saki 'yar karamar ajiyar zuciyar a dai dai lokacin
da ya tsayar da motarsa a wani dan lungun dake dab da
layin gidan nasu
Da ganan ta kara nunfasawa ta dago kanta fuskarta
da alamun tambayar dalilin da yasa ya tsayar da motar
tashi a nan, ya dubeta ido cikin ido ya ce wallahi humaira
bazan daga ba da ga nan har sai kin tabbatarmin cewa, wa
13
LUBABАН
zaki aura ni ko tsohon mijinki kai ni sai kinyimin
alkawarin zaki aureni ma tukun na in matsa daga nan.
Humaira wallahi ba kiji yadda wutar kaunarki ta ke dada
ruruwa a dan wannan lokacinba, ta daga ido ta kalleshi
haklka babu alamun karya ko yaudara a kwayar idonshi.
tabbas sonta yakeyi to meye abinyi dole ya rude, don
kuwa za a iya kwatantashi da wanda yaga samu ya kuma
ga rashi.
Da ganan ta nisa a hankali tace dashi, yaya fahad,
kariga kasan ni kaina ina sanka, so wanda babu algus a
cikinshi to amma yaya bazan iya yi maka alkawari ba,
danshi alkawari a harkar aure gangancine, dan kuwa
nagani saboda sai kaga kai kana taka Allah yana tashi.
Kayi hakuri yaya mu karasa gida in sha Allah ni matar
kace, kada kasa zargi a al'amuran ka. HakIka kaunarka ta
zama jinin jikina, yaya fahad kar kaji komai, ina sanka,
san kuwa ba zai taba gushewa daga gareni ba, ya juyo a
hankali ya dafa hannunta cikin sauri ya cire hannunsa, ya
na ambaton innalillahi wa inna ilaihiraji'un, hakan dayi.
abin tsoro ya bata saboda tunda suke dashi bai taba kai
harınunsa kanta ba, tabbas tasan ba halinsa bane yau ma
tsananin ruda nine ya haifar masa da hakan, ya kifa kansa
akan sitiyarin motar gabanshi ya ringa faduwa cikin
karkarwar baki yace, dan Allah Humaira kada ki zargeni
da laifin da ba nawa ba ni ba ma abocin taба 'уа macen da
ba maharrainata bace. Dan haka ki dauki hakan a kuskure
bari mu karasa gidan.
Da shigar su kewayen hajiyar, sai suka tarad Fahad
da malama a ciki, ga Hajiya da Shafa'atu a gefe, tabbas
irin kallan da saka watso musu tabbas babu tantama
Shafa'atu ta labarta musu komai. Hakan bai kara tabbata a
ransa ba har sai da yaji malam na tambayarsa cewa ina
14
WANDA YACE NAMIJI UBA.NE
bakon? Turus sukayi dan kuwa ko karasa shiga ciki ba
suyi ba, balle ta kaisu ga gaisawa ga malam din amma ya
tambayesu labarin bakon nan take suka durkushe a gurin
suna gaida malam din, gama amsawarsa ke da wuya
yakara tambayar inda suka bar bakon. A nutse Fahad ya
sanar shi cewa yana gidanshi.
"Dan me ka baroshi a can mu dama da muke shirye
shiryen maida ita tunda Allah ya kawo na gidan ba shi
kenan ba sai kawai a hadasu su koma Hajiya tace, a'a
malam bakayi haka ba kamata yai ace an rakata daga nan
koni da yaran ne sai mu bisu domin mutabbatar da
gaskiyar lamari, sannan muma muga gidan kaga sai
zumunci ya kullu a tsakani Allah ya hadamu ke nan,
kuma yarinya ta hada mu," "to ba jinayi kunce yaran nan
yau zai tafi Abuja ba, E amma ai ba wani dadewa zaiyi
ba." "Ni wallahi Hajiya sai in fasa ma tafiyar, in Allah
yaso ko korata ce ayi, kada in tafi in bar su, yazo ya
rudeta ta koma hannunsa ni kuma gaskiya Hajiya ina
sonta sosai." "ya Rasulillahi ashe daman kai baka da
kunya amma ban sani ba? A gaban nawa kake furta
wannan maganar?. Lallai 'ya'yan yanzu baku da kunya
wato kalle kallen banzan ne, na wasan indiya ko turawa
shine yake bude muku ido, har kuna ikirarin kanku ya
waye ina wayewar take, to kaga tashi kaba mutane guri
duk abinda muka shirya ma nemeka kuma da kake wa
kanka fatan a koreka kada Allah yasa katafi din in an
xoreka ai naga da uwar da zaka zauna da matar." Ya
sunkuyar da kai kasa bashi da alamar tashi ta daka masa
tsawa tace wai ba magana nake maka ba?, amma ka tsaya
kana kallona
Daga nan ya mike a hankali ya kalli Humaira ya
sadda kansa kasa, ya mike tamkar wanda kwai ya fashewa
15
LUBABАН
a ciki, ko kuwa kamar wanda аkа umata da tafiya a
tsakiyar tasąssun kwalabe har yakai dab da waje malam ya
kirashi yace dashi, zo ka zauna abinda nake so dakai shine
kaje ka shirya kayan tafiyarka, in sha allahu daga yarinyar
har bakon, ba zan barsu su tafi ba. zan kyalesu harka
dawo shirya yin maganar a kuma shirya maganar ta fiya kanon ina fatan ka fahimta. Yace, "to" yayin da ya kara
kallan Humaira ido cikin ido ta dan kawar da kanta gefe guda bisa alamun kallan da yake mata babu tantama yana
matukar son ganinta to amma bazata iya binshi ba.
"da yaushe zaka dawo ne?" Hajiya ta tambayarshi
yace "in sha Allahu a gobe ko jibi zan dawo, da ikon bi'iznillah." Tace" Allah ya kaimu, Allah kuma ya dawo
da kai lafiya, ga yadda ta lura da iri kallan da yake wa
Humaira tabbas tasan yana san ganinta ne ya yinda ta
kuma kanta yake a kasa Hajiya ta dubi Humaira tace,
humaita jeki can dakin wajen soro ki dauko min wani
kwano yana nan dazu da yara suka kaimin zuciyarta daya
ta tashi ta nufi soron amma shi malam da Fahad sun gane
daf da daki Fahad ya tsaya yana jiran karasowarta.
Tana isowa yace, zo mu karasa daga waje babu wani
kwano da zaki mika mata ni ta turowa ke wallahi dadina
da manya saurin fahimta suna karasawa ya ce toni zani in
shirya a nan zan bar Auwal din inna dawo duk an gama
komai dan Allah ki rike amana kada yazo ya cika ki da dadin zance. Ya kura mata ido na dan lokaci sanna ya
lumshe ido yace Humaira kirikI Fahad a mijinki na biyu
ko kya fuskanci sauyin rayuwa. Ni zan tafi kada in makarа
sai gobe ko jibin nan dai sukayi sallama ya tafi.
Data koma cikin gidan bata komo gunda su Hajıya
suke ba ta wuce dakinsu Shafa'atu ma taje ta sa meta suka
16
A
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
Zauna suna ta maida magana shafa tana cewa Humaira
gaskiya nidai a rike amanar yaya na dan wallahi ya mutu a
kank,i sallah kuwa sai hadata sukayi a wannan lokacin
wat azahar da la'asar.
Dare nayi sallar insha'I gami da addu'ar kawai
Humaira tayi tabi lafiyar katifa acewarta bacci zatayi ama
ina in badda tunane-tunane daya sha mata gaba babu
abinda takeyi.
Da asuba ta tashi tayi salla gami da nafilfilun amma
har gari ya waye tangaran bata kara runtsawaba in badda
tunane tunane babi/abinda takeyi, ita kanta ta kasa gane a
tabbabcin me take abin haushi Fahad ya bar Auwal a
gidanshi balle ta kara ganin shi domin hakIka yanzu kuma
hankalinta yayi gida kuma tabbas tana bukatar labarinsu
in badda kartayi rashin kunya hakika da ta tanbaya ta nufi
can kafin yaya Fahad din ya dawo. Tayi tunanin rubuta
masa wasika a baye ba tare da an sanar da shi ba, tunda
duk gidan sunasan ta auri yayan nasu nan dai ta kasance
cikin tunane tunane amma babu yadda za'ayi ka shiga
daki ba kace bacci ta keyi ba.
Da Shafa'atu taga har wajan karfe goma amma ba ta
fito ba sai ta nufi dakin tana tashinta tace, haba Humaira
ai ya kamara ace kin tashi kinyi wanka haka, ko kyaji
dadin jikinki, ga abinci can ma yana jiranki, dan kuwa ina
jin ko yau ko gonbe zaku tafi kanon, na dai ji su Hajiya
sunata maganar su da mutan gidan kuma a jiya da
daddaren ashe malam yaje ya sami Auwalu sun sha hira,
shine malam yake cewa da Auwalun dama ke kanki
tausayinku yakeji.
Dama wallahi Humaira na gaya miki yayannan naki
yana sonki bawai dan yayi aureba shikenan. Abinda da
yawa mutanan mu suke dauka kenan sai su manta da cewa
17
LUBABАН
aure kaddarane in Allah yayi za'ayi dole sai ka kara koda
kuwa kuna hadiye junanku kudawo da kanku saboda so.
Amma duk irin son da kukewa junanku da zarar ance
namiji zai kara aure, shikenan ku baya sonkune. Ansan
dole da kishi kina da abinki ke kadai ke kike momarsa son
ranki yau kuma ace an kawo wata, komai sai dai kubiyu.
To amma inkajure na dan lokacine kuma wallahi duk
matar da aka wulakanta saboda wata to halintane ya
jawomata. Yanzu Humaira kamar ke, kinga zamuiya cewa
halinkine yajawo miki. Tunda mijinki yana sonki badan
yana kinkiba ya aurowata. Amma kika bi kika dagula
komai. harma kina da bakin kiran namiji da cewa DUK
WANDA YACE NAMIJI UBANE YA MUTU
MARAYA.
Dan Allah ke da kika massa hakan me zai kirawoki?
Da ace muma mata za'a radamana sunayen hakIka da sai
ince muma yadace damu saboda sha'aninmu yana da
wahala. Kuma duk namijin da ya aje mace fiye da ukuma
agida ko biyu to kuwa a jinjinamasa. Wallahi in zaka
shekara kana bautawa mace, dare daya ka 6atamata to
kuwa zata manta da alherin baya, tamace baka taba yimata
komaiba. Wallahi da zakiji irin maganganun da Khadija
take fada akan yayanmu zakisha mamaki. Kai har fada
take wai ita gara ta bar gidanshi dama wai bai cika
namijiba. To dan Allah mace kinafaműga da kazanta
tayaya za'ayi namiji ya ganki ya kyasa har yaji dadin
kusantarki.
Dan Allah kibar maganar nan, tun ba yau ba naке
jinta ni kinsanıma abinda yake damuna' "a'a sai kin fada
walllahi tunanin yadda zanyi da mutanan nan biyu nakeyi
wato yaya Fahad da yaya Auwal. Shafa'atu tayi dariya
tace, kaga 'yar gata mai yaya da yaya ato ai hausaawa na
18
A
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
cewa so, sone, amma son kai yafi to nidai a nawa shawara
gaskiya ki auri yaya Fahad. shifa ba shi da mata yaya
Auwal aishi yana da dankwalar matarshi a gida. Kuma ki
tuna saboda ita ki ka rabu da mijinki na kuma tabbata
labari ya isheta to inakuma da kin koma, kinga itace uwar
gidafa ba keba. Duk kuwa inda zaman aure yake ai da in
zama amarya gara inzama uwar gida."
Dama nasan yayanki zaki tayani za6a, to ammnashi
zaman gidan miji ina ruwansa da amrya ko uwar gida
kowa ya auri namiji ai sabo ya aura, ke dai ki tayani
addu'ar Allah ya zabamin miji na gari, "yaya na ke nan
dan wallahi nagarine sosai,.
Duk dare malam yana zuwa gurin Auwal da kanshi,
kasancewar Auwal ya fahimci akwai soyayya stakanin
Fahad da Humaira, kuma ya tabbata iyaye sun sani, don
haka bai taba nunąwa cewa yana son ganin humairaba
kuma har kofar gidan nasu ya ke zuwa wani lokacin
kasancewar ana kawo masa abinci akoda yaushe, sai yabi
yaron da yake kawomasa har yaga gidan wasa-wasa a yau
akalla kwananşa'uku amma Fahad bai dawoba.
Da ya kwana shida shiru sai hankalinsa ya fara tashi
ya shiga tunanin gida yana tunanin yadda zasu dauki
al'amarin, ya sami malam har masallaci ya snar da shi,
cewa shi in za'a yadda a bashi Humaira su koma Kano, in
Allah ya so sai a hadasu da wani yaga no gidan nasu, a
duk lokacin da Fahad din ya dawo sai su taho gaba daya
saboda yana tunanin yanda zai sami gida, dan kuwa babu
tan tama yasan cikin tashin hankali suke da farko malam
yaki amincewa, da shi cewar su tafi da Humairar, sai ya
ce in har yana ganin ya kagara ya tafi. To yaje suma suna
nan tafe ina sha allahu amma yanzu baza su iya barinsu su
tafi su kadai ba. A nan dai Auwal ya shiga magiya da 'yar
19
LUBABАН
murya wanda daga karshe malam din ya amince da
sharadin za'a hadasu da wasu matan su tafi suka kuma
shirya cewa a washegaarin ranar zasu tafi wata a ranar
Litini ke nan.
Dan suna tsammanın tunda har karshen sati ya wuce
to kuwa da kyarne in har zai dawo da aka sanar da
Humaira a za hiri ba taji dadin hakan ba dan tana ganin
tabbas in har ta amincewa yaya Auwal suka tafi ba, to
kuwa batayiwa Fahad adalci ba, kuma tabbas hakan yana
nufin ta gama wulakantashi ke nan to ama me ba zata iya
yin musuba, sai dai ta najin su tafi tare in Allah yaso ita
zata zauna har sai su Fahad din sunzo tukunna sa taho
tare.
Dan haka tun a daren suka fara kukan rabuwa suna
masu harhada kayansu a wannan dare misalin karfe tara
na dare wani yaro ya shigo gida har dakin su humaira
kasan cewar yasan gidan da yake makotan su ne, yaje
yace wai ana kisarn Humaira a kofar gida in ji wannan
bakon."
Da farko hankalinta yayi masifar tashi dan tunda
Fahad ya dawo da ita gida basu kara hada ido da shi ba
asalima ko sako baya shiga tsakaninsu ta yi mamakin
wannan kira na tsakiyar dare to shin in taje ma me zatace
dashi ta shi daya ta tsinci kanta a matsananciyar jin
kunyar shi shi me zata ce da shi in sun gamu wacce hira
zata amince su raja'a a kanta ba tare da sun jefa kansu a
wani hali na nada banba, tana cikin tunanin sakon ya kara
risakarta cewar ana magana a kofar gida, ta mike rai cikin
kunci ta nufi kofar gidan duk jikinta a rufe tamkar waccе
taci karo da saban saurayi ganin farko.
Da zuwanta ta hangeshi can daga dan nesa kadan da
kofar gidan. Takarasa a hankali tana zuwa ta durkusa har
20
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
cewa so, sone, amma son kai yafi to nidai a nawa shawara
gaskiya ki auri yaya Fahad. shifa ba shi da mata yaya
Auwal aishi yana da dankwalar matarshi a gida. Kuma ki
tuna saboda ita ki ka rabu da mijinki na kuma tabbata
labari ya isheta to inakuma da kin koma, kinga itace uwar
gidafa ba keba. Duk kuwa inda zaman aure yake ai da in
zama amarya gara inzama uwar gida."
Dama nasan yayanki zaki tayani zaba, to amımashi
zaman gidan miji ina ruwansa da amrya ko uwar gida
kowa ya auri namiji ai sabo ya aura, ke dai ki tayani
addu'ar Allah ya zaßamin miji na gari, "yaya na ke nan
dan wallahi nagarine sosai,.
Duk dare malam yana zuwa gurin Auwal da kanshi,
kasancewar Auwal ya fahimci akwai soyayya stakanin
Fahad da Humaira, kuma ya tabbata iyaye sun sani, don
haka bai taba nunąwa cewa yana son ganin humairaba
kuma har kofar gidan nasu ya ke zuwa wani lokacin
kasancewar ana kawo masa abinci akoda yaushe, sai yabi
yaron da yake kawomasa har yaga gidan wasa-wasa a yau
akalla kwanansa'uku amma Fahad bai dawoba.
Da ya kwana shida shiru sai hankalinsa ya fara tashi
ya shiga tunanin gida yana tunanin yadda zasu dauki
al'amarin, ya sami malam har masallaci ya snar da shi,
cewa shi in za'a yadda a bashi Humaira su koma Kano, in
Allah ya so sai a hadasu da wani yaga no gidan nasu, a
duk lokacin da Fahad din ya dawo sai su taho gaba daya
saboda yana tunanin yanda zai sami gida, dan kuwa babu
tan tama yasan cikin tashin hankali suke da farko malam yaki amincewa, da shi cewar su tafi da Humairar, sai ya
ce in har yana ganin ya kagara ya tafi. To yaje suma suna
nan tafe ina sha allahu amma yanzu baza su iya barinsu su tafi su kadai ba. A nan dai Auwal ya shiga magiya da 'yar 19
LUBABАН
murya wanda daga karshe malam din ya amince da
sharadin za'a hadasu da wasu matan su tafi suka kuma
shirya cewa a washegaarin ranar zasu tafi wata a ranar
Litini ke nan.
Dan suna tsammanın tunda har karshen sati ya wuce
to kuwa da kyarne in har zai dawo da aka sanar da
Humaira a za hiri ba taji dadin hakan ba dan tana ganin
tabbas in har ta amincewa yaya Auwal suka tafi ba, to
kuwa batayiwa Fahad adalci ba, kuma tabbas hakan yana
nufin ta gama wulakantashi ke nan to ama me ba zata iya
yin musuba, sai dai ta najin su tafi tare in Allah yaso ita
zata zauna har sai su Fahad din sunzo tukunna sa taho
tare.
Dan haka tun a daren suka fara kukan rabuwa suna
masu harhada kayansu .a wannan dare misalin karfe tara
na dare wani yaro ya shigo gida har dakin su humaira
kasan cewar yasan gidan da yake makotan su ne, yaje
yace wai ana kisarn Humaira a kofar gida in ji wannan
bakon."
Da farko hankalinta yayi masifar tashi dan tunda
Fahad ya dawo da ita gida basu kara hada ido da shi ba
asalima ko sako baya shiga tsakaninsu ta yi mamakin
wannan kira na tsakiyar dare to shin in taje ma me zatace
dashi ta shi daya ta tsinci kanta a matsananciyar jin
kunyar shi shi me zata ce da shi in sun gamu wacce hira
zata amince su raja'a a kanta ba tare da sun jefa kansu a
wani hali na nada banba, tana cikin tunanin sakon ya kara
risakarta cewar ana magana a kofar gida, ta mike rai cikin
kunci ta nufi kofar gidan duk jikinta a rufe tamkar wacсe
taci karo da saban saurayi ganin farko.
Da zuwanta ta hangeshi can daga dan nesa kadan da
kofar gidan. Takarasa a hankali tana zuwa ta durkusa har
20
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
kasa tagai da shi. Humaira! Ya ambata cikin lallausar
murya da sanyar da ita, hakika Auwal ya shiryawa daren
yau kuma hakika bai manta da irin kiran da yake zauta
humairaba, dan haka gaba daya ya nemi tafiya da
tunaninta, ta dago kai a hankali ta kalleshi. Ido cikin ido
wanda shi kuma ya shiga sarrafata da kwayar idonshi ta
hanyar kashe mata su da kuma shigar dasu ciki ciki wanda
nan take, kwado ya bukaci komawa gida dan asali wato
tsundum ta koma ruwa da tsananin kaunar tsohon mijinta,
sai dai me in ta tuno da matsanancin cin mutuncin da ta yi
masa, sai taji tsananin kunyarsa ta kamata, tabbas ta
amince da fadar bahaushe wato dana sani keyace wacce
tun farko bata addu'ar neman tsari ga ita. Dan kuwa tun
da take addu'a bata taba cewa Allah ya rabamu da aikin
dana saniba.
Dan kuwa ko aurensu ya dawo dai- dai tofa aduk
sanda suke tare zata zamto mai tuna abinda ya shiga
tsakaninsu a baya. Ta danyi murmushi ta kara sunkuyar
da kanta kasa, yayi murmushi yace Humaira kenan wata
saban gani menene na sunkuyar da kai haka sai kace wata
bakuwa ko dayake ni na ware sakar, ni kuma zan dasa
sabuwa, har in kawata sakar da adon zaren da yafi waccen
sakar ta farko amma sai da hadin kan ulun, abin nufi in
bai kulleba ko ya cukurkude.
Dafarko Humaira na kirakine dan in baki hakuri
dangane da wautar da nayi abaya. Humaira nasan
lefinane, domin shi kishi yakan fitar damutum daga cikin
hayyacinshi humairta ban yadda da haka ba sai a yanzu
da ya faru dani wallahi Humaira yan kwanakin nan da
nayi sam bana iya runtsawa saboda ina can kima nan sai in
yi ta kawo zargį iri-iri ke ni tunanina da zai gi na har sai
da ya karfafa min cewa anya kuwa handsome bai da
21
LUBABАН
woba? Sai in riga ganin kamar ya dawo rufata kawai akayi
kukaje kuka tare a wani gidan. Wallahi Humaira kishi
bala'ine dan ina ganin da gida daya muke kwana da
handsome ina ganin da tuni na tashi cikin dare na datse
kanshi na huta.
Dan ni a duk lokacin da na rufe idona kuwa babu
abinda nake gani face ke da shi sosai nake ganinku a idan
zuciyata, cewa ga kunan kir-kiri kuna meking love a
junanku dariyar ku, kuwa da sauran nishin ku tsaba na ke
jinsu radau akunnena. A gaskiya kishi bala'ine. Babu
ainda yafi kishi zafi a rayuwa. Allah ma da kanshi ba
yasan ksihi ya ki duba kiga duk saßon da kikayi in har
kika tuba zai gafarta miki amma banda shirka wato
hadashi da wani ko ince hada bautarshi da wani abu na
daban a gaskiya gashi kumata. Matan ma na malam
bahaushe.
a
Dan ba kowane yarene süke yin aure bibbiyu ba sai
ku sai namiji ya hada mata hudu a gida daya alhalin ko
musulince Allah yace "in har kana da hali to kayiwa ko
wacce mace gidan ta da ban." KakIka hakan ma yafi
zaman lafiya, saboda in ba ganin juna ba kukayi ba
kukayi sai ma wata ta manta da rayuwar wata.
Duk da cewa in har mace tana da tsananin kishi to fa
ko an rabasu zargi shi zai haifar da rashi zaman lafiya. То
amma fa hakuri shine ko mai a rayuwa tabbas mata kuna
da hakuri sai muce a gaisheku dole ku kiramu da duk
wanda yace namiji ubane ya mutu maraya. To amma da
za'ayi mana adalci a fahimci wani abu da munso, wato dai
shi aure kaddarace. Kuma a dinga cewa muma fa maazan
ba mu kadai bane muke da laifi.
Dama kowa ya sani karin aure a dayan biyu ya ke.
Wato walau matarace take yi maka abinda ba kaso wato
22
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
yin kazanta, ko rashin iya abinci, ko rashin iya kwanciya,
ko kuma ya zanmto matar fitsararriyace ta kuma rai naka
dole ka auro wata ko ka sami rangwame a zaman ta kewar
taki tunda abine da babu wanda yasan karshen zaman sa a
rayuwa face abinda Allah ya shiryawa bawansa.
Da aure kuma na KAddara. Duk da cewa ko wanne
aure dama kAddarace wato zaka iya samun mace suna
zaman lafiya da mijinta, babu wani makusa a tare da ita
wato abin nufi a nan shine zakiga kiri-kiri ka ajje mace
mai ladabi da biyyaya, ga kunya ga sanin ya kamata ga
haihuwa ga iya girki ga iya kwanciyar, kai ga duk wani
abu da kake muradin samu ga 'ya mace. Amma sai Allah
ya jarabaka da karin aure, badan komaiba sai dan Allah ya
gwada imaninku ku duka, daga kai har matar ta dauro ma
wata daukaka ce Allah zai baka sai ya dora maka nauyi
dan yaga zaka iya adalci a rayuwarka.
Duk da cewar Allah yasan ko zaka iya ko bazaka
iyaba to amma adalci na Allah sai ka ga yana jarabtarka ta
hanyoyi da dama domin ya kara sai ta maka
kwakwalwarka dan haka humira ki dauki auren nan a
kaddara dan Allah karki guje nı wallahi Humaira ni mai kaunar ki ne, ke kanki ai kinsan aure kaddarane ko? Ga yadda ya kwantar da muryarsa ga gami da langabar da kaina sai hakan ya dan so ya bata tausayi da dariya baki daya.
Dole duk girman namiji, ace da shi jinjiri a gaban matarshi. Musamman in ya hadu da matar da tayi sauka akan kissa har ta haddace ta dawo tana fassara, a
fannoninta. Tabbas kwantan kwacin aure nane da yaya Auwal. A zaman mu babu wanda zai ga wata mace yace zai karo a rayuwarsa, in dai ba kaddarar ba, gaskiya nayi wauta matuka saboda da yaya Auwal yi auren niyya ne
23
LUBABАН
kamata yayi ya tsaya ya zabo ya darje tunda dga matan
nan kamar jamfa a jos.
Da yake abin kaddarane sai gashi Allah ya hada shi
da tsohuwa babu kyan babu kyaun halin ai ni wallahi ni
Allah ya keso dan ya dubi zamana da Auwal babu cuta
babu cutarwa, shi da sa baini hadashi da matar da zata je
ra'ayinsaba ya bashi damar kara auren ya kuma barni a
kujerar mikina babu abinda ya shafeni tabbas ko yanzu na
amince so na shine a gaba da son matar shi tunda gashi
suna taren, amma rashina shi ya fitar dashi daga
hayyacinshi, a karo na biyu ke nan da ta karayin dana
sanin shin meyasa ta yiwa Allah butulci tabbas ta yadda
bawai kiyayya bace ta ke sa wa namiji ya karo aure son
mijinta ya kara shiga ranta fiye da son kowa to mene
abinyi shin ya zatayi da Fahad dan hakika bata da
muradin komai tace ta komawa mijinta.
Da yaji shirun yai yawa sai yayi gyaran murya ya
ce," Humaira ya kikayi shiru ko bazaki komamin ba ne?
dan Allah Humaira kiyi min rai wallahi ina sönki so'na
hakIka ba wai na wasaba yayin idanuwansa suka cicciko
da kwalla idanunta suka fara kai kawo da hawaye. ya
shiga magana cikin karkarwar murya tana mai bashi
hakuri shi ma ganin laifinsa ne yakeyi shi ya jawo rabu ita
tana gani lefin tane, sun jima suna neman gafara ga junan
su sai misalin shadaya da rabu suka rabi da nufin in gari
yà waye tin misalin karfe tara na safe zasu dauki hanya
kuma suna komawa a washe gari za'a maida musu
aurensu. Dan gaba dayansu sun bala'in kagauta da suka
kasance sun kebe a junansu.
Daga nan sukayi sallama cikin farin CıKі da
annashuwa hakika Auwal yau bacci harda minshari dan
kuwa yau lahiya lau inji bakatsine tunda sun shirya da
24
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
sarauniyar mata. Itama ta shiga cikin gidan cike da farin
ciki da annashuwa da kin sune kawai a tude, haklka ta
tabbata su hajiya sun zaci ta dawo da yake