Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
ya zabawa Humaira miji to fa yasan babu tantama dansa zai bawa. Nan take ya yanke shawarar barin gidan Fahad ya koma hotel da zama kafin kwana biyun ta cika, saboda yana ganin haka shi zai fi yi masa dadi fiye da kasan cewa tare da Fahad tabbas hakan zai iya haifar da mugun aika aika, dan kuwa babu tantama kebewar su su biyu zai iya ja masa bakar zuciyar daka bashi damar kudura bakar niyya a zuciyarsa. A nana take ya nisa a hankali ya ce "to malam naji na zan tafi wani guri kafin lokacin tafiyar tazo in sha Allahu jibin da sassafe zan zo, dan bazan so bata maku lokaci ba ya mike tsaye ba tare da ya saurari abinda mala zai ceba malam yac ina zaka ne duk dai inda zaka ka zauna ai ba kamar gidan nan ba, in banda abina Auwalu kaima ai ka zama dan gudan, e" ai wani dan aiki ne ya kawo ni gari kuma ban gama ba shine nake san zuwa ina yi shi tunda na kara samun 38 WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3 lokaci yace, "lalai yai daidai Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a kasancewar zaman da yayi ya dan sayi kana nan kaya saboda yasa mu na canji kasancewar da ga shi sai kayan jikin sa ya zo sa'a daya da mota shi ya taho, hakan ya masa dadi. Amma ita Humaira kwayar idanshi kadai ta kalla ta san ranshi a bace yake tabbas, bata manta da yanayin bacin ran yayan ta Auwalba wanda babu tan tama ta tabbatarwa kanta cewa hukuncin da malam ya bayar, ya bata masa rai hakika ita kanta tayi mamakin yadda farat daya malam ya yadda da tsarin Fahad harma ya kara basu damar futa tare alhalin yana sane da cewa ba wasu mutanan a zo a gani ta sani ba a garin, to amma dubara daya da ta ware itace, ta ce da Shafa'atu ta shirya ta rakata dama karyace su dauki yarinyar da batasan kanta ba a matsayin 'yar rakiya. A lokacin da Auwal ya fice waje sam humira daurewa tayi ta dake ta tashi ta bi bayansa yayin da babu wani bata lokaci Fahad ma ya bita su Hajiya kuwa binsu sukayi da kallo hakIka warnan rashin kunyar har ta baci tana fdita ta kira Auwal, cikin hanzari ya waigo idanshi ya kada yayi jajawur, tace yaya Auwal ina zaka koma? A hankáli ya murmusa saboda shi kadai yasan abinda ya hango a kwayar idonta abune da ya saba da ganinshi, a duklokaciń da tsananin kaunar juna ta bijiro mata hakIka in banda shamakin da sharia ta gindaya musu to kuwa da babu tantama sai ya rungume a barshi, taci gabá da kada idanuwa tamkar mai shirin jan hankalin masoyi da ya juya mata baya tace "yaya Auwal ni na san babu wani aiki da kake dashi kuma nasan dalilin da yasa kake san barin gidan yaya Fahad to amma yaya Auwal ni a shawarata da hakuri ka karayi kwannanka nawa a garin nan, yaya sai kwana biyun ne zai daga maka hankali dan gane da futar mu da ya ya Fahad kuwa, kana jifa yace kada mu fita mu biyu to meye zai daga maka hankalin ka har kayi shawarar barin gidan yaya Fahad 39 LUBABАН alhalin kana sane da cewa ba kuwa ka sani a garin nan ba wallahi kuwa? Abinda sukaji an amsa musu daga bayansu ke nana, juyawar nan da sukayi sai suka ga yaya Fahad tsaye ya zube gaba dayan hannayen sa a aljihun wandanshi ya dubi Auwal ya sakar masa murmushin mugunta yace "to kai banda abinka Auwal da kabar gidan ba gara ka ce kaima zaka ba, in Allah yaso sai mu tafi tare, dan tani babu matsala, ma iya samin direba in Allah ya so mu duka ukun mu zauna a baya musata a tsakiya ko ya ka kace Humaira? Kunya mai tasanani ta rufe Humaira, me zaisa Fahad ya nemi maida kansa fitsararrene, ta yaya za'ai yace su sata a tsakiya sai kace wata karuwa, ko tsokanace, ai bai dace yayi ta wannan sigar ba, dan ita zai jawowa, ba mamaki ya haddasawa yaya Auwal mumunan zato a kaina, zai iya tunanin ko haka nake ko kuwa shi Fahad dinne haka dama 6oye min halinsa yayi yanzu ne yake kokarin baiyanar da halayyar tasa a fili. A hankali, ta sakar masa sanyayyiyar hararar da shi ya dauka kallone irin na burgewa ga wanda kaké kauna sannan ta sha kunun da ya kara mata kwar jini da kyallin goshi tace "yaya Fahad me kuma kake nufi da kusani a tsakiiya sai kace wata mai zaman kanta marar kishin kanta, "shi kansa sai yaji jikinsa yayi sanyi dan bai dace yace mata haka ba, bai sake ce da ita komai ba yace in kun gama kya shigo mu shirya mu tafi, "yayin da ya komawarsa cikin gida. A cikin kwan biyun nan sai da Humaira ta rasa, abinda yake mata dadi wato abinda yafi da munta shine Auwal yabar gidan Fahad, amma fa bai bar kofar gidan malam ba. Dan kuwa nan yake wuni haka shima fahd a nan yake wuni duk subi su ishe ta, kowa yana kokarin nunawa dayan yafi karfi a gunta. A safiyar da zasu tafi tunda duku-duku Humaira da Shafa'atu suka kama shiri kan tara tayi kowa ya gama shirinsa tsab sun sun gama shirya yin tafiyar a mota biyu, 49 A WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3 motar fah daka sami direban da zai jata, sai aka hada iyayen a ciki wato da hajya da daya da ga cikin kishiyoyinta da ake kiran ta saima sai kuma matan din da malama da'u wani aminin malam din ne mota gurin Auwal kuuwa sai ya kasance Auwal din ne yake jan motar, Fahad na gefensa. A bayan motar kuma Shafa'atu ce da uwar gayyar tafiyar wato Humaira sun iso garin Kano da misalin karfe daya na rana kai tsaye gidan abba ya nufa da su Humaira tace da Auwal yaya Auwal shin ba zamu fara zuwa can gidan alhajin ba in Allah ya sosai kaje ka sanar da Abban wallahi ni yanzu kunyar mu hada ido da shi, nake saboda nasan na jefashi a cikin wani hali na kaka nakayi yayi dariya gami da sosa keya yace, Humaira ke nan meye abin jin kun ya ashe haryanzi baki yadda da kaddara ba. Ai gidan mu yanzu 'yan hayane a ciki, Abba ne ya ce a zuba 'yan haya, saboda bayan san saka wani dan uwa a dannewa marayu hakkinsu daga karshe a zao a na rigima nakwa gaya miki Hajiya rabi tabar gidan abba ai tun da mama ta koma ita kuma tace gidan zatabari. Ko da yake bamu sami ishashshen lokacin da zamu tattauna ba. A lokacin da Auwal ya taka birki a daidai katafaren gidan da ya daurewa Fahad kai wanda sam duk da Humaira ta bashi labarin dukiyar babanta amma bai kai kudin haka ba, har ya shiga zargin anya kuwa ba 'yar gidan dantata bace, ta boye masa. To hakika in ma ba 'yar gidan bace to hakIka mahaifinta shine ke taka masa baya, to a daidai wannan lokacin ne wata katsetsiyar yarinya ta bayyana da har ta ja kafuwar idan Fahad a kanta hakika yarinyar ta hade karshen hadewa don ta linka humaita kyan diri nesa ba nasaba kai harma kyan fuska da ken fatar jiki ta fita yayin da gabansa ya fara gaduwa, shin menene dalilin da ya jawo idansa ya kafe kaf kan yarinyar. Ita kanta idanta kasa yake lokacin da ta dago kai ta kalli motar da ta ke kokarin tsayawa a kofar gidan sai kuwa ta hada ido da yayanta 41 LUBABАН Auwal, ba wata bace face Khadija ta daka uban tsalle cikin doki da nuna maitar farin cikinta a fili ta nufi yayanta. A wannan lokacin bata ga Humaira ba dan haka ihun da murnar akan Auwal ya kare tace oh yaya ka tafi ka bar kowa cikin tashin hankali wallahi yaya ni dai kusan ince nafi kowa tashin hankali, saboda ni na rasa yayuna har biyu yaya zo mu shiga dama abba bai fita ba ta sakeshi ta koma cikin gida a guje duk abin nan cikin yan mintuna akayisu yayin da idan Fahad na kan ta. Bashi da tabbacin yana kibta idon ko baya kibtawa ita kuwa Humaira mamakin girman Khadija da yadda makerin 'yan mata ya kerata, ta kara kyau haka shi ya hanata motsi balle magana har Khadija ta shige cikin gida batasan da Humaira a motar ba kai bana jin ta kula da wani ma balle tasan ko su nawa ne a motar. Abba da mama gaba daya suka fito cikin doki da murnar dawowar dansu, yayin da alokacin su Humaira duk sun fito ana shirin fitar da kayan da ke motar su shiga dan hato ta su malamma sun fito, to fa a nan kowa yayi curus duk sukayi cirko, ciko. Shin mamaki suke ko kuwa ma tsorone ya kamasu habibu da kadija da Maryam sukayo waje gaba daya arbar da idansu yayi da Humaíra shi ya mantar musu da murnar da wowar Auwal sukayi kanta gaba daya. Cikin murna da zumudi. Gaba dayan su sukayi kasa, suna nan kahdija ta fara kukan murna Humaira ta rukesu gaba daya amma idonta na kan iyayenta. A gaskiya kallo daya za kuwa wadannan dattawa ka tabbatarwa kanka cewa lallai suna ciki da son juna abin ya burge Humaira tunda take a rayuwar ta bata taba ganin iyayenta tsaye kusa da kusa ba fuskar kowa cikin annuri ba sai yau hakan ya kawata ta ya kuma burgeta ya haddasa mata farin ciki da bata taba tsammaninsa a rayuwarta ba sanyayyin hawaye suka kwaranyo mata, fuskarta fal farin ciki da doki. Ta saki kannenata ta nufi iyayenta gaba daya ta rungumosu jikin ta ta saki wani tsadaddun kuka mai kamanni 42 a WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3 biyu saurarar kukan kaďai zakayi kasan kukane na farin ciki ha kukan bakin ciki ba gaba daya aka duru cikin gidan cike da farin ciki. A nanne Fahad ya fara rena kansa su malam kuwa abin ya basu tausayi hakika gidan yana cike da al'umma masu Kaunar junansu anan Fahad ya tabbatarwa kansa tabbas Humaira 'yar gatace gaba da baya. A babban falo aka saukar da bakin nanfa aka shiga hidima da bakI duk wani abu da ya shafi dangin kaiwa a baka kamar su lemon ruwa da abinci an kawowa bakin sai da kowa ya nutsa sannan aka gaisa Auwal ya dan gabatar da su Fahad da iyayensa ga su abba, sannan aka shiga cin abinci cikin farin ciki da annashuwa sai da suka kammala da komai sanna aka nutsu guri guda, aka kara gaisawa. A hankali Auwal ya labarta wa iyayensa yadda suka hadu da Humaira har kawo wannan lokacin da suka gamu. Hajiya ma ta bada labarin rayuwar Humaira, tunda ta je garin zamfara ta sauka a hannunta har kawo zuwa yanzu itama Humaira ta bada labarin dalilin gudunta tace a daren da zata gudu ne tun da farkon dare ta ji abba da Hajiya rabi suna tattaunawa akan tunda nakI yaya Auwal to daga na cika iddadta da sati daya za'a dauran aure da Nasir ni kuwa ba sanshi nake ba. A daren na kwana cikin tashin hankalida kun cin zuciya shiyasa da asubar fari na gudu Abinda yasama ban gaya wa su Hajiya haka ba dan karsu zargi auren dole za'amin na gudu su dawodani gida koda yake dama da niyyar in gudun, amma gidan Alhaji Kabir naso in koma in kama sana'ata a can. Kuma in cigaba da kuratuna don har na kwashi kudina da sarkokina da nufin sai da sarkokin in hada da kudin in hada jari. A hankalin abba ya nisa na dan wani lokuta yace a gaskiya Humaira kin bani mamaki banta 6a zatan a wayonki da kuma hankalinki har zaki iya gudar mu ba, ko da a wuta mukace zamu jefa ki balle auren dole. In banda abinki 43 LUBABАН Humaira aikin dai fi kowa sanin ra'ayina tunda ni da kai na, da kuma bakina na gaya miki cewa bazan taba yi miki auren doleba saboda ni nasan abinda auren dole yake haifarwa. Ya juya ya kalli su malam ya shiga shi musu albarka bisa rike 'yarsa da sukayi bisa amana yaci gaba da cewa, kuma baka sani ba, malam, wallahi mata da yawa kishi yana wahalar da su hakIka na tabbata kamar yadda ta fada yanzu, auren Nasir ne ya sata guduwa karya take kishin ne yafi rinjayarta. Aure da aka daura na Auwal shi yafi tada mata hankali kuma baka san ba malam wallahi duk abin da mahaifin yaran nan yayi dan ya kare martabata, da darajata ne gami da kare shi kansa ran nawa kishi yar Humairar ko kuma in ce matar Auwalun ta yanzu mun taba hada neman auren, babar ita Humaira, duk da cewa a lokacin ma ba san mu takeyi ba ita tafi son mahaifin shi wannan yaron Auwalu, to kasancwar ni an bani aurenta, shine yake tajin haushina yana ganin ya fini, kudi da komai amma aka bani ita kuma yana masifar kaunarta fiye da yan da ake jikinshi, kamar yadda nima na sota. A lokacin da aka bani ita na aura, ni bansan uban yaron nan ba sosai shima Alhaji. ubalen dan dai mai kudI ne kowa ya sanshi saı ya ja Alhaji safiyanun sosai a jikinshi suka bada kai, saboda su ake ware ha'aba ba, ni da aka bani aurenta sai sukejin haushina amma duk da haka ban san Alhaji safiyanu sosai ba ban ma san yana kule da ni ba kamar yadda nasan shi mahaifin Sumayyadin. A hankali ya dubi mama yayi murmushi yace in baki mantaba akwai lokacin da na taba shigowa duk jikina a kurkurje lokacin ina jan mashin harkike tambaya ta meya sameni nace dake faduwa nayi a babur, to ba wani faduwa, face dukan 'yan iskan gari zauna gari banza. wato hayarsu yayi suka tareni suka ringa dukana har sai da nayi suman karya sannan suka rabu da ni a'nan naji suna anbaton sunan wanda ya turosun shi ya sama na san shine, amma alokacin 44 WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3 da yake baki damu da ni ba baki lura da tabbatarwa kannki gaskiyar abinda alhalin ga hoton yatsun hannun wani gabjejen yaro kwance a kumatuna har gurin yayi jajir ko kuma kin gane kika basar dani. Abinda ya sa har ya umarci 'yayan iskan suka lillisani kuwa shine wato kirana yayi har ofishinshi ya bani kudl dubu dari biyar yace in ja jari na karba nayi godiya ina fita naje.na kaisu na boye, ko banki ban kai ba har tsawon wata biyu yasa aka kara kirana yace dani in sake ki yana son ya aura, na tambayeshi dalilin da yasa ya baro wannan umarnin sai buda baki yayi yace, saboda ka sayarmin soyayyar da kake mata har tsabar kudi dubu dari biyar. Nan take na murmusa nace in haka ne ciniki ya tashi kudin ka kuwa zan kawo maka. A lokacin dariyar mugunta yai saboda yana tunanin ya shirya min gadar kara na kuma rubua dan a halin da ake ciki babu yadda za'ayi a hada da kudi hanzuzurutun nairori dabu dari biyar ya kasance har sun kai wata biyu ba'ka 6aba zai yi wuya. A nan ya jawo durowa, ya miko min wata takarda fal da namnobi a jiki kasancewar dama duk kudin dari biyar-biyar ne yace in har ka kawo kudin da suke dauke da wadan nan labobi to mata ta zama taka amma in har lamba daya ta kuskure a cikin kudin tofa mata ta zama tawa kuma wallahi daga yau ko kwana daya ba zata kuma yi ba a gidan ka in kuma ka tabatama to kuwa zan shigar dakai kara, akan ka tabamin matata. A lokacin kallon wawa nayi masa in banda sakarai shashasha wa zai aika ta haka? ama ba yanin nasa na kashe ne suka tabbatarmin mahaukaci ne takardar da ya bani ce ta nisar dani da tuanin cewa lallai mahaukaci da wayo ne. tabbas, ba takardar kadai ya tanada ba. To sai dai kuskurena na sa daya annan mahaukacima yayi wayo balle mai hankali. 45 LUBABАН A nan take naje na dauko masa kudin shi, dubu dari biyar cif babu canjin ko daya. Amma kan inwuce sai da na gaiyato 'yan sanda masu farafaran kaya suka zauna a kofar ofis din (office) tamkar masu jiranshi suma nan kuwa suna gudun kota kwanane da ya gama dubasu tas cikin ishashshu mintina arba'in da biyar kasancewar, a kwai masu tayashi su biyu, sai nan da nan waushi ya kamashi takaici ya lullube masa annurin fuskarshi ya shiga zage-zage yana fadin ko ta tsiya sai na sake ta ya aura in kuwa ba haka ba sai dai muyi auren mu biyu dan babu abinda zai hana shi kusantar ta. Anan take na sake masa suna wazirin mahaukata, sarkin jahilai da naga abin yana nema ya wuce gona da iri, sai na kirawo yansanda nan sukayi gaba da shi, a washe gari suka shigar da mu kotu har aka gama shari'ar babu wanda ya sani sai BaBa wato kakan Humaira (Alhaji kabir da yake BaBа yake ce masa) aka bashi daurin shekara uku, sakamakon rashin kunyar da yayiwa Alkali Akaci tarasa miliyan daya sakamakon bata mana lokaci da yayi da kuma mummunan abinda ya so ya shirya ya karbi kan sa daga zaman gidan yari akan dubu dari uku, A nan ne fa ya kullaceni ya sha alwashin sai ya tozartani har ya ke kokarin shirya yadda za'ayi ya mallake kamfanonina da dukiya ta ya kuma haddasa silar karasa rayuwata a gidan yari, har yana fadin in shi baiyi zaman gidan yari ba ni nati lokain da suka shiga siyasa sai suka yaudari mahaifin Auwalk ya shiga, saboda ta hanyar sace kawai za suci galabata, har auren da suka tursasa tsakanin 'yar sa da Auwal din duk don saboda nine saboda yarin yar tana son Auwalun da dadewa tana ganin shi tace sai shi, to shi ne akace da shi ko ya hada aure ko kuma a bakacin rai na. A gaskiya malam babu abinda zan ce da mahaifin yaron nan saboda ya sadaukar da nasa ran amma in aka duba gaba daya sai a daganta abin a kaddara haka kuma Allah yaso. 46 WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3 da yake baki damu da ni ba baki lura da tabbatarwa kannki gaskiyar abinda alhalin ga hoton yatsun hannun wani gabjejen yaro kwance a kumatuna har gurin yayi jajir ko kuma kin gane kika basar dani. Abinda ya sa har ya umarci 'yayan iskan suka lillisani kuwa shine wato kirana yayi har ofishinshi ya bani kudI dubu dari biyar yace in ja jari na karba nayi godiya ina fita naje.na kaisu na boye, ko banki ban kai ba har tsawon wata biyu yasa aka kara kirana yace dani in sake ki yana son ya aura, na tambayeshi dalilin da yasa ya baro wannan umarnin sai buda baki yayi yace, saboda ka sayarmin soyayyar da kake mata har tsabar kudi dubu dari biyar. Nan take na murmusa nace in haka ne ciniki ya tashi kudin ka kuwa zan kawo maka. A lokacin dariyar mugunta yai saboda yana tunanin ya shirya min gadar kara na kuma rubua dan a halin da ake ciki babu yadda za'ayi a hada da kudi hanzuzurutun nairori dabu dari biyar ya kasance har sun kai wata biyu ba'ka 6aba zai yi wuya. A nan ya jawo durowa, ya miko min wata takarda fal da namnobi a jiki kasancewar dama duk kudin dari biyar-biyar ne yace in har ka kawo kudin da suke dauke da wadan nan labobi to mata ta zama taka amma in har lamba daya ta kuskure a cikin kudin tofa mata ta zama tawa kuma wallahi daga yau ko kwana daya ba zata kuma yi ba a gidan ka in kuma ka tabatama to kuwa zan shigar dakai kara, akan ka tabamin matata. A lokacin kallon wawa nayi masa in banda sakarai shashasha wa zai aika ta haka? ama ba yanin nasa na kashe ne suka tabbatarmin mahaukaci ne takardar da ya bani ce ta nisar dani da tuanin cewa lallai mahaukaci da wayo ne. tabbas, ba takardar kadai ya tanada ba. To sai dai kuskurena na sa daya annan mahaukacima yayi wayo balle mai hankali. 45 LUBABAН A nan take naje na dauko masa kudin shi, dubu dari biyar cif babu canjin ko daya. Amma kan inwuce sai da na gaiyato 'yan sanda masu farafaran kaya suka zauna a kofar ofis din (office) tamkar masu jiranshi suma nan kuwa suna gudun kota kwanane da ya gama dubasu tas cikin ishashshu mintina arba'in da biyar kasancewar, a kwai masu tayashi su biyu, sai nan da nan waushi ya kamashi takaici ya lullube masa annurin fuskarshi ya shiga zage-zage yana fadin ko ta tsiya sai na sake ta ya aura in kuwa ba haka ba sai dai muyi auren mu biyu dan babu abinda zai hana shi kusantar ta. Anan take na sake masa suna wazirin mahaukata, sarkin jahilai da naga abin yana nema ya wuce gona da iri, sai na kirawo yansanda nan sukayi gaba da shi, a washe gari suka shigar da mu kotu har aka gama shari'ar babu wanda ya sani sai BaBa wato kakan Humaira (Alhaji kabir da yake BaBa yake ce masa) aka bashi daurin shekara uku, sakamakon rashin kunyar da yayiwa Alkali Akaci tarasa miliyan daya sakamakon bata mana lokaci da yayi da kuma mummunan abinda ya so ya shirya ya karbi kan sa daga zaman gidan yari akan dubu dari uku, A nan ne fa ya kullaceni ya sha alwashin sai ya tozartani har ya ke kokarin shirya yadda za'ayi ya mallake kamfanonina da dukiya ta ya kuma haddasa silar karasa rayuwata a gidan yari, har yana fadin in shi baiyi zaman gidan yari ba ni nati lokain da suka shiga siyasa sai suka yaudari mahaifin Auwalk ya shiga, saboda ta hanyar sace kawai za suci galabata, har auren da suka tursasa tsakanin 'yar sa da Auwal din duk don saboda nine saboda yarin yar tana son Auwalun da dadewa tana ganin shi tace sai shi, to shi ne akace da shi ko ya hada aure ko kuma a bakacin rai na. A gaskiya malam babu abinda zan ce da mahaifin yaron nan saboda ya sadaukar da nasa ran amma in aka duba gaba daya sai a daganta abin a kaddara haka kuma Allah yaso. 46 WANDA YACE NAMIJI UBA NB 3 A gaskiya al'amarin ya ratsa kowa nan take jikin Fahad yayi sanyi hakika babu, tan tama babu wanda Humaira ta dace ta aura face ta koma gidan 'ya'yanta Auwal, sai dai abinda yake damun kansa shine yadda idonshi ya nace akan Khadija to me Nene haka kada fa shu'umin yayi shu'umancinshi nan dai suka zauna suna ta hira Auwal Fahad Humaira, Shafa'atu da kuma Khadija ga ba daya suka koma wani falo suka kafa tasu hirar duk halin da Fahad yake ciki Auwal na lura da shi, da dare yi Abba ya bukaci Auwal da ya koma gidanshi gobe ya dawo, amma sam yaki dan haka shima a nan ya kwana. A washe gari kowa ya tashi cikin farinciki da annashuwa sallar asubashi ma gaba daya akayi jam'I, gidan bayan kammala cin abincin su kowa ya shiga shiriin yin wanka abinda ya daurewa Humaira kai shine dukkan kayayyakinta suna nan dan haka wasu riga da siket blue kala ta saka da kuma nade kanta tas da wata blue lafiya hakika wannan shigar ba karamin kyau tayi mata ba shafama ta cado tata kwalliyar ta fito a lokacin su Fahad suma sun fito Auwal kuwa ko wanka bai yi ba saboda ya gaji da maimaita kayan jikinshi ya ce sai sunje gidan shi, dan dama shi yace kowa ya shiryo suzo su rakashi nashi gidan suna zauna suna ta faman hira sunhada kai a falo, abinda ya so fadarwa humaira gaba dayane, wato yadda taga Fahad ya rage doki a kanta to me ya jawo haka? Ko kuwa dama halinsa ne ya daukaki mace, tana sakin jiki dashi ya wulakanta ta? Тo koma dai manene ita dama ta tsaida shawarar ina ya dace ta dosa. Abba da su malam sun kasance a falo daya suna hirar duniya a nan ne malam yake ce da abba. A gaskiya da muntahi da niyar nemawa Fahad aure a gurinku dan kuwa dangantaka mai tsanani ta shiga takanin wannan yarinya Humaira d ashi Fahad din to amma a gaskiyar lamari mu kanmu yadda muka fuskanci lamarin mun tattara tunin mu 47 LUBABАН guri daya ba tare da son kai ba hakIka babu inda yarin yar nan ta dace ta koma face gidan mijinta na farko wanda bai ma dace ace anja magana da nisa ba kwana uku mukace zamuyi da sansamune sai muce a mida auran 'yar mu muna nan, dan ya ksance iyayenta mata sun raka ta to amma mu bamusan nakui tunanin ba. Abba ya murmusa yace haba malam mai zai gagara nan ita dai ba wani saban miji zata yi ba ku ma neman wani abu zatayiba abinda ya kamata a nan shine a yau da an jima zamufuta gaba dayan muba in ka gamun bar wata sai dai mama saboda yara (kasancewar haka yake kiran maman) ya dago kai ya dubeta yana murmushi, tayi dariya tace to dama in ban zauna ba wa zai zuna, in na biku wa zai kula da gidan dan naga yaran nan ma suna ta shirye shiryen ficewa daga gidan. Abba yayi murmushi yace haka ne to amma ina ganin kafin ace yaran nan sun fice to kuwa a kirawan su a gaya musu abinda aka shirya shi kuma Fahad sai ya dau hakuri rashin aurensa da Humaira ba zai zama sandiyar rugujewar dangantakar mu ba dan kuwa so da kaunar juna gami da kakkarfan zumunci, kamar ma yanzu aka da sa shi Allah ya hada mu da ku kuma yarinyar nan ita ta hada mu sanan ya kara da cewa dama ban taba zuwa zamfara ba to amma a yanzu dalili mai karfi ya taso Allah ya tabbatar da alkhairi ya Kara sada hankulanmu amin. Amma su su Humaira kowa ya shirya ya fito sun hadu sunata hira, a falo, khadija ce ka wai bata cikinsu amma duka yaran gidan suna nan hatta maryam tanan nanne a kusa da Humaira, gani to ke kamar zata kara bace mata Fahad da kansa ya buda baki yake bawa Auwal hakuri yace hakIka mai da auranka da

Chapter 4 of 6