gidan cike yake
da samari bata wani rufeshi ba saboda kowa da lokacin
dawowarsa ga uwa uba shi kansa malam din tunda shima
bashi da taka mai man lokacin shigowar sa gida
kasancewa akoda yaushe ya na masallaci.
Mrs
Alokacin da ya shiga farfajiyar gidan tsintar kanshi yayi
yana mai faduwar gaba sakamakon ganin motar Fahad da
yayi, a farfa jiyar gidan. Tabbas kuma hakIka babu
tantama shine ya dawo hakika daw warsa ba kara min
bajet ta ke neman ruguza masa ba. Yasan halin fahad
sarai, duk abinda yasa a gaba sa yaga Karshensa
hankalinsa yake kwanciya. lokacin da Auwal din ya shiga
gidan alokacin baifi minti goma da dawowa ba, saboda
kai tsaye ya nufo masa gida saboda yasan babu kowa
aga shi sai mai gadi da 'yan aiki dan haka babu wanda
zai tadawa hankalin tunda kowa yasan halin tafiya.
Auwal nan take ya daure fuska ba bu wata walwala a
tare da shi ya shiga buga kofar shi ma haka Fahad din a
kule yake, cike da zargin shin daga ina Auwal yake?
Zuciyarsa ta tsaya kyam a babu tantama daga gurin
Humaira yake, to me ta kaishi, amsar da bashi da ita ke
nan.
A nan suka zauna a falon cike da zargin juna bayan
sun gaisa ne Auwal yake tambayar sa dalilin dade war sa
a Abuja Fahad ya ce, wallahi zuwa nayi na tarad da aiki
gagarumi a gabana wato wata baiwar Allah ce ta zo
haihuwa munfi awa biyar a kanta amma ta kasa haihuwa
har muka gaji muka kaita dakin tiyata da akayi mata ne
25
LUBABАН
aka samu ashe 'yan biyu ne a cikin nata sai dai kansu a
hade yake kuma cikinsu ma a hade haka muka fito mata
dasu kai lallai Allah mai ikone wato Auwal baka san wani
abuba ana fito dasu, su kama kuka gaba daya duk abinda
daya zaiyi sai kaga tare sukeyi shiyasa muke zargin an ya
kuwa ba da kwakwalwa daya suke aiki ba kuma abin
haushi matar ba musulma bace amma hakan bai sa, ta
yadda da Allah ba, dan bata da addini kwata-kwata.
Auwal ya ce e ai kasan shi Allah haka yake, sai ya
ga dama zai shiryar dakai irin wadan nan isaharorin sunfi
faruwa a gurarensu amma hakan bai sa sun fargaba Allah
dai ya kyauta kuma ba ka sani ba Auwal ni kadai nayi
mata wannan tiyatar hakIka na sami yabo ta fannoni da
dama nan take decta asibitin ya bani hutu na sati biyu
amma dan danace masa ina da uzuri na sam bai amince
ba, har raina ya 6aci raina sosai na kwanta da nufin garina
wayewa zan taho wata sai dai in rassa aikin gaba daya.
Allah cikin ikonsa sai gashi an kawo matar a wannan
daren wallahi tausayin yaran naji shi yasa har na zauna na
dan kula dasu na 'yan kwanakin nan in banda hankalina
ya kasu kashi da dama, kuma itama matsalar da na bari a
gida tana da amfani sosai a kaina to kiwa da babu abinda
zai hanani zama da su har sai wantannin da zasuyi a
asibitin ina kuma basu kulawa ta musamman.
Auwal ina ka nufane? na dawo ban samekaba yayi
masa wannan tambayar ne dan ya kara tabbatar da
zarginsa duk da cewar baya raba dayan biyu burinshi daya
kawai yaji amasar da ga bakinsa dai yanayin sa kawai zai
lura da shii ya bawa kansa amsar tambayar sa ta farko
Auwal ya wangale baki gaba daya ya ce, wallahi
matuniyar na kawai ziyara tunda ka tafi sai yau Allah ya
kaini ni kaina nayi mamaki, inajin karfe tara na wannan
26
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
dare tare ta ruskemu da ita amma gashi har sha daya ta
wuce ta shiga farfajiyar cakon karfe goma sha biyu amma
muna tara amma ai kazo a dai dai da ma gobe ake shirya tafiyar mu kano har itan, dan kai an jiraka shiru da malam
yace in ka dawo kaje ka samemu a can amma tunda Allah
ya dawo da kai ai anyi a dade, kaga sai a dauki hanya da
sanyin safiya.
A zahiri da tika-tikan kankara ya samu yayi inasa
zuban ruwan sama da su, hakIka da yafi so da wannan
annurin fuskar da yake nuna masa wanda hakan shi ya
nuna masa firi falo cewar ya shawo kan matar shi, tabbas
da sake an bawa mai kaza kai abinda Fahad ya fada ke
nan a ranshi dan kuwa babu yadda za'ayi ya amince da
wannan shirin nasu tabbas ya zama dole ya tsinkayi
gidansu da Asubashin farko don yayi wa Humaira dirar
ungulu shin me ma Humaira ta ke nufi da shi. A sanda zai
bar garin zamfara ta amınce da kanta cewar babu wani a
gaban ta face shi to yaya za'ayi kuma kan ya dawo ta
nemi dainkewa da tsohon mijinta. Dole yasan abinyi, dan
haka nan take ya daure fuska.
Abinda Auwal ya lura ke nan shima ya maida tasa
fuskar ya dinke ta tsaf da rashin walwala dan haka a nan
suka tsayar da hirar, kowa ya kwanta cike da tunanetunane gami da tsananin kuncin rai su duka in badda juyi
babu abinda sukeyi shi kawai Auwal ji yake kamar ya
kashe Fahad, badan bashi da mafutaba. Dan me zai ringa
nuna son matar shi uwar 'yayan shi a gaban shi, wanda
yake ganin in anbi diddigi ma yanzu haka sakin bai
sakuba, tunda cikin 6acin rai yai sakin Allah kuwa baya
aiki da tunanin marar hankali mutumin da ya shiga baçin
rai ko dede yake da mutumin da baya cikin hayyacin shi
27
LUBABАН
koma dai menene, wannan kuma ya, wuce, sai dai a kori
gaba a kuma shiryawa abinda za'a tarad da shi a goba.
A wayewar ranar lahadi karfe bakwai a kofar dakin
su ta yiwa Fahad abinka da dan gida babu shamaki amma
tabbas duk da haka da ya karasa ya gaida su Hajiya ko
mutan gidan kuwa da ya gamu da shamakin da ya daka tar
dashi har Humairar ta shiya dan kanta, ta fito hakika
bugun kofar ya rudar da su Shafa'atu ce ta taso cikin sauri
ta nufi kofar dan ta bude a zatanta Hajiya ce dan haka
daga irta sai daurin kirji ta leko saboda tuni Humaira ta
shga wanka itama jiranta take tayi ta fito, itama ta shiga
cikin sauri ya kauda kanshi gami da tambayarta ina
Humaira duk da cewar shi maharrraminta ne amma sai da
taji kunya dan tana ganin ta wuce munzalin da zai ganta a
haka.
A hankali cikin nutsuwa tace dashi Humaira tana
wanka ya danja tsaki kadan nuna alamun ba haka yasoba
ba watiu ita tama kagu ta tafin shi ne har ta shga wanka da
wduri, amma yasan abanyi ya dan zura hannayensa ciki
ajjihun sa yace okey in ta fito kice da ita tayi sauri ta tarad
dani a mota ina jiranta.
A yadda Shafa'atu ta lura da fuskarshi tabbas tasan a
matse yake dan haka sai ta shiga bugawa Humaira kofa
tana ce da ita dan allah tayi sauri ya ya Fahad na jiranta a
motarshi, dan ko wanka bai yi ba, dagashi sai rigar bacci.
A gurguje ta gama wankan ta fito dan tasan tabbas,
babu lafiya to yaushe ma ya dawo tambayar da tayiwa
Shafa'atu ke nan shafatace wallahi ni ma ban sani ba na
dai so in tambayeshi, to amma sai naga sam ba fuska, ke
dai kiyi sauri kije ki sameshi kyaji a bakinshi cikin sauri ta
hanzarta ta shiryawa ta ficè ta sameshi a mota, ya buga
uban tagumi gaba daya gwiwoyin hannunsa akan sitiyarin
28
3
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
motar suke idan shi yai jajir kai ka rantse kuka ya sha'ain
ka fahimci yanayinsa ne kadar zai tabbatar maka da cewa
tabbas bai runtsa idanun shi, daren jiya ba, wanda hakan
ne ya hadda sa masa canjin launin kalar idanshi.
A hankali tamkar motsoraiyar da tayiwa masifaffe
Ôarna, ta shiga gaida shi bayan sallamar da ta sakar masa
da 'yar muryarta mai ki dimashi a duk sanda ya jita baiyi
niyyar murmusawa ba amma kawai sai ya tsici kanshi ga
me sakin fuskar da tun jiya take a tsuke tamau, ya rasa
abinda zai kwaçe masa ita yaji dadi a ransa amma a yanzu
tashi daya zinariyar muryar masoyiyar tashi ta gama
mareta tasa acikin yan fakikan da basu taka kara sun
karya ba ya bude kofar motar ya umarceta da ta shiga
ganin yanayin da yake ciki ya hanata musa masa, ta shiga
a hankali ta zauna shi da kansa ya ratso hannunshi ta
gaban ta ya rufo kofar sannan ya dan kalleta na dan lokaci
ya shiga jan motar, ba tare da yace da ita ko ta tafasa
ba.dan kuwa ko gaisawar da ta masa bai amsaba.
A hankali ya ringa jan motar itama batace dashi
komai ba, dan ita a zatanta gidanshi zai nufa da ita gurin
Auwal. Amma sai labari yasha ban bam, da taga yanufi
inda bama ta taba zuwaba tun iya zaman ta a zamfara
balle ta san sunan inda suke nufa daji ya keta da motar
yahau wata 'yar hanya sai da sukayi tafiya mai nisa
sannan ta kasa jurewa ta tambayeshi inda yake shirin yi da
ita.
A hankali ya dago kai ya dan waiga ya kalleta yai
naida ganinshi ga banya yace da ita
na Humaira
LUBABАН
har yanzu tana wasiwasin gun wanda zata tsaya to da naga
kan in dawo har kun shirya tafiya a yau ke da tsohon
mijinki to sai naga abinda ya kyautu damu shine gara in
kaiki a raba mana ke a biyu kowa ya dauki kasan shi mai
tafiya kano ya tafi mai zaman garin zamfara ya zauna ina
ganin hakan zai fiye mana sauki ko ba haka ba?.
A'yadda ya nuna a fuskarsa tabbas babu alamun wasa
hakan kuma bai nemi ruda taba sai da taga ya ratsa hanya
ya keta cikin daji sosai inda sam babu hanya koda da ta
mutum balle keke ko babir, har ta tsalla ja da hanyar mota
to a nanne gabanta ya fara faduwa kaddai ace Fahad baya
cikin hayyacinshi? tabbas da yana cikin hanklinshi to
kuwa da bai ringa tura kan motarshi cikin dajin nan, ba
tare da tunanin zai iya taka abinda zai hadda masa
fashewar tayar motar sa ba, sai da ya-yi tafiya dai dai
iyawarsa sannan ya sami gindin wata katuwar bishiyar
tsamiya ya tsayar da motar a dede lokacin da wani murti
keken maciji ya fito da gudu daga cikin surkukin wasu
ciyayi ya cilla yai gaba a guje kamar yadda ya gani tabbas
yasan itama taga macijin dan haka sai ya dago kai a
hankali ya dunbeta suka hada ido.
A hanka!i ta sunkiyar da kanta yayin da idanunta
suka cika da hawaye ya danyi murmushi karfin hali yace
"Humaira lallai ruwan idan ki zai tsiyaye, tunda Allah ya
hadaki soyayya da mahaukaci, dan wallahi Humaira
nakan zama mahaukaci akan soyayya dan ni bana sa abu a
raina in hakura in barwa wani balle son mace daya da
daya kamar ke, Humaira ina kaunarki, kauna mai tsanani ina sonki so marar musaltuwa na tabbabta a lokacin da
Auwal ya shiga neman auren ki na farko na tabbabta ya
kayar da masu sonki, da dama. To a wanan karon Allah ya
hadashi takara da mayen karfe.
30
3
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
A gaskiya Humaira na riga na dafe milki to kuwa ban
6areni zaiyi wuya ya kamo hannunta ya dora kan kijinshi
duk da yasan haramcin hakan, yace da ita "Humaira ki ji
yadda zuciyata take bugawa kuma bata taba bugawa face
sai da tsananin sonki yadda zuciyata take bugawa da sonki
Humaira haka kuma kwakwalwata take aiki da sunan ki
Humaira rashin ki kusa dani a matsayin matata zai iya jawowar, katsewar amfanina kwata-kwata a daniya ina sonki, so mai tsanani Humaira shin kin taßajin wanda ya
kashe kansa ya kuma mikawa wani ran da hannunshi to in
kuwa har za'a iya haka a doron kasa to kuwa Fahad zai
iya barwa Auwal ke.
A gaskiya Humaira nariga na tanjama nayi nutso mai
tsanani wand na tabbata kamoni sai gwanin iya ruwan
gaske, dan haka bazan iya fita daga kogin soyayyarki ba,
hatta sai da igiyoyin auren ki a hannuna Humaira na riga
na gama shirya mana rayuwar mu ta aure, kai har rayuwar
‘yayan mu dama yadda zamu tafiyar jikokinmu in Allah
ya bamu to Humaira ta yaya za'ayi in iya daukan wannan
littafin ka co kan in mikawa wani, bakya ganin nayi
gangancin wargaza babin rayuwata da kaina? Humaira
bazan iya hakura ina ji ina gani ki guje min zuwa ga
wanda da zai iya wulakantaki kamar yadda ya
wulakantaki a baya ba. ni kuwa Humaira da a
wulakantamin ke gara in sami makiyin da zai
kacalcalamin rigar mutuncina a tsakiyar kasuwa Humaira
ganin kine yasa na tsani kadaita ka tsakanina da duk wata
mace koda kuwa du bata zanyi a asibiti. Humaira gaskiya
bazan iya rabuwa da ke ba da in rabu da ke gara in tunkari
macijin nan da ya fito yanzu ya sassareni in mace ya fimin
dadī da saukin jin radadi akan radadin da zuciyata zata
tsinci kanta yayin da ta rasaki, kunuwana kuma suka jiye
31
LUBABAН
ki ga wani, balle ace har min jin fatihar daurin auren ki ga
idona ya ganemin zaman ki da wani a matsayin masoya
ma aurata, tabbas dole in shiga rudani marar musaltuwa.
Amma Humaira ina son ki tabbatarmin da halin da na
ke ciki a gurin ki, kuma wanne matsayine nawa a
zuciyarki?" "shiru Humaira tayi ta rasa inda zata sa kanta
tabbas gaskiyar Fahad da yace ta kasa tsayar da zuciyarta
guri daya, to ya zatayi Allah ya hadata da masoya biyu
sara kuna a fagen iya soyayya kala man su da iya
soyayyar su yana iya jan ragamar duk wata 'ya mace duk
taurin kanta to yanzu ita me zata ce da shi.
A nanne ya kara juyowa gurinta gaba daya ya ruko
hannunta duka biyun ya zura ya tsunsa a daya daga cikin
hannuwan nata ya ruke su sosai ya matse hannun na dan
lokaci sannan ya lumshe idanshi ya doshi bakinshi da
hannun ya sakar mata dafin dake manne a la66ansa hakan
kuma ya jawo mata shiga wani yanayiın da in bata yi
karya ba zata iya kiransa da bata taba shigar shi ba, in
kuwa ta ta6a shigar to kuwa ta manta iya kanta ta yadda
da cewa Fahad yafi Auwal iya soyayya ta ko wanne
fannni to amma me bata da ta cewa barawo a hannun mata
ya ringa matsarta yana cewa Humaira me kikace ne?
Humaira kinyi shiru kin barni ina ta zuba.
A nutse cikin sanyin murya gami da kaifafa ta, ta
yadda zata doki zuciyar mai sauraro tace dashi yaya
Fahad, amma kana sane da haramcin da muke aika tawa a
yanzu ko? Ina ganin saurin so bazai iya janmu zuwa fadar
azabar Allah ba ko? In kuwa har kana tunanin cewa
shaukl so ba zai iya janmu wajen aikata aikin saboba to
kuwa zai kyautu a ce ka matsa daga kusa da ni, zuwa
mazaunin ka gyara ga abin kuwa ka sakar min hannun
32
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
cikar kyautatuwar imaninmu kuwa mu zamto masu
ambatan istigifari, na dan lokaci.
A gaskiya yaya mu barwa Allah zabi shi yafi, kada
muje mu zabawa kanmu abida zai zo ya dagula
rayuwarmu baki daya sanin kanka ne ina sonka so mai
tsanani, ina kaunarka kauna marar musaltuwa. Ga tsarin
kunya da kawaici irin na 'ya mace bazai iya barina in zai
yane maka irin tsannin san da nake maka ba in har ka
kyaleni in ji da radadin da zuciyata take ciki to kuwa da
sai ince kamin adalci marar musaltuwa ina mamakin kace
ka matsamin kò ka ta kuramin akan in sanar dakai irin san
da nake maka.
A gaskiya bani da kalaman da zan zaiyana maka irin
san da nake maka face in nuna maka a zahiri a kuma
aikace. Hakan kuma na iya sawa in jawo mana azabar
Allah mai tsanani a kanmu yaya kamin adalci a bar
maganar zaifi, zafafa son kaji irin son da na ke maka
saboda in har hankalinka bai tafi da nisa ba to sai in iya
tunasar da kai cewa mu biyu ne a gurin nan, amma muna
da cukon na ukun mu wato shaidan, sai kuma Allah da ya
haliccemu da yake kallonmu.
A nutse ya shiga, shigar da kwayar idansa ciki-ciki a
zahiri kalamta sun rudarshi sun kuma kAra tsananta sonta
a ranshi ya kalleta yayi murmushi yace, lallai kalamanki
sun ceto ki daga shirrin mayanka, kinsan kuwa tafe nake
da zabgegen, takobina mai suna gayawa jini na wuce, to
amma Humaira bazakimin adalci ba a sanar dani irin son
da akemin ko a hanyá mafi saukl ce, wato mudan tsotsa
minti domin in tsotsi zakin zumar son da akemin.
Amma ka bani mamaki yaya meye amfanin tsotsar
minti ga wacce ba muharrramar ka ba, kaje garin ka tsotsi
zaki kaci karo da daci marar musaltuwa shi kansa
33
LUBABАН
ma'adanar mintin me makon kaci karo da sanyi da
ni'i,amtaccen kamshi kaje, kaci karo da tsannin wari, mai
tafe da matsannancin zafin da ka iya kuna matsotar minti
yaya a gaskiya ni nawa mintin, ban tana darwa manemiba
face sai mijin aurena.
Amına baka da laifi yaya, sai naga laifin nawa ne da
har na sakar maka fuskar da har zaka iya tambayata
mintin da zaka tsotsa. Tabbas kuwa in har zamu dore da
haka to kuwa nan gaba zaka tambayi abinda yafin tsotsar
minti a gurina. Dan haka yaya ka duba lokaci, ka gani tára
har da minti hamsin da shida kasan fa a yau aka shirya
za'a mai dani gurin iyayena, wadanda basu bani fuskar
tsotsar minti a kofar gidan su ba, suka kuma nusar dani
aikata hakan a gidan da suka kaini a matsayin matar sunna
ga mai gidan saboda haka ka mai dani inda ka ďauko ni.
Amma duk cikin tsananin 6acin rai take wadannan
maganganun wanda hakan ya nutsar da Fahad a
matsananciyar kunya tabbas bai san maganar zata ja wo
masa wannan martanin ba kuma shi bai fadi hakan da
nufin yasan zai samu koda kusantar ma'adanar mintin ba
to amma fa da za'a masa tayi da ya gaggauta, koda lasar
ma'adanar mintinne dan haka sai ya dago kai cikin rahsin
kwarin jiki ya dubeta cike da dan munacikin murmushinsa
da ya yi nufin 6oye tsananin kunyar da ya tsinci kanshi a
ciki, yace da ita.
Amma Humaira in har kika gaggauta dauke wutar
annufin fuskarki a gareni, to kuwa da sai in iya cewa ba'a
min adalci ba Humaira in kika duba ai kinsan sam ni ba
haklina bane in da za'a min afuwa in furta manufata to
kuwa da na ce dake wasa nake miki. Haba Humaira nifa
musulmine gaba da baya kuma ina tutiya da adddinina, ba
kuma najin kunya ko shayin a nuna ni a matsayin musulmi
34
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
to dan me zai sa in kasance daya daga ciki mayaudaran
mutane masu yaudarar al'umma da cewa su musul mai ne
alhalin kuma sunfi kowa kwarewa wajen saban Ubangiji
Humaira nasan kusan tar matar da ba muharramar kaba, da
sumba ma kawai (kiss) haram ne to kuma, ina ga mai tsotsar
minti (romance) kuma na san tsananin azabar masani tafi ta
jahili shi jahili Allah zai kama shi da laifin, kin zuwansa ya
nema shi kuwa m,asani fa ya je ya nema ya kuma samu
amma sai yasa kafa ya take, yace shi haka bai masa ba, sai
dai ya gudanar da son ranshi
Ayimin afuwa dan Allah, in sha Allahu bazan kara ba
shaukin so ne ya dauke ni har na yaba gurfatacciyar
maganar cikin mayen so da kauna. Amma hakIka zan
gargadi kaina ko dan gaba in san irin maganar da zata fito
daga bakina. Har kunnuwa su kaiwa zuciya yasa amsa mai
faranta raina. Humaira ina sonki fushin ki dani zai iya jefa ni
cikin halin kaka nakayi."
"Amma yaya kai kanka kasan bai dace ka furta haka a
gareni ba amma shi ke nan, wannan ya wuce sai mushirya
wa tarar abinda ke gaban mu yaya ya dace ace mun bar garin
nan kasancewar, mukadai ne a dokar daji sannan irin wannan
maganganu na shiga tsakaninmu, mu koma gida kada a neme
mu, kaga har goma ta wuce duk abinda zuciya ko rai suka
raya a akanmu abin nufi duk abinda aka zargemu da shi yaya
bamu da bakin futar da kanmu face Allahn da ya haliccemu,
shi kadai zai shedemu shi kaďai zai shedemu dan haka dan
Allah Yaya ka taimake mu ka fitar damu daga cikin zargi
musamman ma ni. Tunda kai dansu ne sun dade da kai sun
san halinka ni kuwa fa su yi tunanin 6oye halina nayi sai da naji zan koma ga iyayena sannan na fito dashi fili tunda baza
su kara ganina ba.
Amma bai dace kiyi wannan tunanin ga iyayena ba Humaira ina alfaharin sanar dake cewa iyayena masu fahimtane sai dai ban gane dai nufinki ba cewa daga yau ba
35
LUBABАН
zasu kara ganinki ba kina nufi dama yaudarata kike sai
munje Kano kice ke gidan ki zaki koma? To wallahji baki
isaba ki dauki zamfara a matsayin gida Kano kwa ki rikekwa
ki rike a ranki tamkar zaki ganin gida ne, in kuwa kin canja
gari to kuwa Abuja kika nufa da mijinki na har a bada aure
na dake kuwa babu gudu babu ja da baya can jin ra'ayinki a
kai na ya kan iya jawo miki dana sani mai tsanani a rayuwa.
A cikin zafin rai ya fizgi motar ba tar da ya kara
sauraranta ba kuma har suka karasa gidan babu wanda ya
Kara cewa wani koda ta tafasa.
A kofar gida suka tarad da malam, da wanı kanan
Fahad da ake kiransa isah da kuma Auwal tsaye a kofar gida
babu tantama akwai abinda suke tattaunawa, wanda
tatsuniyar gizo bata wuce koki, dan gane ga yadda suka zuba
musu ido cikin mamaki shi ya bashi tabbacin akan su suke
maganar.
Alokacin da suka fito daga motar babu abinda ya ruda
Humaira ya kuma kidimata face irin matsananciyar a
zababbiyar hararar da Auwal ya jefo ta da ita nan take
jikinta ya daukar karwa ruda ni kuma ya durar mata a dai-dai
lokacin da ya fiskanci irin kallon da fahar ya tsareta da shi
gaba dayan su durkusawa suka yi a gaban malam cikin
Kunar rai Malam ya hausu da fada ya shiga zazzagin Fahad
yace wai shin yaushe ka dawo? Da mu bamu san da dawo
warka ba kazo ka dauki 'yar mutane kuka fice gidan uwar
wa ka kaita?
A kasa ya zame dishan ya zauna yace jiya na dawo
cikin dare malam shi yasa banz I ba ita kanta Humaira tambayar da ya dace tayi masa ke nanan amma sam ta manta
sai a yanzu ta san lokacin da ya dawo sannan yaci gaba da
cewa malam jiya Auwal yake sanar dani cewa yau za'a tafi
Kano shine na dauketa na kaita gidan abokaina sukayi
sallama a yanzu haka akwai guraren da bamu je ba saboda
lokaci ya kure..
36
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
Abin ya bawa Humaira mamaki ganin yadda tashi daya
ya iya shirya karya, irin wannan alhaliko karkarwa baiyiba, irin ta nuna alamun makaryaci Nan take Malam yace, in
haka ne ka kyauta to amma me yasa baka fada ba?" malam
nayi kuskure kayi hakuri ato nan gaba in har zaka fita da
wani a gidan nan ka ringa sanar da ni ko baka sami gani na
ba ka sanar da mahiafiyar ka, "To" yace da malam din wacсe
ba ta karya wuya.
An koma falon abban aka zauna na mai da yadda
magana take malama yayi shiru yace ato shi dai aure na
Allah ne. dan haka ni yanzu addu'a ita zan shiga yi muku
Auwal dan Allah a kori gaba dan sha'anin mata sai a hankali
kasan mace sai ta shekara tana 6atawa namiji rai yayi shiru
ya jure walau saboda yay\anta ko dan irin san da ya ke mata
ko kuma gudun tonawa gidan shi da 'ya 'yanshi asiri amma
banda mace yanzun nan kana sata mata rai duniya zata ji su
kuma 'yan uwan ta a ara a yafa kaji ana ta ambatan maza da
munayen sunave sai a manta da cea ba duka aka taru aka
zama daya ba kamar yadda suma matan ba duka ne ana gari
ba to mudai maza da hakuri aka san muy dan an ya kansace
mauna da hakuri kuwa gida zai gyaru Allah dai a kyauta don
Allah Fahad a ringa hakuri da rayuwa su mata sune hatun
mu da jin dadin mu kuma sune futu ninmu mafi tada hankali
da na miji, dan wallahi duk yadda kuke da mae, duk ranar da
tsiyarta ta tashi, in ta rikice maka sai ka rasa in da zaka sa
kanka har gara a hadaka da kana nan yara ina ka daka musu
tsawa sayi shiru kuma duk namijin da ya sakarwa mace ta
rmashi to kowa ya shiga uku duk irin san da kukewa maceе
kar ku bari ta raina ku duk inda ya dace kuyi mata fada kuyi
mata.
Amma fa Auwal yau sai dai kayi hakuri da tafiyar nan
ka bari sai jibi saboda got e za'a fara taron limamai na kasa,
domin mu shawo kan matsaloli da ake fuskanta musammam
akan kaddamar da shari'ar nan gashi dai dama tun zuwan
37
LUBABАН
alkur'ani mai girma sahria ta baiyana amma har yau kokarin
kafuwar ta akeyi bil hakki da gaskiya, amma abin na neman
ya gagaга.
A nan ne kwakwalwar Auwal ta tsaya cak da aiki me
kuma malam yake nufi? Ko dai yana nufin daurewa dansa
baya nae kiri krirn. Dan me bazai masa fada ba akan ya
hakura tunda dai yasan abinda ke wakana yana cikin
tunaninne wannan maganar ta doki dodon kunnen Auwal
wato malam ne yake ce da Fahad yau da yamma sai ya
karasa mika Humaira tayi sallamar da sauran jama'a, har
yana kara nanata cewar sallamar tana da amfani tunda anyi
zaman mutunci da su, bai dace kawai suji ta ta fi ba, hakan
bazai musu dadiba daga karshe ya gargadeshi da kada su
dade don kada ya yarda sukai magariba.
A gaskiya hakan ba karamin dadi ya hadda sawa Fahad
a zuciyarsa ba ya kuma haifarwa da Auwal mummunan
Gacin rai a zuciyarsa ba hakika ya tabbatarwa kansa
mahaifin Fahad bashi da nivyar kwantanta adalci a al'amarin
gaba daya dan hakIka yasan in har shi za'abawa damar