An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
WANDA YACE NAMIT UBANENA
Lubabah
(Mrs Ado Dauda Bichi)
LUBABАН
HAKKIN MALLAKA (M) LUBABATU YA'U BABURA
DON KAI
Ala kulli halin mai gida uban 'yayana
Abubakar Adamu (baffa)
Rukayya Adamu (murfat)
Rahama Adamu (umaima)
Zainab Adamu (najla)
GODIYA
Ta tabbata ga sarki Allah, mai kowa mai komai, ala kulli
halin, da kuma iyayena Allah ya saka muku da alkhairi.
Godiya ta musamman ga yayuna.
GAISHEKU
Sadiya Garba yakasai (auren jari)
Bilkisu yusuf ali (sai wani ya zubar)
Amina Aliyu gaya (wayafi lefi)
Fatima aminu baba (auren kisan wuta)
Jamila Ibrahim nabature (mutunci madara)
Ai... atu Aliyu (makirci)
Zainab Auwal (ZUHURA)
Zainab İawan (maza basu da tabbas)
Jamila (hafsat) ZAINAB MS SANI)
FATAN ALKHAIRI
MAJE-EL-HAJEJ HOTORO
IBRAHIM DAURAWA (HAWAN)
2
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
lokci daya jikinta ya kama karkarwa, tabbas dole A
abin ya tsoratata, wand ahar ta shiga tunanin an ya
ba hadin baki akiyi ba da shi fahad din, dan kawai
su mata haka su hadata da tsohon mijinta.. dan in har ba
wani ne ya ganta yaje ya kai masa labarin ba, tana ganin
ba bu yadda za'ayi yasan tana garin na zamfara da zama.
Alhalin ita a saninta duk tsawan shekarun da suk
adauka bata tabajin ya taba ambatar garin zamfara ba
haka kuma tunda suke bata taba jin cewa ya ce yana da
wani abokin ba da sunansa yayi kama da fahad ba, har
garama tasan yana da aboki mai suna faisal, to amma ai
wannan ta sanshi ko labarin makarantar su zai mata sau da
yawa labarin nasa yafi shafar wani waishi hand son boy,
da hakan yake nuna mata cewa shine abokinsa mafi kusa
dashi a makaranta, koda yake bai taba sanar da ita sunan
sa na gaskiya ba.
A hankali Auwal ya sulale ya zauna dirshan a kasa
bisa kafet, amıma duk da haka idanshi kyar akan Humaira,
sam ya kasa ce da ita komai fuskarsa cike da matsanancin
mámaki dan kuwa shi a tunaninshi bai ta ba tunani, har
akwai inda zata je ta iya sakin jikinta haka, har tayi kiba ta kara murjewa, ta koma takar yarinya 'yar shekara goma sha takwas ba. Haka kuma tabbas da za'a umarceshi da
cewa. ya rantse da abinda zai kashe shi cewa duk inda
humaira taje bazata iya soyayya da wani da namiji ba, to kuwa zai rantse da hakan harma ya kara da fadin "in tayi
hakanma kada Allah ya bashi rabon duniya da na lahira,
kamar yadda sauda yawa, wasu marassa tunani suke yiwa
kansu du'a'i sai gashi tun ba'akai ko ina ba ya ganta tana
soyayya da wani hankalinta kwance. Tamkar bata taba
kamuwa da san wani da namiji a duniya ba. Anya kuwa mata suna da alkawari? 3
LUBABАН
Amma su fahad gaba dayansu soro-ro sukayi su na
kallan ikon Allah, domin babu wanda ya fahimci meke
faruwa. Bayan ga wani abokinsu, shima dai abokin sagir
din ne yace kaga shegen kwai, yanzunnan kagama cika
baki akan babu matar da har yanzu kake ganinta da gashi
da kwarjini, irin matarka ta farko har kana Ikirari da cewa
ka rufe soyayya a duniya, har sai Allah ya dawo maka da
ita har kana fankamar in har baka ganta ba kai da aure har
abada don matar da ka aura bama ka hada ta a jerin mata,
don tsabar wulakanci, sai gashi da yake Allah ba'a masa
gatse tun ba a kai ko ina ba ya hada ka da son wacce baza
ka samu ba, tashi daya ka kidime ka dimauce.
A gaskiya, irinku illane shiga daku gidaje shi ya sa fa
ni bana daukar abokina zuwa gidana duk da cewa ban ajje
wata macen a zo a gani ba, balle fahad da ya shiga kogin
soyayyar ya nutsa ya famjamo. ya kamo mace daya da
daya samun irinsu sai an tona!
A nanne sagir yasa dariya harda doka kafa ya ce, "kai
fahad dan Allah ka koma da matar ka shegen kaya, kar
yayi ta zarce don ya shide da yawa sai kace makahon da
ya warke wallahi sam ya fita daga cikin hayyacinshi
A kidime cikin hanzari ya zaburo, tamkar wanda aka
mintsina ko mahaukacin da ya dawə hayyacin shi, ya nufi
fahad har karkarwa Yalwa yake yana zuwa ya zube a
gabanshi yade, na gode na gode hansan boy dan Allah ina
kasa momin humaira?" ya sakeshi a rude ya nufi sagir
yace "sagir wanna itace Humaira matar tawa da nake baka
labari "Nan ma sakinsa yayi ya nufi gaban humaira ya
zube a kasa idonshi duk ya cika da kwalla, ya shiga
magana cikin rawar murya yace, humaira shine kika gudи
kika barni ashe Humaira dama zaki iya rabuwa dani?
Humaira kidubeni kigani zaki yadda Humaira na rame
4
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
nayi baki duk nafita daga kamannina saboda rashinki
Wallahi Humaira ko rasuwar Alhaji bata kidimani kamar
yadda tafiyarki ta rikidaniba, saboda nasan Alhaji amsa
kiran Allah yayi, kuma ita mutuwa tana kan kowa sannan
kuma ita mutuwa shahadace to amma kefa?
A gaskiya bani kadaiba Humaira kin ruda kowa
tunda kowa bai-san halin da zaki fadaba.Saboda Allah
abinda kikayi kin kyauta kenan ki gudu kibar iyayen ki da
danginki, mu masoyanki kin gujemu haba Humaira abinda
kikayi kin kyauta ke nan?
A hankali ya mike tsaye ya fara ja dabaya yana kada
hannu idansa ya kada yayi jajur yana fadin Humaira kin
ban mamaki ban zaci zaki yimin haka a rayuwaba wallahi
ban zataba.Humaira kin cuçeni kin cuci
rayuwata.Handsome kayi hakuri yajuya a gaggauce
gudugudu sauri sauri da nnufin ficewa.
A cikin zafin nama da gaggawa Fahad ya riko
hannunshi yace haba Auwalu menene haka? Kake nema
ka maida kanka kamar mahaukaci, Auwal ya shiga fizgefizge yana gir giza kai,idansa ya kada yayi jajur gaba daya
ya laa daga cikin hayyacinsa, Fahad ya girgizashı cikin
rudani, da daga murya yace haba Auwalu wai meke
damun kane? Sannan kuma ya sassauta murya yace haba
Auwalu katsaya inzo mutafi dan duk na gane inda kasa
gaba saboda Humaira bata boyemin komai ba,kada 6acin
rai ya gusar maka da imaninka.
A hankali ya juya ya kalli su sagir yace, "Don Allah
Sagir kuyi hakuri, su kuwa-sai kawai suka bishi da kallo,
sabøda sun kasa fahimtar komai,ya juyo a sanyaye ya ce
humaira ku tashi mu tafi kallo daya zaka masa kasan
abala'in razdne yake, kan humaira tunda ta zube a
Kasa take shrbar kuka, baya ga kudundune kanta da tayi,
5
LUBABАН
ta tashi a sanyaye, ko gabanta ba ta gani Shafa'atu ce ta
riketa har suka fice ko sallama ba suje sun yiwa matar
sagir ba sukaje suka shige mota suka tafi
A kan hanyta fahad ya sauke shafa'atu ya ce ta wuce
gida. Ga sunan zuwa zasu biya ta gidan shi fahad din ya
kuma gargadeta da ccwa saura ta taje ta labartawa su
Hajiya ta bari zasu zo da kan su, su duka kai tsayc suka
wuce can gidan fahad din.
a shigarsu gaba dayansu a falonsa na baki suka D
zauna duk cikinsu babu wanda yake cikin
walwala kowa idon shi ya kada yayi jajawur baya
ga ita da take ta faman rasgar kukaş wanda ita tuni
hankalinta ya kau daga abinda zai faru face kukan rashin
Alhaji sai dai ta rasa ta inda zata fara yi wa yayannata
Auwalu magana, balle ta tambayi mutuwar alhajin sannan
ga ba la'in tau saya masa da tayi sakamakon tsananin
ramar da yayi tabbas yayi rama ta ban mamaki, jikinsa ya
nuna a galabaic yake, sai dai tufafin da ke jikinsa ne
zuwa agogon sa tafi kan hularshi har ka gangaro kan
takalminsa, kallo daya zaka musu ka tabbatarwa kanka
har yanzu dinke yake a hakar kudi.
Da suka zazzauna a kalla sunfi minti talatin babu
wanda zaice akwai mutane a falon, sakamakon shiru da
sukayi, kowa ya kama gabanshi a babin tunani. An kuma
rasa wanda zai fara magana, sai zuwa can Fahad ya dago
kai ya dubi Humaira ya daga murya, a hankali, ya kuma
raunane yace, "Humaira kukan ya isa haka, karkije ki
jawowa kanki wani ciwon dan Allah kiyi shiru, ya kamata
ace mun tsaya mun nutsu mumu duka, domin mu fuskanci
abinyi ya juya-ya kalli auwal yace.
6
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
"Da farko dai Auwal' zan fara da yi maka ta'aziyyar
Alhajin da naji ka fada, koda yake in nayi amfanmi da
labarin da Humaira ta bani zan iya danganta mutuwar ga
mahaifinka auwalu Allah ya jikansa ya kuma gafarta masa
yasa aljanna fiddausi ce makomarsa. Auwalu hakika dole
hankalin kowa ya tashi dan gane da 6atan humira saboda
humaira yarinya ce kamila mai kamun kai ga hankali,
nutsuwa, da kuma sanin yakamata, tunda a ranar da humira
ta sauka a garin zamfara, wato tun ranar da ta baro garin
Kano ta ke hannin mu ko kuma ince take hannin iyayena.
Amma dai-dai da rana daya ban taba jin ance ga abinda
tayi ba. Kamar yadda banji wanda ya kosa da itaba.
Don wallahi humaira yarinya ce mai shiga rai a
hankali dole fitar ta yai wuya. Auwalu a yanu dai na
fuskanci cewa kaine tsohon mijinta da ta bani labarin irin
soyayyar da kukayi da ita. Kadda ka zargeta hakIka na
tabbabta kana ranta ita ma, sai dai kuma abinımda ba'a
rasa ba.
Da farko abin ya dauremin kai da naga ashe kaine
yaya Auwaldin da ta ke bani labari. Saboda kan in ganeka
a yanzu na dauki mijinta na farko a wawa sakarai dan
babu yadda za'ayi Allah yayi kyauta da mace irin humaira
da ta cika ka'idojin nan guda hudu da amabi ya amma ba
sai ka sami daya daya cikinsu sannan ka auri mace wato
annabi ya horemu da mu auri mace dan kyanta, dan dukiyarta da nasabarta da kuma addininta to amma sai ya jinjina mana da mu auri mace dan addininta shi yafi to
amma humaira ta hada duka, amma harka biyewa mace da
6acin zuciya ka saketa alhalin kana sone da cewa
Duk matar da ta cika hakuri in ta tashi Gacinrai bata
iyaba. Kuma kana sane da cewa mac sai ku shekara goma
7
LUBABАЋ
da ita wani bai ji kanku ba amma a duk lokacin da kaso
tashi hankali a gidan ka, ka ambacu kishiya.
Duk hakurin mace wuyarta ka furta kalmar kishiya
yanzu zaman lafiya ya ragu, sai dai ku shiga takun saka ke
nan, wallahi duk mata haka suke matar da bata nuna kishi
da hauka bama in za'ayi mata kishiya, to ka tabbatar wa
kanka 'yar aljannace, irin. wadanda babu tambraya, to
amma duk abinda zata nuna maka in ka jure shi kenan in
kabita a hankalima wallahi sai tazo tafi amaryar kwantar
da kai, sabida tunfarko ba halinta bane. To shine abin ya
dau remin kai duk yadda kuke da ita har ka yadda bacin
rai yasa ka sake ta akan matar da kake Ikirari da cewa ba
sunta kake ba, asalinma hada ka akayi da ita. Kuma ga
yadda ta siffan tamin ita bata da wani kyan 'ya mace, sai
dai ban sani ba ko tana da babban kyau wato hali da
addini.
Dan kuwa hali na gari da addinin gaskiya sune gaba
ga duk wani kyan fuska ko diri na diya mace komin kudin
ta komin talaucinta.
Daga nanne Auwal yayi farat yace, wallahi
Handsome halin ma bata dashi sallah da azumi kuwa dole
ce akan musulmi saboda haka bani da tabbacin bisa
addininta tunda ni dai naga tana aikata abinda Allah ya
hana wallahi handsome duk dai mu bar abin nan a
kaddara tun ran gini tun ran zane amma ai yanzu na gane
kure na a nanne gaban fahad ya fadI badai yana nufin zai
mai da matarsaba, saboda haka cikin hanzari sai yace.
Dama ai masu iya magana sunce rabon wani shi ke
kashe wani, Auwal ya dubi Humaira yace humaira kinki
kice komai Alhalin na ssanar dake cewa Alhaji ya rasu. A
kalla ko ba zakimin magana ba ai kya yadda mu jajantawa junanmu ya tashi a hankali yanufi gabanta yazauna a kasa
8
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
kan kafet yace, Humaira Alhaji ya rasu baki tambayeni su
mama da Abba, da kannenmuba hakika shirun da
kikayimin shi zai dada dugunzumani dan Allah Humaira
kimin magana, ko rasuwar babanmu mujajanta mana.
Dama tamkar mai jiran kiris, dan haka itama sai ta
zamo daga kujerar tazauna a kasa,ta shiga rera sababbin
baitikan kukan, yaruko hannunta a raunane yace Humaira
Allah yayiwa Alhaji mutuwa, wallahi 'yan dabane suka
haura ta sama suka caccaka masa wuka, don kawai ya na
sanar da gwamna baban su Sumayya gaskiya, yau kimanin
wajan wata shida kenan, tun tafiyarki da kamar kwana
talatin da biyu, Har yau bincike ake ankasa gane wanda
yasa ayi kisan, wallahi mun tabbata ba'a matsabane dan
maban su Sumayyar aka barwa bin ciken wallahi naso in
dawo da binciken hannuna abban ya hana dan mu duk
muna zargin baban na tane. To amma sanin gai bu sai
Allah.
Da har zasu tafi da ni, amma Allah ya kiyaye a nanne
to Hanyar ta dafo kai idanta jawur tace saboda me zasu tafi
dakai" "Humaira saboda nayo binciken dama akawai cutar
da akeson ayiwa abanıa ki aka bukaci Alhajin ya amincс
a shirya zan bar da shi to da ya ki amincewa be shine sukа
lababa suka matsanta akan sai sun bi duk hanyar da zasu
bi su ja ra'ayinsa doni dan siyi amfani da yin garkuwa da
Sumayya ta hanyar aurar min ita sai ta ci gaba da bugun
cikin ki dani ta gano sirrin mahaifin ki sosai dan susan
sirrin dukiyar shi to bayan an yi auren namu ne suka kara
matsa masa, akan alhajin ya kine shine suka zo da wasu
takardu, duk ta shirya cutar abbane, akan yasa hannu ko
su kasheshi, akan ya kI sa hannunne sukayi masa yankan
rago. Adede nanne ya saki kuka mai tsima zuciya.
9
LUBABАН
Da farko Humaira din dif tayi, zuwa can ta saki
ajiyar zuciyar a gaggauce a inda aka fashinci dauke wuta
tayi na dan lokaci sannan taci gaba da kukan tace,yaya
Allah ya jikan Alhaji. Allah kuma ya kara mana dan gana
da hakurinsa. Allah yasa aljannar fiddausi ce makomarsa.
HakIka yaya nayi wauta ba ta kadan ba, yau da, zafin
kishi ya fitar da ni daga hayyacina har ya tsuntsinkamin
tunanina, ya rabani da imanina, azahiri gaskiya sai yau na
gane kuskure na
Da farko na dauki Alhajı akan baya sona, tunda har
yasa akamin kishiya na manta da kulawa da kauna ta
zahiri da ya nunamin tun farko, hakIka nayi kuskure bana
kadan ba na sake kwado yamin kafa a yau yaya nayi dana
sani dana sa ni maras amfani, tunda yau babu ran Alhaji
kuma Alhaji duk yayi hakane dan ya raba ımahaifina da
sharin mugayen wanda har ya rasa ranshi. Yaya na shiga
uku don Allah kayi hakuri yace, "haba humaira babu
komai dama naka Allah ya shirya kuma komai yana da
sanadi dan na tabbata duk ba kin ciki nan da kike ciki
zakiyi matukar farin ciki idan na baki labarin cewa а
yanzu mama ta koma gidan abbaıki ya'kuma dauki duk
sauran kannena, shi ya nau Nauyinmu baki daya
Dan Allah duk wannan ba hukuncin Allah bane? don
Allah ki yarda ki bini muma mu koma mu mai da auren
mu. humaira har yanzu ina sonki. so kuma na gaskiya
wanda babu sirki a cikinshi kinga wannan ma isharacс
Allah ya nuna mana.
Da farko fahad dum yaji a kunnuwansa da ga bisani
sai kuma yaji gaba daya ya sun dau kara sakamakon
neman komen da yaji Auwal nayi hakida kishi bala'ine,
ya fada a ransa. Tabbas humaira tayi gaskiya kishi zai iya
fidda maka imaninka domin kwata-kwata ji yayi ya daina
10
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
tunanin wani tausayi a gareshi fice tsannin kishin da yaji
ya farmasa. Nan take ya shi ga duba a gogo ya dubi
humaira yace. Auwalu dan Allah kayi hakuri in je in
maida ita gidan in dawo sai muci gaba da tattaunawa.
Dan ina gudun malam ya dawo gida ya tambaya ace
bata nan, kuma yaji labarin ni na fita da ita hakika mu
duka ranmu sai ya baci, daga ni har ita tun da bai sanma
abinda ke faruwa ba, dan kuwa na gargadl shafa da kada
ta fada. kai kuma daga bisani na kaika ku gaisa dan ya
hana mu shiga da abokan mu gidan, to amma in nayi masa
bayanin ka ba zai hana in kaika ba.
Dan haka kuyi hakuri kagani kaina ina san tafiya
abuja yau saboda ana min neman gaggawa amma in sha
allahu gobe ko jibi zan dawo dan mu warware matsalar.
Kuma dama zan dawo ne akan ta fiyar mu can kanon,
saboda daman shirin maida ta muke yi. Auwal yayi
matukar farin ciki da yaji cewa ana shi rin maida humaira
Kano a hankali ya dago kai ya dubeta fuskarsa cike da
tsanani murna duk ta cika da annuri ya ce da ita, "humaira
babu komai ku koma gida ni ina nan dan babu inda zani
har sai sun gama abinda sukeyı muntafi tare.
Daga nan ne ta dan bude sirriyar muryarta a hankali
tace, "yama za'ayi haka alhali kana da iyali, wanda na
tabbata yanzu bazata rasa ciki ba, zaka zo nan ka zauna
aisai ka rudata ka kuma ruda matan gidan, ni a ganina ka
tafi kawai tunda muma muna nan tafe."
"Dan kari lallai kema da gan-gan kike ai ko baku
shirya tafiyaba, ai kuma kunsan ba bu inda zan tafi,
wallahi kafata "atarki iyakti ina da iyali da suka wuce ke
ne a rayuwata?" "c haka ne amma ni a yanzu ba matar ka
bace, kaga babu wani wauyina da ya rataya a kanka, itace
dai take da katan nauyi akan ka, baka gudun fargaba ya
11
LUBABAН
janyo mata wata matsalar, kafasan illar fargaba gurin
mace mai ciki, nasan da haka to amma kya bari ta sami
cikin tukunna. kuma ni bance dole tana da cikiba, kinga
ku ta shi, ku tafi kawai karma kisa malam din ya dawo ya
muku fada amma ni tafiya babu inda zani ina fatan kin
gane ya juya ya mikawa fahad hannu ya ce, to handsome
na fa gode kwarai da gaske, sauran godiya kuma, sai ka dawo
duk da cewar Auwal ya fuskanci soyayyacе matsananciya a tsaka ninsu amma sai ya nuna tamkar
babu wata soyayyar da ta shiga tsakaninsu danshi yasan
babu ta yadda za'ayi ya hakura ya bar masa. Anan dai sukayi sallama suka ta fi.
da fitar su gaba daya suka shiga mota ba tare da wani
yace da wani uffan ba, sai da suka danyi nisane sannan
fahad yayi gyaran murya a hankali ya ce da Humaira,
Humaira wato ke sam ma baki damu da bacin rai naba ko?
HakIka ita kanta ta lura da hakan dan kusan tunda
shafa'atu take bata labarin irin 6acin ran Fahad bata taba
ganin ba irin na yau gaba daya ya daure fuskar tayi
murtuk babu wani alamun walwala a tarc da ita.tabbas ga
wanda ya sanshi da fara'ar sa to kuwa ya guji duk wani
tsananin 6acin tai nasa domin hatta kmanninsa sauyawa
suke ita kanta ta dake ne kawai, kuma dadin dadawa ta
dan ganta abin ne da yana taya su jimamin rashin da
akayi.
Daga nan yaci gaba da cewa "to humaira ba wai kin
gamu da tsohoin mijinki ba har ya na karkarwa a kanki,
wallahi sam bai isaba dan babu abinda zai rabani da kew
danshi san karya yake miki tunda har ya iya rabuwa da ke
ni kuwa fa wallahi ba tashin hankaliba Allah yasa wuta
zaki doramin aka dan tsana banga dalilin da zai sa in iya
12
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
tunanin wani tausayi a gareshi fice tsannin kishin da yaji
ya farmasa. Nan take ya shi ga duba a gogo ya dubi
humaira yace. Auwalu dan Allah kayi hakuri in je in
maida ita gidan in dawo sai muci gaba da tattaunawa.
Dan ina gudun malam ya dawo gida ya tambaya ace
bata nan, kuma yaji labarin ni na fita da ita hakika mu
duka ranmu sai ya baci, daga ni har ita tun da bai sanma
abinda ke faruwa ba, dan kuwa na gargadl shafa da kada
ta fada. kai kuma daga bisani na kaika ku gaisa dan ya
hana mu shiga da abokan mu gidan, to amma in nayi masa
bayanin ka ba zai hana in kaika ba.
Dan haka kuyi hakuri kagani kaina ina san tafiya
abuja yau saboda ana min neman gaggawa amma in sha
allahu gobe ko jibi zan dawo dan mu warware matsalar.
Kuma dama zan dawo ne akan ta fiyar mu can kanon,
saboda daman shirin maida ta muke yi. Auwal yayi
matukar farin ciki da yaji cewa ana shi rin maida humaira
Kano a hankali ya dago kai ya dubeta fuskarsa cike da
tsanani murna duk ta cika da annuri ya ce da ita, "humaira
babu komai ku koma gida ni ina nan dan babu inda zani
har sai sun gama abinda sukeyı muntafi tare.
Daga nan ne ta dan bude sirriyar muryarta a hankali
tace, "yama za'ayi haka alhali kana da iyali, wanda na
tabbata yanzu bazata rasa ciki ba, zaka zo nan ka zauna
aisai ka rudata ka kuma ruda matan gidan, ni a ganina ka
tafi kawai tunda muma muna nan tafe."
"Dan kari lallai kema da gan-gan kike ai ko baku
shirya tafiyaba, ai kuma kunsan ba bu inda zan tafi,
wallahi kafata "atarki iyakti ina da iyali da suka wuce ke
ne a rayuwata?" "c haka ne amma ni a yanzu ba matar ka
bace, kaga babu wani wauyina da ya rataya a kanka, itace
dai take da katan nauyi akan ka, baka gudun fargaba ya
11
LUBABАН
janyo mata wata matsalar, kafasan illar fargaba gurin
mace mai ciki, nasan da haka to amma kya bari ta sami
cikin tukunna. kuma ni bance dole tana da cikiba, kinga
ku ta shi, ku tafi kawai karma kisa malam din ya dawo ya muku fada amma ni tafiya babu inda zani ina fatan kin
gane ya juya ya mikawa fahad hannu ya ce, to handsoте
na fa gode kwarai da gaske, sauran godiya kuma, sai ka dawo
duk da cewar Auwal ya fuskanci soyayyace matsananciya a tsaka ninsu amma sai ya nuna tamkar
babu wata soyayyar da ta shiga tsakaninsu danshi yasan
babu ta yadda za'ayi ya hakura ya bar masa. Anan dai sukayi sallama suka ta fi.
da fitar su gaba daya suka shiga mota ba tare da wani
yace da wani uffan ba, sai da suka danyi nisane sannan
fahad yayi gyaran murya a hankali ya ce da Humaira,
Humaira wato ke sam ma baki damu da bacin rai naba ko? HakIka ita kanta ta lura da hakan dan kusan tunda
shafa'atu take bata labarin irin bacin ran Fahad bata taба
ganin ba irin na yau gaba daya ya daure fuskar tayi
murtuk babu wani alamun walwala a tare da ita.tabbas ga
wanda ya sanshi da fara'ar sa to kuwa ya guji duk wani
tsananin 6acin tai nasa domin hatta kmanninsa sauyawa
suke ita 'kanta ta dake ne kawai, kuma dadin dadawa ta
dan ganta abin ne da yana taya su jimamin rashin da
akayi.
Daga nan yaci gaba da cewa "to humaira ba wai kin
gamu da tsohoin mijinki ba har ya na karkarwa a kanki,
wallahi sam bai isaba dan babu abinda zai rabani da kew
danshi san karya yake miki tunda har ya iya rabuwa da ke
ni kuwa fa wallahi ba tashin hankaliba Allah yasa wuta
zaki doramin aka dan tsana banga dalilin da zai sa in iya
12
WANDA YACE NAMIJI UBA NE 3
rabuwa da keba, saboda haka kiyi tunani babu ruwana da
wata dangantakar da take tsakanin mu