kuma ya kirata ya sanar da ita halin da ake ciki. To
ita dai taja bakinta ta yi shiru ba ta sanar da shi abin da
ke nan ba. Da direban ya zo, ta ce su tafi gidan
Mummyn, sai da yamma za ta koma gida, don haka ta
tafi gidan Mummy. Gaisawa kadai suka yi ta shiga
dakinsu ta kwanta. Mick ke tananen nama a cikin, ba ta
son kamshin zuciyarta tashi take yi. Har yamma tana
kwance, Mummy ta kawo mata wannan ta kawo
wancan, da kanta ta fahimci ciki ne ke wahalar da
Naja'atu, sai tayi ma Allah godiya. Farin ciki fal da
zuciyarta.
Daddy ya kira yana tambayarta jikin? Ta ce, "Da
sauki, sai dai tana gidan Mummy." Don haka da ya taso
ya wuce gidan, har cikin dakin ya shiga inda take
kwance, duk tayi laushi. Ya dube ta a sanyaye, itama
RO
Sirin Zuci. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
haka take kallon shi. Sai ya zauna kusa da ita, ya rike
hannunta yana yi mata sannu. Ya ce, "Me suka ce yana
damun ki, kinga yanda kika rame kuwa?" Ta lumshe ido
tana jin nauyin shi, to kuma kamshin turaren shi ma sai
ya sha mata kai, ta ji tana neman yin amai. Don haka ta
yunkura ta tashi ta shiga kewaye, nan ma ya bi ta ya
tsaya kawai yana kallon ta, zuciyarshi na raya mashi
wani abu. Amai take kwararawa sosai, sai da ta gama
suka dawo cikin dakin. Ya tsare ta da ido ya ce,
"Naja'atu ciki gare ki ko?" Sai tayi murmushi tana jin
kunya. Shima murmushin ya yi, ya ce, "Sun fadi maki
haka?" Ta daga mashi kai. Ai murna kamar ya goya ta,
ya rasa inda za ya saka kanshi don murna. Naja'atu tayi
lamo tana jinshi, nauyi take ji sosai. Mummy ta shigo,
ko kunya babu ya yi ma Mummy bayanin Naja'atu ciki
ne da ita.
Mummy murmushi kawai tayi, ta ce, "To Allah ya
ba ta lafiya, saiu ka barta nan ta huta ko kwana biyu ne,
kaga jikinta babu karfi, idan ta tafi can wa za ya kula da
ita?" Maganar tayi ma Naja'atu dadi, amma shi Daddy
bai ji dadi ba. Amma Mummy ta kafe cewa, sai ya barta.
Babu yanda za ya yi, ya barta ya tafi gida. Amma da
dare sai da ya dawo, nan ya yi hira, sai marairaice ma
Naja'atun yake yi. Ita kuma ta san matsalar shi, har ta
rinka jin tausayin shi. To sai dai babu yanda za tayi, ta
san dai za ya takura, za ya yi rashin abubuwa da yawa
da ta saba mashi dasu. Shima abin tla yake tunani ke
nan. Da kyar ta lallabashi ya tafi, Mummy na kallon shi,
sai dai tayi dariya ta ce, "Kayi ka gama."
Kwananta biyu gidan, tana samun kulawa sosai
wajen Mummy. Zainab ta zo duba ta tare da Doctor
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
Dariya ta rinka yi ma Naja'atu. Naja'atu ta ce, "Ki bi
sannu, ai kara ni na sha miya, wa ya sani kila ma har kin
dauka, wannan rawar jikin da naga Doctor yana yi."
Zainab tayi dariya kawai. Ranar Daddy ya zo ya matsa
sai ta shirya sun tafi gida. Naja'atu ta marairaice ba ta
son tafiya. Amma ita Mummy, lura da halin da yake ciki
ya sanya ta ce Naja'atu ta shirya su tafi. Ba ta son yi
mata gardama, don haka ta shirya suka tafi. Tun daga
lokacin Daddy ya dauki duk wani burinshi ya aza kan
Naja'atu da cikinta, ya rinka ba ta kulawa ta musamman,
abun ya tsone ma Farida ido, duk da cewa ba ta san abin
da ke damun Naja'atu, ta dauki zafin kishi ta aza mata.
Ko kallon ta taga Daddy ya yi, sai sunyi rigima. Don
haka Naja'atun ta ce ya yi hakuri ta yafe mashi ranar
aikin Farida ya daina shiga dakinta, ita za ta fito ta gaida
shi. Don haka ba ta samun zama da shi sai ranakun
aikinta.
Wata daya, biyu, na uku cikin Naja'atu ya fito fili.
Ai kuwa Farida ta dauki zafi ta dora ma ranta, ta rinka
yi ma Daddy bala'i. Ya ce, "To ai ba laifin shi bane,
haihuwa ta Allah ce. Itama idan Allah ya kawo za ta
samu." Duk da haka dai ba ta sauko ba. Ya zuba mata
ido, amma ya gargadı Naja'atu ta bi sannu kada ta yarda
ta biye ma ta suyi rigima. Don haka babu ruwanta da
harkar Farida, ko da yaushe tana cikin dakinta, sai in
Daddyn yana gida ne ya ke matsa mata ta fita falo suyi
hira.
Yau da safe Daddy ya leko cikin dakin za ya tafi
wajen aiki, Naja'atu na gyaran dakinta har da goge, ta
juya tana gaida shi. Ya zuba mata ido, tayi kyau sosai,
dan cikin ya zauna daf a jikinta, sai ya kara bude ta, ta
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankja
cika sosai. Ya ce, "Wai ke ba ki iya ki huta ko? Sai k
rinka jajibu aiki." Tayi dariya ta ce, "Yana da kyau in
rinka motsa jikina, haka nan cikin bai yi girman da za ya
hanani aiki ba." Ya jinjina kai yana kallon ta, ya ce, "Za
ni tafi, babu wani abu?" Ta ce, "Babu, sai ka dawo,
Allah ya ba da sa'a." Ya yi murmushi ya yi mata godiya
ya fice
Da ta gama komi, tayi wanka ta fito kicin ta hada
shayi ta zauna falo tana sha, ba ta kula Farida ba, itama
ko kallon ta ba ta yi ba. Sai da ta kunna T.V tana kallon
tashar Nolly Wood, sai ga Farida ta zo ta kashe. Naja'atu
ta bi ta da ido kawai, sai ta tashi ta bar falon ta shige
dakinta. Ita dai ta san ba yanda za'ayi tayi fada ita daya,
dole sai da abokin yi. To ba za ta biye mata ba. Da rana
ma ya dace tayi girkin abincin, amma ba ta yi ba.
Naja'atu ta rinka jin yunwa, don haka ta fito ta shiga
kicin, ta fere dankali dai-dai jikinta, sannan ta kunna
gas, ta zuba mai ta dora. Ya dauki zafi ba ta kai ga zuba
dankalin ba, sai ga Farida ta shigo cikin bala'i ta ce,
"Amma kin san yau ranar aikina ce, don mi za ki shigo
kicin? Ko kinga ni ina yi maki haka?" Naja'atu ta ce,
"Na sani ranar aikin ki ce, amma ai baki bamu abin da
za mu ci ba." Farida ta ce, "To ai ba aje ni aka yi ba don
in dafa maki abinci ki ci, idan kin samu shi Daddyn yana
lallaba ki don kina dauke da cikin shege! Ni ba ki isa in
yi maki wannan wahalar ba."
Naja'atu ta'sha mamaki, ta ce, "Ni ke dauke da
cikin shege ko? Babu tsoro ta amsa, "Eh." Naja'atu ta се,
"Na ji ina dauke da shege, ai ke banga kin dauki dan
halak din ba, kin tsaya kina fama da bakin ciki." Farida
tayi shewa ta ce, "Don nafi karfinshi ne, kema din ai
83
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
rufa maki asiri ya yi ya aure ki, tunda dama tun can gida
tare kuke, meye ban sani ba?" Maganar tayi ma Naja'atu
ciwo, abun har ya kai ga 'yar kazafi? Nan fa suka rinka
yinta babu dadi. Farida ta zo za ta sauke man da
Naja'atu ta dora, ita kuma ta hana ta. Ba ta yi aune ba,
sai dai taga ta dauki frying pan din, ta watso man da
nufin ta konata. Dai-dai lokacin Daddy ya shigo kicin
din, saboda ya shigo ya jiyo hayaniyarsu. Da sauri ya
ture Naja'atu gefe daya, don haka ga baki daya man ya
wanke mashi hannu da jiki. Ai kuwa ya saki wata irin
kara, Naja'atu rayo kanshi da sauri cikin tashin hankali.
Duk da dauriya irin ta da namiji, sai da ya kwalla. Sai
dai ya gode ma Allah da ya sanya ba Naja'atun ce ta
Kone ba.
Da sauri Naja'atu ta dauko ruwan sanyi tana zuba
mashi, amma kamar kara zafin ake yi. Farida kuwa sai
tayi tsuru-tsuru, sai dai duk da haka ta girgiza da ganin
abin da ya faru. Kishi bala'i ne, ita kam nata ya ma zama
hauka. Da dai ta samu ta lallaba ta fice, sai ta shige
dakinta ta kulle. A zatonta dukan ta Daddy za ya yi. Тo
shi ta kanshi yake yi. Naja'atu duk ta rude, tayi nan tayi
can, ta rasa abin da za tayi. Sai ta dauki waya ta kira
Zainab, ta ce, "Zainab Doctor na gida?" Ta ce, "Eh, gaya
nan bai dade da shigowa ba. Lafiya?" Ta ce, "Da sauki
Zainab, ku-kawo mana dauki Daddy ne ya kone."
Zainab tayi salati, ta ce, "Garin yaya?" Naja'atu ta
ce, "Abun ba dadi; ku zo dai yana cikin hali." Ta jefar
da wayar kan kujera ta komo kanshi tana yi mashi fifita,
yanda taga yana shan wahala, har kuka tayi ta rinka yi
mashi fifita, daga wannan tasa wancan. Cikin dan lokaci
wuta ta tashi, ba ta son ta fadi ma Mummy hankalin ta
RA
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
ya tashi. Ranar ta sha haushin rashin iya tukin ta, babu
yanda Daddy bai yi da ita ba kan ta yarda ya koya mata,
amma ta kiya. A ganin ta ba dole bane. Ashe ko dan
lalura irin wannan ka koya. Yanzu ga shi kiri-kiri, tana
gani yana shan wahala, amma ta gaza yin komi, da ta iya
kau da yanzu suna asibiti.
Sai da su Zainab suka iso, Khalid yaga jikin, don
haka ya ce su tafi asibiti. Shi ya dauke su suka tafi.
Zainab mamaki take yi, ta cc, "To wai garin yaya haka
ta faru?" Naja'atu ta ce, "Farida ce, ni ta zo konawa, sai
Allah ya kawo shi tana watsuwa ya ture ni sai ta same
shi." Zainab ta rinka bala'i. Suna isa asibiti ta kira
Mummy ta ce ta zo taga abin da Farida tayi. To itama
yanda taga jikin Daddy abun ya bata mata, dama ita ke
kange Farida, amma yau ta tsane ta kwata-kwata, abin
da tayi rashin imani ne. Yanzu da ta samu Naja'atu yaya
ke nan? To ba Mummy ba, duk wanda yaga jikin Daddy
sai da ya yi Allah wadarai da mata masu irin halin
Farida. Haka kawai zafin kishi ya sanya ka rabu da
imani? Lallai dole ne mata su hankalta, kishi ba hauka
bane, yanzu meye ranar irin wannan?
Kwananshi biyar asibiti, Farida ba ta zo ba. Ko da
yake ta san ba ta da gaskiya, tana kiran layinshi, idan
yaga ita ce baya dauka. Amma Mama ta zo duba shi sau
biyu, har kuka tayi da taga abin-da diyar ta tayi ma
mijinta, ta rinka tsine mata. Sai da Mummy ta ba ta
hakuri, mutane da dama suna fadin raayinsu akan
faruwar wannan abu. Amma shi Daddy jinsu kadai yake
yi, a cikin zuciyarshi ya gama daukar matakin da ya
dace da ita, lokaci kadai yake jira. Sai da ya yi sati daya,
sannan aka sallame shi ya koma gida.
85
Sirrin Züci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
Basu tarda Farida ba ta fita yawon tga. Naja'atu ta
shigab ta gyara mashi dakinshi itama ta gyara nata,
sannan tayi wanka ta dawo falo inda Daddyn yake
kwance, Ya dube ta ya yi murmushi yana kara jin
kaunar a zuciyarshi, har tausayin ta yake ji, ba ta da
lokacin kanta sai nashi. Kwana biyu da ya kone, yanda
baya iya yin barci haka itama ba ta runtsawa. Ya mika
mata hannu ta zauna kusa da shi, ya ce, "Wai ke ba ki
iya zama ki huta kina wahalar mani da Baby da yawa?"
Ya sanya hannu yana shafa cikin, sai ta rike hannun tana
dariya, ta ce, "Wa ya bani hutu, maigida ba lafiya." Ya
yi murmushi ya janyo ta cikin jikinshi yana jin dadi
marar misaltuwa. Naja'atu mace ce ta gari, ta gama
mamaye zuciyarshi da kyawawan halinta.
A hankali ta shigo gidan, jikinta duk ya yi sanyi, ta
raina gaskiya, amma da yake ba ta san kunya ba, sai ta
shiga washe baki za ta cika shi da dumi. Ya daka mata
tsawa, dole ta tsaya. Ya ce, "Ina kika fito yanzu?" Tayi
shiru. Ya ce, "To koma, daga yau ki dauka baki san
wani Daddy ba, na sake ki." Naja'atu ta bude baki cikin
tashin hankali za tayi maganas, ya dora mata danyatsa
akan lebe, tayi shiru tana tararrabin abun. Da ya yi
hakuri ya rabu da ita, wata rana sai ta gyara. Bai sake
magana ba ya ja hannun ta suka shige daki. Abun bai yi
ma Naja'atu dadi ba, amma Daddy ya hana ta magana.
Mummy ma da ta ji tayi fada sosai, ta ce sai a dawo da
na. Yayin da shi kuwa ya yi rantsuwa akarn ba shi ba
Farida har abada. Yanda tayi din nan, idan ta samu
makasar Naja'atu za ta iya kashe ta. To haka ake kishi?
Zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu cikin
gidan Daddy, ya zama dan lelen Naja'atu, duk da tsohon
86
Sirrin Zuci.. 4 Sa'udatu Saminu Kankia
cikin ta ba ta gajiya da yin hidimomin shi. Mummy kau
dadi take ji, sai sanya albarka take yi. Rayuwarsu
gwanin ban sha'awa, akwai fahimta sosai tsakaninsu.
Cikin ikon Allah Naja'atu ta sauka lafiya, an samu da
namiji. Tun a asibiti Daddy ya fara kiranshi Usman,
watau sunan mahaifinsu, ya yi Daddy junior ke nan.
Yaron kyakkyawa kato da shi kamarsu daya da Daddy.
Zainab ta rinka santin shi, Naja'atu ta ce, "Idan kin
sauka kema Allah ya baki kamar shi." Ta сc, "Ba ki sani
ba, shi Doctor ya fi son Baby girl, har scamng ya sanya
aka yi mani, kuma sun ce me yiwuwa ma in haifi 'yan
biyu duk mata."
Naja'atu ta ce, "To Allah ya raba lafiya." An sha
shagalin suna lafiya. Suka ci gaba da renon junior. Da ta
gama wanka Daddy ya kaistu Katsina, satinsu biyu, suka
gaisa da 'yan uwa. Akwai ci gaba sosai ta bangaren s
Malan, ya yi ritaya an ba shi kudin sallamar aiki, đơn
haka ya ce Hajji za ya je ya sauke farali. To da Daddy ya
ji haka, sai ya ce, "Itama Inna ta shirya sai su tafi tare,
ya biya mata." Abun ya yi masu. Daddy ya co, Tta kurna
Naja'atu sai ta yaye junior sai su tafi."
Ko da yaushe Naja'atu kanyi alfahari da auren ta da Daddy, ba ta taba yin nadamar aurensu ba, kullum ci
gaba suke samu sun hada kansu, zamansu lafiya. Babu
irm naci da bin diddigi da Farida ba ta yi ba, dơn ya mei
da ita, amma ya ce sam ba za ya yiwu ba. Ga shi zamim
gidan nasu babu dadi, Mama ta juya mata baya fada
take yi mata sosai. Ga shi auren ya fi samuwa, ko yam
samarin da take dasu da, yanzu duk sun guje. Karatun
ma ba ta ci jarabawa ba, bà tà komi sai yawon bin gidajen kawaye. Idan akayi buki ana can. Wannan shi ne
Sirrin Zuci.. Sa'adatu Saminu Kankia
santatta, don Allah 'yan uwa mata mu rinka kushe kishin
mu, wani lokacin zafin kishi, shi yake kaimu ga aikata
aikin dana sani. Allah ya kyauta.
Zainab ta haihu, ta samu 'yan matanta biyu,
kamarsu daya da babansu masu kyau. Naja'atu ta rinka
santin su, Daddy ya cc, "Kiyi addu'a next time kema
Allah ya baki irin su." Dariya kawai tayi. Sun ci gaba da
zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ci gaban rayuwa.
Da shckara ta zagayo, Naja'atu da Daddy, har da su
Zainab suka tafi kasa mai tşarki suka sauke farali.
Shekara biyu tsakani ta sake haihuwar 'ya mace, aka
sanya mata sunan Mummy, Halimatu Sa'adiya. Itama
Mummy suke kiran ta, kamarsu daya da Naja'atu.
Daddy ya hada kan iyalinshi yana nuna masu so, ko da
yaushe yana alfahari da Naja'atu, ta zama 'yar halak.
Good life irin wadda yake so.
- Allah yasa sauran mata su dauki halaye na gari, su
rinka hakuri da juriya irin na Naja'atu.
Masha Allahu
Sai mun hadu cikin sabon littafi na gaba. WANI
AL'AMARI insha Allahu
Mai Kaunar ku
-AUNTY UWANIN KANKIA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels