ta tafi da dare ya
iso gidan. Maigadi ya iso in da ya tsaya su ka gaisa,
sannan ya je ya kira Naja'atu yasan dai wajanta ya ke
zuwa. Su na zaune falo ya fadi sakon sai ta yi murmushi
ta taso ta fito, ya na zaune cikin mota su ka gaisa ya yi
murmushi ya ce "Ga ni na dawo, kuma na yarda da
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
shawararki ina fatan kinyi ma ta maganar?" Sai ta yi
dariya ta ce "Ina zuwa." Ta koma cikin gida ta kamo
hannun Zainab, ta na biye da ita har wajenshi, ta ce "o
ga ta na kawo maka, kasan an ce waka a bakin mai ita ta
fi dadi." Zainab ta zuba mata ido kamar zata yi magana,
amma sai ta gaza cewa komi, a hankali ta sauke kwayar
idonta akanshi, ta ji wani irin abu ya daki zuciyarta, sai
ta sarda kai tana murmushi, Naja'atu ta dube shi sai ta yi
dariya, ta saki hannun Zainab ta koma cikin gida.
Su ka yi shiru su na jin nauyin juna, Zainab ta
jingina da motar ta daga kai ta na kallon taurari, gabaki
daya Khalid ya canza mata salon tunani da kallon da ta
ga ya na yi mata, to shima kwarjinin yarinyar ya cika
wajen har ya gaza ce mata komi, sai da ya lura ta saki
jiki sosai, a kalla ta gama duk wani nazarin da ya ce ta
yi. Sannan ya yi gyaran murya, ya ce "To ni Zainab na
ma rasa ta ina zani fara, naso ace Naja'atu ta yi maki
bayanin komi, kin ga da yanzu amsarki kawai zan ji to ta
tattara aikin duka ta dora mani. Amma na sani zuwa
yanzu da muke tsaye da ke za ki iya fahimtar wani abu a
tattare da ni, kinga dai yarda tafiyar nan ta taho kuma
kina sane da komi, naso Naja'atu sai dai ga yarda abun
ya kasance, ta zabi wani a kaina, wanda ni ban ga laifin
ta ba, so daban ne, don haka na sanar da ita cewa ta yi
maki magana, idan kin amince mani in karkato akalar
kaunata a gare ki, me yiwuwa haka ta ta cimma ruwa,
kada kiji komi ki fadi mani gaskiyar abin da ke cikin zuciyarki, kin amince.
Zainab ta ji wani irin farin ciki fal da zuciyarta,
samun miji irin Likitan ba karamin alkairi ba ne, ta yarda da shi da halayyarshi, don haka ba ta tsaya
Simin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
wahalar da kanta ba, ta amince mashi dari bisa dari,
mamaki ya yi sosai bai yi tsammanin zaya same ta haka
da sauki ba, a karshe ya yi ma Allah godiya, wani hanin
ga Allah baiwa ne, cikin natsuwa ya ci gaba da yi ma ta
bayanin kanshi da kuma manufarshi akanta, amma ya се
zaya ba da lokaci yanda za su fahimci juna sosai, ta
yarda ba za su rinka fuskantar matsala ba, a zaman
auren su. Zainab ta amince, don haka suka saki jiki suna
hira.
Can cikin gida kuma, Mummy ta fito daga cikin
daki, Naja'atu ce kadai zaune falon tana kallo. Ta zauna
tana kallon Naja'atun, ta ce, "Ina Zainab din kuma?"
Naja'atu tayi murmushi ta ce, "Tayi bako ne tana waje."
Mummy ta ce, "Bako daga ina kuma?" Tayi dariya ta ce,
"Mummy Khalid ne ya zo wajen ta." Ta ji maganar
kamar daga sama, ta ce, "Bawan Allah, bai yi fushi ba
dai? Ina son yaron nan, yana da hankali. Amma kiri-kiri
kin kishi." Naja'atu tayi dariya ta ce, "Nifa Mummy ba
kinshi nayi ba, Allah kuwa ina tausayin Daddy ne, yana
bukatar kulawa. Kuma ba ga shi ya samu Zainab ba."
Mummy ta ce, "Au shirin ku ke nan?" Naja'atu ta се,
"Mummy za'a ba shi ko?" Tayi dariya ta ce, "Me za ya
hana, idan dai ita tana so? Allah dai ya shige mana
gaba." Gaskiya Mummy, ta ji dadin wannan lamari, tayi
ma Allah godiya. Don haka da Zainab ta shigo ta hadasu
su duka ta rinka yi masu nasiha. Sannan ta tabbatar
masu da cewa, in dai ta samu yanda take so, nan da wata
uku, su duka aurar dasu za tayi.
Khalid da kanshi ya mai da Zainab makaranta.
Yayin da suka bude sabon babin soyayya, abun har
mamaki yake ba Naja'atu, yanda suke tafiyar da
55
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
al'amuransu, sai kayi tsammanin sun dade tare. Yanzu
hankalin ta ya kwanta, ba ta jin tsoron komi. Amma shi
Daddy da aka fadi mashi wannan tsarin, cewa ya yi shi
sam ba za ya iya jira sai nan da wata uku ba. Don haka
ya matasa ma Mummy sai da ta je Katsinar da kanta,
gidansu Naja'atu. Malam ya yi farin ciki, ya yi godiyar
Allah da fatan alkairi. Don haka ya ce, "Babu komi,
Naja'tu tasu ce, don haka duk lokacin da suka ga ya yi
masu, to sannan za'ayi." Daddy ya ji dadi, da kanshi ya
debi sati hudu kacal. Ya ce, "Lokacin yake so." Da suka
dawo Mummy ta shirya kudin neman aure da sauran
kayan sanya buki aka kai gidan su Naja'atu. Cikin
kwanaki magana ta kankama.
Wannan karon Daddy da kanshi ya ke hada
lefenshi, sayayyar har da marasa amfani. Amma
idanuwan shi sun rufe, za ya iya yin komi saboda
Naja'atu. Mummy dariya take yi mashi, al'amarin maza
sai su. To itama Naja'atun, takan yi mashi korafi kan cea
ya rinka yi abubuwa da kula, kada ya wahalar da kanshi.
Amma ina, ya yi nisa baya jin kira. Itama Mummy ta
bangaren ta, ta ce ma iyayen Naja'atu, ba ta bukatar
komi, duk abin da ake yi ta dauka, ita ce za tayi. Haka
nan Katsina za su taho ga baki daya ayi buki a gama, su
ataho da amaryarsu.
Ya rage saura sati biyu, Naja'atu ta ce, "Tana son
ta fara tafiya Katsina saboda shirye-shiryen ta." Mummy
ta ce, "Shirin me za ki yi'Naja'atu? kada fa ki je ki dora
masu hidima? Kina gbani dai duk abin da za ki bukata
nayi. To me kuma za ku nema?" Ta ce, "Allah kuwa
Mummy ba saboda haka za ni tafi ba, ina son in dan
samu lokaci in zauna dasu ne, ba wai da na je ba a shiga
54
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
buki." Mummy ta ce, "Shi ke nan, sai ki shirya zuwa jibi
sai Babangida ya kaiki, gobe in Allah ya kaimu za mu je
Sahad Store ki za bi kayan kicin dinki da kanki. Na san
na ture ki, sai sauran hidimomi."
Da kyar da Daddy ya yarda da tsarinta, wai sai dai
ta jira su tafi tare. Sai da Mummy ta sanya baki, sannan
ya amincc. Da ya koma gida, Farida na zaunc cikin falo
ko kallon arziki ba ta yi mashi ba, babu jituwa sosai
tsakaninsu cikin kwanakin, tun ranar da ya zo bai same
ta gida ba, wai sun je unguwa tare da wata kawarta. Da
ta dawo ya rufe ta da bala'i, itama ta rufe idc, suka yi ta
babu dadi. Tun daga lokacin ta tsiri fushi, shima bai
damu ba, ya ci gaba da shareta. To amma yau ganin
komi yana karatolwa, har yanzu ba ta san abin da ake
ciki ba. Sai ya ga ya dace su zauna ya sanar da ita, su
tsara yanda abubuwa za su kasance.
Don haka ya zo ya zauna ya dube ta, itama kallon
shi take yi cike da tsana. Ta sarı dai inda ya fito, yana
like da Naja'atu, kuma kallon, shi kawai take yi ta ga
yanda za'ayi ayi auren. Ko itar da suka yi ranar wajen
wani boka ta je, kuma ya tabbatar mata da cewa babu
wannan maganar, ta je ta kwantar da hankalin ta. Duk
abubuwan da ya ba ta tayi amfani dasu tayi. Hatta
karkashin gadonshi, akwai layoyi, haka kowace
kusurfwa an daga kafet an saka laya, hayaki da sauransy
duk tayi. Abu daya ya rage mata, shima dama take jira.
Ya zuba mata ido fuskarshi babu walwala ya ce,
"Kawo mani ruwa in sha." Ba tayi musu ba, ta je ta
dauko da kofi ta kawo ta aje gabanshi, ta koma ta zauna.
Ya fiddo Paracetamol cikin aljihu ya zuba ruwan ya sha,
sannan ya gyara zama yana kallon ta ya ce, "Magana
57
Sirrin Zuci 4 Sa adatu Saminu Kánkia
nake son muyi, kina da lokacin saurarena ko kuwa?" Tа
yatsuna fuska tana kallon wani sashin ta ce,, "Ina
saurare." Ya ce, "Magana ta da Najalatu ce, kuma dama
na fadi maki auren ta zaniyi. Do haka maganar cc ta
taso, duka bai fi sati biyu ya ragbe ba Don haka ki samu
lokaci ki dadi mani dukkan bukatunn ki, da sauran
abubuwan da kikc bukata, saboda Katsina za'ayi bukin,
sai dai faga baya nan zata dawo kunzaunantare. Don
haka, don Allah Farida, ki nutsu mu hada kanmu, mu
zauna lafiya, ba ni son rashin jituwa irin haka tana shiga
tsakaninmu."
Wani irin duhu ta ji yana gitta mata ido, kanta yana
sarfawa, ga baki daya bakinta ya mutu, ta kasa ce.mashi
komi. Sai kawai ta mike ta bar falon Yabi ta da kallo
yana cizon lebe, sai ya girgiza kai. Idan da sabo ya saba
da rainin wayun Farida; amma lokacii nee zas ya yi
maganin ta.
Cikin daki ta fada kan gado tana kuka, gani take yi
wulakanta ta kawai Daddy yake somyi don baya Kaunar
ta. Ba ta ga duk irin abubuwan da take yi mashi ba na
rashin kyautatawa. Hankalinta ya tashi sosai, idan akwai
abin da ta tsana a rayuwarta, bai wuces Naja'atu. ba
Yarinyar ta tsaya mata a rai. Kwana tayi tana tunanin
abun yi. Don haka washegari yana fita, itama ta fita, ta
san Mama ba ta gida, ta fita wajen-aiki: Don haka kai
tsaye wajen aikin ta nufa. Mama na cikin ofis taз
kwankwasa ta shiga. Ganin yanayin da Faridar takecciki
ya ba ta mamaki, ta zuba mata ido ta cikin farin gilashin,
sai ta sanya hannu ta cire gilashin tana kallon taş taace,
"Ke kuma daga ina haka?"
Farida tga ja kujera ta zauna, zuciyarta ta kare, sai
58
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
ta fasa mata kuka. Mama ta girgiza kai, har ta fara gajiya
da matsalar Farida, duk sanda ta zo da abin da za ta zo
da shi. Ta kasa kwantar da hankali ta daidaita
zamantakcwar ta da mijin ta, abin da ta kasa fahimta ke
nan. Ita rayuwar aurc, halin mutum ke ceton shi, da za ta
nutsu su fahimci juna, zamansu za ya yi kyau, amma
fitinar ta, ta isa. Ta dube ta, ta cc, "Me kuma ya faru?"
Ta cc, "Wai Mama, Daddy aurc za ya yi nan da sati
biyu." Mama tayi murmushi ta cc, "To ya rasa? Ai na
fadi maki, amma kin ki, tunda kin zama sakarya, kin
kasa sama mashi kwanciyar hankali sai ya ki yin auren
shi? Munyi waya da Hajiya Halima, tayi mani bayanin
komi, don haka matsala ke ta duba yanzu. Wallahi kina
zaune za ta shigo ta shiga gaban ki, ai ya yi hakuri dake.
Kuma ni babu wani abun da zan iya yi maki. Duk wani
gyaran da kike so yana nan a hannun ki, ai Daddy bai
kiki ba, kuma ko gober yana sonki. To Farida, sai ya
zauna yai ta wahala kanki, ke ba ki san ki kyautata
mashi ba?"
Kuka ta rinka yi. Mama ta ce, "Da gangan, yanzu
ke ko kunya ba ki ji, duka wata nawa ke nan da yin
aurem ku? Amma ke, ke nan kullum jan fitina, daga
wannan sai wancan, kina biye ma kawaye. Ina gaya
maki, su za su kaiki su baroki, kina ji kina gani za su
kashe maki aure. Kuma wallahi ni babu abin da za ni yì
maki, kwanciyar hankali daya, ko koma dakin ki, ki
kama mijin ki ku zauna'lafiya. Ai ke kika ba shi damar
yin auren, idan da kin tsaya kina kyautata mashi yayа
za'ayi ya samu idon kallon wata diya mace? To nan ma
dai babu taushin, don haka da ta fito ba ta zame ko'ina
ba, sai gidansu Dije. Ta ja ta suka fice, sai Yanye gidan
Sirrin Zuci.. 4 Sa 'adatu Saminu Kankia
malaminsu. Ta fadi mashi komi. Ya cc ta kwantar da
hankalin ta, ta dauka kamar an fasa auren ne. Idan ma
ba'a yi sannu ba, za ya iya haukata yarinyar duka a huta,
tunda dai au ba za ya auri mahaukaciya ba. Sai lokacin
hankalin ta ya kwanta, ta balle jikka ta fiddo kudi ta ba
shi. Ya ba ta wani magani ya ce ta je ta barbada kan
shimfidar da Daddy yake kwanciya, za ta ga abin da za
ya biyo baya. Haka nan ko da wasa kada ta kuskura ta
sake ta dame shi maganar auri, da kanshi za ya zo ya се
ya fasa.
Suka taho cikin farin ciki. Lokacin Daddy ya koma
gida, yana kwance falo ya gama cin abinci. Take away
yayo a Restaurent. Ta shigoko kallon ta bai yi ba, ta
wuce daki. Matsala daya ce, tuni sun raba dakin kwana,
kuma kulle dakin shi yake yi idan za ya fita. Don haka
babu hanyar da za ta shiga dakinshi. Ba ta ga fuska ba,
balle ta bullo mashi da wani abu. Ya jima kwance falo,
sannan ya shiga daki. Ta kasa kunne tana saurare sai da
ta ji shigarshi kewaye. Tayi sanda ta shiga, cikin sauri ta
aiwatar da abin da boka ya sanya ta, ta fito bai sani ba.
Amma kuma kamar yana duba, lokacin da za ya kwanta
da daddare, sai ya kwashe zanin gadon ya saka cikin
kayan wanki ya shimfida wani ya yi kwanciyarshi. Ita
kau duk a zatonta komi ya yi.
Da safe tana kwance ya gama shirin shiya fita,
saboda ranar Naja'atu za ta tafi Katsina. Ya biyata gida
ya sallame ta, sannan ya wuce wajen aiki. Tunda ta tafi,
shima ya fara shirin shi. Mummy ta tura lefen Katsina
aka kai gidansu Naja'atu, kowa ya yaba ana ta sanya
albarka. Daddy ya yi rawar gani. Nan kuma ana saura
sati daya, itama Mummy ta tafi Katsinar, yayin da
10
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
Daddy ya ce sai ranar laraba za ya taho. To ita kama
Zainab jarabawa suke yi, sai ranar juma'a Khalid za ya
biya ya dauke ta su isa Katsinar.
Al'amuran buki sun kankama, Naja'atu ana ta
hidima, ko da yaushe suna tare da Daddy a waya, yana
fadi mata yanda abubuwa suke tafiya. Ranar talata,
Aunty A'isha da kawarta Umaima, suka je gidan Daddy
suka tsara ma Naja'atu dakinta, falo karami da daki
daya, sai kewaye a ciki. Farida ba ta gidan. don haka har
suka yi aikinsu suka gama ba ta nan. Washegari tare da
Daddy za su taho Katsinar. Da dare ya shiga gidan,
Farida na cikin daki. Ya zube kayan da ya shiga dasu
bisa kujera, ya je ya kwankwasa mata kofa, sannan ya
dawo ya zauna. Jim kadan ta fito, sanye da wando baki
da riga body hug. A kule take saboda yaron da ke yi
masu wanki ya sanar da ita an kawo kayan amarya,
kuma ta ga alama. Ta tsaya jikin kujera ba ta ce komi ba.
Ya dube ta, sai ya yi dariya, yanzu ta daina bata mashi
rai. Ya ce, "Zo ki zauna mana, magana za muyi." Ta се,
"Ba sai na zauna ba ina jinka." Ya jinjina kai ya ce, "To
ga kayanan nayi karambani na sayo maki tunda na ce ki
fada kin ki fadi, kuma gobe in Allah ya za ni tafi
Katsina. Idan kuma za ki je, to ki shirya mu tafi, sai an
gama komi za mu dawo."
Ta zumburi baki ta ce, "Idan ka tafi kada ka dawo
ka gani idan za ni fasa rayuwa." Ya yi murmushi ya ce,
"Ni kuma me za ya sanya in zauna can? Sai dar ina son
ki fahimci wani abu guda, wadannan abubuwan da kike
yi ba za su sanya in ji tsoronki ba, sai ma rage ma kanki
kima kike yi. Amma tunda kina ganin haka yha fiye
maki, Allah ya ba ki sa'a. Wata rana ko an ce kiyi, ba za
61
Sirrin Zuci.. 4 Sa ʼadatu Saminu Kankia
kiyi ba." Ya mike ya shige cikin daki ya barta nan tsaye.
Sai ta zube kan kujera, zarginta guda, Naja'atu asiri tayi
ma Daddy, don haka ya makance irin haka a kanta.
Da safe har ya gama shirinshi tana cikin daki, ya
fidda jikkar shi ya kai cikin mota. Sannan ya dawo ya
kwankwasa kofarta ya bude ya shiga, ko'ina a hargitse,
dakin ma ba ta iya zama ta gyara. Shigarshi ta tada ta, ta
bude ido tana kallonshi. Sai ta ja tsoki ta mai da kai ta
kwantga. Ya tsaya kanta hannayen shi zube cikin aljihu,
sai kuma ya daga kafada cikin halin ko in kula, ya fiddo
kudi ya jefa kusa da ita, ya ce, "Na tafi, sai ranar talata."
Ya juya za ya tafi. Ai kuwa tayi tsalle ta diro daga kan
gadin, sai dai ya ji ta fizge rigar shi ta baya. Та сe,
"Wallahi ba za ka fita gidannan ba, sai ka sake ni. Mugu
maci amana, butulu!" Ranshi ya yi bala'in baci, ba ta san
yana kyaleta bane saboda Mummy ta ce kada ya
kuskura ya yi fada da ita, duk abin da za tayi ya rabu da
ita, za ta daina. Amma wannan karon ta kaishi iya wuya.
A fusace ya fizge hannunta daga jikin shi ta fada kan
gadi, sai kuma ta sake yunkurawa ta nufo shi, Wannan
karon ya sharara mata mari, dole ta saduda, ta dafe fuska
tana nadama. Bai kulata ba, ya sanyakai ya fice.
Ko garin Abuja bai bari ba, itama tayi shiri sai
gida. Karya da gaskiya ta shirya ta fadi ma Mama, sai
rantsuwa take yi ta ce ba za ta koma gidan ba. Shi kuwa
Daddy hankalin shi kwance ya biya ya dauki A'isha
suka nufi Katsina. Hidimar buki tana tafiya lafrya, а
tsarin Naja'atu, ba ta yi niyyar yin wata bidi'a ba, amma
Daddy ya kafe kan cewa bai yarda ba, a ganin shi,
Naja'atun za ta ga bai yi murna da aurenta ba, ganin
yanda aka yi hidima lokacin Farida. To ita wannan bai
62
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
dame ta ba, ta ce ta yafe. Duk da haka Mummy ta shirya
masu walimar cin abincin dare, nan ciki gidan ta. Ranar
juma'a, 'yan uwa da abokan arzuka suka hadu aka tayasu
murna, Daddy ji yake kamar ya lashe ta, tayi kyau sosai,
ga kumshi ya tsaru kan fatarta, tana wani irin kamshi na
musamman, na Humra 'yar Maiduguri. Wannan kuma
duk shirin Mummy ne, ta gama kimtsa diyarta, don haka
tunda ya iso, ya ida rikicewa, duk inda ta sanya kafa
yana biye. Ranar juma'ar da wuri Zainab ta iso tare da
Khalid, har gidansu Naja'atu ya je ya gaida malan, ya yi
mashi kyautar manyan riguna na farar shadda har da
turare da kudade masu yawa. Malan ya yi godiya, ya
sanya albarka, da fatan alkairi. Hidimar tayi armashi,
basu zafafa abubuwan ba, anyi komi cikin nutsuwa, aka
tashi cikin farin ciki. Mummy kau murna kamar ta zuba
ruwa kasa ta sha, sai da godiyar Allah take yi. Itama
Naja'atu, kasa yi mata godiya tayi, sai kuka tayi. Hajiya
ta kwabe ta, ta ce ba ta so, da ita da Daddy duk daya, ta
je ta rike mijinta da kyau. Allah ya basu zaman lafiya."
Washegari karfe sha daya da rabi, aka daura
aurensy a kofar gidansu Naja'atu. Kowa ka gani cikin
farin ciki. Naja'atu sai godiyar Allah, har kuka tayi don
farin ciki. Kaunar Daddy wani sirrin zuciyarta ne, ita
kanta ba ta san dalilin da yasa take sonshi ba. Kaunarsu
daga Allah ce, tayi ma Allah godiya da ya mallaka mata
abin sonta, tare da addu'ar Allah ya basu zama lafiya, ya
basu ikon rike juna bisa gaskiya da rikon amana, ya kau
da fitina. Ranar da daddare aka dauke ta daga gidansu
zuwa gidan Hajiya, nan za ta zauna zuwa ranar talata da
za su tafi Abuja.
Daidai gwargwado anyi shagali, amma Naja'atu ta
63
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
ture duk watga bidi'a, kiri-kiri ta soke Dinner Party da
Daddy ya tsara za'ayi. Zainab ta ji haushin ta, kamar ta
doke tga. Wai ta cika son miji, don kada ya sha wahala.
To ita kam wani ra'ayinta ne na daban, ba ta da murnar
da ta wuce tayi ma Allah godiya. A 6angaren Malan, ya
yi rawar gani, dai-dai karfinshi ya yi ma ango sallama
da kudi dubu dari da buhunan abinci. Haka nan itama
Inna ta ba da mai da sauran kayan gara. Da yayar Hajiya
Halima ta karbi kayan cewa tayi, "Aikinta ne, ita ce ya
dace tayi duk wadannan." An gama buki lafiya, ana ta
sanya albarka, kowa ya kama gaban shi. Ita Zainab ranar
litinin ta bi Khalid ya mai da ta makaranta ya wuce
Abuja. Sai su kadai a gidan, Daddy ya rinka wayau,
yana son ya kebe da amaryarshi. Amma fir Naja'atu ta
ki yarda, ba ta yarda ko waya ta hadasu. Haka nan da
dare tana rugan kowa kwanciya, kullum sai ya yi matga
korafi ta waya, ba ta cewa komi sai dai tayi dariya.
Basu bar Katsina ba, sai ranar laraba. Su suka fara
tafiya, sannan Mummy ta bi bayansu. Bisa hanya ya rufe
gilas ruf ya kunna A.C, ga kamshi ya cika motar.
Naja'atu ta haye bisa sit barci yana dan fizgarta, ga shi
Daddy yana matsa mata da mayen kallon shi. Sai ta
rinka jin sanyi, don haka ta makure kanta. Tana jin shi
yana murza 'yan yatsunta da suka sh kumshin lalle ya
kama ya yi ja sosai. Haka nan zabban gwal da ta zuba,
sun kara ma dogayen 'yan yatsun kyau. Tana jin shi ta yi
shiru ta rabu da shi, ta san tsokana ce. Rana ta tafi za ta
fadi, suka shigba garin Abuja, ya juya yana kallon ta ya
ce, "Ba za mu biya gidan Mummy ba fa." Ta tsura mashi
ido duk ta marairaice ta ce, "Nayi tsammanin za ka bari
zuwa gobe, ko Aunty A'isha sai ta rakoni." Ya yi
64
Sirmin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
murmushi yana girgiza kai, sai ya sanya hannaye
duka biyu ya dafe sitiyarin motar, sai da ya yi tafiy
tsawo, Sannan ya ce, "Kin cika son kanki Naja'atu, ya
ce ki tausaya mani, kwana biyu kina bani wahala, kiy
hakuri mu tafi gida, idan an kwana biyu za ni kaiki
wajen Mummyn."
a
Ya dan zuba mata ido, sai ya ba ta tausayi, tayi
murmushi ta jinjina mashi kai. Don haka kai tsaye ya
nufi gidanshi da ita. Bai yi mamaki ba da ya tarda gidan
a rufe, ya san Faridar fushi take yi. Ya nemi layinta
rufe yake, duk da ya tafi ba ta saurare shi ba. Suka fito
tare ya yi amfani da makullinshi ya bude kofar suka
shigba. Gidan ya danyi kura, hakan ya tabbatar mashi
cewa, ta kwana biyu ba ta gidan, ba wai fita tayi ba. Ya
je ya bude ma Naja'atu dakinta ta shiga, shi kuma ya je
yana kwasu kayansu daga cikin mota.
Naja'atu ta shigba cikin dakin, sai ta tsaya kawai
tana mamakin abin da Mummy tayi mata. Ga baki daya
setin'yan italiya ne, ko ba a fada ba, ta san an kashe
naira. Kauna ce ko mai, sai kawai ta ji idanuwanta sun
ciko hawaye. Ta zauna shiru tana gode ma Allah, tare da
yi ma Mummy addu'a. Cikin yanayin Daddy ya riske ta,
ya aje akwatin ya iso kanta yana kallon ta, ya c e, "Meke
faruwa kuma?" Ta ce, "Daddy kalla ka ga abin da
Mummy tayì mani, ko ita ce ta haifeni sai haka, da me
za ni saka mata?" Ya yi murmushi ya janyota cikin
jikinshi ya сe, "Kаada ki samu damuwa, Mummy taña
kaunar ki Naja, fatana Allah ya bamu zaman lafiya da
zuri'a mai albarka, kada ki damu." Ta ji yana neman
zarcewa, sai ta janye jikinta ta shiga kewaye. Daddy
daban ne, kaunar shi wata abu ce mai muhimmanci a
65
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
cikin zuciyarta.
Bayan sunyi sallah, ya fita sawo masu kaji gashin
inji da lemo da madara fresh milk, ya kawo suka ci.
Tana son ta tambaye shi Farida, amma ta rabu dashi. To
shima rashinta a gidan ya tsaya mashi cikin zuciya, har
Karfe tara suna hira ba ta dawo ba. Ta kasa daurewa ta
ce, "Daddy banga Farida ba?" Shima ya zuba mata ido,
sai ya rasa abin da za ya ce mata, baya son ya fadi mata
wata matsala da ta shafi Farida, hakan ka iya janyo
rashin fahimta tsakaninsu. Don haka ya ja bakinshi ya yi
shiru. Itama da ta fahimci akwai wani abu a kasa, sai ba
ta ja binciken ta ba, ta saki maganar suka ci gaba da hira.
Karfe goma ta shiga daki, tayi wanka ta sanya
kayan barci, riga da wando masu santsi jajaye. Ta tufke
gashinta, ta sanya turare masu sanyin kmashi da humra,
ta kara ma dakin kamshin air freshner. Sai ta kwanta
tana karanto addu'o'i. Daddy ya murda kofa ya shigo,
shima ya yi shiri da kayan barci cotton zalla masu taushi
farare, yana rike da robar madara fresh milk. Ya zauna
bakin yana jefarta da mayataccen kallonshi, sai ta ji
zazzabi yana shirin lullubeta, ta kara makure kanta kan
gado. Yayin da wani tunani ya dira a zuciyarta, sai ta
lumshe ido a hankali, tana tuno abubuwa da dama. Ya
aje robar madarar gefe guda, ya shiga kewaye, ya dauro
alwala, ya dawo ya tada ta, ta je tayi alwala ta dawo,
suka yi shirin yin nafila raka'a biyu, suna masu neman
yardar Allah a cikin zamansu.
Ta gaji sosai, ta koma kan gado ta kwanta, yana
kallon ta ya ji wani abu ya daki zuciyar shi. Ya yi saurin
shafa addu'a ya taso ya dawo kusa da ita, ya zuba mata
madara, ya ba ta tana sha, ya rinka janta da hira yana yi
66
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
mata nasiha dangane da zaman su. Ya ci gaba da janta
da hira, yana ba ta labarai masu dadi na ban dariya. Don
haka ya samu kanta yanda yake si, suka yi barci mai
dadi, cikin farin ciki da annashuwa.
Da safe barci yake yi sosai, Naja'atu ta janye
jikinta ta shiga kewaye tayi wanka da ruwa mai dumi, ta
dawo daki tayi shiri, cikin wata atamfa 'yar super fara,
siket da riga