hankalin kowa ya kwanta."
Naja'atu ta runtse ido tana jinshi, yayin da zuciyarta ta ke dakan uku-uku. Khalid ya na sonta, ya na
da buri a kanta, anya zata iya hakura da shi.? Abin da zuciyarta ta rinka tunani kenan yayin da shi kuma ya rinka janta da hira, ta yi imanin har ga Allah abin da ke cikin zuciyarshi ne ya ke fada. Sai ta yi murmushi kawai
tana hango jan a ikin da ke tunkaro ta.
Da yamma ya iso gidan Naja'atu ta fita, su ka gaisa, ya na fara kallonta, kamar zaya lashe ta, ta yi mashi kyau ta goge ta kara girma, sai ya ji ya kara sonta. Ta shigo gaba ya na biye da ita har cikin gida su ka gaisa da Mummy ta yi mashi murna da fatan alkairi, sun jima suna hira sannan Mummy ta koma cikin daki, yayin da Naja'atu ta shiga kicin ta rinka fito mashi da abinci iri-iri, shi kuma kallonta kawai ya ke yi kamar ya lashe ta, shi kadai yasan yarda ya ke jin yarinyar a
ranshi. Har ya ja ta rinka jin nauyinshi, kallon ya yi yawa. Cikin natsuwa ya ke cin abincin su na hira. Har ya
gama ta kwashe kwanonin, ya jata suka koma waje, cikin gidan ya na jin nauyin Mummy ya fi son su kebe daga shi sai ita, ya rinka fadi mata asirin zuciyarshi. Cikin yanayin yammacin da iskan sanyi ta fara kadawa, Naja'atu ta makure kanta cikin kujera tana
sauraren kalaman Khalid duk ya jagiıla mata lissafi,
yanzu da ya ke gabanta, sai ta ke jin ba za ta iya hakura
da shi ba, yayin da wani irin abu daga gare shi mai
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
kamar mashi ya ke cakar zuciyarta, duk sai ta sukurkuce
ta shiga rudu na rashin sanin takamaimai abin da ya
kamata ta yi, "kada fa ta zamo mai ruwan ido?"
Tunanin ta ya tsaya can, yayin da ta hangi maigadi
ya na bude get, motar Daddy ta kunno kai cikin gidan.
Ta zuba mashi ido kawai har yaje ya aje motar, sannan
ta juya ta na kallon Khalid, ya yi dariya, ya ce "Ango ne
ko.?" Itama ta yi murmushi na karfin hali, yayin da
Khalid din ya mike ya nufi Daddy wanda shima ya nufo
shi, su ka yi musabaha, su na gaisawa. A hankali Daddy
ya jefe ta da wani mayen kallo, karara taga tsabar
kishinshi, duk sai ta kara rikicewa, ta tsani ganin bacin
ranshi, kamar ta gudu cikin gida amma ta dake ta zauna,
tana kallon su suna magana amma Daddy ya dan canza
yana maganar kamar ba ya so, matsalarshi kenan zafin
kishi.
Gaba ki daya su ka tako zuwa in da take, ta yi
saurin ce mashi "Ina yini.?" Don ba ta san abin da zaya
ce ba, bai amsa ba sai dai ya ce "Naja." Ya juya ya mika
ma Khalid hannu, suka yi sallama, ya juya zaya shiga
gida, amma sai ya juyo ya ce mata "idan kin gama ina
jiranki." Ta ji gaban ta ya fadi, da sauri ta amsa, "To".
Ya shige abinshi, Khalid ya koma ya zauna su ka ci gaba
da hira, amma da kanshi ya lura cewa hankalinta baya
jikinta, ya rinka nazarinta, ya na tunanin wani abu. Rana
ta tafi yamma zata fadi, ya duba agogo ya na kallonta ya
ce "Bari in bar ki kije yayanki ya na jirankí ko? Gobe da
wane lokaci zani same ki?" Ta dan daga kai tana tunani,
sai ta yi murmushi ta ce "Zuwa dare ko." Ya ce "Shi
kenan Allah ya kaimu." Su ka mike tare zuwa wajen
mota, ya bude sit din baya, ya fiddo leda babba cike da
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
kayan lashe-lashe choculate 'yan kasar waje, da greeting cards masu kyau da tsari, ya ba ta ya ce "Sai yazo goben.' Ta na tsaye ta daga ma shi hannu har ya fita, sai
ta yi murmushi zata koma ciki, suka yi kicibis da Daddy
ya na jefarta da mayen kallonshi, sai ya bata dariya ta
cc, "Oh, ni Naja Daddy ya zan yi da zafin kishinka ne.?"
Ya yi murmushi kawai ya mika hannu ta ba shi
ledar ya zauna bisa kujcra ya na bincike, sai ya zare card din ya mika mata choculate dinta, ta zuba mashi ido ta
ce "Me za ka yi dasu.?" Ya ce Naga ba su da wani
amfani ne shi yasa na raba ki dasu." Ba ta ce komi ba, ya
tsare ta sai ta fadi mashi yarda su ka yi da Khalid ya
sanya ta rinka yi mashi rantsuwa kan cewa ba su yi wata
magana ba mai muhimmanci, sannan ya yarda amma ya gargade ta kan cewa ta hanzarta sanar da shi gaskiya, ba
ya son ya na ganinta da shi. Dariya kawai ta yi ta amsa "to." Ya ta iya da rigimar Daddy?.
Da aka kira Sallah, ya fita Masallaci bai dawo ba sai da aka yi sallahr Isha'i ya sanya ta kawo mashi abinci, ya zauna ya na ci, Mummy na kallonsu bata ce komi ba, bata son ta cika sanya masu ba ki, amma idan ita ce Naja, ba za ta auri mai mata ba, alhalin ga saurayi,
ya mika mata wata leda da wasu card din sabbi a cikin
ta bude ta na dubawa, kalaman masu dadi da sanyaya zuciya, sai ta ji ta fi son su akan na Khalid din, a hankali
ta dago ta na kallonshi, sai suka yi murmushi, Daddy daban ne ya iya sanyaya mata zuciya, don haka fushi ya yi hankalinta ya ke tashi haka nan idan shi ya bata mata
rai, ba ta aje abun a ranta, saboda tasan ba'a zuwa ko'ina
zaya wanke laifinshi.
Dare ya tafi sosai, ya na zaune hankalinshi kwance
A3
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
su na hira, Naja'atu ta rinka yi mashi korafin ya tafi
gida, ya baro diyar mutane ita daya, yana jinta ya yi
shiru ya kyal e ta, sai da Mummy ta fito ta kora shi,
sannan ya tashi ya tafi. Babban takaicinshi guda, idan
ma yaje gidan 6acin rai ne zaya taras, ko kafin ya fito
din nan da yamma, sai da su ka yi dada kaca-kaca da
Farida, saboda ya dawo wurin aiki babu abin da zaya ci
ba ta yi girki ba, wai ba ta gidan ta fita. Ya ce "to waye
ya baki izinin fitar.?" Babu abin da ya fito bakinta sai
cewa ta yi, "ai ba an kawo ni ba ne don ka rinka kulle ni
cikin gida ko kuma kai ina hana ka tafiya in da ka ké
so?" Abun ya bata mashi rai da ya fara fada itama ta
rufe shi da bala'i, rashin hankalin Farida ya yi yawa,
abun ya na damunshi har gidansu yaje ya fadi ma mama
kuma gabanshi tazo ta yi mata fada sai ma ta fasa ma
mamar kuka, ta rinka zakulo laifi iri-iri tana dorama
Daddy, Mama tasan halin Farida, sarai, don haka bata
dauka ba, ta rinka yi mata akan ta rinka zama tana gyara
gidanta da kyau, ta rinka yima mijinta girki da sauran
hidimominshi, amma ina ta yi nisa ita dai hutu ba ta ki
ba ace ya aje mata 'yar aiki da za su rinka yi mata komi,
shi kuma ya kafe ai dadin sai ya yi mata yawa, don haka
yanzu barci kadai ke zaunar dashi gida.
Washe gari tun yamma ya na gidan ya kasa ya
tsare har- dare lokacin da Khalid ya iso ya tambayi
maigadi Naja'atu, ya ce tana nan, don haka ya turo ayi
mata magana, saboda ya kira layinta a rufe tana kicin
tana aikin abincin dare, da ya ke ranar Mick bai zo ba,
yayin da Daddy ke hakince cikin falo ya na kallon
wasan kwallon kafa, maigadin ya leko ya na fadin sako.
Dadd y ya juya ya na kallonshi, ya ce in ji wa? Ya ce
AA
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
"Likitan nan da yazo jiya." Daidai lokacin Naja'atu ta fito daga kicin din Daddy ya hana ta magana, ya ce "Ka fada mashi ba ta nan sun fita." Maigadin ya juya ya fice, yàyin da Naja'atu ta tsaya sokoko ta na kallon Daddy ba ta ji dadin abin da ya yi ba, shima kallonta ya ke yi, cikin ido da wani irin yanayi sai ta kasa magana ta koma kicin.
Khalid na zaune cikin mota maigadin ya sanar da shi sakon da aka ce ya fada. Ya jinjina maganar a
ranshi, ya ce "Amma da ka ce ta na nan ba.?" Ya yi cariya ya ce "Ban san ta fita ba, ina jin muna sallah ne ta fice." Ya jinjina kai, bai ce komi ba, yaja motarshi ya fice, wani abu ya tsaya mashi a zuciya, musamman
ganin motar Daddy a gidan. "Anya ba arar mata baki aka yi ba, aka ci ma ta albasa.?" Ya aje abun a ranshi, ya rinka tafiya ya na tunanin wani abu, jiya da su na tsaye da Daddy ya na lura da irin kallon da ya rinka yi ma ta, haka nan da za ya shiga ya ce ya na jiranta sannan tun daga lokacin Naja'atun ta canja, anya babu wata a kasa? Zuciyarshi ta rinka raya mashi abubuwa da dama, amma
da ya yi tunanin Daddy ya yi aure, sai ya share komi, ya yarda cewa ba ta gidan.
Washe gari da hantsi yazo gidan, Naja'atu na gida
sun jima su na hira, ya ce "Amma ina son ki rinka
kokarin cika alkawari, jiya kin yi mani laifi ke da kanki
ki ka bani lokacin da zani so, shi ne na zo aka ce kin fita,
'sannan kin kama waya kin rufe." Ta yi murmushi ta се
"Ka yi hakuri, insha Allahu ba zani kara ba." Ya harare
ta da wasa, ya ce "To wai ma ina kika je.?" Ta yi dariya
ta ce "Mummy ce ta aike mu ni da Ibrahim, da kafa ma
mu ka tafi, babu nisa ban yi tsammanin zaka zo da wuri
45
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
ba, sai da na dawo Malam Isa ya ce kazo har ka tafi." Ya
jinjina kai ya amince da ita, ya gyara zama ya na
kallonta, ya ce "mu koma kan maganar mu, zuwa wane
lokaci kike jin zamu je Katsina? Ina son in yi ma Malam
halarci, yarda na dauki alkawari, kuma shima ya cika
mani, nasan saboda ni ya barki har zuwa wannan
lokacin, tunda na dawo nasan zaya so ya ga anyi
abunnan da wuri, don haka ki fidda mana rana muje in
yi magana dashi. Sai in tura manya ayi maganar aure, na
fadi maki a shirye nake kuma kema nasan kin shirya, ko
ba naka ba.?" Ya zuba ma ta ido, sai ta yi murmushi ta
ce, haka ne sai dai da kadan yi hakuri ka kara hutawa,
nima akwai nazarin da nake yi.
Ya zuba ma ta ido ya na mamaki, ya ce "Nazari a
kaina, ko me.?" Ba ta ce komi, ba shi ma sai ya rabu da
ita, bai zafafa bincike ba. Da zaya ta fi ya fiddo ma ta
tsaraba akwati guda, har da su Mummy. Zainab da
Ibrahim ta dube shi cikin ido ta ce "Na yi tsammanin
zaka barsu ka zuba lefe? Ya ce "Na lefe daban, wannan
ai tsaraba ce na ce ko? Ta jinjina kai ta yi godiya, duk
sai ya ba ta tausayi, su ka yi sallama ya ja mota ya tafi.
Jikinshi ya fara sanyi cikin yanayin ya shiga
gidanshi, Sulaiman na kwance cikin falo, ya ba za
takardu ya na ta karatu sai ya ji tausayin yaron, babu
abin da ya kai karatu cin rai, to sai dai shi ne rayuwar ya
wuce cikin daki ya zube kan gado ya na tunanin
abubuwa da dama, da kyar ya ji karfin hali ya shiga bayi
ya yi hanka da ruwan dumi ya shafe jikinshi da lotion
mai sulbi ya karama dakin kamshin Airfreshner ya sake
rigar bacci doguwa mai kauri ya daure da belt din ta ya
hau gado, amma ya kasa barci koda ya ke shi kanshi ya
AL
Sirmin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
san lokacin barcinshi bai yi ba, damuwa ce ta sanya yayi
shiru da wuri. Ya rinka saka abubuwa da yawa a ranshi.
Kamar an tsikare shi ya tashi zaune ya dauki waya
ya na neman layin Zainab itama cikin daki ta ke kwance
ta na karatu, ta kalli wayar kamar ba zata dauka ba,
amma ta daure ta dauka ta yi murmushi su ka gaisa ta na
tambayarshi gajiya. Ya ji dadi a ranshi, lokuta da danma
ya kan ji dama Zainab ce Naja'atu ta fi sakewa yi hira
sosai, akan Naja. Ya ce wata tambaya zan yi maki
Zainab, amma don Allah kiyi tsoro Allah ki fadi mani
gaskiya komin dacinta." Ta ji gabanta yana faduwa,
amma ta ce "Ba damuwa, idan dai na sani zani fadi
maka." Ya dan shaki lumfashi ya fesar sannan ya ce
"Me ke faruwa da Naja'atu ne.?" Ta ce "Wani abu kа
gani.?" Ya ce "E to, ni dai ina zargi, sai nake ganin
kamar akwai wani abu da ta ke kokarin boye mani."
Zainab ta ce "Gaskiya bani tsammani."
Ya jinjina kai, ya ce "Shi kenan, bari in yi maki
wata tambayar me ke tsakaninta da Dadd'y.?" Wuta ta
dauke ma Zainab ta rumtse ido tana salati, iata kam bata
so ace ta bakinta ya fara jin wannan maganar ba ga shi
kuma ya daureta, ta jim ta kasa cewa komi. Ya sassauta
murya ya na magana, ya ce "kada ki, ji komi, Zainab ki
fadi mani gaskiya, insha Allahu hakan ba zaya janyo
wata matsala ba, sai ma alkairi." Zainab ta saukar- da
ajiyar zuciya ta ce "Gaskiya ban so ace daga bakina ka
fara jin wannan haganar ba, sai dai ka riga ka daure ni,
koma ban fadi ba, daf ake da azo in da zaka sani don
haka ina son don Allah ka sanya fahimta cikin abun nan,
kada haka ta janyo rabuwarmu da kai maganar gaskiya
Daddy neman Naja'atu yake yi, kuma suna son juna, don
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
gaskiya idan bacin maganarka da ita, da yanzu an yi
aurensu."
Khalid ya rumtse ido yana jin wani abu ya na yi
mashi yawo cikin kai, sai ya rufe ido ya na neman
taimakon Allah, ya ce "Shin Zainab kina jin Naja'atu na
sona har yanzu.?" Ta yi murmushi ta ce "Naja'atu na
sonka, sai dai son Daddy ya rinjayi zuciyarta, idan har
na ce ma ka Naja'atu zata iya hakuri da Daddy na yi
Karya." Khalid ya rinkajuya maganar a ranshi, Zainab ta
ce "Amma don Allah kada ka rike ta a ranka, kasan shi
so yarda ya ke daga Daddy har Naja'atu suna son juna
tun kafin ka hadu da ita, amma su ka kasa fadi ma juna,
ina ganin zuwanka ne ya tunzura Daddy ya kasa hakura,
ya yi mata magana, wanda mu duka mu ka rinka dauka
wasa ne, ganin cewa ya na shirin yin aure, ita kanta
Naja'atu ta rinka kokarin ganin ta yakice shi a ranta, su
ka dan ja da baya amma yanzu abun ya dawo danye
sharaf, a gobe idan aka ce za'a daura masu aure a shirye
su ke."
A hankali ya saukar da ajiyar zuciya yayi ma
Zainab godiya ya rufe wayar sai ya rufe ido ya koma ya
kwanta, sai dai duk irin yarda yaso ya runtsa abun ya
faskara, me ya sa soyayya ta yaudare shi irin haka? Sai
ya rinka jin tausayin kanshi, har safe ya kasa rumtsawa
ya na son Naja'atu zuciyarshi ta rinka raya mashi yaje yasamu Daddy ya roke shi ya bar mashi Naja'atu ita ce
rayuwarshi, amma wata zuciyar ta rinka karanta mashi
ya yi hakuri, sai ma ya daina ganin laifin Naja'atun ya
bar ma Allah komi, tun a ranar ya fara addu'a, Allah ya
ba shi madadin Naja.
Kwana biyu, ya na son zuwa wajenta amma ba ya
Sirin Zoci.. Sa'adatu Samiu Kankia
jin dadin zuciyarshi, don haka ya daga mta, washe gari
ya yi shiri ya tafi Kano, ya ji dadin ganin 'yan'uwanshi,
daga sadiya har Zulaihatu, sun samu ci gaba sosai, su na
zaune lafiya da da yaransu. Kwananshi daya da daddare
ya yi hira gidan Alhaji Buba Aliyu ya na kaunar dattijon
ba ya da kamarshi a rayuwarshi.
Washc gari ya dawo Abuja, har yanzu tunanin
yarda zaya tunkari Naja'atu ya ke yi, amma a zahiri
zuciyarshi ta gama karewa lamarin. Ranar da daddare ya
je wajenta, Zainab na nan ta iso don haka da ya aika tare
su ka fito da suka gaisa ta koma ciki ta ba su waje.
Su ka zauna shiru kamar su na jin nauyin juna, sai
ya sassauta ldanuwan akanshi, a hankali ya yi murmushì
ya ce "Hajiya Naja'atu kenan, yaya jin dadi." Ta yi
murmushi kawai, nauyinshi take yi ya gyara zama yana
kallonta, ya ce 'kinsan abin da ya kawo ni wajenki yau?
Ta zuba mashi ido kawai, ya ce "Laifi ki ka yi mani,
kuma gaskiya, ban ji dadin rufe mani da kike yi ba, idan
za ki tuna, kafin in tafi nasha yi maki magana, kan
dangantakarki da Daddy, amma sai ki ka boye mani ki
ka ce babu komi alhalin da kaina ina ganin wasu
abubuwa da ke faruwa, kinga a nan ba ki kyauta ba, ya
dace da dadi babu dadi, ki fadi mani gaskiya kinga
yanzu idan daban sanya tunani ba, sai in zarge ki da
yaudarata, sai dai kula irin haka ba kyau.
Idanuwanta cike da hawaye ta dube shi, duk sai ya
ba ta tausayi ta marairace ta ce "Na yarda na yi maka ba
daidai ba, amma don Allah ka yi hakuri." Ya daga ma ta
hannu ya ce "is okey, ni ba n ce kinyi mani laifi ba, ai in
da na yi fushi ba za ki sake ganina nan ba kuma na yarda
shi aure nufin Allah ne, wani ba ya auren matar da ba
49
Sirrin Zuci.. 4 Sa 'adatu Saminu Kankia
tashi ba, na gode akan damar da ki ka bani har kika
tsaya ki ka saurare ni, tsawon wannan lokacin. Haka nan
ni ba zani iya yin jayayya da Daddy akan ki ba, saboda
tare na ganku, me yiwuwa ma ki fi sonshi akaina, to
nima ban raina ba, na sani kin soni, kuma nima mai
Kaunarki ne, ina fatan za ki rinka saka ni cikin addu'arki,
Allah ya bani madadinki."
Kalamanshi su ka karya ma ta zuciya, a hankali ta
saka mashi kuka, ta na ba shi hakuri, shima kukan ya
tsuma mashi zuciya, ya rinka jin kukan har cikin ranshi
ya kasa ce mata komi, sai ya tsura ma wasu furanni ido
ya na jin sautin kukan ta da muryata ta na ba shi hakuri.
Ya daga ma ta hannu ya dakatar da ita ya ce "Naja'atu ni
ban ce ina zarginki ba akan wannan abun, so wani sirri
ne na daban a zuciya, ke kanki ba ke ce ke sarrafa ta,
don haka mu duka mu dauka wani nufi ne daga Allah,
Allah ya sa haka shi ne mafi alkairi gare mu ba ki daya."
Ta jinjina kai ta na kallonshi, zuciyarta ta yi sanyi ta yi
Imanin da zuciya daya ya ke maganar, sai ta ji ta natsu
ta goge idanuwanta ta zauna sosai ta ce "To yanzu yaya
za'ayi? Ya zuba ma ta ido, ya ce "Kamar yaya.?" Ta ce
yanzu haka za ka ci gaba da zama ba zaka nemi wata
ba.?" Ya yi dariya ya ce "To da ma ba haka nake zaune
ba? Sai dai insha Allahu zani ci gaba da dubawa, idan na
samu mai irin halayanki sai na yi ko ba yanzu ba.
Naja'atu ta saukar da ajiyar zuciya, tana wani
tunani, sai ta dago tana kallonshi, ta ce "Yanzu ba zaka
iya neman Zainab ba? Ta na da hankali kuma ra'ayinku
zaya zo daya. Wani abu ya so ki zuciyarshi kusan abin
da ya ke tunanin kenan duk cikin kwanakin, sai dai idan
ya duba wasu abubuwa, ya kan sare koba komi Zainab
50
Sirmin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
big girl ce, ni kuma kin san matsayina talaka ne dan
talaka." Ta yi murmushi ta ce "idan dai kana jin kana
sonta to ka neme ta babu wani abu su na da saukin kai,
kuma kana da kafa a wajan Mummy ko gobe ganin bai
ka na take yi, da na yarda da Daddy mai mata, alhalin
ina da kamarka, tasha fadin cewa ta na son ta ga matashi
irin ka mai ilimi da kokarin neman na kanshi, don haka
ba zata ba da matsala ba, itama Zainab din sauki ne da
ita, in dai ka ji zaka iya to ka shiga kawai.
Ya jinjina maganar a ranshi, sai ya dube ta ya ce
"To ki fara tuntubarta ki ji idan za ta amince." Naja'atu
ta yi dariya ta ce "Idan na yi haka kenan nina hada ku,
ba ra'ayin kanka ba ne." Sai ya jinjina kai ya fahimce ta
sosai, ya ce "Shi kenan zani duba." Naja'atu ta zuba
mashi ido sai su ka yi dariya baki daya ya yi mata
godiya kuma duk sai ta ji babu dadi. Har ya tafi tana
tsaye kamar an zare mata lakka, sai ta ke ganin kamar ba
ta kyauta ba, amma bakin alkalami ya riga ya bushe.
Ta koma cikin gida, tana ba Zainab labarin abin da
ya faru, amma ba ta sanar da ita tsarin da suka yi ba.
Zainab ta yi dariya ta ce "Shi kenan hankalinki ya
kwanta kin bi son zuciyar Daddy Allah ya sa shi ya iya
cika maki alkawari, in kuma matarshi ta hana ba shi
kenan ba kin yi sakin na hannu." Nan kuma sai zuciyata
ta buga, halin maza daban ne, sai dai anya Daddy zaya
iya yi mata haka? Ranar ta kwana addu'a ta na neman
taimakon Allah.
Washe gari Zainab ita daya kwance cikin daki ta
na nazarin key point, rana ta yi sosai, amma ba ta fita ba,
akwai abubuwan da ta ke so su zauna ma ta cikin kai,
don haka ta takura kanta cikin daki. Wayarta dake
51
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
manne wajan caji ta yi kira, ta mika hannu daga in da ta
ke ta ciro ta, ganin Khalid ne ya sanya ta yi murmushi ta
aje littafin sannan ta amsa mashi da sallama, ya ce ko na
tada ki barci ne? Ta yi dariya ta ce "Haba dai barci
yanzu fa na neman sha biyu, na tashi tun dazu." Ya ce
"To yaya garin.?" Ta ce "Gari ku za'a tambaya, tunda ku
ke fita cikinshi, mu karatu ba ya bari, yanzu haka
cikinshi nake." Ya ce "Da kyau, sai in ce Allah ya
taimaka." Ta ji dadi ta lumshe ido ta amsa, "amin." Su
ka dan yi shiru, ya na tunanin yarda zaya 6ullo ma ta,
sai ya dake ya ce ina Naja'atu ne? Ta yi murmushi ta ce
"Ina jin ta na falo, ni daya ce a daki, kiranta za'ayi? Ya
ce "A'a rabu da ita ai kuma yanzu ta zama Yayata, ba ta
fadi maki sakon da na ba ta ba ne.?"
Ta ce "Ba ta fadi mani ba, wani abu.?" Ya ce "Ki
samu lokaci ta fadi maki sakon da na ba ta fadi maki na
baki zuwa gobe kiyi nazarin shi sosai, in Allah ya kaimu
da yamma zani zo in ji amsa a bakinki bari in barki ki
huta, sai kin jini." Bai jira ta ba shi amsa ba, ya rufe
wayar. Zainab ta zuba ma wayar ido ta na zargin wani
abu sai ta yi murmushi ta na girgiza kai, ta aje wayar, ta
koma ta kwanta, ta dauki littafi ta na dubawa, amma ta
kasa fahimtar komi, wani abu ya dasu cikin zuciyarta.
Har yamma abun ya tsaya ma ta a rai, amma ba ta yi ma
Naja'atu maganar ba, haka nan itama ba ta sanar da ita
yanda su ka yi da Khalid ba.
Da dare Daddy yazo, su na tare ya rinka yi mata
korafi akan Khalid, wai ta kasa yin wani abu, shi fa ya
fara gajiya da jira. Ta yi murmushi ta ce "Ka cika saka
Khalid a ranka, ni kuwa banga abin da ya tsare ma ka b
a, gashi ma ka yi mashi kora da hali, ya yi fushi ya daina
52
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
zuwa." Ya rinka dariya ya ce "Wai don Allah da gaske
kike.?" Ta ce "Ba haka ka ke so ba? Ya yi hakuri ya
sallama maka." Ya gyara zama ya na kallonta, ya сe
"Yaya aka yi.?" "Da kanshi ya fahimta, don haka ya cе
ya hakura, sai dai daga baya ni kaina sai naga kamar na
yi wauta, kada in yi sakin na hannu." Ya cc "Kamar
yaya.?" Itama kallonshi ta ke yi, ta ce "ka da uwargida
na murda kamnu ka bultse mani." Ya yi dariya ya ce "Ai
mai raba ni da ke Naja'atu sai Allah, kuma za ni nuna
maki ni dan halak ne, ki bani kwana biyu."
Hirarsu ba ta dade ba ranar, ya salame ta sannan
ya shiga wajen Mummy su ka yi magana tsakaninsu. To
kuma washe gari, mummyn ta kira ta cikin daki, ta na
tambayarta in da maganar Khalid ta tsaya, saboda shi
Daddy ya matsa, ya na son cikin satin aje Katsina kan
maganarsu. Naja'atu ta ji mummy cikin natsuwa ta yi
mata bayanin komi, ba ta sarakuwa da Mummy, haka
itama diya ta dauke ta. Mummy ta ce "Kuma kin amince
kina son Daddy za ki aure shi.?" Sai ta ji kunya, ta sarda
kai tana dariya, a hankali ta daga kai itama dariyar ta yi,
ta ce "To Alhamdulillahi, na ji dadi da ke da Daddy duk
daya ku ke wajena, don haka sai kun yi hakuri da juna,
haka nan ki zauna da abokiyar zamanki lafiya, ba ni son
fitina, Allah ya sanya alkairi."
Kwana biyu Khalid bai fullo ba, har Zainab ta fara
shirin komawa makaranta, ana gobe za