har cikin ranta ba ta son
zamanta gidan Daddy yarda taso, Mummy ta barta ta tafi
Katsina ta zauna can sai ta dawo, to ta hana ta ce ta bari
idan ta dawo sun je tare. Don haka ba ta da zabi sai
yarda aka yi da ita, amma alkawari ne ta daukar ma
kanta, komi Farida zata yi, ba zata biye ma ta su yi
rigima ba, insha Allahu lafiya za su rabu.
Da su ka isa, Daddy ya na gaba su na biye da shi
har saman benen, hawa na uku suke ya murda kofar ya
shiga su ka bi bayanshi, Farida na kwance falo sanye da
wata riga body hug, ja, da bakin wando kanta babu
kallabi ta daure kitson da ribon zaune take tana gyaran
akaifa, suka yi mata sallama ta dago kai ta na kallonsu,
ko shi maigidan bata yi mashi kallon arziki ba.
Su ka yi tsaye sororo, Zainab taja hannun Naja'atu
14
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
su ka zauna ta ce mata "Anty Farida ina yini.?" Ta amsa
ma Zainab lafiya lau, amma da Naja'atu ta gaida ta ko
kallon arziki ba ta yi mata ba, taja tsoki ta tashi ta yi
shigewarta daki. Daddy ya jinjina kai cikin damuwa,
amma sai ya share ya ce "Ga daki nan, sai ku shigar da
kayanku, ku zauna ciki." Zainab ta amsa mashi "To."
Amma ita Naja'atu kamar ruwa ya ci ta, kasa cewa komi
ta yi mamakin halayyar da Farida ta nuna mashi take yi,
ai matsayin miji ya wuce wasa a kalla komi ya hada su
ya zama na su kadai su ka sani ba wai har gaban mutane
ta nuna ba, matsalar wasu matan kenan basu iya boyc
damuwarsu ko kuma matsalar dake tsakaninsu da
mazajensu, sai sun fiddo fili har wanda bai san anyi ba
ya gane masu, lamarin sai dai du'a'i.
Ta saukar da ajiyar zuciya, tana kallon Zainab,
cikin halin ko in kula Zainab ta ce "Taso mu shiga daki
mu huta." Su ka shiga dakin lafiya lau da katon gado,
Zainab ta kunna AC ta fada kan gado da alamun gajiya,
yayin da Naja'atu ta zauna a sanyaye take kallon Zainab,
ta ce Zainab kina ganin zamanmu da matar nan zaya
yiwu? Ni gaskiya bani son fitina, tashi ki kaini gidan
Anty Aisha in zauna can, in ke za ki iya ki zauna."
Zainab ta yi murmushi ta ce "Kema din ba in da za ki je
muna nan, idan ba ta iya zama damu ta tafi, ai ba gidan
ubanta ba ne." Naja'atu ta ce "Amma gidan mijinta ne."
Ta ce "Mu kuma na dan'uwanmu ne, ke ba ri fa kiji in
gaya maki, wallahi duk matar da kika ga ana kuka da ita
kan cewa ta buwayi dangin mijinta, ta hana su zuwa
gidan dan'uwansu, samu tayi, sai in shi mijin ya bata
dama, kuma ta yi sa'a ta samu 'yan'uwan da ba su san
abin da suke yi ba, ai dama da irin haka ne suke fara
15
9
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
samun dama, su rinka yi ma mutane iskanci, to mu ba
zamu ba ta wannan damar ba, ai ko shi Daddyn da ya ce
mu zo nan din mu zauna yasan za'a yi haka, amma don
ya nuna mata.matsayin 'yan'uwanshi da shi kanshi
matsayinta, shi yasa ya ce muzo ju zauna din, don haka
ki saki jiki, muna nan sai ranar da Mummy ta dawo."
Naja'atu ta jinjina kai ta mike ta shiga kewaye ta
dauro alwala, sai da ta yi Sallah sannan ta kwanta. Ba su
fita ba haka nan itama Farida ba ta zo in da suke ba, har
yamma tayi Zainab ta sauko taje ta fiddo masu kayansu
dagą cikin mota, su ka shirya cikin daki, sannan su ka
fito falo su na jiran fitowar matar gidan ta fito ta fadi
masu abin da za su kama mata na aikin buda baki, amma
shiru ta yi zamanta cikin daki, suna zaune cikin falo
suka yi tsuru, ga magaruba na karatowa, amma ko
sanwar ruwan zafi ba a dora ba, sau uku Zainab na
kwankwasa mata kofa amma ta ki fitowa. Don haka ta
ce su shiga kicin su dafa abin da suke so. Naja'atu ta се
"A'a, Zainab kada ki farfa, idan muka yi haka mun shiga
hakkinta, kuma duk abin da ta yi ba mu da gaskiya, ba
ki san tsarinta ba don haka mu bari ta fito ai dai ko don
cikinta ta fito ta dafa."
An kusa kiran Sallah Daddy ya shigo gidan ya dan
zuba ma Naja'atun ido, tana kwance kan kujera tana jin
shi ta lumshe ido kamar tana barci yanzu ita tausayinshi
ma take ji ya dubi Zainab wadda har ta fara kulewa, ya
ce ma ta "Yaya.?" Ta ce "Lafiya lau." Ya ledka kicin bai
ji motsin komi ba, ya fito yana kallon Zainab ya ce "Ya
ya ku ke zaune ba a dafa komi ba, yamma ta yi fa."
Zainab ta ce "To ai ba ta fadi abin da za'a dafa ba." Ya
ce "Ta na ina.?" Ta ce "Tun da ta tashi ta shiga daki har
16
P
4
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
yanzu ba ta fito ba." Da saurinshi ya nufi dakin, ba su
san yarda ya yi da ita ba, sai gashi ya fito ya ce "Shi
kenan bari in fita in kawo maku abin da zaku ci, amma
zani tsaya in yi Sallah, akwai lemu cikin firij, sai ku fara
amfani da shi." Ya juya ya fita.
Naja'atu ta bude ido tana kallon Zainab, su duka
suka jinjina kai, lamarin sai du'a'i. Suna cikin daki sun
gama sallah, Farida ta fito ta shiga kicin ta hada tea din
ta mai kauri ta soya kwai ta dauki abin ta ta shiga
dakinta. Lamarin sai ya daina 6ata ma Naja'atu rai a
ganinta har da rashin wayau ke damunta, in har tana da
wayau mijinta ba abin wulakantawa ba ne, to ita da shi
take tunkaho ba ta san cewa duk irin son da yake yi
mata matsawar ta ci gaba da bata ma shi rai sai an wayi
gari babu son sai ma tsana tsakaninshi da ita?.
Da ya dawo yayo masu takeaway, abincin na
Restaurant mai dadi, Zainab ta fita ta karbo masu nasu
su ka zauna cikin dakin nan suka yi buda bakinsu. Da
Asuba kuma tea su ka fito su ka hada su ka sha su duka,
abin mamaki ya ke ba su Zainab ta ce "Za ta kira Mummy ta fadi mata halin da su ke ciki, amma Naja'atu
ta hana ta ce "Ba'a shiga cikin harkar aure, yanzu idan
kin fadi mata ranta 6aci zaya yi, ta tsane ta alhalin mijinta kuma yana sonta, kinga daga nan sai rashin jituwa ta shigo, mu yi hakuri kawai, duka kwana nawa
ne zamu fita mu bar ma ta gidanta?" Zainab ta cе
"Amma Naja'atu kina ganin abubuwan da ta ke yi fa.?"
Ta ce "Na gani, kuma daga ni har ke 'yan kallo ne,
wanda ya aje ta abun bai dame shi ba, sai ke.?
Zainab ta cije lebe cike da takaici shi kanshi
Daddyn ganin sakarcinshi take yi, kamar Farida ace tana
17
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
neman gagararshi? Karfe sha daya su ka yi wanka, so su
ke suje gidan Anty Aisha daga can su karbo dinkunansu,
sun gama shiri su ka fito falon Daddy na kwance kan
kujera da Jarida a hannunshi, yana dubawa ya sauke
jaridar yana kallon Naja'atu abun har ya bata kunya ta yi
mashi kyau yarda yake sonta, to sai dai ya dauki
alkawarin ba zaya shiga harkarta don a zauna lafiya,
amma Farida ba ta yarda da haka ba, har tana ikirarin
matsawar Naja'atu ba ta bar gidan ba to kuwa ita zata
tafi ta bar mata gidan akan haka sunsha rigima daren
jiya, da ya biye mata sai ya kai ga dukan ta.
Ya dan lumshe ido har yanzu akwai damuwa tare
dashi Zainab ta zauna yayin da Naja'atu ta jingina da
kujera gaba ki daya su ka gaida shi, ya saki fuska ya na
amsawa ya zuba ma Zainab ido ya ce, sai ina kuma? Ta
ce gidan Anty Aisha zamu je daga can mu biya wajen
Tela idan ya gama dinkunanmu mu karbo. Ya jinjina kai
sai ya dubi Naja'atu a hankali da sigar sadar da wani
sako gare ta. Ta fahimce shi sarai, amma ta janye
fwayar idonta akanshi tana kallon akwatin talabijin, ana
wasan kwallon kafa, ta yi murmushi ta na jinjina kai,
Daddy daban ne har yanzu yana nan da kwakwar kallon
Kwallon, ga kuma karatun Jarida ya na yi, duk a lokaci
daya ko wane ya ke yi?.
Ya dubi Zainab, ya ce "Amma ba za ku dade ba
ko.?" Ta yi murmushi ta ce "Da wuri zamu dawo, amma
sai ka bamu kudi, an kara mai a mota, ya yi kasa sosai."
Bai ce komi ba ya aje jaridar ya tashi ya shiga cikin daki
bai dade ba ya fito ya ba su su ka yi mashi sallama su ka
fice. Su na tafiya bisa hanya Zainab ta rinka korafin
yanayin zaman gidan, sam ba ta gamsu da shi ba, Daddy
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
bai dace mata ba, ko da ya ke an ce dama abin da ka fi
so ya fi wahalar da kai, me yiwuwa son da ya nuna ma Faridar ne ya janyo wannan rainin tsakaninsu, daren jiya
tana jin rigimar da suka rinka yi, sai dai ta ji dadi kwarai
da ta ji Daddyn ya rufe ido ya yi ma ta bala'i ya kuma jaddada mata matsayinshi to amma yarda abubuwan
suke tafiya rayuwa ba ta da wani tasiri tunda babu mutunci, mutum irin Daddy da ke da son jama'a
musamman 'yan'uwanshi kamata ya yi ace ya aje macen
da ra'ayinsu yazo daya ta haka ne zasu yi rayuwa mai dadi ba wai sakarci irin Farida ba.
To ita dai Naja'atu 'yar kallo ce bata saka abun a
ranta ba, haka nan ba ta da niyyar saka kanta cikin
lamarin ba, gidan Aisha suka sha yininsu suna bata
labarin abubuwan da ke faruwa, Aisha ta ce "Ai ni dama
nasan a rina wai an saci zanin mahaukaciya, matsala ce
babba namiji ya fidda sonshi ga mace har ta fahimce shi
kamar yarda yake matsala ga matan su fidda nasu, to shi Daddy komi Farida komi Farida, yanzu ga abin da Farida ke neman saka shi nan." Zainab ta ce "Amnıa fa
ba laifi yana tsaya akanta insha Allahu zaya yi nasıra."
Aisha dariya kawai ta yi ta ce "To Allah yasa, idan
kuma ya zama mijin tace ba shi kenan ba." Suka yi
dariya baki daya.
Sai da aka yi sallar La'asar suka nufi gida, abun
mamaki gidan a rufe shima Daddyn ba ya nan su ka
zauna bakin kofa su na mamaki, Zainab ta te su koma
gidan Aisha kawai, Naja'atu ta ce "A'a, a kira Daddyn aji." Don haka Zainab ta fidda waya ta kira shi, ya ce
"Yaya Zainab.?" Ta ce "Lafiya lau, mun dawo ne gidan
a rufe babu kowa." Ya се "Babu Kowa? Kuma kun
19
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankiа
Kwankwasa.?" Ta ce "A rufe yake gama kwado an
sanya." Ya dan yi shiru, sai ya ce "Shi kenan ku yi
hakuri gani nan isowa." Zainab ta rufe wayar tana kallon
Naja'atu ta ce "kin ji bai ma san ta fita ba, Allah kuwa
idan yarinyar nan tayi wasa, sai nayi mata dukan tsiya."
Naja'atu ta yi murmushi ta ce "Me ya yi zafi na duka? Ki
rabu da ita tsakaninta da mijinta."
Su na nan tsaye Daddy ya kawo masu makullin,
Zainab ta sauka ta karbo bai tsaya ba ya fita. Da su ka
shiga, su ka aje kayansu cikin faki su ka dawo falo,
Zairab ta ce "To wai zaman mu kenan, kullum sai dai a
sawo mana abinci?" Naja'atu ta yi murmushi ta ce "To
me zamu yi.?" Ta ce "Tashi zaki yi mu shiga kicin kada
mu ma mu zama sakarkarin." Naja'atu ta ce "A'a Zainab
kada ta ce mun yi mata ba daidai ba." Zainab ta ce "To
ita daidai din ce take yi yanzu? Tashi zaki yi kawai mu
shiga kicin Naja'atu ta zauna tana jinjina abin a ranta, ita
dai ta tsani wani ya ce ta yi mashi ba daidai ba, balle
wannan zaman da suke yi dangwalolo kuma tasan duk a
kanta ne take yin haka me yiwuwa da babu wani abu
tsakaninta da Daddy ba zata yi masu ba.
Zainab ta mike ta shiga kicin ta bude firij ga komi
nan a wadace ta leka store nan ma babu matsala, don
haka ta zage ta shiga aikinta. Shiru-shiru Naja'atu na
zaune, don haka itama ta shiga su ka-ci gaba da aiki,
Zainab ta yi ma Daddy waya, ta ce kada ya yi wahalar
sawo abinci gashi nan su na dafawa." Hankali kwance
su ka ci gaba da aikinsu, Zainab ta dora farfesun kaza ta
zauna tana fere dankali yayin da Naja'atu ke tsaye tana
yankan kayan marmari zata hada fruits salad.
Babu sallama ta shigo cikin gidan, ta tsaya cikin
20
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
falo tana waige-waige, hancinta ya cika da kamshi
alamun girki ake yi cikin gidan, sai kuma ta kara
harzuka, da saurinta ta nufi kicin din, ta tsaya bakin
kofa ta ce "Waye ya baku izinin shigar mani kicin kuyi
sanwa?" Gaba ki daya suka juyo suna kallonta, Zainab
ta yi karaf ta ce "Ai ba sai an ba mu izini ba, mu ma
muna da 'yancin yin yarda mu ka ga dama cikin gidan
tunda ba na ubanki ba ne."
Naja'atu ta yi sauri ta dafa ta, ta ce "Ba a haka
Zainab." Farida ta ce "Ke tafi can munafuka, rufe mani
baki ba da ke nake yi ba don ba ni da lokacinki, kuma ke
da kike ikirarin don kin isa ki ka shiga kicin din, don
kina takamar gidan dan'uwanki ne zani yi maganinki, ai
zaya dawo gidan sai ya zaba ko ni ko ke, ko kuma
wannan banzar bakauyar, kuma wallahi da ni mu ke
magana, yanzu a fita a bar mani kicin."
Zainab ta yi murmushi ta ce "Wannan kuma ne ba
ki isa ba, ba kuma ki da hurumin da za ki fidda mu, don
ba duwatsu ne a gidan ba da zaki fita yawonki na banza
ba ki tsaya kin yi ma mijinki abincin da zaya ci ba, balle
mu ma mu samu, sannan kuma kice ba zamu girka ba,
wallahi kinyi kadan, kuma dul iya wulakancin da kike
jin kin iya, kiyi wata rana ko an ce kiyi ba za ki yi ba,
shashashar banza." Farida ta ce "ka da ki kuskura ki
sake zagina." Ta ce "An zaga, kiyi abin da za ki yi."
Rigima ta yi sama tsakanin su, Naja'tu duk ta
rikice ta shiga kwakkwafat Zainab, kan ta yi hakuri ta
rabu da ita, yayin da ita kuma Faridar ta rufe ido ta rinka
dura masu ashar, zuciya ta kashe Zainab ta mike su ka
rukume dambe, cikin yanayin Daddy ya shigo gidan da
saurinshi ya saki ledojin da ke hannunshi ya nufo kansu
21
Simin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
yana kokarin raba su, amma Farida ta ki tsayawa, sai ma
ta maida fadan kanshi, tana cewa "Don mi zaka basu
izinin shigar mani cikin kicin ya ce "Na ba da, an fadi
maki yarda kike sakarya su ma sakarkarin ne, ko kua
yarda kika kasa tsayawa kiyi girki cikin gidanki, so kike
su zauna da yunwa? Idan ba su girka ba me za su ci?
Kuma sannan gidan ubanwa kika je? Wa ya ba ki izinin
fita.?"
Nan kuma sai ta yi sakwat, ya dubi Zainab ya ce
kuje ku ci.gaba da aikinku." A fusace ta wuce daki
shima ya bita Naja'atu na tsaye gefe gudam jikinta har
rawa yake yi, ba ta son fitina, "Wannan wace irin
rayuwa ce.?" Zainab ta gyara jikinta su ka koma suka ci
gaba da aikinsu.
Da daddare da suka yi waya da Mummy, Naja'atu
ta rinka kwabarta, amma sai da ta fadi ma Mummy
komi. Mummy ta ce "Abin da za'ayi, zani yi magana da
Daddyn,ku koma gida kuyi zamanku." Zainab ta ce
"Kiyi hakuri kawai Mummy Daddy yana bakin
kokarinshi idan muka tafi kenan ta samu yarda take so
ki rabu da ita sai naga iyakarta, muna nan zama daram,
idan muka tafi ta yi galaba kanmu kenan, kuma shima
zaya a ba'a yi mashi daidai ba."
Mummy ta ce "Shi kenan amma ki kiyaye kada ki
kuskura in ji an ce kun kara yin dambe da ita, ku zuba
mata ido kawai tunda ba dukanku take yi ba." Zainab ta
ce "Wallahi ko yanzu Mummy ita ce taja, don mi zata
tsaya tana zaginmu kamar kananan yara.?" Mummy ta
ce "Na ji, koma menene ku rinka hakuri." Su ka yi
sallama ta rufe wayar.
To kwana biyu ba a sake rigima ba, sai dai Farida
22
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
ta tsame hannunta cikin harkar gidan, su ke gyaran
falon, kicin da dakinsu, haka nan da yamma su yi aikin
abincin buda baki, daga su sai Daddy ke ci. To su ma ba
su shiga harkarta, iyakarsu da ita gaisuwa wani lokacin
ta amsa wani zubin kuma ko kallo ba su ishe ta ba,
Zainab haushi take ji sosai, sai dai Mummy ta ce kada su
kuskura su kara yin rigima da ita, don haka ba ta biye
mata. Duk aikin da ya kamata suyi, cikin gidan suna yi
Naja'atu dai 'yar kallo ce, bata cika zama falo ba, idan ba
wani aiki su ke yi ba, ko kuma Daddy ba ya gidan amma
in dai yana nan cikin daki zata yi zamanta shima yana
kokarin kauce ma duk wani abu da zaya janyo fitina
tsakaninsu, cikin zuciyarta ta rinka tausaya mashi, duk
ya bi ya rame ya sukurkuce kuma ta san ba wani abu
bane illa rashin kwanciyar hankali, yarda take nazarin
zamantakewarsu sai taji kwata-kwata ta daina sha'awar
zaman gidan shi, yanzu haka ji take yi kamar tana kan
kaya, to ina ga ya auro ta tazo gidan, ai tasan ta bani,
yarda ba ta son fitina wuyarsu zata sha, don haka ta
dukufa addu'a ba dare ba rana, akan Allah ya yi mata
zabi mafi alkairi."
Lokuta da dama idan tana auna zamanta da Daddy
da kuma zama da Khalid sai taga auren Khalid ya fiye
mata kwanciyar hankali, a kalla tasan babu wanda zaya
tsangwame ta, kuma shima ba ya da hayaniya, zaya bata
rayuwa mai kyau fiye da gidan Daddy, saboda matar to
balle kuma ita. Sai dai idan aka yi maganar so, ta yi
Imanin Daddy kadai zuciyarta take so, abin da ke
wahalar da ita kenan. Don haka ta mika dukkan
lamarinta a wajen Allah, tana neman zabinshi kuma
babu laifi tana samun sauki. Idan suka yi waya da
23
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
Khalid yana fadi mata matsayin kaunarta a zuciyarshi,
ita kam addu'a take yi mashi da fatan Allah yasa ya dace
da abin da ya tafi nema.
Rayuwarsu ta ci gaba da tafiya, da dadi babu dadi
sun dai dake, yau Naja'atu na makaranta, Daddy ya
kirata a waya ya ce ta fito ya na jiranta waje. Zaune ta ke
tana wani aiki dole ta aje ta fito, ta same shi zaune cikin
mota ya zuba mata ido sai ta ji wani iri. A hankali ta
sauke kanta, ya ce "Zagayo ki shigo mana." Ta bude
dayan gefen ta zauna, ya dafa sitiyarin motar ya na
kallon titi, kamar yana nazarin wani abu, sai kuma yг
juyo yana kallonta ya ce "Wai laifin me na yi maki?
Yanzu ba ki sakar mani fuska idan na zauna in da kike
sai ki tashi abun ya na yi mani komi ba ina yin haka ne
don kauce ma fitina." Ya zuba mata ido sai ya jinjina kai
ya ce "Na fahimce ki sai dai ina son ki sani, har yanzu
kaunar ki tana cikin zuciyata, kuma ina nan kan
maganata, don haka idan Allah ya kaimu Sallah ta ba da
baya, Mummy ta dawo, zani samu lokaci mu zauna da
ita, a fara maganar nan."
Naja'atu ta zuba mashi ido, ta ce "Daddy kana
ganin abun nan zaya yiwu? Ni fa ina gudun fitinar
matarka, ba za tga barni in zauna lafiya ba." Shi ma ya
ci gaba da kallonta, ya ce "Amma ni za ki aura ba Farida
ba, haka nan ba ita ke iko dani ba, ina da 'yancin yin duk
abin da zaya yi mani dadi, don haka wannan ba hujja ba
ce." Ta yi'shiru tana sauraren shi, ita kadai tasan abin da
take hangowa, to tasan idan zata kwana tana kwatanta
mashi ba zaya yarda ba, don haka ta rabu dashi din ya
fiye mata kwanciyar hankali, rigimar Daddy yawa ne da
ita, dayar ma yaya ya kare da ita balle ya hada biyu.?"
24
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
Ya saki maganar ya ce "Yanzu me kike so in yi
maki?" Ta zuba mashi ido ta ce "kamar yaya.?" Ya cе
"Wai na hidima sallah." Ta yi murmushi ta ce "Na yafe
maka, Mummy ta yi mana dinkuna kala biyu, kuma ga
na biki bamu sanya wasu ba." Ya ce "Na sani amma ni
ganina ke yi kina da hakki a kaina." Ya mika hannu sit
din baya ya dauko leda da shaddoji guda biyu dinkakku,
masu kyau dinkin senegal da leshi dfaya baki da adon
duwatsu ya ce "ke da Zainab shima leshin naki ne." Ta
karkace kai tana kallonshi yarda yake so ta ce "Daddy
hidimar ta yi yawa." Ya ce "Ba ki tunanin cewa nan da
dan lokaci gaba ki daya hidimominki kaina za su dawo,
to ki dauka ina yin rahasal ne in gani in zani iya."
Ta yi dariya ta ce "Sai ka ce wasa.?" Ya ce "Duk
yarda kika ce." A hankali ya rinka janta da hira, don
haka su ka dauki lokaci sosai, duk wata kewar da suke
da ita ta tafi, sai begen junansu, Daddy kamar kada ya
tafi ya shiga cikin wani irin nishadi, duk wata
damuwarshi ta yaye, ya yi Imanin cewa Naja'atu rahama
ce gare shi, mamakin yarda aka yi yarinyar ta shiga
ranshi irin haka yake yi. Ya na shirin tafiya ya ce "Ba ki
gama abin da kike yi ba? Kizo muje in saukeki gida."
Naja'atu ta yi dariya ta ce "Rufa mani asiri, kada
ran uwargida ya baci, ina gudun rigima kayi tafiyarka
kawai idan na gama zani-dauki taxi in koma." Ya yi
murmushi kawai bai ce komi ba, don haka ta fita daga
motar ta rufe mashi tana kallonshi'ta ce "Na gode." Ya
ce "Korata kike yi ko.?" Ta ce "Ba kora ba ce ina son in
gama wani aiki kafin lokacin tashi yayi." Ya yi mata
sallama ya ja ya tafi, itama ta koma ciki tana dariyar
Daddy simple man, amma bai yi dace da mace ta gari
25
ba.
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
Ranar Sallah su ka tashi cikin farin ciki da
annushuwa, na murnar zagayowar ranar suna fatan Allah
ya sa su ga ya badi cikin koshin lafiya da kwanciyar
hankali. Da wuri su ka yi shirinsu za su tafi gidan Anty
Aisha karfe goma an sauko daga masallacin Idi, su ka
fito falon masu gidan na zaune cikin falo, Daddy na
cikin manyan kaya shadda fara sol, yayin da Farida ke
sanye da atamfa 'yar (Super Exaisive) fara, duba daya
Naja'atu tayi mashi ta kauda kai sannan gaba ki daya su
ka gaida su. Cikin zuciyarta ta rinka mamakin ranar
Daddy, farat daya zaka lura da hakan. Ba su zauna ba
Zainab ta ce, Gidan Anty Aisha zamu je me yiwuwa sai
dare zamu dawo." Ya ce "Ba damuwa itama Farida gida
zata je, don haka nima zani yi babu wani abu ko.?" Ya
zuba ma Naja'atu ido ta yi kyau cikin shaddar amma ita
sai ta share kamar bata san yana yi ba. Zainab ta ce
"Zamu zuba mai sai kuma barka da sallarmu."
Yayi dariya ya ce, "kun yi girma da barka da
Sallah Zainab ba ku tausayina ne.?" Ya fiddo kudi sabbi
fil daga aljihunshi ya fidda ya bata su ka fice, gidan
Aisha su ka sha yininsu har da Ibrahim sai yamma suka
fita su ka je gidan Babansu, nan su ka sauke Ibrahim su
kuma su ka wuce gida.
Kwana biyu da yin sallah, suka yi waya da
Mummy ta ce suna shidda suna shirin tasowa. Naja'atu
tafi kowa murna, don gaskiya tana takura sosai da
zaman gidan, ba wani sakewa, don haka su ka shiga
hada kayansu, gabaki daya da kayansu, su ka tafi filin
jirgi tarbar Mummy su na sauka sai gida. Yanci ya samu
su duka addu'a suka yi kada Allah ya kara kaddara masu
26
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
irin wannan zaman. Zainab ta rinka ba Mummy labarin
irin rayuwar da suka yi, Naja'atu ta rinka kwabarta, to ita ma Mummy ba ta dauka da zafi ba.
Ranar da daddare Daddy yazo gidan ya tsare Naja'atu sai ta amsa mashi cewa ta amince a fara
maganar aurensu, Naja'atu tayi tsuru, ita kan abin da take hangowa daban, ya kada ya raya amma taki amsa
mashi ta ce, "Sai dai ya jira idon ta gama nazari zata
sanar dashi." Ya ce "Wane irin nazari zaki yi akaina Naja'atu? Sai dai in ba ki yi kin fito fili ki sanar dani."
Ba ta ce komi ba, yayin da shi kuma ya cika sosai a
karshe fushi ya yi ya tafi. Kwana biyu ko ya zo gidan ba
ya kula ta idan ta gaidashi ba ya amsawa. Tun tana daukar abun da wasa har dai taga da gaske ya ke, don haka itama ta share shi kowa ya ci gaba da harkarshi. Zainab ta rinka kokarin daidaita tsakaninsu amma abun
ya ci tura Daddy ya dauki zafi sosai, gaba ki daya ma ya dan daga ma zuwa gidan.
Sati biyu da dawowar Mummy, ta shirya masu tafiya, Katsina. Naja'atu ta yi murna kwarai ta samu iyayenta da 'yan'uwanta lafiyar kwanansu biyar suka dawo Abuja, ko da yazo gidan suna zaune falo tare da Zainab da su ka gaida shi ciki-ciki ya amsa, ko kallon Naja'atu baiyi ba, ya tuna Zainab ta yima Mummy
magana, don haka itama Naja'atu, ta