Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
tashi ta bar wajen. Zainab dariya take yi masu saboda tasan su duka suna son juna, ko ita Naja'atun dake kokarin dannewa, damuwarta ta fara fitowa yanzu ko jiya Khalid ya kira ta yana yi mata korafin ya rasa gane kan Naja'atun cikin 'yan kwanakin, sai ta kama waya ta rufe, haka nan idan ma ya same ta ba ta sakin jiki suyi hira sosai kamar da, 27 Sirrin Zuci.. 4 Sa ʼadatu Saminu Kankia wai don Allah me ya ke faruwa.?" A zahiri ta san cewa matsalarta da Daddy ce ta jagula mata lissafi, sai dai babu damar ta fito ta fadi mashi haka don haka tayi karya ta ce "matsalar karatu ce kawai amma babu wani abu. Amma shi Dáddy tasan matsalarshi, tsabar kishi ce sai dai bata ganin laifin Naja'atu ita kanta bata yi mata sha'awar zama da Farida a matsayin kishiyarta, yarda Naja'atun ba ta son fitina kwarar ta za'ayi. Haka nan yarda tafiyar ta taho kama ta ya yi ace ya kwantar da kai yana lallashin Naja'atun, ta haka zaya iya shawo kanta tunda yasan tana sonshi, amma wannan fushin da yake yi ba zaya yi mashi maganin komi ba. Idan tayi ma Naja'atu maganar sam ba ta so ta ce "Don Allah ta daina yi mata maganar Daddy." Don haka Zainab ta zuba ida wani lokacin ta yi dariya wani lokacin ta tausaya masu, ganin yarda soyayya ke wahalar dasu. Da hotonta ya kare ta yi shiri ta yi tafiyarta makaranta, Naja'atu ba ta ji dadi ba. Abu kamar wasa, sun kasa sasanta kansu, ta kai matsayin da babu ruwan kowa da kowa, haka ya fiye ma Naja'atu kwanciyar hankali, ta ci gaba da karatunta har Allah ya taimaka ta gama, lokacin Khalid ya ke shirin dawowa. Sun yi waya, ya sanar da Naja'atu, ya na tambayarta, abubuwan da take so, a zuba mata cikin lefe, saboda so yake yi da zaran ya dawo a sanya lokacin auransu." Ta yi dariya ta ce "Ba ni da zabi, duk abin da ka sawo zani yi murna dashi, ni dai fatana Allah ya dawo da kai lafiya, ya sanya an dace da abin da abin da aka je nema." Ya ji dadi ya ce "Na gode Naja'atu, na yi Imanin addu'ar da kike yi man ce take yin tasiri a kaina don haka nake 28 Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia ganin hasken abun na yarda wata baiwa ce Allah ya yi mani da ya hada ni da ke ko kinsan cewa samun mace tagari irin ki yana da wahala, wata babbar baiwa ce Allah ya yi mani. Ta yi murmushi kawai. To kuma ranar su na zaune cikin falo tare da Mummy, Daddy ya yi sallama ya shigo tun da ta juya taga shi ne, ta maida idanuwantga akan akwatin talabijin ba ta sake kula shi ba. Yazo ya zauna su na gaisawa da Mummy, itama nazarinsu ta ke yi, ta na sane da halin da suke ciki, zuba masu ido ta yi taga iya gudunsu, amma yanzu da abun ya fara tsanani, sai ta ke ganin bai dace ba, kusan abun ya farfa zama gaba tsakanin su babu ruwan kowa da kowa. Naja'atu ta mike tana shin tashi, Mummy ta dube ta ta ce "Ina za ki Naja'atu? Zauna muyi wata magana." Naja'atu ta koma ta zauna, yayin da Daddy ya zuba mata ido, zuciyarshi na harbawa da sauri, don haka ta sarda kai ba ta ce komi ba. Mummy ta dubi Daddy ta ce "Wai me yake faruwa ne tsakaninku.?" Daddy ya watsa hannayenshi ya ce "Ga ta nan ta fadi maki." Ta dubi Naja'atun, yayin da zuciyar ta ta kare, а hankali hawaye su ka cika mata ido, sai ta kifa kanta cikin jikinta. Ta juya kan Daddy ta ce "To wai duk meye ya jawo haka?" Ya yi murmushi ya ce "Ba wata matsala ba ce ba, na yi mata magana ne kan cewa ina son ta amince mani a fara maganar aurenmu, to kanshi ne fa ta dauki fushi, kuma ni na fadi mata babu dole, itdan ta ce bata yi ba zani matsa ma ta ba, a kan haka ne ta ke ta wannan abun idan na shigo sai ta tashi ko kallon arziki ba ta yi mani." Mummy ta yi murmushi ta ce "To gaskiya ba ni son irin wannan abun, abin da nake so ka dauka, shi Sirrin Zuci.. 4 Sa adatu Saminu Kankia aurc nufin Allah ne, idan Naja'atu matarka ced zaka ga an yi haka nan in ba matarka ba ce sai dai ka dauki hakuri, don haka a bi komi a sannu." Ta juya kan Naja'atu ta ce "Kin ji dai abin da na fada, bani son irin zaman da kukc yi kc da dan'uwanki, kuma in ban da abin ki, yaya za ki yi da Daddy? Ko shi yaya zaya yi da ke? Duk me yake wahalar da ke cikin 'yan kwanakin nan idan ba shì ba, ga shì nan ku sasanta kanku, bani son sakarci." Ta mike ta shige cikin daki, su ka zauna shiru, ga shi Daddy ya tsare ta da mayataccen kallonshi, duk ya takura ta sai ta ji kamar ta tashi ta bar wajen. Ya yi gyaran murya ya na kallonta, ya ce "Yanzu ba ki ji kunyar abin da ki ka yi mani ba.?" Ta girgiza kai ta ce "Ko daya, saboda nasan ba ni ce na yi fushi da kai ba, kaine ka fara." Ya ce "ko da nayi fushin nayi ne don ki gane cewa kin yi mani laifi, amma ba don wani abu ba, sai kika nuna mani ni ba wani abu ba ne, ga baki daya ma za ki iya rabuwa da ni." Ta yi shiru ba ta ce komi ba, yayin da shi kuma ya ci gaba da yi mata korafi, to ita kam bata ga laifinta ba, kawai dai yana son ya yi tabarmar kunya ne, don haka ya ke kokarin dora mata laifi. Ya gyara zama yana kallonta ya ce "Yanzu ina magana ta kwana, shin kina jin za ki amince da ni ko kuma kin share ni in rabu da ke? Tambayar tayi mata nauyi, ba ta san yarda zata yi da rigimar Daddy ba, alhalin shi kanshi Khalid cikin huro mata tashi wutar ya ke, cikin sati mai kamawa zaya iso kuma ya ce da ya dawo maganar aurensu ce abu na farko da zaya fara yi. Abum ya sakata tsakiya, yayin da Daddyn ya marairaice Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia mata yana kokarin shawo kanta, tun yana magana da zafi-zafi har ta kai ya kwantar da kai yana lallashinta, tausayi ya bata da ya rinka fasa mata sirrin zaman aurenshi, ya cc "Na sani zake yi tunanin ko ina daya daga cikin maza 'yan sha'awa, masu zara wadanda da sun ga macc zasu cc suna so, musamman ganin ban dade da yin aure ba gashi, nazo ina magiyarki amince da aurcna. Na sani sirrin gidana biyayya ne wajenki da kanki kinga irin rayuwar da nake yi har yanzu ban samu kwanciyar hankalin da nake so ba, bani samun kulawar da ta kamata don haka kika ga na makance kanki, na sani kina da kyakkyawar tarbiya da zaki san hakkina ki rinka kyautata mani. Ina kaunarki Naja'atu, zani so ace kanki na dora dukkan jin dadin rayuwata na yi Imanin ba za ki bani kunya ba, zaki yi mani halarci, don haka ki amince dani ki yarda dani in baki amanar kaina." "Kaunata gare ki wani nufi ne daga Allah, lokacin da muka fara haduwa, ba ki sanni ba, ban sanki ba, sai aka samu akasa muka fara da rashin fahimta, Allah ya sani raina ya baci, lokacin da kika rinka fadi mani bakaken maganganu alhalin gashi nayi nadamar abin da ya faru, har na tsaya don in baki hakuri: Duk da cewa raina ya 6aci kina gani saina kasa ce mani komi, saboda wani abu daga gare ki da ya rinka fizgeta don haka na tafi na baki wurin saboda ba zani iya gaya maki magana ba, amma tunda na iso gida tunaninki ya tsaya mani cikin rai, har ta kai na ba Hajiya labarin abin da ya faru, har dare na kasa samun natsuwa, idan na rufe ido ina ganin kyakkyawar fuskarki gaba ki daya sai na daina ganin laifinki, naji ina son in sake ganinki kuma cikin yardar Allah sai Allah ya sa jininmu daya gashi muna zaune tare." Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia "Nasha fama da zuciyata akan tunanin abin da yake damu na dangane dake har mamaki nake yi yarda na cika damuwa dake, a karshe da kaina na gane cewa ba komi ne ka wahalar dani ba, face kaunarki, amma sai na rinka kokarin danne zuciyata domin ganin na cika alkawarin da na daukar ma kaina tsawon lokaci dai haka, ina són ki dauka aurena da Farida rubutacce ne, kuma kema ina fatan mun zama daya, zani yi farin ciki idan har kika amince ki ka dauki ragamarta, Naja'atu kina da halayc managarta da nayi Imanin zani ji dadin zama dake, kuma kinsan ciwona, zaki yi tattalina ki wadata ni da kulawar da na rasa." Naja'atu ta zuba mashi ido tana kallon damuwarshi karara, abin da ya fada gaskiya ne yana bukatar kulawa a kullum takan tausaya mashi bai yi dacen mace ba, idan har ya ci gaba da zama haka rayuwarshi ba zata kai ko ina ba zata rugurguje, meye amfanin mace irin Farida? Irinsu ne suke zama cikin gida su na fama da zafin kishi ba a damu da tsare hakkokin miji ba, balle a kirkiri abin da zaya faranta mashi rai, idana akayi sa'a da mai karamar zuciya sai ya fita waje wata ta same shi ta rike shi tana yi mashi dukkan abin da ya ke so, shi kuma ya na biya mata bukatunta, idan ba ai hankali ba sai ta janye shi baki daya, sai kuma ta samu canji hankali ya tashi ta rinka damunshi da fitina iri-iri wanda in ba sa'a ba, sai ya gwammace yaʼrabu da ita. Kin ga nan sakaci da rashin kula ya jawo, Allah yasa 'yan'uwa mata su rinka kula irin wadannan matsalolin da su ka shafi zamantakewar yau da kullum ta aure. Ta saukar da ajiyar zuciya tana kallon Daddy, sai Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia ta yi murmushi ta ce "Ni ba wai ban damu da kai ba ne, Daddy idan na ce bani sonka nayi karya, sai dai abubuwan ne sun taso ni gaba ka sani nayi ma Khalid alkawarin idan ya dawo za'ayi maganar aurenmu, to yanzu haka ya sanar dani cewa yana nan isowa cikin sati mai zuwa me zani fadi mashi idan ya iso? Ban da wannan ina hangen yarda zamana zaya kasance da matarka Daddy, bani son fitina ka sani, kada in amince maka ya zamto ba a samu kwanciyar hankalin da ake so ba." Ya dan zuba mata ido, amma sai ya yi murmushi ya ce "Insha Allahu ma samu za'ayi, kuma idan kina ganin zaman naku tare akwai matsala, sai in nemi wani gidan ki zauna ke daya." Naja'atu ta yi murmushi tana girgiza ta.ce "Ni ba ne ba zani iya zama da Farida ba, komi zata yi zani iya dauka tunda ba ita ce ta aje ni ba kaina abun yi kasan wani lokaci, ku maza kuke kawo rashin zama lafiya a gidanku, ta hanya fifita daya, ko kuma kasa tsawata ma duka mu bika, sannan kasa tsoron Allah da adalci a tsakaninmu." Ya jinjina kai ya na yaba tunanin yarinyar, sai ya ji ya kara sonta, ya ce "Duk wannan ba matsala ba ce, ni dai fatana ki amince da ni, in har muka samu fahimta tsakaninmu, to insha Allah, ba zamu rinka samun matsala ba." Naja'atu ta jinjina kai, sai tayi murmushi ta ce "Shi kenan sai mu ci gaba da addu'a, Allah ya yi mana zabi mafi alkairi. Amma ina son kayi mani wani abu guda." Ya zuba mata ido yana saurarenta, ta ce "Ina so kayi mani hakuri zuwa lokacin da Khalid zaya dawo, ina son inga mun rabu lafiya dashi." Ya watsa hannayenshi yana kallonta, ya ce "Babu damuwa, ai kin gama kwantar mani da hankali." Ta yi murmushi kawai, 33 Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia Daddy daban ne, ita kadai tasan yarda take jinshi a ranta. Cikin dare ta kasa barci tana tunanin hanyar da zata bullo ma Khalid da ita, maganar gaskiya ba zata iya ci mashi fuska ba, haka nan ba za ta iya yaudarar shi ba, ta yi tunanin ko ta fito fili ta sanar da shi? Nan ma da nauyi, ba za ta iya tunkararshi ido da ido ba, ta ce ba ta son shi Daddy take so, alhalin ita kanta shaida ce tasan shi ita kadai yak e so, sai ta rinka jin tausayinshi. Har safe bata jin dadin zuciyarta, ta na kwance cikin daki ta dauki waya ta kira Zainab, su ka gaisa tana tambayarta karatu. Zainab ta ce "komi lafiya lau dama nayi niyyar yau in yi maki text in yi murna, munyi waya da Doctor ya ce yana tafe nextweek, ya tambaye ni size dinki na underwears da takalmi, to na dai ba shi nawa, tunda ina ganin size din mu daya, ya ce ya tambaye ki kin ki fadi mashi." Naja'atu ta saukar da ajiyar zuciya ta ce "Abin da ya sa na kirawo ki kenan Zainab, abubuwa sunyi mani zafi, jiya har dare ya yi sosai muna tare da Daddy gidan nan, Zainab yaya zani yi da Dadd? Ina tausayin rayuwata, don haka gaskiya na amince da aurenshi don haka nake so ki bani shawarar yarda zani bullo ma Khalid, mu rabu lafiya." Zainab ta ce "Amma Naja kin yi saurin yanke hukunci." Naja'atu ta runtse ido ta na sauraren Zainab, ta ce "To Zainab ya na iya da rayuwata? Ba zani iya jure ganin bacin ranshi ba." Zainab ta yi dariya ta ce "ki fito fili kice kin fi son Daddy kawai, in haka ne ni ba zani cusa maki ra'ayi ba, sai dai idan nice ke ba zani zabi Daddy mai mata ba, ina kallon saurayi." Naja'atu ta ce 34 Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia "Auren Daddy ba ya gabana Zainab, abin da nake dubawa shi ne, Daddy ya na sona, kuma nima ina sonshi, sannan yana bukatar Good wife wadda zata kula da rayuwarshi, kuma ke kin san halin da yake ciki, hankalina ba zaya taba kwanciya ba, idan ina ganinshi cikin wannan yanayin." Zainab ta kyalkyale da dariya, ta ce "karatun da ya yi maki kenan.?" Ta ce "Ba zancen karatu ba ne, ki fahimce ni Zainab." Zainab ta ce "Ai na gama fahimtar ki, yanzu meye matsalarki.?" Naja'atu ta ce "Khalid." Zainab ta ce "Ina ruwanki da Khalid kuma? Kina tunanin shi me zaya sa ki yi ma shi haka? Ki share shi kawai, idan ya iso ya yi kukan ra shin ki, ya hakura ya samu wata, ko kuwa za ki auri mutum biyu ne.?" Naja'atu ta ce "Sai in bashi kanwata ko.?" Zainab ta ce "Wace kanwar, Badiya ko Fatima.?" Naja'atu tayi dariya ta ce "Ke ko.?" Wuta ta dauke ma Zainab, yayin da Naja'atu ta kwantar da murya tana tsara ma Zainab yarda abubuwa za su kasance. Zainab saurarenta kawai take, ko da yake ta jima da shawarar wasu halaye na Khalid din, shi kanshi ya na kula da ita, ta su tazo daya yana yawan yi mata waya su gaisa, haka nan sai dai ta dauki wannan yanayi ne saboda 'yar'uwarta Naja'atu. Ta yi dariya ta ce "Wai ke me kika dauki soyayya ne? Shi fa so daban yake, koda- kike ganin muna gaisawa da shi, ba wai dole ne ya so ni ba." Naja'atu ta ce "Insha Allahu ma zaya so ki, na fara addu'a tun jiya, kuma ke ma kiyi tunani, ya dace ki fara tunanin yin aure, ai karatu ba ya hana aure, Allah kuma Mummy na yawan magana kanki, to ke na lura ba ki ma da lokacin samarin balle ki natsu ki zabi wanda ya dace da ke. Sirrin Zuci.. 4 Sa’adatu Saminu Kankia Zainab ta yi shiru tana wani tunani, wani kuduri ne da daukar ma ranta cewa, ba zata sake yarda da wani da namiji ba, tun akan wani saurayinta Abdullah, da ya nemi bata mata rayuwa, farkon zuwanta Jami'a." Та saukar da ajiyar zuciya, ta ce "Nima tana yawan yi mani maganar Naja, to sai dai akwai wani abin da ya faru a kaina da ya sanya na daukar ma kaina alkawarin ba ni ba da namiji, zan ci gaba da karatuna, har masters, idan ya so lokacin na mallaki hankalin kaina, kuma nasan yarda halayyar jama'a ta ke sauyawa, lokacin zani iya samun wanda halayyarmu tazo daya in aura. Abin da ya faru shi ne, shekarata ta farko a nan Jami'a na hadu da wani saurayi Abdullah Sani, shekara daya muka fara karatu dashi, sai dai ba kwas din mu daya ba, wata rana muka hadu a capteria, ya zauna in da nake zaune, shi ne ya biya mana kudin abincin har da nawa, mu ka fito yana tambayata sunana, na fadi mashi, shima ya fadi mani nashi, da kuma tarihin rayuwarshi, mahaifinshi dan kasuwa ne hamshakin mai kudi su na zaune Kaduna." Cikin dan lokaci muka kulla abota mai karfi, kafin daga baya mu birkice ta koma soyayya. A duk iya tsawon rayuwata ban taba son wani da namiji ba irin Abdullah saboda wannan ne karo na farko da na fara soyayya cikin natsuwa muka rinka tafiyar da rayuwarmu, mun shaku sosai, haka nan mun damu da juna, Abdullah mutum ne can gayu, kuma dan karya yana da kankamba da barazana da son nuna shi wani ne, haka nan Allah ya zuba mashi ruwan kyau don haka ya yi fice cikin makarantar. 36 Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saninu Kankia Rayuwar mu ta ci gaba da tafiya, cikin kwanciya hankali koda yaushe maganar Abdul ita ce idan mun shiga shekara ta biyu da karatun mu, zaya yi ma mahaifinshi magana akan aurenmu, idan ya so da aurenmu sai mu ci gab ada karatun. Da irc-iren wafannan maganganun ya jani jikinshi, na yarda dashi da amincewa dashi, ban taba tunanin yana da wata manufa ta daban ba a kaina, saboda ya na nuna tsananin kishi akaina, ko ganina ya yi ina magana da maza, sai mun yi rigima, don haka na rinka taka tsan-tsan bani son abin da zaya bata mashi rai. Abu guda ne ke hada ni da Abdullah, yanayin mahaukaciyar soyayyar da ya ke nuna mani, ko a gaban wa, sai ya nemi ya rike ni, ni kuwa bani so. Ranar da yayi kissing dinta na rufe idona kai mashi mari, sai ya rike mani hannu ya na kallona bai ce komi ba, ya saki hannuna ya juya ya tafi. A zatona ya yi fushi ya rabu dani kenan, sai dai ko kadan ban yi nadamar abin da na yi ba, saboda nasan 'yancin kaina na kwata, matsawar zani barshi yana yin irin haka to wata rana abin da ya fi haka ma yi mani za ya yi." Abun mamaki washe gari ina zaune cikin inuwa, sai gashi yazo ya zauna kusa dani yana dariyarshi kamar wani abu bai hada mu ba, lokacin ne na dan ji nauyin abin da na yi mashi amma ban tada maganar ba, muka ci gaba da hira. Lokaci ya ci gaba da tafiya, rannan ya ce in zo muje cikin gari yawo, ban yi musu ba na bishi mu ka tafi, mun dan yi yawo ya ke bani labarin yana da kanin mahaifiyarshi da ke zaune nan Zaria, za mu biya mu gaisa. Na ce mashi babu damuwa, muka is agidan madaidaici, flat House, ginin zamani tare muka shiga cikin falon, dan madaidaici, kujeru ne kadai ciki da 37 Sirin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia kayan kallo, sai Allon kwamfuta, da sauran tarkacen ta. Na zauna bisa kujera yayin da shi kuma ya shiga wata kofa, sai gashi ya fito da lemu cikin kofuna biyu, ya na shan daya ya miko mani dayan na karba nayi godiya yayin da shi kuma ya aje nashi kofin bisa tebur ya ce mani ina zuwa. Ya bi ta wata hanya ya shiga daki haka nan sai hankalina bai kwanta da lemun ba, don haka na aje ban sha ba, yayin da na ci gaba da bazarin falon tsarin gidan bai dace da gidan mace ba, ko yaya ne da bambanci. Ban gama wannan nazarin ba, na ganshi ya fito daga shi sai gajeren wando ya na yi mani wani irin dan banzan kallo, gabana ya fadi na rufe ido ina neman taimakon Allah, Allah ya bani sa'a bai iso in da na ke ba, aka kira wayarshi don haka ya koma ya dauki wayar. Ban yi wata wata ba, na fizgi jikkata na fice da gudu. Ranar nayi nadama, na ji haushin kaina da na biye ma Abdullah, a karshe na gode ma Allah da ya kubutar dani daga sharrinshi, mafarin rabuwata kenan da shi, ya yi bin, ya yi daddofa, amma ko kallo bai ishe ni ba, na ce bani ba shi har abada, kin ji dalilin da ya sa nake gudun maza, Naja lamar da ban tsoro, ke kam kin dace daga Khalid har Daddy nayi imanin da zuciya daya suke sonki, kuma su duka zuciyarsu mai kyau ce, sai dai abin da ke kike nufi da kamar wuya Naja'atu ba ki san abin da Khalid ya gani gare ki ba har yazo ya ce ya na sonki, me yiwuwa ni bani da shi, kuma gaskiya bani zon auren hadi irin haka, ana fuskantar matsaloli daga baya." Naja'atu ta ce "Haka ne, to yanzu yaya zan yi ma Khalid? Ina jin naushinshi Zainab." Zainab ta kyalkyale da dariya ta ce "Sai ki aure su su duka, tunda ai kin san 38 Sirmin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia kina son Daddyn, kuma kika yi mashi alkawari." Naja'atu ta ce "Kina daukar maganar nan wasa Zainab, ni kuma so nake yi ki taimaka mani in warware matsalar." Zainab ta ce "To ai abun ne da rikitaswa Naja, Khalid ya na sonki kuma yasha fadi haka, ko jiyan mun yi wannan hirar dashi, gaskiya ba karamar damuwa zaya shiga ba, idan ya ji wannan abun kuskure daya kika yi da kika boye mashi abin da ke tsakaninki da Daddy, da kamar ya sani to kin ga dama yasan dole cikin biyu akwai daya, ko ya same ki, ko kuma ya rasa, yanzu kau bai da wani tunani akanki.n Naja'atu ta saukar da ajiyar zuciya, ta ce "To yanzu Zainab, yaya kenan?" Zainab ta ce "Sai dai addu'a, kici gaba da addu'a, kina neman zabin Allah ba wai son zuciyarki ba, insha Allahu kafin lokacin da zaya iso an samu mafita." Su ka yi sallamea rufe wayar sai ta lumshe ido tana jin tausayin Khaku, ko wace irin dauka zaya yi mata.? Kwanaki biyu ta kasa samun natsuwa, koda yaushe tunanin yarda zata yi da Khalid ta ke yi, abun ya tsaya mata a rai, duk lokacin da su ka yi waya, takan yi tunanin ko ta fadi mashi, amma sai ta kasa, don haka ta dukufa addu'a ba dare ba rana, har zuwa ranar da ya yi mata waya ya sanar da ita ya na filin jirgi su na shirin tasowa, taji kamar kada ya dawo, amma ita kanta abubuwan sun yi ma ta yawa, kara ya dawo ayita ta kare, hakan ya fiye mata kwanciyar hankali, ta yi ma Zainab waya ta ce, "Don Allah Zainab kizo wannan satin, nasan za ki taimaka mani wajen warware matsalata." Zainab ta kyalkyace da dariya ta ce "kina bani mamaki Naja, wai ke da gaske auren Daddy za ki 39 Sirrin Zuci. 4 Sa'adstu Saminu Kankiz yi? Ya na da mata fa." Naja'atu ta ce, "Nì dai ki rabu da ni shan koko bukatar rai." Zainab ta ce "Shi kenan zani z0, hankzlinki ya kwanta." Ta ce "To na gode." Karfe goma na dare jirgin su ya sauka filin saukar jiragen sama na Nnamadi Azikiwe, in da abokinsu Jabir da Sulaiman kaninshi su ka tarbe shi, ya ji dadi sosai, ya rinka mamakin girman Sulaiman, ya zama babban mutum yanzu ya na 300 level a Jami'a. Su ma mamakin yarda yą canza suke yi, ya yi haske da girma akwai alamar koshin lafiya tare da shi. Su ka rinka murna da dokin ganin juna yana tambayar Sulaiman sauran kannenshi ya ce su duka lafiya lau, yasan za su kira su ji idan ya sauka. Da wayar Jabir ya yi amfani ya kira Naja'atu ya sanar da ita sun sauka lafiya, sai dai ya bata hakuri saboda a jiya ba za ta ganshi ba sai gobe, ga shi kuma dare ya mika. Ta yi ma shi sannu da hanya, tare da nuna farin cikinta, ya ji sanyi a ranshi sai ya rinka Kiyastawa a ranshi ko yaya itama ta koma? Yasan akwai ci gaba sosai a tare da ita. Ya fidda kayanshi su ka rankaya sai gida. Washe gari har rana ta fito ya na kwance da ya tashi ya fito falo ya zauna ya na yaba ma Sulaiman, ya rike ma shi gida da kyau, bai ga wata barna ba, sai 'yan sauye-sauyen da ba'a rasa ba, to wannan kuma yasan har da yau da gobe. Ya tura Sulaiman ya sawo mashi sabon layi na Glo da kudi ya zuba ma wayarshi ya kira Naja'atu su ka gaisa ya na tsokanarta ya ce "Ba ki da kirki Naja'atu, shi ne ba za ki zo ki yi ma maigida barka da zuwa ba.?" Ta yi dariya ta ce "Kayi hakuri don Allah, amma Mummy ba za ta barni ba." Ya yi dariya ya ce, "Dadina da ke saurin karaya, nima tsokanarki nake yi, 40 Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia insha Allahu ina nan fitowa zuwa yamma, abun ai da gaske za'a yi shi, babu wani hutu, sai naga na same ki, don haka ki zama cikin shiri, don nima da shirina na iso zani zo mu tsara komi kafin hutuna ya kare ayi abun nan

Chapter 3 of 7