dai-dai jikinta. Ta fito cikin falon, yunwa
take ji, ta hada shayi mai kauri ta sha. Amma shi
maigidan ta dora mashi sanwar kalaci mai nauyi, ta san
shima yana tare da yunwa. Ta inka tariyo wasu
abubujwa da suka faru, sai ta rinka jin tausayin shi.
Daddy ya nuna mata kauna 'yar usuli, kaunar da duk
watga diya mace za ta so ta samu irin ta. Don haka ta
daukarma zuciyarta za ta ci gaba da kula da rayuwarshi
ta rinka kyautata mashi, insha Allahu ba za ta saba
mashi ba, sai dai akan kuskure, wannan ku an ce dan
adam ajizi ne.
Kwana biyu sun samu nutsuwa da juna hankali ya
kwanta. Daddy har wata shagwbaba yake yi mata, ita
kuma don da nan sai ta marairaice ta shigba lallashin shi
tana lallaba shi. Abinci akan lokaci mai dadi da gina
jiki. Daddy ya kara shiga jikin ta sosai, sai suka zama
kamar hanta da jini. Ko da yaushe suna like, baya ko
son fita. Yanzu yanda yake jin Naja'atu a ranshi, ji yake
yi baya iya yin tafiya ta kwana biyu ya barta. Yarinyar
'yar albarka ce, ga tsabta ga ladabi, ba ta gajiya da
hidama da shi. Haka nan duk runtsi idan ya kawo
uzurinshi za ta tsaya ta ba shi lokaci sosai, sai ya
sallameta don kanshi.
To itama ta aza ma zuciyarta son Daddy,
67
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
musamman yanzu da ya shayar da ita zumarshi, ya
karantar da ita yanda za ta soshi. Jin shi take kamar wani
fangare na jikinta, idan ya fita sai ta ji gidan babu dadi,
har zazzabi take yi. Amma da zaran ya shigo, ya ware
mata hannaye ta shiga jikinshi, sai ta ji sanyi a ranta. Ba
ta taba tsammanin ana yi ma da namijin irin wannan son
ba, ashc da can duk shirme take yi, yanzu ne za tayi
mashi na Karshc. Amma da zaran ta tuna ba ita kadai ke
da Daddyn ba, sai hankalinta ya tashi. Musamman idan
ta tuna fitinar Farida. Ko yaya zamansu za ya kasance
idan ta dawo? Tana son tayi ma Daddy maganar, amma
ta lura sam baya so, don haka ta zuba mashi ido kawai.
Yau da yamma yana shirin fita, ya yi shiri cikin
kananan kaya wando Bosch baki, da shat fara mai
dogon hannu, yana tsaye gaban madubi yana taje kai, ta
zuba mashi ido, shima ita yake kallon ta cikin madubi, ta
ji tsakar jikinta tana tashi. Sai ta mike tana shirin fita, ya
aje kum din ya ce, "Ina za ki kuma?" Ta zuba mashi ido
tana murmushi, ta ce, "Ina jiranka falo idan ka gama."
Ya yi dariya ya ce, "Dadina dake tsoro. Shirya mu je mu
gaida Mummy, kullum idan na je sai ta tambaye ki, wai
ta damu da kewarki." Naja'atu ta ji dadi, tana son ganin
Mummy. Sai dai kuma za ta ji nauyin ta, yanzu ta zama
sarakuwarta. Ta fiddo mayafinta da jikka, ta sanya
takalmi flat suka fita.
Sunyi yawo sosai cikin gari, har akayi magaruba.
A National Mosque suka yi sallah,' sannan suka isa
gidan Mummy. Tayi murna da ganin Naja'atu, sai taga ta
canza mata, tayi kyau tayi kiba, alamar koshin lafiya.
Naja'atu ta zauna gefenta suka gaisa. Daddy na zaune
gefe daya yana kallon kaunar su, Mummy na son
68
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
Naja'atu. Sai da suka nutsu sannan ya gaida ta. Ta dubi
Naja'atun ta ce, "Zaman ku lafiya dai ko?" Naja'atu tayi murmushi kawai. Ta ce, "Don Allah, Naja'atu halinki da
na sanki da shi, ki rike shi, ki zauna. lafiya da mijin ki da
abokiyar zaman ki, banda fitina. Ina Faridar kuka
barta?"
Naja'atu ta zuba mashi ido. Shi kuma ya yi ma
Mummy zuru. Ta ce, "Mc ke faruwa ne kake kallona?"
Ya jinjina kai ya ce, "Tunda muka dawo ban same ta
ba." Mummy ta fiddo ido tana mamaki, ta ce, "Amma
baka kyauta ba, da ka dawon ka je gidansu?" Ya girgiza
akai. Ta ce, "Kayi kuskure Daddy, na fadi maka ba sau
daya ba, ba sau biyu ba, sai kayi hakuri, ita kantga
Faridar yarinyar ce, kuma tunda ka tsiri yin aure da wuri
haka, dole ne abuhn ya yi mata ciwo. Don haka sai kayi
hakuri da irin abubuwan da za tayi. Kuma da ka zo ka
tarar ba ta nan, me ya hana ka zo ni ka sameni kayi mani
bayani? Zuwan ka nawa gidan nan, amma baka fada ba.
Kaga yanzu sai suyi tsammanin dama kayi niyyar yi
mata wulakanci ne, tunda ga shi ta tafi baka bi ta ba."
Daddy ya yi shiru, ya san bai da gaskiya, sai dai
abin da yake dubawa, itama Faridar tana da nata laifin,
banda rashin kunyar da tayi mashi ta tafi, kuma taki
saurarar shi ta waya, bai san yanda ta dauki abun a ranta
ba. Haka nan yanda yake jin dadin Naja'atu yanzu har
mantawa yake da wata Farida, baya son ta dawo ta rikita
mashi gida. Yanzu hankalinshi ya kwanta, kaunar
Naja'atu a zuciyarshi wani sirri ne na musamman,
yarinyar tayi mashi halarci, ta san ciwon kanta, yanzu ne
ya san ya yi auri. Tana da hakuri da juriya, ga ladabi
kamar ta kwanta ya takata. Akwai wata baiwa ta
69
Sirrin Zoci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
musamman a tare da ita, wadda ke yin tasiri a kanshi. To
sai dai idan ya tuno Farida, ya kan ji tausayinta, ya san
tana cikin damuwa. Matsalarta daya, rashin wayau, a
ganin shi ai ya nuna mata iya son da take bukata, don mi
ita ba za ta kwantar da hankali ba su hada kansu, su
zauna lafiya. Daga ita har Naja'atun yana son su, kowace
tana da muhimmanci gare shi.
Ya saukar da ajiyar zuciya yana kallon Naja'atu,
tayi mashi zuru, da alamar damu a fuskarta. Tayi
kokarin hade wani abu da ya tsaya mata a wuya, sai tayi
mashi murmushi. Mummy ta ci gaba da yi mashi nasiha
kan zaman shi da iyalinshi. Haka nan itama Naja'atun ta
gargade ta, ta ce tayi hakuri su zauna lafiya banda
rigima. Ta ce ma Daddy shi kuma, Daddy tace ya je, za
ta je gidansu Faridar da kanta."
Sai da dare ya yi sosai suka tafi. Naja'atu ta debi
sauran kayanta dake gidan suka tafi. Da suka isa gida ta
wuce cikin dakin ta, ta shirya kayan cikin loka. Yayin da
shima Daddy ya wuce dakin shi. Tayi wanka tayi shirin
barci, har ta kwanta tana karanto addu'a, shiru Daddy bai
shigo ba. Ta ji wayarshi, ta dauka ta amsa mashi
muryata tayi kasa, shima kasa-kasa ya ce maganar. Ya
ce, "Kin kwanta ce?" Ta amsa, "Eh." Ya ce, "Tasowa za
ki yi, ki zo nan ina jiran ki cikin daki." Ya rufe wayar.
Itama ta kwanta shiru, me Daddy yake nufi? Ita -kam
nauyi take ji. Ta kwanta shiru, amma ta dauri ta tafi. Tа
kwankwasa ta shiga, yana kwance ya zuba mata ido. Sai
ya yi dariya ya ce, "Wai koya maki zuwa turaka za ni
yi? Kada ki saba, can gaba ki kasa zuwa." Ba ta ce komi
ba tayi murmushi kawai. Ta mai da kyauren ta rufe, ya
nuna mata waje ta kwanta. Cikin nutsuwa ya rinka yi
70
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
mata nasiha akan zaman su. Ta ce, "Kada ka ji komi Daddy, na san kana da mata, kuma na aure ka. Ai kuwa
dole ne in yi hakurin zama da ita, ni dai kawai abun da
nake rokonka shi ne, ka zama adali a cikin gidan ka,
kada ka karkata Gangare guda, daga cikinmu duk wadda
tayi ba dai-dai ba, ka tsawatar mata. Haka nan sai ka
zuba ido sosai dangane da zaman mu, ta haka ne za ka
fahimci matsalolin cikin gidan ka. Allah ya baka ikon
daukarf nauyinmu bisa gaskiya da amana."
Ya ji dadi sosai, sai ya ji ya kara sonta, ya matsa a
hankali kusa da ita ya rufe ta da soyayyarshi. Irin
soyayyar dake saurin narkar da Naja'atu, take rikita ta.
Don haka ta makance akan Daddy, ji take ruwa da iska
babu abin da za ya raba ta da shi, sai fa wani nufi daga
Allah. Wadda kullum take addu'a, Allah ya sanya ita da
Daddy mutu ka raba.
Washegari yana gida Mummy tayi waya tana
neman shi. Don haka ya yi shiri ya fita. Ta ce, "Gidansu
Farida za su je." Bai yi musu ba suka tafi. Mama na
gidanb, don haka ga baki daya aka zauna teburin sulhu.
Ita Farida ta dauki zafi sosai, ta ce dukanta ya yi. Yayin
da shi kuma Daddy ya yi rantsuwa kan cewa, ya san dai
ya mare ta, shima zagin shi tayi ta ci mashi kwala. To su
duka anyi masu fada, an sasanta tare da gargadi.
Mummy ta ba da hakuri.
Don haka Hajiya Hafsatu, ta tsare Farida sai da ta
shirya suka tafi tare. Kan hanya bayan sun sauke
Mummy, za su tafi gida, ta rinka yi mashi korafi har da
kuka, wai ya wulakantata don ya yi aure. Shi kuma ya
ce ba haka bane, laifin ta ne, saboda ya neme ta a waya
ya ba ta hakuri, amma taki saurarenshi. Yaya take so ya
71
Simin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
yi mata? Amma dai ya yi kokarin kwantar mata da
hankali. Naja'atu na cikin kicin tana aikin abincin rana
suka shigo gidan, don haka ta aje aikin da take yi, ta fito
tana yi masu sannu da zuwa. Ko kallon arziki Farida ba
ta yi mata ba, ta wuce ta bude dakinta ta shigbe. Daddy
ya dube ta, sai tayi murmushi a hankali bakinta ya
motsa, tana yi mashia sannu. Ya iso kusa da ita, ya
sanya dan yatsa ya shafi kumatunta masu taushi, ta
lumshe ido da sigar shagwaba, suka yi dariya ba ki
daya, ko kadan ba ta bari ya ga damuwarta.
Naja'atu ta koma kicin ta ci gaba da aikinta. Yayin
da shi kuma ya shigar da kayan Farida dakinta, ya dawo
falo ya kwanta yana kallo. Don haka da ta gama hada
komi ta dawo falo ta zauna suna hira da kyalkyatar
dariya. Farida na cikin daki ba ta fito ba, amma akan
idonta tana ganin duk abin da suke yi. Da ta gama abinci
ta hada ga baki daya, ta kawo falo ta shirya. Daddy na
kallon ta, ta je ta kwankwasa kofar Farida, a fusace ta
zo ta bude tana kallon Naja'atu. Naja'atu ta dan saki
fuska ta ce, "Ki zo mu ci abinci." Ta ce, "Na koshi." Та
turo kyauren ta rufe dakinta, Sai ta jinjina kai ta dawo
falo ta zauna, ta dauki filet tana zuba ma Daddy. Ya
zuba mata ido ya ce, "Kin yi ma Farida magana ko?" Ta
се, "Тa сe ta koshi." Sai ya mike ya nufi dakinta, ba ta
san yanda suka yi ba. Sai dai ta gansu sun fito tare sai
cika take yi tana batsewa. Ba ta ce mata komi ba, ta aje
ma Daddy nashi gabanshi, itama ta zuba nata, suka fara
ci. Ita kau sai da ta zuba lemu ta fara sha, sannan ta zuba
abincin dan kadan, tana ci kamar ba ta so. Naja'atu ba ta
kula ba, ta ci gaba da cin abincinta tana kallol.
Daddy ya rinka nazarinsu, shi kanshi ya san
72
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
matsalar a wajen Farida take, ta cika daukar abu da zafi, idan ta sauko za suyi zaman lafiya da Naja'atu. Ya aje cokalin yana kallon su, ya ce, "Kun gane ko? Don Allah bani son irin wannan zaman da kuke yi, Allah ne ya hada ku zama cikin inuwa daya. Don haka sai kunyi hakuri, hadin kanku shi ne kwanciyar hankalin gidan
dani kaina, don haka ku aje komi mu zauna lafiya, ku duka ina son ku, shi yasa na auro ku. Kc Naja'atu kece karama, don haka sai kinyi ma Farida biyayya, ba wai don ta girme ki ba, sai don ta riga ki shigowa gidan nan.
Ku zauna lafiya, ku fahimci junam, bani son fiutina da tashin hankali, daga cikin ku duk wadda ta tada fitina cikin gidan nan ranta za yha бaci. Haka nan kema Farida, ki kama girmanki, kada ki dauka don bani sonki
shi ya sanya na auro Naja'atu. Ba haka bane, aure nufin Alla ne, ku zauna lafiya, daga cikin ku duk wadda taga nayi mata ba dai-dai ba, ta same ni tayi mani magana. Haka nan tsakaninku ma, kada ku dauki mataki da kanku, duk abin da ya faru ni za ku yi ma magana. Haka
ne za ya kawo zaman lafiya a gidan."
Naja'atu ta jinjina kai, ta amince. Yayin da Farida ta buntsuru baki ta ce, "Ina saura kuma? Ai tun farko ba ka nemi a zauna lafiya ba cikin gidan ka, don haka in ta nemi a zauna lafiya sai a zauna. Idan kuma ba ta nema ba, duk wadda ta samu ita za'ayi." Ta mike yana kiranta ba ta kula ba ta shige cikin dakinta. Ya dubi Naja'atu ranshi ya baci sosai, amma sai ya danne ya rabu da ita,
insha Allahu ba za ya biye mata ba ayi fitinar da take
nema. Don haka ya ci gaba da kwatanta ma Naja'atun
kada ta biye mata, komi za tayi, tayi hakuri, sai tayi kokarin kauce ma duk wani abu da za ya kawo rashin
73
Sirrin Zuci.. 4 Sa adatu Saminu Kankia
jituwa tsakaninsu."
Da daddare ba ta ci abinci ba. To daga Daddyn har
Naja'atu sun zuba mata ido, harkar gabansu kawai suke
yi. Haka nan bai fasa nuna mata Kauna da kulawar da ya
saba ba ta ba. Har dare suna zaune falo suna hira, Daddy
ya fara mikewa, ya dube ta duk da langabe ta
marairaicc, ya iso kanta ya mika mata hannu tga mike,
ya je ya kashe kallo ya rufe ko'ina. Ta nufi dakinta, har
tayi shirin kwanciya ya kira tga. Ta fita ta same shi
kwance cikin dakin shi. Ya ce, "Ta je ta kawo mashi
coppee mai zafi." Ta fita, ta hado ta kawo mashi. Ya
zauna yana sha, tana zaune gefenshi. Ba shiri Farida ta
shigo cikin dakin, suk duka suka zuba mata ido, ta tsaya
bakin kofa ta rike kugu, ta ce, "To, ka ce za ki yi adalci
tsakaninmu, yanzu adalcin ke nan, da ta biyoka alhalin
ka san yau aikina ne."
Daddy ya zuba mata ido ya ce, "Amma kin san
duka yau ne sati daya da aurena da Naja'atu, kuma bisa
ka'ida sai gobe ne za ni cika mata kwanakinta. Don haka
damuwar ki yau, ba za ta shafi kwananta ba. Gobe in
Allah ya kaimu za ni fita hannunta shi ke nan, sai ki ci
gaba da rabawa. Kuma kwana daya-daya za ku rinka
yi." Ta rufe ido ta ce, "Sam ba ta yarda ba." Ga baki
daya ma sai ata zagaya ta haye gadoa tayi kwanciyar ta.
Da Naja'atu taga haka, sai ta mike ta fuce ta basu waje,
ta shiga cikin daki ta kwanta, abun ya tsaya mata a rai.
Matar nan 'yar rainin wayau ce, ba ta taba jin kishin
Daddy ba sai yau da taga Farida kan gadon shi. Wani
abu ya tukare ta a zuciya, sai ta rufe ido tana karanto
addu'o'i, har ta rasa wadda za ta karanta. Kishi fitina ne,
amma za ta gani idan Daddy za ya yi adalci.
74
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
Shi kuma a can, bai ce mata komi ba, ya ci gaba da
kurbar coppee dinshi. Da ya gama ya mike yana kallon
Faridar ranshi bace, sai yaga babu dalilin da za ya sanya
ya biye mata tana bata mashi rai, tunda ita sakarya cc.
Don haka ya sanya silifas din shi ya fice daga dakin.
Naja'atu na kwance ta ji shigowar shi, sai ta ji kamar an
zuba mata ruwan sanyti. Ya murda key ya rufe kofar, ya
iso ya ratsa jikinta, a hankali ta saukar da ajiyar zuciya,
ya hana ta magana, ya shagaltar da ita. Suna jin Farida ta
zo tana bugun kofar, sai bala'i take yi, su duka babu
wanda ya kula ta har ta gaji ta tafi. Me yafi wannan
takaici? Wasu matan kuskurfe suke yi wajen nuna wani
abu da ya hadasu da miji har kishiya ta sani, a ganin
Naja'atu idan ita ce ba haka za tayi ba, ko yanzu din nan
da a ce Daddy bai taho wajen ta ba ya tsaya wajen
Faridar, ba za ta je inda suke ba, sai dai cikin ruwan
sanyi za ta dafa shi, ai ta gano sirrinshi.
Da safe da fito, Farida na daki, har ta hada kalaci,
Daddy na kwance cikin dakinta yana barci. Don haka ta
shiga dakin shi tayi mashi gyara na musamman. Cikin
sa'a ta share duk wasu tsubbace-tsubbacen Farida da ta
zuba, ta san dai ita ke dasu. Don haka ba tayi mashi
magana ba ta ja bakinta ta tsuke, ta zuba cikin shara. Karfe goma da rabi ta koma dakinta, barcin shi yake yi cikin kwanciyar hankali. Ta zauna kusa dashi a hankali
tana murza yatsun kafarshi, ya bude ido yana kallon ta. Tayi murmushi ta ce, "Yau baka jin yunwa ne?'Rana tayi fa." Ya yi murmushi ya ce, "Ai laifin ki ne, ba ke ce kika sanya mani gajiyar ba." Tayi dariya ta ce, "Babu
ruwana, kai ne fa?" Ta mike ta shiga kewaye ta cika roba da ruwan dumi, ta fiddo
7
tawul ta kawo mashi ya
shiga wanka.
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
Tare suka fito falon, ya wuce zuwa dakin Farida.
Yayin da ita kuma ta zauna tana zuba mashi kalaci.
Farida na kwance abinta, ya shiga, ko kallon arzuki ba
tayi mashi ba. Ya yi sallama ba ta amsa ba, ya tsaya
kawai yana kallon ta. Sai ta dan ba shi tausayi. To sai
dai ya san hakan da ya yi ba laifi bane, abin da ta kasa
fahimta ke nan. Ya saukar da ajiyar zuciya ya ce, "Kin
tashi lafiya?" Ba ta ce komi ba, ta rufe ido. Ji take yi
kamar ta tashi ta rufe shi da duka, don haka ya rabu da
ita ya fitc, ya zauna suka yi kalaci. Yana shirin fita ya ce
ma Naja'atu, "Don Allah kiyi kokari komi Farida za tayi
cikin gidan nan kada ki biye mata kuyi rigima." Naja'atu
ta jinjina kai tana murmushi, ta ce, "Insha Allahu babu
abin da za ya faru." Tayi mashi rakiya ya tafi, sannan ta
koma ta ci gaba da gyaran dakinta, ta gyara ko'ina fes, ta
wadata shi da kanshi. Ba ta fito ba tayi kwanciyar ta, har
karfe sha biyu, sannan ta fito ta shiga kicin. Ita za tayi
aikin abincin rana, amma daga shi ne za ta ba Farida
aiki. Don haka tunda suka ci abincin rana ta fidda
hannunta daga harkokin Daddy, wanda ta lura, sai
daddafe yake yi dakin Faridar yana lallashinta.
A duk iya tsawon rayuwarta ba ta taba jin kshin da
namiji irin na ranar ba, musamman da dare ya yi taga
Farida ta nufi dakin shi, sai taga kamar ta saka ihu.
Kusan kwanan zaune tayi. Watau shi yasa dai wasu
matan ke haukacewa akan kishiya, amma kuma da tayi
wani tunani, sai ta jinjina ma Faridar, ganin ita ta dade
da shi amma yanzu yana tare da wata. Itama ke nan da
ta same shi ba da dadewa ba, sai da ta rinka addu'a,
sannan ta samu nutsuwar zuciyarta, tayi alwala tayi
74
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kanki.a
nafila tana rikon Allah ya sassauta rnata kishinta, kada
ya fito yanda kowa ma za ya gane. Sai da tayi sallar
asuba, sannan ta samu barci ya dan debe ta.
Karfe takwas saura, tana kwance ta ji shi tsaye a
kanta. A hankali ta bude idanuwan ta tana kallon shi
cikin shiri, yau ofis za'a. Tayi murmushi tana mamakin
barcin da tayi, sai ta yunkura ta tashi ta shiga kewaye ta
wanke baki, sannan ta dawó ta gaida slhi. Ya zuba mata
ido, sai yaga duk ta canza mashi. Ya ce, "Za ni fita ofis
sai zuwa yamma." Ta ce, "Kayi kalaci?" Ya yi
murmushi ya girgiza kai, ya ce, "Bars hi kawai, idan na
fita na samu abin da za ni ci." Ta ce, "Ba za ya yiwu ba,
mu je sai kayi kalaci za ka fita." Sai ya ji dadi a ranshi,
ya yi imanin Naja'atu ta damu da shi da dukkan
al'amuran shi akasin Farida. Sai zafin kishin ba ta damu
da kula da hakkinshi ba, yanzu haka tana can kwance
kuma ya fadi mata fita za ya yi, ba ta yi maganar kalacin
ba, ba ta damu da bai ci komi ba.
Ya zauna falo, ita kuma ta shiga kicin ta soya
mashi plantan da kwai, ta hado da tea ta kawo mashi.
Yana ci suna hira kamar wani abu bai faru ba. Sai ga
Farida ta fito a fusace tana zuba ruwan tijara, don me za
ya zauna da Naja'atu har da ba shi kalaci, wai an shiga
hakkin ta, tunda ranar aikinta ne." Naja'atu ta dube ta
tsab cikin ido babu sauran tsoro, ta ce, "Bari ki ji in gaya
maki, ni nafi karfin in yi wani abu da ya saba ma shari'a,
saboda duk iya abin da zani nema jikin Daddy na same
shi. Kinga ke nan wannan zaman ba za ya kareni da
komi ba, sai dai ina son ki sani cewa, ni ba sakarya ba
ce. Idan ke ba ki san ciwon shi ba, ni na sani. Kuma kin
san aikin naki bane, amma kika zuba mashi ido za ya
Srrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
fita bai yi kalaci ba? To ni ba za ni iya barinshi ba. Idan
kuma kina so a daina shiga hakkin naki da kike
magana, to ki tsare hakkokin mijinki."
Bakin Farida ya mutu murus. Itama Naja'atun ta
sharc, ba ta kara magana ba. Sai ta mai da bala'in kan
Daddy. To shima baya da lokacin ta, ya rabu da ita, ya ci
gaba da kalacin shi. Ga baki daya suka mai da ta
mahaukaciya. Sai ta kwasa fuu, ta shige dakinta. Har ya
gama ya yi mata godiya, ya tafi, ita kuma ida cinye
sauran da ya rage ya isheta, ta koma dakinta tayi
kwanciyar ta.
To haka zamansu ya kasauce, da wuya a yini
ba'ayi cecekuce ba a gidan. Ita dai Naja'atu tayi tsayin
daka akan mijinta, ko Farida ke da aiki, idan dai taga
za'ayi abin da za ya kwari mijinta, to fa za tayi yanda za
tayi taga bai takura ba. Yara jin dadin haka, yanzu
hankalin shi ya kwanta, bai damu da fitinar Farida ba,
tunda Naja'atu na kokarin kyautata mashi, har kagara
yake yi ranar aikinta ta dawo. Yana samun sauki sosai
da kwanciyar hankali. Naja'atu mace ce har mace, ta san
kanta, ta san ciwon kanta, ta iya tarairayar miji, a
bangaren shi ba ta da matsala, don haka ko da yaushe
yafi karkata kan ta, abin da kullum Farida take tsegumi
ke nan. Saboda kullum rana sai ta ji abin da za ya yi
mata fada, amma da wuya Naja'atu ta kuskure shi, ta san
kanshi sosai, kuma tana kokarin kauce ma fitinar.
To ai dama haka abun yake, har kullum mace mai
kwantar da kai tana lallashin miji tare da kyautata mashi,
tana kauce ma fitina, ta fi farin jini ga miji. Amma ita
'yar bala'i, sai dai bakin jini ta zama karfen kafa, har ya
zamto daga maigidan har kishiya sun raina ta. Kai ko
70
Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia
'ya'ya ke gare ta sai sun raina ta. Don haka 'yan uwa
mata sai ayi hattara, ko da yaushe ki zama mai hakuri da juriya. Idan kika samu shaida wajen miji, shi ke nan kin gama sa'a. Amma da zaran ya fahimci ke fitina ce marar
son a zauna lafiya, to wallahi ko kinyi ko ba kiyi ke dai
za'a ce kin yi. Don haka 'yan uwa mata sai a kula.
Lokaci ya ci gaba da tafi, duk irin yanda Daddy
yaso ya samu hadin kan gidanshi abun ya faskara. Sai
dai kawai yanzu ba'a samun yawan rigima kamar da, kowace tana 6angarenta, da wuya ka gansu zaune tare.
To hakan ya dan kawo zaman lafiya a gidan, shima yana iya bakin kokarin shi wajen ganin ya ba kowace hakkinta, akwai jituwa sosai tsakaninsu da Naja'atu,
yana alfahari da aurensu.
Wata hudu da auren su, aka sanya lokacin auren Zainab da Khalid. Saboda Zainab din tana shirye- shiryen kammala karatunta, don haka aka shiga hidima.
Dai-dai gwargwado ko wane bangare sunyi rawar gani. Naja'atu mamakin soyayyar Khalid da Zainab take yi,
kamar dama can sun dade da son juna, idan ka gansu
kamar ta gwaye. Sai ta gode ma Allah da ya sanya suka
rabu lafiya, ga shi yanzu ya samu madadinta.
Da lokacion bukin ya zo, aka sha shagali dai-dai
gwargwado. Nan Abuja aka aje amarya, shi kuwa ango
murna har kunne, kaunar shi da Zainab wani sirri ne na
daban, har mamakin kanshi yake yi, bai ta6a tsammanin
za ya so wata diya mace ba irin haka. Sai ya gode ma
Allah da ya kaddara cewa itama Zainab din tana kaunar
shi.
Naja'atu ta sha hidima kamar ta tsinke ranta, kan
haka ma Farida sai da ta nuna jin zafinta, tana ce mata
79
Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia
zakakka, ba ta kula ba. Ta wahala sosai, don haka ana
gama bukin ta rinka jin ciwon jiki, a hankali zazzabi ya
taho, ga baki daya ta kasa gane abin da yake damun ta.
Ranar kwana tayi kwarara amai, ga shi ranar Farida се
ke da aiki. Da safe Daddyn ya shigo duba ta, ganin halin
da take ciki ya sanya ya dauke ta suka tafi tare ya fara
aje ta asibiti, ya ce za ya je wajen aiki ya dawo sai ya
mai da ta gida.
Ya barta nan likita yana duba ta. Sunyi mata
gwaje-gwaje da aune-aune, sakamako ya basu tabbacin
tana da shigar ciki. Abun ya yi mata dadi, ta san Daddy
za ya yi farin ciki, kullum yana yi masu korafin rashin
haihuwa. To yau ga shi Allah ya kawo.
Daga ofis shi kuma aiki ya yi mashi yawa, ga shi
za sy shiga meeting. Don haka ya yi waya gida ya cе
Mummy ta tura direba ya dauko Naja'atun daga asibiti.
Ita