Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SIRRIN ZUCI NAA SA'ADATU SAMINU KANKIA (Mrs. Sani Abbas) Hakkin Mallaka (m) Sa'adatu Saminu Kankia Copy Right (c) Sa'adatu Saminu Kankia An rubuta a shekara ta: 2008 FATAN ALHERI GARE KU 'Yan'uwana abokan haihuwata Asiya Saminu Kankia Hussaina Saminu Kankia Badiya Saminu Kankia Bara'atu Saminu Kankia Jamila Saminu Kankia Bilkisu Saminu Kankia Halimatu Saminu Kankia Aisha Saminu Kankia (Ummi) Hadiza Saminu Kankia Da kuma Fatima Saminu Kankia 2 Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia SIRRIN ZUCI...4 K wana biyu, babu wata jituwa tsakaninsu. Daddy ya yi kokarin danne kwalamarshi, kwata-kwata ya fita harkarta, da safe in tashi zaya yi wanka ya yi shiri ya yi ficewarshi wani lokacin shi da gida sai yamma, idan ya dawo babu wata walwala, idan ya zauna waje ba ta zama, haka nan idan ba shi ya yi mata magana ba, ba za ta kula shi ba. Sai abun ya rinka daure mashi kai, ya kasa gane manufarta, ba ya son ya rinka biye mata suna sa'in'sa cikin gida, don haka ya kawo idanuwa ya zuba mata, a ganinshi ba wani abu ke damunta ba sai zafin kishi da rashi wayau. Karfe sha daya na safe tana zaune cikin falo, aka kwankwasa kofa ta aje littafin da take karatu, ta mike taje ta bude kofar kawarta ce Zee, su ka rungume juna suna murna sannan gaba ki daya su ka shigo falon. Dai dai lokacin Daddy ya fito daga cikin daki, Zee ta gaida shi, ya amsa babu wani sakin fuska, ko kallon sashin da Farida ta ke bai yi ba, ya dauk. mukullanshi ya fice. Farida ta tabe baki cikin halin ko in kula yayin da Zee ta bishi da ido, tana mamakin abin da ya yi sannan a hankali ta juyo kan Farida ta ce "Meye haka Farida.?" Farida ta watsa hannaye, ta ce "Oho mashi, dan rainin wayau, yau kwana uku kenan yana yi mani vannan fushin sai cika yake ya na batsewa, don na zagi wannan 'yar iskar yarinyar." Zee ta ce "Kada dai in ce wadda suka je party da ita.?" Farida ta yatsuna fuska, ta ce "Ita mana, wai don vulakanci, a cikin gidan nan ina zaune ya kirata a waya suna hira don nayi mashi magana shi ne, ya rinka yi mani bala'i ko a zaton shi in ji tsoron shi? Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia Har yana maganar wai ban daukeshi wata tsiya ba, don ina zama ina karatu, ko kallo, so yake yi in zama kamar jakka cikin gidanshi bani da burin komi sai nashi, in tsaya in ta wahala kanshi." Zee ta ce "Amma kun bani kunya, yanzu duk uwar soyayyar da kuka kwasa tsawon shekaru, ace daga yin aure ko sati bake yi ba an fara irin wanan zaman doya da manyan? Farida ta ce Duk ba yinshi bane nifa tsammani nake yi arinyar asiri ta yi mashi baya ganin kowa da gashin arziki sai ita, kayi magana kuma, abun ya zama dan zani." Zee ta jinjina kai ta ce "To ke wane mataki kika dauka.?" Ta zu ba mata ido, ta ce "Wane fa? Ni kawai share shi ne na yi, kowa haukar gabanshi yake yi, yana dakinshi ina nawa, idan ya ruga ni tashi yayi kalacinshi ya fita, idan ma ni na riga shi ko kallo bai ishe ni ba, har ya gama abin da yake yi ya fita ni dai nasan babu yarda zaya yi dani." Zee tayi murmushi ta ce "Kin ji matsalarki Farida, saurin daukar fushi, ba ki tunanin har da wadannan matakan da ki ka dauka su ka sanya ya ke wannan fushin? Mijinki ne dole ya na da hakki a kanki, kuma fa wannan ce damar da gare ki da za ki yi kokari ki kama zuciyar mijinki, amma wannan fushin ba za ya fidda ki ba, mazan yanzu shu'umai ne, sai da kwantar da kai kina tarairayarsu. Kina ji kina gani su taka ki ki kauda kai, da haka ne za ki ci ribar zama da su, amma wallahi wadannan abubuwan da ki ke yi ba za su'fisshe ki ba." Farida ta yi murmushi ta ce "Ai ri kuma kin ji in da na sha bamban kenan da sauran mata, wallahi in dai sai na kwantar da kai ne wajan miji, ya maida ni boyi-boyi a gidan, sannan za a zauna latiya to wallahi sai dai mu ci Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia gaba da tafiya haka, daga daukar bugu hutawa." Zee ta girgiza kai ta ce "Farida kada ki rinka daka rayuwar da kike yi a gidanku da komi sai an yi maki, aure daban ne, na wahalar take, dan abincin da za ki dafa ma ku ko kuwa gyaran gidan? Ji ba yanzu kin barshi ya fita bai karya ba, ina kike tsammanin zaya je ya ci.?" Ta ce "Sai yaje gidansu wahalalliyar ta bashi." Zee ta yi dariya ta ce 'Kenan kin sakar mata ta rinka jan ragamar mijinki? Kuskure ne babba kike yi, ba ri fa ki ji in gaya maki, ladabi da biyayya da kyautatawa ne ke sanya miji ya mutu kan matarshi har a rinka cewa ta mallake shi, sannan hanya mafi sauri da mace ke kama mijinta, ita ce tsare mashi cikinshi da girki mai dadi mai tsabta, kuma lokacin da yake bukatarshi, muddin kika yi sake wannan yarinyar ta gane logon Daddy kin shiga uku, don kina zaune gidan nan zata rinka aiko mashi da abinci, kuma wallahi ba ki isa kiyi magana ba, don haka ni dai ina shawartar ki ki sauke duk wani girman kai ki rinka kyautata ma mijinki ta haka ne za ki kama shi idan ba haka ba kau kina nan wata zata kama shi kuma ya auro ta ya kawo ta cikin gidan, idan ba ki a sannu ba ta fidda ki ta yi zamanta." Jikin Farida ya fara sanyi, to sai dai ita a ganinta mijin da ta aura don tana sonshi ya na sonta, ba ta ga dalilin da zata dora ma kanta wahalhalun da ba ta saba da su ba, gidansu saboda shi ai in har amarya ba ta hau doki ba, to da kunya kau a tfora mata kayam zata yi iya yinta amma ba zata kashe kanta ba saboda shi. Zee ta rinka yi mata nasiha, ita dai Farida jin ta kawai take yi. Da taga zata matsa mata sai ta tashi ta shiga daki ta kwaso mata album-album na hotunan biki ta jibga su 5 Sirmin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia gabanta su ka shiga dubawa suna hirar biki. A can shi kuma Daddy da ya fita a hankali ya ke tafiya kan hanya tunaninshi guda shi ne in da zaya je ya samu abin da zaya ci, duk abin da ya yi tunanin sai ya ji sam ya tsane shi. Ya sauka daga kan hanya ya shiga wani gidan abinci yayi odar dankali da naman 'yanshila aka kawo mashi da zafin su, ya zauna ya dan fara ci, amma sai ya ji duk ya tsani abincin, yayin da kwakwalwarshi ta gaza daukar mashi abin da ya ke faruwa, wai sunan yana da iyali kenan? Ana yin aure don a huta shi kam bai samu hutun ba, wannan fitinar da me tayi kama? Ga dai kayan abincin kamar banza a gida, amma ba su da wani amfani sai ma lalacewa suke yi ba'a amfani dasu. Ya dan ja tsoki yana kara jin haushin Farida. Halin ko in kular da take nuna mashi shi ya fi komi fata mashi rai, yana takura sosai sai dai ba ya son ya nuna mata damuwarshi ta raina shi. Ya lumshe ido a hankali ya na tunanin Naja'atu, da gida ya ke yasan da ta na can ta hada mashi kalaci mai rai da lafiya, ta kuma zauna tare dashi tana kula da shi, har ya gama idan ma ta kawo mashi ya nuna ba ya son abin ba ta fushi da sauri zata je ta sake shiryo mashi wani. Sai zuciyarshi ta rinka raya mashi sha'awar ganinta ya yi murmushi ya na ganin kyakkyawar fuskarta tana yi mashi murmushi kamar an tsikare shi ya ture kayan abincin ya fito ya shiga mota sai gida. Ya yi sallama ya shiga, Mummy ce kadai zaune cikin falo. Ya shiga ya zauna, su ka gaisa tana tambayarshi iyali, ya yi murmushi ya amsa ma ta "lafiya lau." Ya dauki remote ya shiga latse-latsenshi ya na neman tashar kwallo. sannan ya aje ya ci gaba da kallonshi, ya na sauraren in Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia da zaya ji motsin Naja'atu, bai ji ta ba, kuma nauyi ya ke yi ya tambayi Mummy, minti sha biyar yana zaune, Mummy ta yi baki, don haka ya tashi ya tashi ya shige dakinshi yanzu Ibrahim ne cikin dakin bai kwanta ba ya bude laptop din Ibrahim ya na nazarin wasu abubuwa. Zuciyarshi ta kasa natsuwa, ya dauki waya yana neman layinta shiru bai samu ba, ya rufe wayar duk ya damu har yanzu dai akwai yunwa tare dashi, ba zaya iya yima, Mummy maganar abinci ba, idan ta ji zata yi mashi tambayar ina matarshi.?" Shi kau baya son ya fasa sirrin gidanshi matsalarshi ce shi ta shafa ba zaya ji dadi ba ace sun fara samun matsala tun yanzu, abin da kunya. Ya koma bisa gado ya kwanta. A kalla minti talatin sai ga Ibrahim ya shigo, ya ce mashi "Daga ina kake haka? Ya yi murmushi ya ce "Mun fita ne da Anty Naja, zata yi Computer course ne na wata uku, shi ne muka je ta yi registration." Ya jinjina kai ya ce "Yanzu tana ina.?" Ya ce "Ta nan gida tare muka shigo." Ya ce "Je ka turo mani ita." Tana cikin daki Ibrahim ya kwankwasa mata kofa ta bude tana kallonshi ya cе "Daddy ya na kiranki." Ta ce "Yaushe ya shigo.?" Ya се "Nima na same shi kwance cikin daki. Sai ta aje mayafinta ta fito, tana mamakinshi, ashe dai da gaske ya ke zaya rinka zuwa. Ta yi sallama ta shiga yana kwance ya zuba mata ido, ta yi murmushi ta ce mashi ina yin.?" Ya tallabe kanshi yana kallonta sai ta bashi sha'awa fesfes da ta komi nata a sanyaye baya gajiya da kallon Naja'atu, musamman idan ta yi kwalliya. Ya ce "ke shi ne ba ki fadi mana karatu zaki yi.?" Ta yi dariya ta ce "Kaima dai kasan duk in fadi maka duka jiya ne muka yi maganar da Mummy ta bada aka Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia siyo mani form shi ne yau ta ce in je in yi registration." Sai ya ji ta kara burge shi ta ce "Wai yaushe ka shigo ne.?" Ya ce "Na jima da zuwa, ina ta neman layinki shiru, kin kama kin rufc." Ta ce "Wallahi mantawa nayi na barta nan gida, sai da muka fita na tuna, ya yi murmushi ya ce "matsalarki kenan ba ki san amfanin waya ba." Ta ce "Ai kuwa ina kokari duka mutum nawa nake makana da su? Ai dama kai ne to ban yi tsammanin za ka kira ni ba cikin wannan lokacin tunda nasan kana gida." Ya kalle ta kawai, bai ce komi ba suka dan yi shiru, to ita kam ba ta cika son suna zama cikin daki su kadai ba, duk da cewar tasan ba wani abu zaya yi ba, ita dai tana gudun zargi, sai taga Mummy zata ga basu yi mata daidai ba, don haka bata zauna ba, ta dube shi ta ce "In tafi shi kenan.?" Ya ce ma ta "A'a, me za ki bani in ci? Ta zuba mashi ido ta na mamakin magidanci da ya fito daga gidanshi ya ce wai ya na neman abinci, amma da ta yi nazarinshi da kanta ta fahimci damuwarshì idanuwanshi kadai ta duba, tasan yana tare da yunwa to ba ta yi bincike ba ta ce "Amma fa ba'a gama abincin rana ba, ina jin ko dorawa bai yi ba." Ya zuba ma ta ido ya koma ya kishingida, ya ce "Ni dai duk abin da kika samu ki kawo mani." Ta shiga kicin dan sauran kalacin. da take tsammanin ya rage Mick ya cinye, don haka ta bude firij ta fiddo wani kwano da sauran farfesu kaji, da sukaʻci jiya da daddare sai ta kunna gas, ta dora yana dahuwa a gefe guda kuma ta debi miya ta kara ruwa, ta sanya mai da sauran kayan hadi ta dora mashi sanwar taliya, ita kadai ce abu mai saurin dahuwa da zata ba shi. Mummy Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia ta shigo ta ce "ke kuma wa kike yi ma sanwa haka? Тa yi murmushi tana jin nauyin ta ta ce "Daddy ne zaya ci." Mummy ta girgiza kai, ba ta ce komi ba ta fice tana mamakin abun, tunda ya shigo ta lura akwai abin da ke damunshi, sai dai bata son ta shiga harkar gidanshi, wani lokacin bincike da tambayar ke janyo kace-nace а karshe itama ba za ta samu natsuwar zuciyarta ba, sai dai ana ta ra'ayin gani take yi har da laifinshi, ai matarshi ce a karkashin shi take, don mi ba zaya gwada mata abin da ya ke so ba, zaya kyale ta tana yin yarda taga dama, idan tun yanzu bai lankwasa ta ba sai yaushe.?" Ta kai mashi abincin ya yi mata godiya ya fara ci, sannan ta fito ta dauki lemo (Exotic) ta kai mashi ya ce "Ki zauna mana." Ta ce "Mummy na jira na." Ya jinjina kai ta fito ta ba shi wuri. Da ya gama ya koma ya yi kwanciyarshi, hankali kwance ya yi barcinshi na rana, sai yamma ya bar gidan. Nan din ma ba gida ya nufa ba harkokinshi ya tafi, Farida ta cika sosai, tunaninta ya tsaya kan cewa, duk saboda Naja'atu ne ya ke yi mata wadannan abubuwan, sai dare ya shigo gidan tana zauna falo tana kallon tashar wake-wake ta mawakan America, bata shi komi ba, ta kalle shi ta kauda kai, shi kuma ya zuba mata ido mamakin tsagerancinta yake yi ya kasa daurewa ya daure fuska sosai ya ce "Wai ke don Allah barin in tambaye ki, daukar me kike yi mani.?" Itama ta daure fuska ba ta ce komi ba haushinshi take ji sosai ya ce "Ke yanzu ko kunya ba ki ji, matsayina na mijinki duka ko sati ba mu yi da aure ba ace muna cikin irin wannan rayuwar? To gaskiya ba zani dauki wannan tsarin ba, idan dai kina so mu zauna lafiya to sai kin aje Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia duk wani girman kanki kin dauke ni matsayin miji, jiba yanzu na shigo gida ko kallon arziki ba ki yi mani ba, kuma wai sunan zamana kike yi, ko da kika gana zuba maki ido ba wai don kinfi karfina ba ne, kawai dai ina duba wasu abubuwa ne, babu dalilin da zaya sanya in biye maki mu rinka fitina cikin gida, to sai dai kin kawo ni iya wuya, ki fadi mani meye manufarki?" Ta yi narai-narai da ido tana shirin yi mashi kuka bakinta ya motsa kamar zata yi magana amma ta kasa ta sarda kai tana hawaye ya ce "Iliminki da wayanki bai yi maki amfani ba, Farida a matsayinki na dauka kinsan hanyoyin da za ki rinka kyautata mani matsayin majinki, amma kin zauna ke ba ga girkin ba, babu kuma biyayyar. So kike yi in rinka binki ko kuma so kike yi in rinka shiga kicin din ina girka abinci da kaina? A hankali sautin kukanta ya fara fita, sai kuma ya ji tausayinta ya tsani ya ga mace na kuka, sai jikinshi ya yi sanyi ya koma kusa da ita yana lallashinta, ya janyo ta cikin jikinshi ya na kallonta ya ce "Kin gani, yanzu meye amfanin irin haka, ni ba nufina in takura maki ba, amma a kalla ki rinka kamantawa, ban saba fita in ci abinci waje ba, don haka nake takura, ki yi kokari ki gyara kin ji ko.?" Ta jinjina mashi kai, tana kokarin tashi ya hanata ya lullube ta da soyayyarshi, cikin dan lokaci su ka manta komi. Lokaci ya ci gaba da tafiya, har yanzu dai akwai matsalolin da ya ke fuskanta, to sai dai da yake yana samun kanta sosai, damuwarshi ta dan ragu, lokuta da dama da kanshi ya ke shiga kicin ya sama ma kanshi abin da zaya ci abun ya na damunshi ya yi nasihar ya yi lallashin a karshe da kanshi ya fahimci ba wai son yin 10 Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia ne ba ta yi ba, gaba ki daya bata iya wahalar ba, girkin ma idan ta yi ba dadi har sai ya gwammace ba ta yi ba. Yarda yake samunta koda yaushe a kwance lokacin da tana gidansu yanzu ma hakan take yi. Tun ya na damuwar har ta kai ya ma saba. Da kanshi ya ke yin dukkan hidimominshi, idan zaya tafi wurin aiki, ya gama shirinshi zaya hada shayi ya sha, haka ma kafin ya taso daga can zaya biya ta gidan abincin ya ci ko zuwa ya yi ya tarda ta dafa bai ya ci ita kuma da ya ke dabba ce ba ta damuwa harkar gabanta kawai take yi. Watan Ramadan mai albarka ya kama azumi ake yi gaba ki daya maida buda bakinshi gidanshi, nan ne Mummy ta kasa daurewa ta rinka yi mashi fada, cewa abin da yake yi ba kyautawa ba ne, ya dube ta a marairaice ya ce "Mummy kiyi hakuri, amma idan ki ka hana ni cin abinci nan gidan kin takura ni, ba zani iya cin abincin Farida in koshi ba, idan na biye sai yunwa ta kama ni." Mummy ta ce "To amma wannan ai shirme ne, ka tsare ta ta rinka gyarawa mana." Ya yi murmushi shi yasan matsalar gidanshi, Farida malalaciya ce, son jikinta ya yi yawa tunda aka fara azumin ba ta yin komi sai an yi mata daidai da buda bakin iyaka ta soya kwai ta dafa ruwan zafi a sha tea abinci kuwa ba ya wuce taliya ko Indomie shi kam bai yi wannan sabon ba, ba kuma zaya iya ba. Ya ce "Ni dai Mummy kiyi hakuri dani kawai." Naja'atu na zaune tana saurarensu ba ta ce komi ba, ta dauke kanta sai ta rinka jin tausayinshi kai Allah wadaran wasu matan, to wai idan mace bata iya girki ba me zata yi? Ai ba ta da amfani kenan. Ko don mijinki da 'ya'yanki ai kin dage ki iya girki, to wasu matan sai dai 11 Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia kwalliya da gyaran jiki ka gansu kwas-kwas an fita amma babu ilimin kicin. Ita kam ko da ta taso cikin talauci ta yi kokarin iya abinci daidai gwargwado, musamman na gargajiya, yanzu kuma ta samu Mick don haka ta ida kwarewa, yanzu sai dai ta koya ma wasu. Duk da ana azumi Naja'atu ba ta fasa zuwa makaranta ba, tare da Ibrahim suke fita, a fara sauke shi makaranta, sannan itama a kaita haka nan karfe sha biyu suke tashi zata yi waya direban yazo ya dauke ta, hankalinta kwance take tafiyar da al'amurranta, su kanyi waya da Knalid amma ba kullum ba, yayin da shi kuwa Daddy kullum sai yazo gidan haka nan kamar Ibada duk safiya sai ya kirata sun gaisa. Ita kan da yake yanzu ba gidan ya ke ba sassauta ma kanta karatunta kadai ta sanya a gaba, yayin da shi kuma kullum sai ya kara jaddada mata cewa maganarshi tana nan, dariya kawai take yi mashi ta maida dukkan lamarinta wurin Allah, addu'a take yi sosai cikin watan mai alfarma, zabin Allah ta ke nema ba wai son zuciyarta ba. Watan ya raba tsakiya, Zainab ta dawo gida zata yi hutu, na sati hudu Naja'atu ta yi murna sosai, wani lokacin rashin abokin hira, yana dan takurata ba ta da aboki sai Ibrahim idan yana gida suna tare yana koya ma ta Computer. Don haka ta ji dadin zuwan Zainab, ana shirin shiga goma ta karshen watan, Mummy ta fara shirin tafiya Umra ta ce sai su koma gidan A'isha su zauna kafin ta dawo, shi kuwa Ibrahim ya ce gidan babansu zaya je, amma ana gobe zata tafi da Daddy yazo gidan, Hajiya ta fadi mashi tsarin da tayi ya ce sam bai yarda ba, ai shi ne namiji don haka gidanshi za su je su zauna, amma ai Aisha mace de aurenta ake yi." Sirrin Zuci.. 4 Saʼadatu Saminu Kankia Mummy ta jinjina maganar a ranta ta ce "Anya haka zata yiwu Daddy? Zainab ba matsala ba ce amma zaman Naja'atu da matarka nake hange, bani son fitina." Ya yi murmushi ya ce "Babu wata fitina da za'a yi Mummy, ni fa namiji ne kuma a karkashina take, gidana ne ai kuwa ba ta da ikon hana wani nawa zuwa ya zauna bani son kuma kawo irin wannan idon basu je gidana ba, su ka zauna ina ne za su zauna wanda ya fi kusa.?" Mummy ta jinjina kai ta ce "To ai shikenan, amma kai ma sai kabi a hankali kada ka ce zaka rinka zama da Naja'atu kuna magana ba zata ji dadi ba." Ya ce "Babu komi zani kula." Da ya koma gida ya sanar da Farida, su Zainab za su dawo nan su zauna, saboda Mummy zata tafi Umra." Maganar ta daki zuciyarta ta dube shi a sakarce ta ce "Ka ce dai za ka haddasa fitina cikin gidanka." Ya zuba ma ta ido ya ce "Fitina kamar yaya.?" Ta ce "Dama ai burinka ka takura mani duk abubuwan da kake yi na kyale bai ishe ka ba shi ne zaka kwaso ta ka kawo ta cikin gidan, to wallahi ban yarda ba, sai dai in bar-maka gidan, ita tazo ta zauna." Ya ce "Wannan kuma ke kika sani, amma ke din nan kinyi kadan ki tsara mani abin da zani yi, haka nan ba wai na fadi maki ba ne don in ji ra'ayinki, a'a na sanar da ke ne don ki sani kuma babu fashi, idan ba cin baki da tunani daga Zainab din har Naja'atu wacece bare a wajena? Kuma zaman da zasu yi duka na kwana nawa ne? Ko kuwa idab ba su zo nan sun zauna ba, ina zasu je su zauna.?" To ba ta sake magana ba, amma fa ta cika sosai, ta shiga daki yayi wanka ya yi kwanciyarshi har zuwa safe fushin ta take yi yayi shiri ya fita da wuri, da ya ke asabar ce. Da ya isa ya samu Mummy ta gama shiri 13 Sirrin Zuci.. 4 Sa'adatu Saminu Kankia Karfe sha biyu na rana zasu tashi, don haka babu bata lokaci su ka fito ya sanya Zainab ta zuba kayansu cikin motar Mummy ya ce su tafi da ita, saboda tafiyar Naja'atu makaranta, don haka suka shiga motar har da Ibrahim shi kuma ya dauki Mummy suka tafi filin Jirgin. Mummy ta rinka kwakkwafarshi akan ya yi komi da kula, kada ya jawo abin da zaya kawo rashin jituwa tsakaninshi da matarshi. Haka nan da su ka isa can ma ta kara gargadin Naja'atun cewa kada ta biye ma Daddy ta yi kokarin kame kanta, haka nan kada ta kuskura wani abu ya hada ta da Farida, dole ne ta bita tunda gidanta ya je haka nan kada ta rinka tsoma kanta cikin harkar gidan." a Suna filin jirgin sai da su ka fara shirin tashi, sannan su ka taho. Daddy na gaba shi da Ibrahim motarshi yayin da Zainab ke jan Mummy Naja'atu na gefenta. Ita kam Naja'atu

Chapter 1 of 7