yanzu duk ya yi missing din wannan
shagwabar da ta saba ma shi.
Ya saukar da ajiyar zuciya a hankali ya ce "To
ai kinga irin abubuwan da suka sa nake kara nace
maki har kike ganin laifina, nayi missing din ki
sosai, amma ina nan ina ta addu'a Allah ya nuna
mani ranar da za ki dawo kusa dani in rinka samun
kulawar da kike magana." Naja'atu ta rumtse ido
tana dariya sai ta yi mashi sallama ta rufe wayar
Daddt nema yake yi ya shagaltar da ita.
To bai fito ba ranar anma da daddare ya na
kwance cikin falon gidanshi yayinda Farida ke
zaune gefe guda ta dukufa karatun wani Novel abun
yakan bashi haushi ba ta da lokacin kanta balle
nashi daga karance-karance sai kallo kamar Ibada,
da ta tashi abin ta take karyawa dashi kenan, haka
nan barci ke raba ta da littafi. Ya juya yana kallonta
ba ta ma san yana yi ba, sai ya girgiza kai ya dan
lumshe ido na wani lokaci wani abu ya tsargu cikin
jininshi, sai kawai ya lalubo wayarshi ya kira
Naja'atu, tana cikin daki ta gama sallar Isha'i ta ji
wayar, ta dauka tana ınamakin Daddy, sai ta bude ta
amsa mashi da sallama ya ji muryarta har cikin
zuciyarshi, ya sanya hannu yana shafa kanshi, ya ce
"Ka da dai in ce har kin kwanta.?" Та се "A'a na
gama sallaha ne." Ya ce "To yaya garin, ina labari?
Ta yi dariya ta ce labari ai yana hannunku." Daddy
77
dan zolaya ya saki jiki ya rinka janta da hira, yana
Kyalkyatar dariya.
Farida da ta dukufa karatun littafinta ta rinkа
jin muryarshi sama-sama, yana magana tasan dai a
waya ne, ba ta maida kai ba ta ci gaba da karatun, a
hankali zuciyarta ta fara raya mata wani abu, sai ta
tsagaita da karatun tana sauraren maganar da yake
yi, ya shagalta sosau hira ta yi dadi da Naja'atu, ya
ce "Kina shakku a kaina har yanzu, ni kuma nasha
fadi maki cewa zani baki mamaki, me yiwuwa ranar
da kika zo gidana kin tabbatar da abin da nake
fadi."
Wani azababben kishi ya taso mata, da karfin
ta ta taso ta nufo Daddyn niyyarta ta fizge wayar ta
jefar ta fashe baki daya a huta, amma Daddyn ya
daure fuska sosai, yana jifarta da wani mayan kallo,
sai taja ta tsaya tana huci, yayi ma Naja'atu sallama,
ya rufe wayar bai ce mata kanzil ba, ya mike zaya
bar mata wurin, tasha gabanshi da sauri ta ce "Wai
mahaukaciya ka dauki ne ko me? Da zaka zauna
gabana kana magana da wata 'yar iska." Ya tsura
mata ido ya ce "Amma kin san ke ba ki da iko dani,
ba ki isa ba kuma ki hana ni yin abin da na yi niyya,
wannan 'yar iskar da kike magana, ta fiki hankali da
tunani, don ita ba sakarya bace, irin ki."
Ya raba ta ya wuce cikin daki abinshi, ta fasa
kuka ta fada kan kujera wulakancin Daddy ya isa,
78
duka sati daya da aurensu ba a yi ba, har sun fara
rigima irin haka, sai ta tashi zaune tana tunanin
mufita. A can cikin daki shima ya cika sosai, ya yi
wanka ya fito ya yi nafila, shafa'i da wuturi, sannan
ya fito ya shiga kicin da kanshi ya hado shayi ya
dawo dakin yasha, yayi kwanciyarshi. Lokaci
kankani barci ya debe shi. Can cikin barci ya ji
Farida tsaye kanshi tana magana, ya ture bargon ya
na kallonta ta ce "Watau ma ba kə damu da abin da
kayi ba, shi ne kazo kayi kwanciyarka, ka maidani
mahaukaciya, to wallahi ba zaka yi barci ba, sai ka
fadi mani matsayina."
Ya sa hannu yana shafar fuskar shi, ya ce
"Matsayinki ai ga ya nan na nuna maki, tunda gashi
na aure ki, kuma gashi kina wasa dashi, don haka
nima ina da right din da zani yi abin da nake so ko
kuwa ni bani da iko dake sai kece kike da iko dani?
Ko ko kina tsammanin zaman da kike yi kina
karance-karancen tsiya baki da lokacina baya damu
na? To yarda kike ganin karatun ya fiye maki, nima
abin da rayi ya fiye mani, kuma ban baki a boye ba
don ma ki sani a duk lokacin da na gama shiryeshiryena zani auro Naja'atu, in kawo ta cikin gidan
nan, in ba ki san yarda ake tafiyar da miji ba, sai ki
koya wajenta.
Farida ta rumtse ido tana jin zuciyarta kamar
zata yi bindiga, ta tsani ko ji tayi ya ambaci sunan
Naja'atu, balle har yana maganar aurenta, sai ta cije
lebe tana kallonshi, a wulakance ba ta ce komi ba ta
koma dakinta ta kwanta tana tunanin mafita, dole ne
ta mike tsaya taga ta raba zuciyar Daddy da kaunar
Naja'atu kwata-kwata sai ta zame mashi kamar
dodo, ya ji ya tsani ko ganin ta ya yi.
Shin zata yi nasara? To mu hadu cikin littafi
na hudu kuma na karfe insha Allah.
Taku; Anty Uwanin Kankia
80
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels