wujiga, akwai alamun gajiya tare dashi, sai ta
dan saki fuska ta ce "Ango kasha kamshi." Ya zuba
mata ido a wahale yana murmushi ya ce "Ko kuma na
sha wuya ko.?" Ta ce "Bayan wuya ai sai dadi." Ya
dube ta kawai, sai ta gaida shi ya tashi zaune yana
kallonta ya сс "Yunwa nake ji me za ki bani in ci.?" Duk
abin da kake so muna da shi." Ya ce "Kamar me.?" Ta
ce "Akwai abinci sosai, sai wanda ranka yake so." Ya ce
"Matsalar ba zani iya cin abinci ba, tun jiya nake jin
yunwa da uta na kwana."
Ta yi dariya ta cc "So ka yi ai da kazo ka ci nan
gida, amma dai bari in zo." Ta fito ta shiga kicin ta
shirya mashi kayan shayi, ta kawo mashi ya hada ya fara
sha, sannan ta koma kicin din ta zubo mashi sunasur da
waina da miyar ganye, ta şanshi da son abincin
gargajiya, ai kuwa ya ji dadi don haka ya saki jiki sosai
ya ci abincin. Ta na son ta fito, amma ya hana ta dole ta
zauna tare da shi ta rinka kallon dakin duk kayanshi
suna nan bai tattara komi ba, ta dube shi ta ce "To wai
kai da ke shirin tashi gidan, amma ba ka yi niyyar tattara
kayanka ba sai yaushc.?" Ya zuba ma ta ido da wata irin
siga, ya ce "An fadi maki don nayi aure shi kenan na
tashi daga gidan.?" Ta сe "To me zaka yi.?" Ya ce "Ni
da ke da babbar ajiya, ai in har kinga na bar gidan nan to
na dauke ki ne." Ta yi dariya, ta ce "Sai ka ce wata
tsuntsuwa.?" Yay: dariya ya ce "Shiri na ba'mai wuya ba
ne, idan na samu lokaci zani debi abubuwan da nake
60
bukata, amma don yanzu ba zani saki dakina ba,
idan na zo maki yini, ina zani rinka hutawa."
Naja'atu ta yi murmushi ta ce "Cika baki dai
kilama daga gobe ba zamu kara ganinka ba sai
hali." Ya zuba mata ido ya ce "Haka kike so ko.?"
Ta ce "Ba haka ba ne, wai dadi amarci ya boye ka
ko? Sai ya yi dariya ya jinjina kai ya ce "Tun da
haka kika ce shi kenan sai dai ina mai tabbatar maki
cewa yarda ke kike tsaımmani, ba haka kuma za ki
gani aikin riga kin kasa mani zuciyar gida biyu."
Naja'atu tayi dariya kawai ta duka tana tattara
kwanonin ta cc "Bari in barka kayi shiri, kada ka
makara lokacin yana karatowa." Ta dauko
kwanonin ta fito.
Kicinta koma su ka ci gaba da hidimominsu,
sai da zaya fito ya leko ya na sanye da babbar riga
ta farin yadi, da bakar hula, ya yi kyau sosai, yana
kamshin turarc, ya ce mata zaya tafi. Ta yi
murmushi ta ce "Allah ya ba da sa'a a dawo lafiya."
Ya ce "Ashe tare da Inna aka zo baki fadi mani
ba.?" Ta ce "Mantawa nayi, nima ban yi
tsammaninta sai gasu sun iso dazu." ya ce "Mun
gaisa da ita ne yanzu kin kara yi mani godiya, Allah
ya bada ladan zumunci." Amina ta rinka yi mashi
tsiya ta ce "Ka tafi kada a tashi daura auren baka
kusa aba wani." Zainab ta ce "Ba bakin ba insha
Allahu wannan auren anyi an gama ko bayanan ba
61
za'a fasa ba, don itama amaryar ba zata yarda ba."
Ya dubi Naja'atu yana dariya ya cc "Idan ma an
fasan ai ga wata nan sai in kwaso tawagata azo nan
a daura da ita, shi kenan kowa ya huta."
Naja'atu murmushi kawai tayi ita kadai tasan
yarda take jin zuciyarta kamar ta dora hannu aka ta
saka kuka, yayi mata sallama ya fice sai taji har
wani jiri-jiri yana dibarta shi kenan dai Daddy ya
kubce mata ta zauna bisa kular abinci, tan ajin su
Zainab na ta gulmar Farida to ita kam komi za'a
fada kan Farida yanzu ta gama da ita, tunda ta shiga
gabanta, gani take yi daga yau ta rabu da Daddy.
Zuciyarta ta kasa samun natsuwa don haka ta
fito ta shiga dakinsu ta kwanta kanta yana ciwo
kamar zaya tsage, cikin dan lokaci zazzabi ya
lullube ta ta kudundune cikin bargo zuciyarta cike
da tunani iri-iri dama a dawo ace an fasa daurin
auren." Abin da ta rinka raya ma zuciyarta kenan,
sai dai tasan da kamai wuya, dole ne ta natsu ta
daina yaudarar zuciyarta ta tsaya ma gaskiya, "Anya
ma Daddy ba yaudararta yake yi ba, ya na bata mata
lokaci? Tun da ga shi ya na ta hidimar aurenşhi
hankali kwance jiya ya zubda kudi sosai wajen
party haka nan har cikin dare yana tare da
Amaryarshi suna watayawa, yanzu ma gashi ya
sheka wanka ya ci kwalliya sai rawar jiki yake yi ya
tafi daurn aure, idan ba ya murna ai ba zaya yi haka
62
ba, koda ya ke dama bai taba gaya mata baya son Farida ba, ya sanar da ita su duka yana sonsu, amma
yanzu da kanta ta fahimci cewa ya fi son Parida,
tunda ga shi ya aure ta.
Wasu hawaye masu zafi, su ka rinka fita daga
idanuwanta, tana jin tausayin kanta. Zainab ta shigo
ta same ta cikin wannan yanayin, da ta taba jikinta
ta ji zafi, sai ta fita ta kawo mata magani tasha ta
koma ta kwanta. Cikin ikon Allah da ta samu barci
ta tashi sai ta ji karfin jikinta, don haka tayi wanka,
su ka sha kwalliyarsu anko din shadda ita da Zainab
suka sake ana ta hidimomin biki da su. Har dare
Daddy bai sake shigowa gidan ba, yana can yana
fama da jama'a đon haka ta rinka kokarin ganin ta
circ damuwa daga ranta, so take yi ta dasa ma
zuciyarta hakuri akan Daddy.
Da yamma su ka yi waya da Khalid ya na tambayarta hidimomin biki, ta yi murmushi ta ce
"Alhamdulillahi komi yana tafiya lafiya." Ya ce "To
ki taya mu addu'a mu ma Allah ya nuna mana
lokacin namu haka." Ta yi murmushi ta ce "Amin."
Ya ce "kin fadi ma Daddy ina yi mashi fatan alkairi
tare da murna.
Ta amsa "To:", kawai amma ko giyar wake
tasha ba zata fara sanar da Daddy sakon Khalid ba,
kusan shi ya ma fita kishi idon har ta sanar dashi sai
ya bata rai, shi yasa bata fadi mashi komi dangane
63
da lamarnta da Khalid abin da ya ke dauka ma
kwata-kwata ba su magana ita kau abin da takc
hange daban, ba zata yi kamun gafiyar baidu ba.
Har yamma tana nan gida ba ta je ko ina ba, amma
su Zainab sun tafi gidan Amarya tare da Anty
Nafisa, babbar Yayarsu. Ita kau ta cc "Babu in da za
ta je ta zauna tana taimaka ma Mummy da hidimar
jama'a.
Da daddarc ma, duk Jama'a ana gidan Amarya,
wasu kuma sun tafi daukar Amaryar daga gidansu
zuwa gidanta, don haka Naja'atu tayi shigewarta
cikin daki, tayi sallar Isha'i ta zauna tana ci gaba da
addu'o'inta har dare yayi su Zainab basu dawo ba,
Inna ma suna can gıdan Amarya, ita kuma Mummy
tare ta ke da bakinta, don haka ta zauna shiru ba ta
da abokin hira, ta yi kwanciyarta tana duba wani
littafin addu'o'i tana jin wayar Daddy ya na kiranta,
amma ta ki dauka.
Sai da su Zainab su ka shigo ta ce taje Daddy
ya na kiranta waje. Ba ta yi gardama ba, ta taso tafi,
yayin da su Zainab ke ta shirin tafiya dinner ita kam
bata yi niyyar zuwa ko ina ba, ta gaji kwanciya zata
yi. Ta fito ta same shi zaune cikin mota, ya zuba
mata ido yana nazarinta, ya ce "Zainab ta ce mani
baki jin dadi me ya ke damun ki.?" Ta yi murmushi
ta ce "Kaina ne ya ke yin ciwo, da zazzaßi nasan
gajiya ce kawai." Ya ce "Yanzu yaya za'a yi
64
cnan" Ta kafa mashi ido ta ce kamar yaya.?" Ya
Korasibiti zamu je?" Pa yi dariya ta ce "Abun bai
kai na asibiti ba, ai na sha magani na ji sauki." Ya
ce "Ba wata matsala ko.?" Ta girgiza mashi kai, ya
ce "To gasu Zainab nan sai ku shirya kuje wajan
Dinner na basu ticket a hannunsu." Ta daga kai tana
kallon wani sashin ita kam bata ra'ayin zuwa wata
Dinner.
Shima ya ci gaba da kallonta ya ce "Kada kice
mani ba za ki je ba, don mi zaki yi ta zama gida,
alhalin kowa ya fita.?" Ta dan yatsuna fuska ta ce
"Na gaji ne so nake yi in zauna in huta." Ya ce "Ni
kuma gaskiya in ba ki je ba baki yi mani adalci ba."
Ta dan cije lebenta tana kallonshi, ta ce "Ni Daddy
ba wai bani son zuwa ba ne, ko makacın haka
matarka ba zata ji dadi ba, sai ta dauka saboda wani
abu ne ko jiya kiri-kiri na yi mata magana amma ko
kallon arziki bata yi mani ba, sai ta dauka ina shigar
mata harka ne." Ya ce "To ai ba don ita kika je ba,
ni na gayyace ki yanzu ma sabo da ni zaki je, sai dai
in baki zuwa na san ra'ayin kanki ne."
T'a zuba mashi idc kawai, bata ce komi ba, ta
juya ta koma ciki babu yarda zata yi dole ne ya
shirya su tafi, idan ba haka ba ta bani da korafin
Daddy kilama ya yimata fushin ko da ya ked yanzu
koma ya yi fushin ba za ta gani ba, haka nan abun
ba zaya yi tsanani ba, tunda ba ya gidan sai yazo
65
amma dai yarda shi yake kokarin kwantar ma ta da hankali, ya na sanya ta cikin dukkan harkokinshi,
yana da kyau ita ma ta rinka kyautata mashi. Su
Zainab har sun shirya, don haka a gaggauce tayi
shirinta su ka fito, motar Anty Aisha su ka shiga, su ka tafi.
Sai da gwammace da bata je wajen ba, saboda
shirin da aka yi ya bugi zuciyarta sosai, angon da
Amarya anko suka yi na farin leshi iri daya, ban da
wannan ma, manne da juna suka shigo cikin dakin
taron, sai wani lallabata yake yi sai kace kwąi,
Naja'atu ta kara raina kanta tabbas tana wahalar da
kanta, ba ta san Daddy ya na kaunar Farida ba, sai
lokacin, sun hada kansu sai kuskus dinsu suke yi su
na dariya, ya shagalta ya manta da jama'ar da su ka
tara, sai nuna mata soyayya yake yi, abun har kunya
ya ba ta, fitsarar tayi yawa. Zuciya tazo ma ta iya
wuya, ba ta ankara ba, ta ji hawaye sun cika mata
idanuwa, ta yi dubara ta sanya mayafinta ta share
saukinta guda shi ne da ya ke su Zainab ba su kusa
da ita, ta kifa kanta cikin cinyoyinta tana nadamar
zuwanta wurin, da ta sani ta yi zamanta, fushi ne dai
yayi ya gama, idan ma ya ce daga yau din ya daina
yi mata magana ta kwana gidan sauki, tunda tasan
dole ma sun rabu kenan.
Zuciyarta ta rinka raya ma ta cewa, dama dón
ya wulakantata ne ya matsa mata, sai tazo gashi kau
66
ta gani ta tsani kanta ta tsani Daddyn kanshi, jdanuwanta suka rufe da tsananin kishi, sai taji ta fita tabar fakin taron ya fiyc mata kwanciyar hankali, idan ba haka ba kau, zuciyarta zata iya tarwatsewa, kara ta fito ko taxi ce ta samu ta maidata gida. Ta bude jikkarta ta duba tana da isassun kudi a ciki, sai ta maida ta rufe ta dan
saurara ana ta cashewa Amarya da Ango na cikin fili, su Zainab ma ana ta liki bankalin kowa ya tafi
can, don haka tayi amfani da wannan damar ta mike
ta fice.
Zuciyarta ta yi mata sanyi, ta rinka tafiya da kafa har ta fita daga harabar Otel din, sannan ta
tsaya tana jiran mota. Hankalinta ya yi nisa sosai, wajen tunane-tunane, sai dai ta ji muryar mutum kusa da ita, ta dan razana taja da baya tana kallonshi
a tsorace yanayin shi ya canza sosai, ya ce "Ina za ki.?" Ta daga kanta tana kallon Titi, ba ta ce mashi
komi ba. Ya yi shiru ya na nazarinta ya fahimci matsalarta duk da cewa tana kokarin dannewa yasan
kishi ne, sai ya ji tausayinta, ya jinjina kai ya na yi
mata magana a hankali, ya ce"vi hakuri kizo mu
koma." Ta girgiza kai ta ce "Na gaji ne so nake yi in je in kwanta." Ya ce 'To muje in kai ki" Ta се "Ка barshi kawai, zani samu tasi yanzu." Ya ce "Don Allah Naja'atu kada ki tayar mani da hankali cikin
wannan lokaci. Ta zuba'ma shi ido cike da tsana ta
67
cc kai kaso, saboda ai na san kana wajen, amma don
kada in takura maka ban ce kazo ka maida ni ba, na
fito to sai ka rabu dani ka koma ka ci gaba da
hidimomiu ka."
A hankali ya saukar da ajiyar zuciya, ya се
"Na ji ba ki kira ni ba, amma don Allah kiyi mani
wannan alfarma, ki dawo muje, sai in yi ma Aliyu
magana ya zo ya maida ki." Ba ta ce komi bai, ta
juya tayi gaba shi kuma ya biyo ta, amma sai da ya
riske ta suka jcra har cikin harabar Otel din. Nan su
ka yi karo da Farida, cikin 6acin rai ta rufe Naja'atu
da bala'i ta ce "To munafuka, gani na fito marar
zuciya, yau dai ai kisan nayi tunda gashi ya nuna
baya yi da ke, yanzu ya zama nawa, in kina son
kanki da mutunci, to tun wuri ki fidda tunanin
Daddy a ranki, idan ba haka ba zamu sanya kafar
wando daya dake, banza bakauya." Zuciya tazo ma
Naja'atu iya wuya, wai mace 'yar uwarta ce take
wulakantata haka?.
Ba ta gama wannan nazarin ba, taji Daddy da
kansi ya na bata amsa, ya ce "Ba ita zaki yi ma
rashin kunya ba, ni za ki yi mawa, tunda ni ne na ce
ina sonta, kuma haka ya ke a raina har yanzu, kuma
yarda ki ke takama na aure ki yau, itama ba da
dadewa ba aurenta zani, meye nata a ciki da za ki
tsaya kina fadi inata magana, to na dai gaya maki
bani son irin wannan sakarcin, in har za ki
68
wulakanta Najo'atu a gabana, to kuwa nima zaki iya
yi mani." Da sauri Naja'atu ta juya zata tafi, ya rike
ta yana kallon cikin idonta, ya ce "Na fadi maki ba
za ki bar wajen nan ba, sai an tashi." Ta rumtse ido
tana girgiza kai, ta tsani tashin hankali ta ce "Don
Allah ka rabu dani in yi tafiyata." Ya ce "Ba za ki je
ko ina ba." Sai ta zame hannunta cikin nashi, ta
koma ciki kan hanya ta hadu ta da su Zainab tana
tambayarta abin da ke faruwa, anje an fadi masu
gasu can suna fada da Farida, Naja'atu ta yi
murmushi ta ce "Babu kumi." Su ka koma ciki.
Sun jüna zaune sannan Daddy ya shigo tare da
Faridar, to iia dai Naja'atu ko kailon sashin da suke
ba ta sake yi ba, gaba ki daya ma zama wajen don
dole take yinshi, idab bacin bata son su yi ta
gardama da Daddy da tafiyarta zata yi. Da aka tashi
da wuri ta fita suka yi tafiyarsu, tana sane da cewa
wayarta a rufe take, tasan Daddy zaya neme ta,
amma ta ki budewa ba ta bukatar jin wani abu daga
gare shi, ba zata iya wannan bala'in na matarshi ba.
A can shima Daddy cikir: falon gidan Aliyu ya ke
kwance bisa kujera iri-kiri barci ya faskari
idanuwanshi, ya rinka auna wannan al'amarin, sai
ya rinka ganin ya rabu da Naja'atu kawai shi ne
kwanciyar hankalinshi, yau kukan da Farida ta yi
mashi kafin su rabu ya tayar mashi da hankali, ya
tsani wani ya yi kuka da shi kan wani abu, tabbas
69
abin da Faridar ta ec yana yaudararta zaya iya zama
gaskiya, to itama Naja'atun abin da tako hange
kenan. To sai dai mda ya natsu ya rinka auna
matsayin Kaunar Naja'atu a cikin zuciyarshi, sai ya
ji sam ba zaya ıya rabuwa da ita ba, koma ya ce ya
yi hakuri zueivarshi ba zata lamunce mace mashi.
Ya lalub: way a ya kira layinta, kashen dai yake
ya jima ya na nemanta yasan saboda shi ne ta rufe
wayar, a hankali ya saukar da ajiyar zuciya, sai ya
rufe idanuwanshi yana addu'ar neman taimakon
Allah a cikin lamarın."
Da safe yana kwnace, har yanzu dai bai samu
yin magana da Neja'atun ba, ya kira Zainab yana
tambayarta Naje'atun, ta ce ga ta'nan kwance ba ta
tashi ba." Ya ce "Shi kenan." Ya rufe wayar, ya aje
gefe guda, ya na tunanin yarda zaya yi da yariny.
A can itams Naja'atın tana jin shi da Zainat,
ta yi lamo ta kyale su, sai da tagaji da kwanciya doG
kanta, sannan ta yi wanka ta fito, yawanci bakin de
su ka zo daga nesa, su na ta haramar tafiya, har da
Inna, ta shiga dakir da su Iunar su ka kwana, ta
gaisa da wadanda ba su tashi ba. lokacin da ta sbiga.
gaida Inna, sannan ta zeuma kusa da Ionar, Inoa ta
rinka yi mata rasiha, tarr da gargedata akan ta ci
gaba da zama da mutane lafiya, ba ta son rigima.
Karfe daya da rabi seka tafi soi ta ji knar ta
bisu, zaman Abujar dak ya gundure ta, to tasan
70
Mumny ba za ta bari ba, haka shima Daddyn, idan
ya ji tasan wata rigimar zata dauko ma kanta. Da
yamia ne ya shigo gidan amma bai ganta ba, har ya
fita. Bai ji dadin hakan ba, to amma da ya ke ya lura
gudunshi take yi sai ya sharc ta yaga iya guduntga,
kwana daya, biyu, har zuwa na uku da gama bikin,
duk baki sun tafi Zainab ma ta koma makaranta, su
kadai ne a gidan daga Mummy sai Ibrahim sai kuma
ta rinka kewa, babu Daddy ga shi Zainab tayi
tafiyarta, idan Ibrahim ya tafi makaranta sai ta
zauna ita daya Mummy saboda gajiyar biki ba ta
cika zaman falo ba, kwanciyarta take yi cikin daki
tana hutawa, don haka zaman ya dan fara takura ta,
amma tana kokarin dannewa kada Mummy taga
damuwarta.
Da sanyin marece na ranar Laraba Mummy ta
fita zata je duba wata Kawarta Hajiya Barira, bata
jin daui taua kwance asibiti Ibrahim ma ya tafi
lesson, bai dawo ba, sai ita kadai a gidan da mick
yana aiki cikin kicin ta fito sanye da atamfa 'yar
Holland ruwan kunun kanwa, ta zauna falo tana
kallon wani film a tashar Nollywood hankalinta ya
tafi sosai tana son ta ga yarda zaya kare. A hankali
ya shigo cikin falon sanye da kananan kaya, shirt
fara mai dogon hannu da bakin wanão, idanuwanshi
manne da gilashi muryarshi kasa-kasa yayi sallama
don haka ba ta ji ba har ya shigo cikin felon, sai dai
71
kawai taga mutum tsayc gabanta, zuciyarta ta rinka
harbawa da sauri sai ta rumtse ido tana ncman
taimakon Allah, yayin da wani abu ya tsargu a
jininta, a bangare daya kuma kishi matsananci ya
taso mata, sam ta tsani ganinshi.
Bai ce mata komi ba, ya zauna yana kallonta
kawai, itama ta kasa cewa komi, ta rinka kokarin
hade wani da ya tase mata yana neman hana ta
lumfashi "Me Daddy zaya ce mata yanzu, bayan ya
nuna mata iyakartą, ya nuna bai damu da ita ba, ya
sharc ta tsawon kwanaki. Sai ta ji tausayin kanta,
tabbas son maso wani koshin wahala be, ita kam ta yarda tana tare da wahala.
Ta rinka kokarin sassauta zuciyarta, sannan ta
dube shi ya zuba ma ta ido ta gilashi ya sanya
harshe ya lashi busasshen lebenshi sannan ya yi
gyaran murya ya ce "Naja'atu har yanzu fushin kike
yi baki tausayina ko.?" Zuciya ta tsaya ma ta iya
wuya, rainin hankalin Daddy ya isa kenan ita zaya
azama laifin? Ko da yake ba yinshi ba ne, giyar
amarci ce ke gaya mashi karya. Ta jinjina kai amma
sai ta kasa ce mashi komi, yayin da shi kuma ya
zauna dai dai cikin kujera ya dauki remote ya nemo
tashar kwallo, suka yi shiru na 'yan mintuna sannan
ya aje remotc din ya na kallouta, ya ce shi ne ko
kiyi jajena kwana biyu kuma kin kama waya kin
rufe don kada kiyi magana da ni ko.?" Naja'atu ta
72
dan tabe baki cikin halin ko in kula ta ce "Aí na san
lafiyar ke haifar da shiru, ko so kake yi in kira ka ko
kuma kai ka kira matarka tayi ta tsira mani wani
bala'in, maganar gaskiya Daddy ina gudun fitina,
ina ganin mu hakura da juna kawai shi yafi."
Ya yi murmushi ya ce "Idan ke kina jin za ki
iya hakuri dani, to ni ba zani iya ba, kuma in kika
fadi haka ni baki yi mani adalci ba, idan kika duba
ai ba dani kika yi rigima ba, da Farida kika yi kuma
dake da ita a karkashin inuwata zaku zauna, dole ne
kubi tsarina, kinga kenan babu dalilin da zaya sanya
kice saboda ita kin rabų dani, sai i da ma kinyi
niyyar rabuwa dani din don ra'ayin kanki wannan ba
zani takura maki ba." Naja'ati ta sarda kai ya daure
ta sosai, da igiyar kaunarshi abin haushi sai ma taji
ta kara kaunarshi ya yi wani kyau na rnusamman ya
yi fresh, alamun koshin lafiya da kwanciyar hankali,
ko don ta rabu da ganin shi ne, sai taga ya kara yi
mata girma kwarjininshi ya cika falon duk irin
yarda ta kudurta share shi abun ya çi tura.
Yayin da shi kuma duk ya marairaice mata ya
cikata da hirar soyayyarshi, ya kwanta kan kujera
yana jifarta da mayen kallon nan, ai don da nan ya
ida luguiguitar da zuciyarta, ta kasa tabuka ka komi,
cikin ruwan sanyi ya shawo kanta ta saki jiki suna
hira. Nan Mummy ta dawo ta same su sai dai kawai
ta girgiza kai suka gaisa, ta shige diaki, wani lokacin
haushin Naja'atun take ji ta na ganin rashin
wayaunta akan biye ma Daddy da take yi yana Gata
mata lokaci, idan ita ce tunda har yayi aurenshi
wallahi ko kallo bai ishe ta ba, to ta biyc mashi bata
san me yake fadi mata ba, da yake shagaltar da ita
irin haka.
Da aka yi kiran sallah, ya fita a tunaninta ya
tafi kenan, amma sai ga shi ya dawo da iyayen sayesayenshi, ya yi mata na kayan kwalama har da IceCream. Nan ma su ka dasa wata hirar, yana kara
jaddada mata irin kaunar da yake yi mata, sai ta
rinka ganin kamar ba ya son wata diya mace idan
ba ita ba, to wai ma yana da lokacin Farida kuwa?
To in baya da lokacin ta meye amfanin ajetan da ya
yi gidanshi, ga alamanan ma ta gani,sai wani kara
budewa ya ke yi idanuwanshi sun bude yanayin
kallon da yake yi mata ma ya canza sosai, har tsikar
jikinta ta tashi take yi, to itama Faridar haka yake
fadi mata? Abin da ta kasa tantancewa kenan, halin
maza sai su, tana ganin kokarinsu wajen raba
zuciyarsu da suke yi.
Dare ya fara mikawa, yana kwance abinshi ba
ya da niyyar tafiya, ya sanya ta kawo mashi abun,
ya zauna ya ci hankali kwance. Karfe tara ta dan
wuce Mummy ta fito daga cikin daki, tana kallon
agogo ta ce "Wai Daddy kanka daya da zaka aje
diyar mutane ka zo nan ka zauna.?" Ya dubi
74
Mummun yana shafa kai, sai kuma ya kalli
Naja'atun kunya ta rufc ta, ta sarda kai tana jin
nauyin Munuyn, Mummy ta ce "Tashi maza ka tafi
bani son sakarci, ta harari Naja'atun da wasa ta се
"Kema har da ke, kin zauna kin biye mashi yana ta
tsara ki."
Naja'atu kam ba baki, ita kam bata lura da
lokaci ba, Daddy ya shagaltar da ita sosai, yayin da
shi kuma ya aje remote din kan tabur ya mike yana
kallonta, Mummy ta girgiza kai ta wuce kicin, ya
zuba hannayenshi cikin aljihu, ya ce "Ba ri dai in
wuce kada Mummy ta kai ga dukana, amma don
Allah kada ki rufe mani waya zani kira ki kafin in
kwanta." Ta amsa "To", kawai ya yi mata sallama
ya tafi, ya na fita ta rufe wayarta, Ibrahim ya fito
daga dakin karatu ya zauna su ka dasa hirarsu. Zuciyarta ta yi sanyi, dk wani 6acin rai da ta rinka
fama da shi na 'yan kwanaki Daddy ya wanke shi
fcs, har taje ta kwanta tana tunaninshi da hirarsu ta
yau, wata sabuwar Kaunarshi ta kara mamaye
zuciyarta tabbas yaudarar kanta take yi da take
tunanin cewa zata iya rabuwa dashi, itama tasan ba
zata iya ba, sai dai ta ci gaba da addu'a Allah ya yi
mata zabi mafi alheri.
Washe gari tana bude wayarta text dinshi ya
shigo da kalamai masu dadi, ya na kara jadadda kaunarshi gare ta, tà gama karantawa ta ajc wayar
75
Ihushi farin ciki fal da cikinta, yanzu kam
ta yarda Daddy yana sonta tunda ga shi ya yi auren
bai canza ma ta ba. Ba'a ji ma ba ya sake kira su ka
gaisa yana yi mata tsegumin jiya ta rufe mashi
waya. Ta yi munnushi ta ce "Ni ban dauka wai da
gaske zaka kira ni ba, naga ka koma cikin iyalinka
koda yake laifin Faridar ne da ta baka damar yin
wata waya cikin daren alhalin lokacin ta ne ko
zaman da kayi nan fa jiya ka shiga cikin lokacin ka,
don haka gaskiya ka daina kana shiga hakkinta,
kuma kasan ance bulalar uwargida tana nan an aje
ma amaryarta, ni kam ba zani dauki irin haka ba,
kai ba zani baka damar da zaka saurari wani ba ma,
in dai har kana tare da ni.
Daddy dariya ya rinka yi mata, ya ce "Allah
ko.?" Ta ce "Kana wasa da ni ne." Sai ya ji dadi a
ranshi, matsalar da ya fara fuskanta da Farida kenan
tun ba'a je ko'ina ba, ba ta damu da tsayawa kan
al'amurranshi ba, yarda ya saba yi ma kanshi komi,
yanzu bai samu wani sauyi ba, idan ta zauna tana
kallo mantawa take yi da komi har shi din, haka nan
da safe ma barci sai ta kai azubur kusan shi ke hada
ma kanshi kalaci don haka ya yi kewar Naja'atu
tabbas Naja'atu mace ce tagari wadda tasan ciwon
kanta, koda yaushe tsaye take akan dukkan
al'amurranshi, yana ganin kokarinta ya na jinjina
76
mata