shima iyayenshi talakawane kamar
nata ya dandani talauci ya kuma sanshi, ba ta tsammanin
dan arzikin da ya yi yanzu zaya sa ya raina talaka.
Amma a can ko shi Daddy bai raina masu ba,
itama Hajiyar bata raina ba, tabbas 'yan bani na iya da
dangin mahaifinsu sai sun yi tsegumi, ita kanta Farida
raina mata zata yi, daga nan sai wulakanci ya shigo.
Ranar kasa barci ta yi ta rinka juyi ita daya cikin daki,
tana ta ce wasu abubuwa, sai ta gano cewa yaudarar
kanta kawai take yi.
Ya rage saura sati biyu biki, aka kai lefen gidansu
Farida, Daddy ya zuba ido yaga ko za'a maido saboda
har zuwá lokacin Faridar fushi ta ke yi, amma ga
mamakinshi sai yaga an amsa har da iyayen kayan
tukuicinsu, zuciyarshi tayi sanyi ga abubuwa suna ta
30
karatowa, dole ya daure yajė wajen Farida su sasanta kansu tun kafin mutane su san halin da suke ciki.
Da yammacin ranar ya yi shiri cikin wata shadda Ghalila ruwan cincin bale dinkin tazarce, ya murza hula
kube dinkin Maiduguri, jikinshi yana kamshin
turarenshi Designer, da karfinshi yayi niyyar jinkirta ayi
ta ta kare lokacin da ya fito falo. Naja'atu na cikin daki don haka ya rabu da. ita ya fice, baya son taga shirinshi
ranta ya 6aci, sai da ya fito kan hanya ya kirata ya sanar
da ita ya fita. Ba ta san in da zaya ba, amma zuciyarta ta
raya mata cewa wajen Farida ya nufa ta yi kokarin
danne damuwarta tunda tasan dole ne ta yi hakuri da shi
ta yi mashi fatan alkairi ta aje wayarta koma ta yi kwanciyarta.
Bisa hanya yana tafiya, ya rinka tunanin abin da
zaya fadi ma Farida idan yaje, yasan dai zaya sha tsegumi da korafi. Ya tsaya super market ya yi mata
sayayyar kayan kwalama, sannan ya ida isa, yan kannanta su ka iso suna yi ma shi sannu da zuwa, ya bisu daya bayan ya na raba masu cokulet, Salim ya ruga cikin gida ya samu Farida zaune falo tare da Mama, ya matsa sai ta fito ga Daddy yazo. Haka nan sai ta ji tana sha'awar ganinshi, duk dai da cewa tana jin zafinshi musamman kan halin ko in kula da ya nuna mata, ya san ya bata mata rai, maimakon yazo ya bata hakuri, sai ya sharc ta ya rinka turo mata kalaman yaudara ta waya wadanda da ita take dauka yaiddra ce kawai.
Ta na jin Salim ya na magana ta share shi ta ci gaba da karatun littafi. Mama ta ce "Farida kina ji ana
31
gaya miki Daddy ne amma kin yi shiru." Ta dan bata
fuska ta ce "Mama rabu da shi kawai, me zaya fadi
mani.?" Mama ta daure fuska ta ce "Me ya sa ke ba ki
jin magana? Kin cika daukar abu da zafi, yanzu komi
Daddy ya yi maki, ai ya dace ki share, ko don wannan
uban lefe da su ka zuba maki, idan babu so ai ba za su yi
maki irin haka ba, to me kike so kuma.?" Ta zuba ma
Mama ido, tabbas abin da ta fada gaskiya ne, abokanta
ma sun yaba da lefen da yawa suna fatan Allah yasa su
samu ko rabinshi ne, sai ta taso ta fito.
Siket da riga ne na wani yadi a jikinta, kanta babu
kallabi ta sanya gyale dan yalala ta rufe kanta kafarta da
takalmi silifas 'yan Madina bula, ta na rike da littafin har
ta iso in da Daddyn ya ke zaune cikin mota, ba ta ce ma
shi komi ba, ta jingina da motar tana duba littafin.
Daddy ya dan zuba mata ido, bai ji dadın abin da ta yi
ba, amma sai ya yi murmushi ya fito daga cikin motar ya
tsaya gabanta ya na kallonta kawai, yayinda ya fito daga
cikin motar ya tsaya gabanta yana kallonta kawai yayin
da ita kuma zuciyarta ta ci gaba da harbawa da sauri da
sauri tana jin matsanancin kaunarshi a zuciyarta.
Zuciyarta ta kare sai hawaye, Daddy ya ci gaba da
kallonta, ya ce "To menene kuma Farida? Yanzu ashe ni
bani da kimar da za kiatani hakuri akan ko wane irin
laifi na yi maki.? Liạe na yi maki da za ki dauki
irin wannan ma Farida ko da yaushe mu
'yan Adam ajizar dace ki tsaya ki saurari
ma kin dauki wannan
bayanin da zani
matakin, ya ya kike ?" Muryarta na rawa ta
ce "Au laifina ma kake gani.?" Ya ce "Ban ga kiifin ki
ba, sai dai ya ce komi zani yi ma ki ki rinka yin hakuri.
Farida aure fa zamu yi mu yi rayuwa ta har abada, to
idan tun yanzu ba mu hafa kanmu ba mu ka fahimci
juna sai yaushc.?"
Ta ce "To amma Daddy kai kanka kasan abin da
kayi baka yi daidai ba ni fa kayi ma lafi, a kalla ya dace
ka zo in da nake mu sasanta kanmu, sai ka nuna baka da
lokacina ka zauna kana faman yi mani waya, wannan shi.
ne kulawa?" Ya cc "Na yarda na yi laifi nan, sai dai abin
da ya sanya banzo ba, bani son in zo muyi rigima ne don
haka na baki lokaci ki sauko." Ta tsura ma wata fulawa
ido, ita har yanzu ba ta ji abin da take son ji ba, so ta ke
yi ta ji ya ce "Ba son Naja'atu ya ke yi ba." To ya tsaya
sai wani zagayc-zagaye ya ke yi ma ta. Ta ce "Ni kuma
abin da na dauka, don ka samu wadda ka ke so ne ya
sanya ba ka damu da ni ba."
Ya yi murmushi ya ce "Ke ma ina son ki Farida."
Ta zuba ma shi ido zuciyarta na harbawa, ta ce "Da
kuma Naja'atu ko.?" Sai ya cije lebenshi ya na kallon
wani sashi, yaso ace ta yi hakuri da maganar har sai bayan aurensu, amma yasan rigimar Farida, ba za ta barshi ya zauna lafiya ba, dole ne ya fadi ma ta, ayi ta ta kare. Ya saukar da ajiyar zuciya ya ce "Ina son ki fahimce ni sosai Farida, da ni dake da Naja'atu mu duka
ba mu da iko da zuciyarmu, sai abin da Allah ya yi, sai dai Allah ya sani ina son ki kuma kema in har za ki yi
mani adalci kinsan ina sonki, kuma kinga manufa ta akanki son nake ki zama matata uwar 'ya'yana in Allah
33
ya yarda Haka nan cikin dan lokaci Allah ya jarabce ni
da Kauvar halayyar Najalatu, a karshen magana na tsinci
kaina dumu-dumu cikin kaunarta, ba wai don bani sonki
ba, maganar gaskiya ina son Naja'ata, kuma burina ku
duka in aure ku, in Allah ya nufa."
Kuka ta fasa mashi, ya tsaya kawai ya na kallonta,
уa сс "Ва wai na fadi maki ba ne don ia Sata maki rai.
sai don nasan duk dare dadewa wata rana gaskiya zata yi
halinta, in har Ailah ya kaddara zani anri Naja'atu dole
ki sani lokacin zaкі сс па manufunce ki, amma yanzu
idan kika yi tunani bamu da tabbas akan abun, sai abin
da Allah yayi, don haka ki rahince ni ki kwantar da
hankalinli, mu tsara hidimomin dake gabenmu, mu ci
gaba da addu'a Allah yayi mana zasí mafi alkairi,
sannan ina so ki dasa ma zuciyarki cewa ni inai kaunarki
ne, kma ma ta rashin so ko wani abu ai ya Karc Farida
tunda ga sri ar kawo wannan lokacin, nan da sati biyu
fa kin zama matata, lokaci ya na kurewa, idan bamu
hada kanmu ba yanzu, mu ka shirya yarda harkokinmu
zasu tafi sai yaushe.?"
Ya ci gaba da kallonta da salon yaudararshi, jikinta
ya yi sanyi lakwas, a hankali ta sauke kwayar idonta
kasa, Daddy ya gama da zuciyarta matsalar ba ta iya son
kowa idan ba shi ba, me yiwuwa hakan ya lura da shi
yasa ya ke wahalar da iia. Tana so ta yi mashi wata
tambayar, amma ya hanata ya ce "Mu aje wannan
maganar gefe daya Fariia, inda ba yau zaa yi ba, ba
gobe ba, don haka muyi wadda ke gabarmu, yaya
maganar kaya kin gani sun yi maki ko akwai abin da ba
34
a sanya ba?" Ta yi murmushi ta ce "Sun yi." Ya ce
"Kada ki ji komi idan akwaı abin da bai yi maki ba, ki
sanar dani, a shiryc nake in yi komi akanki don in
tabbatar maki kaunata gare ki." Ta cc "Allah kuwa yayi
babu matsala, mutane na yabawa, nima na yaba." Ya cc
"To A lhamdulillahi, sai sauran shirye-shirye."
Daddy dan dabara, ya tattara hankalinta akanshi,
ya raba ta da duk wata damuwa, dole ta saki jiki, su ka
isara komi yarda take so, sai dai ya yi kokarin rage wasu
bidi'o'in da taso ayi, ba don komi ba sai don kauce ma
bacin ran. Naja'atu, itama ko yanzu yasan tana cikin
damuwa. To babu laifi Farida ta fahimci bayaninshi, don
haka su ka tsara komi a saukake. Dinner party ne da
za'ayi ranar da aka kai amarya, za su yi tare dashi, amma
duk wasu hidimomin ya barsu na mata kawai, to ita kam
ba haka taso ba, sai dai ya ce ta yi hakuri shi haka yake so."
Kiri-kiri ta kasa ganin laifin Daddy, duk kuwa da
cewar tasan ya yi ma ta ba daidai ba, su ka sha hirar da
su ka dade ba su yi ba, har dare ya na gidan, sannan ya yi mata sallama ya koma gida. Suna zaune falo ya shiga, ya sanya Naja'atu ta kawo mashi abincinshi, yana ci ya
na yi ma Hajiya bayanin shirye-shiryen da suka yi da Farida, na shagalin biki. Naja'atu ta yi jagale tana kallonshi, sai dai ta ji tausayin kanta ta kwantar da kanta bisa hannun kujera tare da rumtse ido, sai ta shiga addı' akan Allah ya raba ta da son maso wani, tabbas koshin wahala ne, ita kam ta yarda tana cikin wahala. Akan Daddy kiri-kiri ta rufe idanuwanta karfi
35
tana nema da
Nar Nya ma Khalid baya, ko jiya sunyi waya yana
Korati ne yasa take rufe wayarta? Sai ya rinka kira ba
Ta kafe kan cewa wayarta a bufe take sai
da diake tufewa, sai dai rashin kyan network. Amma a
ahiri rufe wayar take yi don kada ya kirata a gaban
Daddy ranshi ya baci. Dole ne ta daina yaudarar kanta ta
tsaya ma gaskiya.
Shirye-shiryen biki suka ci gaba da kankama,
Mummy koda yaushe cikin hidima take, a bangaren
Daddy shima ya bugo katin daurin aure da na biki suna
ta rabawa, Naja'atu ta kara raina kanta, duk sai tà ji ta
1sani zama Abujar. Ta shiga damuwa sosai, Daddy ya na
fura da ita, ya rasa yarda zaya yi ya shawo kanta, sai ya
rinka jin tausayinta cikin dan lokaci duk ta sukurkuce, ta
yl rama. A fangaren itama Naja'atun, tausayin kanta
take yi sosai, so ta ke da karfin tsiya ta yakice Daddy a
ranta, amma hakan ya faskara saboda koda yaushe kara
kusanta kanshi ya ke yi da ita, ta yi kukan zuci ta yi na
sarari a karshe ta dukufa addu'ar Allah ya zaba ma ta
abin da ya fi zama alkairi.
Ya rage saura kwana takwas biki, Daddy ya kawo
mata kayan cin biki kala biyar ita da Zainab masu tsadar
gaske, har da jikka da takalmi mahadinsu ya ce ta shirya
uje ta ba da masu dinki, tun da Zainab na makaranta, ta
ve sai cikin satin da za'a fara biki za ta iso. Naja'atu ta
kafe kan cewa ba za ta karbi kayanshi ba, Mummy tayi
masu. Ya ce "Amma kyautar Mummy daban take da
awa ko.?" Ta ce "Na sani, sai dai ka barsu kawai na
Ya zuba mata ido ya ce "Naja'atu so kike yi ki
36
tayar mani da hankali ko? Na sani da ciwo, amma duk
abin da ka yi hakuri da shi zaka ga bayanshi, don Allah
kada ki karya mani zuciya, ina bakin kokarina fa."
Kuka ya kubce ma ta ba ta cc komi ba, ta dauki
ledar kayan ta shiga daki da su, Daddy ya jima zaune ya
na tunanin lamarin mata sai su, ko yau din nan sai da
Farida ta same shi Ofis tana yi masa korafi kan
Naja'atun, to sai dai jin dadinshi guda, ita Naja'atu ba ta
korafin, da wuya ta yi mashi magana kan Farida, sai-dai
da ya kalle ta ya kan ga damuwarta a fili, duk ta rame
al'amarin sai du'a'i.
Ranar Talata ana gobe za'a fara biki, Mummy zata
aiki direba Katsina ya dauko ma ta wasu kaya can
gidansu, don haka Naja'atu ta kuduri niyyar binshi ta yi
tafiyarta ta huta. Cikin daki ta shirya kayanta cikin
jikka, da 'yan kayan amfaninta na shafe-shafe ta daga
karkashin kayanta in da ta ke ajiyar kudi wasu tun irin
wadanda Khalid ya ba ta ne kafin ya tafi, bata yi komi
dasu ba, babu abin da zata saya, Daddy ya tsaya mata
kan komi daidai da cakulet sayo ma ta yake yi da yawa
ta aje tana sha. Hak nan itama Mummy na iya kokarinta
duk wata idan tayo sayayyar kayan amfanin gida, zata
sawo mata har da pad, da ma duk wani abun da tasan
zata bukata, don haka ba ta da matsala kan komi, duk
wasu kudin da za su shigo sai dai ta aje su, don haka
yanzu ta kwashe su ta zuba jikka tana son tayi ma
iyayenta tsaraba.
Sai da ta kimtsa komi, sannan ta fito falo wajen
Mummy, in da take jiran direban ya dawo daga shan mai
37
ta ba shi sakon. Ta isa ta zauna, tana kallon Mummyn a
marairaice, itama kallonta take yı tana lura da yanayin
da take ciki, ta dora ma ranta damuwa sosai, kuma tasan
duk saboda Daddy ne. Naja'atu ta kwantar da kai, ta ce
"Don. Allah Mummy kiyi hakuri ki barni in bi
Babangida inje Katsina, ina son in karbi takarduna na
makaranta." Mummy ta zuba ma ta ido ta ce "Ki ce dai
kina son ki gudu kawai." Ta girgiza kai ta ce "Ba haka
ba ne, zani dawo." Mummy ta yi murmushi, ta ce "Kada
ki boye mani komi Naja'atu, na sani saboda auren
Daddy ne kike son tafiya, ko ba haka ba.?" Naja'atu ta
sarda kai ba ta ce komi ba, Mummy ta jinjina kai ta ce
"Ba zani hana ki abin da kike so ba, ina lura da halin da
kike ciki Naja'atu, bani jin dadi, amma in har hakan
zaya sama maki kwanciyar bankali, to ki shirya ku tafi,
amma kiyi mani alkawarin cewa zaki dawo."
Zuciyarta tayi sanyi, ta ce "Allah Mummy zani
dawo." Mummy ta ce "Sai ki shirya ku tafi, Allah ya
kiyaye hanya." Sai ta ji kamar an yi mata bushara da
gidan Aljanna, zuciyarta ba za ta iya jure ganin Daddy
da wata ba, da sunan wai aurensu ake yi, kara ta daga
masu daga baya ta dawo, lokacin tasan komi ya lafa,
yana can gidanshi tasan ba ko da yaushe zata rinka
ganinshi ba, hakan zaya taimaka mata ta yi saurin yakice
shi daga zuciyarta.
Ta na cikin daki Mummy ta kirata, ta shiga cikin
daki ta same ta, ta kawo kudi har dubu hamsin ta ba ta,
ta ce "Ki kaima Babanku dubu ashirin ya sayi kayan
azumi, tunda ga azumin nan tafe, sai ita ma Salamatu ki
38
bata dubu ashirin, dubu goma ki rike sai kisi
hidimominki, ga atamiofinan ki kaima Salamatu, sai na jiki a waya."
Naja'atu kamar zata yi kuka, samun mace mai
mutunci da ta san hakkin dan Adam irin Hajiya Halima
yana da wuya, ga dai dukiyar Allah ya bata, amma sam
bata dauki kanta wata tsiya ba, ta yi ma ta godiya ta jc ta
shirya kayan a jikkarta direba ya iso, suka dauki hanya.
Sai ta ji hawaye sun cika mata ido, ta sanya
mayafinta tana sharewa, sai dai hankalinta ya kwanta
daganin wani Gacin ran kara acc ba ta kusa, Insha
Allahu zata yi iya bakin kokarinta taga ta fidda Daddy a
ranta.
Karfe biyar na yamma Daddy ya shigo gidan
dawowarshi kenan daga Ofis ya zauna falo ya na ta zuba
ido yaga Naja'atu ta bullo, duk dai da cewa ta 6ata
mashi rai, na rufe wayarta da ta yi, tun a ofis ya ke
kiranta bai samu layin ba yanzu da ya iso yunwa ya ke ji, so ya ke ta ba shi abinci amna shiru bai ganta ba. Ya
naaune ya na tunanin ya tashi ya wankwasa kofar ta,... ga Mummy ta fito, tana tambayarshi ofis. Ya lumshe ido cike da gajiya ya ce "Alhamdulillahi Mummy." Ta na zama, wayarta ta yi kira, ta duba taga Naja'atu ce, sai ta yi muımushi ta bude, Naja'atu na yi mata bayanin sun sauka gida lafiya. Ta yi murmushi cike da mamaki, ta ce "Kai anma kinyi sauri Naja'atu, sai kace iyakarku Kaduna.?" Naja'atu ta yi dariya a ce "To na gode, ki gaida mani da mutanen gidan, Allan ya huta gajiya."
Daddy ya zuba mata ido cike da mamakin abin da
ya ji tana fada, ya kasa daurewa ya ce "Ina Naja'atun ta
tafi.?" Mummy tayi dariya tga ce "Gida ta tafi, tare da
Babangida su ka tafi, shi ne ta ke sanar da ni cewa har
sun sauka." Makoshinsa ya ida bushewa, har ya gaza
cewa komi, ya sanya hakori ya cije lebenshi, yayin da
idanuwanshi su ka kankance saboda bacin rai, Naja'atu
ba ta taba yi mashi abin da ya 6ata mashi rai ba, irin
tafiyar nan da tayi. Ya fesar da wani iska mai zafi ta
bakinshi, ya ce "Mummy me yasa ba ki sanar dani zata.
tafi ba.?" Ta yi murmushi ta ce "Ai ba wani shirya ma
tafiyar ta yi ba, nima sai yau din ta sanar dani wai tana
so taje ta karbi takardunta makaranta, to naga ta damu
don haka na rabu da ita, me yiwuwa hakan zaya fiye
mata kwanciyar hankali."
Daddy ya jinjina kai ya ce "Ta dora ma ranta
damuwa ne da yawa, na fadi mata ta kwantar da
hankalinta, to ita gani take yi idan nayi aure zani rabu da
ita, kuma ni na san ina iya bakin kokarina, ita kanta
Farida korafi take yi mani wai na hanata yinw asu
hidimomin da take son yi, kuma ba don kowa ba sai don
kada Naja'atun ta 6ata ranta, duk bata ga wannan ba shi
ne ta tafi, dole dai sai ta bata mani rai." sai yaba
Mummyn tausayi, ta rinka kokarin kwantar mashi da
hankali, ya tashi ya shiga cikin dakinshi ya kwanta kan
gado, abincin da bai ci ba kenan, ya rinka neman layinta
amma shiru ta rufe wayar ya shiga rikici sosai, mata
fitina ne, idan ba ka da isasshen tunani sai su haukataka.
40
A can birnin Dikko kuwa, Naja'atu ta isa gida
hankalinta kwance, cike da farin cikin ganin 'yan'uwanta
da iyayenta, Inna kuwa mamaki ta yi ta ce "ku da ku ke
shirin yin biki, kuma kika taho."?" Ta yi murmushi ta ce
"Ai zani kuma ne kafin ranar bikin shi." Shi kuwa
Malam Abdu murna ya rinka yi yana yi ma Hajiya
Halima addu'a, kan daukalr zumuncin da tayi, wa zaya
ga Naja'atu ya dauka diyar talakace Masinja kamarshi,
gaba ki daya rayuwarta ta canza tayi clean ta.goge, sai
kace tana rayuwa a Turai, Naja'atu ta kawo sakon
Hajiya ta basu, sannan itama ta kara masu da nata,
sauran kannenta ma kowa kudi ta bashi ta ce su yi
dinkunan Sallah ta hutar da Baba, Malam Abdu ya rinka
godiya yana sanya albarka, tare da addu'ar fatan Allah
ya dawo da wannan yaron yaga auren Naja'atu babban
burinshi kenan.
Da daddare da ta bude wayarta, sakonnin text na
Daddy su ka ringa shigowa babu adadi yana yi mata
korafi, ta rinka karantawa tana girgiza kai, sai ta saukar
da ajiyar zuciya ba ia goge ba ta bar su sunyi waya da
Khalid, ta sanar dashi tana Katsina. Ya ce "Katsina
kuma? Kuna shirin biki za ki tahe, gaskiya baki kyauta
ba." Ta ce "Insha ABanu zani koma kafin ranar bikin ina
son in karbi takarduna is makaranta, tunda na samu
dama." Ya ce "Wannan na yana da kyau, sai dai ya dace
ki koma ayi bikin nan dake, ka dafa ki ja Daddy ya ce ba
zaya halarci namu bikin ba idan lokaci ya yi, sai dai ki
bi a hankali kada ki rinka zuba bikin ba idan lokaci ya
yi, sai dai ki bi a hankali kada ki rinka zuba kwalliyar
41
nat ta ki mai daukar hankali kije wani ya janye mani
ke. la yi dariya ta ce "shi kenan sai in rinka sanya
mkab, babu wanda zaya ganni." Ya rinka dariya ya сс
"A'a, abun bai yi zafi ba har haka, ki dai kebe kanki ne
kawai, kada ki shiga in da maza suke da yawa, ke don ba
ki san yarda kike ba ne, kina da wasu qualitics na
musamman dake saurin jan hankali da namiji gare ki, ba
kowa ne zaya iya yin hakuri da ke ba, don haka ko aure
muka yi gaskiya hijabi za ki rinka sanyawa dogo, har da
nikab, amma a cikin gida sai zuge mani harda belt ni
zani kalla."
Naja'atu don datiya har ta na kwarewa, kishin
Doctor ya yi yawa, sai taji ta kara sonshi, a ganinta so ne
ke kawo kishi, Allah ya bata ikon sonshi irin yadda yake
sonta. Suna gama magana ta rufe wayar baki daya, ba ta
son Daddy ya kirata. To sai dai da ta kwanta sam ta Kasa
barci, ta na tunanin Daddyn kowane hali yake cıki? Kila
ma yana can yunwa tana damunshi ta sanshi ua
shagwaba komi sai ta yi mashi, abinci warnan baya iya
ci sai ta zubo mashi kuma ta zauna tare dashi idan ba
haka ba sai dai ya zauna da yunwa. "Amma da ta tuno
Farida da shiryc-shiryen auren sai zuciyarta ta raya mata
cewa kilama yana can tare da Faridar ya manta da ita
yana ta harkokinshi. Ta runtse idanuwanta təna jin kishi
matsananci, ta rinka tunani iri-iri cikin zuciyarta, a haka
barci barawo ya yi awon gaba da ita.
Washe gari da wuri ta yi shirin tafiya F.C.E don ta
kammala takardunta, saboda halin rayuwa a kalla ko dai
ba za ta yi aikin ba, ya zaınto tana da takardun ta a
42
hannu. Sai yamma ta dawo gida, amma cikin sa'a ta
kammala komi, hankalinta ya kwanta da Baba ya dawo
ta kai ma shi takardun ta ce ya aje mata su hannunshi'ya
duba ya na sanya mata albarka, zuciyarta ta yi fes, tana
jin dadin zama cikin 'yan'uwanta duk ta manta da wata
damuwa, ta na kokarin yakice Daddy a ranta, ko da safe
ta kira Mummy sun gaisa ta rufe wayarta ba ta kira
Daddy ba, kuma da ta son shima ya kira ta. Haka ma da
daddare ta sake kiran Mummy ta na son matar ta yi
kewarta, Mummy ta sanar da ita Zainab ta iso, don haka
taba Zainab din wayar, ta karba tana yi ma Naja'atun
korafin ba ta kyauta ba, da ta taho, gashi yanzu ta isa,
gidan ya yi mata shiru ba ta da abokiyar hira." Naja'atu
dariya kawai ta yi mata yayin da Zainab din ta rinka yi
'mata magajiya akan ta daure ta dawo ayi komi gabanta,
ta ce "Idan kuma ba za ki dawo ba saboda ni, da
Murimy, to ki dubi girman Allah ki dawo, Daddy ya
shiga damuwa sosai, ko abinci ba ya ci sosai, ko magana
aka yi mashi ba ya tankawa, wallahi Naja'atu Daddy ya
na sonki ni kam na yarda da haka, don haka ki dauka
aurenshi da Farida wata kaddara ce rubutatta babu
wanda ya isa ya hana, kuma kema zaya aure ki. Allah ne
ya kaddara cewa ita ce matarshi ta farko, dole haka
za'ayi."
Naja'atu ta yi murmushi kawai, ita tasan abin da
take da hangowa, Daddy ba ajinta ba ne, ya wuce da
iyawarta, don haka yanzu ba ta da sauran wani abun
akanshi, to sai dai da ta kwanta cikin dare ta kasa barci,
ta rinka auna matsayin kaunarshi a zuciyarta, tabbas in
43
har ta ce zata iya rabuwa da Kaunar Daddy ta yi karya,
Kaunarshi a jininta take madadin tayi sauki kullum Kara
ruruwa ta kec yi, ya ta iya da rayuwarta? Ta rinka tariyo
kalamanshi masu sanyi da yake fadi mata, sai ta rinka
jin tausayinshi, tana tunanin halin da ya ke ciki, kwatakwata kasa runtswa ta yi, har safe.
A can shima Daddy kusan kwanan zaunen ya yi,
da farko yana ganin laifin Naja'atun akan abin da ta yi,
kuma ta rufe waya ta ki saurarenshi to amma cikin dare
da ya rinka auna komi sai ya samu kanshi da jin
tausayinta, ya sani Naja'atu na kaunarshi, dole ne ta
shiga kowanc irin hali, yanzu tana can cikin damuwa,
kamar ya bude ido ya ganshi Katsina, duk irin yarda
yaso ya samu kwanciyar hankali abun ya faskara, ba
zaya iya jure ma rashin ganin ta ba na wani lokaci, dole
ne ya dauki mataki. Har safe ya na kwance cikin daki,
ya fara hutun shi na sati biyu da ya dauka tunaninshi
guda yarda zaľayi Naja'atu ta dawo.
Karfe tara daidai ya tashi zaune yana wani tunani,
sai ya mike da karfinshi ya fada kewaye ya yi wanka ya
fito ya yi shiri da kananan kaya shudaye, ya jawo
dirowa da yake ajiyar kudi ya cika aljihunshi ya dauki
makullanshi da waya ya fito. Babu kowa cikin falon, ya
isa ya kwankwansa kofar Mummy, sannan ya tafi falo
ya zauna, jim kadan sai gata ta fito tana kallonshi tasan
cewa babu lafiya, ta zuba maşhi ido ta ce fita zaka yi
ne?" Ya cc "Katsina zani je." Cike de mamaki ta rinka
kallonshi, ta "lafiya.?" ya ce "Zani je in taho da Naja'atu
ne, in ba ta dawo ba, hankalina ba zaya kwanta ba." Ta
44
vi murnaushi ta zauna tana kallonshi ya ce "Amma ai da
kayi hakuri ya kwanta da kaina zani tura a dauko ta."
Ya saukar da ajiyar zuciya ya na kallonta ya ce
"Mummy bari dai inje, ko ba za ta taho ba idan dai na
tabbatar babu komi sai in barta." Mummy ta jinjina kai
ce "To shi kenan, Allah ya kiyaye hanya, Aliah